Hausa Novels

Diyam Hausa Novel Complete

Diyam Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: diyam

“Madaidaicin dakin karatun mai dauke da dalibai 36 yayi shiru bakajin motsin komai sai na takardu, sai kuma very clear voice din lecturer da take gabatar da lecture ga dalibai masu karantar ilimin law a makarantar Blavatnik school a cikin Oxford University.

Darasi ne suke yi akan marital laws, inda malamar take yi musu bayani dalla dalla game da dokokin da suka shafi auratayya.

Saboda kasancewa daliban sunzo ne daga mabanbanta kasashe, wannan yasa malamar take daukan kasashe daya bayan daya take musu bitar dokokin kasashen da niyyar in sun gama sai su hadu suyi comparing aga wadanne ne sukafi kyau kuma wadanne chanji ya kamata a samar.

A yau ne kuma malamar tashigo kasashen nahiyar Afrika. Ta fara da Nigeria, the giant of Africa. A nutse ta fara karanto wa daliban dokokin da kasar Nijeriya take dasu wadanda suka shafi auratayya.

Suna tsaka da daukar darasin ne suka ji snicker, malamar ta dakatar da karatun da take yi ta dago kanta a tare da duk sauran daliban suka kalli sashen da dariyar ta fito.

A extreme end of the class room, sitting alone like an abandoned island, wata kyakkyawar budurwa ce wadda kallon farko in kayi mata daga nesa zaka ce kyakykyawa ce, in ka matso kusa da ita kuma sai kaga tafi yadda kake tunani kyau, as kana cigaba da kallon ta kyawunta yana cigaba da bayyana a gare ka.

Da yawa a makarantar ana yi mata kallon balarabiyya amma nigerians suna ganin ta suke fahimtar cewa tasu ce, kabilar fulani ce, kabila mai dangantaka da larabawa.

Daga ganinta zaka fahimci ita kanta bata san cewa tayi dariyar ba. Shirun da taji ajin yayi da kuma feeling na cewa ana kallonta ya saka ta dago kanta da sauri, dara daran idanuwanta a bude kuma ta saka su a cikin na malamar da take tsaye a gaban desk dinta.

Suka tsaya suna kallon kallo sannan malamar tace mata “why do you laugh? Are you finding this funny?” Ta girgiza kanta da murmushi a gefen kumatunta.

Malamar ta koma kusa da podium ta tsaya tana kallonta sannan tace “where are you from?” Still kanta a kasa tace “Nigeria” malamar tace “menene ra’ayinki game da wadannan dokokin na auratayya a Nigeria.

Kina ganin sunyi dai dai ko kina da gyara?” Shiru ta sake yi na wani lokaci, sannan tayi karamar dariya tana girgiza kanta, fuskarta na nuna cewa akwai abinda yake damunta, suddenly kuma sai tayi magana “bani da gyara ma’am.

Saboda all those laws da kike lissafawa a rubuce kawai suke, maybe for the sake of the likes of you da zasu nema for educational purposes, amma ba wai amfani ake yi dasu ba” malamar looked interested, tace “so, can you tell us the situation of marriage in Nigeria?” Nan take murmushin fuskar budurwar ya dauke, ta hadiye wani abu a makogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta tana kallon rubutun da yake gabanta.

“You have a very beautiful handwriting kanwata” taji muryarsa a kunnenta as clear as if yanzu yake gaya mata.

Ta dago kanta tace “in Nigeria ma’am, northern Nigeria to be precise, marriage is just like a form of legal slavery” gabadaya hankalin yan ajin ya koma kanta, har wadanda ada suke yan rubutun su yanzu sun juyo suna kallonta.

Ta cigaba cikin yaren turanci mai dauke da nigerian accent “tabbas kafin aure akwai kalmomin i love You, amma yawanci a baki suke tsayawa basa karasawa zuciya, daga zarar anyi aure miji will have a feeling similar to feeling din da master yake ji a lokacin daya sayi slave.

Like since I pay your dawry it means like I own you, you belong to me. Sai ya manta da cewa shi da matar belong to each other. Wadansu mazan ko first year ba zata wuce ba zasu juye su zamarwa matar like total stranger, like bata taba sanin sa ba a rayuwarta.

Surbajo for life.

 

 

Name: [DIYAM HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


Leave a Comment

error: Content is protected !!