Hausa Novels

Elhaj Hausa Novel Complete

Elhaj Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*ELHAJJ*

 

 

Free page 1

 

Written by

Mrs A.M

 

Marubuciyar

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*

 

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

 

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

09066728387

 

 

*SANARWA SANARWA*

 

 

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

 

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

 

 

*LOCATION KANO*

 

08062073990

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

 

Ta dukufa sosai tana duba littafan addinin dake kan center table, idonta sanye da farin glass din da take sawa duk lokacin da zata karanta abu ko zata yi amfani da waya.

 

Tana sanye da red lace a jikinta wanda ya haska ta dinkin ya zauna a jikin ta yai mata dass, tayi kyau sosai kasancewar ta fara sol, tana da kyau dai dai nata don baxa a kirata da mummuna ba.

 

Sam hankalin ta bai fada mata zuwan sa ba, har sai da taji ya dafa ta dagowa tai ta zuba masa idonta da ke nuna tsantsar kaunar sa a tattare da ita, lumshe masa idon tai kafin ta cire glass din idonta, mike wa tai cike da shagwaba tace “ba dai fita zaka yiba ELHAJJ”.

 

Lumshe mata ido yai kawai yana kallon watch din hannun sa, turo baki tai tana bubbuga kafa a kasa tace “kai dai koh, dama nasan baxa kamin magana ba share ni za kayi kawai”.

 

Hannun sa yasa ya shafa kumatun ta, kamar wanda bakinsa yake masa ciwo yake “kin girma fa..h, ki daina abin yara 30 yrs kike fa”.

 

Kwanciya tai akan faffadan kirjin sa tace “haba dai Elhajj ai ni yarinya ce har ynxu a gun ka, bana girma”.

 

Gajeran murmushi yai yace “uhm, na fita”.

 

Matsa wa tai daga jikin sa tace “bye”.

 

Fita yai cikin takunsa dake nuna nutsuwar sa, yana isa compound din security dinsa dake sanye cikin black suit suka mike da sauri, gaishe sa sukai cikin girmamawa, ba tare da ya amsa suba ya shiga bayan motar da suka bude masa, da sauri suma daya ya shiga driver sit dayan kuma ya zauna a kujerar mai zaman banxa.

 

iPad dinsa ya dauka ya shiga aiki da ita, cikin girmamawa Wanda ke zaune a driver sit din yace “Sir ina zamu je?”

 

Sai da ya dau wajen 3 minutes kafin ya bude baki da kyar yace “new site”.

 

Daga kai yai yace “ohk Sir”

 

Tafiyar 15 minutes ya kaisu ga wani building mai masifar kyau, fadar kyaun sa bata lokacin ne amma ya hadu iya haduwa, ta ko ina glass ne.

 

A gurin da yake ajiye motocin sa security din yai parking, da sauri dayan ya fito ya bude masa kofar, bai jima ba ya fito don yana da meeting din da zai yi mai muhimmanci.

 

Tafiya yake suna take masa baya har suka iso inda zai hau private elevator dinsa, sai anan suka matsa amma basu bishi na cikin sauri suma suka shiga general elevator wanda kowa zai iya amfani dashi.

 

Kusan a tare suka fito daga ciki, bayan sun isa 5th floor wanda anan ne meeting room din yake.

 

Cikin nutsuwar data zame masa jiki ya shiga dakin taron, kowa ya hallara da alama shi kadai ake jira, bai tsaya wani gaishe gaishe ba kawai suka fara magana akan abinda ya tara su.

 

Sun dauki kusan 2 hours suna magana wanda duk akan kayan da zai shigo dasu ne daga companyn sa dake China, wanda tun kafin zuwan kayan manyan yan kasuwa sun bada kudi su, don kowa yasan Elhajj baya sai da baragurbin kaya.

 

Office dinsa daya gama haduwa ya shiga bayan gama meeting din nasu, zama yai yana cire hular kansa, a hankali ya dauki remote din AC ya kara sanyin ta kasancewar sa ma’abocin son sanyi sosai.

 

Bude kofar akai aka shigo, bai bude idon saba don ya riga yasan ba wanda zai shigo masa office kai tsaye sai aminin sa Salim.

 

Zama Salim yai a kujerar dake kallon tasa yace “Elhajj ina ta fada maka tun jiya Ka kara duba abin nan fa, ni mutumin bai kwanta min ba sam gani nake kamar cutar mu yazo yi kawai”.

 

Bude lulu eyes dinsa yai akan Salim tabe baki yai yana dan gyara zaman sa yace “na riga na fada ma nayi signing, kuma ni banga alamun cutar mu yazo yi ba and wannan deal din fa mai kyau ne ka sani zamu samu profit sosai”.

 

Girgiza kai Salim yai cikin kokarin fahimtar dashi yace “kudade masu yawa fa kasa Elhajj kuma ni banga amfanin sa kudin ba, wannan abin in kana so zaka iya Sawa a fara yi a company ka fah, mai yasa sai Ka basa kudin”.

 

Bottle water ya bude ya kurba kadan kafin yace “taimakon sa nai, kasuwancin sa yana son mutuwa kuma ni banga wani aibun hakan ba, bafa kyauta na basa ba kasuwanci zamu yi tare nida Shi meye damuwar kane Salim”.

 

Shiru Salim yai kafin yace “shiknn tunda har hankalin Ka ya kwanta da wannan business din bkm”.

 

Shiru sukai dukan su sai karar AC kadan kadan, mikewa Salim yai yace “bara naje ina da wasu clients da zasu zo muyi magana”.

 

Daga masa kai kawai yai hankalin sa akan computer dinsa da yake duba wasu design na textile din da zai shigo dasu.

 

 

*********

Ihu take tana kuruwa kamar wacce ake yankata, duk mutanen gidan sun fito sai kallon ta suke suna Allah ya kara.

 

Kara murde mata kunne Baba yai yace “ba tambayar ki nake ba ina kika kaimin kudi na don ubanki”.

 

Zillo tai tana kokarin kwace kanta tace “haba Baba don Allah, ni bani na daukar ma kudi ba wallahi meye hadina da kudin ka kuma fisabilillahi kawai salon dai dole sai an yiwa mutum sharri, wallahi Allah yana sama kuna yana kallo”.

 

Bige mata baki yai yace “rashin kunya zaki min, wa kike zagi ni Umma data fada min ehe”.

 

Turo karamin bakin ta tai tace “da Umma nake ai Baba, Allah yana kallo kuma wallahi baxan yadda ba sai na rama”.

 

Hannu yakai zai kara mangare mata baki tai saurin kauce wa tana turo baki.

 

Umma dake tsaye a kofar dakin ta tace “don Ubanki *DIJE* ni kike zagi karya na miki na kece kika dau kudin ba, a gabana kika fito daga dakin sa kina boye abu a zani”.

 

Da karfi dije ta fincike kunnen ta daga hannun Baba daya tsaya yana sauraran abinda Umma take cewa, kallon Umma tai da manyan idon ta tace “nidai nasan bani bace kuma duk Wanda ya dauka yasa ake zargina Allah ya isa wuta balbal baxan yafe masa ba”.

 

Inna fure dake zaune a tsakar gidan tana tankade kukar da take siyar wa tace “ai Malam daka kyale ta Ka rabu da tambayar ta don in har wannan fitsararriyar ce baxa ta fada ma gaskia ba, kuma tunda har Yaya tace ta ganta da idon ta tofa ba shakka ta ganta din kuwa”.

 

Hararar ta dije tai tace “Inna fure ba ruwan ki wallahi ba dake muke ba, kar ki shiga fadan daba naki na atoh ki barni kar na shiga harkar ki kizo kina cewa nayi miki rashin kunya”.

 

Janyo ta Baba yai yana dafe kansa yace “wai don Allah baxa ki nutsu bane, sai yaushe zaki yi hankali kullum baki da aiki sai yiwa manya rashin kunya”.

 

Rau-rau tai da idonta tace “toh Baba kana kallon fa, so kake nayi shiru na zuba ido ai ta soka min maganganun da zasu sa hawan jini kama ni ynxu Baba”.

 

“Ikon Allah” Baba ya fada yana kallon, juya wa yai kawai ya dubi Mama dake yiwa Aisha jikar ta kitso, cikin haushin yadda tun da aka fara maganar nan bata sa baki ba yace “ynxu Maman Hajara kina kallon abinda yarinyar nan take amma baxa kiyi magana ba kin mana banxa kamar baki san muna gun ba”.

 

Tabe baki tai ba tare data kalle sa ba tace “Malam mai zan ce ni kuma, ai gani nai dukkan mutanen dake tsakar gidan nan sun isa su hukunta dije shiyasa na kyale ku kuyi mata duk hukuncin da ku ka ga dai-dai ne, abinda na sani shine kawai y’ata baxa ta taba sata ba”.

 

A harzuke Baba yace “kina nufin karya duk ake mata knn?”

 

Sai a lokacin ta dago ta kalle sa tace “eh toh zan iya cewa haka Kam”

 

Tsaki yai kawai ya juya don yiwa dije magana sai dai wayam ya gani alamu ta gudu, girgiza kai yai yace “wannan yarinya Allah ya shirye ta ita bata san ta girma ba wai?”.

 

Tabe baki Umma tai tace “ina ta sani kuwa, kullum gata nan tana yawo da hijab sai tsami da take, da anyi magana tace yar islamiyya ce ita”.

 

Inna fure ta cafe da fadin “shiyasa ni ko wanke wanke bana bata toh yarinya ce kazanta ta mata katutu kamar mahaukaciya”.

 

Girgiza kai Baba yai ya sa kai ya fice daga gidan cike da takaicin kudin sa da aka dauke masa.

 

Ni kuwa tunda na samu na fita daga gidan ban tafi ko ina ba sai hausawa a kafa gidan Yaya Hajara, ina tafiya a hanya a hankali kamar ba dije ba sai dai duk wannan tafiyar da nake mai kama da yanga cikin dauda nake, don ash din hijab dina ya koma dark brown sbd rashin tsafta sosai duk yayi jirwaye.

 

A hankali na tura kofar gidan ina sallama, Yaya Hajara dake zaune a tsakar gidan ta tana girki tace “wa’alaikumussalam shigo nasan laifi kika yi shine kika lallabo nan, Allah dai ya shirye ki”.

 

Bakina na turo ina shigowa cike da shagwaba nace “kai don Allah Yaya Hajara, wai ba gurin Wanda zanje ya dinga lallaba ni ne, ita Mama kullum tana hantara ta tana cemin kazama, su Umma kuwa dama ai ba’a maganar su kema kuma gashi nan wallahi sai na hada kayana na gudu haba kun ishe ni fah”.

 

Da mamaki Yaya Hajara take kallonta, mike wa tai a hankali sbd cikin ta daga girma tace “ki gudu ki tafi ina Dije?”.

 

Ba tare da shakkar komi ba tace “karkashin gada mana can Lagos”.

 

Salati Yaya hajara ta kamayi tace “ikon Allah, yaushe zaki yi hankali Dije shekaru 15 amma har ynxu dai kullum jiya i yau”.

 

Zama tai akan kujerar katakon dake tsakar gidan tace “nidai ba wannan ba, ki taimaka min ki zuba min abinci wallahi yunwa nake ji, kinsan girkin Inna Fure ne kuma sbd mugunta irin tata baxa tayi girki da wuri ba sai mun lallasu”.

 

Girgiza kai Yaya Hajara tai tace “baxan baki abinci ba sai kin yi wanka kin cire wadannan kazaman kayan naki”.

 

Da sauri na mike nace “tab baxan yiba gaskia haba don Allah taya Zan yi wata wanka kamar wata yar ruwa, shekaran jiya jiya fa nai wankan kuma kice mai wanka ynxu”.

 

Kamar Yaya Hajara zata make ta tace “ni dai na rasa wata iriyar yarinya ce keh Dije kazanta tayi miki yawa wallahi, rabon ki da wanka tun shekaran jiya wata iriyar mace ce keh”.

 

Turo baki nai nace “ba wankan da zanyi gaskia, nifa ina son kamshin da jikina yake in banyi wanka ba”.

 

Tafa hannu Yaya Hajara tai tace “warin kike so dije?”?

 

Juya manyan idon ta tai tace “kwarai kuwa, har shinshinawa nake naji kamshin baki ji dadin da nake jiba”.

 

Ganin zare ido baxai sa Dije tai abinda take so ba tace “toh ynxu dai in kin yadda zaki cire kayan ki tas kiyi wanka na baki wani kisa sannan ki bude kanki na wanke miki shi ni kuma zan baki 200”.

 

Shiru Dije tai tana tunanin wanna opportunity din, da sauri tace “toh na yadda amma dai zaki fara bani kudin na rike a hannuna don karma ki min wayo”.

 

Daki ta shiga ta dauko dari biyun tace “gashi, karba tai da sauri tace yauwa na ngd, kamar kinsan dama ina kicin matsi ina bukatar kudi”.

 

Banxa tai mata sai kujera data jawo ta zauna, wanke ma Dije kai take da ya dankare sbd datti, ta jigata sosai kafin ta gama wanke kan sai tsaki take ita ba abin tayi mita ba tasan tsaf Dije zata ce ta fasa wankan.

 

Ruwa ta nuna wa Dije tace “dauki wannan kije ki dirje jikin ki sosai, na ajiye miki sabulu da soso har da sabon brush in baki wanke ko ina ba sai na karbe kudina”.

 

Turo baki kawai Dije tai ta shige toilet din, ta fi minti 20 a ciki sannan ta fito ta don bata tsaya algus ba tunda an biya ta sai data wanke ko ina ta wanke bakin ta sosai.

 

Zanin da Yaya Hajara ta bata ta daura a jikinta ta fito sai baxa dogon gashin ta yake, taji dadin wanka da wankin Kan don ko ta ina iska shigar ta take yi.

 

Dakin Yaya Hajara ta shiga a ciki ta same ta tana zaune akan gado ta mike kafafun ta, har zata zauna itama Yaya Hajara ta nuna mata kayan da ta ajiye mata akan gado tace “kar ki sake ki zauna min dauki kayan nan ki sa, ga turare can a kan mirrow fesa a gabana ina kallon ki”.

 

Hararar gefe Dije tai tace “kamar ya na fesa turare nifa kinsan bama shiri da turare Yaya Hajara, in na fesa ji nake kamar numfashi na zai yanke”.

 

Tsaki yaya Hajara tai tace “iskancin banxa, ba wani kamar numfashin ki zai yanke kawai so kike ki dinga hamami kina bugawa”.

 

Kwal kwal da Ido tai tace “ynxu nice nake hamami ina bugawa Yaya Hajara”.

 

“Kwarai ko karya nai miki ne ehe, zaki fesa ko sai na tashi gani kikai ba’a bugun ki shiyasa kike abinda kika ga dama”.

 

Tana zumburo baki ta fesa turaren ta zura sabon pant dn da Yaya Hajara ta ajiye mata, bra tasa wacce Yaya Hajara ta siya in ta haihu tayi amfani da shi, da fushi da komai ta sa doguwar rigar.

 

Sai kuma ta karasa gaban mirror tana kallon kanta, wankan nan da tai ya kara fito da farar fatar ta, fara ce sol irin farin nan natural, tana da manyan ido wanda suke dake da light brown eye ball, sai siririn hancin ta daya dace da fuskar ta sosai, mai da kallo ta tai kan karamin bakinta da yake jajir kamar yasa jam baki, shafa gashin kanta tai tana nannade sa ta daure, tana da dogon gashi har tsakiyar bayanta, da kuma gefe gefen fuskar ta, tun daga girar tama dake a ciki in Ka kalla zaka san tana da Suma sosai.

 

Boobs dinta ta kalla da suke a kumbure tubarkalla sai tai saurin dauke idon ta, don ita fa kunya suke bata a cewar ta tayi kankanta da wadannan manyan abubuwan, ga hips tubarkalla da mazaunai kamar za’a daura cup, ba Wanda zai kalli structure din ta ya yadda cewa 15 years take.

 

Murmushi tai ta juyo ta kalli Yaya Hajara dake kallon ta tace “gaskia nayi kyau sosai Yaya kin ganni kuwa kamar wata yar India, ban fa dace da Nigeria ba gaba daya Sam”.

 

Tabe baki Yaya Hajara tai tace “kije palour abincin ki yana can ni bacci zanyi, in zaki tafi ki tashe ni”

 

Gyada kai tai ta fita zuwa palourn tana cewa “ai bama zan tafi ynxu ba sai na gama cika ciki na kuma na Jira baban Aisha ya dawo nasan da leda yake shigowa yau kason da ni za’a yi, sai dai In Mama yanka ni zatai Kam”.

 

Zama tai ta cika cikin ta sosai, Karin ta biyu don ita Kam Allah yayi ta da ci sosai, ruwa tasha ta kwanta akan kujera sai bacci…..

 

 

Ya kuka ji salon book din😉, littafi ne mai dauke da cin amana, tausayi, tsantsar soyayya…..

 

 

*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*.

 

09066728387

 

 

Comments Nd share plz

 

 

Mrs A.M🥰

[10/10, 9:14 pm] +234 916 272 2945: 🤎🤎🤎🤎

*ELHAJJ*

🤎🤎🤎🤎

 

Free page 2

 

Written by

Mrs A.M

 

Marubuciyar

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*

 

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

 

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

09066728387

 

 

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

 

 

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

 

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

 

 

*LOCATION KANO*

 

08062073990

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

 

Ba ita tashi ba sai da Yaya Hajara tazo ta tashe ta, lokacin sallah yayi.

 

Mika nai na mike ina fadin “gaskia da baki katse min bacci naba Yaya Hajara, ina cikin mafarki mai dadi ynxu kin katse ni”.

 

Banxa Yaya Hajara tai mata ta shige warta dakin mijin ta, ganin haka yasa na mike ina turo baki, alwala nai nayi sallah.

 

Kallon Agogo nai dake makale a jikin bangon palourn, da sauri na mike nace “wayyooo an shiga islamiyya tun dazu, ynxu ya zanyi”.

 

Shiru nai ina tunani nasan in na tafi islamiyya tofa daga nan gida zan wuce knn baxan dawo gidan Yaya Hajara ba na Jira dawowar Baban Aisha, dakin Yaya Hajara na shiga na dauko hijab dinta dogo har kasa nasa, duk iskanci na bana wasa da islamiyya don anan kam brain dina yana mugun ja, last year na gama haddar Qur’ani ynxu littafai kawai nake yi sai kuma muraji’a da muke kullum.

 

Fitowa nai dai-dai lokacin da Yaya Hajara ta fito daga dayan dakin, kallona tai tace “sai ina kuma sarkin yawo”.

 

Turo jajayen lips dina nai cike da shagwaba nace “Islamiyya fa zanje, lokaci ma ya kure sosai amma dai zanje gaskia”.

 

Daga kai tai tace “daga nan gida zaki wuce knn koh”.

 

Daga kai nai nace “insha Allah, ki kawo kudi na siya wa Aisha alawa a makaranta”.

 

Zama tai akan kujera tace “ynxu ke alawar da za’a siya wa Aisha ma sai kince na bada kudin, ina zaki kai son kudi ke kuwa Dije”.

 

Kamar zan kuka nace “gaskia ku daina cemin Dije sai kace wata yar kauye, suna na Khadija suna mai dadi amma an bata min ai duk laifin Kaka ne data bata min suna haka kurin sbd sunan ta aka samin sai tace sai dai a cemin Dije shi kuma Baba ya yadda nidai an cuce ni gaskia”.

 

Yaya Hajara data saki baki tana kallona tace “ynxu dai ita kakar kike fada wa haka, bayan ta mutu ma baxa ta huta ba Dije”.

 

Daga kafada nai nace “ni ai ba Allah ya isa naja mata ba kawai dai nayi yan fad`e-fad`e ne akan yadda ake batan suna ynxu dai shiknn kawai bara naje islamiyyar sai wata ran kuma, don ba nan kusa zan Kara zuwa ba kullum nazo sai kin sani nai wanka haba..”

 

“Allah ya kiyaye” kawai Yaya Hajara ta ce mata don ita ta gaji da surutun Dije ko gajiya bata yi.

 

Fita nai a gidan a kafa nake tafiya ta a nutse har na isa karkasara unguwar mu, a kasan layin mu islamiyyar take ko da naje ba wanka ya tare ni akan makara, aji na shiga na zauna na maida hankali na sosai, dama kuma ni bani da kawa bama a kawancen dani wai na cika kazanta, kawata Yayata ce kawai da ita nake shawaran komai.

 

Sai 6 muka tashi ban tsaya komai ba ma nufi kanti, ina zuwa na mika dari biyun hannu na nace “gashi bani omo na 100 da sabulun 40”.

 

Miko min yai ba tare daya min magana ba don ya san halina ina karba na wuce gida.

 

A hankali nayi sallama yadda nasan ba Wanda zai ji ba kowa tsakar gidan da alama duk suna dakin su ko yaran kuma basu kai ga dawo wa daga islamiyya ba.

 

Labule na daga na shiga dakin mu ina sanda kamar wacce tayi sata, saki Mama tai tace “zaki shigo ne ko sai na janyo ki mara kunya”.

 

Shigowa nai ina bubbuga kafafu a kasa cike da shagwaba nace “kai Mama don Allah maimakon ki dinga riritani kina dora ni akan cinyar ki tunda nice auta amma sai hantara ta kawai kike…..”

 

Girgiza kai tai tace “a haka Zan dinga ririta ki din kina kazanta da rashin kunya ai sai dai kiga ana ririta wasu badai ni na ririta kiba”.

 

Zama nai ina turo baki, kamar zanyi kuka na nuna Aisha dake bacci akan cinyar mama nace “kin ga fah mama kin wani dora wannan yarinyar akan cinyar ki bayan nice nan autar ki ba ita ba”.

 

Girgiza kai Mama tai tace “ynxu dai da Aishan kike kishi yarinyar da bata fi shekara hudu ba”.

 

Daga kai mai ina mar mar da ido, girgiza kai kawai Mama tai tace “wannan kayan Hajara ce ta saki wanka koh?”.

 

Daga kai nai ina murmushi na cire hijab din nace “har wanke min kai tai amma sai da ta bani 200 sannan na yadda”.

 

Rangwashi na Mama tai tace “Allah ya shirye ki, wankan ma wanda ke zai amfana sai kin karbi kudi”.

 

Turo baki mai ina sosa kan nawa na Mika mata ledar hannu na nace “Mama kinga fa nace ta bani ne sbd na siya mana Omon wanki da sabulu namu ya kare kuma Baba baxai bada kudin da zamu siya ba sai karshen wata kin san shi fa”.

 

Shiru Mama tai tana duban Dije cike da kauna, Ashe duk shirmen ta tana kula da sabulun su daya kusa karewa, murmushi tai tace “Allah ya miki Albarka amma da baki karbar mata kudi ba’ai koh, ki wa kanki fada don Allah ki dinga tsafta aure fa za’a miki wata ran Dije”.

 

Boye fuskata nai a bayan Mama nace “tab ba auren da zanyi mama ina nan tare dake kawai sai nayi aure nifa ko saurayi ban da shi, ina kallon yadda Hajjo take ta tara samari amma ni ba Wanda yake cewa yana Sona”.

 

Dariya Mama tai tace “taya za’a ce ana sonki bayan kazanta kike, ita hajjon baki ga kullum take wanka ba tana sa turare amma ke turaren ma sai ana fama kafin kisa”.

 

Sosa bayan wuya na nai nace “toh Zan kiyaye Mama, zan dinga tsallaken kwana daya daya ai nayi kokari ko kuma xan dinga sa alumun”.

 

Tabe baki kawai Mama tai tana kara volume din radion ta.

 

 

********

Cikin takun sa cike da kasaita yake fitowa daga building din, gefen sa Salim ne magana suke akan wani business da Elhajj din yake son fara wa, na sabon companyn da zai bude wanda za’a dinga leda da robobi.

 

Mota Elhajj ya shiga yace “sai gobe ma karasa Salim na gaji sosai”.

 

Dariya Salim yai yace “tab! Lallai tunda yau Elhajj guda ya gaji dole kowa ma ya gaji”.

 

Murmushi Elhajj yai Wanda ya sa dimples dinsa lotsawa gaba daya, girgiza kai yai yace “Allah ya shirye ka”.

 

Dariya sosai Salim yake yace “sai anjima a gaida Madam”.

 

Daga kai yai ya rufe motar, ba tare da ya kalli Driver din ba yace “Gidan Momma”

 

Cikin bin Umarni yace “ohk sir”

 

Yana bayan motar yana zana wani sample na atampa da yake son a masa irin su, ya dukufa a zanen har suke iso, bai fita daga motar ba sai da ya gama zanen ya tura sannan ya fita daga motar.

 

Masallacin dake jikin gidan ya fara shiga yai sallah, tare suka fito shida Papa suna tafiya a tare amma ba Wanda yai ma wani magana.

 

Sai da suka shiga cikin palourn suka zauna sannan ya kalli Papa yace “ina wuni”

 

Daga kai Papa yai yace “lafia Elhajj, kuna lafia?”

 

Daga kai yai a hankali ba tare da yai magana ba, murmushi Papa yai yace “miskilancin naka har yau dai bai sauka akai naba koh”.

 

Sunkuyar da kansa yai yana sakin murmushi kadan

 

Shigowa Momma tai bayanta masu aiki ne dauke da flask na abinci da tray, Zama tai tana dariya fuskar ta a washe tace “son sannu da zuwa ynxu kazo amma koh”.

 

Murmushi yai ya daga Kai yace “Ina wuni Momma”.

 

Murmushi tai tana kallon sa tace “lafia qalau son, ya gida da harkokin?”

 

A gajarce yace “Alhamdulillah”

 

“Masha Allah”, ta fada tana mikewa zuba masa zobo Mai sanyi tai ta mika masa tace “gashi nasan tunda ka fita ba lallai kaci abinci ba”.

 

Bai Mata musu ba ya karba yana kaiwa bakin sa idonsa akan TV, sai da ta tirsasa shi yaci abincin kadan don baya cin abinci sosai sai fruits.

 

Mike wa yai zai fita bayan yai musu sallama da sauri tace “son kaje gurin Malam kuwa, ya min magana rannan yace kana lafia dai koh”.

 

Hade rai yai sosai kawai yasa kai ya fita, kallon Papa tai kamar zatai kuka tace “ban san me yake damun son ba ya dauke kafa daga zuwa gurin Malam gaba daya, kuma in an masa magana ya shiga hade haden rai”.

 

Daga kai Papa yai cike da jimamin sabon sauyin da yake gani a tattare da dan nasa yace “Nima na lura da hakan don ya chanja sosai ba kamar yadda yake ba, duk da miskili ne amma ynxu abin yafi worst”.

 

Rausaya kai Momma tai tace “sai addu’a kawai zamu cigaba da yi masa”.

 

Sai da ya tsaya ya siya wa Saudat tsire don yasan tana son sa sosai sannan suka karasa gida.

 

Cikin nutsuwar yake tafiya hannun sa rike da jakar sa sai ledar tsiren ta, da sallama a bakin sa ya shigo tana kwance akan kujera tana kallon Sunna TV, da sauri ta mike ta taho a guje ta fada jikin sa.

 

Dan murmushi ya saki yana tapping bayan ta yace “sannu da zaman gida”.

 

Sakin sa tai tana turo baki tace “uhm sannu koh, ai kai xanwa sannu Elhajj kai ka gaji sosai muje kayi wanka”.

 

Bai ce komai ba yayi gaba tabi bayan sa, Sama suka hau inda dakin sa yake, fita tai ta barshi don tasan bai cika son takura ba a irin wannan lokacin daya dawo a gajiye.

 

Wanka yai ya zira jallabiya ash colour, turare ya fesa ya fito palourn saman Wanda ya kasance nasa, a nan ya sami Saudat ta tasa tsiren a gaba tana ci.

 

Murmushi ya mata kawai ya sauna a kan kujera, watermelon juice din da take masa kullum ya dauka ya fara sha yana kallo, sai da ya gama shayewa tas sannan ya kalli Saudat da zuwa lokacin itama ta gama cin tsiren nata.

 

Mike wa yai yace “muje mu kwanta”,

 

Dan mika tai tace “muje Elhaji na”.

 

Tare suka kwanta ba tare daya neme taba don yasan koya neme tama sai dai ta sa masa kukan shagwaba, tun yana kokarin neman ta sosai har ya hakura sai in ita ta nema da kanta tunda bata cika son yana neman ta ba….

 

 

*********

 

Yau Monday zamu koma school, tunda na tashi nake kunkuni da bata rai bana son makarantar boko kamar me, bama yadda ake kirana da kazama, kuma ina gane karatun dai-dai gwargwado kawai dai bana son zuwa ne don ana takura min da tsokana.

 

Mama tana lura dani ta min banxa, sai kunkuni nake shiryawa nai cikin uniform dina Riga da wando sai hijab mai girma har ya kusa gwiwa ta, nayi kyau sosai kuma anyi sa’a yau nayi wanka ga kayana a wanke.

 

Jakata na rataya a baya na kalli Mama nace “nidai gaskia Mama wannan abun ya ishe ni ynxu haka zamu tafi ba’a gama abinci ba gaskia su Umma suna gasa mu wallahi, koko ne fa zasu dama kawai amma sun tsaya nauyin jiki haba don Allah kamar ba Mata ba”.

 

Make mata baki Mama tai tace “ke ban hana ki wai yin rashin kunya ba don gidan ku, na rasa ina kike koyar wadannan maganganun haba, kullum baki da aiki sai yiwa manya rashin kunya”.

 

Buga kafata nai a kasa nace “Mama lokaci fa ya tafi haka zamu tafi ban sha komai ba haba haba ayi adalci a lamarin nan”.

 

Hajjo ce ta turo kofar palourn tace “ki fito zamu wuce ko zaki tafi da kanki”.

 

Hararar ta nai nace “toh sarauniyar iyayi gani nan zuwa, an gama kunun ne?”

 

Tsaki Hajjo tai tace “aikin banxa mutum sai shegen ci kamar gara, to ba’a gama ba sai ki zo mu wuce ai koh”.

 

A harzuke na taho kusa ita nace “ni kike fadawa maganar banxa, sa’ar kice ni?”.

 

Wani kallo ta min tana Jan tsaki tace “aikin banxa kawai, ai baki kai matsayin da zan tsaya ina fada Miki magana ba wallahi, banxa kazama nafi karfin ki”.

 

Kut** bansan lokacin danai jifa da jakata ba na rarumo wuyanta, cikin duka karfin da Allah ya bani na hankada ta wajen kofar ta fadi ban bata damar mikewa ba na mara mata baya na hau ruwan cikin ta ina danna Mata naushi na baki.

 

Da sauri Mama ta fito daga dakin kokarin daga ni Mama take amma sai kara sukuwa nake akan cikin hajjo ina bata naushi, ita kuwa ta kasa ko cizo na don duk na hana ta damar da zata cije ni ko ta dake ni.

 

Ihun yaran gidan ya fito da Baba daga dakin sa da sauri, jan burki yai yana kallon yadda Dije take dukan hajjo duk ta hada mata jini da majina,.

 

Zuwa yai ya sa kafa ya hambare ni nayi baya na bugi da bango, wani ihu nasa ina mikewa tsaye da sauri ina sosa hannu na inda na buge.

 

Kallona Baba yai yace “wata iriyar muguwa ce keh, zaki hau cikin ta ki dinga duka”.

 

Sosa hannu na nake na kalli Hajjon dake tsungunne Umma na zuba mata ruwa tana wanke bakin ta daya fashe.

 

Turo baki gaba nai nace “rashin kunya ta min fa”.

 

 

 

 

*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*

 

09066728387

 

 

Comments Nd share plz

 

 

Mrs A.M

Leave a Comment

error: Content is protected !!