Hausa Novels

Duniya Biyu Mabanbanta Complete Hausa Novel

Duniya Biyu Mabanbanta Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Duniya Biyu Mabanbanta Complete Hausa Novel

FREE PAGE

Ahankali yake saukowa daga stairs katafaren falon dako gidan shugaban kasa sai haka, yana sauka ahankali yana gyara zaman necktie din wuyanshi da hannu daya kasancewa dayan hannun na rikeda wata briefcase brown, daidai lokacin wata babban mace da a kalla zatai 57 tana sanye da shiga na alfarma tabude kofar wani daki wanda ga dukkan alamu kitchen ne sabida kamshin girke girke daya cika ko’ina tafito bayanta kuma wata maid ce dake sanye da uniform din masu aiki tana rike da babban warmer da alamu abinci ne aciki ta tsaya a bayan matan ganin uwar dakin nata ta tsaya itama, ganin matashin yasa batare data kalli maid dinba tace “kai kulan dining Shafa” sanan tacigaba da tafiya daidai matashin yakarasa saukowa daga stairs yakaraso gabanta, kafinma yay magana ta mika hannunta takai kan necktie din dayaketa fama dashi da hannu daya ta shiga gyaramai, dan murmushi yasaki cikin wata yar karaman natsassiyan murya yace “Barka da safiya Ammi” batare data amsashi ba ta sauke hannayenta kasa ganin tagama gyaramai ta kalli fuskarshi damuwa karara ya bayyana akan fuskarta amma saitai shiru batace mai komiba, kallon datake mai yasa adan shagwabe yace “Ammi, menen…..?” wuceshi tayi tai dinning taja kujera tazauna tadau mug tareda bude flask ta tsayaya ruwan zafi sanan ta waigo ganin har lokacin yana tsaye inda ta barshi yasa tace “anan zaka tsayane kana kallona ko ba break zakayi ba?”

 

 

 

 

 

 

Ayanda tamai maganan yasa yagane fushi take dashi kuma yasan dalilin fushin, karasowa yayi yaja kujeran gefen ta ahankali ya ijiye briefcase din hannunshi kan dayan chair dat is next to him sanan yazauna ahankali, mug din shayin dayasha kayan kamshi ta turomai gabanshi cikeda fushi tadau plate mai kyau fari kal kal ta debamai soyayyan Irish sanan ta kallai babu alamun wasa akan fuskarta tace “pepper soup ko ketchup? Wanne zan samaka?” murya chan kasa yace “ketchup” daukan bottle din ketchup tayi tabude tazubamai a gefen chips din dayawa dan tasan Allah yazubamai son ketchup sabida shi kadai agidan nan takesa ayo cefane harda na ketchup dan shi kadai kesha ita haryau abin baimata bane ko dandane batayi. Turamai plate din tayi gabanshi zata zare hannunta daga jikin plate din yakama hannunta yarike hakan yasa tadago idanunta ta kallai, dan shiru yayi yana kallonta sanan yadan sauke ajiyan zuciya asanyaye, murya chan kasa yace “I promise bazan dade ba kinji Ammi please” dan lumshe ido tayi cikeda takaicin shi sanan tabude su, batason tamai masifa hakan yasa ta sassauta murya tace “gobe fa bikinka haba Waleed bazaka iya daukan break kahakura da zuwa aikin nan ba, yakamata kaje kaga Ilham ko, you suppose kaje kaganta kaji medame dame take bukata, yaufa dinner ku mesa kake hakane? Kai baka gajiya da aiki, safe aiki, rana aiki dare aiki dukkai kadai bakagajiya?” tai maganan sounding a bit harsh sanan tai shiru tana kallonshi, ahankali ya saukar da kanshi kasa kaman bazaiyi magana ba saikuma yace “am doing all wat am doing for Dad Ammi, I’m doing it for him” yay maganan tareda dago kanshi ya kalli mahaifiyar tashi sosai yaga jikinta yay wani irin sanyi, hannunta takai ahankali ta shafa full sajenshi dakeda mugun laushi yana kyalli sosai tace “Waleed, Boy listen” tai maganan ahankali tace “I know u are doing all this for your father and trust me, I know duk inda mahaifinka yake he is proud of you cus he gave birth to such eloquent hard working youngman da burinshi shine yataimaki Al Umma, but in this Life Waleed you need to balance somethings, bazaiyu kullum aiki aiki aiki ba, u are needed awasu wajajen, za’ayi bikinka but bikin baya gabanka kwata kwata kabar su Khaleel da Hammad sumaka komi that isn’t right kagane?” gyadamata kai yayi ahankali, sanan tace “abinda nakeso dakai yanzu, I know how much this work means to you dan haka bazan hanaka zuwaba, kaje but ana tasowa daga sallan juma’a kadawo kazo kafara shirye shirye, take a break of 2weeks aure zakayi kaji” gyadamata kai yayi amman harga Allah yasan yanada rai da lafiya bazai iya yaki zuwa wurin aiki harna tsawo kwana goma shahudu ba but bazai iya gardama da Ammi ba. “now eat karkai latti” maganan Ammi ya katse shi hakan yasa ya karbi fork din datake bashi ya shigacin Irish din yana dangwalawa a ketchup, yadanci badayawa ba yadau shayin ya shanye sanan ya goge bakinshi yatashi yana kokarin daukan briefcase din yace “ina Mum Ammi? Naje dakinta bata ciki” murmushi Ammi tayi tace “Mum dinka nachan ana harkan biki, ni banmasan ina tanayi ba, wuce katafi sabida kadawo dawuri” gyadamata kai yayi yadau briefcase din yafito waje, babban compound ne mai bala’in girma sai amsa gaisuwan masu aiki yake, gaban wata jeep yayi da wani mutumi katoto ke tsaye agabanta yana sanye da bakaken suit, yana ganinshi yabude mai baya hakan yasa ya shiga ya zauna, yamaida kofar ya rufe sanan yawuce ya shiga mazaunin direba ya kunna motar aka budemusu Gate suka fita.

 

 

 

 

 

Karanta Littafin Yarima Ashaman

Tafiyan wajen minti talatin sukayi kaman zasubar garin Abuja sanan direban yay horn agaban wani tangamemen Gate wanda sojoji guda hudu ke tsaye agaban wajen rike da bindigogin su da alamu gadi suke an rubuta WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLED (Gidan Marayu da Gidan Nakasassu) asaman tangamemen Gate din, sojoji na sarama motan alamun gaisuwa, aka bude gate din akayi daga ciki direba yaja motar suka shiga, titi ne har titi kaman sun shiga wani gari daban suka hau tafiya, manyan fulawowi sun ratsa dan dandamalin tsakiyan titin daya raba titin shiga da titin fita, babban wurine da girman shi zaiyi girman wani babban University, daga farko farkon babu wani gini ta wajejen sai sport yard, wajen kwallon, wajen buga long tennis, basket ball sune awajen, almost tafiyan 5 min sanan sukakai wajen wani tangamemen masallaci mai kyau gaske an rubuta WARBAI MASJID ajiki da larabci, sanan sai wani katon story building da aka rubuta Boys Section ajiki mai girman gaske, babu kowa agaban wajen sai wasu yan yara haka dake sanye da uniform na makaranta su kusan goma da wasu ma’aikata maza ke taredasu suna sanye da jeans saikuma riga dayakasance uniform ne dan yanada logo WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLED rubuce ajiki, yaran nakasassu ne dan wasu hannun guragu ne dasu, wasu idanunsu wani kala, wasu nada katon kai, wani kuma shanyayyen hannu saidai dukkansu atsaftace suke fes fes, kallo daya zaka musu kagane suna samun special kula, suna sanye da clean uniform da white sucks dinsu ga jakunkunan makarantan suke goyedashi da ko wanne akwai sunanshi ajiki sabida a dinga ganewa dan jakunkunan iri dayane sanan ajikin school bag din shima akwai logo orphanage home din akai, agogon hannunshi ya kalla ganin tara saura yasa anatse yace “stop the car” parking direban nashi yayi baijira yafito yabude mai ba yabude motan yafito cikin dan fushi dan yanayinshi ya nuna haka, yaran suna ganinshi sukahau ihu suna tsalle irin na yaran nan sukai wajenshi da gudunsu. “Teacher, Teacher, oyoyo” kowanen su burinshi yakamo hannunshi yarike kosu kamashi, murmushi yayi daya karama fuskarshi wani irin kyawu da cikan haiba, ahankali ya tsugunna dan tsayinsu yazo daidai cikin harshen turenci yace “Hello Children” suma cikin harshen turenci sukece “Hello Teacher” sosai yaran ke tsalle tsalle banda mutum daya cikinsu da yake kuka mara sauti sai hawaye yake sharewa da bayan hannu, maaikatan dake kallonsu cikeda girmamawa suka gaidashi. “Barka da shigowa Dr” bai tsaya amsa gaisuwan suba strictly yace “why are this children late? Maiya faru ba’a kaisu school dawuri ba?” daya daga cikin ma’aikatan ne yace “Dr gabaki dayansu basuyi homework bane antsaya amusu ne” “what happen da baku zauna dasu kun ko yamusu ba jiya? Kunzaci am paying you all ne dan kuyi yanda kukaga dama?” yay maganan babu wasa dan inhar kan yarane or duty nasu he can question, baya daukan raini, saisa suke mugun tsoronshi, cikeda girmamawa daya daga cikinsu yace “mun shafa’a ayakuri Dr, hakan bazai kara faruwa ba in sha Allah, dan Allah kayakuri” “sorry teacher” yaran suka fada ganin yanayin fuskarshi yanuna he’s a bit angry, kasa magana yayi sabida sun bashi hakuri yadauke kanshi yamaida hankalin shi kan yaron dake kuka, tashi yayi ya daukeshi yace “why are you crying namiji?” murmushi yaron yayi yadaura hannunshi kan necktie dinshi yana kallo abin yama daukemai hankali, necktie din yakama yana kallon fuskar yaron yace “you like it?” gyadamai kai yaron yayi da sauri hakan yasa yay murmushi yace “okay zansa akawo muku naku anjima okay” washemai baki yayi yaron yayi cikeda jin dadi hakan yasa ya saukar dashi kasa yace “a tafi school to, bye” “bye Teacher” suka fadi dukansu atare sanan suka wuce school ya tsaya yana binsu da kallo, babu abinda yake so kaman yaga he’s the reason behind this innocent children smile, yakai kusan 5min yana kallon yanda suke tafiya suna wasa suna tsalle tsalle maaiktan na tattarosu sanan ya kada kai yawuce yashiga motar da direban yabude mai sanan yamaida yarufe yakoma gaba yaja motar sanan suka tafi.

 

 

 

 

Babbban gidan marayu ne da nakasassu, akwai wani dankareren building da aka rubuta kitchen and dinning ajiki, anan both ma’aikata da yaran gidan marayu ke zuwa suci abinci, wani babban story building ne dake kusada kitchen din shi kadai ne building din da aka katangeshi an rubuta girls section ajiki, sai ta dayan bangaren haggu wani babban school ne, akeai nursery har zuwa SS3 ga qualify teachers sanan akwai islamiyya inda kullum by 4 yara da manya zasu tafi islamiyya ai karatu 6 suke tashi kowa ya dawo gida dan lumshe ido yayi yana tunawa da mahaifin shi shi yasan he can never be like his father dan baitaba ganin the most generous person in this world like his father ba, baban shi nada taimako, ga son zumunci ga karfafama talakawa saisa bayan ya rasu he set up this orphanage home din in his memory dan lada yadinga kaiwa gareshi, setting it up wasn’t easy within the first two yrs dayay establishing nashi government sukai approving sanan sukai licensing orphanage din dan a yanzu ko tsintar yara akayi saidai gwamnati subada izini akawo yaran gidan, sanan gwamnati nabada tallafi dudda baya bukatar tallafinsu he has morethan enough that can keep the orphanage running in the next hundred years.

 

Ahankali yabude idanunshi jin motar yay parking, budemai direban yayi hakan yasa yafito yana bin parking space din admin block din dayaji flowers da kallo komi looking neat a perfect kaman a dubai, wani guy ne fari dogo dudda baikai Waleed din tsayiba yafito daga wani office yana sanye da bakin suit da necktie awuyanshi, hannunshi rikeda wata pad ta apple yana saukowa daga dan stairs din da bazasu wuce guda 10 stair case ba dazasu sadashi da kasa yana tunkaran su, hannu ya mikamai yana murmushi irin ta tsokana dinan yace “Ango I didn’t expect to see u here today na dauka sai anjima zamu hadu a dinner” dan hararan shi yayi yace “Mr P.A tell me wat we got today?” dan dariya guy din yayi yace “P.A badadi abakinka dan baka saba cewaba malam, better call me da sunan da babana ya yanka raguna biyu ya lakaba min ARHAM ABDULLAH” dan murmushi yayi daya mugun lobar da dimples dinshi yawuce shi yafara hawa staircase din batare daya juyoba yacigaba da tafiya a binshi, sanin bazai sake cemai komiba yasa yadan dan danna screen din ipad din dayake rikeda shi yana biyeda shi abaya yace “all right let’s see wat we’ve got here” sanan yadan sauke ajiyan zuciya yace “okay Boss, you have five major abubuwa da zakayi yau, number 1 is zakai magana da company Tata marcopolo dakasa su aikomana da 5 marcopolo buses dazamuyi amfani dashi for excursion dazamuje yankari game resort next week, sai the second thing is zaka shiga theatre by 9 surgery yaron nan dakeda outgrowth awuyanshi, abu na uku is zamuje girls section we need to inspect bunk dinsu da Iyami tamana complain are due for changes, abu nahudu kanada meeting da all the employees bayan sallan juma’a by 2:30, sai last abunda zakayi shine letter dakace zakama state government” gyadamai kai yayi daidai sun karaso gaban office dinshi, hannunshi yadaura ajikin wani glass haka dake manne agaban kofar, wani blue wuta glass din yakawo sanan yay scanning hanunshi sanan kofar tabude ya shiga ciki Arham biyeda shi, babban office ne, hadadden gaske dan tsayawa bayanin shi is a waste of time, office ne dayasha office furnitures na zamani, suit dinshi yacire yay hanging akan wani designers hanger sanan yawuce yaja kujeran shi ya zauna, shikuma Arham ya zauna a kujeran baki yana facing nashi yana jiranshi yay magana yaji amsan shi, agogon hannunshi Waleed ya kalla anatse sanan ya saukar da hannun yace “by nine zan shiga operation din, I think you will handle waya da company Tata marcopolo, and u will handle inspection of the girls section bunks, meeting with all the employees should be prospone cus banda time yau, you should tell secretary ya tura musu message kan na daga meeting din till further notice, tura letter ma to state government I don’t think bazai yuwu yau ba maybe jibi nasami time zanyi, zaka iya tafiya kaje kai aikinka” kallonshi Arham yayi hakan yasa yace “wat?” ahankali Arham yace “talk to me X-Man, I know something is wrong with you, talk to me yaushe muka fara boyema juna issues?” dan hararan shi yayi yadauke kai batare dayace komiba, “X-Man” Arham yakirashi ahankali, cikin dan fushi Waleed yace “how many times do I need to explain this to you P.A time for work should always be time for work, ba’a hada aiki da friendship, please go and do your job I pay you for it, we will talk anjima” cikin fushi Arham ya tashi daga kan kujeran dayake kai yace “kasan problem dina dakai?” dago idanunshi dasuka dan chanza launi Waleed yayi ya tsareshi dasu, cikeda jin haushin shi sosai yace “you are so weak but u hide under the face of rudeness, you know what? You sucks, kuma kar Allah yasa kafada lemme go and do job din da you pay me for it” yabugi table din da hannu yay kara sosai sanan yajuya zai fita, sosai yaji wani iri kiranshi yayi. “Arha……” bugomai kofan yayi hakan yasa ya lumshe ido tareda daura hannunshi kan saman goshinshi yana nishi ranshi duk abace saikuma yadaki table din yace “f**k!” dan gajeren tsaki yayi yatashi, wani kofa dake cikin office din yaje, hannunshi yasa kan kofar itama kaman wanchan kofar yay scanning hannunshi sanan yabude mai ya shiga ciki, hadadden dakine da babu abinda babu aciki, gaban wani fridge yaje yabude, kwalaban wine ne kala kala, dauko daya yayi yadau glass cup yakoma kan hadadden Italian bed din dakin yazauna, yabude wine din ya tsiyaya a cup ya ijiye kwalban akasa sanan yadau cup din yakafa abaki ya shanye, zare cup din yayi daga bakinshi yana yatsine fuska sabida daci sanan ya ijiye glass cup din ya kara kallon agogon hannunshi, ganin tara saura yasa yafito, fita daga office din yayi ko kadan ranshi ba dadi yay hanyar babban clinic din orphanage din sai gaidashi ake amma baiko iya amsawa.

Direct office dinshi ya shiga ya chanza kayanshi zuwa kayan shiga theater sanan yafito ya shiga theater din.

Leave a Comment

error: Content is protected !!