Sirrin Rike Miji

Domin Ke da Mai gidan ki Sirrin rike miji

Domin Ke da Mai gidan ki Sirrin rike miji

 

 

 

 

Maigida na qwarai ka ji tsoron Allah, ka sani wannan matar da ka ajiye amana ce a wuyarka ka kare ta daga duk abin da zai 6ata sunanta, ka ba ta abinci yadda ba za ta yi sha’awar na wani ba, ka ba ta sutura yadda ba za a ga tsaraicinta ba, ka biya ma ta buqatunta na shimfida yadda ba za ta yi sha’awar wani da namiji ba._

 

_In ka ga ba ka iyawa to ka nemi magani, Allah bai saukar da wata cuta ba sai da ya sauqaqa mana hanyoyi daban-daban wadan da za mu iya magance su, kenan ba ka da hujjar da ba za ka nemi magani ba, mace tana da haqqin jima’I a wurinka kamar yadda kake da shi a wurinta:_

*ﻭﻟﻬﻦ ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻬﻦ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ*

_Suna da haqqoqi kwatankwacin wadan da suke kansu gwargwadon hali._

_Baqara 228_

 

_Kame sha’awar mace wajibi ne kamar dai sauran abubuwan da suka wajaba a kanka,_ _(Ibn Taimiyyah RL yana ganin wannan gwargwadon qarfin namijin ne da kuma macen)_

_To amma babu adalci namiji ya riqa kallon buqatuwarsa kawai ga mace, sai lokacin da ya ga damar zuwa da kuma yanayin yadda ya ga dama,shari’a ta saka komai a kan mizani ta kuma ba kowa haqqinsa, da yawa matan wasu ko tun zamanin manzon Allah da na sahabbai sun riqa kai kukan mazajensu sabo da shagala da addini tare da mantawa da shimfidunsu._

 

Wadan da suma din wata ibada ce mai zaman kanta,wace Allah yake ba da lada a duk lokacin da aka aikata ta, har wani (R.A) yake cewa: “Shin wani zai biya

buqatarsa (ta jima’I)sannan kuma ya sami lada?”

Annabi (S.A.W) ya ba shi amsa cikin hikima “Ashe ba ka gani ba da zai saka a haram (wato zina) yana da zunubi?”

To kuwa tun da ibada ce, dole mu koyi

yadda za mu yi ta, domin kauce wa shigar shedan.

 

Sannan ka sani kai maigida na qwarai, rashin biya wa mace haqqinta yakan

haifar da 6arna da dama, ka sani zaman lafiyarka shi ne ka yi wa ruwa hanyar da zai riqa wucewa, amma in ka toshe shi

har ya cika ya batse, to fa zai yi wa kansa, ka tabbatar da cewa ba za ka ji

dadin abin da zai faru ba.

 

Wasu matan sukan nemi maza afacebook ko a sarari sabo da qarancin jima’in da suke fama da shi ne, ba shakka zunubi ne mai girman gaske mace ta yi zina ko da ba ta da aure bare kuma tana da shi, kai ma yalla6ai kana da kamusho a ciki, tun da ka qi kare mata sha’awarta.

 

Wani fiqihu da nake karantawa {Wata mace ta zo wajen Umar bnl Khattab RA

take cewa “Sarkin Musulmi, mijina mai yawan azumi ne da rana da qiyamul laili cikin dare, ni kuma ban son na kawo qararsa alhali yana ibada ne”

Sai ya ce “Kai madalla da wannan miji na ki” sai ta riqa maimaita masa maganarta shi kuma yana dada ba ta amsa Daya,

har sai da Ka’ab bn Siwaril Asadiy ya ce “Sarkin musulmi, wannan matar fa tana kawo qarar mijinta ne,sabo da nisan da ya yi wa shimfidarsa” Sai Umar RA ya ce “To tun da ka fahimci maganarta, to ka yi hukunci a tsakaninsu”

Sai matar ta fadi cikin waqa cewa mijinta ya shagala da ibada bai iya biya mata bukata, mijin ya tabbatar da haka, sai Ka’ab ya ce masa a duk kwana hudu tana da haqqin jima’I a kansa, wato kwatankwacin matan da zai iya aure kenan}.

IN BA ZA KA IYA BA KA NEMI MAGANI•

 

“`muhaɗu a darasi na gaba insha Allah“`

.

Leave a Comment

error: Content is protected !!