FACALA HAUSA NOVEL

FACALA HAUSA NOVEL

*FACALA*

_matar wa da matar kani_

Writed by: ~maman sabon yaroooo~

Pg 1

Bismillahirrahmanirarrahem

💊

💊

💊

💊

💊

‘Gaskiya Samira kina hakuri da wannan makwafciyar taki ni bazan iya zamada irinsu ba kam.

‘ikon Allah kinshigo gida Babu sallama sai korafi kike??

‘ai kaji ga irinta nan tun daga kofar gida nike kwada sallama bakijiba sabuda wannan karar da aka kure gidan nan dashi …

‘ni shigo daga ciki in Kuma korafin zaki tsaya yi awaje to

‘ya kinzo min da kayan ?

‘Nazo dasu amma gaskiya Kuna dawowa kiba abul yakawo min agoben sabuda Nima lace dinnan nikeson sawa bikin makwaftan mu.

“To shikenan muna dawowa zan Aiko Miki dashi

‘kai !! kai !! kai abul me ummi tayi maka ka mareta Kai azzalumin inane? To wlh karka Kara inba haka ba zan kakkaryaka agidan nan saina barka akwance..

Can daga cikin daki maman abul din kefadin Aiko kice za’ayi karye karye don kuwa wlh bawacca ta isa ta nakasa mun yaro abarni da jidali inaaa

Nan maman ummi tace oky lallai ma yanzu haka zakice wato kin daure mishi ?

‘Wani irin na daure mishi? Inaji kina fadin Zaki kakkarya yaro badole in magana ba?

‘To shikenan don Allah abul yakara dokar ummi yagani wlh kinji na rantse

‘sai Kuma kiyi,

Duk wannan cecekuncen da akeyi tsakanin maman abul da maman ummi uwar mijinsu najinsu tana gyara shinkafar yin wainata don daman wainar siyarwa takeyi amma tanajinsu kamar ba surukanta ba

Itako maman kalifa nacan ta kure tv adakinta sai wakar jaruma ke tashi tana bi

Aysha ko na can dakinta dayake kowacce nada kitchen adakinta

Su shiddane matan ya’yanta hudu daga ciki suna zaune ne anan cikin gidan Kuma kowacce mijinta daban babban wansu alhaji auwalu shine kawai yake zaune agidanshi kusa suke Amma matan shi biyu ne shi.

Haka suke zaune sai kanin mijinsu da bai aure ba saurayi akwai Mata guda uku suna gidanjen aurensu

Mijin maman ummi yanada shagon Saida kayan provision awaje

Daya daga cikin kannen mijin nasu ne ta haihu zasu suna shine maman abul ta ari lace din kawarta.

Washe gari zasu tafi gidan sunan dasafe suna shiryawa

‘mamammu kinga naje dakin maman abul ta koroni kuma mama bakiga ba tasa sabon leshi …

Uwar mi yakaiki dakinsu? Sabuda ke jakace inace jiya jiyannan ya mareki uwarshi tabi bayanshi Amma sabuda bakida zuciya shine yau Kika koma dakinsu……

‘Haba saude wani irin mugun alkaba’i kike jifar yarinyarki dashi ne haka, akan shirmen yara sai zagin yarinya kike …

Kawarta madina ce data biyi mata zasu gidan sunan tare ke Mata wannan maganar

‘madina bazaki gane bane Kiri kiri fa jiya yaron nan ya mareta amma babu tsoron Allah maimakon ta mishi fada sai ma Fadi take Wai karwacca ta taba mata da.

‘wani irin wulakanci ne wannan da iskanci Zaki barwa mutane buta babu ruwa aciki? Sakarya kawai batasan komiba sai shirme arayuwarta…

Mijin aysha ne kemata wannan tujarar don daman dabi’arsa kenan ko agaban waye kuwa inta mishi laifi zai ci Mata mutunci ba ruwanshi.

Itama ko batai kwaron bakiba tace haba habu taya zaka rikamin irin wannan zagin Yara ne suka zubarda ruwan Koko laifinane su yakamata kayiwa magana ai baniba haka kurum zakazo kana min ihu akaina ..

‘Wato ke bakida kunya ina fadi kina fadi ko sabuda kin rainani nan rigima ta kaceme suko mutan gidan ko ajikinsu inda sabo sun saba

Karshe gidan sunan da Aysha batajeba kenan tunda daman kanwarsa ce to yazo ya zageta acewarta.

Can gidan sunan kuwa bayan sun isa sai maijego ke tambayar ina Aysha?

Caraf maman abun ta karbe tace aiko bazata samu damar zuwaba suna can suna zuba fada itada habu kinsan kuwa batazuwa ko Ina yau indai adangin habune…

Maman abul haka take bada labari tiryan tiryan madina tace to adaibi ahankali fadan miji da matane saiku koma gida kigansu sun dinke ato

‘oho dai bawani dinkewa dazasuyi mumfa San komi indai ayshane ko girki tabaryi yau,

‘lallaima aiko tana ruwa azamanin nan daman akwai sauran mace Mai irin wannan halin?? Don kunyi rigima da miji har taki girki?

‘hu’um indai ayshane ta wuce nan bama girki ba har magana bazasiyiba

‘Kai maman abul daki daya kuke kwana harda zakice ko magana bazasuyiba heeeeee aka kwashe da dariya nan har aka tashi sunan caftar ayshane.

Washe gari dasafe gidan babu wani walwala don dama ayshace kusan shugaba agidan to ko bude dakinta batai ba yaranma da babansu suketa buruntu har suka gama shiryawa zuwa makaranta .

Sai shabiyu narana ta fito ta shima sakone wani yaro yakawo mata da wata kawarta ta bayar akawo Mata

Harzuwa yamma misalin karfe biyar kawarta dija ta kawo Mata ziyara suka shige daki,

Dijar ke tuhumarta cewa ke Aysha meke faruwane jiya kikazama abun nishadi agidan suna?

‘banganeba, jiya ai banje sunan ba

‘eh inasane bakijeba amma anje Miki donkuwa duk abunda kikasan yafaru haka aka zayyaneshi agidan sunan bama anan aka tsayaba don kuwa harda Karin magi da gishiri Koda yake banace magi da gishiri ba gaskiya aka fadi tunda gashi nan alamu sun nuna baki komiba agidan nan ba daman ance bazakuyi magana da habu ba harna tsawon wasu kwanaki …

‘Tabdijam tirkashi wace algungumar ce ko ince wacce munafukarce tace haka Kai tsaya ma basai nayi dogon bincike ba gidannan cike yake da annamimai da munafukai Kuma tabbas bazai yiwuba ai bawacce bata fada da mijinta kaf gidannan sai maman kalifa….

saurin katseta dija tayi tace har itama tana fadan kawai ta ita takunta ne yasa bakwa ganewa to wlh in baki canjaba kece akasa tun wuri kinemi hanyar hukunta miji bawai gaba da dauke wuta ba,

‘To dija wlh zamada habu bakowacce mace zata iyaba akan buta fa ko ince akan ruwa abuta fa ya dingamin tijara agidannan fisabilillahi meye ruwa abuta?

‘aiko bari kiji Kinga wlh babu abu mafi haushi da tunzura miji irin yazo ya dauki buta yaji kwambar babu ruwa aciki to wlh harzuka maza yake Kuma Yana fadi kina fadi shikesa kiji anyi abunda za’azo ana danasani do kuwa sakin aure yafi afkuka in Kika tsaya Kuna tanki tanka da miji iya gaskirki ki daure kiyi shiru kita fadin innalillahi WA’INNA ILAIHIRRAJU’UN azuciyarki inhar bazaki iya daurewa kice yi hakuri ba to ki maimaitawa azuciyarki kitashi ki shige daki daga nan saiki nemi hanyar hukuntashi cikin sanyi in Kuna on top dinnan kice yadena yi Miki fada atsakar gida yabari in Kuna ku biyune yayi Miki

‘himm banki takiba dija wlh taurin Kaine da habu ba yadda banyi dashi ga shehiyar bakar zuciya kamar tsohon kuturu

‘to ke ki Kara kulawa gaskiya ni bazan jure ya madidi dakeba ne kalli maman ummi ta girmeki fa maimakon amatsayin ta na matar wan miji ta kwaba miji …..

‘wa ce Allah kin tuba wannan babban kwabone …….

Ya kukaji🤣🤣🤣💊💊💊

[10/07, 8:27 pm] +234 810 321 0755: 💊 *FACALA*💊

_matar wa da matar kani_

Writed by ~*maman sabon yaro*~

Shafi na biyu

Yau jumma’a tun sassafe maman abul ta fitoda wanki ta jibge bakin kofar dakinta, tashige cikin dakin tana sharowa, maman ummi itama saita fitoda nata wankin ta aika Yara su siyo Mata sabulu kafin minti talatin ta cika igiyar gidan da kayan ta sai karfe takwas maman abul ta fito da Shirin yanzu zata fara nata wankin

‘kutumesin can lallaima to ai igiyar nan baban abul yakawo ta gidan don haka cire kayanki tunda dai abun y’ar hakane ai kina kallo na fitoda wankin zanyi sai Kuma kafin in gama shara da mofin kizo kiwani cika igiyar da shanya bazata sabuba…

‘Kinga Samira banison rashin kunya da rashin ganin ta ido niba tsaranki bane dazaki kalleni kina wannan surutan

Dai dai nan Aysha ta leko tace ‘hehe dadina da gobe saurun zuwa nan kukaje gidan sunan ba irin sharrinda bakumin ba gashi an ganku arana

‘Kinemi Wanda ya Miki gulma can yarinya kinsan dai ni ba sa’ar yinki bace maman ummi ke wannan maganar …

‘ai nan kikafi auki Abu kadan kice ke babbace bakison raini to wlh ni babu ruwana da girmanki ko shekarunki in tsoho baiji kunyar hawa jakiba jaki bazaiji kunyar kada shiba ehe.

Duk wannan abun dasuke maman kalifa na cikin daki ta kure tv ado gwanja na waka ita Kuma kan injin sakarta yau riguna uku ta keson yi donma ta tsaya yin abun Kari

Haka maman abul ta stinke igiyar shanyar nan maman ummi ta zaburo zata Kai Mata duka mijinta ya hana yakuma ce karta Kara Koda magana akai

Kai tsaye nan waje yaje yacewa kaninsa baban abul din kenan dayajawa matarsa kunne don kuwa inba hakaba zaibar maman ummi ta fasa Mata baki..

Baban abul bamai magana bane sammm don haka iyaka yace mishi to kayi hakuri baima tambayi ko meyafaruba

Har yamma tayi daman al’adar gidan ne kowacce da la’asar takeyin wankanta Mai anguwa taje Mai zaman gida nan zasuzo kofar dakin uwar mijin nasu akafa shafta

Ranar banda maman abul amasu zaman kofar dakin sabuda wannan yar tanki tankan da akasamu tsakaninta da maman ummi akan igiyar shanya haka Kuma maganar da aysha tayi na cewa anyi munafurcinta agidan suna don haka bazata fito ba yau

Maman kalifa Kuma ta fito Amma a kofar dakinta ta tsaya tana dura zobo a gora don tana Saida zobo da pure wata kanwarta sadiya tazo tana tayata.

‘assalamu alaikum

Matar babban yayansu dake makwaftaka dasu ce ta shigo gidan amaryar kenan lawisa nan tasamu guri tazauna ana tattaunawa ba’a dau lokaciba maman kalifa ta gama dura zobonta kanwarta takwashi botikan taje bakin famfo wankewa ita Kuma tashiga ciki don jera abunta a firij

Nan firar tazama daga Aysha sai maman ummin sai lawisa sunata kus kus don basa daga murya bare kaji me sukecewa

Kanwar maman kaliface dayake famfon na kusada su ne tajiyo maman ummi da lawisa na cewa ke aysha ai maman abul ce takai maganar rigimarku keda habu gidan sunan sai maman ummi kecewa bana gaya Miki cewa bani bace dazu shine harkike son sauke fushin ki akaina alhalin ni ma kinsan samira ba kyaleni takeyiba himmmm

‘dama an gayamun ai indai nice wlh koma wacece dai dai nikeda ita ehe mutum yajida halin mammakon da mijinshi keyi ehe ace kana zauneda miji ga yara amma komi sai dai ayi cikin mitsiltsila ba wadata alhalin akwai yadda za’ayi

‘nikam Kinga shiyasa bana kula koma menene tunda wlh ko yau dasafen nan baban su Amira dubu uku yabani kudin ankon bikin gidanmu.

Lawisa ke fadin haka sai maman ummi tace Kai bikin kanwarki haryazo dinne??

‘eh sauran sati hudu gashi Kuma baku kawo kudin ankon ba ananne ta daga murya tace maman kalifa sauran sati hudu nefa bikin gidanmu Wanda nabaku kyallen ankon nan tun watan daya wuce …

Sai anan maman kalifa din tafito tana cewa ‘ikon Allah har abun ya matso haka nawama kikace

‘dubu uku ne

Daki ta koma tafitodo dubu biyu tace ‘gashi in an kawo zan cika dubu dayan.. Allah Sanya alkhairi

‘amin aike daman bani shilafarki wlh nasan zaki riga kowa badawa daman ..

Ita dai tana bada dubu biyun tai gaba sabuda girki ta Dora aciki lokacin Kuma kanwarta ke bata larin abunda taji suna Fadi nan ta hau kanwar tata da fada tace meye naki na sauraren hirartasu konace Miki inason ji ne?

‘in inason ji dabakiganni a wurinba?

‘karki kara min irin haka kinganni nan banason rigima ato

‘Allah baki hakuri bari intafi gida

‘eh kigaishesu indai gulamace dason jawowa mutum rigima badaniba dauki naira dari kihau mashin

‘ngde

Datazo wucewa tacewa su maman ummi din sai ajinmanku tai waje abunta batareda tajira taji mezasucena dan dama tasan inbai musu sallama ta wucesu to yayarta zata Mata fadane shiyasa

*FACALA*

_matar wa da matar kani_

Writed by ~*maman sabon yaro*~

Shafi na uku

Yau aka wayi gari uwar mijin su babu lafiya an kaita clinic har ruwa akasa mata don haka bata dawo gidaba wannan dalilin yasa suketa shiri zasu je dubiya dayake clinic din babu nisa da kafa zasu je

Misalin karfe biyar suka shirya suka rankaya su duka acan suka tararda matan alhj auwalu duka biyun

‘ah maman fati ashe kuna nan Kuma fa sai da nai tunanin haka cewa kilan Kuna can muma wlh tun lokacin dasafen naso mufuto to sai Aysha tace kilanma bazaku kai sallar azahar ba zaku dawo

Maman abul ke wannan maganar sabuda tun asubahi aka kawo matar nan asibiti amma basuzo duba jikinta ba amatsayinsu na Wanda suka kwana gida daya sannan Kuma uwar mijinsu ce.

‘eh wlh bare Kuma ni daman na aza ko in habu yadawo ne zamuzo to shima dai tun safen ban ganshiba,

Aysha kefadin haka tana kame kame sai ita maman kalifa ce ta aje bakar leda akan Dan teburin dake gefen gadon tace ‘sannu mama ga malitina kisha,

Anan aysha tadan karasa gurin Maryam dake zaune a dayan gadon rugume da jaririnta (itace kanwar mijinsu data haihu akai suna) ‘mai jego ashe kinzo ya babyn

‘lafiya iyaka amsar tabawa ayshan kenan

Dakin cike yake don kuwa ya’yan ta Mata ukku dake aure kowacce tazo Kuma dayake jikin dasauki Kuma yamma ne lokacin ziyara ne shiyasa ba’a koreso ko ahanasu shigowa ba.

Saratu ita babbar yarta mace itace ta saka wasu kulolin abinci aleda tacewa maman kalifa gashi in zaku tafi kijeda kular abincinki mun gode naso in wanke anan to babu omo Kuma muna saran dazarar ruwan nan yakare zasu sallemeta zamu dawo gida.

‘bakomai anty saratu Allah yabata lafiya mun gode Allah don wlh kwanan asibiti sai dole bare clinic dinnan da sauro kadai ya isa yasa mara lafiya yaki warkewa koma yakara mishi ciwo

Maman mama baki ta tabe afaikace tana girgiza kai

‘to Allah yakara sauki kuzo muje gida don yamma tayi ni daman miya nayi nace innadawo sai in tuka tuwo akawo muku to Ashe bama kwana zakuyiba .. .

Maman abul ce tai wannan maganar maman ummi kuwa cewa tayi ai gwara ke ni saina koma zan hada duka biyun kumuje muyi harama

‘to ni munyida baban kalifa zai biyo mu koma gida tare

Budar bakin Aysha sai cewa tayi Allah muma yabamu abun hawan dai

Nan suka fita su uku maman abul sai Aysha sai maman ummi sukabar matan alhj auwalu da maman kalifa a asibitin

Kiran wayar uwar gidan alhj auwalu akayi akan cewa anzo za’a duba Kaya dayake tana saida gwanjina da takalma masu saukin kudi sai awayar takecewa ai suyi hakuri sai gobe yanzu bata nan … Saratu tace ‘ah ah maman fati jeki ba’a haka cinikinefa mukuma anan din kinga tama samu sauki sannan Kuma bawani Abu kikeyiba don haka jeki ba’a wasada sana’a..

‘to shikenan Allah Kara lafiya bari in sauri in karasa kafin nan in Fara kiransu ince sujirani gani nan kusa…. Allah Kara lafiya

Bayan fitarta yarage daga su biyar kenan yaranta uku sai amaryar alhj auwalu da maman kalifa suma ba’a jimaba jamilu auta kenan ya iso dayake ya girma shekarumshi ashirin da bakwai ya iso yabawa anty saratu kudi yace gashi kudin sallamar nizanje inyi sallah naga magriba ta gabato kilan kafin indawo ruwan yakarasa sai mu wuce gida tareda abokina muke Yana gyara parking awajene saimu koma amotarshi nan suma maman kalifa sukai musu sallama sukace zasu koma don baban kalifan ya kirata cewa yasamu faci ahanya bazai samu karasowa da wuriba.

‘kinsan daman imashirin in zamu wuce zan biyo ta gidanki wlh tsumi ne hadadde Wanda babu irinshi don dai nikam bantaba Shan tsumi irin wannan ba… Amaryar alhj auwalu ke ma maman kalifa wannan maganar ahanyar su ta komawa gida.

‘kai keko kinjiki haryafi irin Wanda nike dafawa kin mance da kanki kike santin tsumina…..

Hakane nakin yanada kyau sosai amma wannan dinnan kam ba magana kedai kijarabashi himmmmmm Zaki ban labari

A asibiti kuwa bayan su maman kalifa sun wuce sai anty saratu tace ‘wai himmm wlh matannan basuda mutunci ace Sam taya ace uwar mijina batada lafiya ankaita asibiti tun asuba wai banje dubata ba sai bayan la’asar sannan kuma dana tashi zuwa haka naje hannu na dukan cinya wlh shiyasa akace daka haifi gwamna gwara ka haifi matar gwamna

‘sosai ma kuwa ji lalacewa Wai a asibitin ma suna kokarin yadawa juna magana wai suma Allah yabasu abun hawan nan

‘baki ga maman ummi ita harda tabe bakiba .

‘nifa duk cikinsu gwaramin maman kalifa itace daine ta aiko abinci darana Kuma baban kalifa dasafe yakawo Mata shayi yanzuma da tazoda maltina guda biyu

‘kenifa har ita din wlh yo maltina ai ana baban kalifa dayake siyowa ne ta dauko haka abinci sai dai ace ita ta girka amma ai baban kalifan ne yasiyo kayan abincin

‘eh dukda hakan gwara ita su sauran suke cida kansu? Ina suma dukiansu babu wacca ta ke cida kanta amma ko ruwa sun kasa rikowa

Dai dai nan jamilu ya shigo yana ‘ruwan yakare ko?

‘Sauran kadan

‘Wai akan me kuke magana ne?

Akan matan nan mana baka gani ai tare muke dakai a asibitin saifa yamman nan sukazo ace kafdinsu suzo zikau dayake ba uwarsu bace shiyasa.

‘ah ah anty saratu karkiga laifinsu Yan uwanki zaki zaga basu ba ina su suka daure musu gindi da harsuke wannan iya shegen …

‘kumafa gaskiyarka ne jamilu wlh harsa laifinsu kalli baban ummi amatsayinsa na babba amma tunda ya zo misalin karfe takwas baikara dawowa ba baikuma Kira yaji yajikinta yakeba Amma in matarsa zata haihu haka yake isarmu kuma baya barin asibiti harsai ta haihu an sallameta.

‘Allah dai ya kyauta wlh ni shirgin matan nan shiyasa Sam bana shiga wlh Kun ganni nan ko abincinsu baci nikeba gwarama maman kalifa itama ba kullum ba don ni banson raini….

Haka suma su maman abul suna tafe suna tufka gulma fadi takeyi kujimin gulma ashe ta zagaye ta aika musu abinci kuma don munafurci harda tahowa da maltina wlh na dade banga makirar Mata irin zaituna ba (maman kalifa)

Maman ummi tace ‘ni abunda yafi bani haushi ace munzo wuri tare amma tawani zagaye wai mijinta zaizo su dawo gida tare harni zata gayawa miji lokacinda baban ummi keda mota wlh sai in shekara banje anguwa a kafa ba kaini ko makota amota ake kaini fa amma shine yanzu shine harni za’a kawowa kadifirin Wai za’azo daukarta mashin ne fa bama mota ba wannan in suka samu mota zamuga iko kenan

‘ni bawannan ba kujimin abunda ya isheni wai daga nace masu jego ya baby Wai lafiya sai kace nina sakawa mamansu ciwo

‘ke inagafa harda fushin bakije sunaba ne Allah kimata uziri

‘yoni harna mance ma dawani suna bare in tuna Wai banjeba

‘daman ni bawai na damuda zancen dangin miji bane don wlh komi kayi baka burgesu Kuma Kuna nan zakuji yadda anty saratu zata gwaleta ni shiyasa wlh duk mai rawar jiki da dangin miji sai dai in kalleshi kunsan dai nice farkon suruka agidan ko? To wlh haka dafarko farkon nan nike wanke kayan waina yamma nayi in zauna gyara kayan miya harda rana fa haka nike zama tsintar shinkafa kai ai wlh na bautu shiyasa ni wannan shisshigin da zaituna keyi bawani damuna yakeba don kuwa in dan su sota ne wlh bazasu taba son ta ba dazasu so wani agidannan wlh barin nice nida lokacinda aka auroni Maryam na yan’mata don hatta bilkisu shekaranta daya da aure lokacin anty saratu ce Kai ce zan iya cewa ta girmeni amma shine kalli yadda Maryam da bilkisun ke wani Shan qamshi

‘keko baroleba ita fa bikisu mijinta da abun hannunshi Amma Maryam fa duk bulace fa mun sani kawai dai kallon kowa nike

Aysha ke wannan maganar

Maman abul tace ‘wai ni Kam Kun lurada kayan da kejikin maman fati sabon kayane fa wlh matar nan na shiga Kaya kaji

‘Himmmm kin ma lurada kayan kenan itafa a sutura zata kare aikinta kenan dinke dinke ai teloli na cin kudinta

‘wai meye nawani damuwa da kayan matan nan wlh ni ko luradasu banyi ba mts da haka taja bakinta tai shiru

Sai Aysha ce tace ‘wai daman maman ummi baban ummi yariga alhaj auwalu aurene?

Eh sai da aka auroni da wata uku kafin a auro maman fati ammafa gini ya tsayayi donshi ya ce bazai zauna da uwarshi ba Amma kalli yanzu shine Dan gwal muda muka daure muke zaune da tsohuwar tasu mune bola karkatacciyar kukansu mai dadin hawa .

Har suka karasa gida suna zancen nan

Karfe tara dai dai su maman habu suka shigo gida alhamdulillah jikin dasauki don kuwa da kafarta ta shigo gida sai dai ahankali take takawa sannu sannu

Nan kowacce sai tururuwar zuwa sannu da zuwa sukeyi maman abul kecewa ai tun magriba Nike tunanin ko kilan sai gobene to nakira baban abul yake cemin ah ah yau din dai ne zaku dawo

Itama maman ummi sai cewa tayi eh ni ai bini bini kadan sai leka hanyar kofar gida sannu mama

Aysha ma ba’abarta abaya ba cewa tayi nifa tunda aka idarda sallar issha’e Nike tsaye bakin kofa inga shigowarsu ikon Allah sai gasu Allah yakara lafiya Amin

‘akoda muka dawo kowa tunanin mama yake shiyasa kuka mun zo

Duk wannan maganganun dasuke babu maman kalifa aciki don ita batama shigo ba kokarin awannan maganganun shine su nuna cewa ai sunfi maman kalifa son maman

Ana haka saiga fati yar alhj auwalu ta shigo da kular abinci kanwarta fadila na biyeda da ita kular miya sunyi sallama sunce gashi inji antynsu tace dukkansu suci ….

Takarasa gurin anty saratu ta sauke kular gamida zubewa nan kusada ita suna gaisheta

Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwan

Dai dai lokacin maman kalifa ta shigo da bokiti babba cike da ruwan zafi yanata turiri harta na cewa su maman ummi dasukayi dafifi su Dan matsa zata wuce haka ta wuce ciki da ruwan zafin kafin ta fito tacewa anty saratu ‘anty ga ruwan wanka ku taimaka mata tayi wanka zatafi jin dadin jikinta ….

‘to amma ai da anfara wanke bandakin ne abu tun jiya rabonshi da wanki…. Caraf maman ummi ta tashi ‘aiko hakane bari in wankoshi hata mike sai maman kalifa tace anty saratu ai na wanke bayin tun magriba harda dakin na share…. Tana fadin haka tayi waje dai dai kofar dakin saiga jamilu ya shigo nan ta ce wa jamilu bari in bawa kalifa abincinka yakawo maka

Dole anan saratu da bilkisu zasu kwana itako Maryam jego take mijin yazo duba maman daga nan ya dauketa zuwa gida .

Cikin dare ana hira tsakanin jamilu da anty saratu da bilkisu suke fadin yadda matan gidan suke dirama nan anty saratu tace kai Gaskiya wannan karon in garin Allah ya waye sai nayi magana wlh wannan iya shegen da matan nan keyi ya isheni da uwarsu ce haka zasuyi Koda yake tabakin naka ne wlh MAZAJENSU zanwa magana harda alhj auwalu su don isa ma ko lekowa baduyi ba sai wani abinci suka aiko to ce musu akai yunwa mukeji? Bazata sabu ba wlh kaf dinsu sai kowacce sai ranta yabaci wlh

Maman ce tace ‘kinga saratu banason rigima don Allah kibarsu suje kowa yayi nagari kansa dadin abun kowacce ta haifa ai zatagani ….

‘himmmm iyaka abunda anty saratu tace kenan kowa ma shiru yayi don kuwa tabbas sunsan saifa tayi magana

Anty saratu itake bin alhaji auwalu sannan tanada zafi but wani lokacin tanada sanyi amma fa zafin yafi yawa Kuma batada wasa bata kyale kowa ba har alhj auwalu din …………

~maman sabon yaro~

FACALA

[*FACALA*

_matar wa da matar kani_

Writed by ~*maman sabon yaro*~

Shafi na hudu

‘Inawa kowa barkada safiya ..

Anty saratu ce ta tara Yan uwanta maza adakin mahaifiyar su ‘dafarko dai kunsan wannan Kiran danike muku ba rokon ku kudi zanyi ba ko neman gafara nakiraku ne don in ji shin dasaninku matayenku ke tsula tsiyataku iri iri agidannan itadai umma Kuna sane ba fada takeba ansha fadamin cewa suna Mata rashin kunya dukda nasan daman ba kunya ne dasuba bacin dalilin rashin lafiyar nan bazan yarda ba sai gashi Kiri Kiri agabana sun wulakanta mahaifiyar mu agabana jiya bawacce ta je dubota a asibiti sai yamma sannan da yunwa muka wuni sai bayan dawowarmu ne ba kunya ba tsoron Allah sukazo da kinibibinsu suna mana kame kame suna borin kunya to wlh bazata sabuda ku gakunan rid’a rid’a jere Kun girma harkun aje iyali Amma mahaifiyar ku. Bata hutaba daga cikinta sai cikinta auta amma kullum da asussuban fari ta fita tana gidin murhu tana hura wutan waina haba haba yaushene zata huta kenan? Ko naira dari dari ne kuke bata AKULLUM zai isheta cin abinci don haka nataraku ne yau ayi wacce za’a ayi tsakanin mu don kuwa yanzu hawan jini likita yace tanashi sai dai yace in akabi ka’ida aka bata kulawa zata samu lafiya harta warke gaba daya yanzu hawan jinin mataki na farko yake.

‘nidai gaskiya bansan irin zaman da su habu da matayensu keyi anan gidan ba amma dai koma mene kiyi hakuri umma kigafarcemu. Alhj auwalu ne yayi furucin

Jamilu ne yace ‘ni dai aganina yadace bayan an kammala taron nan suma matan akirasu aja musu kunne don wlh karsu na tadawa uwata hankali ehe tunda dai bazaman jiransu takeba bare suce suna dawainiya da ita.

‘Hakane jamilu cewar anty saratu

Hakako akayi hatta gidan alhj auwalu Saida aka kirasu matayen nan dasuke gidan ma kowacce tazo anty saratu dince tayi magana tace ‘inafatan kowacce tashinshino dalilin kiranta inma bata shinshino ba to dalilin Kiran shine kowacce daga yau karta kara niman fitina da son tashin hankali agidannan wlh don bazai yiwuba kullum kukenan kananun fitintinu da gulmace gulmace,

Sai anan ne baban ummi yasa baki yace ‘sannan magana ta gaba shine daga yau umma ta dena girki agidannan kowacce intayi abinci zatasa Mata kuma likita yahanata cin gishiri sabuda haka akiyaye.

Ko akwai mai magana acikin ku? Kowa tayi shiru sai maman kalifa ce tace nidai abunda zance shine umma ki gafarcemu kuma kiyi hakuri Allah huci zuciyarki ubangiji ya Kara lafiya daga haka tamike ta fita

Kimanin sati biyu da kafa wannan sharadin nacewa umma bazatayi girki ba Kuma atsawon wannan lokacin suna zuba abincin su Kai mata har gasan kai abincin akeyi kowacce rigen kaiwa take don burgewa da son nuna kalan abincin data girka.

Yau da gobe sai maman ummi ta fara dangarewa in tasa rana bazatasa abincin yamma ba da baban ummi yafara ganewa don saida tayi tsayin kwana biyar bata sa mata abinci sau biyu arana kafin ya lura sai ya tambayi dalili nan caraf tace Wai abincin yanayin yawa ne kwanuka biyar sunyi yawa shiyasa ma suka raba in mutum uku suka bayar da Rana mutum biyu sai su bayar da dare

Bai wani damuba yabar maganan ahaka maman abul itama tadauki sahu sai taki sa abincin inko tasa to dan kadan zatasa itama Aysha tabi sahu sai ya Zama daga maman kalifa sai gidan alhj auwalu ne kawai ke bawa umma abinci sau biyu arana ita maman kalifa sau ukune ma Kam take bata don tana Sanya Mata shayi dasafe in dumame sukaci haka take saka wa umma

Yau maman kalifa tafara sana’ar awara but iyakar banki kawai ake kaimata awarar a take away takesawa guda goma ta yayyanka kabeji da albasa da cocumber 500 take away daya

Washegari sai aka samu karin mutane biyu suma sunaso sai Kuma yazama zasuje gaisuwan mutuwa kanin mijin anty saratu yarasu sai maman kalifa tace suyi gaba zata karasa aikin awaranta tazo daga baya ahanyarsu ta tafiya ne maman abul tace ‘wai ni kunga wani sabon abu? A ace duk sanar da matar nan keyi bai ishetaba sai ta hada da wani awara kuji min masifa nan suka kafa shaftar ta har suka isa gidan gaisuwar sun so sufadi wani abun gameda rashin zuwan maman abul sai kuma suka tuna anty saratu bata daukar haka tana iya zuwa gidan ta titsiyesu

Wasa wasa sai awara ta karbi maman kalifa nan kishi yafara turnuke sauran saiko maman abul tafara yin warar amma wata yarinyar makwafciyarsu ke fita dashi tana Saida Mata sai ita ma Aysha tafara Amma ita kanwarta ce kezuwa ta daukar Mata tana kaiwa anguwarsu itako maman ummi zobo tafara da pure water

Ita maman kalifa batace komiba sodayawa sai anshigo ance abada zobo sai maman ummi tayi zaraf tace na nawa zo nan itadai maman kalifa batace komiba ana haka sai itama maman abul tafara saka nan gida ya kacame da sana’a ko maman kalifa tayi zobon baya karewa haryayi tsami ta zubar sabuda ko anzo siya sai maman ummi tabi yaro tana Kai zonan kokuma ta tura ummi kofar gidan duk yaronda zai shigo sai ta tareshi in zobo yazo siya ko pure water sai ta karbi kudin takaiwa mamanta itako maman kalifa yaronta karamine bai girma ba Kiri Kiri sana’ar zobon da tun satin farko datake gidan tafarayi yazo ya gagareta

Sai ya zama iyaka awarar takeyi da kunun ayah ana Kai Mata banki to yauda gobe in bankin basu siya dayawa ba yana zama kwantai saita fara rage hannu don haka samunta yaja baya ganin haka taiwa yayanta magana daya taimaka yasamo Mata koyarwa a makarantar abokinshi tunda tayi sakandare ahaka da kyar da sidin goshi donma abokinshi ne ya dauketa zatana kulada baby class

Sha biyu take dawowa zuwa wannan lokacin anfara rigima tsakanin maman abul da Aysha akan awaran don kuwa yanzu kowacce batada Mai fitar Mata dashi iyaka azo gida asiya to dazarar anzo din sai ayita rigen rigen karbe kudin ahannun yaro ga maman abul duk wannan kyalesun da maman kalifa tayi bai Mata ba sai yamma si tsiri wannan zaman dandalin dasukeyi suna yada habaici

Yau maman kalifa ta biya kasuwa ta siyo kashin dari da hamsin naman dari biyu sai cefanenta na dari da hamsin duka dai dari biyar takashe tadawo gida karfe hudu kowacce ta fito zaman kofar dakin umma kamar yadda sukeyi maman abul ce tafara cewa ‘kai komin bakincin tanda sai munci waina sana’ar awara muna nan munayi ba gudu bajada baya ehe .

Caraf maman ummi tace to fa Mai zaisa kibari ai dai baki hana kowa yayi ba ko?

Maman kalifa najin haka tagane cewa da ita suke daman tana zaune afalonta ne sai ta tunoda cefanenta datayi darana tako tashi ta wanke namanta ta dora a tukunya ta yanka albasa isasshe nan da nan kamshi ya wade gidan sai ka dauka wani naman rago ake suya jamilu yashigo gidan yana fadin ‘Kai wannan qamshi haka lallai yau zamuci dabge nan maman kalifa tace ‘aikuwa dai gashi nan don tafito wanke alayyaho ne lokacin sai jamilu yace Kai miyar alayyahon ke zabga wannan qamshin ? Kodayake daman tunda naji qamshin nan nasan kece ‘kai baba jamilu bakada dama lallai kace matarka akwai aiki agabanta tafadi hakan cikin raha sai yace ‘to ni ina zan zauna da matar da bata iya girki ba ai saima naji kwarewar yarinya a fagen girki kafin inkai kudin aurena gidansu …. ‘Allah yazaba maka nagari to yace ‘amin daga haka ya shige dakin umma

*FACALA*

_matar wa da matar kani_

Writed by: ~maman sabon yaroooo~

Pg 1

Bismillahirrahmanirarrahem

‘Gaskiya Samira kina hakuri da wannan makwafciyar taki ni bazan iya zamada irinsu ba kam.

‘ikon Allah kinshigo gida Babu sallama sai korafi kike??

‘ai kaji ga irinta nan tun daga kofar gida nike kwada sallama bakijiba sabuda wannan karar da aka kure gidan nan dashi …

‘ni shigo daga ciki in Kuma korafin zaki tsaya yi awaje to

‘ya kinzo min da kayan ?

‘Nazo dasu amma gaskiya Kuna dawowa kiba abul yakawo min agoben sabuda Nima lace dinnan nikeson sawa bikin makwaftan mu.

“To shikenan muna dawowa zan Aiko Miki dashi

‘kai !! kai !! kai abul me ummi tayi maka ka mareta Kai azzalumin inane? To wlh karka Kara inba haka ba zan kakkaryaka agidan nan saina barka akwance..

Can daga cikin daki maman abul din kefadin Aiko kice za’ayi karye karye don kuwa wlh bawacca ta isa ta nakasa mun yaro abarni da jidali inaaa

Nan maman ummi tace oky lallai ma yanzu haka zakice wato kin daure mishi ?

‘Wani irin na daure mishi? Inaji kina fadin Zaki kakkarya yaro badole in magana ba?

‘To shikenan don Allah abul yakara dokar ummi yagani wlh kinji na rantse

‘sai Kuma kiyi,

Duk wannan cecekuncen da akeyi tsakanin maman abul da maman ummi uwar mijinsu najinsu tana gyara shinkafar yin wainata don daman wainar siyarwa takeyi amma tanajinsu kamar ba surukanta ba

Itako maman kalifa nacan ta kure tv adakinta sai wakar jaruma ke tashi tana bi

Aysha ko na can dakinta dayake kowacce nada kitchen adakinta

Su shiddane matan ya’yanta hudu daga ciki suna zaune ne anan cikin gidan Kuma kowacce mijinta daban babban wansu alhaji auwalu shine kawai yake zaune agidanshi kusa suke Amma matan shi biyu ne shi.

Haka suke zaune sai kanin mijinsu da bai aure ba saurayi akwai Mata guda uku suna gidanjen aurensu

Mijin maman ummi yanada shagon Saida kayan provision awaje

Daya daga cikin kannen mijin nasu ne ta haihu zasu suna shine maman abul ta ari lace din kawarta.

Washe gari zasu tafi gidan sunan dasafe suna shiryawa

‘mamammu kinga naje dakin maman abul ta koroni kuma mama bakiga ba tasa sabon leshi …

Uwar mi yakaiki dakinsu? Sabuda ke jakace inace jiya jiyannan ya mareki uwarshi tabi bayanshi Amma sabuda bakida zuciya shine yau Kika koma dakinsu……

‘Haba saude wani irin mugun alkaba’i kike jifar yarinyarki dashi ne haka, akan shirmen yara sai zagin yarinya kike …

Kawarta madina ce data biyi mata zasu gidan sunan tare ke Mata wannan maganar

‘madina bazaki gane bane Kiri kiri fa jiya yaron nan ya mareta amma babu tsoron Allah maimakon ta mishi fada sai ma Fadi take Wai karwacca ta taba mata da.

‘wani irin wulakanci ne wannan da iskanci Zaki barwa mutane buta babu ruwa aciki? Sakarya kawai batasan komiba sai shirme arayuwarta…

Mijin aysha ne kemata wannan tujarar don daman dabi’arsa kenan ko agaban waye kuwa inta mishi laifi zai ci Mata mutunci ba ruwanshi.

Itama ko batai kwaron bakiba tace haba habu taya zaka rikamin irin wannan zagin Yara ne suka zubarda ruwan Koko laifinane su yakamata kayiwa magana ai baniba haka kurum zakazo kana min ihu akaina ..

‘Wato ke bakida kunya ina fadi kina fadi ko sabuda kin rainani nan rigima ta kaceme suko mutan gidan ko ajikinsu inda sabo sun saba

Karshe gidan sunan da Aysha batajeba kenan tunda daman kanwarsa ce to yazo ya zageta acewarta.

Can gidan sunan kuwa bayan sun isa sai maijego ke tambayar ina Aysha?

Caraf maman abun ta karbe tace aiko bazata samu damar zuwaba suna can suna zuba fada itada habu kinsan kuwa batazuwa ko Ina yau indai adangin habune…

Maman abul haka take bada labari tiryan tiryan madina tace to adaibi ahankali fadan miji da matane saiku koma gida kigansu sun dinke ato

‘oho dai bawani dinkewa dazasuyi mumfa San komi indai ayshane ko girki tabaryi yau,

‘lallaima aiko tana ruwa azamanin nan daman akwai sauran mace Mai irin wannan halin?? Don kunyi rigima da miji har taki girki?

‘hu’um indai ayshane ta wuce nan bama girki ba har magana bazasiyiba

‘Kai maman abul daki daya kuke kwana harda zakice ko magana bazasuyiba heeeeee aka kwashe da dariya nan har aka tashi sunan caftar ayshane.

Washe gari dasafe gidan babu wani walwala don dama ayshace kusan shugaba agidan to ko bude dakinta batai ba yaranma da babansu suketa buruntu har suka gama shiryawa zuwa makaranta .

Sai shabiyu narana ta fito ta shima sakone wani yaro yakawo mata da wata kawarta ta bayar akawo Mata

Harzuwa yamma misalin karfe biyar kawarta dija ta kawo Mata ziyara suka shige daki,

Dijar ke tuhumarta cewa ke Aysha meke faruwane jiya kikazama abun nishadi agidan suna?

‘banganeba, jiya ai banje sunan ba

‘eh inasane bakijeba amma anje Miki donkuwa duk abunda kikasan yafaru haka aka zayyaneshi agidan sunan bama anan aka tsayaba don kuwa harda Karin magi da gishiri Koda yake banace magi da gishiri ba gaskiya aka fadi tunda gashi nan alamu sun nuna baki komiba agidan nan ba daman ance bazakuyi magana da habu ba harna tsawon wasu kwanaki …

‘Tabdijam tirkashi wace algungumar ce ko ince wacce munafukarce tace haka Kai tsaya ma basai nayi dogon bincike ba gidannan cike yake da annamimai da munafukai Kuma tabbas bazai yiwuba ai bawacce bata fada da mijinta kaf gidannan sai maman kalifa….

saurin katseta dija tayi tace har itama tana fadan kawai ta ita takunta ne yasa bakwa ganewa to wlh in baki canjaba kece akasa tun wuri kinemi hanyar hukunta miji bawai gaba da dauke wuta ba,

‘To dija wlh zamada habu bakowacce mace zata iyaba akan buta fa ko ince akan ruwa abuta fa ya dingamin tijara agidannan fisabilillahi meye ruwa abuta?

‘aiko bari kiji Kinga wlh babu abu mafi haushi da tunzura miji irin yazo ya dauki buta yaji kwambar babu ruwa aciki to wlh harzuka maza yake Kuma Yana fadi kina fadi shikesa kiji anyi abunda za’azo ana danasani do kuwa sakin aure yafi afkuka in Kika tsaya Kuna tanki tanka da miji iya gaskirki ki daure kiyi shiru kita fadin innalillahi WA’INNA ILAIHIRRAJU’UN azuciyarki inhar bazaki iya daurewa kice yi hakuri ba to ki maimaitawa azuciyarki kitashi ki shige daki daga nan saiki nemi hanyar hukuntashi cikin sanyi in Kuna on top dinnan kice yadena yi Miki fada atsakar gida yabari in Kuna ku biyune yayi Miki

‘himm banki takiba dija wlh taurin Kaine da habu ba yadda banyi dashi ga shehiyar bakar zuciya kamar tsohon kuturu

‘to ke ki Kara kulawa gaskiya ni bazan jure ya madidi dakeba ne kalli maman ummi ta girmeki fa maimakon amatsayin ta na matar wan miji ta kwaba miji …..

‘wa ce Allah kin tuba wannan babban kwabone …….

Ya kukaji

*FACALA*

_matar wa da matar kani_

Writed by ~*maman sabon yaro*~

Shafi na biyu

Yau jumma’a tun sassafe maman abul ta fitoda wanki ta jibge bakin kofar dakinta, tashige cikin dakin tana sharowa, maman ummi itama saita fitoda nata wankin ta aika Yara su siyo Mata sabulu kafin minti talatin ta cika igiyar gidan da kayan ta sai karfe takwas maman abul ta fito da Shirin yanzu zata fara nata wankin

‘kutumesin can lallaima to ai igiyar nan baban abul yakawo ta gidan don haka cire kayanki tunda dai abun y’ar hakane ai kina kallo na fitoda wankin zanyi sai Kuma kafin in gama shara da mofin kizo kiwani cika igiyar da shanya bazata sabuba…

‘Kinga Samira banison rashin kunya da rashin ganin ta ido niba tsaranki bane dazaki kalleni kina wannan surutan

Dai dai nan Aysha ta leko tace ‘hehe dadina da gobe saurun zuwa nan kukaje gidan sunan ba irin sharrinda bakumin ba gashi an ganku arana

‘Kinemi Wanda ya Miki gulma can yarinya kinsan dai ni ba sa’ar yinki bace maman ummi ke wannan maganar …

‘ai nan kikafi auki Abu kadan kice ke babbace bakison raini to wlh ni babu ruwana da girmanki ko shekarunki in tsoho baiji kunyar hawa jakiba jaki bazaiji kunyar kada shiba ehe.

Duk wannan abun dasuke maman kalifa na cikin daki ta kure tv ado gwanja na waka ita Kuma kan injin sakarta yau riguna uku ta keson yi donma ta tsaya yin abun Kari

Haka maman abul ta stinke igiyar shanyar nan maman ummi ta zaburo zata Kai Mata duka mijinta ya hana yakuma ce karta Kara Koda magana akai

Kai tsaye nan waje yaje yacewa kaninsa baban abul din kenan dayajawa matarsa kunne don kuwa inba hakaba zaibar maman ummi ta fasa Mata baki..

Baban abul bamai magana bane sammm don haka iyaka yace mishi to kayi hakuri baima tambayi ko meyafaruba

Har yamma tayi daman al’adar gidan ne kowacce da la’asar takeyin wankanta Mai anguwa taje Mai zaman gida nan zasuzo kofar dakin uwar mijin nasu akafa shafta

Ranar banda maman abul amasu zaman kofar dakin sabuda wannan yar tanki tankan da akasamu tsakaninta da maman ummi akan igiyar shanya haka Kuma maganar da aysha tayi na cewa anyi munafurcinta agidan suna don haka bazata fito ba yau

Maman kalifa Kuma ta fito Amma a kofar dakinta ta tsaya tana dura zobo a gora don tana Saida zobo da pure wata kanwarta sadiya tazo tana tayata.

‘assalamu alaikum

Matar babban yayansu dake makwaftaka dasu ce ta shigo gidan amaryar kenan lawisa nan tasamu guri tazauna ana tattaunawa ba’a dau lokaciba maman kalifa ta gama dura zobonta kanwarta takwashi botikan taje bakin famfo wankewa ita Kuma tashiga ciki don jera abunta a firij

Nan firar tazama daga Aysha sai maman ummin sai lawisa sunata kus kus don basa daga murya bare kaji me sukecewa

Kanwar maman kaliface dayake famfon na kusada su ne tajiyo maman ummi da lawisa na cewa ke aysha ai maman abul ce takai maganar rigimarku keda habu gidan sunan sai maman ummi kecewa bana gaya Miki cewa bani bace dazu shine harkike son sauke fushin ki akaina alhalin ni ma kinsan samira ba kyaleni takeyiba himmmm

‘dama an gayamun ai indai nice wlh koma wacece dai dai nikeda ita ehe mutum yajida halin mammakon da mijinshi keyi ehe ace kana zauneda miji ga yara amma komi sai dai ayi cikin mitsiltsila ba wadata alhalin akwai yadda za’ayi

‘nikam Kinga shiyasa bana kula koma menene tunda wlh ko yau dasafen nan baban su Amira dubu uku yabani kudin ankon bikin gidanmu.

Lawisa ke fadin haka sai maman ummi tace Kai bikin kanwarki haryazo dinne??

‘eh sauran sati hudu gashi Kuma baku kawo kudin ankon ba ananne ta daga murya tace maman kalifa sauran sati hudu nefa bikin gidanmu Wanda nabaku kyallen ankon nan tun watan daya wuce …

Sai anan maman kalifa din tafito tana cewa ‘ikon Allah har abun ya matso haka nawama kikace

‘dubu uku ne

Daki ta koma tafitodo dubu biyu tace ‘gashi in an kawo zan cika dubu dayan.. Allah Sanya alkhairi

‘amin aike daman bani shilafarki wlh nasan zaki riga kowa badawa daman ..

Ita dai tana bada dubu biyun tai gaba sabuda girki ta Dora aciki lokacin Kuma kanwarta ke bata larin abunda taji suna Fadi nan ta hau kanwar tata da fada tace meye naki na sauraren hirartasu konace Miki inason ji ne?

‘in inason ji dabakiganni a wurinba?

‘karki kara min irin haka kinganni nan banason rigima ato

‘Allah baki hakuri bari intafi gida

‘eh kigaishesu indai gulamace dason jawowa mutum rigima badaniba dauki naira dari kihau mashin

‘ngde

Datazo wucewa tacewa su maman ummi din sai ajinmanku tai waje abunta batareda tajira taji mezasucena dan dama tasan inbai musu sallama ta wucesu to yayarta zata Mata fadane shiyasa

_matar wa da matar kani_

Writed by ~*maman sabon yaro*~

Shafi na uku

Yau aka wayi gari uwar mijin su babu lafiya an kaita clinic har ruwa akasa mata don haka bata dawo gidaba wannan dalilin yasa suketa shiri zasu je dubiya dayake clinic din babu nisa da kafa zasu je

Misalin karfe biyar suka shirya suka rankaya su duka acan suka tararda matan alhj auwalu duka biyun

‘ah maman fati ashe kuna nan Kuma fa sai da nai tunanin haka cewa kilan Kuna can muma wlh tun lokacin dasafen naso mufuto to sai Aysha tace kilanma bazaku kai sallar azahar ba zaku dawo

Maman abul ke wannan maganar sabuda tun asubahi aka kawo matar nan asibiti amma basuzo duba jikinta ba amatsayinsu na Wanda suka kwana gida daya sannan Kuma uwar mijinsu ce.

‘eh wlh bare Kuma ni daman na aza ko in habu yadawo ne zamuzo to shima dai tun safen ban ganshiba,

Aysha kefadin haka tana kame kame sai ita maman kalifa ce ta aje bakar leda akan Dan teburin dake gefen gadon tace ‘sannu mama ga malitina kisha,

Anan aysha tadan karasa gurin Maryam dake zaune a dayan gadon rugume da jaririnta (itace kanwar mijinsu data haihu akai suna) ‘mai jego ashe kinzo ya babyn

‘lafiya iyaka amsar tabawa ayshan kenan

Dakin cike yake don kuwa ya’yan ta Mata ukku dake aure kowacce tazo Kuma dayake jikin dasauki Kuma yamma ne lokacin ziyara ne shiyasa ba’a koreso ko ahanasu shigowa ba.

Saratu ita babbar yarta mace itace ta saka wasu kulolin abinci aleda tacewa maman kalifa gashi in zaku tafi kijeda kular abincinki mun gode naso in wanke anan to babu omo Kuma muna saran dazarar ruwan nan yakare zasu sallemeta zamu dawo gida.

‘bakomai anty saratu Allah yabata lafiya mun gode Allah don wlh kwanan asibiti sai dole bare clinic dinnan da sauro kadai ya isa yasa mara lafiya yaki warkewa koma yakara mishi ciwo

Maman mama baki ta tabe afaikace tana girgiza kai

‘to Allah yakara sauki kuzo muje gida don yamma tayi ni daman miya nayi nace innadawo sai in tuka tuwo akawo muku to Ashe bama kwana zakuyiba .. .

Maman abul ce tai wannan maganar maman ummi kuwa cewa tayi ai gwara ke ni saina koma zan hada duka biyun kumuje muyi harama

‘to ni munyida baban kalifa zai biyo mu koma gida tare

Budar bakin Aysha sai cewa tayi Allah muma yabamu abun hawan dai

Nan suka fita su uku maman abul sai Aysha sai maman ummi sukabar matan alhj auwalu da maman kalifa a asibitin

Kiran wayar uwar gidan alhj auwalu akayi akan cewa anzo za’a duba Kaya dayake tana saida gwanjina da takalma masu saukin kudi sai awayar takecewa ai suyi hakuri sai gobe yanzu bata nan … Saratu tace ‘ah ah maman fati jeki ba’a haka cinikinefa mukuma anan din kinga tama samu sauki sannan Kuma bawani Abu kikeyiba don haka jeki ba’a wasada sana’a..

‘to shikenan Allah Kara lafiya bari in sauri in karasa kafin nan in Fara kiransu ince sujirani gani nan kusa…. Allah Kara lafiya

Bayan fitarta yarage daga su biyar kenan yaranta uku sai amaryar alhj auwalu da maman kalifa suma ba’a jimaba jamilu auta kenan ya iso dayake ya girma shekarumshi ashirin da bakwai ya iso yabawa anty saratu kudi yace gashi kudin sallamar nizanje inyi sallah naga magriba ta gabato kilan kafin indawo ruwan yakarasa sai mu wuce gida tareda abokina muke Yana gyara parking awajene saimu koma amotarshi nan suma maman kalifa sukai musu sallama sukace zasu koma don baban kalifan ya kirata cewa yasamu faci ahanya bazai samu karasowa da wuriba.

‘kinsan daman imashirin in zamu wuce zan biyo ta gidanki wlh tsumi ne hadadde Wanda babu irinshi don dai nikam bantaba Shan tsumi irin wannan ba… Amaryar alhj auwalu ke ma maman kalifa wannan maganar ahanyar su ta komawa gida.

‘kai keko kinjiki haryafi irin Wanda nike dafawa kin mance da kanki kike santin tsumina…..

Hakane nakin yanada kyau sosai amma wannan dinnan kam ba magana kedai kijarabashi himmmmmm Zaki ban labari

A asibiti kuwa bayan su maman kalifa sun wuce sai anty saratu tace ‘wai himmm wlh matannan basuda mutunci ace Sam taya ace uwar mijina batada lafiya ankaita asibiti tun asuba wai banje dubata ba sai bayan la’asar sannan kuma dana tashi zuwa haka naje hannu na dukan cinya wlh shiyasa akace daka haifi gwamna gwara ka haifi matar gwamna

‘sosai ma kuwa ji lalacewa Wai a asibitin ma suna kokarin yadawa juna magana wai suma Allah yabasu abun hawan nan

‘baki ga maman ummi ita harda tabe bakiba .

‘nifa duk cikinsu gwaramin maman kalifa itace daine ta aiko abinci darana Kuma baban kalifa dasafe yakawo Mata shayi yanzuma da tazoda maltina guda biyu

‘kenifa har ita din wlh yo maltina ai ana baban kalifa dayake siyowa ne ta dauko haka abinci sai dai ace ita ta girka amma ai baban kalifan ne yasiyo kayan abincin

‘eh dukda hakan gwara ita su sauran suke cida kansu? Ina suma dukiansu babu wacca ta ke cida kanta amma ko ruwa sun kasa rikowa

Dai dai nan jamilu ya shigo yana ‘ruwan yakare ko?

‘Sauran kadan

‘Wai akan me kuke magana ne?

Akan matan nan mana baka gani ai tare muke dakai a asibitin saifa yamman nan sukazo ace kafdinsu suzo zikau dayake ba uwarsu bace shiyasa.

‘ah ah anty saratu karkiga laifinsu Yan uwanki zaki zaga basu ba ina su suka daure musu gindi da harsuke wannan iya shegen …

‘kumafa gaskiyarka ne jamilu wlh harsa laifinsu kalli baban ummi amatsayinsa na babba amma tunda ya zo misalin karfe takwas baikara dawowa ba baikuma Kira yaji yajikinta yakeba Amma in matarsa zata haihu haka yake isarmu kuma baya barin asibiti harsai ta haihu an sallameta.

‘Allah dai ya kyauta wlh ni shirgin matan nan shiyasa Sam bana shiga wlh Kun ganni nan ko abincinsu baci nikeba gwarama maman kalifa itama ba kullum ba don ni banson raini….

Haka suma su maman abul suna tafe suna tufka gulma fadi takeyi kujimin gulma ashe ta zagaye ta aika musu abinci kuma don munafurci harda tahowa da maltina wlh na dade banga makirar Mata irin zaituna ba (maman kalifa)

Maman ummi tace ‘ni abunda yafi bani haushi ace munzo wuri tare amma tawani zagaye wai mijinta zaizo su dawo gida tare harni zata gayawa miji lokacinda baban ummi keda mota wlh sai in shekara banje anguwa a kafa ba kaini ko makota amota ake kaini fa amma shine yanzu shine harni za’a kawowa kadifirin Wai za’azo daukarta mashin ne fa bama mota ba wannan in suka samu mota zamuga iko kenan

‘ni bawannan ba kujimin abunda ya isheni wai daga nace masu jego ya baby Wai lafiya sai kace nina sakawa mamansu ciwo

‘ke inagafa harda fushin bakije sunaba ne Allah kimata uziri

‘yoni harna mance ma dawani suna bare in tuna Wai banjeba

‘daman ni bawai na damuda zancen dangin miji bane don wlh komi kayi baka burgesu Kuma Kuna nan zakuji yadda anty saratu zata gwaleta ni shiyasa wlh duk mai rawar jiki da dangin miji sai dai in kalleshi kunsan dai nice farkon suruka agidan ko? To wlh haka dafarko farkon nan nike wanke kayan waina yamma nayi in zauna gyara kayan miya harda rana fa haka nike zama tsintar shinkafa kai ai wlh na bautu shiyasa ni wannan shisshigin da zaituna keyi bawani damuna yakeba don kuwa in dan su sota ne wlh bazasu taba son ta ba dazasu so wani agidannan wlh barin nice nida lokacinda aka auroni Maryam na yan’mata don hatta bilkisu shekaranta daya da aure lokacin anty saratu ce Kai ce zan iya cewa ta girmeni amma shine kalli yadda Maryam da bilkisun ke wani Shan qamshi

‘keko baroleba ita fa bikisu mijinta da abun hannunshi Amma Maryam fa duk bulace fa mun sani kawai dai kallon kowa nike

Aysha ke wannan maganar

Maman abul tace ‘wai ni Kam Kun lurada kayan da kejikin maman fati sabon kayane fa wlh matar nan na shiga Kaya kaji

‘Himmmm kin ma lurada kayan kenan itafa a sutura zata kare aikinta kenan dinke dinke ai teloli na cin kudinta

‘wai meye nawani damuwa da kayan matan nan wlh ni ko luradasu banyi ba mts da haka taja bakinta tai shiru

Sai Aysha ce tace ‘wai daman maman ummi baban ummi yariga alhaj auwalu aurene?

Eh sai da aka auroni da wata uku kafin a auro maman fati ammafa gini ya tsayayi donshi ya ce bazai zauna da uwarshi ba Amma kalli yanzu shine Dan gwal muda muka daure muke zaune da tsohuwar tasu mune bola karkatacciyar kukansu mai dadin hawa .

Har suka karasa gida suna zancen nan

Karfe tara dai dai su maman habu suka shigo gida alhamdulillah jikin dasauki don kuwa da kafarta ta shigo gida sai dai ahankali take takawa sannu sannu

Nan kowacce sai tururuwar zuwa sannu da zuwa sukeyi maman abul kecewa ai tun magriba Nike tunanin ko kilan sai gobene to nakira baban abul yake cemin ah ah yau din dai ne zaku dawo

Itama maman ummi sai cewa tayi eh ni ai bini bini kadan sai leka hanyar kofar gida sannu mama

Aysha ma ba’abarta abaya ba cewa tayi nifa tunda aka idarda sallar issha’e Nike tsaye bakin kofa inga shigowarsu ikon Allah sai gasu Allah yakara lafiya Amin

‘akoda muka dawo kowa tunanin mama yake shiyasa kuka mun zo

Duk wannan maganganun dasuke babu maman kalifa aciki don ita batama shigo ba kokarin awannan maganganun shine su nuna cewa ai sunfi maman kalifa son maman

Ana haka saiga fati yar alhj auwalu ta shigo da kular abinci kanwarta fadila na biyeda da ita kular miya sunyi sallama sunce gashi inji antynsu tace dukkansu suci ….

Takarasa gurin anty saratu ta sauke kular gamida zubewa nan kusada ita suna gaisheta

Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwan

Dai dai lokacin maman kalifa ta shigo da bokiti babba cike da ruwan zafi yanata turiri harta na cewa su maman ummi dasukayi dafifi su Dan matsa zata wuce haka ta wuce ciki da ruwan zafin kafin ta fito tacewa anty saratu ‘anty ga ruwan wanka ku taimaka mata tayi wanka zatafi jin dadin jikinta ….

‘to amma ai da anfara wanke bandakin ne abu tun jiya rabonshi da wanki…. Caraf maman ummi ta tashi ‘aiko hakane bari in wankoshi hata mike sai maman kalifa tace anty saratu ai na wanke bayin tun magriba harda dakin na share…. Tana fadin haka tayi waje dai dai kofar dakin saiga jamilu ya shigo nan ta ce wa jamilu bari in bawa kalifa abincinka yakawo maka

Dole anan saratu da bilkisu zasu kwana itako Maryam jego take mijin yazo duba maman daga nan ya dauketa zuwa gida .

Cikin dare ana hira tsakanin jamilu da anty saratu da bilkisu suke fadin yadda matan gidan suke dirama nan anty saratu tace kai Gaskiya wannan karon in garin Allah ya waye sai nayi magana wlh wannan iya shegen da matan nan keyi ya isheni da uwarsu ce haka zasuyi Koda yake tabakin naka ne wlh MAZAJENSU zanwa magana harda alhj auwalu su don isa ma ko lekowa baduyi ba sai wani abinci suka aiko to ce musu akai yunwa mukeji? Bazata sabu ba wlh kaf dinsu sai kowacce sai ranta yabaci wlh

Maman ce tace ‘kinga saratu banason rigima don Allah kibarsu suje kowa yayi nagari kansa dadin abun kowacce ta haifa ai zatagani ….

‘himmmm iyaka abunda anty saratu tace kenan kowa ma shiru yayi don kuwa tabbas sunsan saifa tayi magana

Anty saratu itake bin alhaji auwalu sannan tanada zafi but wani lokacin tanada sanyi amma fa zafin yafi yawa Kuma batada wasa bata kyale kowa ba har alhj auwalu din …………

~maman sabon yaro~

FACALA

_matar wa da matar kani_

Writed by ~*maman sabon yaro*~

Shafi na hudu

‘Inawa kowa barkada safiya ..

Anty saratu ce ta tara Yan uwanta maza adakin mahaifiyar su ‘dafarko dai kunsan wannan Kiran danike muku ba rokon ku kudi zanyi ba ko neman gafara nakiraku ne don in ji shin dasaninku matayenku ke tsula tsiyataku iri iri agidannan itadai umma Kuna sane ba fada takeba ansha fadamin cewa suna Mata rashin kunya dukda nasan daman ba kunya ne dasuba bacin dalilin rashin lafiyar nan bazan yarda ba sai gashi Kiri Kiri agabana sun wulakanta mahaifiyar mu agabana jiya bawacce ta je dubota a asibiti sai yamma sannan da yunwa muka wuni sai bayan dawowarmu ne ba kunya ba tsoron Allah sukazo da kinibibinsu suna mana kame kame suna borin kunya to wlh bazata sabuda ku gakunan rid’a rid’a jere Kun girma harkun aje iyali Amma mahaifiyar ku. Bata hutaba daga cikinta sai cikinta auta amma kullum da asussuban fari ta fita tana gidin murhu tana hura wutan waina haba haba yaushene zata huta kenan? Ko naira dari dari ne kuke bata AKULLUM zai isheta cin abinci don haka nataraku ne yau ayi wacce za’a ayi tsakanin mu don kuwa yanzu hawan jini likita yace tanashi sai dai yace in akabi ka’ida aka bata kulawa zata samu lafiya harta warke gaba daya yanzu hawan jinin mataki na farko yake.

‘nidai gaskiya bansan irin zaman da su habu da matayensu keyi anan gidan ba amma dai koma mene kiyi hakuri umma kigafarcemu. Alhj auwalu ne yayi furucin

Jamilu ne yace ‘ni dai aganina yadace bayan an kammala taron nan suma matan akirasu aja musu kunne don wlh karsu na tadawa uwata hankali ehe tunda dai bazaman jiransu takeba bare suce suna dawainiya da ita.

‘Hakane jamilu cewar anty saratu

Hakako akayi hatta gidan alhj auwalu Saida aka kirasu matayen nan dasuke gidan ma kowacce tazo anty saratu dince tayi magana tace ‘inafatan kowacce tashinshino dalilin kiranta inma bata shinshino ba to dalilin Kiran shine kowacce daga yau karta kara niman fitina da son tashin hankali agidannan wlh don bazai yiwuba kullum kukenan kananun fitintinu da gulmace gulmace,

Sai anan ne baban ummi yasa baki yace ‘sannan magana ta gaba shine daga yau umma ta dena girki agidannan kowacce intayi abinci zatasa Mata kuma likita yahanata cin gishiri sabuda haka akiyaye.

Ko akwai mai magana acikin ku? Kowa tayi shiru sai maman kalifa ce tace nidai abunda zance shine umma ki gafarcemu kuma kiyi hakuri Allah huci zuciyarki ubangiji ya Kara lafiya daga haka tamike ta fita

Kimanin sati biyu da kafa wannan sharadin nacewa umma bazatayi girki ba Kuma atsawon wannan lokacin suna zuba abincin su Kai mata har gasan kai abincin akeyi kowacce rigen kaiwa take don burgewa da son nuna kalan abincin data girka.

Yau da gobe sai maman ummi ta fara dangarewa in tasa rana bazatasa abincin yamma ba da baban ummi yafara ganewa don saida tayi tsayin kwana biyar bata sa mata abinci sau biyu arana kafin ya lura sai ya tambayi dalili nan caraf tace Wai abincin yanayin yawa ne kwanuka biyar sunyi yawa shiyasa ma suka raba in mutum uku suka bayar da Rana mutum biyu sai su bayar da dare

Bai wani damuba yabar maganan ahaka maman abul itama tadauki sahu sai taki sa abincin inko tasa to dan kadan zatasa itama Aysha tabi sahu sai ya Zama daga maman kalifa sai gidan alhj auwalu ne kawai ke bawa umma abinci sau biyu arana ita maman kalifa sau ukune ma Kam take bata don tana Sanya Mata shayi dasafe in dumame sukaci haka take saka wa umma

Yau maman kalifa tafara sana’ar awara but iyakar banki kawai ake kaimata awarar a take away takesawa guda goma ta yayyanka kabeji da albasa da cocumber 500 take away daya

Washegari sai aka samu karin mutane biyu suma sunaso sai Kuma yazama zasuje gaisuwan mutuwa kanin mijin anty saratu yarasu sai maman kalifa tace suyi gaba zata karasa aikin awaranta tazo daga baya ahanyarsu ta tafiya ne maman abul tace ‘wai ni kunga wani sabon abu? A ace duk sanar da matar nan keyi bai ishetaba sai ta hada da wani awara kuji min masifa nan suka kafa shaftar ta har suka isa gidan gaisuwar sun so sufadi wani abun gameda rashin zuwan maman abul sai kuma suka tuna anty saratu bata daukar haka tana iya zuwa gidan ta titsiyesu

Wasa wasa sai awara ta karbi maman kalifa nan kishi yafara turnuke sauran saiko maman abul tafara yin warar amma wata yarinyar makwafciyarsu ke fita dashi tana Saida Mata sai ita ma Aysha tafara Amma ita kanwarta ce kezuwa ta daukar Mata tana kaiwa anguwarsu itako maman ummi zobo tafara da pure water

Ita maman kalifa batace komiba sodayawa sai anshigo ance abada zobo sai maman ummi tayi zaraf tace na nawa zo nan itadai maman kalifa batace komiba ana haka sai itama maman abul tafara saka nan gida ya kacame da sana’a ko maman kalifa tayi zobon baya karewa haryayi tsami ta zubar sabuda ko anzo siya sai maman ummi tabi yaro tana Kai zonan kokuma ta tura ummi kofar gidan duk yaronda zai shigo sai ta tareshi in zobo yazo siya ko pure water sai ta karbi kudin takaiwa mamanta itako maman kalifa yaronta karamine bai girma ba Kiri Kiri sana’ar zobon da tun satin farko datake gidan tafarayi yazo ya gagareta

Sai ya zama iyaka awarar takeyi da kunun ayah ana Kai Mata banki to yauda gobe in bankin basu siya dayawa ba yana zama kwantai saita fara rage hannu don haka samunta yaja baya ganin haka taiwa yayanta magana daya taimaka yasamo Mata koyarwa a makarantar abokinshi tunda tayi sakandare ahaka da kyar da sidin goshi donma abokinshi ne ya dauketa zatana kulada baby class

Sha biyu take dawowa zuwa wannan lokacin anfara rigima tsakanin maman abul da Aysha akan awaran don kuwa yanzu kowacce batada Mai fitar Mata dashi iyaka azo gida asiya to dazarar anzo din sai ayita rigen rigen karbe kudin ahannun yaro ga maman abul duk wannan kyalesun da maman kalifa tayi bai Mata ba sai yamma si tsiri wannan zaman dandalin dasukeyi suna yada habaici

Yau maman kalifa ta biya kasuwa ta siyo kashin dari da hamsin naman dari biyu sai cefanenta na dari da hamsin duka dai dari biyar takashe tadawo gida karfe hudu kowacce ta fito zaman kofar dakin umma kamar yadda sukeyi maman abul ce tafara cewa ‘kai komin bakincin tanda sai munci waina sana’ar awara muna nan munayi ba gudu bajada baya ehe .

Caraf maman ummi tace to fa Mai zaisa kibari ai dai baki hana kowa yayi ba ko?

Maman kalifa najin haka tagane cewa da ita suke daman tana zaune afalonta ne sai ta tunoda cefanenta datayi darana tako tashi ta wanke namanta ta dora a tukunya ta yanka albasa isasshe nan da nan kamshi ya wade gidan sai ka dauka wani naman rago ake suya jamilu yashigo gidan yana fadin ‘Kai wannan qamshi haka lallai yau zamuci dabge nan maman kalifa tace ‘aikuwa dai gashi nan don tafito wanke alayyaho ne lokacin sai jamilu yace Kai miyar alayyahon ke zabga wannan qamshin ? Kodayake daman tunda naji qamshin nan nasan kece ‘kai baba jamilu bakada dama lallai kace matarka akwai aiki agabanta tafadi hakan cikin raha sai yace ‘to ni ina zan zauna da matar da bata iya girki ba ai saima naji kwarewar yarinya a fagen girki kafin inkai kudin aurena gidansu …. ‘Allah yazaba maka nagari to yace ‘amin daga haka ya shige dakin umma ita Kuma maman kalifa ta shige dakinta don harta gama wanke alayyahon

Suf suf kowacce ta shige dakinta don bakaramin haushin maganar jamilu sukaji ba don daman sunajin haushin yadda maman kalifa tai banza dasu sannan wannan kamshin girkin ya kular dasu 🤣

Kuyi hakuri 2dys dinnan ayyukan MUTANENE sukamin yawa 🤝🏻 ita Kuma maman kalifa ta shige dakinta don harta gama wanke alayyahon

Suf suf kowacce ta shige dakinta don bakaramin haushin maganar jamilu sukaji ba don daman sunajin haushin yadda maman kalifa tai banza dasu sannan wannan kamshin girkin ya kular dasu 🤣

Kuyi hakuri 2dys dinnan ayyukan MUTANENE sukamin yawa 🤝🏻

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.