Doctor Maryam Hausa Novel Complete
Doctor Maryam Hausa Novel Complete
KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…
[*DOCTOR MARYAMAH*
*By* *Zainab Habib Mom Islam*
_AREWA WRITERS ASSOCIATION_
*MARUBUCUYAR*
ZAINABU ABU
ZAZZAFAR KISHI
LADIDIN ƘAUYE
NANCY ƳAR ƘARYA
JININ ABBANA
LAMARIN ƘADDARAR AURENA
GUGUWAR ZALUNCI
YARINYA MAI TAƁARGAZA
SIRRIN ZUCIYA
AND NOW
*DOCTOR MARYAMAH*
Wanan littafin free ne amma rashin comments zai iya sanyawa ya koma na kuɗi gareku masoya ina godiya da nuna soyayya
*GARGAƊI!! GARGAƊI!!* Duk wanda ya juyamin littafi kokuma ya fitar min dashi wato masu siyar da littafin Allah ya isa haƙiƙa bazan yafe ba dan free ne .
Banyi wanan littafin dan cin zarafin wata ko wani ba hasali ma ƙirƙira ne ba gaskiya bane in yazo dai dai da labari ki/ ka to hasashe ne kawai ina fatan zaku bani haɗin kai.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 1-2
11:am Wata budurwa ce ke gudu a wani katafaren jeji mai cike da sarƙaƙiya ga abubuwan ban tsoro a cikinsa ,bakajin kukan komai sai na tsuntsaye sai nunfar fashi take tana ci gaba da gudun , tana cikin gudunne taci karo da wani ƙaton saurayi dogo fari mai ƙiba ga tsayi dan ganinta tayi wada a gabansa, budurwar da zatayi 19yrs baƙa ce tana da kyan diri kana ga kuma ƙiba amma ba sosai ba duk da tsayin da take dashi sai taga ai wanan mutumin zai iya ɗagata da hannunsa sbda tayi masa ɗaukar basamude “keee ina zaki!!” budurwar taji muryarsa tana amo cikin kunnuwanta ,Antyna nake nema sun kashe ta sun kashe Abbana suna kashe yaya Nawas ni kuma na gudo “budurwar ta faɗa tana mayarda nunfashi tare da kuka , waye kee?”shiru bata bashi amsa ba sai ma rugawa da gudu da tayi bai yi wasu taku mai nisa ba ya cafko ta tare da cewa “ke kinsan koni waye a wanan jejin ?”girgiza kai tayi tana kuka tare da cewa “dan Allah kayi haƙuri ina neman su Antyna ne “wata irin dariya mutumin yayi tare da cewa “babu ke babu ganin iyayenki abda ni akasa na kashesu ke kuma rayuwar jeji ce taki tunda shegun kanki suna firgitani cikin dare , karka cutar dani ka fito min da Antyna dan Allah…..!
Somin taɓi ne inason ganin karɓar da zakuyi masa shiyasa sbda in shirya sambaɗo muku shi cikin lokaci .
Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta
-
Hausa Novel AppApp
-
Hariji By oum Apnan
-
Bariki na Fito
-
Nakasa ba Kasawa ba ce
-
Siradin Rayuwa
-
Bororoji Hausa novel
-
Life Partner Hausa Novel
-
Heedayah Hausa Novel Complete
-
Duniya ta Amna
-
Zaman Hostel Complete
-
Mahabeer Hausa Novel
-
Matar Makaho
-
Banida Gata
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
-
Kyawuna Jarabta ta
-
Jiddatul khair
-
Wacece Ni Hausa Novel
-
Ahali Daya Hausa Novel
-
Abraham Hausa Novel
_AREWA WRITERS ASSOCIATION_ Page 3 -4
Wata irin tsawa ya kuma daka mata wacce take barazanar firgita ta ya juya ta shammace sa ta ruga da gudu har tana shirin faɗuwa , taɗan yi nisa ya kuma cafkota kasancewar gudunsa da nata da ban banci yace “ko kiso ko karki so na zamo mijinki tunda yanzu baki da gata a duniya zan maye miki gurbin kowa naki inma kin koma bazaki ga gidanku ba sbda ya zamo toka!! tama kasa ci gaba da kuka sbda wata irin damƙa da yayi mata kamar babu ɓurɓushin imani a tare dashi tare da zame ɗan kwalin kanta da dogguwar rigar jikinta ya tunttsure da wata iriyar dariya mara daɗin ji yana cewa “haka zaki dinga rayuwa a wanan jeji cikin wanan kayan naki “kallon jikinta tayi daga ita sai bra da ɗan mini skrt bai kai guwai wa ba ta tare ƙirjinta da hannunta tare da kallon irin shigar dake jikin mutumin ,ganye ne sanye a ƙugunsa ga dukka alamu sutura ba damuwarsa bace sbda duk da ganyen daya ɗaure
kwankwason sa dashi bai hana aga wani part na gurin ba ,
kawai da kanta tayi gefe zuciyarta na mata ƙuna , ta durƙusa a gurin tare da ɗaga hannu sama tace “ya Allah kayi min tsari da…taji an bige mata baki har zubar jini ya farayi ta fashe da kuka sai ƙarasa sauran adu’ar tayi a cikin zuciyarta , cafko mata hannu yayi tare da cewa “in kikayi min gaddama zan ɓalle hannun inga mai ɗaukar mataki “babu shiri tabi duk inda ya jefa ƙafa haka suka dinga tafiya a cikin jejin har suka iso bakin wani katafaren kogi ya zauna tare da ɗorata kan cinyarsa yana dariya a karo na barkatai , wata jaka ya ciro dake rataye a kafaɗarsa ya ajiye ta a ƙasa tare da buɗewa ” sai ga hotuna sun baiyana da sauri buruwar war ta miƙe tare da matsowa gurin hotunan hoton mahaifinta ta gani da hoton mahaifiyarta da hoton yayanta duk an ɗiga jini a jiki kuka tasa tana cewa “ka fitomin da su ka fito min dasu bakinta na fitar da jini , fizge hoton yayi tare da cewa “sun mutu babu
labarinsu ya wurga hoton cikin wanan kogi tare da cewa “kogi ka ƙari ƙa samu “waro ido tayi a cikin ranta tace “ƙarin me kuma ?” bayan ya maga jefawa ne ya rungumo budurwar tare da cewa “wanan kukan naki garama ki dena keda rayuwar garinku ko wani guri kunyi bankwana nima matata ce ta mutu tama fiki kyau shiyasa zan maye gurbi dake bari in samo miki kifi a rafi “ya ƙarashe maganar tare da miƙewa ya faɗa kogin sai gashi ya fito da wani tafkeken kifi a hannunsa , ya samo dotse ya haɗa ciyayi da wasu busassun ƙirare ya haɗe
duwatsun guri ɗaya sukayi wuta ya soke kifin da wani dogon icce ya fara gasawa , cikin ƙanƙanin lokaci kifin ya gasu ya yaje ya samo ganye mai girma ya sanya kifin a kai tare da raba kifin gida biyu sbda yayi saurin hucewa , duk wanan aikin da yake budurwar ko kai hankalinta gurinsa batayi ba sbda haushinsa gami da tsanarsa da takeji a ranta , ajiye mata kifin yayi a gabanta tare da cewa “maza kici “bazanci ba “ta bashi amsa ba tare da ta tsorata ba , kallonta yayi da manya manyan jajayen idanu yace “zan wurgaki cikin rafinnan “ganin baya dariya ko yayi ma sai dai kaga haƙwara yasa ta tsorata dan a rashin imaninsa zai iya ta fara ci babu wani daɗi amma haka ta dinga ci kamar zatayi amai tayi rabin kifin daya miƙo mata tace “ta ƙoshi “wani kallo da yayi mata ne ya sanyata ce babu shiri , sai da ta ciye tsaf sanan ya ɗauki ɓarin kifin ya wurga cikin ƙogin yace “ga kifi na baka “ita kam wanan lamari na firgi tata musamman wanan kogin anya kuwa na gari ne ?
“ta tambayi kanta , kasancewar da agogo a hannunta taga har ƙarfe uku batayi azhar ba kasancewarta bata wasa da sallah ” zanyi sallah ” meenene sallah “ya tambayeta gaishe da Allah in roƙesa buƙatuna nasan yana jina kuma dana roƙesa zai amsamin , koda mutumin yaji haka ya ciro wata sabuwar wuƙa a gefen ganyen dakw jikinsa ya kwantar da ita da niyar zai yankata ,ihu take amma muryarta bata fitowa kasancewar danne mata mmaƙogwaro da yayi , ko me ya tuna sai ya fasa tare da ɗagota ya tsayar da ita cak cikin muryarsa mai amo yace “inkika ƙara ambato sallah sai na kasheki tsoro da firgici sukashigeta tashi ɗaya tace “na dena “wata mahaukaciyar dariya yayi kana ya haɗe rai tare da cewa “kin tsira “ya miƙe ya nufi cikin wani jeji dake saman wani dutse ,sai da ya hau kan dutse sanan yayi magana da ƙarfinsa yace “in kika motsa daga indda kike zan fara shirye shiryen kasheki!!
dumm taji gabanta ya mugun faɗuwa yana barin gurin ta miƙe har zataje kogin tayi alwalah sai tayi tunanin ko kogin tsafi ne ,ta koma wani guri tayi niyar taimama bayan ta gama haka tayi sallah babu komai a jikinta ta ɗaga hannu sama tace ‘ya Allah kaga halin da nake ciki ya rabissamawati ya zuljalalu wal’ikram ka fitar dani daga wanan rayuwar ka tseratar dani daga gurin wanan azzalumin ya Allah kaga inda nake roƙonka babu sutura ta kirki a jikina tun tasiwata ban taɓa hakan ba kuma ban taɓa tunanin yin hakan ba Allah ka amshi adu’ata nayi tawassali da alƙur’ani mai girma , tana cikin adur taji an zuba mata wata bulala mai azabar zafi haka ta ɗago idanunta cike da hawaye ta ƙwalara ƙara ta kallu mutumin ta haɗe hannayenta tare da cewa “na tunba nima ganina nayi a haka “finciko gashin kanta yayi tare da cewa “kafin in tafi me nace miki “shiru tayi kuka yaci ƙarfinta sai da ya kuma zuba mata bulalar a zabure tace “kace kar in tashi “waye yace “kiyi dungure ?
“cikin zuciyarta tace “innalilahi wa’inna ilahir raji’un tabbas Allah yayi halittu iri iri wanda wasu daga cikinsu basu mayarda bautarsa ibada ba , takurewa tayi a guri ɗaya tanajin jikinta ya ɗau zafi sbda azabar bulalar da yayi mata , tinkarota ya farayi a tsorace ta miƙe ta fara ja da baya yana mata wani irin murmishi mai kamada kuka tunda ba kyau yake masa ba , ja da baya take har taci karo da wata bishiya ta kusa faɗuwa saura taku kaɗan ya kamata Allah ya nisantashi da ita , gudu take yana binta tana gudu yana binta har ta kuma cin karo da wata bishiyar da tayi sabadiyar da ya damƙo kashin kanta kamar zai cire …..!
Karfa ku manta wanan littafin ƙirƙira ne inhar babu comments mai zafi da shar’hi sai weekend zaku dinga zamu .
*Ga mai buƙatar littafin SIRRIN ZUCIYA book 2 zai biya 300 regular vip 600 acct no 3175689751 Zainab Habibu first bank shedar biya ta *07064551049 in kuma kati ne mtn zakiyi screen shot na hoton katin ki turo min pls banda VTU*
Ga masu buƙatar littafin YARINYA MAI TAƁARGAZA book 2&3 zaku biya 500 ta acct ɗina 3175689751 Zainab Habibu first bank shedar biya ta 08141799224 banda VTU pls.
Mom Islam.
Name: | [Doctor Maryam Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Dan allah a sakemana sauran littafin doctor maryam allah yakara ilimi albarkam annabi (s.a.w)
MUN GODE
Gsky wannan littafin ya hadu Dan Allah da sosamune a Dan sake Mana sauran Mgd Allah Kara ilimi Mai albarka