Esha Hausa Novel Complete

Esha Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: ESHA

 

_By maman Nurul_

_Hudah_

 

Same name,but different story….EEsha is my first book Zan sabonta shi ne I bet wanan zai kayatar kamar inda na farkon ya kayarta,same name,different story …….let go there……..

 

 

P 1-2️

 

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

Wata had’adiyar tsadaden mota ne ta paka a gaban company da za ayi auctioning sakamakon bashin banki da kamfanin ta ci bata biya ba adadin lokacin da aka d’ibar Mata tayi shine bankin ke auctioning kamfanin

 

Fitowa yayi cikin tsadaden suit Baki da ta ciki navy blue da kallo d’aya zaka Masa kasan kudi ta zauna saboda shigarsa kadai ta Isa ta sanar maka dashi din ko wanene,fari ne tas a kallo d’aya zaka gano fulanin asali ne gashi kyakyawa fari,bakar glass ne idonsa Babu ko alamun Wasa a fuskarsa he is darmmm serious,a shekaru zaiyi shekara 42-43

 

Take me baya mabiyansa sukayi zuwa ciki inda suka tarar da rumfa da kujeru zai zauna security Suka karaso da sauri sukayi me jagora high table a gaba

 

Wani cika yake Yana batsewa Kamar Wanda ya gan Kashi Suka zauna yayi crossing legs dinsa Yana d’an girgiza ta

 

Babu b’ata lokaci aka Fara abinda ya Tara jama’a wani me sanye da blue shadda yace”ni na bada miliyan biyar”

 

Alhaji adamu yace”miliyan 7″

 

Wani adekunle yace”miliyan 7 da Rabi ”

 

Daga hannu official din yayi yace”miliyan 7 da rabi,bakwai da rab……”

 

Be karasa ba Kawu Kabir yace”na bada miliyan goma Sha biyar”duk aka juya ana kallonsa dan kowa yasan property din be fi 5milion ba but saboda kowa Yana son a ce ya samu garab’asar nan shiyasa suka Kai har 7.5,but wanan wanene Haka zai bada har million 15 lallai me kudi ne

See also  Matar Gurgu Hausa Novel Complete

 

Haushi alhaji sule yaji yace”na Kara 500 akan saman nashi

 

Aka Kara maimaita million Sha shidda ba Wanda yayi magana har za a buga table kawu yace”na bada million talatin “wurin shiru ya dauka ana kallon kawu da ko a jikinsa sai kafa yake girgizawa

aka ce million talati 1,miliom talati 2 million talatin uku”Babu Wanda yace komai har aka buga aka ce kawu ya Zo yayi sighning document sanan yayi payment

 

Tashi yayi cikin Isa sai cika yake Yana batsewa har ya Kai table sai kawai ya Ciro waya Kamar an kirashi ya Kara a kunni

 

Tafiya yake Yana kallonsu da gefen Ido ganin hankalinsu baya kanshi yayiwa guards dinshi sighn da Ido suka ja baya a hankali sai ji akayi sun ja mota

 

Mamaki ya Kama jama”a wurin Suka bi motar da kallo

Littafan Hausa Novels

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

D’aya daga cikinsu yace”mu jirashi kila ya samu emergency Amma inda ya narka kudi Haka ai bazai so ya rasa ba ni nama ji kamar an ce gidan mai zaiyi anan din ko??”

 

Duk sun yarda emergency ya samu din shiyasa

 

__________

 

Suna Hawa babban layin gali yace”ai sai ka biyani ko malam ‘

 

Tabe baki yayi yace”Kai dai anyi tababbe wallahi ai ka Bari mu Kai kofar gida ko??”

 

Gali yace”waye zai Kaika kofar gida so kake motar alhaji yayi datti anguwan ku da duk kwata ne ah’ah wallahi ba inda zani ka sallameni a hanya

 

Kawu yace”nifa in nayi kudi bazan tuna da Kai ba saboda bazan mance wanan wulakanci da ka min ba,gashi dai na fara Kiran miliyoyi Ina shiga manya mutane garori suna can Baki sake suna jirana Basu san ko taro bani dashi ba Amma naji lafiya da na Shiga manya watoh gali ni burina a duniya shine inyi kudi in Zama babba shine ai na Fara rehearsal kafin inyi kudin”

See also  Abokin Kwana Hausa Novel Complete

 

Daga hanci gali yayi yace”iska na wahalal da me kayan Kara Kai yanzu K B bazaka wa kanka fad’a ba yariyar nan macece ka barta da aikin maza kullum cikin Nima take sai ta Tara ka kwashe kudi kayi harkarka dadin abin ma ita *EESHA* din ba kanwar latsa bace wallahi kawa kanka fad’a

 

Kawu ya saki Baki yace”ikon Allah ka gan kawar uwa me fad’a a ji ai sai ka paka ka fad’a hadisi tunda islamiyar ne banje ba da kake maganan Eesha ba kanwar latsa bane toh uwata ce ita ko dukana zatayi paka Dan Allah in sauka ga tawaga na Yan rakiya in sallamesu

 

Gali yace”toh Ina mashin dinka”

 

Kawu na fitowa d’ayan motar dake binsu ya paka

 

Kawu ya ciro dubu biyu ya Mika me yace”aini yanzu ba zancen mashin na Zama audio jina yafi ganina Dan kiri-kiri dai Ina son zuwa wuri amma Babu Hali bani da jumuri takawa,yariyar Nan Esha ta hade mashin dina da babban wayana ta saida Wai ta gyara Keke napep dinta ai gali Bari Ina ganin jarrabawa da wanan yariya ”

 

Gali ya juya 2k din yace”dubu biyu fa na gan ka bani”

 

Kawu K B ya jingina da motar yace”bani in baka so in Banda iya shege Kai motar naka ne Ina a irin wanan aikin kake Samu na tumatir

 

Gali ya ajiye kudin cikin dash board yace”Amma Amana Bata ce Haka ba dubu biyar mukayi da Kai Amma ka sab’a alkawari ”

 

Kawu yayi tafiyarsa yace”gobe in na Kira ka karka zo tunda ba Dole”

See also  Jarababben Namiji Complete

 

Karasawa yayi motar ya bawa Abbas dubu uku yace”gashi a maida musu motarsu da glasses din Nan da kuka sa kamar makafi dan girman Allah Abbas kana zuwa kayi wanka tsami kake wallahi duk sun cakud’e da tularai sai sani atishawa yake ‘

 

Abbas dai juya kudin yake Yana mamaki dan fa dubu biyar akayi dashi duk kawu na Lura dashi ya basar kamar be Gane ba

 

Yace”Bari in maidawa masu wanki da guga nan kayansu Kan su ce sai na Kara kudi

 

Abbas yace”toh sai mun fito da yamma”

 

Kawu yace”Kar Wanda ya kuskure ya Zo gidanmu yau dan akwai show kudin da Eesha a gida kudin da take Tarawa zata biyawa Fahad kudin makaranta na kwashe toh kasan ita ba fahimta abubuwa take ba,ta kasa fahimta Shiga cikin manya nan da Kuma rehearsal din nan ke bani lafiya da tuni zuciyata ta buga da bakin talauci da takaici

 

Salim yace”toh kayi Mata aure mana”

 

Kawu ya Kama hab’a yace”Kai wanan tayi karfi ba hurumina bane, Amma Zan duba da na gan me mahaukacin kudi had’asu Zan wallahi amma fa tare zamu tare in bazai iya ba ya hakura ”

 

Tafiyarsa yayi ya barsu da takaicinsa shi ba a shirya abu dashi sai ya canza Kuma sun rasa meyasa gobe in ya dawo sai su kasa Yi Masa musu…..

 

Laundry shop yaje direct ya shiga wani dan d’aki ya canza Kaya zuwa asalin nashi ya fito Wai sai yanzu yake nadamar d’aukar kudinta

 

**********######

 

Garejin Mobil

 

Maman Nur

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top