eNaira Payment Solutions Limited

eNaira Payment Solutions Limited

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: eNaira wallet

Amfanin e-Naira, Tsarin Shi Da Kuma Yadda Ake Amfani Da Shi

 

Ga wasu amfanoni guda 7 da eNaira ke tattare da shi:

 

1- Saukaka cinikayya a cikin gida da wajen Najeriya;

 

2- Tabbatar da ingantaccen tsaro a yayin gudanar da cinikayya;

 

3- Bai wa kowa daman karba da kuma aika kudade cikin sauki da arha da kuma sauri, walau a cikin gida Najeriya ko a kasashen waje.

 

4- Taimaka wa tsaron kasa, domin zai bai wa hukumomi daman sanya ido kan shige da ficen kudi don gano masu haramtacciyar manufofi.

 

5- Shigo da mutanen da basu samun damar cin moriyar amfani da bankuna cikin tsarin amfani da fasahar zamani wajen mu’amala da kudade.

 

6- Bayar da daman samun tallafin kudi daga gwamnati kai tsaye, cikin sauki da kuma sauri.

 

7- Taimaka wa tsarin karban haraji ta hanyar rage kashe kudin da ake yi wajen mu’amala da takardun kudi.

 

Wadannan kadan kenan daga cikin irin tarin alfanun da wannan nau’in kudi na eNaira ke tattare da shi.

 

Yadda tsarin eNaira ya ke shi ne; ana mu’amala da shi ne ta hanyar manhajar waya mai suna eNaira Speed Wallet. Ma’ana kafin mutum ya mallaki eNaira, dole sai ya fara saukar da manhajar na eNaira Speed Wallet, sannan kuma ya yi rajista. A manhajar eNaira Speed Wallet din ne ake adanawa da turawa da kuma karban eNaira din.

 

A da kafin fitowan wannan kudi na lataroni wato eNaira, abu ne mai wahala ka tura kudi zuwa ga wani wanda ba shi da asusun banki, musamman ma idan a kauye ya ke ko a wajen Najeriya, sai dai a yi ta ‘yan dabaru, kamar tura katin waya da dai sauran su. To amma a yanzu, eNaira ya kawo mafita ga wannan matsalar. Yanzu idan mutum na so ya tura kudi zuwa ga wani wanda ba shi da asusun banki, kawai matakan da zai bi guda uku ne kaman haka:

 

1 – Ya canja kudin daga Naira su koma eNaira, ta hanyar tura nairan daga manhajar asusun bankin sa zuwa manhajar na eNaira Speed Wallet. Ko kuma ta hanyar ziyartar sahihan jami’an canjin eNaira, ko jami’an bankin sa, domin su karbi takardun nairan sai su shigar da eNaira zuwa ga manhajar eNaira Speed Wallet din sa.

 

2 – Sai ya tabbatar da wanda zai tura ma din ya mallaki manhajar eNaira a wayar sa kuma ya yi rajista.

 

3 – Sai ya karbi lamba wato ‘Payment code’ na manhajar eNaira na wanda zai tura ma kudin.

 

Shi ke nan, bayan ya tabbatar da biyan kudin, kudin na eNaira za su tashi daga manhajar eNaira na wanda ya tura zuwa manhajar eNaira na wanda aka tura ma din.

 

Daga nan kuma shi wanda aka tura ma din, zai iya kashe kudin nasa na eNaira ta hanyar yin sayayya wato biyan kudin kayayyaki tare da manhajar tasa ta eNaira Speed Wallet.

 

Matukar dai kantin da mutum yai sayayya suna karban eNaira, to zai iya biyan kudin kayayyakin da ya saya a kantin ta hanyar haska hatimin QR code na kantin ko kuma turawa zuwa ga lambobin ‘Payment code’ na kantin, duk dai ta hanyar amfani da manhajar na eNaira Speed Wallet.

 

Ahmad Bala

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.