Hausa Novels

Direban Gidan Mu Hausa Novel Complete

Direban Gidan Mu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Direban Gidan Mu Hausa Novel Complete

01

 

Yau ma kamar kullum suna zaune su biyar suna karyawa a dining area…

 

Janan ce ta kalli Abba tace “Abba ni kam dama ka barmu muna driving da kanmu wallahi zamu iya”

 

Kallonta yayi fuskarshi d’auke da murmushi yace “kiyi hak’uri Janan nafi son driver yana kaiku daga baya idan karatunku yayi nisa zan iya baku mota,ita fauziyya ma da take l2 bata yi magana ba sai ke da kike yin diploma”

 

“Amma Abba…..”

 

“Kimin shiru Janan,na gama yanke hukunci driver na jiranku a waje Idan kun gama ”

Tashi yayi ya haye upstairs ya barsu.

 

Ran Janan a b’ace ta kalli Mameey tace “dan Allah mameey ki saka baki a maganar nan Abba ya fahimce mu,we ar matured enough ba sai ana had’a mu da driver ba”

 

“Dalla rufa mana baki malama,ta ina kika zama matured? a hakan?”

 

“Haba Yaya fahad nayi tunanin ma zaka lallab’a Abba”

 

“Baza’a lallab’a shi ba,sai k’arya kawai,kinfi son kina Murza kan mota kina nuna ke ‘yar wani ce?to baki isa ba,Dan ma Abba baice zai had’a ki da security ba”

 

Wani d’an guntun hawaye ta goge tare da fad’in “shikenan”

Tashi tayi kawai ta fice.

 

Mameey ta bita da ido tare da fad’in “Allah rage miki wannan zafin ran Janan”

“Zan gyara tane ki barni da ita mameey” Fahad ya fad’a rai a b’ace

 

Fauziyya kam babu abinda ta iya cewa dan ranta ya b’aci sosai.

 

******

 

“Janan fito mu tafi”

Fauziyya tayi maganar tana tsaye daga bakin k’ofa.

 

Janan dake tsaye jikin mirrow ta gyara d’orin d’an kwalinta ta d’au jaka”

 

A farfajiyar gidan ta tsaya tana kallon securities d’in,can ta hango direban tsaye jikin mota”

 

“Mts Ali direba ba,wallahi baka isa ba”

 

“Janan muyi hak’uri kawai”

 

“Aunty wallahi bana son naji kunya na muzanta a cikin friends”

 

“To ya ya muka iya?”

 

“Zanyi maganinsa”

Kawai tayi gaba.

 

Suna isa ya bud’e musu k’ofa,tsaki tayi tare da cewa “aikin banza kawai”

 

Ya San dashi take amma kawai ya shareta.

 

Sun fara tafiya a cikin mota kawai ta daka masa tsawa “dakata Malam”

Yayi saurin yin parking.

 

“Bani key”

 

Juyowa yayi ya kalleta cike da mamaki dan hatta Fauziyya sai da tayi mamakin maganar.

 

“Ka bani mana ka tsaya kana kallona kamar maye,wama ya sani ko mayen ne”

 

Mik’a mata yayi sannan ya bud’e motar ya fita,itama fitowar tayi tana masa kallon wulak’anci,”mtsw matsiyaci kawai”

 

Shiga tayi ta tada motar tare da watsa masa ‘ura”

 

“Janan kar Abba yayi fad’a”

“Karki damu Yaya fauzah na d’auki duk fad’an da dai in wulak’anta”

“To Allah ya kyauta”

“Ameen”

 

Sai da ta fara dire fauziyya a skul sannan ta wuce tasu.

 

********

 

Yana tsaye jikin mainar gidansu idonshi gaba d’aya sun kad’a sunyi jajir,duk kanin jijiyar dake fuskarshi ta fito ta bayyana,ranshi gaba d’aya a b’ace yake.

 

Ummi ta goge hawayen idonta tace “Yaya idan babu dama kawai a hak’ura dan bana son rasa ka kamar yadda na rasa Aunty hafsa da baba”

 

Umma ta kalleta ta daka mata tsawa “ki rufa min baki Ummi,me kike nufi?mu barsu suci bulus,wallahi bazai tab’a yuwuwa ba dole Aliyu ya k’watar mana ‘yancinmu,yanzu gashi nan karatunki ya tsaya tun daga aji hudu na sakandire bazai yuwu ba”

 

“yaya…”

 

“Yi shiru Ummi” ya katseta sannan ya cigaba da fad’in “zanyi iya bakin k’ok’arina dan ganin na karb’o mana ‘yancinmu”

 

Kai ya saka ya fice daga gidan ranshi a b’ace.

 

************

 

Gidansu Zuhra ya wuce dan yasan nan ne kad’ai idan yaje hankalinsa zai kwanta dan ko babu komai Zuhra ta San darajar d’an Adam tana da girmama mutane.

 

_Zuhra fara ce kyakkyawa,tana da diri sosai doguwa ce amma ba can ba,tana da tarbiyya sannan akwaita da ilmin addini kuma mahaddaciyar qur’ani ce sai dai batayi karatun boko ba iya karta firamare skul_…

 

Aliyu na isa k’ofar gidan yasa aka kirawota.

 

Bata wani jima ba ta fito fuskarta d’auke da murmushi,ganin yanayinsa ne yasa itama ta daina murmushin ta k’araso inda yake

“Waya tab’a min angona?”

 

Kallonta kawai yake ba tare da wani sauyi ba.

 

“Pls ka fad’a min damuwarka”

“Kece damuwa ta”

Ya bata amsa tare da zama a dutsen da suka saba hira akai.

 

Zama tayi kusa dashi tare da fad’in “dan Allah ka fad’a min damuwarka wlh hankalina ya tashi”

 

“Zuhra na tsani Janan wlh bana ko k’aunar ganinta dama ba sonsu nake ba amma ta k’ara sa min tsanarta ji nake kamar na kasheta ita da mahaifinta da duk wani masoyinsu”

 

“Me?kisa fa angona”

Ta fad’a a razane tare da kallonsa,shima kallonta yake yana k’ara jin zafin a ransa.

 

“Wacece Janan?”

 

Tambayar da tayi masa ne ya sashi dawowa hayyacinsa dan bai ma San yayi wannan furucin ba.

 

Rasa amsar da zai bata yayi gashi ta kafa masa idanu tana jiran amsa.

 

“Kayi shiru”

 

“Wata yarinya ce tana neman raina min hankali,wai har yanzu su baffa basu gama yanke lokacin bikinmu ba?na gaji da ganinki a titi”

 

Cike da jin kunya tace “da amfanin gona ya fito za’ayi bikinmu kasan bikin ‘yar fari sai da Babban shiri”

 

Murmushi yayi sannan yace “Allah ya kaimu lokacin”

“Ameen Angona”

 

Haka suka zauna suna ta hira tare da tsara rayuwarsu.

 

********

 

Tun da maigadi ya bud’e gate ta hango Abba da Ali a tsaye.

 

Gabanta ya fad’i ta kalli Fauziyya tace “Aunty Fauzah wancan munafukin ya kai k’ararmu wajen Abba”

 

“Hmm ni kam ba ruwana wlh ke kika karb’i key dama sai da nace karki karb’a ”

 

“Karki wani damua na d’au laifin”

 

Suna yin parking ta suka fito dukkansu fuskarsu d’auke da rashin gaskiya.

 

Suna isa Janan tace “sannu da gida Abba”

 

Mari ya d’auketa dashi sannan yace “bani key”

a tsawace

 

Mik’a masa key d’in tayi hannunta rik’e da kuncinta.

 

“Abba pls kayi hak’uri”

 

“Rufa min baki kema”

Ya sake kallon Janan yace “na soke miki driving ko kina so ko baki so Aliyu ne zai rik’a kaiki ko ina kuma ita Fauziyya zan bata mota ke kuma ke kad’ai zai rik’a kaiwa tunda baki da kunya,ke daga yau na mayar da Ali DIREBAN GIDANnan”

 

Kallonshi kawai take fuskarta d’auke da k’walla.

 

“Ku bar min gurin nan”

 

Da sauri fauziyya taja hannun janan suka shiga ciki.

 

 

 

 

_Alk’alamin Sadeey_✍

[9/29, 8:13 AM] Aishat A Muha’d: 🍁🍁🍁

*DIREBAN GIDANMU*

🍁🍁🍁

 

 

_by_

*_SaNaz deeyah_*👄

 

“`Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv“`

 

 

02

 

Suna shiga falo ta zube ta fara dirzar kuka.

 

Da sauri mameey ta taso ta rik’eta tana tambayar abinda ya faru.

 

Fauziyya ce tayi mata bayanin komai.

 

Janyo Janan tayi tana rarrashi tare da fad’in “ki daina musawa babanki Janan kin san shi baya da wasa kuma kaifi d’aya ne”

 

Ta d’ago idonta da suka gama rinewa tace “akan direba Abba zai mareni,ya zubar min mutumci a gabanshi”

 

“Ya isa haka kiyi hak’uri”

 

Ranar haka ta yini a bedrum d’inta tana kuka,ko abinci sai da aka tilasta mata sannan ta fito taci.

 

Bayan sallar isha’i Abba ya sa aka kirawota,nasiha yayi mata sosai akan babu kyau wulak’anta d’an Adam sannan kuma ya rarrasheta har zuciyarta tayi sanyi,fahad kuwa gaba d’aya lamarinta haushi yake bashi.

 

 

 

******

 

Haka ta hak’ura Ali ya cigaba da kaita makaranta amma kullum cikin zaginshi take tana nuna masa tsana k’arara.

 

A satin kuma aka sayowa Fauzah motarta sabuwa k’yal k’irar ‘prado’.

 

Yau ma kamar kullum tana zaune a bayan mota tana latsa waya shi kuma yana driving a nutse.

 

‘Dago kai tayi ta kalleshi tare da jan dogon tsaki “dalla malam kayi da jiki sai jan mota kake a k’asaice kamar ta tsohonka,Malam kar kasa na makara fa”

 

Da sauri yaja burki ya tsaya yana kallonta.

“Kallo na kake? To ko motar babanka ce kaifa direbana ne wall…………”

Wuyanta ya shak’o Wanda ya hana ta k’arasa maganar.

 

“Karki k’ara ambatar mahaifina ki zaga” sakin wuyan yayi ta zaro idonta a tsorace cike da mamaki tace “ni ka shak’e?to wallahi a bakin aikinka”

 

“Zan miki abinda yafi shak’ewa idan har kika cigaba da zagin babana”

 

“Ni kam yau sai ka bar aiki a gidanmu tunda har kasan shak’a to tabbas zaka iya kisa”

 

“Na yarda zan bar aikin koda kuwa baki saka an koreni ba ni zan bar gidanku da kaina” ya fad’a yana goge hawaye.

 

Abin ya mutuk’ar bata mamaki ganin yana zubda hawaye _gaskiya yana son shi da yawa_ ta fad’a a zuciyarta.

 

Har suka je skul ba wanda ya sake yima wani magana tana son ta bashi hak’uri amma tana ganin kamar zai rainata ne.

 

Tana fitowa daga motar su Raihan suka k’araso,Lubna tayi saurin k’arasa jikin motar tace “sannu Aliyu ina yini”

“Lafiya lau ya karatu?” Ya amsa cikin sakin fuska.

 

“Karatu Alhamdulillah ya mantawa dani”

 

Da sauri Janan ta juya suka had’a ido tayi saurin janye k’wayar idonta daga kanshi.

 

“Ban manta dake ba saboda kina da matuk’ar mahimmanci a gurina”

 

“Nagode da wannan matsayi da ka bani”

“Nine da godiya”

“A’a ni dai Dana samu kyakykyawa handsome yayi appreciating d’ina”

 

“Lubna idan kin gama surutun ki samemu a hall”

Janan ta fad’a ranta a b’ace dan tana jin haushin yadda lubna ke kuranta Ali har tana fad’ar yana da kyau a gabanshi salon ya raina masu aji.

 

“Karku damu zan taho”

Lubna tayi maganar.

 

Ali kam sakin jiki yayi yana hira da lubna dan ya San Janan tana jin haushin hakan.

 

 

Suna zaune bayan Janan ta gama yiwa Raihan narrating duk abinda ya faru.

 

Murmushi Raihan tayi sannan tace “yana da kyau ki bashi hak’uri saboda kema bazaki so a zagi naki ba,ban San yaushe kika koyi wulak’anci ba Janan da ba haka kike ba”

 

“Wallahi yanzun ma ba haka nake ba,kawai dai na tsaneshi saboda yayi min sanadin hanani driving”

 

“Ba dad’i amma kiyi hak’uri kuma ki bashi hak’uri tunda har kikaga yayi kuka tabbas baiji dad’i ba”

 

“Amma kuma bana son ya rainani”

“Bazai rainaki ba durk’usawa wada ba gajiyawa bane Janan”

“Shikenan nagode da shawararki insha Allah dayazo d’aukana zan bashi hak’uri”

 

 

 

Tun k’arfe biyu take tsaye tana jiranshi shiru babu alamun shi.

 

Waya ta d’aga zata kira kawai taji kiran Fahad ya shigo.

Da sauri ta d’aga tana fad’in “wai ina sakaran direban nan bayan nace masa k’arfe d’aya zan gama lecture gashi har biyu ta wuce”

 

Daga d’ayan b’angaren Fahad yace “marainin wayon naki bayanan saiki fad’an Inda kike zanzo na d’auke ki”

 

Gabanta yayi mummunan fad’uwa _ba dai da gaske ya ajje driving d’in ba_

“Kin min shDireban Gidan Mu Hausa Novel Completeiru ko bakiji ne”

“Ina k’ofar library” ta fad’a a sanyaye.

 

“Ya dai lafiya?”

Lubna ta fad’an tana kallonta.

 

“Wai bayanan Yaya Fahad ne zaizo d’aukana”

 

“Oh my god,shikenan yau bazan ganshi ba,naso na sake ganin kyakykyawar fuskarshi gaskiya ban tab’a ganin kyakykyawan namiji kamar Aliyu ba,ina son shi matuk’a”

 

“What?so fa?”

“Eh”

“Wane so bayan akwai engaged a kanki da Besty ko kin manta?” Janan ta fad’a cikin b’acin rai

 

“Na sani”

“Kin daina son Bestyn?”

“Kamar ya bayan har an mana baiko”

“To su biyu zaki aura ne?”

“Ya kike min tambaya kamar ‘yar jarida?”

“Dole na miki saboda kin bani mamaki wallahi”

 

Dariya tayi tace “kin San dai bazan tab’a auren direba ba barema direbanki,kawai ina son soyayya dashi ne saboda in fita kunyar friends dama ace yana da kud’i zan iya barin muktar na aureshi amma in rasa wazan aura sai direba”

 

“Amma kuma zakiyi soyayya dashi”

 

“Eh direba baya da wani value ai”

 

Cike da mamaki Janan ke kallonta dan batayi tunanin haka daga bakin lubna ba.

 

“Baya da value fa kika ce?shi ba mutum bane ko ba Allah ne ya hallicce shi ba?”

 

“Shi mutum ne amma talaka baya da daraja a waj…………”

 

“Dakata lubna” Janan tayi saurin katseta.

 

“Na tsani a wulak’anta d’an Adam”

 

“Ai ba wulak’anta shi nayi ba,ina son shi amma bada aure ba”

 

“Kina son yaudarar zuciyarshi,lubna karki cutar da d’an Adam baki San lokacin da zai miki rana ba”

 

“Amma kuma ke kike wulak’anta shi?”

 

“Laifi yayi min amma ni ban tsaneshi ba kuma banji dad’in abinda kikai ba”

 

“Oho dai nikam sai anjima” da sauri ta bar gurin.

 

Tana tsaye tana tunani har Yaya fahad ya k’araso,da sauri taje ta bud’e gaban mota ta shiga dan ta San halinsa da fad’a.

 

Suna cikin tafiya ta kasa daurewa tace “Yaya kamar ma daga office kake?”

“Eh”

“Ina drivern yake”

“Oho ni dai kawai mameey tace in biyo in taho dake”

 

Bata ji dad’i ba dan har ta fara zargin kanta amma ba damar ta fad’a ma fahad.

 

Har suka isa gida yana ta surutu amma amsar da take bashi bata wuce um ko um um.

 

Suna zuwa gida ta shige bedrum ba tare da tayima kowa magana ba.

 

Tana kwance kan gado kusan minti talatin tana tunanin Ali meyasa ma tayi masa haka.

 

Tashi tayi zaune ta d’an ja tsoki tare da fad’in _akan me zan damu kaina?idan ya rasa aikin shi yayiwa Kansa_

 

Cire kayanta tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta shirya ta fito falo..

 

“Mameey Aunty Fauzah bata dawo ba?”

 

“Eh sai six”

“Okay bara naje gun Abba muyi hira”

Bata jira amsar mameey ba ta wuce side d’in daddy.

 

Sati guda babu Ali ba labarinsa dan kullum Fahad ko Fauzah ne ke kaita skul tana son tambayar ko lafiya amma ta kasa tunda babu Wanda yayi mata zancensa ko Fauzah da take tunanin zata fad’a mata wani abu game da rashin zuwansa.

 

Yau kam bayan sun fito daga lecture ta kalli Raihan tace “yau sati guda Ali baya zuwa tun ranar Dana fad’a miki na zageshi”

 

“To ke meya dameki?”

 

“Dole in damu Raihan,wallahi kusan kullum da abin nake kwana a raina”

 

“Son shi har yayi girma haka a zuciyarki”

 

 

Da sauri suka juya dan ganin mai maganar.

 

 

 

 

 

 

_Alk’alamin Sadeey_✍

[9/29, 8:13 AM] Aishat A Muha’d: 🍁🍁🍁

*DIREBAN GIDANMU*

🍁🍁🍁

 

 

_by_

_*SaNaz deeyah*_👄

 

 

“`Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv“`

 

 

03

 

Lubna ce ta k’araso fuskarta d’auke da murmushi tace “ai na dad’e da sanin cewa direbanki kike so hakan ne yasa kika daina min magana na tsawon sati tun lokacin da kikaji nace zanyi soyayya dashi,Besty ma yace zaizo yaji dalilin dayasa kika daina kulani”

 

Ran Janan ya b’aci sosai da har baza tayi mata magana ba amma jin zafin abin yasa tace “ke kika ja na daina miki magana domin talaka da mai kud’i matsayinsu d’aya a gurin Allah,Wanda yafi wani shine wanda yafi tsoron Allah”

 

“Hmmm to ai saiki aureshi tunda kina tausayinsa”

 

Duk kansu suka mik’e tsaye..

“Zan iya aurenshi tunda ba haramun bane”

 

“Kin ga sai a buga a jarida da gidan radio cewar ga wata ta auri direbanta”

 

‘Daga hannu tayi zata mareta,Raihan tayi saurin rik’e hannunta.

 

“Ki sakeni in nuna mata kuskaranta meyasa zaki hanani Raihan?”

Tayi maganar tana zubda hawaye.

 

Nan da nan jama’a suka taru.

 

Lubna kuwa tayi ta fad’a tana cewa a barta taga me zatayi mata,dan Asara ta rasa wa zatayi soyayya dashi sai drivernta.

 

Kuka sosai Janan take yi,Raihan tayi saurin janyeta suka shiga cikin lecture hall d’in.

 

Tunda ta shiga kanta yake a k’asa tana kuka,su Khalid ‘yan dprtmt d’insu suka zo suna tambaya amma Raihan tace su k’yaleta kawai dan kar abin ya sake damunta.

 

“Gaskiya lubna bata kyauta ba ai babu dad’i dizgi”

Zakiyya tayi maganar lokacin data dafa Janan.

 

“Ki k’yalesu kawai na San dole zasu shirya sun samu tsab’ani ne kawai”

 

Janan ta d’ago kai ta kallesu,fuskarta sharkaf da hawaye tace “a cikin taron jama’a tayi min haka,to zan aure shi zanyi soyayya dashi inga abinda wani zaice ko kuma naga abinda zatayi sai ta kaini gidan radio da hujja” hawaye ta goge ta d’auki jakarta ta fita.

 

Raihan na mata magana ta shareta kawai.

 

Napep ta tara abinda bata tab’ayi ba,kwatance tayi masa ya kai ta har k’ofar gida.

 

Tayi knocking maigadi ya bud’e ganin itace yasa shi saurin matsawa.

 

Tana shiga taga Ali zaune a kan bencin maigadi.

 

Ta d’an kalleshi fuskarta d’auke da hawaye,shima idonsa a kanta yake,kamar zata masa magana sai kuma kawai ta wuce ciki.

 

“Uhmm yarinyar nan akwai rigama”

 

“Da wulak’anci ba”,Ali ya fad’a yana kallon inda ta wuce

 

” ai bata da wulak’anci akan yayarta”

 

“Allah ya shirya”

“Amin”

Maigadi ya amsa.

 

Tana shiga bata Tatar da kowa a falo ba,dan haka tayi saurin wucewa bedrum d’inta.

 

Wani sabon kukan tayi mai isarta sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa..

 

Tana fitowa taje bakin mirror ta tsaya tana murza mai a jikinta ta kalli madubi taga yadda fuskarta ta d’an kumbura.

Mai ta murza a jikinta ta fesa turare sannan ta zura doguwar riga nylon ta fita.

 

‘Dakin mameey ta wuce,tarar da ita tayi a kwance hannunta d’auke da waya da alama ta gama amsa kira ne.

 

Zama tayi kusa da mameey tayi shiru na tsawon lokaci sannan tace “mameey bakiga na dawo ba?”

 

Tashi tayi zaune ta kalleta tace “mamaki kika bani ai”

 

Murmushin k’arfin hali tayi sannan tace “mameey ina son in fara sanin yadda talakawa keji,saboda ban San inda rana zata fad’i ba”

 

“Amma kin San wannan ganganci ne ko?kin san halin babanki sai yayi fad’a”

 

“No mameey pls karki fad’a masa kinsan zaiyi fad’a”

 

“Oh kinsan da hakan amma kika dawo ba ki kira an d’aukeki ba?”

 

“Am srry Baran kuma ba”

 

“Ki kiyaye”

 

“Insha Allah mameey”

“Yawwa”

“Mameey ina Aunty Fauzah?”

“Tana skul”

“Okay Yaya yana office ba?”

“Kema ai kin Sani”

 

Hira suka cigaba dayi cikin raha da annashuwa.

 

Ranar dai haka ta yini duk abinda take sai ta tuno Ali direba har ta fara zargin kanta akan maganar lubna.

 

*********

 

Tana jingine da fuskar gadon hira suke k’asa-k’asa.

 

Fauzah dai duk ta rasa mafita gaba d’aya gani take kamar abinda take shirin yi ba mai d’orewa bane.

 

“Gaskiya ina tsoron abinda nake shirin yi Zuby”

 

“Ban gane tsoro ba”

“Saboda duk abinda nake yi ina yinsa ne a b’oye wallahi duk ranar da aka gane na shiga uku,musamman Janan da ta samin ido zata Iya b’aro jirgina”

 

“Hmmm Fauzah kenan,Janan kike tsoro k’aramin alhaki,kefa macece karki bani kunya mana”

 

“Amma zuby karki manta *direban gidanmu* ne fa”

 

 

“Sai me a ciki,naga shima d’in d’an hannune da kinje masa da buk’atarki zai biya miki”

 

“Ta ina zan fara”

“Ki fara kamar irin kina son shi sai daga baya kina saka kayan da zasu ja hankalinsa kin gane ai”

 

Murmushin k’asaita tayi sannan tace “zan k’ok’arta”

 

**********

 

Yau da wuri ta shirya dan bata so tayi latti.

 

A gurguje ta kammala break fast sannan ta samu mameey a d’aki tayi mata sallama.

 

“Kin fad’ama driver?”

“Eh tun jiya na ce masa ina da lecture k’arfe 8”

“To Allah ya tsare”

“Ameen mameey”

 

Da saurinta ta fita dan gani take kamar zai gudu.

 

Tana isa taga ya bud’e mata back seat duk sai taji ba dad’i duk da dama haka yake mata ko yaushe..

 

Sun fara tafiya tana son tayi magana amma zuciyarta na bugawa haka tayi shiru ta kafa masa ido yana driving abinshi.

 

Suna shiga gate a dai-dai central mosque tace ya tsaya

 

Parking yayi kamar yadda ta umarceshi,ta d’auki jakarta har ta fito sannan ta juyo tace “kayi hak’uri da duk abubuwan da nayi maka insha Allah bazan sake ba,zan kiraka idan mun gama lectures”

 

“Masoya yau kuma anan aka keb’e”

 

Da sauri suka juya suka kalli ko wacece dama ita Janan ta san itace.

 

 

 



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Direban Gidan Mu Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!