Doctor Rumaysa Hausa Novel
Tag: DOCTOR RUMAYSA
Mallakin
Maryam Yusuf (Ummu Juwairiyyah)
SAHIBAR ROYAL STAR
*ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION*
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*RASHIN UWA NE SANADI* Na SALMA YAR LELEN ROYAL
*HUBBUL HAYAT* Na Miss Aishatouh
*MR ASHRAF* Na Maman Fauzan
*RUBUTTACEN AURE* Na Sadeey
*DOCTOR RUMAYSA* Na Ummu Juwairiyyah
Duk daga alkalunman marubutan Royal Star Writer’s Association
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, amincin Allah su kara tabbata ga manzon Allah S.A.W, ina rokon Allah yanda na fara wannan littafi lafiya, Allah yasa na gama shi lafiya.
Sadaukarwa:- na sadaukar da wannan book zuwa gareku yan kungiyata, alkhairin Allah ya kai muku har izuwa gadon baccin ku
Shafi na daya
______________Da sauri na tashi ba tare da wani ɓata lokaci ba, dalilin wani irin mugun aman da na ji ya taho min, fashewa na yi da kuka mai tsanani, domin kuwa duk karfina ya kare sam ba ni da kuzari, ga shi kuma ina da lecture by 8:30, wanke bakina na yi, na fito, a ya yin da na gama amayo komai na cikina, a haka dai na daure na ida kammala sauran ayyukana.
Aunty ce ta fara min fada, “wai HASINA, har yanzu baki kammala ayyukan ba ne? Ni fa ba na son shiririta, kwana biyu din nan, sai nake ganin komai za ki yi sai a slow” “Don Allah Aunty ki yi haƙuri, Allah ba na jin dadi ne, wani iri na ke ji na, Aunty wallahi jikina duk ba karfi, kawai ayyukan nan ma karfin hali ne na ke yi” Hasina ta fada agalabaice.
“Iyeeeee Hasina! Ke ki kalle ni nan, ke! Na ce ki kalli Idona na gasgata hashashena”, Aunty ta fada a fusace “innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Hasina ciki ne da ke? Uban wa ya mi ki ciki? Ki min magana tambayar ki na ke fa, na ce wane dan iskan ne ya miki ciki? Hasina kin cuce mu, kin ci amanar mu, wannan shi ne tarbiyar da na mi ki?” Aunty ta fada tare da fashewa da kuka mai tsanani.
“Wayyo Aunty, wallahi ba ciki ne dani ba, kinji rantsuwar musulunci, Allah Aunty ba ni da ciki, wani irin wawan mari Aunty ta dauke ni dashi, ta na fadin, “Hasina wa ya miki ciki? Ina miki magana za ki ce min ba ciki ne dake ba? Rumgume ta Aunty ta yi sosai ta na rarrashinta, “don Allah ki gaya min gaskiya Hasina wa ye ya miki ciki?, don Allah don soyayyar ki da manzo Allah, Hasina ki gaya min gaskiya, budar bakinta ke da wuya ta ce “Aunty Abdul Halim ne ya mun ciki, dan gidan Alhaji Yahaya” Hasina ta fada ta na kuka mai tsanani.
Aunty suman tsaye ta yi, ya yin da, kanta ya dinga tsara mata, “na shiga uku yoo ni Asma’u, hasbunallahu wa ni’imal wakil, wa ne Abdul Halim din? Wanda na sa ni, dan Alhaji ko kuwa? innalillahi, Abdul Halim ka cuce mu, ka ci amanar rayuwarmu, Hasina kin ci amanar rayuwata, don na ce ki je aikatau gidan Alhaji Yahaya shi ke nan sai ki lalata rayuwarki,
Hasina kin san yanda nake sonki, kin san yanda nake ji dake amma shine kin zabe ki wulakanta ni, yanzu me ki ke son na ce da Mama, innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, yoo ni Asma’u na shiga uku, Hasina….. Kuka ne ya fi karfin Aunty, “Aunty don Allah ki yi hakuri, wallahi shi ne ya ce zai aure ni, wallahi Aunty……”
“Wallahi ki ka sake furta ko da alif ne Hasina zan ci mutunci ki” shi Abdul Halim ne har ya isa ya miki dadin baki, ai kuwa kin cuce kanki da kanki, me na hana ki, kullum wa’azina guda, ki rike mutuninki, Hasina mutunci fa ya fi kudi, to me ya sa za ki yi disappointing dina? Aunty ta fada ta na mai kukan bakin ciki.
WACE CE HASINA?
Hasina y’a ce awajen Malam Hamza, ita ka dai iyayenta suka haifa, Aunty kuma kanwar Mamanta ce, Aunty ta na matukar ji da Hasina fiyeda tunanin mai tunani kusan ma mutane basu san ba ita ta haife ta ba, saboda a wajen ta Hasina ta tashi, ita ce ta raineta kasancewar Malam Hamza tallaka ne sosai, ko abunda zasu ci ma wata ran sai ya buwaye su, ita ma Aunty mijinta ba wani mai kudi ne ba, amma ya na da rufin asiri, Mijin Aunty a Abuja ya ke aiki shiyasa ita ma Hasina ta bi Aunty su ka koma Abuja ya yin da shi Malam Hamza a wani k’auyen Sokoto ya ke zama tare da matarsa Hauwa wace suke kiranta da Mama, wannan kenan.
••••Flash back••••
“Don Allah Mommy ki yi haƙuri, ki ce Islam ta kai masa abincinsa dazu na je na kai masa amma baya nan, kuma yanzu kaina ne ke min ciwo” Hasina ta fada a marairace, “oh sannu my dear, Allah ya sawwake fatan dai kin sha magani ko?” Cewar Mommy, “a’a” Hasina ta fada kamar zata yi kuka, “au to me ya sa ba ki sha ba?” Maza je ki ci abinci sai ki sha magani kinji?” “To Mommy nagode, Allah ya kara girma”
Mommy ta kasance mace mai mugun son Yaya mata kasancewar ita bata haifa ba, Ya’yanta bakwai amma dukkan su maza ne, ta na matukar kaunarsu fiye da tunanin mai karatu, ba ka isa ka ce za ka nuna mata laifin yaranta ba ta yarda, sam Ya’yanta ba sa laifi, shi ya sa ta ke matukar son Hasina, ita kuwa Hasina aikatau aka kai ta gidan Alhaji Yahaya waton gidan Mommy, Abdul Halim shi ne babban danta, sai Aliyu Haidar, sai Abubakar da Abdallah, sai Ahmad, sai kuma autanta waton Fu’ad, dukkan su ba’a Nigeria su ke ba, suna outside Country waton U.K (London) acan su ke karatu sai dai shi Ahmad ya na dan zuwa Nigeria akai akai, tunda yaga Sai’luba ta kawo Hasina gidansu ya ji wani irin kaunarta a ranshi, ya ji shi fa ba wanda ya ke so in ba Hasina ba, amma kuma ya kasa furta mata.
Hasina yarinya ce yar kinmanin shekaru goma sha biyar a duniya, kyakyawa ce sosai, fara sol, son kowa kin wanda ya rasa, mai siririyar hanci ga ta da dan k’aramin baki mai zagaye da pink lips, gashin idonta zara-zara dasu, with a small cycle face, diri kuwa ba’a magana tamkar ita ce ta yo kanta, exactly coca cola shape, kamar wata babbar buduwar komai ya ji a jikin ta so Masha Allah, shiyasa ko wane irin d’a namiji ya kalleta in dai shi din cikaken namiji ne, to dole sai ya ji wani abu a ransa game da ita. Dawowansa daga U.K kenan shi ne yasa ta kawo masa abinci dakinsa, to ita maganar gaskiya ta na mugun jin tsoron Abdul Halim, ko ido ba ta son h’adawa dashi bare ma magana, ko kyat ya ce mata yanzu nan za ta firgice saboda tsananin tsoronsa da ta ke ji, shigowa parlourn gidan ya yi dauke da sallama a bakinsa, amma ba wanda ya amsa masa kasancewar ba kowa a gidan, Mommy na wajen aiki, kitchen ya nufa direct ai kuwa ya ci sa’a ta na a kitchen sai aikin wanke-wanke ta ke ta faman yi, rumguma ya kai mata daga baya a gigice ta saki glass cup din hannunta ta shiga kwala ihu, Abdul Halim rufe mata baki ya yi da tafin hannunsa ya na fadin “dallahcan matsoraciya Allah kin cika tsoro, da ace Mommy na a kusa aka zaki to na min asiri, you are not romantic at all” Abdul Halim ya faɗa ya na mai jan dogon tsaki.
Mu je zuwa wannan salo na daban ne yar kuwa kada ki bari ayi wannan tafiya ba ke
Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah ce Sahibar Royal Star
DOCTOR RUMAYSA
Mallakin
Maryam Yusuf (Ummu Juwairiyyah)
SAHIBAR ROYAL STAR✨
*ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION*
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
“`Being a good human being does not depend on your religion, race, skin color or culture. It depends on how good your heart is and how well you treat others.“`
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, amincin Allah su kara tabbata ga manzon Allah S.A.W, ina rokon Allah yanda na fara wannan littafi lafiya, Allah yasa na gama shi lafiya.
Sadaukarwa:- na sadaukar da wannan book zuwa gareku yan kungiyata, *Royal Star Writer’s Association* alkhairin Allah ya kai muku har izuwa gadon baccin ku🥰💃
Shafi na biyu
____________Don Allah Yaya ka yi haƙuri ka cika ni, wallahi kar Mommy ta gan mu, ta kusan dawo da ga aiki, Hasina ta fada ya yin da duk ilahirin jikinta ke rawa, wani irin hot, hot kisses Abdul Halim ya shiga kai mata, daman albarkatun kirjin ta sun dade su na tsone masa ido, hot romantic ya shiga kai mata, in da Hasina ta fashe da kuka mai tsanani,
Sai da ya gama lugwuigwuya ta iya son ranshi sannan ya barta, Hasina in banda zafi ba abunda na shanun ta ke mata kasancewar ba d’a namijin da ya taba mata makamancin abunda Abdul Halim ya mata yau, a wunin ranar sosai ta ci kuka har ta godewa Allah, ko da Mommy ta dawo daga asibiti, tambayarta ta shi ga yi ko ciwon kan ne har yanzu, domin kuwa kallo daya za ka yi mata ka tabbatar da ta ci kuka sosai,
“Hasina lafiya me ya saka ki kuka?” Cewar Mommy “ba komai” Hasina ta fada atakaice domin kuwa ta tuna da gargadin da Abdul Halim ya mata dazu kar ta yarda ta gayawa Mommy, idan kuma ta yarda ta gayawa Mommy to ta gama aiki a gidan ke nan, ai kuwa ta so ta gaya wa Mommy amma tunawar da ta yi, sai kuma ta yi shiru ta fasa Mommy,
Mommy kara tambayarta, ta yi, “My daughter kin sha magani kuwa?” “E Mommy na sha, Hasina ta sake bata amsa atakaice, “To sannu Allah ya kara sauki, je ki daki zan karasa miki sauran ayyukan” cewar Mommy, ai kuwa Hasina ta ji dadi domin kuwa, jikinta duk ya mata ciwo, d’akinta ta shiga kasancewar a gidan ta ke kwana tunda Aunty da mijinta suka koma Sokoto, Mommy kuwa ta neme alfarmar a bar mata Hasina,
Hasina bata so Aunty ta amince ba, amma sai kuma ta ji tausayin Mommy sai bata ce komai ba, ita ma ta amince zata tsaya a gidan Mommy, amma kuma yanzu ta dawo da na sani, ina ma ace tare da Aunty suka koma Sokoto yanzu da wannan dan iskan bai saka ta a gaba ba, ko da ta koma dakin nata sosai ta shiga rera kuka na tausayin kanta,
Wani kyakyawan sauri ne naga ya na sauƙowa daga matattakalar jirgin da saukar su ke nan, ya yin da ya dinga kallon ko ina kamar wa ni JJC, sosai guy din ya hadu iya haduwa Ahmad ke nan dan gidan Alhaji Yahaya da Hajiya RUMAYSA waton *DOCTOR RUMAYSA*,
Driver ne ya shiga gaishe shi, wanda tundazu ya ke ta zaman jiran saukarsu ai kuwa cikin girmamawa shi ma ya shiga gaishe da drive din na su, Ahmad ya na da abin burgewa sosai domin kuwa ko kadan baida girman kai, ga shi da mutumci da ganin darajar dan Adam sam ba shi da wulakanci,
Direct drivern ya ja su sai G.R.A sosai Mommy ta yi murnar dawowar dan nata, abinci kala-kala aka hada masa abun sai wanda ya gani, hmmm Mommy ke nan, mace ce mai matukar kaunar Ya’yanta kuma bata iya boye ba, Ahmad hug ya kai wa Mommynshi in da ya shiga gaisheta tare da tambayar ta ina y’arta waton Hasina,
“Au wai Hasina ta na kitchen pepper chicken na ce ta hada maka, kira Mommy ta kwalawa Hasina,da sauri ta fito ya yin da ta shiga amsa kiran da Mommy ta yi mata, sosai ita ma ta yi murnan ganin Ahmad ko ba komai ai yanada mutunci sosai kusan gidan ba wanda ya ke kwanta mata a rai irin Ahmad da auta waton Fu’ad,
gaishe shi ta shiga yi tare da nuna tsansar murnar ta na gani sa, shi ma Ahmad din sosai ya ji dadin ganinta, Abdul Halim ne ya shigo dakin tare da gaishe da Mommy Ahmad ma gaishe shi ya shiga yi, “Au Ahmad saukar yaushe? Ahmad, shi ne ko ka gaya min zaka dawo ko?” Cewar Abdul Halim, ” Ayyah ka yi haƙuri big bro ni ma ban yi tunanin a yau ne zan dawo ba shiyasa” cewar Ahmad, “okay to ai shi ke nan ba damuwa” Abdul Halim ya faɗa in da ya maida kallonsa ga Hasina tare da ce wa,
“Hasina ki kawo min abincina pls” wani irin mumunar faduwa gabanta ya yi, “magana fa nake da ke” Abdul Halim ya faɗa “to shi ke nan” Hasina ta fada kamar wa ce ba ta so maganar ba, sum sum ta wuce kitchen kamar wace kwai ta fasawa aciki, tsoro ne karara kwance a saman kyakyawan fuskarta, abinci ta zuba masa a cikin wasu kyakyawan warmer’s direct part dinsa ta nufa, knocking ta shiga yi, gani tayi kofar ta bude da kanta ai kuwa ta yi sauri ta shiga ta ajiye masa tray din hannunta asaman dan k’aramin royal table din da ke cikin dakin,
da sauri za ta fita daga dakin ya ce “ke dawo, wa ki ke tunanin ya yi feeding dina?” Maza dawo ba ki gama aikin ki ba, kuma wallahi ki ka yi misbehaving to zan shayar da ke mamaki ne.
Mu je zuwa
Comment and share fisabilillahi lover’s
Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah ce Sahibar Royal Star🪄
[18/07, 10:07 am] : *DOCTOR RUMAYSA*
Mallakin
Maryam Yusuf (Ummu Juwairiyyah)
SAHIBAR ROYAL STAR
*ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION*
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Assalamu alaikukum dftn kuna lpy, sister’s agaskiya ina matukar jin dadin Comment dinku fiyeda yanda ku ke zato, ngd sosai da ku ka karbe wannan book na wa, ina matukar godiya, ku cigaba da bani hadin kai ni ma insha Allah zan cigaba da sambado muku posting akoda yaushe domin kuwa farin cikin ku shi ne takenmu🥳
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, amincin Allah su kara tabbata ga manzon Allah S.A.W, ina rokon Allah yanda na fara wannan littafi lafiya, Allah yasa na gama shi lafiya.
Sadaukarwa:- na sadaukar da wannan book zuwa gareku yan kungiyata, *Royal Star Writer’s Association* alkhairin Allah ya kai muku har izuwa gadon baccin ku🥰💃
Shafi na uku
____________Hasina jiki na rawa ta dawo daga baya, tare da fara bashi abincin a baki, lumshe ido ya shiga yi, alamar abincin na masa dadi, shi dai ya na matukar jin dadin girkinta sa bo da gaskiya Hasina ba daga baya ba wajen iya sarrafa girki, ita din boss ce a fannin iya girki, “ke idan ki ka gama ban ce ki tafi ba, ki gyara min dakina, kuma daga rana irin ta yau ke zaki na gyara min dakina, kar ki kuskura ki bari na aiko a kira min ke, kin ji ko? Gyada mishi kai ta yi, “Ke! Ina miki magana za ki dinga amsa min da body contact,” Abdul Halim ya faɗa atsawace “don Allah ka yi haƙuri na daina” harara ya maka mata ba tare da ya ce komai ba, sai da ta gama bashi abincin a baki tass,
Sannan ta tashi ta fara yi wa dakin hankali, ta gyara ko ina saf-saf sai kamshin turare ke tashi, Ahmad ne ya shigo dakin dauke da sallama abakinsa “au wai daman gyara mishi daki ki ka tsaya yi? To ina Islam na zata ita ce mai gyaran daki ko? “E Yaya ita ce, amma Ya ne ya ce yau ni ya ke son na gyara masa, shi ya sa, cewar Hasina, Ahmad sam bai kawo komai a ransa ba, “to ai sai ki zo muje tunda kin kammala ko? tundazu ina can ina jiranki ki zo ki zuba min abincina, har na gaji da jira shi ne Mommy ta ce na zo na gani ko me ya tsaida ke” cewar Ahmad,
“Ayyah Yayana ka yi haƙuri, yanzu mu je na zuba maka”, Hasina ta fada, sosai Abdul Halim ya ji wani irin azabbaben kishi wai don ta raina masa hankali zata wani ce wa Ahmad Yayanta, uhmmm zai koya mata hankali ne, juyawa ta yi ko za ta gan shi, amma kuma wayam babu alamarsa, ai kuwa ta yi maza ta ficce daga dakin, ta bi bayan Ahmad, a dinning ta tarar dashi ya na jiran ta zo ta yi serving din shi, ai kuwa serving din na shi ta yi zata wuce kitchen ya ce “My Hasi ki dawo mu yi fira” Hasina tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba, ta ce “Yaya ka na magana ne?” “Ai kin ji abunda na ce” “rufe fuska ta yi tare da ce wa “to Yaya kai da za ka ci abinci wane iri fira kuma za ka yi, kawai ka bari har idan ka kammala ci sai mu yi firar ko?” Cewar Hasina, “Okay haka ki ka ce ko?” Cewar Ahmad, “e Yaya haka na ce” Hasina ta fada, “to ai shi ke nan” Ahmad ya fada,
••••Bayan wata uku••••
“Hasina magana fa na ke miki, don Allah ki amince da ni, wallahi bazan ci amanar ki ba, na miki alkawari da gaske na ke zan aure ki, Allah sonki ajinina ya ke, ina matukar kaunar ki fiyeda tunanin ki, da zaran na kammala karatuna to zan fito na gayawa duniya ina sonki, su Daddy su je su nema min auren ki” “a’a wallahi ni Yaya banda dadin baki, yaushe za ka iya aurena, kai da ka ke dan masu kudi, ni dai Yaya don Allah ka kyale ni, duka duka nawa na ke, ni fa karamar yarinya ce, don Allah Yaya ka kyale ni, Hasina ta fada ashagwabe,
sosai yanayin da ta yi maganan ya ta da tsigar jinkinsa, Abdul Halim ji ya yi kamar ya rumgume ta, ya danne ta ya biya bukatarsa da ita, domin kuwa sosai ya ke jin sha’awanta, belle ma yanda ta yi magana yasa ya kara ji ya na son kusantarta, “Allah kanwata da gaske na ke, ina sonki kuma aurenki zan yi, kin ji kawai ki yarda da ni”, ita dai ta na jin tsoron amincewa dashi, “to ni Yaya ka bari zan yi tunani” Hasina ta fada, “to shi ke nan” Yar Lelen Yaya Abdul Halim” sosai yanda ya yi maganar ya bata dariya, ai kuwa sosai ta shiga kyalkyala dariya harda su rike ciki, ga tudun nonowanta nan ga fili ana gani Abdul Halim sai latsa baki ya ke ta yi, ji ya yi kamar ya sa bakinsa ya sha mata su,
Mommy ce ta sauko parlourn tare da kwala mata kira kasancewar yau bata fita asibiti ba, da gudu ta fito daga kitchen ta na ce wa “Mommy ga ni, ina kwana” “lafiya qlau fatan kin tashi lafiya, yau me haka dafa muna ne” cewar Mommy, “laaaa Mommy abincin da na saba dafa ne fa, Harish sai planten da kidney source” Hasina ta fada, “okay to a zubo min nawa ko?” Cewar Mommy, “to Mommy an gama” da saurinta ta koma kitchen still Abdul Halim na nan a in da ta bar shi, amma a labe gudun kar Mommy ta shigo ta gan shi, abincin ne ta zubuwa Mommy ko da ta dawo Mommy har ta wuce dakinta, ai kuwa da sauri ta koma kitchen tare da ce wa “Yaya ka yi sauri ka fito ta wuce dakinta” ai kuwa kamar jira ya ke da sauri ya ficce daga kitchen ya wuce part din shi, aka dai su ka cigaba da gudanar da rayuwarsu in da Hasina ta amince ita ma ta na sonsa, ai kuwa kullum sai zuba soyyayarsu su ke,
Yau ma kamar ko da yaushe Abdul Halim ne ya bi ta har kitchen ita kuwa sai faman yanka salak ta ke ta yi, yana rumgume da ita sai mamatse na shanunta ya ke ta faman yi, daman su ne su ka fi tsone masa ido, kai da ka kalle ta zaka san cewa ana taba nonowan nata, domin kuwa sun kara cicciko sunyi bul-bul dasu, awasu lokunta ma Abdul Halim yakan wada sa’arsa ya yi ta mata dadin baki, to yau ma hakan ne ya kasance, “don Allah Hasina ki bar aikin nan haka mana, zo muje dakina ki min wanka kin ji?” Cewar Abdul Halim, “a’a ni dai Yaya kar Mommy ta dawo ta ga bana kusa, ni dai ka bari sai zuwa da dare Allah na maka alkawari zan zo, sai na maka duk abunda ka ke so” cewar Hasina, “Allah Hasina da gaske ki ke” Abdul Halim ya faɗa, “e mana Yayana da gaske nake, idan ka ga ban zo ba, to rasa yanda zan yi na yi, kai sai ka zo,
Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar shi, yau ko banza zai biya bukatarsa da ita amsa mata ya yi da “to shi ke nan my wife to be” ita kuwa nan ta sake yarda da gaske ya ke zai aureta, ya yin da ya cigaba da mamatse ta, ita ma biye masa ta yi, suga shiga romantic din juna, sosai ta ke jin dadin abubunwan da ya ke mata, uhmmm Abdul Halim ke nan, ya bala’in iya sarrafa mace, har ta manta da a ina ta ke, sai da ya gaji sannan ya kyale ta, ita ma direct dakinta ta nufa ta yi wanka ya yin da Islam da ke gyaran daki ta bi ta da kallon tuhuma, “me ki ke ta kallona” cewar Hasina, “a’a ni na isa na ce wani abu ne, yi haƙuri ba kallon ki nake ba” Islam ta fada tare da ficewa daga dakin,
Kasancewar ta masa alkawarin zata zo, karfe tara dai-dai ta sace hanya direct part dinsa ta nufa, a dai-dai kofar shi ta tsaya za ta yi knocking kenan, ya fito ya ya rumgumeta tare da…..
Mu je zuwa
Comment and share fisabilillahi lover’s
Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah ce Sahibar royal star
Leave a Comment