Duhun Inuwa Hausa Novel Complete

Duhun Inuwa

Duhun Inuwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

Duhun Inuwa Hausa Novel Complete

Life is too short to wake up in the morning with regrets. So love the people who treat you right, forget about the ones who don’t. And believe that everything happens for a reason. If you get a chance, take it. If it changes your life, let it. Nobody said it would be easy, just that it would be worth it.

Duhun Inuwa

ALLAH YASA MUDACHE AMEEEEEEEEEEEN

 

 

 

 

 

 

SHARHI

 

 

 

A duk lokacin da mai rubutu ya kafa alƙalaminsa akan takarda ba yana nufin dole zai rubuta irin RAYUWARSA bane, ko irin RAYUWARKU. Malami yakan faɗakar ya tsoratar akan abinda ya dace. Haka shima marubuci yakanyi rubutu domin faɗakarwa ko nishaɗantarwa akan abinda rubutunsa yazo dashi. Idan yasa ƙyaƙyƙyawa, ba dole sai yanada irin wannan ƙyawun bane, domin kuwa kowa yasan a duniya akwai ƙyawawa. Idan yasa mai ƙarancin ƙyau (domin UBANGIJI bai halicci mummuna ba, kowa da irin ƙyawun da yay masa na halitta), ba dole sai yana a cikin wannan jinsin bane, sai dan rubutunsa a haka yazo. Idan yasa mai arziƙi, badan dole sai shima yanada arziƙin ba. idan yasa mai mulki, ba dole sai ya kasance jinin mulki ba. Idan yasa talaka, ba dole sai ya kasance talaka ba. Abinda kawai nasani alƙalamin marubuci zai iya taɓa kowa. Mai kuɗi, talaka, mai mulki, ɗan ƙauye, ɗan birni, musaki, mai ilimi, jahili, ƙyaƙyƙyawa, mai ƙarancin ƙyawu. Mai ƙyawun hali, mugu dama kowa da kowa. Duk kuma abinda ya taɓo idan zaka nutsu wajen zagaye cikin duniya koda ace da tunani ne sai ka samu mai kamanceceniya da LABARIN. Shiyyasa kuskure ne mai KARATU ya tsuke tunaninsa akan dole sai abinda ya sani MARUBUCI zai wallafa ko ya faɗa. Idan akasin hakan yazo kuma shi a gurinsa marubuci baiyi dai-dai ba. Karka manta ALLAH ya haliccemune yaruka daban-daban, jinsi daban-daban, yanki daban-daban, launi daban-daban, addinai daban-daban, Bai zama lallai sai abinda kai ka sani ko kake gani zai rubuta ba. MARUBUTA da yawa sun sha rubuta LABARANSU ko RAYUWARSU a littatafai daban-daban batare da kunsan nasu bane ba. Saboda basu fito sun sanarma duniya nasun bane ba. Dan haka ina roƙonku idan LITTAFI yazo muku, ku karanta kawai badan lallai sai yazama RAYUWAR wanda ya rubuta ɗin tazam dai-dai da abinda ke ciki ba. Kawai kadai duba darasin dake ciki ka amfana, akasinsa watsar, yi farin ciki da farin cikin da yazo dashi, dan wani abun akan rubutashine kawai domin ƙawata labari ko nishaɗantar da mai karatu wajen cire masa wata keɓantacciyar damuwarsa. Ina fatan za’a fahimceni.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
JINJINAH GA

 

Aunty Billy Abdul

 

Aunty Aisha Aliyu Garkuwa

 

Aunty Safna Aliyu Jawabi❤️✍️🙏

 

Aunty Asmy Jafar❤️✍️🙏

 

Aunty Asmy Baffa❤️✍️🙏

 

Aunty Hafsat Rano❤️✍️🙏

 

Aunty Sarat Al kaseem ❤️✍️🙏 (mmn nussey)

 

 

 

 

GABATARWA 😇😇😇

 

 

“`Godiya ta tabbata ga ubangijin talikai mai rayawa a sanda yaso da kuma ɗaukar rai a sanda yaso,

ina roƙon Allah yadda ya bani ikon fara wannan book ɗin lfy ya taimakeni na ƙareshi lfy,,

Banyi wannan book ɗin dan cin Zarafin wani ko wata ba, kawai labarin ya taɓa min zuciya ne 😭😭😭 kuma har nakasa samun sukuni akan wannan zaluncin da a kayiwa SHADOW wannan dalilin yasa naɗauki alƙalamina✍️ na dawo bakin aiki😎.

Allah kabamu ikon aikata maikyau ka hanemu da munanan Abubuwa, Allah kasa mu amfana da darasin dake ke cikin wannan book mu watsar da marasa kyaun da ke cikinsa Ameen…….

 

 

GARGAƊI

 

 

Ban yarda wani ko wata su sauya min book ɗina ba ta ko wace hanya.

 

 

 

 

SADAUKARWA

 

NA

 

sadaukar da wannann novel ɗin ga ɗaukacin masoyana masu son cigabana 😘😘😘

 

 

GAISUWAR BANGIRMA

 

zuwa

 

ga

 

Ɗaukacin jama’ar PERFECT WRITER’S ASSOCIATION Allah yayi riko da hannayenku Taurari

 

 

BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

 

 

FAGE

 

0️⃣1️⃣

 

 

 

Misalin karfe 5:30 na yamma wasu masoya ne zaune a kan fararen kujerun roba, fira suke cikin farin ciki da Nishaɗi. kallo ɗaya za kayi musu ka fahimci suna matuƙar so da ƙaunar junan su, saboda ba abunda kake gani akan fiskukin su sai yalwa taccen murmushi mai matuƙar ƙayatarwa.

 

Saurayin ne ya kalli budurwar tasa cikin sakin fuska yace my noor tambayarki fa nakeyi kinyi shuru, nace wane event ne Kika shirya za kiyi.

 

Sunkuyar dakai tayi tare da saka hannuwan ta ta rufe fuskarta alamar kunya.

 

ɓata fuska yayi kamar zaiyi kuka yace haba my Noor wai meyasa kike min irin haka ne? a duk lokacin da nake miki maganar auren mu sai ki dinga nuna min jin kunya. gaskiya ni bana so ai idan da sabo mun zama ɗaya, ƴan kwanaki ƙalilan ne fa suka rage mana muyi aure, idan bamuyi shiri tun yanzu ba sai yaushe kenan?

 

 

Ɗan muskutawa tayi ta gyra zaman ta tare da sunkuyar da kanta kasa, a hankali cikin sanyin muryar tace kayi haƙuri my Shadow, ba wai ban damu da shirin bikin nan bane wallahi matuƙar kunyarka nakeji musamman ma da bikin nan yayi gab, sai na keji duk abubuwa suna sauyamin ba kamar da ba.

 

 

Murmushi yayi mai cike da nishaɗi yace wllhy kina bani mamaki my Noor, sai nakeji a raina kamar baki damu dani yadda na damu da ke bane.

 

 

Dasauri ta ɗago ta kalle shi ta shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta ce haka dai kake gani, but na damu da kai fin yadda ka damu dani, kuma lokaci yana zuwa zaka gani.

 

 

Murmushi yayi mai sauti tare da tashi tsaye yace tohm zan tafi ranki ya daɗe, dama na faɗa miki akwai gurin da zanje, amma sai naji ba zan iya zuwa ba ba tare da nazo naga Haskena ba. Ya ƙarisa maganar yana murmushi.

Ita ma murmushin tayi tace nagode Sosai my Shadow.

 

Ba godiya a tsakaninmu my Noor fatana kawai shine idan munyi aure karki zamar min DUHUN INUWA ki riƙe amanata Noor ni mutum ne wanda ke son magana ta gaskiya da gaskiya, bana son ɓoye ɓoye akan komi duk abunda zaki faɗa yaza mana gaskiya ne, koda ace naji zafin abunda kikayi tohm zanfi jin farin ciki idan kin faɗa min gaskiya akan kiyi min ƙarya, idan kin kiyaye wannan tohm ni bana da wata matsala Noor.

 

 

Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallonsa tace na daɗe da sanin wannan my Shadow. kuma insha Allah zan zama mai kiyayewa akan duk abunda baka so, sanin kan kane ba abunda nake ɓoye maka a rayuwa, kuma insha Allah ba abunda zan ɓoye maka nan gaba.

 

Allah ya yarda Noor,,,

 

Ameen ya Allah Mijina,,,

 

Salama yayi mata tare da hawa machine ɗinsa ya ta dashi yatafi. saida taga fitarsa daga gidan sannan ita ma tashiga gida tana murmushin jin daɗi.

 

 

 

Bayan sati biyu da faruwar haka shirye shiryen ɗaurin aure ya kan kama saboda duk wani event da akeyi kamin ɗaurin Aure an riga da an gabatar dasu.

Sai Diner da za’a gabatar gobe idan an ɗaura aure.

 

Amarya Noor ansha kyau ta ko ina ta gibta sai tashin ƙamshi kakeji na mussamman.

 

Ta ɓangaren shadow kam ba dama yau gaba ki ɗaya ya kasa samun zama saboda baƙine suke zuwa na nesa wanda idan sukace sai gobe ne zasu zo tohm fa ba shakka baza su samu halartar ɗaurin auren ba.

 

 

Yanzu haka ma wasu Abokanan sa ne ya tarbo wa ƴan da sukayi Bautar ƙasa tare dasu a gombe.

daya ke su ƴan asalin gomben ne, kuma sunyi zaman mutunci sosai da Shadow hakanne ma yasa su kaci Alwashin zuwa sokoto idan aurensa ya yazo.

 

Fira suke mai cike da nishaɗi da kewar juna. ɗaya daga cikinsu ne mai Suna Kamal ya kalli Shadow cike da tsokana yace angon Noor, wannan Noor ɗin da ace baka sameta ba da (maybe) gidan mahaukata ne kawai zai iya ɗaukarka, cox ban taɓa ganin wanda ya sadaukar da lokacinsa da kumai nasa akan soyayya ba kamar kai. (sometime’s) fa har tausayi kake bani cox nasan halin mata basu da tabbas sun ƙware agurin karya zuciyar mutum wllhy.

 

Dariya Shadow yayi sannan yace kai Kamal ai ko matan ma suna suka tara, ni nan na yarda da Noor kuma na yarda da tarbiyar gidansu na yarda da soyayyar ta agareni ta gaskiya da gaskiya ce. wannan dalilin yasa bana saka Noor acikin ƴan matan wannan zamanin, har abada ina da (confidence) a kanta, ita ɗin ta musamman ce a rayuwata.

 

 

 

Kamal mai yasa ka cika biyar diddiƙi ne wai? ka ɗauka ko wace yarinya kalar Sadey beb ɗinka ce? wace tasan kan yaudara da karya zuciyar samari.

Haidar ya faɗa yana bushewa da wata irin dariyar ƙeta da son

Ƙufulal da Kamal ɗin.

 

 

Ai kuwa yayi nasarar haka dan nan take Kamal ya fara hauhawa kamar farashi.

ya murtuƙe fuska kamar ba Kamal ba mai son wasa da dariya,

ya kalli Haidar rai a ɓace yace wai Boss bana faɗa maka mun rabu da wannan yarinyar ba.

kuma na faɗa maka bana son maganarta, but kai na lura duk lokacin da kayi nufin baƙanta min rai sai ka dinga min maganar ta ko?

ya faɗa yana ɗauke kansa gefe ɗaya irin shi a dole an ɓata masa rai ɗin nan.

 

 

Shadow ne yakashe fitinar ta hanyar bawa Kamal haƙuri yana dariya yace kai amma kuwa Sadey beb bata kyauta mana ba.

Ni nazata idan ba kai bazata iya rayuwa ba. a dai yadda take nuna damuwarta akan ka gaskiya banyi zaton kwanton ɓauna tamaka ba kamal.

 

 

Tsaki kamal yayi yace wallahi ashe ga baki ɗaya ƙarya da yaudara ne a cikin kalaman ta.

Amma ai tayiwa kanta dan ita ce tayi rashi bani ba yafaɗa yana shafa sajen da ke kwance akan dogowar fuskarsa. shi a dole mai kyau ne.

yace maybe ma anan nasamu Wata mai sa’a tayi wuf dani, dan naji ance ƴan matan garin nan akwai soyayyar gaskia da iya kula da saurayi ko? ya faɗa yana kallon Shadow.

Dariya sukayi ga baki ɗayan su.

 

fira suke cikin nishaɗi

A haka har suka ƙarasa gidan su Shadow da ke a unguwar Minannata.

 

 

RANA BATA ƘARYA.😞😞

 

Ayau 15/12/2021 dan dazon jama’a suka taru domin shaida ɗaurin auren

Ahanaf Muhammad Imran (Shadow) da

Noriya Mukhtar Salah (Norr).

 

Kamar yadda aka Saba idan anzo ɗaura aure dole sai mutane sun haɗu dangin ango dana amarya bayan kowa ya hallarane aka zauna domin gabatar da abunda yatarasu agurin.

 

Hankalin Shadow ya koma kan abokansa da suketa faman zolayarsa.

 

Saiji yayi Gurin yakaraɗe da muryar wani ba banbaɗe. inda yake cewa Alhmdllh an ɗaura auren NORIYA MUKHTAR SALAH da angonta AL-ƘASEEM MUHAMMAD IMRAN akan sadaki naira dubu ɗari cif lakadan ba ajalanba.

 

Shadow ne ya tashi da sauri har Yana tangadi ya kalli abban sa yace Abba kunyi kuskure fa sunana Ahanaf Muhammad Imran ba Al ƙaseem Muhammad Imran ba. Abba da Al ƙaseem aka daura auren Nan bani ba? Dan Allah Abba kagaya musu wannan sunan ƙanina ne ba nawa ba.

 

Abba me yake faruwa ne? Dan Allah agyara sunan nan Abba, Shadow ya faɗa cike da ruɗewa da firgici kwallah fal idanunsa.

 

Wanda yaketa faman Kira da Abban ne yakama hannunsa yace Ahanaf muje gida sai nayi maka bayani kaji.

 

Dasauri ya kwace hannunsa daga na mahaifin nasa.

Cikin murya Mai Amo da nuna zallar bacin Rai yace Abba baxan bar Nan gurin ba har sai kun gyara wannan Rikitaccen Al amarin da kuka kulla.

Dan girman Allah Abba kugyarashi tunkan hankalin mutane yadawo Nan su fahimci halinda ake ciki.

 

Abba Norr fa da Al kaseem? Me nayi muku ne haKa Mai zafi da har zaku dauki fansa ta wannan hanyar?

Abba idan har laifi na maka kayi min komai Amma Banda hanani auren Norr dan Allah, wllhy Abba Ina sonta Kuma bazan iya rayuwa ba idan har Bata.

Abba karka jefa rayuwar ɗan ka a cikin DUHUN INUWA plxx.

Abba ko dai ba kaine mahaifin… Kafin ya rufe bakinsa sai jin wani zazzafan Mari yayi tasssssssssss a kumatunsa.

 

 

Ɗagowa yayi da sauri ya kalli mahaifin nasa cike da matuƙar mamaki.

Yau shine Abba ya mara Kuma akan gaskiyar sa?

 

Abba da ko faɗa baya bari ayi masa bare a ɓata masa rai saboda Yana da sunan mahaifin sa.

Amma yau har da Mari.

Shin kodai mafarki nakeyi ne? Shadow ya tambayi kansa cike da rudani.

 

Ba mafarki kake ba Ahanaf wannan zahiri ne cewar Abba dake ta faman sauke nunfashi cike da ɓacin rai.

 

Abba ya ƙara da cewa Ni mahaifin ka Muhammad Imran na daura auren Noriya Mukhtar Salah da na Al kaseem Muhammad Imr….. Ai kafin ma ya rufe bakin sa Nan take Shadow ya zube ƙasa ba alamar Numfashi a tare dashi.

 

 

 

TIR ƘASHI🙆🙆🙆

 

Taya hakan tafaru?

 

A Ina matsalar take?

 

Menene dalilin da yasa su Abba sukayiwa Shadow hakan?

 

Anya kuwa Norr zata yadda da Ƙaseem a matsayin miji?

 

Shima Ƙaseem Zai karɓi Norr a matsayin mata duk da yasan irin sonda yayan sa yake mata?

 

Ko dai Shadow yanada wata matsala ne?

 

Ku dai ku kasance tare Dani Nabeelah Shehu Binji Dan jin yadda wannan Al Marin Mai matukar sarƙaƙiya zai kasance.

 

 

 

Nabila binji

09064314811

09161107610

 

 

 

 

 

More comment

More taping

 

 

 

 

Share Fisabilillah

DUHUN INUWAH

 

 

 

 

STORY

 

AND

 

WRITING

 

BY

 

NABILA S BINJI

 

 

 

 

 

Hadiths of imam An-Nawawi

 

Verily the creation of each one of you is brought together in his mother’s womb for forty days in the form of a nutfah (a drop), then he becomes an ‘alaqah (clot of blood) for a like period, then a mudghah (morsel of flesh) for a like period, then there is sent to him the angel who blows his soul into him and who is commanded with four matters: to write down his rizq (sustenance), his life span, his actions, and whether he will be happy or unhappy (i.e. whether or not he will enter Paradise).

 

By the One, other than Whom there is no deity, verily one of you performs the actions of the people of Paradise until there is but an arms length between him and it, and that which has been written overtakes him, and so he acts with the actions of the people of the Hellfire and thus enters it; and verily one of you performs the actions of the people of the Hellfire, until there is but an arms length between him and it, and that which has been written overtakes him and so he acts with the actions of the people of Paradise and thus he enters it.

 

 

 

BISMILLAHHIR_RAHAMANIR_RAHIM

 

 

 

Fage

 

0️⃣2️⃣

 

 

 

 

Al amarin da ya janyo hankalin sauran mutanen da ke wurin kenan Wanda da tun farko Basu fahimci me ke faruwa ba.

 

Da sauri Al ƙaseem yazo gurin da Shadow yake kwance a ƙasa ya durƙusa kan gwiwowinsa yaɗa goshi yaɗaura shi a saman jikinsa, Yana girgizashi cike da tashin hankali yake cewa Yaya Shadow Dan Allah katashi karka mutu ka barni idan kamutu nima mutuwa zanyi, wallahi in dai Norr ce ni Nan zan rubuta Mata takardar saki da hannuna,

Yaya ban san menene dalilin da yasa su Abba suka yanke wanann mummunan hukuncin ba,

Amma kasani koma Mai menene dalilinsu ni bazan taɓa lamuntar wannan zaluncin ba Kuma zanyi kumai dumin farin cikin ka Yaya.

Dan Allah katashi kaji tausayina Yaya banida wani ɗan uwa a duk faɗin duniyar nan da yawuce ka, dan haka ba abunda bazan iya sadaukarwa ba saboda kai yaya.

Ƙaseem ya faɗa Yana fashewa da wani matsanancin kuka Mai taba zuciya.

 

Duk mutanen gurin sun fahimci abunda ke faruwa, kuma sunyi matuƙar mamakin wannan sauyin da aka samu Mai cike da rudani da Al ajabi. Sudai sun san Ɗaurin Auren Ahanaf suka zo, amma kuma sunji mai shelar ɗaurin aure yana cewa an ɗaura aure da Al ƙaseem ba Ahanaf ba.

wanda duk duniya ta sheda cewa Al ƙaseem ƙanene agurin Ahanaf na jini kuma suna matuƙar kaunar junan su, idan kagansu baza ka taɓa cewa su saƙo bane, saboda ba wannan rashin jituwar a tsakanin su, idan kagansu zaka iya rantsewa tagwaye ne banbancin su kaɗan ne shi Al ƙaseem farine tas saɓanin Shadow da ba zaka iya kiran shi fari tas ba kai tsaye.

 

Cikin ɗaga murya Ƙaseem yace Dan Allah wani yataimaka min da ruwa, ba ɓata lokaci Kamal Abokin Shadow ya bayar da gorar ruwan da Shima yanzu ya ɗauko su a Mota domin ceton ran Abokinsa, an zuba mishi ruwan yakai sau ukku amma ko motsawa baiyi ba na nuna alamar cewa Yana Raye cikin tashin hankali Ƙaseem ya warce gorar ruwan daga hannun Kamal ya zuba su gabaki ɗaya a fuskar Shadow.

 

Wani dogon numfashi yaja tare da tashi zaune yana zare ido kamar wani taɓaɓɓe,

Kalle kalle kawai yake da alamar akwai wanda yake nema, ganin bai ga wanda yake neman bane yasa shi mai da kallon sa a kan Al ƙaseem ya ƙure shi da manyan idanunsa da sukayi ja kamar barkono, da sauri Al ƙaseem ya sunkuyar da kasan sa ƙasa cikin tashin hankali da baƙin cikin wannan ranar fiye da kowace rana a rayuwar sa.

Kafin zuwan wannan lokacin yana cike da matsanancin farin cikin auren Yayan sa kuma Garkuwansa.

Amma a yanzu yama kasa tantance a wane hali zuciyarsa take ciki.

 

Cike da tashin hankali Shadow yace Ƙaseem Ina Abba yake? da sauri Ƙaseem ya goge hawayen idonsa yace ya Shadow Ina ga fa kamar Abba Ya tafi gida.

 

Cikin sauri Shadow ya tashi tsaye yanufi mota cikin sassarfa har yana tuntuɓe da nufin zai ja Motar da kansa. da sauri Haidar ya mara masa baya ya riƙesa tare da buɗe Masa gefen Mai zaman banza yasashi aciki ba musu ya zauna saboda shi duniyar ma gabaki ɗayanta juwa masa takeyi sunkuyar da kansa yayi ƙasa cike da tashin hankali. rufe murfin motar Haidar yayi tare da koma wa side ɗin driver ya zauna,

Yayi wa motar key yabar gurin a 360.

 

 

Shima Al kaseem Tashi yayi tare da bin bayan Kamal suka Shiga Mota suka marawa su Shadow baya.

 

Anan aka bar mutane kowa Yana furta Albarkar bakinsa akan wannan abun da yafaru, da yawan mutanen gurin laifin iyayen yaran suke Gani musamman ma Alh Muhammad Imran Shi da har ya iya ɗaga hannunsa ya Mari Ahanaf a cikin wannan halin, tohm Wai menene ma dalilin wannan abun da suka akaita? Ko ma dai menene dalili zamuji Nan ba da jimawa ba insha Allah cewar Wani dattijo Yana gyara zamar babban rigar sa.

 

 

Tafe suke cikin Mota ba Abunda kake ji Sai matsanancin bugun zuciyar Shadow Wanda yake sauke numfashi da kyar kamar Wanda yake dab da barin Duniya. kallon sa Haidar yayi cikin tausayawa da jimamamin wannan lamarin yace kadinga furta Kalmar Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raju’un Zaka Sami sauƙin abinda kakeji a ranka friend. Kuma ka kwantar da hankalin ka insha Allah bazaka Rasa Noor ba.

Yazama lallai su Abba su Gaya Mana dalilin wannan abun da suka akaita, insha Allah Kumi zai zo da sauƙi friend,

Haidar ya fada Yana kokarin danne damuwar sa da son kwantar wa Abokin nasa hankali, Amma Shi kadai yasan Abunda yake ji a zuciyar sa.

 

Ko ɗagowa Shadow beyi ya kalli Haidar ba balle har ya aikata abinda yace Masa shidai Kawai burinsa yaganshi gida gaban mahaifiyarsa da mahaifinsa ya tambaye su dalilin da yasa sukayi Masa Hakan, yasan Koda ace kowa zai juya Masa baya a duniyar Nan tohm tabbas mahaifiyarsa da Norr ɗinsa bazasu taɓa juya Masa baya ba,

wannan dalilin yasa yanzu su Kawai yake burin Gani Koda zai Sami salama a rayuwar sa, Shi Gani ma yake kamar ba tafiya Haidar din yake ba.

 

 

Minannata Gidan su Shadow

 

Hada Hadar biki Kawai ake da shirya abinci Yan Ɗaurin aure kafin su dawo.

 

Tsaye take Tana faɗawa mai aikinta yadda take son abubuwa su kasance.

Kawai Sai hango shigowarsa tayi tun a yanayin driven ɗinsa ta fahimci akwai matsala fitowa yayi daga motar Yana zuba sauri kamar zai kife yanufi part ɗinsa, gabanta ne yayi mummunan bugawa hankalinta yatashi sosai Dan Rabon da taga Abba acikin wannan halin bazata iya tunawa ba.

Bayansa tabi da sauri aranta Tana fatan ace bawani mummunan abune yafaru a gurin ɗaurin auren ba.

 

Palo tashiga Amma Bata ganshi ba Hakan yasa ta nufi bedroom dinsa direct ƙirjinta yana matsancin bugawa da sauri sauri. hannunta ta ɗaura akan ƙofar ta Murɗa bakinta dauke da sallama tashiga dakin, hangoshi tayi a tsakiyar ɗakin ya rungume da hannayensa a baya Yana Safa da Marwa.

Ƙarasawa tayi gurin da yake cikin tsinkewar zuciya tace Abba Mai yafaru? Ina Ahanaf din Wani Abu ne yafaru a gurin ɗaurin auren? Ta jefo Masa waɗan Nan tambayoyin a lokaci ɗaya.

Ko Kallonta ma beyi ba Barre ta sa ran zai amsa Mata tambayoyin ta.

Baki ta bude da nufin Kara yi Masa Magana Sai taji an turu ƙofar an shigo,

Juyawa tayi Dan ganin wanene, Ido hudu tayi da Ahanaf saida kirjin ta ya buga da ƙarfi a lokacin da taga Yaron nata abun Alfaharin ta cikin sassarfa ta karaso gurin da yake tsaye kamar an dasashi Tana ƙarasawa ya faɗa jikinta tare da fashewa da matsancin kuka Mai cin Rai.

 

Tabdijam hankalin Ayiya yayi matuƙar Tashi ganin yadda jarumin ɗanta yake raira Mata kuka kamar mace tabbass tasan wannan lamarin ba ƙarami bane, dalilin da yasa itama ta fara kukan Kenan. Ba Abunda kake ji a ɗakin Sai sautin kukansu Abba ne yadaka musu wata irin gigitaciyar tsawa yace Sufitar Masa daga ɗaki Shi ɗakinsa ba gurin kuka bane.

 

Cike da mamaki Ayiya tabishi da kallo tace Anya kuwa yau Abba kana cikin hankalinka kasan mekake cewa kuwa?

 

Bana cikin hankalina Haj Shuwa duk abinda yazo bakinki Zaki iya fada kinji, Amma Dan Allah abinda nake so daku shine kufita kubarmin ɗakina plxx.

 

Ba in da zamuje Abba har Sai ka Gaya Mana menene dalilin da yasa ka ɗaura auren Norr da Ni saɓanin Yaya Shadow, Al ƙaseem ya faɗa hawaye kwance a idanunsa,

 

Wani irin Jiri ne ya fara daukan Ayiya Wanda yasa taji gabaki ɗaya duniyar ta tsaya Mata Cak, zaunawa tayi dabar a kasa cike da matsancin tashin hankali tama kasa buɗe baki tayi Magana, Kuma ta daina Jin duk Wani Magana da suke a tsakaninsu tunda take a Duniya Bata taɓa Shiga tashin hankali irin wannan ba.

 

Tsawar da Abba yadakawa Al ɗaseem ce tayi nasarar dawo da ita Duniyar da muke ciki.

 

Yace Kai yanzu Al ƙaseem har kayi kwarin gwiwar da Zaka tsaya a gabana Ina Fadi kana Fadi? Tohm wallahi bari kaji na faɗa Maka kana kuskuren sakin Noor Kai ba Ɗana bane Kuma Allah ya’isa ban yafe Maka ba.

 

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raju’un, Lahaula Wala kuwatah illah Billah Shadow yafada cikin sautin kuka.

 

Al ƙaseem ya bude baki da nufin sake Magana cikin sauri Shadow ya Tashi tsaye ya rufe Masa baki tare da girgiza Masa Kai alamar Kar yakara wata Magana.

 

Hanyar fita Abba yakama da nufin bar musu ɗakin gabaki ɗaya.

cikin sauri Ayiya Tashiga gabansa har tana tangadi kamar wata Yar maye tace Abba ba inda zakaje baka faɗa Mana menene dalilin ka Na aikata wannan abun ba.

 

Tsayuwar sa yagyara yana kallon cikin idanunta yace bawani dallili Shuwa kawai nadaiyi ra’ayin haka ne, shiya nayi saboda da Ahanaf da Al ɗaseem dukansu ƴaƴana ne ina da ƴancin yanke hukuncin da Naga Dama akan su, sbd haka ki matsa daga Nan na wuce Shuwa.

Ba inda zakaje baka faɗa Mana dalin wannan abun da ka aikata ba Wallahi Muhammad.

 

Cikin mamaki ya Kalle ta yau Shuwa da Fadin sunansa ba kunya ko Kara? Abunda Bai tabaji ba Kenan a tsawon rayuwar sa da ita, murmushi yayi yace lallai kuwa kin Isa Shuwa Kuma Nagode sosai da tsayayya.

 

Zagayeta yayi da nufin fita daga ɗakin tayi saurin riƙo rigarsa tana cewa Ina Zaka tafi kabar mu a cikin DUHU? tabbass bazaka fita daga ɗakin Nan ba har Sai ka…. Wani wawan Mari taji a kumatun Wanda ya razana ta tare da yin baya kamar zata Faɗi.

 

Dasauri Shadow yatare ta tafaɗa jikinsa ya rungeme ta ajikin sa Yana Jin Wani irin baƙin ciki Wanda tun zuwansa Duniya Bai taɓa cin karo da makamancinsa ba.

Idonsa yadɗago wa ƴanda sukayi ja kamar garwashi ya zubasu akan fuskar mahaifinsa,

Wanda izuwa yanzu ya kejin baya ma ƙaunar ganinsa gabaki ɗaya,

Tabbass da a ce ba mahaifinsa bane yataɓa masa Ayiya da ko waye sai ya ɗanɗana kuɗarsa. hannunta yakama yakaita bakin gado ya zaunar da ita.

 

Shikuwa Abba ficewa yayi daga ɗakin

Ransa a matuƙar ɓace.

 

Shadow Juyawa yayi ya kalli Al ƙaseem cikin murya wace take nuna tsantsan damuwa yace karka kuskura ka musawa Abba akan duk wani abunda kaga zai aikita, kuma karka kuskura sakin Noor idan dai bashine yayi maka umarni da hakan ba.

 

Buɗe baki yayi da nufin magana Shadow ya ɗaga masa hannu yace bana son jin komai daga bakin ka dan Allah Ƙaseem.

juyawa Ƙaseem yayi fuuuuh yabar ɗakin kamar zai tashi sama saboda tsananin ɓacin rai.

 

Gurin Ayiya ya nufa wace take zaune tun ɗazu a inda ya ajiye ta kamar wata butun butumi.

Zubewa yayi ƙasa akan gwiwoyinsa ya kamu hannayen ta yace Ayiya dan Allah ki saurari abunda zan faɗa miki, kar kiyi wani abu wanda zaisa mutanen da ke gidan nan susan Halinda muke ciki.

koma menene kibari har mutane su watse dan Allah Ayiya yafaɗa tare da matse hannayen ta sosai acikin nasa.

 

Zare hannayenta tayi cikin nasa cikin ɓacin rai tafara magana. Ahanaf bazan taɓa lamuntar wanan abunba, wannan zalincin yayi yawa ko da ace ba akan ƴaƴana wannan abun yafaru ba to ni nan mai iya tsayama koma waye ne dan ganin yasamu adalci. bare akan yarana.

Ahanaf saidai kayi haƙuri a wannan ƙaron bazanja bakina nayi shuru ba wallahi, kuma kaji na rantse.

 

Kansa yadafe tare da furta ya Allah wannan wace kalar jarabawa ce ya Ubangiji ina neman afuwarka ka sassauta mana wannan lamarin, wannan Rana ce dana ci buri akanta najima ina tsumayin zuwanta da muradin ganinta.

dana san haka zata kasance dani da na roƙi Allah karma ya nunamin wannan BAƘAR RANAR.

Yaƙarisa maganar cikin matsanan cin kuka tare da ɗaura kansa akan ƙafafun Ayiya, bayansa ta dinga bugawa a hankali cikin sigar rarrashi.

 

A gidansu Noor kuwa tuni labari ya riski mahaifiyar ta najin saɓanin da aka samu gurin ɗaurin auren. ciki tashin hankali ta miƙe tsaye tare da cewa wllhy bazai yuyu ba wannan ai hauka ne ma.

 

 

 

Nabeela Binji ce

 

 

Nabeelah Shehu Binji

 

09064314811

Or

09161107610

 

 

 

 

More comment

More taping

 

 

 

 

 

Share FisabilillahMuna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Duhun Inuwa Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.