Hausa Novels

Fa’idodin amfani da Nonon Akuya

Fa’idodin amfani da Nonon Akuya

 

 

 

 

 

 

 

 

Yaushe rabon ka dayin amfani da Nonon Akuya?

 

Daga cikin Fa’idodin amfani da Nonon Akuya:

 

Nono na daya daga cikin abubuwan sha masu amfani ga lafiya da gina jikin dan Adam.

Tun tsawon zamanin da suka gabata ake amfani da shi a matsayin maganin rigakafi ga cututtuka da dama, saboda yana ƙunshe da sinadarai masu mahimmanci ga lafiyar jiki.

 

Duk da cewa muna iya samun nono daga dabbobi da dama, kamar nonon saniya, nonon rakumi, da na akuya, da kuma tsirrai kamar su madarar waken soya, madarar kwakwa, da sauran su.

Amma galibin mutane sun ta’allaka da amfani da nonon dabbobi, musamman ma nonon saniya.

Rashin kula da sauran nau’o’ikan nono da ake da su, ko dai saboda qarancinsu ko rashin sanin fa’idarsu.

 

Amfanin nonon akuya nada alaka da ta yadda yake ƙunshe da minerals da vitamins da ake bukata a jikin ɗan adam da yawa idan aka kwatanta da nonon saniya.

 

AMFANIN MINERALS DA VITAMINS DA AKE SAMU DAGA NONON AKUYA:

 

Nonon akuya yana ƙunshe da vitamin da minerals masu yawa fiye da sauran nau’ikan nono, waɗanda suke da mahimmanci don bada kariya da lafiyar jiki.

 

Waɗannan minerals da vitamin sun haɗa da:

 

■ Vitamin B5: Vitamin ne da ke taimakawa wajen samar da kuzari a cikin jiki da kuma kawar da gajiya da kasala.

 

■ Biotin ko vitamin B7: yanada matukar amfani wajen samun lafiyar jijiyoyi sadarwa (nerves) da lafiyar fata da gashi.

 

Vitamin A: Wani muhimmin vitamin ne dake kara lafiyar gani da fata.

Nonon akuya na taimakawa wajen yakar yamushewar fata, kawar da kurajen fuska, da kuma hana fata bushewa.

 

Zinc: Nonon akuya na kunshe da zinc mai yawa bugu da kari kuma ga yawan sinadarin Selenium.

Wanda hakan ya sanya shi ya zama lafiyayyen abin sha wanda ke taimakawa wajen Inganta ayyukan jiki ga masu larurar Parkinson disease.

 

Calcium: Nonon akuya yana dauke da calcium mai yawa, wanda ake bukata a cikin tsarin daskarewan jini (blood clotting) girman kasusuwa da hakora.

Calcium din da ake samu a cikin nonon akuya yana da sauƙi ga jikin ɗan adam yayi absorbing din shi idan aka kwatanta da calcium din da ake samu a cikin sauran nau’ikan abinci.

 

Potassium: Nonon akuya na dauke da sinadarin potassium, wanda keda alaka da jijiyoyi sadarwa (nerves), tsoka, da hawan jini a jikin dan adam.

 

Phosphorus: Nonon akuya na dauke da sinadarin phosphorus wanda ke taimakawa wajen ci gaban girman kashi da hakora, baya ga rawar da yake takawa wajen samarda kuzari daga abinci.

 

Iodine: Nonon akuya na dauke da Iodine, wanda ke da alhakin aikin thyroid gland yayi ayyukansa na hormonal yadda ya kamata.

 

Chlorine: nonon akuya na ƙunshe da wadataccen adadin sinadarin chlorine, wanda ake bukata sosai wajen kare lafiyar tsarin narkewar abinci

 

Magnesium: Likitoci suna ba da shawarar shan Nonon akuya ga mutanen da ke fama da karancin magnesium domin yana dauke da sinadarin magnesium mai yawa.

 

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.

 

Bashir Suraj Adam

Leave a Comment

error: Content is protected !!