Dena Kulani Hausa Novel Part 1
Dena Kulani Hausa Novel Part 1
*GWANDOU* ..1
_©2022._
*DENA KULANI* .
_Page._ 1
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ .
“`DEDICATED TO MOMMAH..“`
••••••••••••••
*IBRAHIM ALI WAKKO PALACE* …
Matashiyar budurwa ce zaune a ɗaya daga cikin manya royal chairs ɗin da ke zube acikin haɗaɗɗen parlourn, kishingiɗe take a ɗaya side ɗin kujerar da take zaune, hannun ta ɗauke da wani book da alama shi take dubawa.
Zirrrr-zirrrr! Kukan da wayarta keyi shine ya mayar da ita daga duniyar littafin da tafaɗa, hannu ta miƙa ta ɗauki wayar haɗi da ɗaurawa a kunnen ta.
“Na’am Khadijah, lafiya ƙalau nake kamar ke, bansan me ta cikin wayar ta gaya mata ba naga ta zare idanuwa haɗi da xabura tare da faɗar yaushe?
O.ok-ok bari nayi sauri Nima aduba min tawah”.
Saurin ajiye wayar tayi agefen kujera saura ƙiris ta faɗi,batama lura ba saboda tsananin saurin da take zabgawa.
“Ummah-ummah! Wa’ec tafito wallahi Ummah exam ta fito”, take ta faɗa ba ƙaƙƙautawa.
Ganin wanda yake zaune a gefen Ummah da gani suna tattauna wata magana mai muhimmanci ne, yasa ta fara tattnatsuwar ta.
Kallo na nakai gun wadda take kira da Ummah nayi,Masha Allah wata matashiyar matace Zaune a saman sallaya yayinda wani matashin saurayi yake zaune a gefen ta kallo ɗaya zaka yi musu ka gane cewa dukan su jinin Fulani na yawo a jikinsu.
“Lafiya oum-salmah kike min wannan kira kamar zaki ƙara Arar baki,meya faru” Ummah ta ƙarasa faɗa tana mai zuba mata idanuwa.
Ganin yanda tayi tsuru-tsuru da idanuwa ne yasa Ummah girgiza kai haɗi da kallon saurayin dake zaune a gefen ta wanda shima ya zubawa Oum-salmah idanuwa yana mata kallon mamaki janye idanuwan ta tayi daga kansa tare da faɗar Abdul…na’am Ummah…kaje ta baka cards ɗinta na wa’ec aduba mata, dan nasan idan nace sai gobe yarinyar nan bazata samu baccin kirki ba.
Littafan Hausa Guda 1000 Download
Ok Tauyayi, ke.. je…..maganarsa ce ta maƙale ganin yanda tayi wata sufa kamar fatalwa, kasa rufe baki yayi saboda ganin ikon Allah, murmushi Ummah tayi tare da faɗar “Allah ya shirya ki Salmah”da Ameen yaah Abdul ya amsa dan tana buƙatar addu’ar.
Shigowar tane yasa Ummah ƙara Binta da kallo haɗi da haɗar”kifayi a hankali,duk kinbi kin susuta kanki… Uhm!!”Tauyayi”
Ummah Salmah ta ƙarashe faɗa idanuwanta na cikowa da hawaye.
Miƙawa Yaah Abdul slip ɗin tayi haɗi da faɗar”Please yaah Abdul dan Allah kayi sauri…ɗagowa yayi tare da hararar gefen ta haɗi da faɗar matsamun aka kada kifaɗa akaina, dan nalura kinyi loosing control ɗinki, saura balance.
Tura baki tayi tare da komawa gefen Ummah ta zauna,…zaro wayarshi yayi daga cikin aljihu, ganin ya fara duba slip ɗin tata hakan ya tabbatar mata da cewa acikin wayarshi zai duba mata,nan take kuwa jikinta ya ƙara tsuma,Rufe idanuwan ta tayi tare da cusa fuskarta a tsakanin cinyoyin ta, addu’a kuwa babu kalar wadda bata jawowah amma kowacce daga tafara daga tsaka sai kuma tafara ta kasa ƙarasawa…wannan shi ake kira da Anxiety.
Yes..yes..yes! Jin irin yanda yaah Abdul keyi shine ya mayarda ita a hayyacinta,saurin miƙewa tayi kamar zata kife ta ƙarasa gunshi…zubewa tayi dai-dai ƙafafun sa tare da tambayar sa”menaci yaya,menaci? Nasamu?…kin samu sister,kinsamu gaba ɗaya B, zaro idanu Ummah dake gefensu tayi tare da faɗar B, fah kace Abdul …kuma gaba ɗaya?
Ɗagowa yayi daga inda yake zaune tare da nunawa Ummah fuskar wayar tasa, Masha Allah Ummah tafara faɗa haɗi da fara shafa kan Salmah da tayi relax a gefen ta.
Bari naje a fito mata da ita faɗar Abdul yana mai miƙewa tsaye dan barin ɗakin murmushi ɗauke saman fuskar shi,iyye Salmah yar jami’a yafaɗa yana mai barin ɗakin.
Ɗago kanta tayi tare da faɗar Ummah Abba zaiyi farin ciki koh?…ehh mana kin taɓa ganin ubanda ƴarshi zata samu alkhairi yaƙi farin ciki?,jinjina kai tayi tare da faɗar nakusa zuwa higher school hmmm! Waya ganni…
………..
*AMBASSADOR ABDULLAHI SHAMS P.*
°°°°°°Ma’aikata ne zube acikin harabar gidan,yayin da kowa yake kan aikin sa duk da kasan cewar magrib ta gabato…wani kamtamemen gida ne wanda kallo ɗaya zakayi masa kagane cewa lallai duniya ta zauna a hannun masu gidan kuma har ila wayau suna kan jin daɗin su.
…fihh..fihhh horn ɗin da naji anyi shine ya mayar dani ga kallon hanyar katafaren get ɗin gidan wanda kusan masu gadi har biyu ke fakon shi da kuma ƙoƙarin buɗashi idan har ɓuƙatar hakan ta kama.
Wata dalleliyar farar mota ce ƙirar “Toyota Camry 2020, ta Kunno Kai acikin filin harabar gidan yayin da wani zazzafan sauti ke tashi acikin ta.
Masha Allah wata matashiyar budurwa ce ta fito daga cikin motar wadda aƙalla shekarun ta bazasu gaza sha tara(19) ba aduniya, sanye take da riga da wando waɗanda suka kama jikin ta sai kuma after dress data ɗora saman tufafin wadda taji aiki da jajayen stones, zan iya cewa itace abunda ta taimaka wajen rufe ƴan madaidaitan mazaunan yarinyar.
Ɗaya ƙofar motar naga anƙara buɗewa yayin da wata yarinya ƙaramar wadda shekarun ta bazasu wuce 6-7 ba aduniya da fito daga ɓangaren, latsar wayar dake hannun ta take yi hankali kwance ba tareda wani damuwa ba…El~herm kenan ƙarama,ɗiya ta Shida kuma last born, agidan ambassador Abdullahi shams.
Wani ma’aikaci ne yayi saurin ƙarasowa gurin su,..cikin girmamawa yake gaida babbar wadda ake kira da Ameerah”Barka da dawowa ranki ya daɗe” ɗago idanuwa tayi tareda barin kallon wayar dake hannun ta, yawwa tafaɗa tana mai janye jikin ta daga gun motar da take jingine, keys ɗin motar ta cilla mishi tana mai juyawa haɗi da faɗar “Na Manzo, komai abishi bisa kan tsari, yanda aka saba ba abinda yake haɗe komai a ware yake ok.
An gama ranki yadaɗe yafaɗa yana mai saurin juyawa domin cika umarnin hajiyar sa.
……da sallama ɗauke a bakin ta tashiga babban parlour nasu,wanda a kallo ɗaya zaka iya kwatanta shi da aljannar duniya…ɗauke yake da kayan alatu na morewa rayuwar zamani, Masha Allah tsayawa bayanin ɓata lokaci ne, amma zaku iya kwatanta wa..iya tunanin ku..yaya gidan hamshaƙin ɗan kasuwa wanda ya mallake kamfanoni daban-daban, wanda kuma yake da hannun jari da ƙasashe da dama A faɗin duniya,shin ya muhallin shi da kuma iyalan shi zaku kasan ce?.
Wata ƙofar naga ta nufa inda Ni kuma na rufa mata baya domin ganin inda ta dosa.
Sallama ta ƙarayi a karo na biyu tareda ƙarasawa cikin madaidaicin parlourn wanda a yake ɗauke da wasu Italian chairs set ukku…, Wai ku bakwa jine sai faman sallama nake yi kun wani shareni…to mu ina mukaji cewar Shemaah, Shema’u itace wadda Ameerah take bima a shekaru.
“toke Malama waya kasa dake ne balle ki ɗauka..wama ya kawo ki gidan nan yanzu?…uhmm! so gida sai kace ba satin can kikazo ba, mtssww.
Mayarda kallon ta tayi gun babbar yayarsu Balkisu wadda itace ɗiya ta biyu agurin Hajiya na’eemah da kuma Ambassador Abdullahi shams, Ah aunty bilki yaushe a gari,zuwa haka ba sanarwa?…to uwata yi haƙuri kinji..nayi kuskure ban nemi izinin kiba da yake igiyar auren nawa a hannun ki take ko?..kai aunty me yayi zafi haka, Allah ya huci zuciyar ki..ta ƙarashe faɗa haɗi da zama a saman ɗaya daga cikin kujerar parlourn.
*(ASALIN IBRAHIM ALI WAKKO* )
~~mahaifin Alhaji Ibrahim haifaffen jihar Borno ne wanda ya tashi yana rayuwa acikin mai duguri,tareda matarsa da kuma ƴaƴansa ukku mata biyu da kuma namiji ɗaya, Hindatu, Ummu Salamah da kuma Ibrahim.
Alhaji Ibrahim sun tashi cikin gata da kuma jin daɗi,da yake mahaifinsa mutum ne shi mai neman na kanshi da kuma jajircewa wajen biyawa iyali buƙatun su gudun faɗawa halaka.
Duk da kasan cewar mahaifin Alhaji Ibrahim baiyi boko ba amma ya ginu da burin saka nashi iyali don kaucewa jahilci da kuma neman madafa dan ba’a san me gobe zata haifar ba.
Cikin ikon Allah kuma,sai ya sami iyali jajirtattatu masu buƙatar ilimi, acikin ƴaƴan nasa daya mallaka ba bora afagen ilimi,tun daga fannin arbiya har kan ilimin zamani (boko).
Hindatu itace babbar, sannan Ibrahim sai kuma ƙaramarsu wato Salamah,sun tashi cikin soyayya da ƙaunar juna..haka dai rayuwa taci gaba da tafiya yau daɗi gobe a kasin hakan, bayan jan wasu shekaru kuma, sai Allah ya ɗauki rayuwar Alh Ali wakko bayan ya aurar da ƴaƴansa mata, a inda shi kuma Ibrahim yake a mataki na biyu a jami’a…mutuwarda ta taɓa iyalinsa da kuma maƙota tareda ƴan uwah na nesa dana kusa.
Kasancewar a lokacin boko kamar a kyauta ne, sannan ba kowa yake yin shiba saboda suna mishi wata mahanga ta daban yasa Alh Ibrahim yasamu damar cigaba da karatun sa tareda taimakon wasu wakilai na makarantar su ba komai kuma ya jawo hakan ba sai dan kasancewar sa ɗaliba mai ƙwazo.
Haka dai rayuwar taci gaba da tafiya yau daɗi gobe akasin hakan har zuwa lokacin da ya kammala karatun sa,a sannan ne kuma ya samu yarinyar da yake so har soyayyar takaisu da aure… To masu karatu karku shagala labarin mu yafara ne A gidan Alh Ibrahim Ali wakko, a inda yanzu yake tareda matar sa da kuma ƴaƴan sa biyu da Allah ya mallaka masa, a yanzu haka yana aikin gwamnati (civil servant) a inda yake da babban muƙamin permanent secretery of finance…
**ASALIN*
( *AMBASSADOR ABDULLAHI SHAMS* .)
_to be continue_ …
🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*©GWANDOU.*
[11/10, 8:36 pm] +234 814 290 4255: 🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU* ..
_©2022_ .
*DENA KULANI* .
_Page.2_
*ASALIN*
( *AMBASSADOR ABDULLAHI SHAMS* .)
…Mahaifin Ambassador Abdullahi haifaffen jihar Kano ne,a inda mahaifiyar sa take ƴar asalin ƙasar Niger a garin agadaz,.. dangin ambassador Abdullahi masu arziƙi ne,yayin da wasu ma suka ce sungadi arziƙi tun daga kakannin ka kanni.
Ambassador Abdullahi shams ya gadi arziƙi ta uwa da uba dan kuwah ko dangin mahaifiyarsa ba baya ba wajen dukiya, suna cikin jerin masu arziƙi na farko a ƙasar niger.
A yanzu haka ambassador Abdullahi shams,babban ɗan kasuwa ne wanda sunan sa yazagaye kaff, ƙasashen duniya,yake kuma da hannayen jari a ƙasashe da dama.
Yanzu haka yana tareda mahaifiyarsa da iyalinsa a garin Abuja Nigeria,.. ƴaƴansa shidda (6)maza biyu mata huɗu,Balkisu Al-ƙasim, Muhammad, Shema’u, Ameerah,sai kuma El-herm.
Matarsa Hajiya na’eemah bata ga maciji da talaka ko ƙadan, wannan aƙidar Tata itace ta zauna ajinin ƴaƴanta mata musamman balki da Shema’u dan ita ameerah hankalinta bai zaunu ba kuma yawancin zamanta a gurin kakarta take yinsa saboda basa wani shiri da mahaifiyarta…ba komai ya jawo hakan ba kuwa sai ɗan banbancin halayyar da suke dashi a tsakaninsu.
*CI GABAN LABARI* …
…Matashin saurayi ne zaune akan dining, dogo ne fari tass, sanye yake da shadda kaftan ruwan zuma,wadda ta ƙawatu da aikin brown ɗin zare.
Abincinsa yakeci hankali kwance batare da wata damuwa ba yayin da yake aiki da wayar shi murmushi ne kwance akan kyakkyawar fuskarsa,hakan zai nuna maka cewa yana wani nishaɗin ne.
Jan ɗaya daga cikin kujerin da akayi ne ya mayar dashi daga duniyar nishaɗin daya lula, murmushi ya saki yana mai ajiye wayar dake hannun shi,tareda faɗar “good morning mommy,.. murmushi Hajiya na’eemah tayi tareda faɗar “morning dear, numfashi taja sannan taci gaba da magana, meya hana Muhammad dawowah ne?hmm! Ko har yanzu yana fushi ne?.
Ajiye cokalin dake hannunsa Al-ƙasim yayi tareda juyowa ya ƙara fuskantar mahaifiyar tasa, No mommy ba wannan dalilin bane ya hana shi dawowah ba akwai ƴan ayukkan da yake so ya kammala ne, dan har mun shirya tafiyar tare kuma sai wani aikin ya taso masa shine kawai dalilin.
Numfashi ta sauke, haɗi da kallon ɗan nata,tareda faɗar”ka tabbatar Wannan ne..ehh! Mommy…ok shikenan dama na tambaya ne dan nasan halin murɗaɗɗen halin shine.
Fitowar ameerah ne yasa suka bita da kallo gaba ɗayansu,sanye take da kayan bacci hakan ne ya tabbatar musu da cewar lokacin ta tashi daga baccin, Good morning mommy, ta ƙarasa faɗa haɗi da zama ɗaya daga cikin kujerin dining ɗin, “welcome back brother,ta faɗa tanamai fara serving na kanta… thanks sister, ya exams…kwanaki dady yake gayamun kin kusa kammala exams ɗinki.
Cokalin dake hannunta ta ajiye tareda kallon mommy sannan ta mayar da kallon ta agurin shi, wai yaya ƙasim kar-dai kacemun bakasan har exams ta fito ba, lallai kam, gashi har ameerah na batun wucewa ƙasar Paris karatu,..cike da mamaki ya furta”Paris kuma mommy, duk makarantun da suke acikin Nigeria basuyi ba har sai ta sake zuwa ƙasar waje karatu? Uhm!.
To meye aciki, naga dai kaima a waje kayi karatu kuma yanzu haka acan kake rayuwar ka, wani abun yasa meka ne?…naga dai acan tayi secondary school gashi kuma ta gama lafiya ƙalau dan haka kar nakuma jin wannan maganar.
Nifa mommy a naija zanci gaba da karatu na, dan haka karma ki kawo min wani zance dan nagaji da rayuwar can… rayuwar doka anan kawai zan cigaba da karatu na, tomm.
Faɗar ameerah tana mai cigaba dacin abincin ta hankali kwance ba tareda tasake cewa komai ba…bazakiyi anan ba nace, bazakiyi ba dole kije ƙasashe masu cigaba kiyi karatu hankali kwance,kai kuma idan har bazaka goye bayan taje waje karatu ba na fitar dakai acikin maganarr…buga teburin da akayi shine ya dakatar da’ita daga ƙarasa maganarta.
Dakata Malama,shin dakike wannan maganar karatunki ko nawah,haba dan Allah karfa kiso ki takurawa rayuwata yanzu fa nakai matakin da zan iya yanke wa kaina ehh! Ko a’ah! So be careful ok.
Juyawa tayi cikin fushi,cike da sassarfa take taka matakalan da zasu fitar da ita daga dining ɗin kamar zata tashi sama.
Ruwan da Al-ƙasim ya miƙa mata sune suka mayar da’ita daga nisan da tayi,ajiyar zuciya take ta saukewa ba ƙaƙƙautawa.
Kinga illar fitar da’ita wajen ko?,..yanzu mommy ki duba fah kigani secondary kawai tayi a ƙasar London amma ki dubi idanuwan ameerah yanda suka dawo tsakiyar kai, batajin maganar kowah..idan zaki yarda da magana ta mommy yanzu haka ameerah tanashan ƙwayoy…whatttt!!..mekake shirin faɗa ne ƙashim..kafita daga hankalinka ne? Kodai kafara ƙiyayyar ƴan uwanka ne? Ƴar tawa?..calm down mommy..bafa nafaɗa danki tayarda hankalin ki bane, kawai dai abinda nake hasashe ne ok.
Kaci ƙaniyar ka dakai da hasashen, Ni banyi shashanci da kuruciya taba,dan haka bazan haifi ƴan iska ba..sorry mommy.
Kwafa tayi sannan taci gaba da faɗar” Bama wannan ba..kunyi magana da hajjoo (balkisu)?..kallon ta yayi cikin yanayin dake nuna mamaki sannan yace” bayan gaisawa kuma akwai wani magana da zamu tattauna da’ita ne?…ok kenan bata gaya maka komai ba..ehh! Nikam ba abinda muka tattauna..but tunda gaki kuma ina ganin abu ɗayane kifaɗamun kawai ok.
“Bari nazo” faɗar mommy tana mai mayarda hankalinta gun wayar ta.
“Hello,..hajjo kisameni a dining area yanzun nan kinji.
Ajiye wayar tayi tana mai ƙara fuskantar sa…Uhm! Ya ayyukan naku daddynku ya gaya mini cewa abubuwan sai gaba suke Masha Allah..
ehh! Alhmdllh gaskiya komai yana cigaba da tafiya da kyau, yanzu haka Ni ina ƙoƙarin zuba hannun jari da wasu kamfanoni da suke a ƙasar _england_ da kuma _Paris._ .”wow that’s my son” faɗar mommy tana washe haƙora.. lallai yarona ya zama babban mutum.. Muhammad fah..mug ɗin da ke gefen shi ya jawo tare da ɗaukar ƙaramin cup ɗin dake gabanshi, tsiyaya lemon dake ciki yayi sannan ya ɗago..no mommy kinsan fah my bro bayason ana fallasa mishi secret then,yafiso yafaɗa da kanshi,so kijira dawowan shi..zai gaya maki komai about him ok.
Al-ƙasim!..takira sunan shi tana mai kafeshi da idanuwa…”Yes mom”yafaɗa cike da sakalci,..gayamun me Muhammad yayi achieving banason shashanci..kodai har yanzu yana tareda damuwa ne.. Please ƙasim karkamin ƙarya.
“Hhhh” best mommy in the world..ok ƙasim dariya ma nabaka..no sorry mommy..kawai dai inaso kigane cewa Muhammad fah yayi forget da komai ya kama aikin shi,..tunda kuka nuna bakwason yayi aikin lafiyar ya tattara ya watsar,..yanzu haka Muhammad ƙasa biyu sukayi masa request na haɗa hannun jari dasu.. _Qatar_ da kuma _U.k_ sannan kuma ya kammala ginin babbar University da yake yi a ƙasar nan kuma acikin garinnan na Abuja..wadda take ƙunshe da fannoni da dama.. sannan yananan yana nema mata greatest teachers daga ƙasashen waje har nan gida Nigeria..sannan makarantar tana ɗauke da special and desirables men and female hostels..so calm down mommy your son’s wanna be famous of the world.
“Wow!Alƙasim ka faranta mun rai ba kaɗan ba,ina alfahari daku ta ƙarashe faɗa tana mai murmushi irin na ƙasaitattun matan nan,to maganar aure fa,Kanada wadda kake nema ne?
Gaban sane yayi wani dukan ukku-ukku,cike da gargada ya fara faɗar,
“mom..mom..Ina..da but..ƙarasowar Hajjo gurin ne ya katse mishi maganar da yake kanyi.
Barkan ku da hutawa hajjo ta faɗa tana mai ƙoƙarin zama…tsayar da’ita mommy tayi ta hanyar cewa”no hajjo muje can cikin parlour dan maganar bata nan bace,kinsan ƙannan naki sai nayi da gaske..naji yafara kawomin zancen yanada wata..muje naji ƴar waye acikin ƙasar nan.
Dariya hajjo ta saka tana mai kallon ƙasim da dayi wani kalar tausayi duk jikinsa yayi sanyi,gaba mommy tayi tana mai faɗar “hajjo!..jawomin kan ƙanin nan naki nayi dashi yanxun nan.
“Oya tashi muje mana”cewar hajjo tana mai ƙoƙarin jan hannun shi,ɗan ɗagowa yayi tareda leƙawa ta bayanta ganin mommy tayi nisa ne yasa ya mayarda hankalin shi gurinta tareda faɗar”Please sister ki taimakeni da wannan alfarmar,nasan mommy na ɗaukar shawarar ki sosai idan kinka bata shawara zata ɗauka kinji..wai menene kaketa wani magiya kaje kai tsaye ka gayan abinda kake so mana.
Wayarshi yayi saurin jawowa.. buɗe ta yayi tare da shiga cikin galleries ɗinsa,hoton wata yarinya ya shiga tareda mika mata wayar.
Wow! Wacece wannan, tanada kyau.. murmushi ƙasim yayi tare da jinjina kai,”but who’s her father? Faɗar hajjo tana mai tsura mishi ido.
ya mutse fuska yayi tare da kallon ta.. menene kuma na wani tambayar babanta.. tambaya nayi dan nasan ƴar gidan waye..”to sannu mommy.. ahh..sannu tunda haihuwa na kikayi da zaki wani tsureni da tambaya,barima kawai na gaya maki ita ba ƴar kowan kowa bace,..abinda nasani kawai su talakawa ne..babanta babban malami ne a garin su..daga ƙarshe abunda zan gaya maki shine itace matar da zan auraah…
Idanuwa hajjo ta fitar waje haɗi da faɗar”whatt”…..
🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU* 😍
Leave a Comment