Hausa Novels

Dinyar Makaho Hausa Novel Complete

Dinyar Makaho Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Dinyar Makaho Hausa Novel Complete

*Gargaɗi*:

Ban yadda wani ko wata ya juyamin labarina ta fuskar da bata dace ba,wannan littafin mallaki nane don haka a kiyaye.

Dinyar Makaho

*SADAUKARWA:*

Wannan littafin sadaukarwa ne ga uwayen ɗakina guda uku.

 

1-Hassana ɗan larabawa

2-Nabila dikko

3-Nabiha Aminu.

4-Bintu Umar Abbale

 

Allah ya ƙara muku lafiya da kaifin ƙwaƙwalwa da kuma basira.

 

*GAISUWA:*

Ina gaida masoya na ni ummu maher(miss green)aduk inda suke ina gaida marubuta baki ɗaya.

———–

 

*BismillahirRahmanirRahim*

 

1-2

 

*Noor pov*

———————

 

. . . . . .A hankali nake tafiya ina hawaye,na kalli kayan jiki na duk sun ƙoƙe sun lalace uniform ne na ƴar makarantar secondary,sai dai ina da tsafta sosai badon tsaftar dana ke dashi ba,da babu abinda zai hana munin uniform ɗin.

 

Jakar hannuna ma irin ta leda ce duk ta yage,kana i’ya hango ƴan tsurarun littattafan dake ciki waɗanda baki ɗayansu basu fi guda biyar ba.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Sandal ne a ƙafa ta wanda shima ya gaji da siɗewa,nacin son makarantata shine yasa har yanzu ban dai na zuwa ba,amman kullum cikin zagi da tsangwama nake awajen ƴan makarantar mu.

 

 

Ni Noor na yabi kai na,saboda ni ba ƴar kowan kowa bace amman ina da kyau na nunawa sa’a.

Fara ce ni ƙal,ga dogon hanci,ƙaramin baki,mantan idanuwa,gashi ma ina dashi don har yankeshi nake.

 

 

Mutane da dama suna tankani akan kyaun dana ke dashi,sai dai ni ɗin malama ce ta fannin addu’ah.

Don bana taɓa zama ba tare da azkhar ba,tun ban kai ko’ina ba nake sanye niƙab da hijabi.

 

Ba na taɓa saka mayafi in fita,kullum hijabi nake sanyawa in fita. Kuma idan ma na ce zan saka mayafin ina na gansa,ni a wancen ƙarnin na ɗauka wasu ƴaƴan masu gata ne ke sanya shi,amman fa ni baya burgeni sam don mayafin baya cikin tsari na.

 

 

Makarantar na da nisa sosai da gida,haka kuma nake takawa inje,ƴaƴan gata kuwa sai dai a basu kuɗi su hau abin hawa.

Amman ni ko da wasa ma ban taɓa tambayar kuɗin ba,tunda nasan ba samu zanyi ba.

 

 

Shiyasa sai inyi daɓe kullum,har in isa makarantar don ni bani da wannan gatan.

Ina zuwa kai tsaye na tsaya wajen da ake assembly.

Duk kunyar kai na ta ishe ni,saboda yawancin ƴan matan duk uniform ɗinsu sabbi ne,idan kuma ba sabo bane to bai wani sha jiki ba.

 

 

Amman nawa duk ya yage,yasha manni da kuma fa-ci ga uban humra dana shafa me ƙamshi sai ka ɗauka uniform ɗinma sabbi ne.

Ƴan matan sai kallo na suke suna harara ta,wasu ma har toshe hanci suke wai wari nake.

Duk abinda suke ban taɓa tanka musu ba,amman tabbas abin yana cin zuciyata sosai amman tambayar dana ke yiwa kai na bai wuce,yadda mutane basa gane da arziƙi da rashinsa duk na Allah ne ba.

 

 

Sunfi son suga ne kuɗi nan zaki ga suna rawar ƙafa da rawar kai,amman ni a tsarina nafi son kasancewa ta ahakan,don haka jalla rabbi yaso ya ganni.

Ni shugabar makaranta ta wakilta don yin addu’ah,don haka na fito na fara rero addu’o’i kamar wacce aka yiwa wahayi.

 

 

Sannan na rufe da suratuk fatiha,wanda na rera ta da sanyayyiyar murya ne daɗi da taushi.

A nitse na yi karatu na,ya tafi da ɗibban jama’a don na iya karatu sosai ga ilimin addini har dama na boko ɗin.

 

 

Ni ce nake zuwa ta ɗaya acikin ajinmu,haka ma islamiyya har musabaƙar alƙur’ani me girma nasha cin ta.ayanzu ma haka an saka sunana a cikin gasar alƙur’ani me girma na ƙasa.

 

 

Ina komawa gida gabana ya fara faɗuwa sosai,don daman sabo nane matuƙar na fita to idan zan dawo sai naji gabana yana faɗuwa.

Ko don yanayin gidan namu ne oho?ko kuma saboda tsabar tsoro nane oho?.

 

 

Kai tsaye ɗakinmu na shige,babu kowa a tsakar gidan Inna Hafsatu ta gama abin cin ranar da take yi na siyarwa.

Yaran gidan mu kuwa duka sun tafi talla,kaf gidanmu babu yaron da yake zuwa makaranta sai ni.

Nima kuma ɗin ba mahaifina ne ya saka ni ba,ƙanin mahaifiyata ne ya saka ni don yaga yadda nake son karatun shiyasa ya sakani.

Yaransa kaf makarantar kuɗi sukeyi,kuma kaf ɗinsu babu wanda ake biyawa ƙasa da dubu talatin.

Amman ni uniform dana je na gaya masa,cewa ya yi wai in lallaɓa da wannan idan zan shiga S.s 1 wato aji huɗu ya canjamin.

 

 

Ranar daya faɗamin wannan maganar ƙwana na yi ina kuka,mahaifiyata sai rarrashi na take yi wacce ke ƙwance rai a hannun Allah.

Don komai sai anyi mata,kuma ni ce ke yi mata komai har tsarkin bayan gida dana fitsari.

Mahaifiyata bata da ƙanwa mace namiji ɗaya ne,kuma shima ƙanin tane amman baya taimaka mata da komai.

 

Ina tuna wannan na shiga cikin ɗakinmu,na hangi mahaifiyata tana cen gefe ƙwance,da alama ma ta yi wani abune a ƙwance kuma ta rasa yadda za ta yi.

Na goge hawaye na na ƙarasa kusa da ita na ɗago ta,ina kuka sosai ta ɗan shafa kai na tana ɗan murmushi wai duk don in ƙwantar da hankalina.

 

 

Amman ina kuka yaci ƙarfina sosai,na rungume ta na fara kuka me tsuma zuciyar me sauraro.

 

 

Ahankali ta fara magana bakinta yana kakkarwa ta ce.

 

 

“Haba Noor bana son kina kukan nan don Allah”.

 

Ɗan murmushi nayi wanda masu iya magana suka ce yafi kuka ciwo,sannan na ce”haba umma ya zama dole in damu fa,shiyasa nace miki ni gwara in daina zuwa makarantar nan,tunda babu wanda zai iya kularmin dake.”.

 

Ina faɗar hakan na fashe da kuka me mugun ciwo.

 

Kallona mahaifiyata take,sannan ta saka tafin hannunta ta fara sharemin hawaye,duk jikinta ya yi sanyi itama.

 

Ta rungumoni sosai ajikinta,tana kuka har ruwan hawayenta na taɓa bayana,sai naji zafin hawayenta tamkar zafin ruwan zafi me tafarfasa zuciyar duk wani bil’adama.

 

“Ya isa kukan haka uwata kinji?bana son kina yawan kuka a shekarunki bai kamata kina shiga irin waɗan nan tension ɗin ba”.

 

“Hmm umma kenan kada ki damu,na riga dana saba da komai wallahi ke dai addu’ah ya kamata ki bini da i’ta sai kiga rayuwata tana albarka.”

 

Shafo gefan kumatuna tayi sannan ta ce”to Allah ubangiji ya yi miki Albarka uwata ya baki miji nagari abin son kowa,me tausayinki akoda yaushe ko da kuwa bayan rai na ne”.

 

Da sauri na kalleta wasu hawayen suka ƙara wankemin fuska sannan na ce”Umma!don Allah ki daina yawan zancen mutuwar nan baki ɗaya zuciyata bata yimin daɗi,please don Allah Umma”.

 

Na faɗi hakan ina fashewa da kuka,Ummana ta ce”Allah sarki Noor mutuwa ta zamar mana dole,ko da cuta ko babu cuta idan mutuwa tazo dole ne ta ɗaukemu,don haka ki cire komai aranki ko da na mutu,ki yi rayuwarki cikin farin ciki,domin ni nasan Allah bazai taɓa tozarta ki ba,yadda na taso bansan iyaye na ba,bansan daga inda nake ba haka na taso cikin rayuwar ƙunci da nadama,na fara tunanin canjin rayuwa sai kuma na haɗu da namiji maras imani,wanda a kullum bai wuce yaga ya ƙonamin rai ba,haƙiƙa duk macen da ta dace da samun namiji nagari ta more rayuwarta duniya da kuma lahira.”

 

Kallon mahaifiyata nake sosai,duk tausayinta ya cikamin zuciyata wasu hawaye masu zafi suna ta zubomin,wata irin muguwar tsanar mahaifina na ƙara ninkuwa a ƴar ƙaramar zuciya,wacce akullum bata ƙunshe da farin ciki sai baƙin ciki.

 

Na juyo muryar mahaifiyata tana ce wa.

 

 

 

“Haƙiƙa mahaifinki ya yimin ƊINYAR MAKAHO ne,ban taɓa tunanin zai juyamin baya ba,sai gashi ya juya min baya alokacin dana ke mararin kasan cewa dashi,amman ina godewa Allah daya bani ke a matsayin ƴa Noor haƙiƙa ke ƴa ce tagari,me son farantamin akoda yaushe”.

 

 

Ta shafa kai na sannan ta ce”Allah ubangiji ya yiwa rayuwarki albarka ɗiya ta”.

 

 

Ta faɗi hakan tana ƙara matseni acikin ƙirjinta tamkar wani zai ƙwaceni.

 

 

 

Haka na wanke mata jikinta tass,ina ɗan jin kunyar yin haka don ko babu komai mahaifiyata ce,aƙwai kunya a tsakaninmu amman babu yadda zanyi ƙaddara ta riga fa ta,sai haƙuri da kuma addu’ah shekara ɗaya kenan da Allah ya jarabci mahaifiyata da lalurar mutuwar ɓarin jiki,rana ɗaya akaga ta daina komai da kanta sai dai ayi mata.

 

 

Na shafa mata turare sai ƙamshi takeyi,ina kallonta ina shafa mata tana murmushi tana kallo na,duk sanda nake hidimta mata sai inga tana kallona tana murmushi,idan na tambaye ta ba’asi sai ta ce babu komai.

 

Naji muryarta tana ce wa”Oh mama na aƙwaiki da son ƙamshi Allah dai ya baki namiji me son turare sai aje ayi ta bulbulawa.”

 

Sosai nake dariya har da tuntsirawa sannan na canja kuma yanayi zuwa kalar kuka na ce”Ayya Umma ni ai na cire babin aure arayuwata,ni babu abinda na sani sai kula dake da son kasancewa dake,yanzu kuma idan nayi aure fa duk bazanyi miki hakan ba,don haka don Allah umma ki daina zancen auren nan ya riga ya wuce.”

 

Kallona ta yi sosai sannan ta ce”Emilli ni fa bana son kina haka fa?idan baki yi aure ba zama zakiyi ina kallon ki kamar tv ko kuwa me?don haka ki dai na ma wannan zancen”.

 

Ta faɗi hakan tana kallona,na yi mamakin faɗin Emilli da tayi don bata fiya faɗar wannan sunan ba,tafi faɗar Mamana amman ba ta faɗar Emilli.

 

 

Ƙwaso kayan da mahaifiyata ta ɓata na yi,Inna Hafsatu bata tsakar gida,Sai Inna Saudatu da Ƙawarta Sahura.

 

Na ɗan raɓa na wucesu zuwa wajen famfo,don yanzu ko sannu na yi mata sai cibi ya zama ƙari,don wani lokacin har gwara Inna Hafsatu da Inna Saudatu, sam ba tada tausayi da imani ko kaɗan.

 

Wata irin muguwar dariya ta kyalkyale da ita sannan ta ce”hmm ni fa wallahi Sahura ina mamakin wasu mutanen?”.

 

Sahura ta ɗanyi dariya sannan ta ce”ƙawata dame fa?”.

 

 

“Hmm da abubuwa mana,wai ace mutum ya dinga kashi da fitsari a zaune kamar wata saniya ko kuma raƙuma”?.

 

Wata mahaukaciyar dariya suka k’elƙele da ita,sukayi tafi abinsu Inna Saudatu na kallo na tana watsomin wata irin muguwar harara.

 

 

Jikina ya yi wani irin mugun yin sanyi,ban san sa’adda na saki wani irin kuka me mugun ƙarfi ba.

 

 

.i’na kuka i’na wanke kayan mahaifiyata waɗanda ta ɓata,raina duka babu daɗi ahaka har na gama na share wajen tas tas,har na ɗibi kayan zanje in shanya sai kuwa Inna Saude ta ce”Ke!kada ki kuskura ki ɗoramin wannan banzan kayan kashin a kan igiyata,idan ku kun saba da ƙazanta ato ni dai ban saba da i’ta ba,don haka maza wucemin da gani tun kafin in canja miki wannan aljannat fuskartaki.”

 

Kasa cewa uffan na yi saboda abin Inna Saude ya fara i’sata,don dai tasan ko da za tayi rawa akai na bazan ɗago in kalleta ba,shiyasa take tsokana ta salo salo,don dai in kulata wani abu ya faru ayimin wani sharrin.

 

 

Sai bayan tafiya ta Sahura ƙawar Inna Saude ta ce”caɓɓijan gaskiya wannan yarinyar idan baku tashi tsaye ba,sai ta hana yaranku aure acikin gidan nan,don haka wallahi tallahi ki tashi tsaye.”

 

Ta faɗi hakan tana wani hararar baya na,Saude Ta ce”ke Sahura ni fa ban gane abinda kike nufi ba?”.

 

 

“Hmm zaki gani yanzi kuwa,abinda nake nufi shine matuƙar maza na ganin wannan yarinyar to fa babu zaman lafiya,don baza a kalli yaranku a matsayin mata ba,aradun Allah a matsayin maza za’a kallesu,don kin san yadda wannan yarinyar take da shegen kyau kamar aljana,ga diri kamar ita ce ta ƙera kanta,don haka wallahi tun wuri ki tashi tsaye daman.”

 

Ta faɗi hakan tana kallon Saude don tajo me zata ce.

 

 

Saude ta ce”hmm kuma kin san Allah ban taɓa wannan tunanin ba?ni dai kawai wani lokacin sai inyi ta kallonta,ina mamakin yarinyar don tun tana ciki muka hanata zuwa duniya,amman kuma sai gashi tazo shiyasa ni abin yake bani mamaki wallahi.”

 

 

 

“Hmm ni dai Saude abinda zan gaya miki wallahi guda ɗaya ne,ko da kina mamaki don kin rasa yadda zakiyi da i’ta a’a baza ki barta tazo ta hana ƴaƴanki aure ba,yanzu don Allah ki duba ki gani?ga Safara’u ga Halima ga Aisha,Ga jidda duk ƴaƴanku ne kuma dukkansu babu sa’ar Noor aciki sai Jidda itama Jiddar ta bawa Noor wasu watanni don haka dai ki dage wallahi,don idan ma baki dage ba ƴaƴan Hafsatu sayi aure su bar naki azaune babu mashin shini.”

 

 

“To yanzu Saude me kike ganin za’ayi?”.

 

 

“Hmm abu ɗaya nake ganin za’ayi shine muje wajen boka,don mu amso magani akan ya sanyawa maza muguwar tsanarta ta yadda za ta rasa mashin mashini har abada.”

 

Tafi suka sanya da shewa,ni da mahaifiyata muna jiyosu acikin ɗaki,Ina jin Mahaifiyata na ce wa.

 

 

“Hmm Allah ya ƙyauta,ya shirya mana zuri’a baki ɗaya ina amfanin son duniya alhali rabuwa zamuyi da ita?ko munaso ko bama so.”

 

Na juyo ina kallon mahaifiyata,tana matuƙar burgeni don ƙwata ƙwata bata damu da rayuwar duniya ba,abinda yake gabanta shine ta bauta mahaliccinmu tamkar yana ganinta.

 

Ko da take fama da ciwo ko da yaushe acikin bautawa Allah take,rayuwarta baki ɗaya ta tafi ne a bauta.

 

Na rungumeta ina jin wani irin sanyi araina.

 

 

shafa kai na tayi sannan ta ce”wai uwata baza kije islamiyya bane?”.

 

Ɗan turo baki nayi sannan na ce”kai Umma na don Allah ki kyaleni Allah yau bana son tafiya in barki ke kaɗai,alhali babu me kulamin dake ni yanzu ma na dai na zuwa makarantar ma kawai wallahi”.

 

Na faɗi hakan cikin shagwaɓa ni daman gani auta kuma ƴar fari.

 

Ɓata rai mahaifiyata tayi sannan ta ce”haba mamana don Allah ki daina wannan zancan,saboda me zaki fasa makarantarki akaina?so kike tunda nu banyi ba kema ki taso cikin duhun jahilci ko me?gaskiya ban yarda ba.”

 

“To Umma duk abinda kike so nima inason shi,Allah dai ya baki lafiya me ɗorewa”.

 

Murmushi ta ɗanyi sannan ta ce”to Allah yayi miki albarka ƴata ya haskaka miki rayuwarki ko da bayan rai na”.

 

“Amin”.

 

Na ce ina me rashin jin daɗin kalmarta na mutuwa,duk sanda ta faɗi hakan duk sai inji babu daɗi araina amman babu yadda zanyi don nima na yadda da mutuwa ɗati bisa ɗari tunda ni ɗin na kasance musulma me yadda da ƙaddara me kyau ko mara kyau.

 

Na shirya cikin dogon hijabina har ƙasa,duk da ya ɗan sha jiki amman duk da haka ina ɗan maleji,wannan ɗin ma dana samu na ƙawata ne Hadiza don itace ta barmin shi da tayi sabon uniform,kusan shekara biyu kenan yanzu ni kuma har yanzu ba’a samu damar yimin sabbi ba.

 

Don haka nake lallaɓa abina,don masu iya magana sunce guntun gatarinka yafi sari ka bani.

 

Na ɗakko jakata na rataya,na samu humra na wanda shima Hadiza ce ta bani na bulbulashi don ni aƙwaini da wankan turare,don da ni wata me kuɗice kuɗina duk aturare zai ƙare.

 

Mahaifiyata tayi murmushi sannan ta ce”oh ni Emilli gaskiya aƙwaiki da son turare, yanzu wannan turaren da Hadiza ta baki har kin kusa ƙarar dashi?.”

 

nayi murmushi sannan na ce”hmm umma ki gane ina son turare ne wallahi”.

 

Ta yi dariya ta ce”gaskiya nafi kowa sanin hakan”.

 

Ba ɗabi’a ta ce yin ƙwalliya idan zan fita ba,don haka ko hoda ban shafa ba amman yanayin fuskata sai ka ɗauka har ƙwalliyar ma nayi yadda ta bada fashion kyau tsantsa.

 

Na yiwa ummana sallama sannan na tafi,har na ɗaga labule mama tace”ayya Emilli bakici abincin ba?”.

 

Na kalli ƙwanon da aka zubamin abinci,abincin wani ɗan tsurut dashi na ce”idan na dawo naci Umma”.

 

Tasan hali na idan nace zanci to ba cin zanyi ba,saboda haka tace.

 

“Ato ni dai gashinan duk inda zakije ki dawo kici,don kinsan yau azumi nake”.

 

Na yi murmushi kawai na tafi,don nasan tsokana ta takeyi ba wani abuba don tasan ba lallai inci ba.

 

 

ina fitowa na hangi Anty Inna Hafsatu tana abincin dare wanda ta saba yi akowacce rana.

 

Na wucewa ta don ko na gaishe tama bata amsawa,Bilkisu na gefenta ta zama kamar wata bazawara don ayanzu tana da kusan shekara talatin babu aure,abinda ta sani shine ta fice abinta kuma baza ta dawo ba,wani lokacin sai tayi ƙwana uku har sati sai ta gama yawon ta zubar ɗinta sannan ta dawo.

 

 

“Ke!”.

 

na jiyo muryar Bilkisu tana kirana cikin tsawa.

 

Zuwa nayi na tsugunna agabanta,sannan na ce”Anty Bilkisu gani”.

 

hararata tayi sannan ta ce”ke yanzu har kinyi babban ƙugun da zakizo ki wuce mu muba zauna?ni da mahaifiyata ko?saboda wannan nakasasshiyar mahaifiyar taki ta koya miki baƙin hali ko?”.

Sunkuyar da kaina na yi,kalamanta na ƙarshe da ta faɗa sunfi ƙonamin rai na,na share hawaye na sannan na ce”to kiyi haƙuri ban ganku bane”.

 

Ta zabura za ta dake ni,wani da ake kira Ali yazo siyan abinci ya ce”haba Bilkisu wannan fa bai kamata ba,kawai ku samu yarinya ku mayar da ita kamar ja. . . . .

 

 

Tun Kafin ya ƙarasa Inna Hafsa ta ce”Kai!!Ali babu ruwanka da shiga tsakaninsu wannan yarinyar da kake ganinta micijin sari ka noƙe ce,ba tada mutunci ko kaɗan ita fa ganin kanta take kamar ƴar sarkin sarauniyar kyau,shiyasa take wani haɗe fuska wai ita isashiya.”

 

 

Ali ya ce”duk da haka dai babu kyau takurawa mutum don haka gaskiya ku kiyaye”.

 

“To sannu ubana?ina ruwanka da maganar gidanmu?kada ka ƙara sakamin baki acikin duk lamurana idan ba haka ba,zan saɓa maka lamba ato”.

 

Ta faɗi hakan tana wani ya mutsa fuska,ta kalleni sheƙeƙe sannan ta ce”tashi ki bani waje banza wacce ba tada asali”.

 

A razane na juyo ina kallonta,a rayuwata babu kalmar dana tsana irin kalmar ‘rashin asali’wacce kullum suke jifa na da ita.

 

Ni dai nasan kaf ƴaƴan babanmu babu wacce tayi kama dashi idan ba ni ba,nasha tambayar mahaifiyata akan wanene mahaifina?tunda kullum sai nasha irin wannan gorin,amman amsar ɗaya ce shine mahaifina,ta kance min in kalli fuskata in kalli ta mahaifina don inga irin kamannin da mukayi dashi,idan na kalla sai dai in fashe da kuka,saboda ni ban san abinda yasa suke jifana da wannan mummunar kalmar ba.

 

Ina hawaye na wuce makarantar Islamiyya ba tare dana biyawa Hadiza ba,wanda a kullum na saba biya mata amman yau saboda tashin hankalin dana ke ciki yasa kawai na wuce.ina jin wani irin mugun ciwon kai na gefe ɗaya wanda ya addabe ni.

 

Ina zuwa na tarar babu wasu mutane masu yawa da sukazo,don haka na ɗakko shimfiɗar ajinmu nayi,na sunkuyar da kaina a tsakankanin cinyata na rushe da kuka me ƙarfin gaske.

 

 

 

Ina cikin kukan dai naji kamar wani yana tsaye kusa dani,ga wani ƙamshin turare kamar na sanshi.da sauri na ɗago idanuwa waɗanda suka rine sukayi jawur.

 

Da sauri na tashi cikin kunya na ce”ya sayyadi ina wuni”.?

 

“lafiya ƙlau”.

 

Ya amsa yana kallon idanuwana, wanda ko da ba’a gaya maka ba kasan nasha kuka sosai,ga farar fatata ta ƙara wani irin ɗau,tayi ja sosai saboda kukan dana sha.

 

“Ki sameni a office”.

 

Ya faɗi hakan yana yin gaba abinshi,a hankali na tashi na bishi duk jikina ya yi sanyi don na hango damuwa sosai a tattare dashi.

 

Ina shiga office ɗin na tsugunna kai na yana ƙasa,na jiyo muryarsa yana ce wa.

 

“Noor ki ɗago idanuwanki ki kalleni,sannan ki faɗamin abinda yake damunki”.?

 

Shiru nayi ina cigaba da hawaye na,don ba kasafai na fiya faɗar matsalar gidanmu ba,don babu me sharemin hawaye ƙarshe ma sai dai a ƙara haɓɓaka matsalar.

 

“Ina magana kinyi shiru Noor”.?

 

Na ɗago jajayen idanuwana cikin sanyi na ce”babu komai ya sayyadi”.

 

yana yi fuskarsa ce ta ƙara canjawa ya ce”ƙarya kike Noor,ni malaminki ne so banga abinda zaki ɓoyemin ba”.

 

Ganin ransa ya ɓacine yasa na gaya masa komai,ba don rai na yaso ba sai don babu yadda zanyi.

 

Kallona ya yi a hankali sannan ya ce”Noor kiyi haƙuri ki saka Allah aranka,ki sanya aranki ke baki da wata dabara ko wayo idan ba Abinda Allah ya tsara miki arayuwarki ba,ni ɗinnan da kike ganina idan har na baki tarihin rayuwata to tabbas zakiga ke naki ba komai bane”.

 

 

Da sauri na kallesa ina mamakin jin abinda ya ce,don ni a ganina kamar babu wani ɗan adam daya kai ni shan wahala aduniya.

 

“Eh Noor ki kalleni sosai,nasan zakiyi mamakin jin hakan daha gare ni,amman ba abin mamaki bane halin rayuwa ne,idan kana ganin kai kafi wani to tabbas wani ya fika,haka abin yake kada ki daɗa kada ki rage.”

 

 

Kallonsa na ƙarayi a karo na biyu,na sunkuyar da kai na sannan ya cigaba da magana.

 

“Tashi ki tafi aji,naga an fara taruwa ammsn insha Allah zanxo har gida,don in ƙara duba jikin mama insha Allah zan baki labarin rayuwata kaf.”

 

Ɗan murmushi nayi sannan na ce”to ya sayyadi na gode sosai.”

 

Ya tsaya ya rungume hannayensa a ƙirji yana kallona,duk sai naji kunya ta kamani sosai sai naji ya ƙara kirawo sunana cikin wata iriyar murya me nuna tausayi ƙarara.

 

“Noor”!.

 

Dawowa na yi sannan na ce”Ya sayyadi”.

 

Muryata na rawa saboda ganin fuskarsa kamar aƙwai damuwa.

 

“Ki ƙara haƙuri da rayuwa kinji”.

 

murmushi na yi na wuce sannan na ce”to ya sayyadi”.

 

Na wuce ina jin zuciyata fara ƙal……✍🏿

 

*Hmm fans bazan san ƙaunar da kuke nunamin ba,har dai kuna ƙauna ta to ku taya ni da share,tare da sanyayyan sharhi(comments)ta nanne zan san lallai kuna ƙaunata.*

 

domin yin magana dani kai tsaye👇🏻👇🏻

07068606171

 

 

*miss green ce🫵🏾*

 

 

 

*TALLAH*

Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi’at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. “Wai ƙamshi kina nufin Badi’at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?”

“Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi’at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi.”

“Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?”

“Bari na faɗa miki akwai…

 

Humra

Kulacca

Sudanese Humra

Kulacca ta gashi.

Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.

Turaren mopping

Room freshner

Turaren turara kaya.

Turaren wuta na toilet

Sannan akwai ingantaccen maganin infection

Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.

Wanda zasu shiga daga ciki kuma

Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas

Kabbasa

Setin kujerar tsugunno

Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.

Ina bayar da sari.

 

Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?

 

“Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.

 

08179523215

 

 

*TALLAH*

A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

 

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽

 

*ingantaccen maganin infection *

 

Ingantaccen maganin basir

 

Ingantaccen maganin gyaran nono

 

Ingantaccen maganin gyaran hips

 

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

 

Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah

 

Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

 

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

 

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

 

Akwai zallan hadi na amarya

 

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

 

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽

 

Akwai gumbar Madara

Akwai gumba me rubutu 🤐

Akwai gumbar kankana

Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)

Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)

Akwai gumbar hasi

Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉

Akwai gumbar gero

Akwai gumbar ridi

Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐

 

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽

 

Akwai tsumin kankana

Akwai tsumin baure

Akwai tsumin rubutun Ayar Allah

Akwai tsumin kwakwa

Akwai tsumin giginya

Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)

Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌

 

Akwai rubutun mallaka

Akwai zoben mallaka

Akwai hayakin mallaka

Akwai zani na mallaka

Akwai hadin ci da kaza

Akwai hadin yan shillah

(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)

Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉

 

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉

Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.

*_📲Typing_*.

 

 

 

*_🪁ƊINYAR MAKAHO…!🪁_*

_(Ta nuna a hannunsa)🍀_

 

 

 

 

 

_*UMMU MAHER(MISS GREEN ce)🍀*_

 

 

_*AREWA BOOK👉🏼*_

 

ƊINYAR MAKAHO:: https://arewabooks.com/book?id=6387a8e97dd221ff54205a4f

 

 

 

*GAWURTATTU 5🔥*

————————

 

 

P. 3&4

 

 

. . . . . ..ina komawa aji na tarar da Hadiza har tazo ita da wasu ƙawaye na,harara ta tayi sannan ta ce”oh ta ya sayyadi bada kanki asare kije gida kice ya faɗi”.

 

Murmushi nayi na zauna ba tare dana ce komai ba.don daman ni ba mutum ce me yawan surutu ba,muna cikin hakan ya sayyadi ya shigo ajinmu ya yi mana ƙari.

 

Sosai nake kallonsa saboda yadda yace wai rayuwarsa tafi tawa muni,ni abin har mamaki yake bani?gashi dai ahaka Allah ya hore masa komai daidai gwargwado,ga mahaifiyarsa ga mahaifinsa ga ƙannensa kuma suna zaune lafiya klau,to banu wanda zaiyi tunanin aƙwai wata a ƙasa.

 

 

 

 

 

*_FRANCE🇫🇷🇫🇷_*

 

_State paris_

 

. . . . .ƙwance yake akan faffaɗan gadonsa wanda ya yi matuƙar haɗuwa,sosai yake bacci cikin wani kyakkyawan blanket ɗinsa,me laushi da kuma santsi baccinsa yake hankali ƙwance tamkar dai ba shida wata damuwa.

 

Wayarsa dake silent itace ke ta faman ruri alamar tana buƙatar taimako,tun farkawarsa ta farko yaji ƙarar wayar amman sai yaƙi ɗauka ya yi niyyar cigaba da bacci amman sai ya miƙe cikin fushi ya ɗauki wayar.

 

Ba tare daya duba waye ba ya ce”wani igiot ɗinne yake damuna”?.

 

Ya faɗi hakan cikin da ɗaga murya,shiru akayi daga cen ɓangaren ba tare da anyi magana ba,ya samu damar ɓalle bottle ɗin rigarsa kamar wanda zai yi faɗa,ya yi tsaki ya ajje wayar ya cigaba da masifarsa.

 

Ya shige banɗaki yana maganarsa,babu ruwansa da addu’ah ya shige haɗaɗɗan koman wankansa ya zauna aciki,ya ɗauki remote ya kunna tv ɗin dake manne ajikin kyakkyawan banɗakin,yadda kasan baza a bar duniya ba haka banɗakin yake.

 

Hmm wasu na cen suna fama da talauci,abinda zasuci ma yana damunsu tamkar dai Noor baiwar Allah,wasu kuma banɗakin ma tamkar babu agidan saboda langa langa za’a saka arufeshi don dai a samu wajen yin ɗahara,amman wasu sai kaga ban ɗakin tamkar ɗaki tsabar haɗuwa.

 

Ya Allah ka rufa mana asiri duniya da lahira amin.

 

 

Har bacci ya fara ɗaukesa ya tuna cewar yana da meeting aɗakin shugaban ƙasa,don haka ya tashi ya yi wanka,ya fito ya zauna gaban mirror tamkar wata mace.

Ya fara shafa wani lotion me mugun ƙamshi da sanyaya zuciya,Ya ɗakko cort fara da wandonta ma fari ƙal,ƴat cikin kuma baƙa ya ɗaura agogonsa me matuƙar tsada,wanda ya yi mugun toomuch da kayansa,ya taje ƙwantaccen gashin kansa tamkar na larabawa ko indiawa.

 

 

YARIMA yazeed kenan,mahaifiyarsa asalinta balarabiya ce wacce ta gaji sarauta agurin mahaifinta sarkin Masar suna da ƙarfin Sarauta da kuma mulki sosai.

 

Su biyune ƴaƴansa Gimbiya Zulaihat da kuma Umar Farouk,Tayi aure da mahaifin Yazeed shekara ashirin da tara kenan,ayanzu Yazeed yana da shekara ashirin da 27.

 

Kyakkyawane sosai Yazeed,mahaifinsa ɗan asalin Nigeria ne Kuma anan ya girma,ɗan sarautane gaba da baya kuma ayanzu shine sarki.

 

Kada kuga na ɓoye sunan garin da kuma sunan Masarautar nayi haka ne saboda labarin gaske ne,kuma komai yana son sirri.

 

 

Yarima Yazeed shi kaɗai ne namiji awajen mahaifinsa,sauran duk matane su goma sha ɗaya ne mata,su uku ne awajen mahaifiyarsa,daga shi dai ƙannensa ƴan biyu.

 

Yazeed irin yaran nanne sangartattu waɗanda duk abinda sukayi dai dai ne,hakan ya samo asaline ga mahaifinsa don yana masifar son Yazeed ɗin.

 

Mahaifiyar Yazeed babu ruwanta,a kullum tana nuna masa hanyar dai dai sai dai sam Yazeed baya ɗauka,baya jin magana ko kaɗan gashi yaro ƙarami amman abinda zaiyi wani babban ma bazaiyi ba.

 

Ga shegen miskilanci,da girman kai ba da kowa yake magana ba sai wanda yaga dama,kuma ba kowacce magana yakeyi ba,zaiyi wuya kaga yayi magana ya ƙara maimata ta,haka yake ƙannensa ƴan biyu suna matuƙar jin tsoronsa,don ma bai fiya zama a Nigeria ba kullum yana ƙasashen waje musamman ma Ƙasar France.

 

Don yana da kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da shugaban ƙasar France ɗin,Don Yarima Yazeed Allah ya yi masa basira da fikira,tun yana yaro yake masifar son zane zane,na gidaje dogaye da kuma maras tsayi,kai bai tsaya anan ba har zane zanen gadaje na titi masu matuƙar kyau da ƙawa.

 

Wanda ko su kansu turawan basu iya wannan aikin ba,Tun da Iyayen Yarima sukaga inda fikirarsa take shikkenan suka mayar da hankalinsu akan ta yaya zasuyi don suga ya cika burinsa na zama me tsara zanen gine gine.

 

To daya ke abin na masu dashi ne,sai ga Yarima ya cika burinsa don iyayensa sun bashi gudunmawa sosai.

 

Suka kaishi France acen yaje yayi karatunsa kaf,tun daga Primary,secondary,high institution,duk acen yaje yayi bai cika zuwa ba sai dole.iyayensa ke ziyartarsa don wani lokacin ma Gimbiya Zulaihat ita ce ke zuwa ta yi hutu wajen Yarima Yazeed sai tafi wata ɗaya tana cen.

 

 

To fa aɗan wannan zaman ne Mahaifiyar Yazeed ta gano wasu abubuwa dan gane da halayyar ɗan na ta.

 

Idan ya fice tun safe bazai dawo ba sai ƙarfe sha biyu na dare,bayan ta tambayesa bai ɓoye mata komai ba yace yaje Club ne.

 

Sosai hankalin Fulani Zulaihat ya tashi,ta rasa inda zata saka rayuwarta,bata taɓa tunanin irin rayuwar da ɗan ta yake ba.

Ashe yana cen wata uwa duniya yana aikata saɓon Allah,Ta nuna masa ɓacin ranta sosai.

 

Shi kuma Yazeed ya kasance me gudun ɓacin ran iyayensa musanma ma mahaifiyarsa don yana matuƙar ƙaunarta sosai,Har zuciyarsa ya nuna mata insha Allah ya daina zuwa.

 

Taji daɗi sosai da sosai,don tasan tunda yace ya daina to tabbas ya daina ɗin,don tafi kowa sanin ɗan nata yana matuƙar jin maganarta tare kuma da yi mata biyayya.

 

Ta baro ƙasar france cike da kewar ɗanta,tare kuma da jin daɗin jin maganarta da yayi,Tasan sarai Yazeed baya ƙarya ko zaka kashesa to tabbas gaskiyar nan zai faɗa komai ɗacinta,gashi baya shakkar kowa idan ba ita mahaifiyarsa ba,shiyasa akullum take me yi masa addu’a akan Allah yasa ya zama me sauƙaƙƙen hali.

 

 

 

 

NOOR POV

 

 

 

. . . . .a tare muka taho da Hadiza,muna tafiya muna hira sai ta ce”wai Don Allah Noor in tambayeki?”.

 

Murmushi nayi sannan na ce”ina jinki”?.

 

 

“Yauwa don Allah wai aƙwai wani abune a tsakaninki da Ya sayyadi?”.

 

Ɗan murmushi nayi sannan na ce”ikon Allah me kika gani?”.

 

Murmushi tayi sannan ta ce”Noor kenan wallahi ni nasan aƙwai wani abu,idan ka kalli idon ya sayyadi zaka ga sonki ne ƙarara acikin zuciyarsa,kawai dai kina ɓoyewa ne ke da shi,baƙwasan mu ƴan baƙin ciku mu sani”.

 

“Hhh kai gaskiya Hadiza kina da fassara wallahi,ni fa nace miki babu komai tsakanina dashi,ke kin sani Hadiza bani da wata aminiya kaf faɗin duniyar nan daya wuce ke,sai kuma Hafsa ƙawata ta boko,amman da aƙwai wata alaƙa da ke ce zaki fara sani,don banga amfanin ɓoye miki ba don kinga kema bakya ɓoyemin komai na ki”.

 

 

 

“Hmm to Allah dai ya tabbatar da alkhairi, don idan ke baki ga abinda na gani ba,to ni na gani wallahi don ke daman Haka kike Noor,sai dai wai wani ya hango miki wani yana sonki amman ke sai ki kasa ganewa”.

 

Murmushi kawai nayi don nasan,halin Hadixa aƙwai jan magana shiyasa ma nayi shiru,don ni ba mutum ce me musu ba maganar ma ba kowacce nake yi ba musamman idan abu bai shafe ni ba.

 

Hadiza ta ce”Noor ina son muyi wata magana dake,amman wallahi ina tsoron gaya miki don ban san yadda zaki ɗauko maganar ba”.

 

Dafa kafaɗarta na yi sannan na ce”to Hadiza faɗi mana kinga na kusa zuwa gida,kuma nasan hankalin Umma yana kai na yanzu,don haka ki faɗi maganar taki inji”?.

 

Janyo ni tayi wani lungu,sannan ta zauna akan wani dandamali,hawaye na fitowa ta cikin idaniyarta sannan ta ce”Noor kaf duniyar nan ayanzu banida wanda ya kaiki Noor,saboda ke ɗin me hankalice da kuma sanin ya kamata,tun da nake dake baki taɓa bani gurguwar shawara ba,nasan kuma ayanzu ma bazaki bani shawara marar kyau ba.”

 

Ta faɗi hakan hawaye na cigaba da ƙwaranyowa daga ƙwarmin idaniyarta.

 

 

Shiru nayi ina kallonta,sai naji duk tausayinta ya kama ni sosai,na matso kusa da ita na saka hannayena,na share mata hawayen da suka ɓata mata idanu,sannan na juyo da ita tana fuskantar fuskata muka haɗa idanu sosai sannan na ce.

 

“Hadiza wai bana hanaki faɗar cewa ni kaɗai ce dake aduniya ba?Allahn daya halicceki yafi kowa sonki da kuma ƙaunarki,tunda dai shine ya halicceki baya ga haka ma ga iyayenki duk araye”.?

 

 

“Hmm Noor kenan kina bani mamaki wallahi?sau nawa muke wannan maganar dake?ke kanki kinfi kowa sanin iyaye na dukansu basa sona balle kuma ƙaunata,Mahaifiyata tun ina shekara biyar suka rabu ita da mahaifina,tun daga wannan lokacin rayuwata ta shiga matsanancin hali,don har yau dana ke baki wannan labarin,mahaifiyata bata taɓa nemana ba wai tana da wata ƴa,shima mahaifina dai dai da rana ɗaya bai taɓa cemin wai ga inda mahaifiyata take ba?tunda mahaifina ya yi aure ya auri Baba Hanne shikken ni na zama tamkar wata banza,don dani da banza duk ɗaya muke awajen mahaifina,babu ruwanshi da yadda nake gudanar da rayuwata,Wannan matsalar dana ke ciki Noor zata iya sanadiyyar rasa rayuwata.. . . .”

 

 

Sai ta fashe da kuka me ƙarfi.

 

 

 

 

kallonta nayi sannan na ɗago haɓarta akan tafin hannuna sannan na ce”haba Hadiza na sanki fa da haƙuri,don Allah ki daina saka damuwa aranki,ki zamo me haƙuri da addu’ah akoda yaushe,kamar yadda Ya sayyadi ya faɗamin ɗazu,mu ɗan adam muna yin kuskure wani lokacin,bamu fiya yadda da ƙaddara ba kuma alhali yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin shika shikan musulunci.”

 

Na faɗi hakan ina kallonta.

 

Kukanta ta cigaba dayi sannan ta kamo hannuwa na duka biyu ta ɗora akan ƙirjinta ta fashe da kuka sannan ta ce.

 

 

“Hmm Noor halinda nake ciki duk yafi wannan Noor,idan na baki labarin abinda yake damuna sai kin girgiza ainun,sai kinyi mamakin abinda ke faruwa.”

 

Kallonta nayi sannan na ce”haba Hadiza sai ja min rai kike kuma kinsan umma na gida tana jira na,don Allah Ki faɗamin kinsan bana son ganinki cikin damuwa”.

 

“Noor ƙanin Matar Babana ke son lalatamin Rayuwata”.

 

Sosai na waro idanuwa na duka a waje,tsoro duk ya kamani na kasa cewa komai saboda firgici da kuma mamakin jin hakan.

 

 

A hankali ta miƙe jikinta duk yayi sanyi sannan ta ce”Hmm Noor daman nasan zakiyi mamaki sosai,yau kusan ƙwana biyu kenan dana je gidansa ya nemeni da wannan mummunar maganar,Noor nayi mamaki kuma na tsorata sosai,ashe dukkanin hidimar da yake min ashe so yake ya fanshe abinsa.”?

 

Ta kalleni tana hawaye.

 

Nima hawayen nake sosai sannan na ce”Haba Hadiza kinsan da wannan maganar amman kuma kikayi shiru kamar babu abinda ke damunki”?.

 

“Hmm Noor kenan,to yaya zanyi da rayuwata?wa nake dashi da zangayawa?so kike na gayawa yayarsa ƙaninta na nemana?ko kuwa so kike na faɗawa Baba na?wannene acikinsu zai yarda dani”?Noor na faɗa miki ne don ki sani kuma ki tayani da addu’ah”.

 

 

 

“insha Allah Hadiza zan tayaki da addu’ah,kuma babu abinda zai sameki sai ikon Allah,Amman Hadiza kin faɗawa Baba Hassana kuwa”?.

 

“Ban faɗa mata ba Noor na rasa ta yadda zanyi in faɗa mata,don ba ƙaramin firgitani yayi ba akan cewa duk wanda na faɗawa to na zama gawa,kema na faɗa miki ne don zuciyata ta samu salama,yanzu dana faɗa miki na rage jin raɗaɗin dana keji”.

 

“Kuka na fashe dashi sannan na ce”Hadiza me yasa xakiji tsoronsa?don yace miki zaki xama gawa?Shi daba Allah ba?Allah ne kawai yake da rai da kuma mutuwa,babu wani bawa daya isa ya kashe wata rai face da hukuncin ubangiji,don haka kada kiji tsoro ki faɗa mata Allah zai kawo mana sauƙi insha Allah,idan kuma bazaki iya faɗa mata ba to ni zanje in sameta in faɗa mata,sai a haɗashi da hukuma don idan ba haka ba,zai lalata miki rayuwarki ƙarshe kuma kiyi nadamar yin shirun.”

 

Da sauri Hadiza ta rufemin baki sannan ta ce”Noor ki rufamin asiri don Allah,mutumin nan yana da kuɗi ba kaɗan ba koda an haɗashi da hukuma bazai kamu ba”.

 

Saurin cire hannunta nayi daga bakina na yarfeshi gefe sannan na nuna ta cikin fushi na ce”yafi ƙarfin Allah ne?wallahi Hadiza ki tashi ki farka idan ba haka ba,zai lalata miki rayuwarki abanza da hofi,ƙarshe yace bai ma sanki ba kinga wa gari ya waya”?.

 

 

 

 

Fashewa tayi da kuka sannan ta rungumeni ta fashe da kuka me ƙarfi.

 

Rungume ta nayi sannan na fara shafa bayanta a hankali tamkar ƙaramar yarinya,har ta tsagaita da kukan na ta nima har yanzu kukan nake na tausayin ƙawar tawa,wato duk rayuwar da kake ciki sai kaga wani ya fika.

 

“Noor ki tafi gida kin bar Umma ita kaɗai,kuma bana so ki ɓoyewa Umma wannan maganar,saboda nasan Umma aƙwai ibada,kuma bayan haka ma Umma tamkar uwa na ɗauke ta,nasan zata taya ni da kai kuka wajen ubangiji.”

 

 

Sallama mukayi da ita,ta kama hanyar gidansu tana tafiya tamkar wacce ƙwai ya fashewa aciki.

 

Nima duk jikina babu daɗi,ga matsalar dana ke ciki ga ta aminyata Hadiza,abin ya damu ƙwalƙwakwata ina ta tafiya ina sauri-sauri don inzo gida in kalli sanyin idaniya ta wato mahaifiyata,duk baƙin cikin dana ke ciki idan na kalli mahaifiyata ina jin sauƙin raɗaɗi sosai.

 

 

 

 

Na tsallaka titi na farko na taho don tsallaka na biyu sai naji. ..

 

 

da gudu Drivern ya fito daga cikin motar yayo kai na,ganin har jini ya fara ɓata wajen dana ke shima ogan nasa da sauri ya fito,yayo kai na farar cort ɗinsa ta jiƙe da jini ya ɗagani cak.da sauri suka shiga cikin motar duk hankalinsu a tashe.

 

 

General hospital suka nufa,wato aminu kano teaching hospital taimakon gaggawa aka fara bani,aka shiga dani emergency don bani taimakon gaggawa.

 

 

Zagaye kawai saurayin yake don duk hankalinsa ya tashi sosai,Wayarsa ce ta fara ruri amman bai iya ɗaga wayar ba saboda tashin hankali,tunda yaka bai taɓa buge ko da ɓera ba balle kuma mutum.

 

Ganin kiran ya yi yawa ne yasa ya ɗaga,daga cen ɓangaren aka fara magana.

 

 

“Haba Ahmad baka saba kaiwa haka ba?lafiya kuma har yanzu baka dawo ba”?.

 

“Hajiya wallahi yau ina cikin matsanancin tension ne,na shiga cikin wani hali sosai wata yarinya na buge yanzu”.

 

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.

 

 

“Ahmad wani asibiti ne?”.

 

Faɗa mata sunan asibitin ya yi sannan ya ajje wayar,ya zauna ya kalli rigarsa wacce duk jini ya ɓatata,hankalinsa ya ƙara tashi sosai yana addu’ar Allah yasa kada ta mutu don ta zubar da jini sosai.

 

 

Ba’a fi minti talatin ba sai ga Mahaifiyar Ahmad,duk itama hankalinta a matuƙar tashe.

 

Ta kalli rigar Ahmad ɗin wacce duk jini ya ɓatata,tsoro ya kamata sosai ta ce”sannu Ahmad me ya akayi hakan ta faru”?.

 

“Hmm Hajiya ƙaddara,da kuma rabon sai na fito daman sai da kika ce kada na fito amman yanayin aikina yasa babu yadda zanyi dole dai sai na fito hakan ta faru.”

 

Kusan minti talatin sannan likitocin suka fito,da sauri Ahmad ya ƙarasa kusa dasu yana tambayarsu ya jikin na ta.?

 

Likitan ya ce”kai ne ka buge ta?”.

 

“Eh nine na buge ta,gama ɗan sandan da muka taho dashi”.

 

 

Likitan ya kalli ɗan sandan sannan ya ce”ok ka biyoni office”.

 

Yana faɗar hakan Ahmad yabi bayansa don yaji abinda likitan zaice,gabansa sai faɗuwa yake kamar zai faɗo ƙasa.

itama Hajiyar Ahmad ɗin binsu tayi don hankalinta ya kasa ƙwanciya,yadda taga jini ajikin Ahmad to ta tabbatar da cewa wannan yarinyar idan bata mutu ba,to tabbas tasha wuya sosai.

 

 

To acen ɓangaren kuma,mahaifiyar Noor na cen duk hankalinta ya gama tashi,gashi ita ba ƙafa ba balle ta tafi nemanta.

 

Ta rasa yadda za tayi,daman tana da alwalarta ta yi sallarta a zaune,ta ɗaga hannayenta sama tana kuka tana roƙar ubangiji.

 

“Ya Allah kaga xuciyata,kaf duniyar nan daga kai sai manzonmu muhammad(S.A.W)dasahabbansa da kuma matayensu,sai ƴata Noor kaf duniyar nan bayansu sai ƴata,ina masifar sonta har cikin ƙoƙon xuciyata,Noor shekararta Shida a ciki na,ba shekara ɗaya ba har shekara shida,haka nasha wuya na haifeta ya Allah duk inda take Allah ka karemin ita da karewarka,sannan Allah ka tsaremin ita da tsarewar ka,ba wayo na ko dabara ta ba,Allah na tabbatar da ka amshi roƙo na,Ya Allah kai ne kace mu roƙeka zaka amsa mana,to Ya Allah na kawo kuka na gare ka akan rashin dawowar ƴa ta gida,Allah ka tsaremin ita Amin ya Allah”.

 

Dai dai nan ta shafa,tana shafawa taga an ɗaga labulen ɗakinta..ta hango hasken fitilar nefa a tsakar gida,wacce ita babu wannan gatan a ɗakinta,tunda ta lalace shikkenan yau kusan shekara biyu kenan tun sanda ta fara wannan ciwon.

 

“Ke!”.

 

Sai lokacin ta gane wanda ya ɗaga mata labule,Mahaifin Noor ne tsaye sai harararta yake kamar zau dake ta.

 

Ta daure daga wani mugun haushinsa da take ji ta ce.

 

 

“Ina yini Baban ya. . . .”

 

Da sauri ya dakatar da i’ta da faɗin”ke Fatima kiyi a sannu fa,rashin mutuncin da kikeyi dake da ƴarki ya fara i’sata,ya za’ayi yarinya ta fita tun rana amman har yanzu kusan ƙarfe takwas na dare bata dawo ba?ko daman haka kika koya mata?don taje yawon karuwanci ta samo miki abinda zakiyi ƙarya?don dai nasan badon yunwa ko don wani abuba,don dai kinsan gidana ba gidan yunwa bane”.?

 

Sosai take kuka hawaye ya wanke mata fuskarta,ta tsani cin mutuncin Isma’il sam be sam mutuncin ɗan adam ba,shiyasa san bata fiya shiga hulɗarsa ba,musamman ma yanzu da ba tada lafiya.

 

“Ba dake nake ba?kinyi min shiru munafuka sai ana magana kiyi wani wuƙi wuƙi da idanuwa na rashin gaskiya ko?to bari kiji idan na ƙara auna minti talatin bata dawo ba,to sai ranki ya yi mummunan ɓaci,don sai kin fita kin bar min gida na”.

 

 

Sosai gabanta yayi wani irin mugun bugawa,Fatima ta dafe ƙirjinta wasu hawaye masu mugun zafi suna ƙwaranyowa daga ƙwarmin idanuwanta.

 

Lallai rashin imani irin na Isma’il ya yi yawa,yanzu ayadda take ɗinnan idan ya kore ta ina zata je?idan ya kore ta dawa zata haɗu,mutane nagari ko akasin haka?.

 

Inna Saude tana ganin shigowar mijinta ta ɗaure fuska ta yo da ɗaurinta gaban goshi sannan ta ce”oh amman Isma’il kana bani mamaki?yanzu da kaje tattaunawa kukayi ko me?baka kore ta ɗin ba?shine ka dawo min nan kana wani hura hanci?”.

 

“Ai na bata nan da wasu mintina,wallahi indai bata dawo ba korarta zanyi daga gidana don daman wallahi ta isheni,mata kamar wata musaka ita ba ƙafa ba ita ba wata mamora ba.?”

 

 

 

***********

 

Suna zama likitan ya ce”yauwa daman na kiraka ne saboda inyi maka bayanin komai,wannan yarinyar ta zubar da jini sosai,ta yadda dole ne sai anyi mata ƙarin jini,don ma jininta me ƙarfi ne sosai da an rasa rayuwarta baki ɗaya,amman Allah ya taƙaita karaya ɗaya ce a ƙafarta sai kuma ƙarin jini da za’ayi mata Leda huɗu sai wasu magunguna da zan rubuta mata yanzu.”

 

Wasu ƴan rubuce rubuce ya yi sannan ya ɗago ya ce”yauwa to waɗan nan magungunan zaka sayo,sannsn maganar jini kuma siya zakuyi ko zaku bayar?”.

 

Da sauri Ahmad ya ce”zan bada Leda ɗaya sai in siya guda uku ɗin”.

 

Hajiyarsa ta ce”kai Ahmad ka siya mana?meye dalilin da za a ɗibar maka jini kuma kaima kasan ba kada lafiya”?.

 

“Babu komai Hajiya a ɗiba ai taimako ne,shi taimako ana yinsa ne don taimako don gyara lahirarka”.

 

 

Ba don ran Hajiya yaso ba ta haƙura kawai,ta bar zancen don yanzu ba lokacin da za’a zauna ana musu bane.

 

 

8:00pm Dai dai lokacin Ya sayyadi ya sauka akan lifan ɗinsa,ya tsaya aƙofar gidan ya kasa shiga,ya samu wani yaro ya aikasa gidan ya ce.

 

 

“Kai idan ka shiga kace wai Noor tazo inji ya Sayyadinsu”.

 

yaron ya ce”to”.

 

Daman ɗakin Mahaifiyar Noor ne a farko,don haka kana shigowa da ɗakinta zaka fara cin karo.yaron ya shiga ɗakin ya ce”wai inji ya sayyadinsu Noor wai tazo”.

 

Da ɗan sauri Umman Noor ta ɗago hawaye duk ya gama wanke mata fuskarta,ta ce”kai kace wai haryanzu bata dawo daga makaranta ba,nima nemanta nake yanzu.”

 

Tana faɗar hakan ta fashe da kuka me tsanani.

 

 

Yaron yana fita ya ce”wai ance har yanxu bata dawo daga makaranta ba, mamanta ma nemanta take”.

 

 

Sosai gabansa ya yi mugun faɗuwa,ya kalli yaron sosai kamar yaga hoto,ya rasa wani irin tunani zaiyi to ita Noor a ina ta tsaya ne?.

 

Wata dabara ce ta faɗo masa ya hau mashinsa ɗinsa,bai tsaya ko ina ba sai gidansu Hadiza don yasan duk inda Noor take to Hadiza ta sani.

 

 

Allah ya taimakesa ya sameta a ƙofar gidansu,da alama aikenta akayi ya sauka ya ƙarasa ya ƙwala mata kira don yaga ta kusa shiga gida.

 

Cikin tsoro ta juyo ta ce.

 

 

“a’ah ya sayyadi lfy kuwa na ganka haka”?.

 

“Ina fa lafiya Hadiza?ƙwarki aka nema aka rasa,shine naxo don inji ko kinsan inda take?tunda nasan aminiyarki ce kuma tare kuke tahowa”.

 

Tunda ya fara maganar ta tsaresa da manyan idanuwanta,ta dafe ƙirjinta tana cewa”inna lillahi wa inna ilaihi raji’un na shiga ɗaka ban fito ba..ɗaxu fa tare muka rabu,ta tafi gida nima na tafi wallahi tun daga nan ban ƙara sanin inda tayi ba”.

 

Ta faɗi hakan tana fashewa da kuka sosai,jin ihunta yayi yawa ne yasa ya sayyadi ya ce”ke Hadiza shiga gida,ba kuka zakiyi ba addu’ah zakiyi”.shima cikin dakiya ya faɗi hakan don bai san yana mugun son Noor ba sai yanzu.

 

Yanzu ta ina zai fara nemanta,ya share hawayen fuskarsa da handcachep ɗin hannunsa,sannan ya hau machine ɗinsa yabi hanyar gidansu Noor.

 

Ya tsallaka titi na farko ya tsallaka na biyu,sai wani tunani ya faɗi masa,ya sauka daga kan machine ɗin nasa ya gaisa da wasu samari daya gani sannan ya ce.

 

“Don Allah bayin Allah ɗazu bakuga wata yarinya ƴar fara ba?sanye cikin uniform ɗin makarantar islamiyya tana da ɗan matsakaicin tsayi.”?

 

Wani daga cikinsu ya ce”haba mlm mufa tun safe muke wajen nan,tamkar masu jiran taimako nan ce majalissarmu sai dare muke tashi,kuma mutane da yawa suna zuwa wucewa,wasu mu kallesu wasu kuma bama sanin sun wuce,amman mu bamu ga wannsn yarinyar da kake nufi ba.”

 

Da sauri ɗayan ya ce”a’ah fa ku tsaya ko dai wacce aka buge ce ɗazu a mota?don ma bamu san ƴar waye ba da tuni mun shaida a gidansu.”

 

Da sauri ya sayyadi ya ce”inna lillahi wa inna ilaihi raji’un,don Allah ina kuka ga sunyi”?.

 

“To mlm muda ba binsu mukayi ba?ta ina zamu san inda sukayi”.

 

Ɗaya daga cikinsu ne ya faɗi hakan.

 

Da sauri Ya sayyadi ya hau machine ɗinsa zuwa gidansu Hadiza,ya aika yace yana kiranta Hajja kishiyar mamanta sai masifa take tana cewa.

 

“shi kuma wannan ya sayyadin uban me zaiyi miki da daddaren nan kamar wani tsohon ƙwarto.?”

 

Ita dai Hadiza saka hijabinta tayi ta fita da gudu.don ko saurarenta bata yi ba,ta fito waje don tunda ya sayyadi ya shaida mata ba’a ga Noor ba,taji duk hankalinta ya yi matuƙar tashi.

 

Aguje ta fito tana gaki sannan ta ce”ya sayyadi an ganta”?.

 

Bayanin komai yayi mata sannan ya ce”yanzu shge gaba muje gidansu Noor don mu sanarwa da mahaifiyarta komai.”

 

Tana kuka ta shige gaba,tana gudu kamar ƙaramar yarinya Ya sayyadi na binta a baya har suka zo ƙofar gidan.

 

 

 

Da gudu Hadiza ta shigo gidansu Noor,kai tsaye ɗakin mahaifiyar Noor ta nufa tana ta haki kamar zata faɗi.

 

Umma na ganinta ta ƙara sautin kukanta tana cewa”Allah sarki Hadiza ashe kinji labarin ɓatan Noor ko”?.

 

fashewa Hadiza tayi da kuka sannan ta ce”umma yanzu ya sayyadi yake shaidamin wai wata yarinya ɗazu an buge ta,kuma ana tunanin Noor ce yanzu haka ni da ya sayyadi zamu bi asibiti,zamu fara zuwa general hospital don mu duba muga ko Allah zaisa a dace”.

 

Inna Hafsatu dake laɓe jikin labule tana jin duk abinda ke afkuwa,ta ce”Hmm Allah dai yasa ta mutu ma kowa ya huta.”

 

Ya sayyadi da Hadiza suka wuce asibitin don dubawa,Ita kuma Umma na gida sai kuka take carbi yana hannunta tana ja tana kuka,Noor ita kaɗai ta mallaka a rayuwarta ba tada kowa sai Noor,ta taso cikin rayuwa ta ƙunci da baƙin ciki saboda ta kasance ita ƴar tsintuwa ce,tun tana ƙarama aka yarda ita wani bawan Allah ya ɗauketa,yana da mata ɗaya sai ɗa ɗaya shima bayan an tsinceta ne aka haifesa,sai dai matar mutumin ba tada mutunci ko kaɗan,ita dai kanta kawai ta sani sai na ɗanta to a haka tayi wannan rayuwar har Allah ya kawo lokacin da tayi aure.tana tunanin canjin rayuwa ashe wani bala’in ta ƙara afkawa.

 

 

Don kuwa ko wata ɗaya bata yi ba,ta fara cin karo da masibu kala kala don awajen Isma’il kawai take samun farin ciki sai mahaifiyar Isma’il ɗin,don daman sanda ta auri Isma’il matansa biyu itace ta uku,ta aure shine badon kuɗinsa ko kyau ba,don Isma’il aƙwaishi da kyau ga fari kamar tsada,don kana ganin Noor kasan cewa ƴarsa ce.

 

 

 

*****

 

*Yarima pov*

 

 

. . . . .kai tsaye taronsa ya wuce a ɗakin shugaban ƙasar France,har kowa ya hallara shi kaɗai ake jira.

 

Ya zauna yana fuskantarsu,suma duk hankalinsu yana kansa suka gaisa sannan suka fara abinda ya kawosu ya huɗe taswirar wata gadar jirgin ƙasa da yayi wadda ya za na ta,babbar hanya ce ne nisan tsiya wacce idan tafiya mutum zaiyi,sai ya yi ƙwana uku huɗu akan hanya ba tare daya je,hanya ce akan dutse wacce turawa da dama suka yi yunƙurin yi amman basu samu basirar yinta ba,sai gashi yaro ƙarami ya zana ta ya fitar da hanyoyi daga cikinta.

 

Yazeed aka bawa ƙwangilar yin aikin,shugaban ƙasa ya ware kuɗi tsaba akan wannan hanyar,don yana bala’in jin daɗin aikin Yazeed don yaro ne me fasaha da kuma basira kuma gashi ba mutunne me cin amana ba,don ko nawa zaka basa ya ajje maka indai ba kuɗinsa bane to ya yi watsin makauniya dasu.

Suna fitowa daga taron yaji wayarsa ta cigaba da ringing,yaƙi ɗagawa sai daya fito daga wajen sannan ya samu wani waje wanda aka kewaye shi da fararen kujeru ya samu ɗaya daga ciki ya zauna,ya rage cort ɗinsa sannan ya ɗauko wayarsa ya buɗe yaga alamar an turo masa message,ya buɗe message ɗin ga abinda message ɗin ya ƙunsa.

 

 

*Yazeed umminka ce ina ta kiranka kaƙi ka ɗaga ko?ka manta da umminka ko to shikkenan na gode*

 

Duk cikin yaren larabci ta turo masa da saƙon.

 

 

Ɗan murmushi yayi ya shafa ƙwantaccen gashin kansa,sannan ya yi calling no ɗin Mahaifiyarsa wacce yake jinta har ransa don shi aduniya yana matuƙar son mahaifiyarsa.

 

I’tama kuma ya sani tana masifar sonshi da ƙaunarsa,tana tattalinsa sosai kamar wani ƙwai ko kuma ɗan jariri.

 

Tana ɗagawa taƙi yin magana tayi shiru,kamar yana ganinta ta ɓata fuska sosai tamkar tasha kunun tsamiya.

 

Shima kamar yana ganinta ya ce”Ummi yanzu nasan kin turɓune fuska kamar kinsha magani ko?sorry my ummi ayimin afuwa abubuwane da dama suka shamin kai.”

 

Nan ma ƙin magana tayi,sai yaji duk babu daɗi sai ya fara magana cikin shagwaɓa tamkar yaro ya ce.

 

 

“Ummina kin dai na so na ko?.shikkenan bari in kashe wayar gobe zan dawo Nigeria”.

 

Murmushi Fulani Zaulahait tayi,don daman tasan abinda zaice kenan kuma daman itama abinda takeso kenan,har ta gaji da yiwa Yazeed mitar ya dawo gida amman abu ya cutura,sabon da Yazeed ya yi da France bata tunanin zai dawo gida ta sauƙi,amman ta fara wani tunani akan abinda zaisa ya dawo gidan dole.

 

“Ummina kinyi min shiru ko”?.

 

“To me zance maka Yazeed?kai fa yanzu ba ƙaramin yaro bane,kasan abinda ya dace fa?yanzu idan har munason mu ganka sai dai muzo inda kake?ina son in ganka Yazeed amman kaƙi dawowa in ganka inji daɗi,kana son maganar da mutane sukeyi akanka ta tabbata ko”?.

 

 

Ya fara magana cikin shagwaɓa sannan ya ce”Ummi na wacce magana mutanen sukeyi?”.

 

“Hmm bazan faɗa maka ba Yazeed amman ina masifar son in ganka,kuma kasan ba zai yiwu inzo France yanzu ba,saboda Twins suna gab da dawowa daga America kaga kuwa bazan taho in barsu ba”.

 

“Yanzu Ummi kinfi son waɗannan emogies ɗin dani ko?”.

 

“Eh nafi sonsu ɗin,ai su suna jin magana ta ba kamar kai me taurin kai ba”.

 

Taɓa kansa ya yi kamar tana ganinsa sannan ya ce”haba Mom nifa kai na babu tauri,har yanzu ni kid ne(yaro).

 

Murmushi tayi son tasan halin shagwaɓa irinta Yazeed tasan idan ta biye masa sai su ƙwana yana mata shagwaɓa abinda ko ƙannensa basayi.

 

“To shikkenan tunda kanka babu tauri,ni na kashe wayata randa kayi niyyar dawowa.ka kira ni…. . .✍🏿✍🏿✍🏿.

 

————-

 

*Sirrinki*

 

Ki kasance meyin sallah akan lokaci,yin sallah akan lokaci yana ƙara kusantaka da Allah.🙏🏼

 

 

*Bazan ga ƙaunar da kuke nunamin ba,har sai kun taya ni da share da kuma comments me ratsa zuciya,ina alfahari da masoyana aduk inda kuke.*

 

 

Masu yimin copy na littafi,kuna ɗorawa amadadin ku kukayi,babu komai bazanyi Allah ya ida ba,sai dai in gode muku don na san duk cikin love ne,amman aji tsoron AllahMuna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Dinyar Makaho Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!