Hausa Novels

Doctor Eshaat Hausa Novel Complete

Doctor Eshaat complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Doctor Eshaat Hausa Novel Complete

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

Bismillahi rahmani rahim

 

 

1️⃣&2️⃣

 

Tafiya take a hankali kamar bazatayiba Kuma gashi gari ya akwai hadari sai iska mai karfi hade da kura ama ko ya damaita, tafiyanta kawai take ciki kwanciya hankali kamar ba komai.

 

 

A gaban ta kadan na hango Yar black beauty

 

Ta juyu tace” Essha Essha takirata har sau biyu kiyi sauri fa imbahakaba walahi zan wuce kisan zamu iya rasa Nepep a yanda gari yake a haka ko? Ama wance aka Kira da Essha ko d’ago kanta batayi ba sai murmushi ta kawai takeyi,

 

can naji wani sauti murya lalausa nacewa haba bestie nasa ki,Kona ki tafiya nasa dole ne kijirani,wance aka Kira da besty ta nufota ta zungure mata kai tace” walahi Allah Essha kina kureni.tace”haba bestie yihakuri kimin afuwa ta rike kunne,

ok naji yi sauri munkarasa gida, Essha ta amsa da tomuje.

 

Suna fitowa baki hanya sukayi sa’a Nepep. Bestie tace” mishi Mai Nepep Bukar Ari’i zamuje ta Yumaco, mai nepep ya amsa da ok nagane shigo muje. Suna shiga suka Soma hira biki da suka fito na wata Yar ajisu. Essha tace”

kisan maiye besty? Bestie tace ni akuyane da zan sani, sai kawai duk suka fashe da dariya, ama wlh guri KAMU na ya burgeni da kiyyi niyya aure kenan sai mugayato Mai decoration din ta miki cewa Essha.

 

Bestei tace” Lallai yariya ki rainani ke baki ce zakiyiba sai ni. Essha ta Bata amsa da iyye toh ni wlh Banda niyya aure.inshaallah sai nayi karatu likita.

 

Ni da Allah kiyi shiru da wanna batun bakisa fa nufi Allah.ba sai dai kice haka. Cewan bestei.

daidainan mai nepep yace” mun’iso fa cewa Mai Nepep;

yawwa ga kudika mun gode.

 

 

Bayan sun sauka Essha tace” Toh besty saina shigo anjima tafada tana murmushi,da Allah min shiru haka jiya kika shayani baga ki ba, please forgive me natsaya waya da Khalid ne har nayi bacci . Naji ,Khalid kam Yana ban tausayi tundashi yayi niyya aure yanzu kekam ba tabbas cewa besty.ni da Allah ki kyalleni Bata soyaya da aure nakeyiba,karutuna kawai.toh Essha Allah yazabe mana mafi alkhari. Ameen ta amsa ta shige gida.

 

Assalamualaikum? Wa’alaikumusala Amir ya amsa kanita Mai bi mata.mufeedat autarsu ta taso da gudu tazo ta rugumeta, Oyoyo Sis Essha ,yawwa autar mummy. Ina mummy ? Tana kitchen,kisan daddy Yana azumi yau alhamis, Eh hakane.baza naje na same ta, Wai Walid baka gani bane? Oh sorry sis,game Dina ne yatafi dani,kisan motar race Dina inbaka concentrate ba zaka fadi, dats y naki juyawa,Kuma sis saina fiki iyawa. Common jare yimin shiru naji. Daddy ya dawone? Eh ama su fita da khairat sunje chemist ta taka kusa. Subhanallahi Allah yakiyaye na gaba.Ameen duk suka amsa.

Ta wuce kitchen wurin mummy. Mummy? Mummy? Mummy? Na’am haba Essha wana Kira haka kamar kiyi makanta,ko sallama fa bakiyi min sai kwala Kira cewa mummy.ohh so sorry mummy na.ya gida? lafiya lau.ya Kamu toh,wallahi mummy baki ga guri ba ya hadu,bara kigani. A Ina akayi mummy ta tambaya. A Ta’al Conference Hotel ne. Tafito da wani hadede waya daga ciki jakata sai walkiya yakeyi( iPhone x+)kenan.

Mum kigani,wow ama ya hadu, amarya ma turbakallah .ai mummy Bari kawai sufito amare. Kedai kalleni da shirmeki kije ki chanza Kaya kizo kishirya mun kan dinning daddy ku yakusan dawowa cewa mummy. Essha tace Wai wazai gamin khairat yanda za’a ririta kafana.kedai baruwaki jekiyi aiki Dana saki. Kk mummy. Ta wuce dakita gwani kyau dashi.tana chanza Kaya ta dawo ta Taya mum na jera Kaya aka dinning.suna gamawa aka fara Kira sallah mahgrib .

 

 

Doctor Essha

By J hajara

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
 

3️⃣&4️⃣

 

Kowa yatashi sukayi sallah,suna jira daddy su yadawo.can sai gashi sun shigo shi da khairat.

Assalamualaikum? Wa’alaikumusalam duk suka amsa. Welcome back dad? Yawwa Amir. Wai Ina autar gida na ne? Walid ya amsa da cewa ai Tana jika daddy Wai tayi fushi da Kai,kafita da khairat baka fita da ita ba. Haba autar daddy zo yi hakuri,kiga khairat ciwo taji a kafa zo ga ice cream na kawo Miki ke kadai Zaki Sha Kar kiba kowa kijiko? Eh ta daga Kai Tana musu gwalo. Duk suka za zauna a dinning, mummy tayi serving nasu.wata hadadiyar farfesu kazane ,sai white rice& stew da coslow da coconut juice.kowa yayi shiru ba abunda kakeji sai Kara cokali. Daddy yakashe shiru da cewa Essha kiduba Jamb naki ko? A’a ,sai da safe Ina shiga gidasu summaiya( besty)zan duba .saboda nayi register da number tane,ok Allah yabaki nasara.Ameen.

Mummy tace toh Abba Essha ya magana tafiyamu bikin kaduna gashi gobe Friday? Yace eh dazun muyi waya da hajiya na tace itama zantaje,na mantane ba fadamikiba.mummy Nima zanje? Cewa walid.a’a maganar haddu ku,Kai da amir, khairat babu inda zukuje, mum nifa inji mufeedat? A’a autar daddy zabarki a gida da sister Essha da daddy ko,saura naji wani yatabata acikiku, kuga abinda zamuku. Oh mummy ki shagwaba yariyana Allah amir cewar amir.eh din kubar min kayana.

Daddy yakalli mummy yace my dear inaga fa bazaki samu zuwa ba Essha ne zantaje ita da hajiya na. Essha da ji haka nandanna ta kore . Kowa na rige rige Bata ruwa. Mummy tace ya’akayi haka? mummy korewa nayi. Sannu ,ko magana tafiya ne? Ta amsa da a’a daddy . Toh gobe kishirya da misali karfe biyu zaku wuce da hajiya da driver,Nan take taji gabanta ya fadi tayi shiru. Amir yace Sis Essha daddy na magana fa, na take ta dago Kai tace toh dad Allah yakaimu ameen daughter bakiso tafiyane ? Cewa daddy,mum ta amsa da cewa ai dole taje, kasan Bata taba tafiya ba. Walid yace Nima mum banta ba bafa . A’a ku sai next tym zakuje inshallah.toh daddy. Akira sallah Isha duk suka Mike. Amir da Essha suka kwashe plates zuwa kitchen, khairat na tsokanarshi,yace Zaki warke ai Kuma zan Rama, Eh din ta amsa. Zan kamaki ai, mum ta amsa da cewa khairat baki da kunya ko? Yaya ki kegayama haka? Mummy kiyi shiru ki kyaleta zan kamata ai.

Essha tace haba babba yaya,Yaya amir kamata afuwa kasan Bata ji dadi jikita.naji. duk suka Gama kwashe kaya.su amir da daddy suka wuce massalaci ,mum ta wuce room dinta,su khairat ma haka.

Essha na shiga dakita ta fada wanka sanan tayi alwala ta fito, Tana fitowa tasami wayata nata Kara.tana dubawa taga k.suna data sa a number Khalid.tayi pick yanata sallama taki amsawa, daya bangare naji Yana cewa Haba soulmate harda sallama ne kike fushi dashi? Ta tura baki kamar Yana gabata tace toh bakai bane .haba love kiyi hakuri bazan karaba, ta amsa da cewa aguri nafa munjira ka,har tsawo two hours baka zo ba har aka fara iskana fa. Da Allah kiyi hakuri love, Allah daddy na ne ya tsayar dani. Ohh shikena tunkace daddy ne ba matsala. Yawwa tawa, toh yakike,lafiya lau, ya biki kamu. Lafiya. Saura namu Koh? Tayi shiru Bata amsaba.yace yakikayi shiru ? Can ta amsa da Allah yanunamuna. Essha yakamata kibar magana school dina. I promise u inkizo gida na zanbarki ki karasa . Tace ni gsky a’a don bayarda da cigaba karatu mace a gida mijitaba, gwara kawai tayi a gidasu. Ama love bakiyarda dani bane nayarda mana . Hmmm yaja dogo nufashi, toh yanzu sai yaushe zangaki? Ina ga fa sai Monday ranar da zamu dawo. Ina zaki? Biki zamuje ni da hajiya a kaduna. Eyya ni gaskiya tafiya biki na bai kwanta min ba ya fada. Wlh Nima haka don inaji wani matsanaci faduwar gaba narasa dalili. Kita addu’a kiji ko? Allah ya shige mana gaba ta amsa da ameen. Da Allah love ki kulamin da kaki? Kar kadamu. Ok ki gaida mun hajiya zantaji good night sweet dreams.take kashe wayata. Ta nufi baki gado ta zauna, inta fa gaskiya tafiya kaduna nan bai kwanta mata ba. Ta naji a jikita kamar wani abun zai samaita. Can tace auzubillahi

 

 

 

 

 

Chimaa I miss u

 

 

*Doctor Essha*

 

 

Writen-by- j hajara

 

 

 

 

 

 

5️⃣& 6️⃣

 

 

Tace” auzibillahi ta kori shaidan ta Mike ta shimfidar danduma ta gabbata da sallah Isha Tana idarwa ta gabatar da Azkar tana gamawa ta Mike ta nufi wardrobe ta ciro wata simple pink gown na bacci tasa yakai mata har kasa. Ta dauki hijab tasa,ta fito parlor.

 

 

tasamu suna kallo tashar B4U movies asa film din ENTERTAINMENT kowa sai dariya( sbd film din na barkwaci ne). Jiki a sanyaye ta nufi daddy ta tsuguna, daddy yace” ya akayi daughter?

 

Daddy dama inaso naje gidasu sumy ne,inaso zaduba jamb.

 

Daddy yace” Essha maiyasa baza kibari da safe kiduba? Essha tace” A’a daddy gobe fa da karfe 7:00am ina da lecture Kuma fa bazan dawo ba sai 6:00pm,

 

toh kije Kar ki Dade, ga amir ya rakaki.

 

Oh daddy amir ya fada Yana tura baki,

daddy yace” yimin shiru basan tauri kai tashi kuje .

 

Suka fito suka shiga gidasu sumy( bestie) dayake tsakanisu ba nisa. Gate nasu Essha na kalo nasu sumy . Suka shiga da sallamarsu . Aka amsa,

su tarar da dad, mom sai Yaya nazeer (babba yaya sumy). Amir sai mita yakeyi kasa kasa Yana tura baki. Mum ta tambeyeshi Wai wayataba kane?

 

Ya amsa da cewa ba Sis Essha bane nandana ba nisaa shi ne sai na rakata. Yaya nazeer yace” haba boy, inbaka rakata ba waye zai rakata? Essha tace” shareshi da Allah big Bros ka kulashi ne.

 

Amir yace mum kijita fa? Yi hakuri amir.

 

Mum Ina besty? Tana daki,tace” okay bros one minute ta daga ma amir yatsa. Yamaka mata harara, sai sanan daddy su sumy yace” amir ya school, lafiya klau, toh Allah yabada sa’a, Ameen daddy.

Daddy yace”yanxu dai amir ku girma ku daina Kira mana sallah koh? a’a daddy ba time ne. Toh a gyara kajiko,

Inshallah daddy.

 

Essha daki sumy ta haura, daki yayi kyau, teddy ne manya manya guda biyu sucika sama bed, tayi sallama bataji ba, da allamu waya takeyi. Don sai murmushi takeyi. Essha tace” ke Wai da Allah dawa kike waya ne? Sauri fa nake zan wuce. Ta” amsa da Rabin Raina mana, Wai bashir? Eh man. Toh da Allah ki katse Kira Nan don nasa bagamawa yanzu ba, abun zanduba a wayaki, ga amir na jira na a kasa.bestie tace” Naji naji Essha. Sweetheart zankiraka anjima kasan inbana kashe yanzu ba Essha hanamu sakewa zatayi.daga cikin wayan ya amsa da okay bye ki gaisheta,

 

Tace”zantaji bye.ta katse kira.essha Tace”

Bestie wayaki zakiban jamb Dina zan duba sauri nakeyi.

 

Ok gashi , sumy ta Mika mata. Tana dubawa, Sumy tace “dazu muka Gama waya da mutumiki, Wai da Allah zakije kaduna da gaske?

 

eh Esshata amsa da Kai,

 

sumy ta marairace fuska tace “eya bestie zanyi missing naki gashi zaki wuce bani. Karkidamu bawani dadewa zamuyi ba Monday zamu dawo, Kuma kiga shiyasa na shigo na sallameki gabadaya, Allah sarki ni Khalid ne yaban tausayi, Wai yanaji wani iri a jikishi kamar kar kiyi tafiya na. Wlh Nima hk bestie tun lokaci da dadnina ya fadamin nakeji faduwar gaba. Toh Allah yasa yazama alkhari ameen. Can sukaji Kara shigowar message a wayar sumy. Suna budewa suka sa ihu sanda su mum suka firgita, ya nazeer da gudu ya hauro . Yana tambayasu Mai ye samaiku, ba mgn sai murna. Sumy ne ta Mika mishi wayata, Yana dubawa yaga jamb results din Essha tasamu 252🤗. Yace” wow little sis congrats,

Thanks Yaya ai dole kiyi ihu, Essha buriki yakusa cika. Mum da dad suka hauro . Maiye faru? Ya nazeer ya gayamusu. Wow congratulations daughter ; Thanks ta amsa . Ta juya tace mum sai da safeku da murnata, sumy tace” bazaki jira na raka kiba? a’a na hutar dake . Tana sauka tasamu amir tace” tashi muje yace yadai sis da wuri haka? Eh ta fada. Suna tafiya a hanya Tana bashi labari Jamb nata har suka karaso ciki gate nasu, sai murna yakeyi kamar shine yasamu. Suna karasowa ta tsaya Tana ma gateman mgn aka ya kulle gida bamai fita. Ya amsa da toh. Amir ya wuce ciki ko sallama baiyiba yace” mum,dad sis Essha tasamu 252. Mum tace Allahu akbar, alhamdullila. That’s my daughter ai tayi gado na ne, daddy yace” ah ‘ ah abun gori ne, ai sai duka suka fashe da dariya, dad yace” Ina Essha din? Amir yace Tana zuwa daddy kafi yagama rufe baki sukaji sallamarta, su amsa kosa na mata congrats. Walid yace” sis Essha dole na poping Miki champagne a jiki kiyi kokari . Tace” walahi Kar ka kuskura, Allah daddy kayi mishi magana.

 

A’a walahi daddy sai na mata ai Ina tayata celebration ne Koh? khairatTace” eh man, Nima zantayaka. Duka su biyu suka nufi dinning area, khairat ta bude fridge ta fitar da champagne guda ta rike daya tabama Walid daya. Duk suka nufota,suka balle murfi, suka fara mata wanka dashi, daddy ne ya dakatar dasu, yace”ya isa kar kusamin likitana tayi mura. Essha wani University kikasa? Tace’ Dad A.B.U(Ahmadu bello University z). Daddy yace”Oh natuna, yanzu dai kowa yaje ya kwanta kuga har autana yau tariga ku bacci. Amir da Walid suka amsa da ok dad, good night, yawwa good boy’s Allah yatashemu? Ameen. Mum tace” Essha zo ki dauki mufeedat ki kaita daki,toh mum. Khairat tama mum,dad peck a kumatu , tace” mum dad goodnight? Daddy yace kiyi addu’ a fa kamin ki kwanta dun nasaki. Daddy I will inshallah bazamantaba. Good yace. Suma suka nufi nasu daki. Essha na kwantar da mufeedat itama ta wuce zuwa nata daki. Wanka ta karayi sanan ta canza kaya, ta dauki wayata, ta bude WhatsApp ta daura results nata a status, friends nata mata congrats, Tana musu reply. Sai around eleven tayi addu’a bacci ta kwanta. Aciki bacci Bata samu nutsuwa ba sai mugaye mafarke mafarke take tayi,nandana ta farka da wani Kara sanda mum da dad suka farka, da gudu suka karaso dakita, da sauri su karaso wurita. Dad yace” lafiya Essha? Maiye samaki? Bata iya amsawa ba, sai ajiya zuciya da zufa ta ketayi. Mum ta dauko ruwa Mai sanyi ta bata, ta yayye mata gashi kanta da ta barbazo a fuskata tace” sannu Essha, maiye samaiki, zatayi magana daddy yatare ta da cewa yi shiru Essha ba ‘ afada mugaye mafarki. Ta gyada Kai Alama gamsuwa. Mum tace” yi addu’ a ki canza gefe kwanciya kijiko? Eh ta amsa murya na rawa. Mum da dad suka fita a daki jiki a sanyaye . A zuciya ta tace ya Allah ka kawomin dauki basan maike shiri faruwa Dani ba.

Washe gari a makare ta farka around 7:00am tayi sauri sauka da addu’a tashi a barcci a bakita, tayi sauri shiga toilet ta Dora alwala tafito da shimfidar danduma ta gabbata da sallah asuba ta Dade zaune Tana addu’a, Tana shafawa, ta Mike ta dauki wayata Tana dubawa taga missed calls din Khalid ne Dana besty, suka cika waya, batayi harama kirasuba, dun tasan besty ta shiga lecture , Khalid Kuma intakirashi ,. Za su iya jimawa suna waya gara taje ta gaida su dad, inta dawo ta kirashi,. Ta jawo teddy slippers nata dake karshi gado ta saka, ta fito jiki a sanyaye, ta Tara dasu amir a parlor suna karatu, duk suka hada baki sukace” good morning sis ? Ta amsa da fara’a da morning my joygivers, how was ur night? Suka amsa da alhamdullila, Ina mum da dad? Dad yaje dauko hajiya,

 

dakashi? Amir ya amsa da eh Wai batask driving bala driver Wai yacika gangaci, toh Allah yakawo su lafiya, ameen. Ina mum da Kareema(Yar aikisu) ta tambaya? Suna kitchen suna hada ma hajiya koko da kosai. Walid yace” wlh hajiyan nan tacika iyayi,mum tafito daga kitchen ta amsa iyye Walid mamana kake cewa tacika iyayi? A’ a mum afuwa da khairat nakeyi, oh nine sa’a ka koh? A’a goggo khairat () mayarda wuka. Taja kwafa. Ina kwana mum, lafiya. Mum tace” zonan Essha ta taho a hankali. Zauna mgn zamuyi, maike damuki? Na lura tun lkc da daddy ki yamiki mgn tafiya ki ka rage walwala, kobakison tafiya ne? Aa mum. Toh kisanki ranki kinjiko baby, Yan uwanki na kaduna Basu da matsala Kuma ai ba wani dadewa zakuyi ba, yau Friday, Sunday ko Monday zakudawo inshallah ,ki sanki ranki kinji ko, eh ta daga kai. Yawwa humaira n, bani wanan smile naki nan, ta washe hakora sai shining sukeyi, yawwa dats my doctor ( inkanaso ga ni fariciki Essha toh ka Kira ta da doctor). Toh ki Taya Kareema hada Kaya breakfast, kinga daddy ki sun kusa da gari lafia, sai kinje ki hada kayaki ko? Owk mum, ta wuce kitchen ta Tara da Kareema na jerewa a ciki tray, tace” kawo natayaki, Ina kwana aunty Essha? Llfy , yasu ummaki? Lfy. Yawwa hada flasks sai kizo ni zanfitar da wanan. Kareema tace” nagode anty, suna Gama jerewa tace “mum baza naje nashirya, okay sai ki fito.

 

 

 

 

 

 

 

More comment more typing

 

 

 

 

Comment

and

share

 

 

 

Doctor Essha

 

Written-by j hajara

 

 

 

 

 

 

7️⃣&8️⃣

 

 

 

WACECE ESSHA

 

 

Asali sunata *AISHA AHMAD* haifafiyar gari uke ne, dake jahar Nasarawa . Mahaifita cikaikenyin suna shi AHMAD YUSUF NOMA, Dan asali gari uke. Aiki ne ya dawo dashi gari Lafian bare bare da zama.

 

 

Matar daya hajiya Fatima, Yana da kanne biyu, Alhaji Adam(daddy karami) da Aunty Jamila suna kirata da(big mum)Tana aure a kaduna,

Mahaifisu ya jima da rasuwa, yanzu maihafiyarshi ne kadai a raye, sunata Hajiya maimuna , ama suna kirata da hajiya uke, Tana zama a uke , anyi anyi ta dawo lafia da zama taki.

 

Daddy yata mukammai kala kala tun daga kan councilor,har zuwa Dan majilasa, yanzu hk Yana aiki ne a government house dake lafia.

 

 

Mummy Kuma business woman ce Tana safara zanuwa, Tana da babba shagota a shendam road.

Allah ya albarkaci su da yara biyar, Aisha( Essha), Yusuf(amir), ummulkhairat, Abdullahi( Walid) sai autarsu mufeedat.

Alhaji Adam Wanda akafi sanni da daddy karami, matarshi daya, Mai kirki ( anakirata da auntyn yara) yara shi bakwai, Abdulhamid, salis, aina’ u, khamis, hafsat , hanan sai Hassana daya ta koma.

 

Sai big mum( aunty Jamila) yara ta itama hudu, usman, Yusuf anakirashi da Abba, hunaisat, Sameer tunda daga kanshi Bata Kara haihuwa ba, ayi magani har agaji. Mijata babba Dan kasuwa ne, big mum ta rige su dad aure don Tana da shekara sha bakwai babasu ya aure da ita. Yanzu haka hunaisat za’a aurar.baya tayi candy nata, tace ita aure kawai take so.

 

Essha tayi primary and secondary school nata a Hall mark international academy dake ciki gari Lafia, Ta sauke alqur’ani maigirma da saura littafai na addini, ta zana WAEC nata da jamb last year, batasa mu jamb ba, shiyasa tasake maimatawa har Allah ya Bata sa’a tasamu a Wana shekara, Amir na jss3, khairat da Walid suna Jss 1, mufeedat na nursery 2.

 

Essha hadadiyar yariyace wance bazata wuce shekara shabakwai ba, Tana nan fara ba can ba, baza a sata a siririya ba bakuma za sata a Mai jiki ba, fuskana Mai Dan tsayi, hanci har baki, idon na ya manya manya ba Sosaiba, farare kal kal, lumsheshu, kullum kamar maiji bacci, bakita Dan karami, pink lips gareta, a jiki kuwa ba a magana, dun tana daga ciki jere yanmata da akekira masu coca cola shape, dukiya fulani nan a cike yake dam, haka hips kamar zansu fado.

 

 

 

Kawanta daya tak ko Kuma ice aminiya, *summaiya*, tare suka tashi, tun suna yara har girmansu, sumy ya ce ga Doctor Abbas jibrin, daddyta babban likatane, sai mahaifiyarta hajiya ikilima.

 

Su biyu Allah yaba iyayasu, nazeer, sai ita summaiya, sumy tun last year da suka zana jarabawa tasamu FULAFIA ( federal University lafia) Tana karata mass com.

 

 

Essha tun da taso da buri karatu likita ta taso, sallah ta biyar a kullum sai ta roki Allah yacika mata buri ta. Shiyasa ma Bata kulla samari, komai naci saurayi hk zaigaji ya barta. Sai a kan *khalid*, sun hadu ne a wata super market taje shipping shima naci da magiya yayi ta mata sanan ta kulashi,Kuma ashe abokin Bashir ne saurayi bestie. Shiyasa takara bashi dama .

 

Wanna biki da zasu je a kaduna na yariya big mum ne wato hunaisat.

 

 

 

CIGABAN LABARI

 

Ta gama hada kayata tsab a karamin wani purple trolley, Tana Gama hadawa, tajiyo sallama kareema. Ta amsa.

 

KareemaTace” aunty inason na gyarami ki dakin.

 

Essha tace’ huta abiki Kareema zan gyara.( Essha iri yarane nemasu tausayi da jikan Dan Adam). KareemaTace” toh aunty.

 

Tana aje trolley a gefe bed, ta soma jin ringing din wayata dake gefe side bed.

 

Tace” kareema” da Allah Mika min wayana , tayi sauri ta dauko mata dun tana matukar Bata girma, tana dubawa taga sis hunaisat. Ta daga waya oh amarya .

 

Hunaisat tace” karkimin magana nayi fushi dake, nagama gayawa friends Dina special sister na zata zo tun biki na sati daya, shine kika gwasileni, wato ma ba dun dad yace” ki zo ba bara kizo ba koh? Essha tace” Haba mana my amarsu Allah jamb ne ya rikeni .

 

Toh naji yanzu da wani lokaci Zaki zo? Ina ga fa sai two zamutaso. Eya sis sai two maiyasa? Nine ban dan jin dadi ba,

 

Eya Allah ya baki lfy sis aman ban ji dadin ace duk event din bikina ace ba ki aciki, Wai Kuma sai two zakutaso, haba yantzu fa 9:00 da Allah kuta so da wuri gasu yaya Abdulhamid, su aina’u da hafsat tun shekara jiya suka zo, ama ke har yau. Haba cewa hunaisat.

 

Yi hakuri sis Allah hajiya uke nake jira. Tace” toh dole ne sai ki zo da ita?? Essha tayi dariya ai dole sai dan tsofofi. Oho dai naji saina gaki, ok sai munzo ta kashe waya.

 

Oh ni Essha Wana surutu na hunaisat kamar ba amarya ba,

kareema tace”ai aunty zatayi ta daina, hk yayana ana saura kwana biyu daure aure ta adabi mu da surutu, ranar daure aure kuwa sai kuka Essha tayi dariya tace” lallai kam.

 

 

 Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [ Doctor Eshaat Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

37 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!