Dr Jamal Hausa Novel Complete

Dr Jamal Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Dr Jamal Hausa Novel Complete

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

 

 

*Page 1*

 

 

Mallan Adamu haifafen garin Zaria neh, yana zaune a Unguwar Iya dake cikin zaria city, Yana zaune da matarsa Amina da y’arsu guda d’aya mai suna Jaleelah anma ana ce mata Ummy saboda sunan Mahaifiyar mallan Adamu ne…

 

 

Jaleelah yarinya ce y’ar shekara goma sha takwas, tanada Ilimin addini daidai misali, Na boko ne bata samu ba dan a primary five ta tsaya kasancewar Mahaifinta baida hali, ga kuma chuta ta Makanta data sameshi lokaci guda..

 

 

Hakan ne yasa Ummy da Mama suka kasance cikin wani hali har takai Ummyn ta koma Suyan wara kofar gida dan su samu abin rufawa juna asiri. Ummy yarinya ce Mai tarbiya gata kyakyawa ga diri hakan ne yasa samari ke b’ulb’ulowa tako ina suna santa saida yawancin su da maganan banza suke zuwa hakan ne yasa bata kulasu.

 

 

Saurayinta d’aya mak’ocin su Sunanshi Bilal, yana matuk’ar tausayama halinda su Ummy suke ciki duk da shima ba wani k’arfi gareshi ba, lebura neh so dayawa yakan sayo d’an kayan abinci daidai gwargwado ya kawo gidansu Ummy, hakan ba b’aramin d’adi yakema Mahaifanta bah.

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Yau tana shara a tsakar gida ta jiyo tarin Baba gashi Mama ta fita taje mak’ota barka, tsintsiya ta aje dasauri ta k’arkad’e hannunta a jikin k’od’adiyar zanin atamfan dake jikinta, kwance ta sameshi yana tari sosai, idanunshi sun jujuya, tsugunnawa tayu gabanshi ta fashe da kuka

 

 

“Sannu Baba, Sannu Allah ya baka lapia”

 

 

Tarin yake ba k’ak’autawa,

Kuka take duk ta rud’e dama ita abu kad’an kesata kuka, fitowa daga d’akin tayi dasauri ta ja hijabinta dake igiya tayi waje, a xauren gidan ta had’u da Mama tana ganinta ta k’ara fashewa da sabon kuka

 

 

 

“Mama jikin Baba ya tashi”

 

 

Ai ba shiri Mama ta shiga gidan hankali tashe, d’akin ta shiga ta tarar dashi kwance sai aman jini yakeyi, nan da nan Mama ta fashe da kuka tana tsugunne gabanshi, Ummy ta shigo d’akin dasauri idanunta cikeda kwalla

See also  Nimcyluv Novels

 

 

 

“Mama mu kaishi Asibiti”

 

 

D’agowa Maman tayi hawaye na bin idanunta

 

 

 

“Da wani kud’i zamu kaishi Asibiti Ummy?, kinsan bamuda kud’i”

 

 

 

Fita tayi da gudu kamar tab’abba ta fita kofar gida tana waige waige, kuka takeyi sosai lokaci guda tana Addu’a, daky’ar ta samu me napep ta tareshi tace

 

 

“Mahaifina ne baida lapia dan Allag badan niba ka taimaka min mu fito dashi”

 

 

 

Bah musu ya fito daga napeep din suka shiga gidan, har lokacin Mama na zaune gaban Baba tana kuka, ganin Ummy ta shigo da wani yasa ta d’ago dasauri

 

 

 

“Mama mu kamashi akaishi Asibiti”

 

 

 

Bah musu suka kamashi suka fito dashi, komawa Ummyn tayi ta shiga d’akinta ta d’auko wani k’ullin bak’in leda

a hankali ta kwance ledan, kud’i ne yan dari biyar ta rungume kud’in tareda fashewa da kuka, kuka take sosai tana cewa

 

 

“Kayi hak’uri ya Bilal zanyi anfani da kud’inka”

 

 

Ta maida kud’in ta kulle ta fito daga gidan dasauri, Asibitin Gambo sawaba suka nufa, suna lsa ta biya mai keke napeep nurses sukayi Emergency dashi, Suna nan tsatsaye wata nurse ta fito tana rik’e da wani paper a hannu

 

 

 

“Ku kuka kawo wannan patient din koh”

 

 

Mama ta matso

 

 

“Eh mune”

 

 

Papern ta mik’a mata tana cewa

 

 

“Magunguna ne da zaku siya, sai kuma zaku biya kud’in gado”

 

 

Dam! Gaban Mama ya fad’i dan ko sisi bata fido daashi bah, papern tasa hannu ta k’arba, Ummy ta karaso wajan ta karb’i papern a hannun Mama

 

 

“Na magani neh”

 

 

Gyada kai Mama tayi dan tama kasa magana

 

 

“Barinje in amso”

 

 

Tana juyawa Mama ta k’wala mata kira ta juyo dasauri tareda Amsawa, k’arasowa inda take Mama tayi tana kallan cikin idonta

 

 

 

“Ummy ina kika samu kud’i da kike cewa zakije ki siyo”

 

 

 

Inda inda ta soma idanunta cikeda kwalla, Mama ta daka mata tsawa

 

 

 

“Bah dake nake magana bah”

 

 

 

Fashewa da kuka Ummy tayi jikinta ya soma rawa

 

 

 

“Wallahi Mama bah abinda kike tunani baneh, Wallahi Ya Bilal ne ya bani ajiyan kud’in”

 

 

 

“Saboda kuma bakida hankali shine kika d’au kudin zakiyi anfani dashi”

 

 

Kamin tayi Magana Sukajiyo Muryan Bilal din daga bayansu yana cewa

 

 

 

“Mama yanzu nake zuwa gida Ilyasu mai faci yake cemin kuna asibiti”

 

 

 

K’irk’iro murmushi tayi

 

 

 

“Wallahi jikin Mallan d’in neh ya tashi”

 

 

 

Tunda Ummy taji muryanshi kanta ke k’asa, kallanta yayi ya saki Murmushi, Baice mata komai bah ya janye papern dake hannunta yana dubawa

 

 

 

 

Ya d’ago ya kalleta lokacin Mama ta bar wajan ta koma gefe

 

 

 

“Hrt ya jikin Baban”

 

 

 

K’anta a k’asa tace

 

 

 

“Dasauk’i basu dai bari mun ganshi bah”

See also  Taimiyyah Hausa Novel

 

 

 

 

Lalluba aljihunshi yayi fuskanshi da alamar damuwa, muje muji nawane kud’in maganin. A tare suka jera har zuwa pharmacyn, lissafi aka musu harda kud’in gado dubu goma sha biyar, wani miyau Ummy ta had’iye dakyar tana kallan mutumin, d’agowa tayi ta kalli Bilal din murya chan k’asa tace

 

 

 

“Ya Bilal mu d’auki Baban kawai mu koma gida”

 

 

 

Girgiza mata kai yayi dasauri yace

 

 

“Aa Hrt, ko zamu koma gida ne kid’auko kud’in nan”

 

 

 

A kunyace tace

 

 

 

“Ga kud’in nan”

 

 

 

Mik’amai tayi kanta a k’asa, amsa yayi ya irgo dubu goma sha biyar ya biya ya rage dubu biyu, suna dawowa suka samu ana chanza mai d’aki zuwa ward.

 

 

 

A Tare suka shiga d’akin, Mama ta mai godiya sosai ganin an sayo maganin da duk abinda ake buk’ata, Itama Ummyn tamai godiya shidai baice komai bah sai Murmushi kawai dayake.

 

 

 

 

Bilal kyakyawan saurayi ne d’an shekara Ashirin da biyar, Bak’i ne shi anma ba wulik ba, yana yanayi da Black americans, Yanada tsayi da fafad’ar kirji, idanunshi dara dara masu kyawun gaske. Mahaifinshi d’an Asalin Garin Yola neh, su biyu iyayenshi suka haifa shida k’aninshi Bahar, Mahaifinsu ya rasu tun yanada shekara Ashirin, Yanzu suna tareda Mahaifiyarsu ne. Mak’ota ne dasu Ummy tun tasowanta Allah ya d’aura mai santa da kuma tausayinta na halinda suke ciki, zan iya cewa shine kusan k’arfin gidansu Ummyn Wannan knan..

 

 

Ummy Abduol✍🏻

 

♠♠♠♠♠♠♠♠

♠♠♠♠

*JAMALUDEEN*

♠♠♠♠

♠♠♠♠♠♠♠♠

 

 

 

By *Ummy Abduol*

 

 

 

 

Dedicated to my *Late Siblings*

 

 

 

*Page 2*

 

 

Satin Baba d’aya aka sallameshi, duk d’awainiyar su Bilal ya d’au nauyi har aka sallamesu suka dawo gida. Albarka kam Bilal yasha shi wajan Baba da Mama Ummy koh rasa bakin godiya tayi..

 

 

 

Bayan sun dawo Ummy ta koma bakin sana’arta na tuyan wara a k’ofar gida, sam Bilal baya san suyan datakeyi anma ba yanda zeyi haka ya hak’ura duk da zuciyarshi da ke misi suya kullum idan ya dawo aiki ya ganta k’ofar gida..

 

 

 

Yauma kamar kullun tana k’ofar gida tana suya, sam yau ba ciniki duk ta damu gashi yau basuda ko k’wayar hatsi a gidan kuma bataso Bilal ya sani dan d’awainiyar tasu tana ganin yayi yawa, Tana cikin tuya taji Muryan Bilal a bayanta cikin sanyayar Muryansa

 

 

 

“Sannu da aiki Hrt”

 

 

 

Da d’an murmushi ta juya ta kalleshi, sanye yake da wandan jeans duk ya fatattake daga guiwa, da bak’ar riga itama kod’adiya, fuskanshi da kayan jikinshi duk siminti duk yayi butu butu, da alama daga wajan aiki yake

 

 

 

“Sannu da dawowa”

 

 

 

“Yauwa sannu Hrt, ya kasuwa”

 

 

 

 

Fuskanta d’auke da murmushi tace

 

 

“Lapia lau”

 

 

 

 

“Fad’amin damuwarki”

 

 

 

Duk’ar da kai tayi tana y’ar fara’a

 

 

 

“Babu wata damuwa”

 

 

 

“Bai dace dakeba Hrt ki rink’a b’oyemin damuwarki, babu wanda zak’i fad’ama damuwarki duk duniya daga Baba da Mama sai ni. Duk inda nake ko me nake sai nayi tunaninki, ina sanki Ummy bazan iya rayuwa baki bah, a duk sanda kike cikin damuwa ina ganewa saboda tsananin damuwa da nakeyi dake”

See also  Love Cycle Hausa Novel

 

 

 

 

Hawaye ne suka cik’a mata ido, tabbas abinda Ya Bilal ya fad’a gaskiya ne akan irin sanda yake mata, anma dole ta rink’a b’oye mata damuwan da suke ciki saboda shima ya rink’a hutawa da d’awainiyarsu. Magananshi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi

 

 

 

“Hrt fad’amin meke damunki?”

 

 

 

Murmushi tayi tana kallanshi

 

 

 

“Babu komai Ya Bilal”

 

 

 

 

D’an dutsen dake kusada ita yaja ya zauna ya kafeta da idanunshi

 

 

 

“Ashe har akwai ranan da zaki b’oyemin damuwanki Hrt, nayi tunanin a iya zaman mu da soyaiyar dake tsakanin mu da kuma shak’uwa ba abinda zamu b’oyema juna. Ina sanki Ummy kuma bazan fasa fad’a miki zan iya yin komai akan sanda nake miki bah”

 

 

 

Kuka ke k’okarin kufce mata anma ta shanye ta dake tana cewa

 

 

 

“Ya Bilal ba abinda zance maka saidai Allah ya saka da alheri ya baka lada, ya kuma saka a aljanna. Kayi mana komai nida Iyayena wanda y’an uwanmu basu mana bah. Bansan dame zan saka maka ba Ya Bilal, Ina so n.. ”

 

 

 

Saurin k’atseta yayi ta hanyar d’aga mata hannu

 

 

“Ya isa Hrt, bana buk’atar godiyanki. Damuwarki kawai nake san ji”

 

 

 

 

“Ya Bilal yanzu fa ka dawo daga aiki ko gida bakaje bah”

 

 

 

Kallanta yayi tareda marairaice fuska

 

 

 

 

“Hrt pls mana fad’amin, bana iya jure ganinki haka”

 

 

 

K’arya tamai da cewa kanta ke ciwo, duk da bai yarda ba anma ya bita a hakan dan yaga bataso s fad’amai. Wani yaro ne yazo siyan awaran da kanshi ya iriga ya bashi Ummy nata kallanshi da murmushi, wani sanshi da tausayinshi ne ke k’ara shiga zuciyarta.

 

 

 

Mik’ewa yayi yasa hannu a aljihu ya ciro d’ari biyar ya mik’a mata

 

 

 

“Hrt ki rik’e wannan idan kuna buk’atar wani abu”

 

 

 

Duk da suna da buk’atar kudin anma tayi saurin girgiza kai

 

 

 

“Aa bama buk’atar komai”

 

 

Hannunta ya rik’e ya chusa mata kud’in a tafin hannunta yana kallan fusanta

 

 

 

 

“Hrt bana san musu pls, anjima zanzo muje chemist”

 

 

Bai jira mai zatace ba yabar wajan ya shiga gida.

 

 

Binshi tayi da kallo harya shiga gida sannan ta sauke ajiyan zuciya ta cigaba da suyanta. Cikin ikon Allah ta saida waran da wuri ta shiga da kayan gida.

 

 

Mama ta samu tsakar gida tana hura wuta

 

 

 

“Sannu da aiki Mama”

 

 

“Yauwa sannu Ummy har kin gama?”

 

 

 

“Eh Mama ya jikin Baba”

 

 

 

“Dasauk’i kinga ma wuta zan hura na d’aura mai ruwan wanka”

 

 

 

 

Kayan ta aje ta amshi aikin a hannun Maman, hura wutan tayi ta d’aura ruwan sannan ta lek’a ta gaida Baban. Albarka ya soma sa mata harda hawaye dan yana matuk’ar tausaya ma Iyalin nashi. Kud’inda Bilal ya bata ta nunama Baba yana gani ya fashe da kuka, Itama Ummyn kukan ta soma tana rarrashin Baban

 

 

 

“Allah ya sakama yaron nan da Alheri”

 

 

 

 

Mama dake bakin kofa ta amsa da Ameen.

 

 

 

“Ku cigaba da hak’uri Ummy, komai yayi farko zaiyi k’arshe, jarabta ce haka Allah yaso, ku cigaba da min Addua”

 

 

 

Mama itama ta fashe da kuka

 

 

 

“Allah ya baka lapia Mallan, insha Allahu zaka warke ka cigaba da walwalanka yanda kake da”

 

 

 

Ummy ta mik’e ta fita daga d’akin, hijabinta tasa ta fita tayo musu chefanen d’an abinda zasu ci abinci ta dawo gida. Tana shiga ta tarar da Ya Bilal zaune a tsakar gida shida Mama suna hira..

 

 

 

Ummy Abduol



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

​

 

 

Name: [Dr Jamal Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top