Dubu Jikar Mai Carbi Hausa Novel
[24/07, 11:48 am] +234 803 192 1625: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER’S ASSO…
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 1
Babban gida ne mai É—auke da É“angare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taÆ™aice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haÉ—a Kakanni, ‘ya’yaye da jikoki. Garin ÆŠangwauro yana É—aya daga cikin Æ™anana Æ™auyukan da ke cikin Æ™waryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin ÆŠangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laÆ™abi da gidan ‘Ya’ya da yawa.
Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba.
Bisa ga al’adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taÆ™aita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi.
A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu, ai ita ma Kakanta ne.
Sumi sumi sumi ta tashi da yaÆ™unannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron Æ™arshe daga shi sai fita Hali dubu ta É—ora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, “Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace.” Lokaci É—aya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta Æ™al don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haÆ™uri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya Æ™arasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, “Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?” Kamar sabuwar Marainiya haka ta É—ago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon Æ™ofa ta kuma duÆ™unÆ™une kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haÉ—in baki dukansu suka kalli bakin Æ™ofar suna neman Æ™arin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu Æ™ofar da É—an yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, “Me ye a cen É—in?” Hali dubu ta kuma kallon Æ™ofar ta rushe da kuka tana cewa, “Baffa ne!” Cikin haÉ—in baki duka suka ce, “Baffa kuma? Wane Baffan?”
Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, “Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!” Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faÉ—a-faÉ—a ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu.
Can É—akin Yaya Babba ta shiga ta haye Æ™arshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama’a a gidansu. Domin ba Æ™aramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar Æ´ar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faÉ—o mata ta yanda za ta kore jama’ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba’in da mutuwar da sauran baÆ™i tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin Æ´an uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba Æ™aramin daÉ—inta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga É—akin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba Æ™aramin daÉ—i ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya.
Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata.
Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haÉ—a kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen.
DA DADDARE
Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da Æ™ananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin bacci da yake tashi daga É—akunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa’i cikin É—aya daga cikin É—akunan Æ´aÆ´an gidan. Sai da ta ci baccinta ta more sannan ta farka cikin talatainin dare ta ji gidan tsit kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki ta zaro kayan marigayi Baffa ta saka rigarsa da babbar riga har da hula ta naÉ—a rawaninsa ta É—auki zabgegen carbinsa ta maÆ™ala ta fito, hasken farin wata ne ya haska mata hanyar da za ta rinÆ™a bi har fice daga sashen gabaÉ—aya. Can wurin da ya zamewa Marigayi Baffa mai carbi wurin alwala can ta je ta tsugunna, daga nesa idan ka hango Dubu a tsugunne sai ka rantse da Allah Baffa ne, sai da ta waiga hagu da dama sannan ta taÆ™arÆ™are ta fara zabgo kaki irin yanda Baffa yake yi, Baba Sule da ke kwance cikin baccinsa ya fara jin alamar kaki tamkar yanda mahaifinsu yake yi duk asuba. Fakare ya yi yana zare idanu, yana cikin wannan yanayin ya sake jin an yi kaki har da irin tarin tsofaffin nan da Baffa yake yi. Janyo wayarsa ya yi yana dubawa ya ga Æ™arfe biyun dare, nan take ya hau murza idanu yana sake kasa kunne. Dubu kamar ta san ana sauraronta ta kausashe murya sai ka rantse da Allah Baffa ne yake magana ta fara cewa, “Tabbas rayuwar barzahu daÉ—i gare ta.” Baba Sule ya waro idanu wace cikinsa na karta masa, don ya tabbata hatta dabbobin gidan da suna magana za su ce sun shaida maganar Baffa ce cikin daren nan.
Dubu na tsugunne ta ji alamun tahowa wata zuciyar ta ce mata ta tashi ta É“uya, wata kuma ta ce ta zauna ta ci gaba da abin da take yi. Tarin Inna Furai ta ji ta saci kallonta ta hangota da Æ´ar buta a riÆ™e za ta je banÉ—aki. Dubu wani kakin ta sake yi tana daga tsugunne, hasken farin wata ne ya hasko mata mutum durÆ™ushe da fararen kaya da rawani tamkar marigayin mijinsu. Gabanta ne ya yi mummunan faÉ—uwa ta fara motsa baki cikin addu’a don a zatonta mugun gamo ta yi.
ÆŠauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raÉ—au a kunnenta yana cewa, “Wato ita dai rayuwar barzahu daÉ—i gare ta. Babban daÉ—in idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka.” Inna Furai na jin haka ta dafe Æ™irji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, “Yau na haÉ—u da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roÆ™eka karka jarrabe ni ta wannan fannin.” Dubu na jin haka ta miÆ™e tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, “Wuni É—aya har na yi abokai miliyan É—aya da É—ari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara É—auka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa É—aukan amarya.” Inna Furai tuni fitsarin da take riÆ™ewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta.
Dariya ce ta so Æ™wacewa Dubu amma ta maze ta ce, “Ƴan uwana Æ´an sama Jannati! Ku zo na fara samo muku Æ´ar uwa.” Inna Furai ta saki salati tana cewa, “Yau na haÉ—u da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo Æ™arshe.” Dubu sunkuyar da kai Æ™asa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, “Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da Æ´aÆ´anki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi’u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haÆ™iÆ™a sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana.”
Baba Sule tuni cikinsa ya É—uri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta Æ™ara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, “Ki isarwa da mutanen gidan nan saÆ™ona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu É—auki É—aiÉ—ai. Shi kuma na É—aki da yake laÉ“e yana sauraronmu, shi kuma É—auke shi za mu yi gabaÉ—aya.” Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube Æ™asa. Gabanta ne ya faÉ—i ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maÆ™e murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma’ajiyar kayan Baffa ta lallaÉ“a ta shige ta kwanta.
Ihun da Dubu ta yi ba Æ™aramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a É—auke shi matuÆ™ar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riÆ™e Æ™am, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riÆ™o mata hannu ta ce, “Don Allah sakarni Uban Æ´an naniÆ™a.” Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba.
Daga É—aki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya É—aga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miÆ™e tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faÉ—i yace, “Wa nake gani kamar Inna a Æ™asa.” Sahura ta dafa kafaÉ—arsa ta ce, “Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture.”
Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a É“ata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haÆ™ura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, “Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare.” Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa.
Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga Æ™ofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaÉ—aya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun Æ™ofa firgigit ta miÆ™e sai ji ta yi Sule ya riÆ™e hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raÉ—a ya fara cewa, “Kada ki yi magana za su yi sama da ke” Waigawa Sahura ta yi tana kallon Æ™ofa don ita a tunaninta masu buga Æ™ofar ne za su yi sama da ita. Suka Æ™arajin bugun Æ™ofa Auwalu yana cewa, “Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faÉ—i.” Sahura ta ja guntun tsaki ta ce,
“To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu.” Baba sule ya sake Æ™asa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faÉ—a ya ce, “Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waÉ—annan Æ´an sama jannati ne suka rikiÉ—a. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar É—ari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miÆ™e tana fusgar hannu ta ce, “Sakarni ko Æ´an Æ™asa jannati ne babu abin da zai hanani fita.”Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi.
Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taÉ“a irin wannan wasan da shi, don haka ta sake É“ata fusaka ta ce, “Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?” Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake Æ™anÆ™ance murya ya ce, “Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni.” Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miÆ™e tana Æ™oÆ™arin fisge hanunta amma abin ya ci tura don Æ™arfin mace dana namiji ba É—aya.
Auwalu da ke jin Æ™usur-Æ™usur a É—aki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga Æ™ofar É—akin ma’aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta Æ™walla masa kira tana cewa, “Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji.” Auwalu ya waigo ya ce, “Shiga É—aki Inna zan kai na dawo.”
Dubu na daga É—aki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanÉ—a sai da ta zo daga bakin Æ™ofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, “Wato ita rayuwar barzahu daÉ—i gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na É—auki mai É—akin nan.” Cikin Yahanasu ne ya kaÉ—a nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari. Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, “Amma ita Yahanasu za mu É—aga mata Æ™afa sai dole ta bi sharaÉ—inmu ko ba haka ba Æ´an sama jannati?” Dubu ta sake sauya murya ta ce, “Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faÉ—a É—akin.” Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, “Wallahi ku faÉ—a ko meye zan bi.”
Dubu ta maÆ™ale murya ta ce, “Dole ki zama makauniyar Æ™arfi da ya ji muddin kika buÉ—e idonki sai dai ki wayi gari a Æ™iyama.” Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, “Wallahi na rufe har abada ba zan sake buÉ—e su ba amma don Allah karku cutar da ni.”
Dubu har da Æ´ar tsawarta ta ce, “Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?” Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, “Na rufe wallahi na rufe.” Dubu ta saki murmushin mugunta a Æ™asan zuciyarta tana cewa, “Yau zan ga Æ™aryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna.” A fili Dubu ta ce mata, “Maza tashi tsaye ki rungume bango.” Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taÉ“o bango.
A hankali Dubu ta zura kai ta leÆ™a ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faÉ—a É—akin cikin sanÉ—a. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta É—aga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a Æ™eya, sai ta fara wani gunji tana cewa, “GargaÉ—in yan sama jannati kenan.” Tana faÉ—ar haka har ta fice daga cikin É—akin.
Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buÉ—e idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo.
Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake É—urar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata.
Lokacin da Auwalu ya Æ™arasa É—akin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan Æ™aramin gado, sannan ya fara tashin Æ™anwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba Æ™aramin É—aga hankulan mutanen É—akin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riÆ™o hannunsa ta ce, “Auwalu! Yau na haÉ—u da zazzagar rayuwa. Don haka ka haÉ—o mini kawunan Æ´an uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace.”
Auwalu da sauran mutanen É—akin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta Æ™ara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, “Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faÉ—i ba.” Wannan magana ba Æ™aramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta É—ago ta ce, “A kan bulikiya na faÉ—i! Lantan bana son zazzagar wulaÆ™anci. Kai Auwalu ka tara mini Æ´an uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba.” Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga É—akin. Haka ya rinÆ™a bi É—aya bayan É—aya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa Æ´an uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daÉ—in daÉ—awa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faÉ—i a hanyar banÉ—aki sai ya wartsake masu tafiya É—akinta na yi masu jaje suma suna yi.
Kafin wani lokaci tuni É—akin Inna Furai ya cika da Æ´aÆ´anta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su É—aya bayan É—aya sai kawai suka ga ta É—aga riga ta ce, “Larai bisimillah” Larai zuciyar ta É—aya ta É—auka Inna Furai so take a Æ™arasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuÉ“e mata riga. Cikin Æ™araji Inna Furai ta fisge tana cewa, “Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka” Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci É—aya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, “Inna ki yi hakuri me kike so?”
Inna Furai ta É—ago mamanta É—aya ta ce, “Mahaifinku ya zazzage mini albarka É—azu nan domin daga zuwansa lahira har ya haÉ—a kai da Æ´an sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaÉ—aya ba amma Auwalu ungo sha ka ji.”
[24/07, 11:48 am] +234 803 192 1625: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER’S ASSO…
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 2
Auwalu sam bai fahimci inda maganar Inna Furai ta dosa ba, don tun da ya ji ta ambaci Mahaifinsu ya tabbatar da zafin ciwo ne yake damunta da kiÉ—imewar rashin da aka yi musu. Saboda gudun faÉ—anta ya sa ya wayance da cewa, “Inna ban fahimci abin da kike faÉ—a ba. Amma kuma duk wanda ya mutu kin san sai dai mu bishi da addu’a ita ce mafita.” Inna ta yi Æ™uri tana kallonsa sai zuwan can kawai ta fashe da kuka. Lantan da ke gefe takaici da baÆ™in ciki gabaÉ—aya suka turniÆ™e ta, don gani take kamar har da biyu Inna Furai take lanjarewa. Kasa haÆ™uri ta yi ta ce: “Furaira don Allah ki shafa mana lafiya ki bar mu, mu ji da abin da yake damunmu. Haka kawai ki tayar mana da balli a tsakiyar dare akanki aka fara mutuwar miji? Ko kuma ke kaÉ—ai kika san zafin miji muna zaune ki ishe mu da zancen fatalwa. Ki barni na kwanta na yi baccin da ban samu na yi shi jiya ba.”
Inna Furai ta fyace majina da gefen zaninta ta waiga ta ce, “Wallahi babu Æ™atuwar Matar da za ta zo mini É—aki ta nemi kawo mini zazzagar albarka ido biyu. Idan ba za ki iya ba ki tashi ki fice dama ni bana gayyar tsintsinya da bulugari, bare kuma mafici abin banza.” Lantan jin maganar Inna Furai ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta zaburo a hasaale ta ce, “Ban da Æ™addara da rashin É—an’uwana da na yi, me zai kawo ni É—akinki kaico Allah ya jiÆ™anka Yaya Mamman. Wai yau jininka ake wulaÆ™antawa saboda Æ™asa ta rufe mata ido, kai jama’a É—an’adam butulu. Wanne irin karamci ne ÆŠan’uwana bai yi miki ba?”
Inna Furai ta jingina da Æ™arfen gado sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, tana yi tana fatar majina. Abin duniya goma da ashirin ne damu su Auwalu, don haka kowa ya yi jim! Babu wanda ya iya tofa magana É—aya sai gani suka yi Inna Furai ta fara haÉ—a Æ´an kayayyakinta na sawa da ke kan gado. Sabi’u ya ce: “Inna lafiya kuwa wai me yake faruwa ne kike haÉ—a kaya?”
Inna Furai ta juyo a fusace ta ce, “Zaman ku a nan bai amfane ni da komai ba. Kuna gani ta gama zazzage mini rashin mutumci a ka babu wanda ya tanka mata. Wallahi ko ku bi mini haƙƙin zazzagar albarkar da ta yi mini a ka ko kuma yanzu na fice na baku wuri ku yi yanda kuke so. Gara ni tawagar Malam da Æ´an sama jannati ta zo ta É—auke ni ko kowa ya huta, dama na kiraku ne domin mu kashe mu binne amma da alama ku dai ba Æ´an goyo ba ne, don na lura za ku iya zazzage mini sauran albarka da ta rage mini a kaina.
Gabaɗaya shiru suka yi suna nazarin abin da yake damun Mahaifiyarsu, don rikici sun san Mahaifiyarsu mace ce mai matuƙar rikici amma wannan karon gani suke har da mutuwar mahaifinsu da ta taɓa ta.
Lantan na gama sauraron Inna Furai ta miÆ™e tsaye tana shartar Æ™walla, É—an Æ™ullin kayanta da ke Æ™arÆ™arashin gado ta janyo ta fara kiciniyar É—orawa a ka tana matsalar hawaye. Da sauri Auwalu ya miÆ™e ya riÆ™e kayan yana cewa, “Inna Lantana don Allah ina za ki a tsohon daren nan?” Lantan ta kunto mayafinta ta yafa a kanta ta ce, “Auwalu don Allah karka kawo mini maganar da za ta tunzurani har ta kai ga na nemi shaÆ™e wannan tsohuwar har lahira. Duk irin cin mutumcin da ta yi mini a gabanku baku gani ba za ka taso tsalo-tsalo kana tambayata ka bar ni yau ko Æ™asa da sama za ta haÉ—e ba zan kwana a gidan nan ba.”
Nan fa hayaniya ta fara ta shi a cikin gidan, Inna Furai na gama saurarar maganar Lantan ta sa hannu bibbiyu ta dafe Æ™irji a razane tana zare idanu kamar wacce ta yi tozali da kumurcin maciji. Bata tanka musu komai ba sai gani suka yi ta sauko Æ™asa daidai wurin da Lantan take tsaye ta fashe da kuka haÉ—e ta rungumo Æ™afafuwan Lantan tsam a jikinta. Tana cikin kuka ta É—aga kai ta dubi Lantan tana cewa, “Wallahi ba za ki bar É—aÆ™in nan ba sai kin zazzage ragowar numfashin da nake shaÆ™a, Lantan yau ni kike muradin kashewa a gaban Æ´aÆ´ana. Ai kuwa ko ba yanzu na mutu ba na rataya a wuyanki Kai Auwalu ku shaida haka.”
Inna Furai ta juya ga su Auwalu tana musu mugun kallo ta ce, “Allah na tuba wacce uwar na haÉ—a da su bayan alaÆ™ar haihuwa? Da su Auwalu da Sabi’u kuma ni kam gara ma a ce ban da kowa tun da babu mai tare mini faÉ—a a gidan nan. Har ana niyyar halakani da sauran rayuwa kai jama’a Lantan an ya kina tsoron Allah kuwa? Duk wanda ya kashe wani dai wuta za shi.”
Lantan ta yi tsalle can gefe abin ka da da marar jiki, can gefen babban gado ta matsa tana cewa, “LaÆ™adi ja’akum… Tuf! Aniyarki ta faÉ—a kanki karki ja mini masifa ki maÆ™ala mini sharrin kisan kai ina zaune Æ™alau.” A wannan karon Inna Furai bata tanka mata ba sai gani suka yi zaraf ta fice daga É—akin, da sauri iyalanta suka bi bayanta suna roÆ™on ta dawo É—aki saboda dare.
Tana fita ita ma Lantan ta sa Æ™afa ta fito ganin haka ba Æ™aramin É—aga hankalin su Auwalu ya yi ba, musamman shi da yana tsaye a nan ne amma zuciyarsa na wurin Yahanasu yana tunanin halin da take ciki. Inna Furai na ganin Lantan ta fito ta bita jiki a sanyaye kamar kazar da ake jefa da gishiri ta ruÆ™o hannunta sannan ta fashe da kuka. Ita ma Lantan zuciyarta ce ta karye sai kawai ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan Inna Furai ta ce, “Yanzu Lantan da na barki tafiya za ki yi a daren nan?” Lantan ta fyace majina a haÉ“ar zaninta ta ce, “Ina zan iya tafiya na barki Furai kina cikin jimamin rashin miji, Furaira rashin miji tashin hankali ne har kin tuno mini da rasuwar Mahaifinsu ÆŠan’iya kai rayuwa babu tabbas Allah ya jiÆ™anka Malam Mudassiru.” Lantan ta rushe da matsanancin kuka. Rabe ya matso da niyyar rarrashinsu Inna Furai ta doke hannunsa tana cewa, “Allah wadaran naka ya lalace. Wallahi kaf gidan nan banga wanda zai hanani zazzage muku albarka ba. Wai kamar yanda Lantan take a wurina ta tashi za ta tafi cikin dare amma babu mutum É—aya da zai hanata tafiya kaico! Wallahi kun ji jiki Æ´an bakinciki bantaÉ“a sanin bakwa Æ™aunar aminiyata ba kuma Æ™anwar Mahaifinku ba sai yau.”Inna Furai na gama maganar ta ja hannun Lantan suka bar su Auwalu a tsaye sake da baki.
Ba su da zaÉ“i haka suma suka bi su Inna Furai ciki, cikin Æ™aguwa Auwalu ya ce, “Inna za mu iya tafiya yanzu?”
Inna Furai ta saki salati ta na kallon Auwalu da wani yanayi har sai da ya tsargu ya É—an fara sosa Æ™eya sannan Inna Furai ta ce, “Wallahi kai dai Auwalu na riga da na san matsayina a wurinka. Tun mahaifinka na raye har ya mutu ban taÉ“a musa wa maganarsa ba, sai yau don Æ™asa ta rufe masa ido?” Ta fashe da kuka tana ci-gaba da cewa, “Ban shirya mutuwa da shiga jahanna ba. SharaÉ—i fatalwar mahaifinku ta bani sai na shayar da ku mama kamar yanda na shayar da ku kuna yara, kuma ban ga wanda zai hanani bin umarninsa ba.”
Lokaci É—aya suka É—auki salati gabaÉ—aya saboda ta’ajibin jin maganar Mahaifiyarsu, Larai cikin matsananciyar damuwa ta ce, “Inna kin san me kike faÉ—a kuwa? Yanzu kina nufin Baba ne ya yi miki fatalwa? Inna don Allah kar wani abu ya ruÉ—e ki ko ya tsorata ki saboda wanda ya mutu ya mutu kenan ba zai Æ™ara dawowa ba. Sai dai idan shaiÉ—an ne yake son razanar…”
A hassale Inna Furai ta katse Larai da cewar, “A’uzubillahi minasshaÉ—anirrajim. Ba zan ga shaiÉ—an da idona ba Larai kafirta ni kike son yi da za ki haÉ—a ni da ShaiÉ—an la’anannan Allah?” Larai rasa hanyar da za ta É“ullowa Mahaifiyarta ta yi don gabaÉ—aya sun rasa gane kanta. Lantan da ke gefe ta kalli Larai ta ce, “Wallahi ki tubar wa Allah idan ba haka ba, azabar Allah tuni za ta yi fata-fata da ke. Kuma ni gani nake maganar Furaira tana kan hanya don ni kaina lokacin da Malam Mudassiru ya rasu har gizo ya riÆ™a yi mini a tsakar É—aki. Don haka ku yi biyayya idan ba haka ba duk cikinku babu mai kaucewa azabar Ubangiji, musamman kai Rabe da ka fi tsoka wallahi tuni wuta za ta tsotse namanka ka lalace a jahannama.”
Ganin wannan lamarin yana Æ™oÆ™arin zama babba ya sa Auwalu ya zame jikinsa ya je Shagon Soro ya taso Yayan mahaifinsu ya sanar da shi halin da ake ciki. Har É—akin Inna Furai ya shiga yana shiga ya same ta, ta yashe riga a sama tana kumfar bakin Larai ta tsugunna ta fara karÉ“a tun da sauran mazan taurin kai za su nuna mata. Da sauri ya É—auke kansa gefe don bai yi tsammanin abin da suka faÉ—a da gaske ba ne. Nan take ya shiga yi mata nasiha amma duk da haka Inna Furai ta shafawa idonta toka ganin haka ya sa ya fara lallashin ta bari zuwa safiya sai a san abin yi. Da Æ™yar da suÉ—in goshi aka samu shawo kan Inna Furai ta haÆ™ura zuwa safiya sannan kowa ya kama gabansa. Bayan tafiyarsu Lantan ta zabga uban tagumi sannan ta ce, “Yanzu Furaira da idanunki biyu kika yi tozali da Yaya Mamman ni fa É—azu Æ™arya na kirfo da na ce ina ganin Fatalwar Mudassiru, saboda yaran nan sai su raina mu ni kuma a duniya babu abin da na Æ™i jini irin raini.”
Inna Furai ta miÆ™awa Lantan hannu ta ce, “Lantan taÉ“a ni na ji.” Da sauri Lantan ta kai hannu tana shafa hannunta. Inna Furai ta mirtsika ido ta ce, “Billahilazi idan har wannan taÉ“awar da kika yi mini mafarki ce to a mafarki na ga Malam. Wallahi da idanuna na ganshi a wurin zaman alwalarsa amma tun da baku yadda ba nan gaba na kuma ganinsa nasa ya fitowa kowa a zahiri.” Kamar wacce aka tsamo daga ruwan sanyi haka jikin Lantan ya yi sanyi ta rasa abin faÉ—a don hantar cikinta ta fara kaÉ—awa musamman da ta san Inna Furai ba ta yin rantsuwa sai da Æ™waƙƙwaran dalili. Kwanciya suka yi sai dai kowa da abin da yake wassafawa a cikin zuciyarsa.
Duk cikin ƴaƴan Inna Furai babu wanda ya fi farinciki da tafiyarsu irin Auwalu saboda zuciyarsa gabaɗaya hankalinsa yana wurin Yahanasu don ya san a wannan lokacin tuni ta yi fushi sai ya yi aikin rarrashi. Yana tafe yana haska fitila har ya ƙarasa ɗakin, sai dai turus ya yi a ɗan tsorace yana karewa ɗakin da Yahanasu kallo. Fitsarin da ya ƙarasa gangarawa ƙafarsa ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, matsawa ya yi gefe yana leƙa fuskar Yahanasu da ke manne da bango ya ce,
“Yahanasu lafiya kuwa?” Yahanasu na jin muryar Auwalu ta rushe da kuka tana cewa, “Auwalu fatalwar Baba na gani wallahi shi ne har cewa ya yi za su tafi da ni.” Cikinsa ne ya bada wani sautin Æ™ulululu! Da sauri ya ja baya yana dafe Æ™irji ya ce, “Kina nufin da gaske kema kin ga fatalwar Baba?” Yahanasu ta nuna masa gadon bayanta ta ce, “Duba ka ga shatin carbinsa a bayana har dukana ya yi da shi kuma ya ce daga yau kar sake buÉ—e idona.” Tsoro ne ya mamaye zuciyar Auwalu musamman da idanunsa suka yi tozali da shatin carbin Mahaifinsu ruÉ—u-ruÉ—u a jikinta. Hankalinsa bai Æ™ara tashi ba sai da ya hango wani guntun likkani a gefen Æ™afar Yahanasu. Da sauri ya fisgota suka faÉ—a gado jikinsa na rawa ya ce, “Yahanasu wallahi maganarki haka take kin ga Likkafani can a Æ™asa.” Yahansu na jin haka ta Æ™ara rintse ido tana kuka kamar hawayenta za su Æ™are. Auwalu ne ya yi ta maza ta miÆ™e cikin sanÉ—a ya banko musu Æ™ofa da Æ™arfi ya sa sakata.
Duk abin da yake faruwa a kunnen Baba Sule da Sahura har zancen Likkafani, wannan maganar ba ƙaramin ɗaga musu hankali ta sake yi ba. Don da har bacci ya fara yunƙurin awon gaba da su kukan da Yahanasu ta rushe da shi ne ya wartsakar da su tare da sa su yin carko-carko kamar masu shirin ko ta kwana.
Dubu tun da ta koma ta yi luf sakamakon motsinta ya so tashin Hasiya Matar Rabe, don haka ta yi kasaƙe daga haka ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita don hatta sallar Asuba sai da aka yi da gaske sannan Dubulliya ta samu gabatar da ita.
Washegari.
Jama’ar gidan gabaÉ—aya kowa ya tashi an ci gaba da harkoki kamar ba taron mutuwa ba. Sai dai gabaÉ—aya labari ya watsu a ko’ina Inna Furai ta yi ido huÉ—u da fatalwar Maigaidansu, labarin da wasu suka riÆ™a ganin kamar tsufa da rikici ne yayin da wasu suke ganin tsabar dukan da mutuwar ta yi mata ne. Sai dai babban abin da ya ja hankulan mutane ganin É—akin Baba Sule da Auwalu ya rufe. Ko motsinsu babu wanda ya ji bare a sa ran za a ga fitowarsu.
ÆŠakin Baba Sule aka fara zuwa ana bugawa, Sahura ta zabura za ta miÆ™e saboda ta ji muryar mutane don ta yanda ta ayyanawa zuciyarta muddin ta samu ta fice daga É—akin to ba za ta Æ™ara kwana a gidan ba sai gidan Mahaifinta. Sai dai tana miÆ™ewa caraf Baba Sule ya damÆ™i hanunta yana cewa, “Ina za ki tafi ki bar ni?” Sahura ta Æ™irÆ™iro murmushin yaÆ™e ta ce, “Ai mutanen gida sun tashi ka ga muma sai mu fita zaman É—aki ba zai kai mu ba.” Baba Sule ya yi fakare yana nazari sannan ya ce mata, “Sahura yau ko bayan gida za ki shiga wallahi sai dai mu tafi tare, don ba zan bari matattu su tafi da ni da kwana na a gaba ba.” Bugun Æ™ofar ne ya tsananta don haka suka taso riÆ™e da hannun juna suka zare sakata, sai dai suna buÉ—e Æ™ofa kyallen likafanin da Dubu ta soka musu ya faÉ—o. Daga waÉ—anda suke tsaye a Æ™ofar É—akin har su na cikin É—akin bazama suka yi a guje, suka yi cikin gida. A cen É—akin Yaya Babba suka yada zango sai dai har lokacin Baba Sule yana riÆ™e da hannun Sahura. Yaya babba sakin baki ta yi tana kallon Baba Sule da ya yi tsamo-tsamo a cikin mata ta ce, “Sule me kake yi a kan cinyar Uwani?” (Uwani Æ™anwar Mahaifiyar Sahura ce.) Baba Sule gabaÉ—aya zuciyarsa a dagule take saboda gani yake rayuwarsa ta zo Æ™arshe.
Ba baka sai kunne. Baba sule ban da hawaye babu abin da yake yi. Wannan shirun da Baba Sule ya yi ba Æ™aramin É“ata ran Yaya Babba ya yi ba, don haka ta dube shi ta ce, “Bana son iya shege kai Sule idan ba za ka yi magana ba, ka fice mini daga É—aki ko na kwashe maka albarkar da ta yi saura a kanka.” Baba Sule ya sake matsar Æ™walla ya ce, “Inna wallahi Fatalwar Baba ce za ta tafi da ni matukar na saki hannun Sahuwa Æ´an sama jannati ne za su tafi da ni.” Ku san mutuwar zaune Yaya Babba ta yi saboda labari ya risketa daga wurin kishiyarta ga shi ÆŠan cikinta ma ya sanar da ita.
Nan fa gida ya hautsine hantar cikin kowa ta kaɗa saboda fargaba, Sai da Yaya babba ta yi da gaske sannan Baba Sule ya saki hannun sahura. Ai kuwa yana sakin hannunta ta ranta ana kare. Baba Sule na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ƙyar aka samu aka tsayar da su a soron gidan tare da tura Baba sule cikin ɗaki don Yayan Mahaifinsu gani yake kamar gamo ne suka yi. Dubu ban da dariyar mugunta ƙasa-ƙasa babu abin da take yi.
Sai daga baya aka farga da su Auwalu da suke ɗaki don haka da sauri Yayan Mahaifinsu ya je ya sa suka buɗe ƙofar da ƙyar, Auwalu yana maƙale da Yahanasu don gani yake idan ya sake ta kamar Fatalwar Mahaifinsa za ta yi awon gaba da ita.
Malam Idi shi ne yayan Mai Carbi, tara mutane gidan ya yi gabaÉ—aya yana yi musu nasiha da nusar da su illar yarda da amincewa abin da suka yi tozali da shi. Sai da ya gama wa’azin sannan ya bawa Inna Furai damar ta yi magana.
Inna Fuarai ta karkace ta ce, “Yaya Idi yadda na ga Fatalwar Malam na ga Annabi. Ganin idona na ganshi kuma har umarnin shayar da su Auwalu ya yi.” Sai da suka gama jin jawabinta tsaf sannan aka ce Yahanasu ta yi faÉ—i abin da ta sani, Yahanasu da ta buÉ—e ido da kyar tana sunne kai Æ™asa don duk yanda hankalinta ya É—an kwanta har Yaya Idi ya sa ta buÉ—e ido bata gama sakewa ba. Ta fara yi musu bayani dalla-dalla sanna ta É—ora da cewa, “Kuma da bakinsa ya sanar da ni duk wanda ya wayi gari da likkafani a É—akinsa to gaba shi za su É—auka. Shi ya sa na ce tawa ta Æ™are.” Auwalu ya rumgumota yana cewa, “Ba za ki mutu ba Yahanasuna” Yaya Idi ya yi jim sannan ya ce, “Idan na fahimta wani ne kawai yake son razanar da mutanen gidan amma babu damuwa ku bar mini komai a hannuna zan san yanda zan É“ullowa lamarin.
Dubu tana gefe tana jin duk wainar da ake toyawa don haka ta saci jiki babu wanda ya lura da ita, kuma babu wanda ya taÉ“a kawo ita za ta aikata wannan abin. Dubu na tafiya ta wuce É—akin Marigayi ta zaro wasu kayansa da yake zuwa sallar juma’a da su. A wanke suke a goge fari Æ™al da su, sai da ta bubbuÉ—a su ta je bakin katangar banÉ—aki wacce mutum zai iya haurawa ta wurin ta ajiye, hularsa ta saÆ™ale a jikin wata itaciyar tunfafiya sai kuwa ta kwaso a guje ta shiga wurin taron da suke gabda kammalawa. Ihu take kwarawa kamar wacce ake É—anawa wuta tana cewa, “Wayyo Allah na ga Fatalwar Baffa na gani zai tafi da ni. Kafin ka ce wani abu tuni wurin ya watse sai takalma da É—ankwalaye da aka barsu suna cin karen su babu babbaka. Yaya Idi sai da ya yi kusan adungure biyu sannan ya samu ya shige É—akin Inna Furaira. Hularsa kuwa ta yi tsalle ya fi sau biyar kafin ta samu sukuni faÉ—uwa can bakin Æ™ofa.
[24/07, 11:48 am] +234 803 192 1625: *DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER’S ASSO…
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
FREE PAGE 3
Ƙananan yaran da aka bari a ƙofar ɗakuna ban da kiran sunayen iyayensu babu abin da suke yi, ƴan madaidaitan cikinsu waɗanda suka fara sanin ciwon kansu ne suka samawa kansu mafita suka nemi maɓoya. Sauran marasa wayo sai ihu suke suna buga ƙofar ɗakin da iyayensu suka shiga. Yaya Idi saboda firgita bai san lokacin da ya wuce can ƙarshen gadon Inna Furai ba, mutumin da ko falon Inna Furai baya iya ƙwaƙwaron tsayuwa, a cewarsa yana Yayan miji haka sam bai kamace shi ba. Rabon shi da shiga ɗakin Inna Furai tun wata doguwar rashin lafiya da ta yi sama da shekara goma, lokacin da ya je dubata amma a wannan ranar shi ne har tsakiyar gadonta. Ban da ɗigar da gumi babu abin da gemunsa yake yi saboda tashin hankali. Lantan can ƙarƙashin gado ta shige ban da ƴan idanuwanta babu abin da kake iya hangowa, ta ƙwale kai a jikin ƙarfe gado ya fi sau biyar duk don ganin ta ɓoye kanta ba tare da an hangota ba bare tawagar fatale su kawo mata farmaki.
Inna Furai zaman ƴan bori ta yi zanin jikinta ya jiƙe sharkaf da fitsari don gani take wannan zuwan da Fatalwar nan ta yi zuwanta ne, don a ganinta saɓawa umarnin fatalwar da tayi na sake shayar da ƴaƴanta ne ya sa, fatalwar nan ta yi dirar mikiya domin ƴan sama jannati su tafi da ita. Badariya tuni ta ƙwaƙume Yaya Idi da ke gefenta, duk yanda Badariyya ta kai ga jin ƙyanƙyamin gemun namiji sai ga gumin gemun Yaya Idi na ɗiga a sai tin fuskarta. Gabaɗaya mutanen cikin ɗakin ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Ita ma Dubu tuni ta bi yarima don kar wani ya yi saurin gano shirinta saboda ko kaɗan bata son ta samu matsala, ta tabbata muddin ta ci gaba da razana su babu wanda zai ƙara koda nan da kwana biyu ne.
Bayan wasu Æ´an mintuna Yaya Idi ya É—ago sai a lokacin ya lura da wacce take gefensa a maÆ™ale da shi suna haÉ—a ido ya watsa mata harara, da sauri ya matsa gefe yana cewa, “Subhanallah! Astagafirullahi wa’atubu’ialhi ke matsa gefe matsa-matsa” A razane ita ma ta ja baya tana yamutsa fuska alamar Æ™yanÆ™yami, don ita kanta bata san lokacin da ta Æ™waÆ™ume Yaya Idi ba don ta san kowane ne shi. Ya kalli Dubu da ke can bakin Æ™ofa da yake ita ce Æ™arshen shiga sannan ya ce, “Ke Dubu wai da gaske kike kin ga Fatalwar Mamman?” Dubu ta yi wani fakare sai kawai ji suka yi ta rushe da wani irin kuka har tana wani furjin yawu kamar wata Æ™aramar yarinya.” Yaya Idi ya yi zuru yana kallonta a zuciyarsa yana fatan kada Allah ya sa ta tabbatar da abin da ta faÉ—a da farko. A Æ™agauce Yaya Idi ya sake cewa kamar zai yi kuka, “Ke Dubu wannan kukan ba ke kaÉ—ai za ki yi shi ba ki sanar da mu musan halin da mu kanmu muke ciki.”
Dubu ta tsagaita da kukan sannan ta fara cewa, “Na ga fatalawar Baffa ido da ido don har cewa suka yi za su fara É—aukan Innarmu da Innar su Sabi’u. Kuma wai sun ci alwashin duk wanda ya haure shekara Arba’in a gidan nan sai sun naÉ—e masa Æ™afafuwa kamar alkaki.”
Tashin hankali wanda ba a samasa rana. Inna Furai na jin ance za a tafi da ita da Yaya Babba hantar cikinta ta sake kaÉ—awa gumi ta ko’ina sai keto mata yake yi. Don har kusan suman zaune ta yi saboda waÉ—ansu irin taurari ta rinÆ™a gani suna yi mata gizo a tsakar idonta. Tun daga abin da Dubu ta faÉ—a babu wani abu da Inna Furai ta sake fahimta a Æ™waÆ™walwarta, don sama-sama ta rinÆ™a jin wani yuuuuuu a zatonta wannan abin da ta fara ji Æ´an sama jannatin ne suka fara kawo mata farmaki. Cikin fitar hayyaci Inna Furai ta fara cewa, “Ikon Allah Ikon gaske! Kai Auwalu kana ina ne? Ke Larai don Allah a cikinku wani ya É—auke ni ko a kafaÉ—e ya fice da ni tun fatalwa bata tafi da ni. Auwaluna! Auwaluna na ci burin ganin ÆŠanka amma da Æ™yar idan zan samu wannan damar ka kawo mini Yahanasu idan ya so mu tafi da ita ko da Fatalwar sun tafi da mu na yi mata raino a cen barzahun idan ta haihu.” Dubu juyawa ta yi ta rinÆ™a É“aÉ“É“aka dariya Æ™asa-Æ™asa saboda ta lura tuni Inna Furai ta riga da ta fita hayyacinta, don fitsari ma ta yi ya kai sau uku daga shigarsu É—akin.
Lantan tun da ta ji labarin naɗe ƙafafuwansu kamar Alkaki, ta sake firgicewa wani buhu da ke gefenta ta fisgo wanda yake ɗauke da dawa kusan kwano biyu, bata bi ta kan dawar ba ta watsar da ita a gefe ta fara tura kanta a ciki. Don yanda Lantan take ji da ace akwai hanyar da za ta fitar da ita daga cikin ƙarƙashin gado ta tuni ta fice ta yi hanyar zariya. Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali shi ne zancen naɗe ƙafafuwansu da ta ji ance Fatalwa za ta yi mayar da su kamar alkaki. A duniya babu abin da ta fi so da ƙauna a jikinta kamar santala-santalan ƙafafuwanta, wannan ya samo asali ne sakamakon kirarin da marigayin mijinta yake yi mata akan Doguwa mai tsawon alheri tsawo rabin kyau ƴar fillo.Wannan kirari ba ƙaramin baƙanta zuciyar Lami kishiyar Lantan yake ba saboda ita gajeriya ce, kuma hatta bayan rasuwar mijinsu idan wani abu ya haɗo Lantan da Lami haka za ta yi ta hura hanci tana yi wa Lami habaici. To kuwa idan aka mayar da ƙafafuwanta kamar Alkaki ai ta shiga-uku don ta tabbata idan aka naɗe mata ƙafafuwa, ta san ko tsahon turmin gidansu ba za ta kai tsayi ba.
Lantan bata gama tunani ba ta riski maganar Dubu cikin kuka tana sake cewa, “Kuma har ce mini ya yi a cikin Æ´an uwan sa zai aiko a tsotsewa wani ko wata roman da ke cikin ƘwaÆ™walwarsu. Saboda gonar Mahaifinsu da suka taÉ“a danne masa.”
Lantan na jin haka ta ci gaba da karanto duk wata addu’a da ta san ta taÉ“a biyata a bakinta. Saboda ta san badaÆ™alar da suka shuka akan gonar Mahaifinsu. Hatta kalmar larabci indai Lantan ta santa a baki haka za ka ji tana maimaitata ya fi sau goma. Ta yi kiran sallah da tayar da iÆ™ama ya fi sau biyar, idan ta biya addu’ar shiga banÉ—aki sai ka ji ta fara, “Labbaikallahumma Labaik” Idan ta dire sai ka ji ta sake cewa, “Hayya’alal salah” haka ta rinÆ™a yin addu’a don neman kariyar Ubangiji, amma addu’a har da ta shiga abin hawa haka ta rinÆ™a maimaitawa. Tana gamawa sai ka ji ta sake cewa, “WalaÆ™adkarramna bani adama…” Bata iya direwa sai ta Æ™ara kamo wata kalmar hatta sunayen Annabawa da Sahabai waÉ—anda ta san sunansu haka ta rinÆ™a biyawa.
Ana cikin haka suka jiyo muryar Baba Munkaila a bakin Æ™ofar Inna Furai yana cewa, “Lafiya kuwa mutanen gidan nan tun daga babban zaure nake sallama shiru ga Æ™ananan yara suna ta kuka.” Ya Æ™arasa maganar yana bubbuga Æ™ofar É—akin, da Æ™yar Yaya Idi ya ta so ya fara Æ™oÆ™arin zare sakata.
A can É—akin Yaya babba dirama ake yi da ita akan dole sai an barta ta fito wai sai dai Fatalwar ta É—auketa ita da Dubu don ba za ta iya jure rashin Dubu ba. Hadiza da ke riÆ™e da kubar É—akin ta ce, “Inno don Allah ki yi haÆ™uri ki zauna na san Dubu ba za ta zauna a waje ba, kuma ni fa gani nake sharrin shaiÉ—an ne amma babu wata fatalwa.” Yaya Babba ta sake share Æ™walla ta ce, “Kaico rayuwa ban taÉ“a sanin haka zuciyarki ta Æ™eÆ™ashe ba Dije, wannan wacce irin falsafar rashin imani ce? Kowaccenku na riÆ™e da ÆŠanta amma ni kun hanani nemo Marainiyar Allah. An ya kuwa Dije?” Hadiza babu yanda ba ta yi ba amma fir Yaya Babba ta kafe, don ban da ruwan hawaye babu abin da take yi. Hadiza na buÉ—e Æ™ofar Yaya babba ta fice da sauri tana Æ™walawa Dubu kira. Da sauri Dubu ta taho aikuwa caraf Baba Munkaila ya damÆ™i hannunta bayan ya gama jin labarin abin da aka bashi dangane da fatalwa. Yana fisgota ya zuba mata ranÆ™washi a ka yana cewa, “Wallahi sam ban yarda da abin da wannan shaiÉ—aniyar yarinyar nan ta faÉ—a, ke a gidan uban wa kika ga fatalwa har ta baki saÆ™o?” Yaya babba na ganin haka ta Æ™arasa wurin Æ™afar Baba Munkaila ta yi zaman dirshen sai kawai ta fashe da kuka. GabaÉ—aya ido ya dawo kanta, Baba Munkaila ya sassauta murya ya ce, “Inno lafiya kuwa?” Yaya Babba ta É—ago ya dubi Mukaila ta janyo hannunsa ta ce, “Ka dake ni kawai Munkaila na ce ka dakeni ka huce takaici. Kaga sai na tabbatar da falsafar rashin mutumcinka yanda ya kamata.”
Baba Abubakar da shigowarsa kenan ya hango taron jama’a yana zuwa ya ga Mahaifiyarsa ce mutane ke zagaye da su. Har Æ™asa ya russuna yana tambayar Mahaifiyarsa. Yaya Babba ta share hawaye ta ce, “Allah ya yi maka albarka Garba! Don Allah ka ga ya mini me na tsare wa Munkaila da Dije? Munkaila dai ya fi jin haushina. Garba ka gaya mini wacce tsiya suke tsinana mini, bayan Allah da ma’aiki waye gatana wa zai tsunduma ni a aljannah?” Baba Garba ya jinjina kai ya ce, “Inna wai me yake faruwa ne? Me suka yi miki?”
“Tsoronsu kake ji da zan yi magana ka amsa Æ™asa-Æ™asa. A cikinsu ka gaya mini akwai Malam ko kuma akwai ni. Ban da Allah da Manzonsa wa yake Æ™aunata, ya hore mini lafiya da abin da lafiya za ta ci?” Yaya Babba ta yi maganar cikin Æ™unan rai. Baba Abubakar ya ce, “Ayi haÆ™uri Inno”
Yaya Babba ta zuba hannuwa biyu tayi tagumi ta ce, “Garba ni wace ce a wurinku?” Baba Abubakar ya bata amsa, “Ke Mahaifiyarmu ce Inno”
“Idan na tsinewa su Munkaila wa billahi sai ta ka kama su ko ba haka ba?”
“Inno abar maganar tsinuwa don Allah.” Baba Abubakar ya faÉ—a cikin sanyin murya. Yaya babba ta kuma rushewa da kuka sannan ta ci gaba da cewa, “Don Allah mecece tsinuwa da zan tsinewa Æ´aÆ´an cikina. Idan na tsine musu na É“alÉ“ace duniya da lahira ko ina da wasu Æ´aÆ´an bayan ku?” Baba Abubakar ya yi Æ™asa da murya ya ce, “Inna don Allah ki yi haÆ™uri kin ga duk mutane kallonki ake yi.”
Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, “Ka yi mini iyaka da Munkaila ko a hanya ya ganni kar ya nuna ya sanni, balle a lahira ya yi gabas na yi yamma. Haƙƙi É—aya na san Munkaila yana bina, lokacin da aka yi masa shayi (kaciya) don Allah Garba ka biya shi cinyar kazar da na ci, ko ba za ka biya shi ba Garba?” Baba Abubakar ya rasa abin faÉ—a sai kawai ya girgiza mata kai. Yaya Babba ta ci gaba da cewa, “Me marainiyar Allah ta yi masa da zai Æ™ullace ta har ya sheganta mini ita? Don Allah Garba ka tambayar mini shi ta wurin da Dubu ta zama shegiya? Ka tambayi munkaila Ni Indo Kakarta ce shegiya ko matattun iyayenta?”
Baƙin ciki ne ya cika Baba Munkaila domin jikansa ya ba shi abin da Dubu ta faɗa ba gaskiya bane saboda ya san wacece ita, amma gani yake meye laifinsa don yana son hukunta Dubu domin ta faɗi gaskiyar magana. Gani yake idan ya yi haka shi zai kawo musu ƙarshen duk wannan guje-gujen da ake yi. Tun da tun farar safiya ya ji labarin abin da ya faru yake tantama akan Dubu don kowa ya san irin hatsabibancinta.
Wata uwar harara ya watsawa Dubu sannan ya kalli Mahaifiyarsa ya ce, “Yanzu Inno saboda na hukunta Dubu shi ne ya É“ata miki rai? Tun da haka ne na zame hannuna daga cikin sabgarta shi kenan?”
Yaya babba ta wara hannuwa alamun abin ya mata daÉ—i ta ce, “SadaÆ™allahul azeem! Kana jin me ya ke faÉ—a ko Garba, dama me Munkaila yake yi wa Dubu? Ka gaya mini waye yake shiga lamuran Dubu bayan Allah da manzonsa idan ba ni ba?” Baba Abubakar ya sake Æ™asa da murya ya ce, “To duk na ji wannan Inno amma don Allah ki taho mu tafi É—aki.”
Yaya Babba ta yi biris da Baba Abubakar tana cewa, “Don Allah ka yi mini iyaka da Dije saboda tsoro nake ku tafi ku bar ni da ita a É—aki É—aya, kar a wayi gari ta maÆ™ure ni na mutu har lahira.” Cewar Yaya Babba tana satar kallon Hadiza.
Rass gaban Hadiza ya faÉ—i da jin kalmar Mahaifiyarta, da sauri ta ce, “Inno ni kuma? Ni ce zan kashe ki?”
“Duk gidan nan babu wanda ya Æ™ullace ni yake jin haushi kamar Dije dubi irin kallon da take yi mini, haushina take ji saboda na ce ta buÉ—e mini Æ™ofa na je wurin Dubu. Don Allah Garba ka gaya mini me na yi mata ko zargina take akan mutuwar mahaifinku?” Sam wannan maganar bata yiwa duka Æ´aÆ´an Yaya Babba daÉ—i da cikin yanayin rashin jin daÉ—in maganarta ya ce, “Haba Inno me kike yi haka ne kowa fa a wurin nan ke yake kallo saboda Allah me mutane za su É—auka jiya-jiya Mahaifinmu ya rasu amma kina wannan abubuwan.” Ya Æ™arasa maganar yana dafa Æ™afarta.
“Sakar mini Æ™afata Garba.” Yaya Babba ta faÉ—a a hassale. Ba musu ya sakar mata Æ™afa. Sai kawai ta miÆ™awa Hadiza hannu ta ce, “Allah ya jiÆ™anki ba don kin mutu ba Dije don Allah taimaka min zan koma É—aki, ko a baÆ™ar zuciyar Munkaila kina ga zai kaini É—aki?” Hadiza ta girgiza kai tana murmushi, Yaya babba ta ci gaba da cewa, “Don Allah ki ce Garba ya matsa daga gabana ko na fice na bashi wuri.” Gefe Baba Abubakar ya matsa Dije ta samu ta lallaÉ“ata suka shige da Yaya Babba É—aki. Suna niyyar tafiya daga wurin suka ji Æ™arar abu tim! Daga bayansu. Da sauri suka waiga sai gani suka yi Inna Furai ce da Æ™aton buhunta tana ja Auwalu shima yana ja wai dole a barta ta fita ta yafewa zaman cikin gidan. Ita ma sai da suka sha fama da ita sosai sannan suka samu ta koma É—aki. Baba Abubakar ya dubi Dubu yace,
“Dubu ince idan muka je da ke za ki iya nuna mana ta wurin da kika ga fatalwar?” Dubu ta gyaÉ—a kai suna haÉ—a ido da Baba Munkaila ya watsa mata harara. Shi kansa Baba Abubakar zuciyarsa raya masa take tabbas akwai wanda yake son tsoratar da mutanen cikin gidan tun da wanda ya mutu ya mutu kenan har abada baya Æ™ara tashi. Dubu suka tasa a gaba tana gaba suna biye da ita a baya, sai wani É—ari-É—ari take ita Allah dole tsoro take ji.
Zu-gar mutane ne suka yi dafifi don ganin ta wurin da Dubu ta ga Fatalwa da idonta. Ita kuwa hakimar kanta sai Æ™ara girma yake musamman yanda ta ga mutane kowa ambatarta yake ana jinjina mata bisa ga Æ™oÆ™arinta na tunkarar wurin. Daga can hanyar banÉ—aki suka hango wasu fararan kaya, daga nan wasu suka fara cin burki, sai kuma hular Marigayi Mai carbi da iska take kaÉ—a ta sama-sama. Mamaki da ta’ajibi ne ya kama su hatta Baba Munkaila sai da ya zubawa kayan ido, É—aya tsagin na zuciyarsa na son aminta da abin da Dubu ta faÉ—a sakamakon kayan da ya gani. Amma yana tuna wace ce Dubu zai ji ya Æ™i aminta da komai.
Baba Abubakar ne ya yi bismillah ya É—ebo kayan yana Æ™are musu kallo zuwa can ya kalli Dubu yana shirin yi mata magana, sai kuwa ta zabura tamkar wacce aka É—anawa wuta. Can bayan Zulfa’u ta maÆ™ale tana cewa, “Baba Habu wallahi tsoro nake ji.” Baba Munkaila ya karÉ“i kayan yana jujjuyawa sannan ya ce, “Amma gaskiya ana raina wa mutane hankali.” Baba Abubakar ya yi gaba yana cewa, “Dole mu san abin yi amma tabbas akwai wata a Æ™asa. Da alama wani ne yake son kawo yamutsi amma kowa ya kwantar da hankalinsa komai ya zo Æ™arshe.” Baba Munkaila ya hau muzurai yana zare idanu ya ce, “Koma wane ne ni da hannuna zan ci ubansa don na san na gida ne yake aikata wannan abubuwan. Amma duk wanda yake da hannu cikin wannan tafiyar sai na kusa tsinka shi gida uku.” Ya Æ™arasa maganar yana yi wa Dubu kallon idan ma ke ce za mu gauraya da ke.
Kafin wani lokaci tuni maganar fatalwa ta fara zaga cikin garin ÆŠangwauro, har da masu isar da labarin abin da bai faru ba. Kasancewar kowa da abin da yake ji shi yake idarwa.
************
“Dubu ki kwantar da hankalinki idan ma don wannan ne kamar an yi an gama a wurina. Ba dai ni na haifi Garba ba?” Yaya babba ta Æ™arasa maganar tana kallon Dubu cikin sigar lallashi.
Dubu ta tura baki gaba tana cewa, “To ai ke sai an gama magana da ke lafiya Æ™alau sai kawai daga baya ki sake shawara, gaskiya ni dai ko ki sa mu koma birni gidansa ko kuma ki ce su dawo garin nan wallahi sai mun fi cin daÉ—i tun da anan me muke ci kamar ba ke kika haifeshi ba.” Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, “Ba zan koma birni ba domin Malam har wasiyya ya bari akan kar mu kuskura mu bar gidan nan to kin ga saÉ“awa miji haramin ne amma Garba ko ya Æ™i ko ya so dole ya dawo gidan nan da zama.”
Baba Munkaila ne ya kawo kai zai shiga ɗakin Mahaifiyarsu amma ya ga mutane sun yi carko-carko a ƙofar ɗaki ya tambaya ko lafiya.
Hadiza ta taÉ“e baki ta ce, “Inno ce suke shawara da Dubu shi ne ta koro mu waje.” Haushi ne ya Æ™ara kamashi don ya san duk iskancin da Dubu take yi Mahaifiyarsu ce take É—aure mata. ÆŠaga labulen É—akin ya yi suna haÉ—a ido da Yaya Babba ta ce, “Kai Munkaila ka tara mini Æ´an uwanka yanzun nan ina son magana da ku!” Kallon Dubu ya yi ya ga ta yi É—ai-É—ai a cinyar Yaya Babba, gudun neman magana ya sa bai tanka ba ya amsa ya fice. Don baya raba É—ayan biyu Dubu ce ta kitsa mata wata maganar.
Ba a ɗauki lokaci ba Iyalan Yaya Babba suka cika a ɗakin kowa da abin da yake ƙissimamawa zuciyarsa. Dubu na ganin haka ta saci jiki ta tafi haɗa kayan aikinta domin da alama tana ganin wankin hula zai iya kaita dare, don ta ga mutanen gidan ba su da alamar tafiya.
“Na san za ku yi mamakin ganin wannan taron amma ba wata doguwar magana bace. GabaÉ—ayanku so nake idan an yi sadakar bakwai kar wanda ya sa Æ™afarsa ya fita daga gidan nan akwai babban taron da za mu yi gabaÉ—aya gidan nan. Musamman kai Garba tun da kaine babba.” Yaya Babba ta yi maganar tana É“ata fuska don kar wani ya nemi kawo mata wargi. Suma ganin haka ya sa babu wanda ya musa mata sai dai cikin ladabi É—ayan bayan É—aya suka ta shi suka fita kowa yana wani lissafi daban a zuciyarsa.
Baba Munkaila yana lura da duk wani shige da ficen Dubu sai dai kamar yanda ya sa mata ido ita ma tana ankare da shi. Yi ta yi kamar babu wani shiri da take haÉ—awa don shi kansa a wannan lokaci ya fara rage zarginsa a kanta.
Tun da yamma ta kawo kai doshin magriba Æ™afafuwa suka fara janyewa daga cikin gidan kowa daga alwalar magriba ya riÆ™e abarsa don kowa a tsorace yake. Wannan dalilin ya sa zaman cikin gidan ya gunduri Hajiya Nafisa Matar Baba Abubakar da iyalanta. Allah ya sani ita dama ba ma’abociyar son zaman Æ™auye ba ce, don ta kusa shekara biyar ba ta kwana a garin ba sai dai taje ta dawo a ranar, haka ma daga É“angaren Æ´aÆ´anta shi ya sa basu cika wani sakin jiki da mutanen gidan ba.
Bayan Sallar Isha’i.
Daga cen bayan ɗakin Marigayi suka fara jin kiran sallah da muryar Marigayi mai carbi. Kasaƙe mutane gidan suka yi aka rasa mai zuwa kiran Mazan da ke ƙofar gida don sanar musu da abin da yake faruwa. Don kowa hantar ciki ta kaɗa saboda lokacin dare ma bai gama yi ba don ko tara na dare bata yi ba.
Tana gama kiran sallar ta fara wasa wuÆ™a ji kake , “Kuyat! Kuyat” Sai da ta Æ™ara matsowa hanyar cikin gidan ta fara wani irin kuka mai kamar haniniyar doki. Gidan tsit ya yi kamar an yi ruwa an É—auke tun da Dubu ta ji haka cikin muryar marigayin Kakanta ta fara cewa, “Da alama yau za mu É—ebi mutanen gidan nan da yawa. Amma duk wanda ya cinye tuwon daren yau ya tsira ba za mu taÉ“a ko ta fatarsa ba.”
Daga can ɗakunan mutanen ɗakin nɓa jin haka suka fara kantamar tuwon da ko minti ashirin ba a yi da kwasarsa ba. Da zafinsa suka rinƙa ci saboda tsira daga kaidin tawagar fatalwa. A ɗakin Inna Furai faɗa ne ya ɓarke tsakanin Lantan da Inna Furai akan suɗin kwano har Lantan ta ji haushi ta kwalawa Inna Furai silba a goshi.
Dubu na daga wurin da take laÉ“e tana jin hayaniyar mutane sai da ta kintaci lokaci, ta fara wani irin nishi mai ban tsoro tana cewa, “Duk wanda ban ji sautin tusarsa ba shima wallahi babu mai hanamu É—aukansa a daren nan.”
Godiya, next please
Moufi 18ans