Duk So Ne Sila Hausa Novel

Duk So Ne Sila Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: DUK SO NE….*

 

 

 

 

 

 

 

*MMN SUDAIS ce👌🏼*

 

 

 

*🌙MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙*

 

 

*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’*

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~~~~~~~~

 

 

 

*Assalamu alaikum wannan book na sadaukar dashi ga uban yarana Dr. M. Yusuf D. Allah ya ƙara mana zaman lafiya da kaunar juna AMEEN*

 

 

 

 

 

 

Gaskiya masoyi yayi💃🏻

 

 

Ya Allah ka barmu da masoyan mu🥰

 

 

 

 

 

 

 

Page 2<

 

 

 

 

 

 

 

 

Babbar yayar mu tayi mana nasiha me tsawo kafin ta jiyo kaina, ta nuna man mahimman cin haƙuri da juriya da daukar ƙaddara mai kyau ko marar kyau

 

tace in mata arziki na Auri lamido ita ta naji ajikin ta insha Allah bazanyi danasa nin auren saba

ta ce “me sunan mama komi yayi zafi maganin shi na wurin Allah, ki ƙara dagewa da *Addu’a* saikiga Allah yakawo maki haske ta inda bakiyi tsamma ni ba”

 

sosai nisihar ta tasa man natsuwa acikin raina naji ɓacin raina danake ji yayin man sauki

 

suma su yaya Rukayya suka ƙara kwantar man da hankali sai naji hankali na yafara dawowa jikina harsuna zolayata da Amarya ba gyara nayi masu murmushi kawai,

 

sai sa’adiya tace “yaya Mamy karki damu nasan inda zan kaiki inda zakisami gyara abinda ake kira gyara, sosai zakifito kamar yarinya *yar* *shekara* *23* ” saida na saki baki ina kallan ta sannan “nace Sa’adiya kenan a can zasu kwashe man *shekara* *5* din”

sai duka parlorn aka kwashe da dariya

 

sai yaya Sa’adatu tace “kedai me sunan mama anyi yar renin hankali bafa shekarun naki za’a kwashe ba, gyara ne zakisha wanda zemaida ki yarinya danya sharab” sai nayi yar dariya “nace nifa yaya Sa’adatu nagane nufin ta gyaran ne kawai bazanyi ba, haba wane gyara kuma ana zaune ƙalau”

 

yaya Maryam zatayi magana babbar yayar su tadaga mata hannu tayi mata alamar tayi shiru

sai suka ji aƙalla kiran sallar mangarib

dole taran yashi, kowa ya tashi domin bada Farali…….

 

 

 

 

 

*Yanzu* *wasan* *zai fara💃🏻* *( zamu shiga labarin )*

 

 

 

 

 

*Abuja Nigeria*

 

 

Maasha Allah gaskiya gidan nan yahadu ciki da wajan sa, kai ko gidan Governor sai haka unguwar da gidan ke ciki sai wane da wane ze iya zama, yo ko Abujar kake saikaci katada ka ke iya zama cikin ta, kai gidan fa akwai kyau saboda yana cikin sahun gidajen dasukafi kowa ne haduwa, ba wani bane ma mallakin gidan illa *°ABDUL* *HAMEET* *MUHAMUD* *LAMIDO°*

dawowar sa kenan daga masallaci sallar issha, yana zaune a katafaran parlorn sa wanda yaji Royal chair yana zaune a daya daga cikin kujerun parlorn yayi shiru, me sunan mama ce tayi kane-kane a zuciyar shi, shi abin har mamaki yake bashi ko lokacin da yake matashin sa beyi wann zazzafar soyayyar ba, bare yanzu da yake a *38* *years* what is happening to me° ya dan gyara zaman shi yana ƙara nutsawa a tunanin kozegano dalili,

 

kukun sa ne yayi masa sallama yace “sir dining table is ready” yadago ya kalli kukun alamar yaji, besan yayi magana

dan kar tunanin kamo bakin tsaran da yake ya kuɓuce masa,

 

kukun yajuya yafita yana ƙara mamakin ogan su tunda yafara neman Auren nan yayi mugun canza halayyar sa, yanzu becika san magana ba, haka fara’arsa taragu, mafi yawa yafi zama cikin tunani kukun ya ce °komisa? saice kai ba ruwana zandai taya oga da addu’a Allah ya bashi nace ta kwarai mai karki kamar ogan, dan oga badai mutunci ba.

 

Lamido bayan fitar kukun saiya ji gaban sa yafadi da yatuna da abinda ya faru *a* *America* lokacin yana shekarar ƙarshe a karatun sa,

*a* *University* *of* *Chicago* , hankalin shi yadan tashi kan ko me sunan mama tasami wann history din ne shiyasa take ƙin auren ne,

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
can km yace “kai impossible” ya shafa kan sa ya ƙara cewa “kai da wuya ma ace zata san wann issue din, dan ko Hajiyar sa (Maman sa) be tsam ma nin ta sani,

to bare kuma relatives din shi, duk dai yasan beda laifi a lokacin amma ba kowa ba ne ze yarda…….

 

sai ya gyara zaman sa yadan zame ya kwanta akan kurerar dan daman akan 3sitter yake zaune

 

damuwar da ya sama kansa ko yunwar ma saiji be jin ta, can kuma sai ya miƙe tsaye hankali sa a tashe yace “ya salam” yana me dafa sitin heart din shi jin yadda take bugawa, nan da nan idan shi yayi jah,

tunowa da yayi da rigamar auren shi na farko, yaciji leɓan sa na ƙasa komi yana ƙara kwance masa,

 

ba shakka me sunan mama taji labarin rigamar auren shi na farko shiyasa take ƙin auren shi,

yace °subahanallah” sai kuma yace “Allah yasa dai bata fada ma yan’uwan ta ba,

ai duk saiyaji miyan bakinsa yaƙahe, ya isa kusa da dispenser din dake falan yadauki kofin dake saman ta ya danna yaci ka kofin da ruwa maisanyi ya shanye yaƙara cikawa ya shanye saida yasha wajan kofi 4 sannan yaji dama-dama

 

cikin wayoyin sa daya aje abisa Center table ne yaji daya daga cikin su tana neman agaji yataka zuwa inda wayoyin suke yadauki wanda aka kira yakai kunnan sa

Abokin sa ne kuma babban Aminin sa Abdullah Abubakar

 

yana dagawa yafara yimasa sheganta ka yana masa dariya,

shadai lamido murmushi kawai yake dan beda kuzarin da ze mayar masa,

 

saida Abdullah yayi masa tsiya san ransa sann yafara yimasa baya nin dalilin kiran akan daukar Amarya daga Katsina zuwa Abuja

Lamido yace ok ya kuka yi arranging din tafiyar ne? sai Abdullah yace “munyi arranging mutum 5 za suyi rakiya, sai lamido yace ” why not yar rakiyar ta ta ace masu mutum 9 har ita goma kenan, tunda private jet 10 seater ne,

sai Abdullah yace ok hakan ma is alright,

sai lamido yayi shiru yana sauraren Abdullah akan walimar za’ayi immediately after the wedding sai lamido yace ok hakan yayi komi ana iya yin sa a Katsina din ba matsala amma a wane hall ne za’a walimar? sai Abdullah yafada masa

sai lamido yace yauwa hall din yayi

sai Abdullah yace yau she zeje Katsinar

sai lamidon ya bashi amsa yace “insha Allah ranar Alhamis zandira katsinar (wato ana gobe daurin aure),

 

sun dade suna wayar suna tsara komi yadda akeso ko nace Abdullah yake masa bayanin yadda aka shirya din

saboda komi na hidimar bikin yana hannun Abdullah din…….

 

 

##########

*✨✨✨✨✨✨*

 

 

Bayan munga sallar issha munci Abinci sai Sa’adiya ta matso kusa da Ni tace yaya Mamy “bari nakira matan nan mai gyaran Amare muji ko zata sami zuwa nan Katsina, kinsan gari-gari ake daukar ta dan gyaran Amarya kawai”

nace “haba Sa’adiya bacce maki ni ba wani gyaran da zanyi, kar ma ki walahar da matar mutane, Sa’adiya tace “dan Allah yaya Mamy ki amince ayi maki gyaran nan, haka kike so mu kai ki gidan yaya Abdul din gayan ki,

Please yaya Mamy gyara fa shine mata ce”

 

haushi yaƙara kama ni nace Allah Sa’adiya kifita idona kafin ranki yaɓaci dole ne sai nayi wani gyara can” nayi wani tsaki nadauki wayata na miƙe zan koma daki na kwan ta saboda sa’adiya ta bata man rai da shirman ta

 

sai babbar yayan mu tace me sunan mama koma kizauna, saina koma na zauna babbar yayar mu ta kalle ni tace “haba me sunan mama yaushe kika koma haka ni ban sani ba, ban san ki da kafewa ba, ina jin tun dazu mungama babin Auren lamido kin amince man, to ina ganin duk wani shirye-shiryen Auren zaki amshe sa da hannu biyu,

sai ace ƙanwar ki Sa’adiya ce keta fama dake akan shirin,

 

nan babbar yayan mu te tayi man fada-fada nasiha-nasiha sann tace ma Sa’adiya taba ta number matar mai gyaran Amaren

 

aiko Sa’adiya cikin sauri ta lalubo number a wayar ta tamiƙa ma babbar yayan mu saida ta duba time taga ko 9:pm beyi ba sann takira number matar,

 

aiko tana kiran no.tashiga ba a dauki wani lokaci ba matar tadaga bayan sun gaisa da babbar yayan mu sann tayi matar banin komi sai matar tace “yanzu dai akwai wasu Amaren dake gidan ta tana shirya su amma zata turo mana yaran ta yan mata su 2 insha Allah zasu hada ni yadda ya kama ta duk da dai anbasu shirin a ƙurarran lokaci amma tace badamuwa zasu yi iya yin su”

 

sai babbar yayan mu tayi mata godiya nace “bakomi in ya kama subita har gidan ta a ida gyaran sai suje tunda kince yan mata ne” sai matar tace “yauwa hakan yayi masu saboda su sunfi san abasu amarya a ƙalla sati 2 shine ƙaran cin kwana kin da suke so abasu”

 

sai babbar yayar mu nace “maasha Allah to ga ƙanwar ta nan zata baku Address yadda zaku gane sosai” sai ta miƙama Sa’adiya wayar sun fara gaisawa da matar irin gasuwar sanin juna sann Sa’adiya tace “zata yi masu text din Address din sai matar tayi mata Sa’adiya godiya sosai tace insha Allah goben da wuri zasu taho sann suka yi sallama cikin raha…..

 

 

 

 

*✨✨✨✨✨*

 

 

Bayan sun gama waya da lamido ne tayi shiru

ranta inyayi duba yaɓaci, bata ta tsammanin ze ƙara a Aure duniya ba, tarasa abinda kemata dadi, duk plan din su na shekaru, wann Auren na lamido ze iya ruguje masu shi, auren da yazo masu a bazata, basu shirya masa ba, to yanzu miye mafi tar su ne

 

sai ta dauki waya ta kira Jamila tace mata ta nemi izini wurin mijin ta tazo tana san ganin ta akwai matsala, Jamila tace “to insha Allah bayan la’asar tana nan zuwa”,

ta kashe takira Ma’azu shima tace tana neman sa, shima yace insha Allah ze shigo anjima yanzu yana wurin aiki ne

sai kuma tace bari taji ko Bashir ya dawo daga Kaduna daya ce mata zeje,

bayan takira shi sun gaisa tace kadawo kuwaa? yace ‘mata a-a sai ma Alhamis ze gama abinda yakai shi kadunar, amma baze dawo ba, kawai ze wuce Katsina ne daurin auren lamido

 

sai yace koda wani

abu ne? sai te sauri tace a-a bakomi, daman dan ji lafiyar ka kuma na ji ko ka dawo ne,

sukayi sallama ta aje wayar tana hararar wayar kamar ita ce Bashir din……..✏️

 

 

 

 

 

 

 

*🌻BY ASIYA I B🌻*

*08180251350*

 

 

*Please share it🙋🏽‍♀️*

 

 

*Allah yagafarta ma mahaifan mu AMEEN😰*

[24/08, 1:05 pm] +234 803 192 1625: *🌻DUK SO NE….💘*

*(SILA😍*

 

 

 

*MMN SUDAIS ce👌🏼*

 

 

 

*🌙MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 

*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’*

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~~~~~~~~

 

 

 

*Assalamu Alaikum jama’a wann shine book din na farko a social media Ina ruƙan Allah yayi man jagoranci akan saƙwan da nake so na isar zuwa gare ku Allah yasa ya amfane mu baki daya nagode Allah yasa story na yazo ma ku yadda kuke so🥰*

 

 

 

 

Allah yahadamu da masoyan mu nagari

 

 

 

 

 

Page 1<

 

 

 

*Shimfida….*

*London*

*Metropolitan*

*University*

 

 

 

 

Zaune take a gefen class dinsu tana duba wani book saboda anjima suna da test, tana sanye da english wear amma bamasu bayyana tsireci ba, sun dace da kalar fatar ta, ta ɗora jacket peach ta kamfanin kenzo da takalmin ta peach shima na kenzo ɗin, ta natsu a karatun da take, masha Allah zance dan haɗuwa wanda ake kira haɗuwa to yarinyar nan ta kai komi nata tsaf kamar ita ta zabarma kanta kyakykyawa ce ta ajin qarshe, ko mata yan uwanta tana daukar hankalinsu to bare maza. kuma yarinya ce qarama only 16 years haka amma yadda take anatse sai ka dauka takai irin 19 ko 20 years ɗin nan

 

can naji ace “lucky” sai naga beauty din nan ta dago kanta tana kallan tahuwar kwalli daya qawarta a school ɗin da idanuwanta manya masu daukar hankalin duk wani dan Adam ( Famela tarigata zuwa school ɗin dasati 2)

 

Dole sukirata da Lucky saboda Allah yabata hazakar karatu sosai da saurin kwashe abinda ake koya masu atake dan har tayi saukar alqur’ani yanzu haka hardarsa take akanta,

 

Tazo London metropolitan University ne karatu watanni 5 kenan dafara karatun amma day take da yake suna da gida acikin birni London ɗin

 

Famela ta iso kusa da ita ta ce “kaga Alhuddahuda sarkin karatu wai test dinma saikinyi mata karatu” tayi wani murmushi dani kaina Saida nasaki baki Ina kallan ta lallai yarinyan nan akwai baiwar kyau

 

Famela ta ce “Dodan naki ne fa yazo”, nan da nan naga fara’ar dake fuskarta tabace baki daya, Famela tayi murmushi tazauna kusa da ita tace “kinga please kidaure yaudai muje ko gaisawa kuyi, yau yabani tausayi sosai yace man koya kira wayarki baki dauka why? me sanka ai be kamata yazama maƙiyin ka ba, amma kin dauki tsanar duniya kin dora masa, gentleman wanda mata dayawa keso ya kulasu amma ke kinsamu kina yanga”

 

dasauri ta dago ta kalli Famela tare da mamaki a fuskarta Famela tayi Yar dariya tace “ai gaskiya nafaɗa”,

 

ta gargiza kanta ahankali tayi magana da muryarta maidadin sauraro tace “to ki riƙe gaskiyar taki ni daman kitashi muje cafeteria naci abinci dan yau ko karyawa ban tsaya nayiba nafito, makara nayi bayan nayi sallar asuba na dan koma bacci sai wajan 9:am natashi gashi bansan nayi miss din lecture ko daya”

 

Famela tace “Aiko ni nasan wannan, to wai lucky ya zamuyi da gentleman dinki dake san ganin ki afujajan, tabbas akwai abinda yake so yafada ki, kituna fa saboda ke yadawo da wasu harkokin sa a garin London, haba aikin dan tausaya masa mana”

 

Saita “sigh” tasa hannu tadan dafe kanta because batason yawan magana tace “Dan Allah meela wai nawane SHATIMA yabiyaki dan kiyi masa kamfe ne? kifada man zan linka maki kudin dan ki shafa man lfy da yiman maganar sa”

 

Famela ta tuntsire da dariya tace “Amma lucky kin cuceni da kika maidani lashe moni,

ta hade hannuwan ta wuri daya alamun roƙo tace please mubar maganar sa haka nan inya gaji da jira yatafi ni tashi muje nayi breakfast sai kawai tafara hada books dinta tana sawa cikin jikkarta dole itama Famelar tamiqe dan tafiya…….

 

 

 

 

 

 

*Tushan labari*

*Katsina State*

 

 

 

“Haba dan Allah me sunan Mama kowa yana faɗa maki gaskiya amma kin wani share mu kamar ba dake mu ke magana ba duk wannan taran saboda ke mukayi shi ga Yaya Maryam daga Abuja Yaya Rukayya daga Kaduna ni da Sa’adiya daga Kano duk da dai biki ne yakawo mu garin amma harda °issue ɗinki yahana mu komawa gidan auran mu, to wallahi in karasa mai faɗa maka kaji kayi asara”

 

“miye aibun LAMIDO kike kinsa❓

duk wanda yaga kulawar dayake maki zai gane yana tsananin sanki amma ke kince baki auresa, abisa wane dalili? Kinsa bawan Allah yakoma kamar wani zararre”….. oh ni Sa’adatu naga abinda yafi qarfina🤔

 

Babbar yayar su Hjy Murja tayi dai shiru tana kallan su saboda sun gama yanke hukunci da ita da yayyansu maza da kawu Shehu insha Allah juma’ar nan mai zuwa za’a daura mata Auren da LAMIDO……

 

Dan gaskiya sun bincika beda makusa sai ma nagartarsa dasuka qaraji kuma su sun san badan kudin dake garesa yasa zasu bashi me sunan Mama ba a’a sai dai ance shedun duniya sune na ƙiyama… gata kowane bangare jama’a sansa suke da’ace zai tsaya takarar gwamna a garinsu tsaf zai dare kujerar

 

Dan sune ma suka hana shi yafaɗa mata daurin auran’ Dan sunga abin nata bame ƙarewa bane, da an tarota nan saita bule can ita Auren ne gabadaya bata ra’ayi saboda an shata tawarke maza basa gabanta ko kadan

 

sai yaya Rukayya tace “sa’adatu kibar bata bakinki inajin duk Yaya Maryam ce ke daure mata gindi tana wani lallabata kamar wata yarinya’ Aure dai kin yishi Dan kawai ƙaddarar mutuwar Aure yasame ki sai kice bazaki sake aure ba, to idan ma so kike mu huce murabu dake kiyi kome gidan Baban su Umar wallahi kinyi ƙarya’ Alhamdulillah tunda dai kingama idda”

Sa’adiya te karaf tace “yau ko satin ta biyu dagama iddar ba, kodazata koma sai ansake daura masu wani Auran”

Yaya Sa’adatu tai sauri tace “insha Allah bazata koma gidan Auwal ba mutumen da be san darajar haihuwa ba ace har mace tana da Yara har 4 da kai ka iya sakinta ba da wani Babban dalili ba”

Sai ya Rukayya ta ce aiko shi ke da babban dalili na auren tsohuwar guzuma mai shekaru 44 da yayi ne wanda aka ce bata haihuwa

Sai Sa’adiya ta ce daman yace ma yaya Mamy shi ya gaji da haihuwa shi a tsarin yaran da yake so ya haifa 5 ne amma wai sai gashi har sun kai 7

 

Babbar yayarsu Hajiya Murja tace “to Allah ya kyauta ai mazan ne sai haƙuri,” yanzu dai dan Allah kubar maganar haka nan ta isa”

Sai yaya Maryam bayan ta sallame sallar la’asar dayake tana kabbara sallah kenan suka fara yima me sunan Mama cari itace ƙarshan Alwalla sai tazama itace ƙarshan sallar

tace “haba Rukayya yaza kice Ina daure ma Me sunan Mama gindi wanda a dalilin ban san Auwal ya maidata gidan shi na dauketa na maidata kusa dani, ko kunsan Auwal zuwanshi Abuja 3 neman bikwan me sunan Mama, bantaba yarda yahadu da ita ba kuma itama inajin sai yanzu takejin zuwan nasa, saboda shi layin wayarta na cire nasama mata wani to daman ita kusan ba damuwa tayi da kiraye kirayan waya ba shiyasa farar daya bata gane ba, ta kance man wai ƙawayan ta nayi mata complain ta whaeapp insun kira layinta baya shiga na kance mata matsalar network ne watarar zai gyaru, Aiko Ina tabbatar da ta gama idda na maida mata layin, harta whaeapp nasa tayi blocking din Auwal din danma kar yayi amfani da ta wajan whaeapp yamaidata gidanshi, in kunga yaqin da nayi wajan ƙara sata tsanar kome sai Kun sara man amma shine Rukayya zakice wani…..

 

Babbar yayarsu Hjy Murja ta daga ma Yaya Maryam hannu tace “wai bacce abar maganar haka nan ba”, ina san kubani hankalin ku nan”

 

Tunda suka fara yiman faɗa ban ɗago kaina ba sai alokacin na ɗago ina share hawayan dake idona

 

duk da naga su Yaya Rukayya sun maida hankalin su ga Babbar yayar mu amma sai na kalli Yaya Maryam nace “amma Aunty kinsan yadda haduwar tafarko da LAMIDON ta kasan ce bame Dadi bace, yanzu baki tunani ko dan daukar fasa ne yasa yake san ya aureni” sai naji idona yaƙara kawo ruwa, sai kowa yamaida kallansa ga Yaya Maryam yana san jin ƙarin bayani sai yaya Maryam tadan rude ta ce mun “kedai me sunan Mama Akwai ki da maido hannun agogo baya” taƙare maganar tana hararata saina ƙara sadda kaina ƙasa raina yana ƙara baci wasu hawayan masu zafi na ƙara zubo mani niba yarinya ba akeso aiman Auren fin karfi ko nace na dole

 

sai yaya Rukayya ta ce “wai Yaya Maryam kinbarmu cikin duhu fa, gaskiya haka nan ba dalili me sunan Mama bazata ƙi mutuman nan mai nagarta ba, tunda ita ba yarinya bace da hankalin ta, tasan abu maikyau da aka sin shi, ni gaskiya harta fara bani tausayi please miya faru ne”

 

Ita dai Yaya Maryam tayi shiru taƙi kalan kowa a parlorn, tana tsoran ta fada komai zai iya wargajewa,

 

da Babbar yayarsu ta fahimci duk yadda akai da akwai matsalar da bakowa ya kamata yajiba musamman Sa’adatu mai zafi, sai te saurin cewa “nace kubani hankalin ku nan” sun sake juyowa ga Babbar yayarsu Amma kowa yaso yaji dalilin rudewar Yaya Maryam akan tambayar da me sunan Mama da tayi mata akan LAMIDON.

 

Alhamdulillah Allah yajiƙan mahaifiyar mu tabamu tarbiya dai-dai gwargwado saboda bayaban kaiba munfi dakinsu Yaya Badiya tarbiya, ga Maman mu takoyar damu bin nagaba sosai da sosai takance ko bayan raina zakuyi alfari da hakan

Gashi tahada kanmu, sosai muke kaunar junan mu, mu 9 tarasu tabarmu

Yaya Mansur shine babba adakinmu ko ince shine babba duka gidan kasancewar Maman mu ce uwargida muna ce masa Alhaji Babba nan Katsina yake zaune da iyalan shi

Sai maibi masa Yaya Abubakar Alhaji qarami shi kuma muke ce masa Shima anan Katsina yake zaune da iyanlan shi

Sai yaya Murja wanda muke kiran da Babbar Yaya ita majin ta rasuwa yayi, bayan rasuwar Maman mu bada jimawa ba mijin nata yarasu, sai tadawo dakin Maman mu da zama, Daman duka rayansu 4 ne biyu sun rasu tun suna qanana, 2 ne maza Allah yaraya mata su, duk sunyi Aure da iyalan su

Sai yaya Maryam dake Aure Abuja itama da zuri’ar ta

Sai yaya Rukayya dake Kaduna itama da yaran ta

Sai yaya muktar dake Lagos da zuriar sa

Sai yaya Sa’adatu dake Aure Kano

 

Sai ni da nayi Aure a Katsina sai autar mu Sa’adiya da itama Kano take Auren

duka dakin mu kowa yayi zuria mai yawa Alhamdulillah

Kuma muna da rufin Asiri dai-dai gwargwado

 

Dakinsu yaya Badiya kuma suma su 9 ne Maman su Gwaggo Binta ta haifa amma 4 sun rasu saura su 5

 

Yaya Mudan shine babba adakinsu sai yaya Badiya

Yaya Zulai

Sai Hauwa’u da Salma su nagirmesu, Hauwa’u ce tsaran autar ɗakin mu Sa’adiya sai ya kasance Salma ce Autar gidan mu kenan Dan Sa’adiya ta girme ta

 

Alhamdulillah zance gida mu akwai zaman lfy Dan Baban mu kafin yarasu (Dan yariga Maman mu rasuwa da shekara 4) Saida yadage sosai Allah yatemake sa sannan kam mu yahadu danko sam Gwaggo Binta batasan hadin kan gidan mu ko kadan Allah ya Amince ma Baban mu kam mu yahadu Amma mazan sun fimu haɗa kansu

 

A garin Katsina a Yar’adua muke zaune, iyaye na yan’ nan cikin ganin Katsina ne matar baban mu ce yar ƙauyan kurfi……

 

 

Saida Babbar yayarmu taga duka mun bata Attention dinmu sannan tafara dayi mana nasiha akan zumunci da mahimmancin sa kamar yadda tasaba yimana tun bayan rasuwar Maman mu, nasihar ta mai shiga jiki,

sai kuma kowa jikin sa yayi sanyi……✏️

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*🌻BY ASIYA I B🌻*

*08180251350*

 

 

 

*Please share it🙋🏽‍♀️*

 

 

*Allah yagafarta ma Mahaifanmu😰*

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.