Dogon Yaro Hausa Novel Complete
DOGON YARO
*(Jancy)*
NA INDO CE..
*ELEGANT ONLINE WRITER’S*
Na kuÉ—i ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE
*shafi na 1*
Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262
30/6/2022
Bismil-lahirrahma-nirrahim.
Yar Hannu Complete Hausa Novel
Matashin Yaro ne wanda be wuce shekaru 19- 20 ba, sanye yake cikin ƙananun kaya jar riga da baƙin wando sai hula hana sallah da ya kifata tayi masa rumfa akan fuskar sa, pink lips ɗinsa ne sukafi ɗaukar hankalin me kallonsa a daidai lokacin saboda yadda yake motsasu yana yin fito a hankali.
Wanda ke gefensa ne yace, ” DOGON YARO wannan jan ajin naka fa bashida ma’ana anan gurin dan ba’a gaban ta bane”
Sassayan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa yayi taku uku cikin nutsuwa da kuma cika, sannan ya fara magana, “idan ban dawo da rai ba fa karkiyi kuka”
a É—aya bangaren Zeety tace, “bana son irin wannan maganar a bakin ka Jan nasan ba’a nasara akanka karka manta fa koda yaushe tsawo kake Æ™arawa baka gajarcewa haka a kowane lokaci sama kake Æ™arawa a wannan karon ma idan kabari, Na’im yayi nasara akanka?? ai kasan kwanan zancen ko??”
Æ´ar Dariya yayi kafin yace, “idan kuma nayi nasara wace kyauta ce tawa???”
Murmushi me sauti tayi tace, “sai ka dawo”
Murmusawa yayi yace, “ban yarda ba”
Daidai lokacin ya isa gurin motarsa abokansa dake gurin suka buÉ—e masa motar ya shiga mazaunin direba, Na’im ya bashi hannu sukayi musabaha yace, “Dogon Yaro gudun kere sa’a yau za’ayi dan haka karka bari wannan koÉ—aÉ—É—iyar yarinyar ta hanaka Æ™oÆ™ari”
Dariya yayi yace, “ashirye nake, haba ai ko tana motar kasan mahaifiyata ce kawai zan É—auka a motata na saurara duk dattin kanka baka kaini kasada ba kaima ka sani, (na rabaka)”
Ihu suka sa tareda faÉ—in “sai da kai DOGO Jancy”
Shikam dariya kawai yakeyi sai da ya rufe motar ya gyara zama sannan yace, “wai kina saurare na kuwa??”
tace, “ina jinka suna ta fasa maka kai ko?? shiyasa kake wani Æ™ara jin kanka”
yayi dariya kafin yace, “Shikenan Naji kuma na yarda sai na dawo ko?”
Tace, “Allah ya tsare”
Wauta da zallar ƙuruciya suke gwadawa akan babban titin wanda babu mutane sai tsilli tsillin ababen hawa haka suke zuga gudu tareda ƙiriniya ba tareda tunanin rai da lafiyarsu ba,
Yau ma kamar kullum Jancy ne ya take wasan ta hanyar yiwa Na’im fintinkau.
ko tsayawa ya saurari surutai da koÉ—ashin da sukeyi beyi ba ya wuce gida dan kuwa hankalinsa yayi can.
Da gudu ya shiga layinsu ba tareda ya saurara ba kai tsaye ƙofar gidansu ya dosa, wata ƴar budurwa ce take tafiya a hankali kanta a ƙasa. ba tareda tunanin komai ba yayi kanta da motar tareda danne ƙararrawa. ihu ta fasa tareda dafe kai ta rintse ido da ƙarfi.
Ƙiris ya hana yayi sama da ita sai yayi gefe ya tsikara parking ya fito ya nufo inda take cikin ƙasaitaccen takunsa.
Jin shiru bataji ta a lahura ba yasa ta buÉ—e ido a hankali tana son fuskantar inda matsalar take, tafa hannuwan sa yayi a bayanta tareda cewa, “gani nan”
firgigit tayi ta tsallake zuwa gefe tana zazzare ido, ya tuntsire da dariya kafin yace, “matsoraciyar banza sai shegiyar yanga a titi yangar kwalba ba mai”
MurguÉ—a baki tayi tace, “lallai ma wallahi kaci mutunci kaci zarafin ka raina kima da daraja ka latsawa tsorona basirarsa”
Gaba yayi yana dariya yace, “idan kin gama gaya musu sai ki shigo ciki ko?”
Bin bayan sa tayi tana murguÉ—a baki, a falon Ummi tana tsaye cikin kiÉ—ima tana zarya, ganin sun shigo suna raha yasa ta sauke Æ´ar ajiyar zuciya fuska a tsuke tace, “halama ba a hayyacin ki kike ba?? kin dokawa mutane Æ™ara haka kinsa hankalina ya tashi na zata ma wanine ya taÉ“a ki”
Ta turo baki tareda cewa, “Ummi wallahi Jancy ne yayi kaina da mota saura Æ™iris ya buge ni kuma gudu yake ko shafata yayi da ita inaga bazan rayu ba”
Maida kallonta tayi kansa cikin sanyi tace, “Jannah kasan adadin Æ´aÆ´an da na haifa suka mutu kuwa?? ku biyu ne kawai nasan daÉ—in ku banaso ku dinga wauta da rayuwarku dan nima inason na dinga buÉ—e ido in ganku”
Jancy ya murmusa tareda ringumeta yace, “Nan? mu rabonki ne tinda har muka kawo yanzu, da ace ba me tsawon rai bane ni Ummi kin fini sanin adadin shekarun mutuwa ta a yanzu, ina fatan na sameki lafiya”
Taja numfashi ta sauke tana murmushi tace, “madallah da kai Jannah ina lafiya lau”
Yace, “to ki dena damun kanki da ihun Magen Ummin nan”
da sauri tace, “eh kai kuma Muzurun Aba ko??”
Dariya yayi yace, “amma dai kinsan Mage tafi kalar mayu daman”
Zatayi magana Ummi tace, “Natiee zo ki kalmashe min gashin nan dan Allah na gaji da rashin kitso”
Kafin Natiee tayi wani motsi tini Jan ya dira a bayan Ummin yana cewa, “me zakiyi da kitsonta Bayan ina nan Ummi salon ta gwaguye miki gashi”
Ummi ta murmusa tace, “naga ai ka Æ™i tsayawa kayi min ne shiyasa”
a tsiwace Natiee tace, “gaskiya Ummi ya tashi nayi miki da can da kike son yayi mikin ba Æ™i yayi ba sai yanzu ze dawo yace zeyi ai kuwa baka isa ba, kullum fa shine yake miki kitso idan nace zanyi sai ace aa gaskiya nidai Ummi yau nizanyi miki”
Jancy ya harare ta sama da Æ™asa tareda cewa, “iyee???? eh lallai to bazakiyi É—in ba idan kuma kinada Æ™arfi kisamin duka”
Ummi tace, “kunga banason kace kacen nan naku Natiee jeki ki kawo masa abinci”
Juyawa tayi tana cewa, “ai kuwa lokaci nagaba nice zanyi mata kama dena murna”
Kafin tayi nisa yace, “kinga ni bazanci komai ba sai Abana ya dawo dan haka ki dawo ki zauna”
Komawa tayi ta zauna tana kumburo baki.
Ummi ma taɓe baki tayi dan tasan dama ba lallai ya cin ba.
Shiru ce ta biyo baya har na É—an wani lokaci. Jan ne ya katse shirun da cewa, “Ummi wai da yaya kikafi wannan É—iya gashi subhanallah ko ni na zuciya sai na tara gashin da ya ninka nata oohh ga son iyayi ga muni Allah yaban mata kyakkyawa kamar Ummi na ba kamar ta hannun dama na ba”
Ummi dai dariya tayi tace, “Allah ya shiryeka Jannah ka fiye neman fitina”
Natiee kuwa Æ™ara murguÉ—e baki tayi tace, “barakallah masha Allah maye yaci kansa, kuma wallahi kasan babu matar da zaka aura wadda zata fini kyau”
Yace, “haba Æ™anwati yawa ne kike wallahi kinsani dai”
Tace, “ba wata yawa ko a mafarki bazan yarda ba, ko ita wannan diddigar larabawan da ka mayancewa kasan wallahi na fita komai kuma a banida gashin dai nawa ya ninka nata sau uku amma a hakan ka ganta ka Æ™yasa bare kuma ni”
Dafe kai yayi tareda cewa, “ahh? Natiee abun kuma tonon silili ya koma??”
Ummi tace, “ina gida a zaune ashe har kafara jawomin magana??? bari to Aban naka yazo zan gaya masa aure kake so”
da sauri Yace, “Ummi dan Allah kiyi haÆ™uri kuma yarinyar nan Æ™arya take kawai dan ta haÉ—a mu faÉ—a ne”
Ido Ummi ta zubawa Natiee, kawai sai ta sunkuyar da kai dan kuwa duk abunda ze ɓatawa ɗan uwanta da mahaifiyarta rai bata ƙaunarsa.
Ummi ta murmusa sannan tace, “Jannah!! sa albarka akanku shine muradina a koda yaushe, ina fatan Allah ya haÉ—a ka da abokan mu’amaka nagari”
Natiee ce kawai ta amsa da “amin” shi kuwa shiru yayi dan kunya ta gama ritsa shi yasan dai Ummi ba yarinya bace ya tabbata ta gane komai kawai tayi musu kwance kwance ne”
Da yake kitson nata ba wani aiki bane manya manya ne guda shida kawai yayi mata dan haka ba wani É“ata lokaci ya gama ya tashi.
Kai tsaye É—akinsa ya nufa kan gado ya faÉ—a tareda sauke numfashi ya lumshe idonsa yana ambaton “La’ilaha’illallah” ya kai tsawon minti biyu yana kwance kafin ya miÆ™e cikin sanyin jiki ya nufi É—akin wanka yana tafiya yana lumshe ido.
koda ya fito a gaban madubi ya zauna yana ƙarewa kansa kallo murmushi yayi tareda shafar kansa sannan ya fara shiryawa cikin nutsuwa da kamala tareda tsantsar haiba,
mayuka da turaruka ya mulka sannan ya nufi ma’ajiyar kayansa ya fito da wata riga iya guiwa me maÉ“allai sai É—an guntun wandonta.
Sai da yaƙara fesa turare sannan ya koma bakin gado ya zauna tareda janyo wayarsa yafara dannawa cikin nutsuwa, ɗan bakin nan nasa a tsuke kamar ba shine ya gama surutu ba.
Natiee ce ta shigo tana cewa, “kun fara jarabar ko??”
Ba tareda ya kalleta ba ya murmusa cikin muryarsa me matuÆ™ar É—aukar hankalin me sauraronta yace, “bamu fara ba tukunna”
Tace, “ai nasan bakuda aikin da ya wuce waya ne narasa ma me kuke cewa”
Yace, “ina ruwanki?”
Tace, “na shanye”
Yace, “banida damuwa da hakan”
Banza tayi masa ta dawo kusa dashi ta zauna, a hankali tace, “Jan? yau ma tsere kaje kayi ko?”
Sai a lokacin ya É—ago fararen idanunsa ya É—ora akanta tareda motsa pink lips É—insa yace, “eh”
Tace, “ai dama na sani É—an kasada kawai”
Murmushi yayi gami da maida hankalinsa kan waya kamar baze magantu ba sai kuma yace, “babu wanda ya neme ni??”
kafin ya gama rufe baki tace, “eh kuÉ—i ne kai da za’a wani neme ka?? me za’ayi da kai??”
Jinjina kai yayi yace, “wai me nayiwa Æ™anwata ne yau??”
Gyara zama tayi tana cewa, “anzo gurin hakan nakeson ji, wato ainafin sharaÉ—i zan saka nan gaba idan Ummina ta warware gashinta nice zanyi mata kitso sannan kuma yau banaso kaje wajen Zeety ka zauna a gida karkaje ko ina”
Shiru ya É—anyi kafin yace, “haka ne?”
Tace, “eh É—in”
Yace, “zanyi hakan”
tace, “yauwa ko kai fa? yanzu dai babu wanda yazo nemanka amma nasan zasu zo yanzu ma kuwa ka shirya”
dummm dumm dumm zuciyarsa ta shiga harbawa a take yanayinsa ya canja cikin sanyi yace, “Natiee kin tabbata?”
Cikin tausayawa tace, “abunda ya zama wajibi ne shiyasa kaji na faÉ—a”
Lumshe ido yayi tareda jan numfashi, ko saukewa beyi ba kuwa yaji ana ƙwala masa kira DOGO!!!! DOGO!!! DOGO!!!!!!.
Shafar kansa yayi tareda rintse idonsa da ƙarfi yana ambaton sunan Allah a cikin zuciyarsa.
Natiee tace, “Jan ka tashi kaje tin kafin yazo ya sameka”
Girgiza kai yayi tareda cewa, “aah bazani ba”
Cikin marai-raicewa tace, “Dan Allah Jannah katashi”
Ummi ce ta faÉ—o É—akin kamar anjefo ta, a kiÉ—ime tace, “Jannah tashi kaje mana!! ko kafi so azo aci zarafinka a gabana????”
MiÆ™ewa yayi tareda girgiza mata kai alamar “aa”
Kamar zata fashe da kuka tace, “Jan? me kayi yau kuma? meyesa baka gujewa É“acin rai?”
Rungumeta yayi tsamm cikin rawar murya yace, “Naan”
tace, “kayi sauri fa”
janye jikinsa yayi daga nata ya nufi waje, yana fita daga sashin yayi karo dashi.
Cikin hargowa yace,………….
Share fisabililah.
Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem.
*INDO CE..*
[27/10, 4:14 pm] +234 907 988 5632: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*
NA INDO CE..
*ELEGANT ONLINE WRITER’S*
Na kuÉ—i ne😂
200 kacal
VIP
300
FREE PAGE
*shafi na 2*
Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262
“Ban hanaka zuwa kayi mana parking É—in banza ba?? kai ba’a isa a faÉ—a kaji ba ko??”
Ƙasa yayi da kai cikin Æ™unar zuci yace, “mantawa nayi”
Wasu kyawawan maruka ya zuba masa lafiyayyu har uku sannan yace, “ni zaka gayawa ka manta?? ni zakai wa rashin kunya kai ga É—an iska ko?”
Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi
Matar Makaho Complete Hausa Novel
Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam
Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd
wani marin ya Æ™ara haÉ—a masa yana huci Fauzy da take gefe tace, ” Æ™ara masa wallahi Faisal mara tarbiya dama ya gama yimin rashin kunya É—azu”
Jancy da yayi Æ™asa da kai cikin son kare kansa yace, “kayi haÆ™uri dan Allah”
a harzuƙe Faisal ya ƙara hawa kansa da tafka har saida gefen bakinsa ya fara jini saboda azabar marukan da yake watsa masa na rashin tausayi da rashin imani.
Sai da ya gaji da dukansa sannan yace, “ba zakaje ka gyarata ba kuma?? saboda kai kaÉ—ai ne É—a a É—auki wannan danÆ™areriyar motar anbaka, sai nasa an faffasa ta ma kowa ya huta”
Jiki na rawa Jancy yayi waje a kiÉ—ime ya manta ma yabar mukullin a É—aki, Natiee ce ta miÆ™e tana sharar Æ™walla tace, “Ummina bari na kai masa mukullin”
Ummi kasa magana tayi kanta na ƙasa tana wasa da zubukan yatsunta idanunta da suke zubar hawaye ma kawai sun isa nuna irin raɗaɗi da zugin da takeji, maganin kar ya shigo tayi ido huɗu dashi sai ta tashi ta koma sashinta, a bakin gado ta zauna ta fashe da kuka me tsanani ban tausayi.
kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Natiee take tafiya har ta isa gashi, shima ya tawo da nufin ɗaukar mukullin suka haɗu, karɓa yayi da sauri ya koma ya shigo da motar.
yana ajiyeta Kai tsaye É—akinsa ya wuce sai da yasa mukulli ya kulleta gam sannan ya zame a gurin ya fashe da kuka me tsuma zuciya.
Allah me yadda yaso bashida wata damuwa a duniya wadda ta wuce ƴan uwansa mahaifinsu ɗaya amma sun maidashi kamar shaiɗan sun tsaneshi basa ƙaunar ganinsa kowannen su bashida burin da ya wuce ƙaga masa sharrin da ze jawo masa ƙuntata da ɓacin rai shi kuma tashi ƙaddarar kenan.
Ya daÉ—e yana kuka a gurin har ya gaji ya dena sai kansa da yake masa wani azababben ciwo, sai da aka kira sallar Magrib sannan ya tashi ya É—auro Alwala.
Bayan ya idar da sallar ya É—akko AlÆ™ur’ani ya shiga karantawa cikin nutsuwa tareda fatan samun salama daga zafi da Æ™unar da zuciyarsa takeyi.
Sai da yayi sallar isha’i a wajen sannan ya tashi yana Æ™oÆ™arin kwantawa yaji murya Abansa yana kiran sunansa.
Da sauri ya tashi ya buÉ—e yana murna.
Hannu Aba yasa ya tallafo haÉ“arsa yana Æ™are masa kallo cikin tausayawa yace, “Yaro!!! fuskarka tayi jajur shatin yatsune sosai akanta waye???”
Ƙasa yayi da lumsassun idanunsa hakan ya bawa hawayen da suka cicciko damar ɗigowa.
Aba yace, “mahaifiyarka ta kasa gaya min kaima haka??, Meyesa kuke son É“oyemin abunda ya shafeni? Æ´an uwanka ne ko??”
FaÉ—awa yayi jikinsa ya Æ™anÆ™ameshi sosai cikin harshen fulatanci yace, “Abana meyesa basa sona wane laifi na aikata musu da suka tsane ni? kenan kuskure ne kasancewata Æ™aninsu??”
cikin sanyi Aba yaja hannunsa ya zaunar dashi sannan yace, “ba kuskure bane sune dai suke aikata kuskuren kayi haÆ™uri ka jure komai wata rana sai labari, ka gaya min waye ya taÉ“a ka yau?”
Girgiza kai yayi yace, “aa Abana dani dasu duk abu É—aya ne suyi komai kawai lokacin su ne karkace musu komai, amma kasani akwai ranar da zata zo wadda ko yatsa É—aya daga cikin su ya nuna min sai na karya yatsan”
Ya ƙarashe maganar cikin shashshekar kuka tareda tsananin ƙunar zuci.
Ummi da ta shigo yanzu ce ta daka masa tsawa da cewa, “kulll Jannah!!!!! karka bari naÆ™ara jin makamancin irin wannan furucin daga bakinka, ko Jaafar shine autansu kuma kasani sama yake da kai ban yarda kayi rashin kunya wa yayyen ka ba koda da minti É—aya suka girmeka, banaso”
Aba yace, “bazeyi ba ma dan ba halinsa bane amma ni zanyi ruwa da tsaki a ciki tinda ni na isa dasu”
da sauri tace, “banaso fa idan kayi musu faÉ—a duk akansa zasu juye raina ne ze Æ™ara É“aci a banza”
Jinjina kai Aba yayi yace, “Yaro!! bana son ganin kana kuka kayi haÆ™uri ka dena ai na dawo”
Lafewa yayi a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya akai akai, Aba ya goge masa ƙwallar da tayi shaɓe shaɓe akan fuskarsa yana yi yana hura masa iskar bakinsa a hankali, hakan da yake masa kuwa ba ƙaramin daɗi yakeji ba ajiyar zuciya har har bibbiyu yake haɗawa kamar ƙaramin yaro.
sai da ya samu nutsuwa sosai har bacci yafara shirin É—aukarsa sannan Aban yace, “tashi muje kaci abinci”
Ba tareda yayi magana ba ya tashi..
lokacin da suka fito Ummi ta gama shirya musu abincin dan haka suka zauna kawai,
Kamar kullum a baki Aba yake bashi yana ci kaɗan kaɗan yana yi yana shagwaɓa.
Share fisabilillah.
Alƙalamin
Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
​
Name: | [Dogon Yaro Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV