Fakiri Hausa Novel
Tag: FAƘIRI
*Daga alkalamin✍️*
*KHADEEJA UMAR*
(UMMU HAMNAT)
*🌙✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙✨*
*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”🌍’* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Wannan littafin na FAƘIRI nayi shi ne don faɗakarwa da nishaɗantarwa idan yayi kama da rayuwar wani akasi aka samu
Sadaukarwa ga ahalina Umar family allah ya kare ku aduk inda kuke tare da sauran ƴan uwa musulmai
Wannan shafin naki ne sweet heart Jidderh umar kiyi yanda kike so dashi
Da sunan Allah mai rahmah maijin ƙai
*1&2*
“Assalamu alaikum, wai ana sallama da Nadiya a waje” wani yaro ya fada bayan ya shigo cikin gidan mu
Tun kafin ya rufe baki na zaburo daga cikin karamin dakina cikin masifa ina zaro mashi manyan idanuwana nace “wuce kace bata nan”
“Kai kace tana zuwa”mama dake fitowa daga cikin madafi ta faɗa ma yaron dake shirin juyawa,
Tashi nayi cikin fushi na shiga cikin karamin ɗakina don daukar mayafi na don nasan ba wanda zai zo wurina sai sababbe FAƘIRI kuma ba daman nace ban fita mama ta aza min faɗa,ina turo baki na fita daga gidanmu
Zaune yake jikin dan barandar kofar gidanmu sallamar da nayi baisa ya dago daga danna rakani kashi da yake tabawa ba sai dai cikin sanyi muryanshi wanda yake kara ma izzar shi kwaijini, zama nayi dan nisa dashi ciki ciki nace “barka da yamma” don ya tsani ince mashi ina wuni
Sanye yake cikin riga fara da wando brown yan gwanjo amma,sunsha wanki da guga duk da son tsufa sai kamshi yake,
Dago kanshi yayi ya kalleni da idanuwanshi da suke rikitani tsawon minti biyar yana kallona sannan ya kauda kanshi ya mike tsaye cikin kasaitar da ta zama mashi jiki kamar ba dan talaka ba yace “gobe zan dawo idan kinyi shirin ganina”
Cikin mamaki nabi jikina da kallon sanye nake da zani daban riga daban, nan take na bata fuska don nasan abunda yasa ya mike kenen,ya tsani yazo na fito cikin irin wannan shirin duk da cikin kwalliya nake harda kamshin humra nake,amma saboda wulakancin faƙiri wai gobe zai dawo duk kewarshi da nayi kwanarshi hudu baizo ba,
Kallon yanda ta bata kyaukwawan fuskarta yayi sanyayyar murmushin daya kara ma fuskarshi annuri yayi, “shiga gida” yayi min nuni da kofar gidanmu
Kallon fuskarshi nayi ganin yanda yaci seriou yasa na fashe da kuka na ruga da gudu na shige gida,lumshe idon shi yayi sannan ya juya don barin wurin
Da kallo mama tabini ganin yanda na shigo ina kuka kai ta girgiza “allah dai ya shirya ki Nadiya” tacigaba da aikin ta,
__________ tafiyar shi yake a natse kamar kullum yauma yana isa dai dai majalisa matasan dake layi gidansu Nadiya, yabi layin matasan yana musabiha dasu bayan yayi masu sallama,
Wani matashi da ake kira da Awwal yace ” bismillah mallam Faƙiri” yana bashi wurin zama
Murmushi yayi don ya riga da ya saba da wannan suna da Nadiya tayi sanadiyar ya bishi tun yan unguwar na fadi a bayan idon shi har yanzu sunar ya bishi a anguwar nasu “a,a mallam Awwal gida zani” nan yayi masu sallama ya wuce
Yana bada baya Musa yace “wai saboda mai yasa kuke ce mashi faƙiri fisabillilah”
Dariya Awwal yayi “gaske kai bako ne a layin nan, kasan yarinyar nan Nadiya yar gidan mallam kabir mai saida kayan gwari?”
Musa ya jinjina kai “kwarai waye baisan wannan yarinyar ba ko saboda kwalisar ta anguwar nan”
Awwal yace “to shi ke niman ta da farko duk mamaki muke saboda kaf matasan anguwar nan idan nace maka har da magidanta suna sonta kwarjinin ta da tsiwar ta da ganin yanda masu kudi suke kara kaini kofar gidansu wurin ta yasa duk muka labe gefe, amma wani abun mamaki lokacin da Faƙiri ya fara zuwa wurin ta sai gashi tas ta kori masu zuwa wuri ta sai shi kadai, bayada komai sai waccan izzar da ka gani amma a haka take mutuwar son shi, kasan abun mamaki ita tasa mashi suna Faƙiri har gashi ya bishi kuma baya fushi ko an kira shi da haka hatta yara haka suke kiran shi”
“Cabdijam yanzu wannan yarinyar take tsayawa da wannan duk haduwar ta?” musa ya fada cikin mamaki
Dariya sauran matasan sukasa “ko kaima zaka gwada sa,ar ka?”
Baki Musa ya rike “wa! wannan tafi karfina”
Wani da ake kira da shamsu yace “nima fa lokacin nan naso wannan yarinyar amma saboda kwarjinin ta na gagara tunkaran ta har wannan talakan faƙiri ya sameta”
Haka suka cigaba da hiran su shidai faƙiri baisan sunayi ba.
**********
“Shawarar nidai dazan baki Nady shine wallahi ki tashi tsaye, wannan Faƙirin ba banza ya barki ba ace duk tulin samarinki yana zuwa duk suka watse, she kenan kullum ba abinda yake tsinana maki common dan kudin hira baya iya baki shekara biyu,wallahi Nady kinci baya” kawata aminiya ta bilkisu ta faɗa cikin bacin rai
Tagumi na cire “to ya zanyi billy wallahi ina matukar sonshi,ko nayi niyar shuka mashi rashin mutunci daya tsaya gabana sai naji na kasa”
Cikin jin haushi tace “kinji ba,wallahi ba banza ya barki baka, kamarki ace mai kwadago gidan biredi ana bashi dari biyar shine saurayin ki,! kwaffa tayi ki shirya zan rakaki wurin kawun Sahiba yana dan bada taimako ko allah zaisa ki rabu da alaƙakai”
“Nifa billy ina tsoro bana son zuwa gidan boka,haka kawai na rasa imani na” na faɗa ina kauda kaina saboda nidai ina son faƙiri na,sai data min rantsuwa ba boka bane sannan na yarda jibi zamu.
Washegari
“Yanzu mai kike son na miki” Faƙiri ya faɗa, muna zaune dakalin gidan mu bayan sallar isha
Turo dan bakina nayi “nifa na faɗa maka baba yace ka turo tun last week kuma banji kayi wani motsi ba”
Murmushin shi mai sanyi yayi “insha allah zuwa sati na sama su babale zasu iso,kinsan yanayin garin yanzu sai a hankali, daga adamawa zuwa nan sai ka shirya, ni kuma kafin su iso zan balle asusu na naga nawa na samu,Allah dai yasa na samu ko na baiko ne kafin na tara na sadaki” faƙiri ya faɗa
“Kar ka wani wahalar da kanka duk abunda ka samu allah ya anfana”
“Ayi haka gimbiya ta, kimar ki ya wuce haka, ko dako ne zan fara saboda na wanke ki cikin yan uwanki,bari na tafi kinsan baba baya son kaiwa dare sosai nima na gaji don yau ba karamin aiki nayi ba da kyar na haɗa dubu ɗaya”
Tausayin shi ya kamani don nasan saboda nine yake kure kanshi wurin aiki “Don Allah kabar kure kanka bana son wani abu ya same” na fada duk nayi kalar tausayi
Cikin farin ciki yace “ba abunda zai gutseren maki ni gimbiya”
Kafaɗa na daga “nidai a,a ,ko kasan abunda yake kara birge ni a tare da kai”
kai ya girgiza har lokacin murmushi baibar fuskarshi ba
“Kalar fatar ka da kullum take kara fresh tana kyalli kamar mai kwana ac bamai aikin biredi ba, da idanunka masu matukar daukar hankalin duk wanda ya iya jure ma kallon su”
Sanyayyar dariya ya sake “gashi kuwa kullum aikin karfi nake kuma ban taba san ac ba,
Kurama hannayen shi masu cike da gargasa ido tafunan hannayen shi ko da ban taba ba nasan sai sunyi laushi, tafin da yayi kusa da fuskata yasa na dawo daga tunanin da nake “ki shiga gida sai kuma gobe idan Allah ya kaimu” sallama mukayi na shige gida..
Hello fans wannan karan na dawo maku da wani sabon littafi FAƘIRI zaiyi matukar kayatar daku don wannan littafin yazo ne da wani salo na daban, kar kuji komai comment kawai nake da bukata wannan karan free book ne asha karatu lafiya.
*Ummu hamnat ce*
Comment
&
Share fisabilillahi
[02/10, 8:53 pm] +234 816 330 9566: *🛖🛖FAƘIRII🛖🛖*
*DAGA ALKALAMIN ✍️*
*Khadeeja Umar*
(Ummu hamnat)
3&4
Ƙarar wayata shi ya tadani daga baccin daya kwashe ni bayan gama azkar din sallar asuba, ba tare dana duba mai kira na ba na jawo nasa a kunne na “hello” na faɗa cikin muryan bacci
“Assalamu alaiki” muryan daya daki kunnena yasa na bude idona tare da wartsakewa
“Afwan My, assalamu alaikum” don nasan baya kaunar ya kira waya ince hello
Amsawa yayi kamar kullum cikin sanyayyar muryan shi, tafiyar gaggawa ta sameni zuwa lagos, wani aiki abokina ya faɗa min zan dan samu ɗan canji, shine zan tafi yi” faƙiri ya faɗa min
Tashi zaune nayi ina turo baki ina hararen wayar kamar yana ganina cikin tsiwa nace “nifa wannan tafiye_tafiyen ya isheni yaushe ka dawo daga kano wurin aikin kwadogo sannan yanzu sati daya kace zaka tafi wani gari,kai kenan kullum baka zama, to nidai ya isheni haka ba inda zaka”
Shiru yayi yana sauraran masifar da take mashi,idan halin ya motsa mata koshi bata bari,duk da yanzu tsiwar nata yayi sauki ba kamar daba “Naadyy”
Dif nayi jin yanda ya ambata sunana wanda yasa tsigar jikina tashi,duk wani karsashi da nake dashi ya tafi
“Baki son ina niman kudin dazan aure kine, kinfi son Baba ya gaji da jira na ya miki aure?” ya faɗa cikin rarrashi
“Nifa ba komai yasa bana son kana yawan tafiya ba, hanyar yanzu bata da kyau kullum kace zakayi tafiya cikin zullumi nake har ka dawo, please My idan ta nine ka zauna wuri daya bana son wani abu ya sami my faƙiri” na karasa faɗa da dariya
Shima murmushi yayi “na miki alkawari wannan karan sati biyu ne kawai zanyi,kuma idan na dawo sai na kwashe sati biyu ba kara tafiya ko ina ba”
Kuka na fashe dashi cikin shagwaba nace “ni wallahi ban yarda ba haka kullum kake cewa sannan ko sati ba kayi da kaji wani aiki zaka kara tafiya”
Wani annuri ke fita kan fuskarshi jin yanda ta damu dashi “na miki alkawari wannan karan hakan bazata faru ba” haka ya cigaba da *🛖🛖FAƘIRII🛖🛖*
*DAGA ALKALAMIN ✍️*
*Khadeeja Umar*
(Ummu hamnat)
3&4
Ƙarar wayata shi ya tadani daga baccin daya kwashe ni bayan gama azkar din sallar asuba, ba tare dana duba mai kira na ba na jawo nasa a kunne na “hello” na faɗa cikin muryan bacci
“Assalamu alaiki” muryan daya daki kunnena yasa na bude idona tare da wartsakewa
“Afwan My, assalamu alaikum” don nasan baya kaunar ya kira waya ince hello
Amsawa yayi kamar kullum cikin sanyayyar muryan shi, tafiyar gaggawa ta sameni zuwa lagos, wani aiki abokina ya faɗa min zan dan samu ɗan canji, shine zan tafi yi” faƙiri ya faɗa min
Tashi zaune nayi ina turo baki ina hararen wayar kamar yana ganina cikin tsiwa nace “nifa wannan tafiye_tafiyen ya isheni yaushe ka dawo daga kano wurin aikin kwadogo sannan yanzu sati daya kace zaka tafi wani gari,kai kenan kullum baka zama, to nidai ya isheni haka ba inda zaka”
Shiru yayi yana sauraran masifar da take mashi,idan halin ya motsa mata koshi bata bari,duk da yanzu tsiwar nata yayi sauki ba kamar daba “Naadyy”
Dif nayi jin yanda ya ambata sunana wanda yasa tsigar jikina tashi,duk wani karsashi da nake dashi ya tafi
“Baki son ina niman kudin dazan aure kine, kinfi son Baba ya gaji da jira na ya miki aure?” ya faɗa cikin rarrashi
“Nifa ba komai yasa bana son kana yawan tafiya ba, hanyar yanzu bata da kyau kullum kace zakayi tafiya cikin zullumi nake har ka dawo, please My idan ta nine ka zauna wuri daya bana son wani abu ya sami my faƙiri” na karasa faɗa da dariya
Shima murmushi yayi “na miki alkawari wannan karan sati biyu ne kawai zanyi,kuma idan na dawo sai na kwashe sati biyu ba kara tafiya ko ina ba”
Kuka na fashe dashi cikin shagwaba nace “ni wallahi ban yarda ba haka kullum kake cewa, sannan ko sati ba kayi da kaji wani aiki zaka kara tafiya”
Wani annurin farin ciki ke fita a fuskarshi “kin yarda dani?” faƙiri ya faɗa
Ciki_ciki nace “uhm”
“Na miki alƙawarin wannan karan zaki matukar farin ciki idan na dawo” haka ya cigaba da rarrashi har kuɗin wayarshi ya ƙare sannan mukayi sallama
__________________ “Anty Nadiya Mama tace ki tashi baccin nan haka karfe tara tayi” ƙanina Nazir ya faɗa bayan shigowa cikin daƙina
Hararan shi nayi tare da zaburo mashi “to ala gulma a kwance ka ganni ɗan allah fita ka bani wuri”
Marairaicewa yayi “kai anty Nadiya komai naki na masifa ne, daga faɗa maki saƙo” faɗin Nazir
Tashi nayi zan kamashi ya ruga da gudu na bishi, “Mama kinga anty Nadiya zata doke ni”
Rike haba mama tayi “oh ni hauwa wai yaushe wannan yarinyar zatayi hankali, uyya maza ki wuce kiyi wanka kizo ki karya, har rana tayi kina shegen bacci”
Tsayawa nayi cikin shagwaba ” ba wannan faƙirin bane ina bacci na ya tadani wai tafiya zai kuma yiba”
“Bana rabaki da kiran wannan bawan allah faƙiri ba, mahaifinki zan faɗa ma inaga shi zakiji tsoron, shi kuma na rasa wannan tafiye_tafiye nashi da baya cikekken sati biyu ya tafi”
Ruwan zafin da mama ta daura min na juye “Mama bari nayi sauri na manta billy zata biyo man zamu gaishe da Sahiba bata jin daɗi”
“Kinsan ki da nawan shiri shine kikayi kwanciyar ki, sai ki hanzarta kiyi wankar ki karya” Mama ta faɗa tana shigewa daƙinta
***********
Zaune muke gaban mallam Buba gabana ba abunda yake sai faɗuwa don ni bana kaunar abunda zai haɗani da irin mallaman, katse mana shiru yayi baya ya gama jin duk bayanin dana mashi,
“Mallama Nadiya ki damki kasar nan a hannunki” mallam Buba ya faɗa
Cikin ɗar_ɗar zuci na ɗibi kasar a hannuna na damke kamar yanda yace,tsawon minti biyar sannan yace in zuba kan wani faranti,yanda yace haka nayi, wasu zane yayi saman kasar sannan ya dan dakata tsawon minti goma, ni kuma ba abinda gabana yake sai faɗuwa,
Ɗago kanshi yayi ya kalle ni “tabbas akwai alheri mai yawa tsakanin ki da wannan yaro sannan baki da wani miji face shi duk da akwai tarin ƙalubale mai yawa a taraiyarku amma tabbas duk wani abinda zai faru shine dai mijin naki”
Billy ce tayi magana ganin yanda na sankame a zaune “yanzu mallam ba yanda za,ayi, ka taimaka wallahi kwata_kwata bata dace dashi ba, don allah kayi wani abu farin jinin nata ya dawo”
Murmushi mallam Buba yayi “yarinya kenan duk wanda yace maki zai iya hana wannan auren tsakanin su wallahi karya yake,bari na faɗa maki ko shine berar masallaci ƙarewan talauci to shine dai mijin ta,don haka taje tayi hakuri”
Zabura nayi na mike ina nuna shi da hannun “karya kake munafiki ba yanda za,ayi kace shine wai mijina na fasa son nashi kuma aurene bazan aure shi, idan ma haɗa baki ne kukayi to ka faɗa mashi karyan shi tasha karya kamar ni ace na kare da auren wani faƙiri duk tarin masoya na” na faɗa cikin tsiwa
Billy ce da Sahiba suka rike ni suna kokarin kulle min baki “haba Nadiya ki bar haka mana”
“Ku barni da wannan tsohon banzan taya zaice faƙiri shine mijina na har abada”cikin tsiwa nake faɗa
Mallam Buba cikin rashi damuwa yace “duk abinda zakiyi sai dai kiyi amma faƙiri shine mijin ki”
Bala,i da masifa ba irin wanda banyi ba kamar zan doke mallam billy da sahiba na rikeni da kyar suka samu suka fito dani daga gida sai tsine mashi nake ,don ji nake duniya ba wanda na tsana sama da faƙiri tunda naji mallam Buba yace wai shine mijina na har abada..
************
Motoci ne kirar zamani mercedes suke sheka gudu kan titi hanyar airport kimanin guda biyar basu zarce ko ina ba sai baki wani tangamemen get din dayama wani hadadden gida kawanya, hon suke saki da alama suna uzurin da su shiga gidan da sauri gate din ya bude kanshi wanda mamaki ya kamani da alama wannan gate din tare yake da security mai karfi, a hankali motocin suka sulale suka nufi fankaɗeɗiyar farfajiyar gida, suna gama tsaida motar da sauri security suka firfito suna zaran idanu tare da kalle_kallen gidan kafin ɗaya daga ciki ya buɗe kofar motar tsakiya da alama suna jiran ogan nasu ya fito,
Nima ido da hanci na bude ina son ganin wannan mutumin mai mukami ake bashi wannan tsaron
Taku Ummu hamnat
Comment
&
Share fisabillahi
[02/10, 8:53 pm] +234 816 330 9566: *🛖🛖FAƘIRII🛖🛖*
*DAGA ALKALAMIN ✍️*
*Khadeeja Umar*
(Ummu hamnat)
5&6
Matashi ne wanda bai gaza shekaru talatin zuwa talatin da biyu ba ya bayyana daga cikin motar,baza,a kira shi wani kyakkawa can amma jin daɗi da hutu yanda suka zauna a jikin shi yasa kyauwun shi fitowa, cikin takun zaratan maza ya doshi kofar mashigar falon gidan security na take mashi baya,sai daya isa kofar falon sannan suka dakata, kai tsaye ya shige ciki, aljannar duniya shine wannan falo, wata kyaukkawan bafullatan mata ne zaune kan ɗaya daga cikin royal chair da sukama falon ƙawanya masu kalar Sky blue,faɗaɗa murmushin saman fuskarta tayi ganin wanda ya shigo bayan sallamar da yayi,
“Lale maraba da ɗana Abbas,saukar yaushe?” shine abunda ta faɗa da fara,ar ta
Tugunnawa yayi gabanta yakai zaune “Ummi barka da gida, yanzu na sauka,mun sameku lafiya?” matashin daya shigo ya faɗa
Lafiya kalau Abbas ya wurin su hajiya?”
“Suna gaisheku”
“To madalla, ya kuma koƙari da hakuri da abokin naka?” ta faɗa fuskarta na ƙara washewa da murmushi
Bata fuska Abbas yayi “Ummi fushi nake dashi haka kawai ya mayar dani bilbili bana can bana nan,Allah Ummi na kusa bankaɗa shi garin nan”
“To wannan dai tsakanin kune, ya maganar da mukayi kwanaki an dai_ dai ta ko?”
Gyara zama yayi “abunda ya kawo ni kenen Ummi na samu na shawo kan wancan matsalar companyn can, jiya kuma manager H & H design yace masu hannun jari sun tada balli COE suke da bukatar gani wannan karan, na rasa abunda sulaiman yakeyi,har daya dauke shi tsawon wannan lokacin bai dawo ba, da zaran na mishi magana sai yace saura kaɗan komai yazo karshe”
“Ka cigaba da hakuri Abbas wannan shirin duk ku kuka shirya shi, lokacin dana nuna rashin bada goyan baya nan ka same ni ka kawo min kabli da ba,adi har na yarda, gashi yanzu tsawon shekara biyu abu yaƙi ci yaƙi cinyewa” ta faɗa da damuwa
“Ba komai Ummi acigaba da mishi addu,a komai zai tafi dai _dai da yardar allah”
“Allah yasa kullum cikin mishi nake,
**********
Hararar wayar dake ƙara kusa dani nake kamar ita tamin laifi, sunan faƙiri ne ke yawo saman screen din wayata, wani haushin shi ke kara kamani,”i hate you”na faɗa ina ƙara tsaki,wayar na kashe jin ta dauki sabon kira
Mama ce ta leko dakina “lafiya kike tun jiya da kike dawo kike fushi?”
Har na bude baki zan faɗa mata na tuna tabbas Mama taji labarin naje wurin wani mallam sai taci mutuncina balle Baba yaji “daga yau ba ruwa na da faƙ..Sale babu ni babu shi” hawayen takaici na zobo min
“Bana son shashanci shekara biyu kuna tare dashi duk kin kori masu zuwa wurin ki sai yau kice babu ke babu shi, kinsan dai mallam bazai kara bari ki shekara a gidan nan ba tun bara kika gama makaranta”
Kuka na fashe dashi “Allah Mama bani bane na koresu wannan faƙirin ne yamin asiri duk suka bar zuwa,ni kuma yanzu bana sonshi na fasa aurenshi”
Innalillahi wa inna ilaihirraji,un yanzu Nadiya ina kika samu wannan tunanin, asiri”ta faɗa tana tafa hannayenta
“Da gaske nake mama idan ba asiri bane ta yaya daga zuwan shi duk kowa yabar zuwa”
“E lalle Nadiya wannan maganar a kunnen mahaifinki idan kin fara hulɗa da kawayen banza sai inji, muhammadur rasulullah,”
Kuka nake ina shesheka , ganin da gaske nake yasa ta shigo zama tayi kusa dani tare da kamo fuskata tana share min hawaye,”Nadiya yi shiru ki saurare ni”
Sai dana natsu sannan ta fara min magana cikin rarrashi “Nadiya ina son ki saurare ni da kyau, ni wacece a gareki?”
“Mamana mahaifiyata uwata abinda alfaharina”
Kin yarda bazan taba cutar dake ba duk tsanani”
Kai na jinjina mata don ban fahinci dalilin da yasa mama take min waƴannan tambayoyin ba
“Idan har ki yarda akwai Allah kuma kin yarda shike bada wa kuma shi ke hanawa karki kara tunani wani ɗan adam ya isa ya cutar dake,duk wani abu da zai sameki ki fawwala ma allah sai kiga komai yazo maki da sauki, maganar baki son Sale bana son in ƙara ji don nasan kina kaunarshi , wasu ne can daban suke niman su hure maki kunne, yana sana,ar shi dai_ dai gwargwado kuma kowa ya shaide shi mutum kirki ne baya da abokin faɗa,mai zai sa kiyi tunanin dole sai kin aure mai arkizi bayan ko mu iyayenki cikin rufin asirin allah muke, daga yau bana son kara jin makamanciyar maganar nan, allah shi yasan dai dai addu,a kullum muke maki allah ya zaba maki miji na gari, watakil Sale shine alheri gare ki tunda kikaga duk kowa ya watse shine kawai ya tsaya,Allah yasa abokin arzikin kine” haka Mama ta cigaba da bani magana har hankalina ya kwanta
_________”wai kina nufin har yanzu Nadiya batayi aure ba” yusif ya tambayi Farida ƙanwarshi
“Yaya kenan kaima ka sani da tayi aure da ka samu labari ko kowa bai faɗa maka ba momy sai ta sanar dakai” cewa Farida tana jan baki
Dafe kai yayi cikin damuwa “yaya shi yasa momy ta hana a faɗa maka saboda tasan har yanzu baka bar kaunar nadiya ba” farida tace cikin damuwar ganin halin da ɗan uwan ta ya shiga
Tashi yayi “zan tafi gida idan momy ta dawo ki gaishe ta”
“Bazaka dawo da daddare ba?” ta tambaye shi
Kai ya girgiza mata “sai dai gobe”
Cikin tausayi ta bishi da kallo idan ba dan momy itace ta haifesu ba da tace momy ta cutar da yaya yusif tun rabasu da Nadiya da tayi har yau bata kara ganin farin ciki a fuskar shi ba, gashi ta mishi aure da ba abunda ya kara mai sai cutuwa, ” idan rabon kace Nadiya Allah ya sausauto da zuciyar momy ta amince da muradin zuciyar ka ya Yusif
Bayan kwana uku
Tafiya muke mun taso daga islamiyya sanye muke da hijabai kalar brown har kasa , sahiba ce ta rike baki cikin mamaki “ke bilki ashe haka wannan ƙawar taki take, ni wallahi da mutane da faɗin masifar ta ban taba yarda ba sai ranar nan”
Hararan billy nayi ganin yanda take min dariya “Sahiba bana son fa wulaƙanci ya zaki ce min masifaffiya”
Billy ce ta karbe cikin sauri dan tasan halina yanzu ina iya fara saida halin akan wannan magana “ba haka take nufi ba, amma kema kinsan abunda kikayi ranar baki kyauta ba ko ba komai babban mutum ne bai kamata ki zage shi ba daga faɗin gaskiya”
Zaburowa nayi cikin tsiwa “na zage shi don ma ban haɗa dake ba, daga cewa zaki kaini wurin mallam sai ki bige da kaine wurin dan duba, ki bata min imani na kai allah ya isa na wallahi” na buga mata tsaki na wuce
Haba Sahiba ta rike “cab ashe kina aiki anan haka halin ta yake”
“Kadan kenan daga abunda zata iya” billy ta faɗa cikin tabbatarwa
“Zanso ko naji tarihin wannan soyayyar ta da Faƙiri don nasan ba ƙaramin hakuri yake da halin ta ba”
Dariya billy tayi “a haka kuma ba ƙaramin farin jini mutane gare taba duk wannan masifar nata,bullowar faƙiri ne kawai ta danyi sanyi”
“Lallai ya cire tuta”
“Baza kisan ya cire tuta ba sai kinji kalar gwagwarmayar da yasha kafin ya samu zuciyar ta, gobe juma,a bamu da tahfiz mu hadu a gidansu zan lallaba maki ita ta baki tarihin ta”
Zan ko so jin wannan tarihin ….
More commen
More typing
*Ummu hamnat*
[02/10, 8:53 pm] +234 816 330 9566: *🛖🛖FAƘIRII🛖🛖*
*DAGA ALKALAMIN ✍️*
*Khadeeja Umar*
(Ummu hamnat)
Page 7&8
“Kafin ki ji labarin soyayyarmu da faƙiri ya kamata kisan wacece ni”bayan yanda bilkisu tayi ta fama rarrashi kafin na yarda zan faɗa masu.
Sahiba da ta matsu taji labarin tace “gaskiyarki ya kamata nasan ko ke wacece yanda labarin zaifi bada armashi”
Tushen labari
“Kamar yanda kika sani sunana Ayshatu sunan kakata data haifi babana naci shi yasa ake kirana Nadiya, kakana mallam muhammad mutumin sokoto ne zama ne ya kawo shi garin minna tare da matar shi inna shatu yara biyu kawai allah ya basu daga Musa sai ƙanwar shi fatima, mallam Musa yana matakin karshe na secondary allah yama mahaifinsu rasuwa ta hanyar karamar jinya na kwana biyu, tabbas sun girgiza don sun rasa babban jigo na rayuwar su,tun daga rasuwar karatun Musa ya dakata domin shi ya dauki dawainiyar gidansu, a wahala haka ya cigaba da biya ma ƙanwar shi kudin makaranta har lokacin data gama secondary shi kuma yana ta buga buga duk inda ya samu aikin karfi yana yi, da gama makarantar fatima wani dan makocinsu ya nime aurenta ba jimawa aka sha biki duk da basu dashi amma Musa ya fitar da fatima kunya,
Rayuwa ta cigaba da tafiya musa bayan wasu shekaru shima Musa ya aure Mama na hannatu, sai data shekara biyu sannan ta haifeni ba daɗewa da haihuwata allah yama inna shatu rasuwa, rayuwa tacigaba da gangara masu bayan wasu shekaru, ina da kanne biyar duka maza abubakar ke bina yanzu yana boarding ajin karshe sai muhammad,bilya , nazir mansur,da asim,
Goggo fatima kuwa ƙanwar baba yanzu haka tana daga cikin manya mata don mijin ta yanzu babban mai kudi ne tana da yara biyar Yusif, maryam fa,iza nafi,u , hauwa ƙwata _ƙwata na rasa abunda yasa bata jituwa da mama a yanda na samu labari ba mama taso baba ya aura ba wata ƙawarta taso shi sosai wannan rashin jituwar ya shafe ni wanda zan iya ce maki bata kauna ta kuma sai ta shekara bata tako kafar ta gidan mu ba.
“Nadiya bazakiyi ki gama sharan nan kiyi shirin makaranta ba kinsan yanzu karfe nawa?” mama dake cikin kicin ta faɗa
Tura baki nayi cikin shagwaba daman ba sharar nake so ba ” mama yanzu zan gama”
Fitowa tayi daga kicin “ni dai ajiye min shara ta kije kiyi wanka, na rasa wani irin nawa allah ya baki, yanzu kafin ki fito daga wanka har ki shirya wani sabon aiki ne”
Koda na samu ta amsa sharar na dauki bokiti na ruwan zafin da ta sirka min na shige wanka,ina ji tana ta mita a waje,duk yanda nakai da nayi hanzari kafin bilkisu ta biyo min sai da ta same ni ban gama shiri ba balle na karya,
“Oh ni bilki kullum sai kin sa an min bulalar latti” bilkisu ta faɗa bayan shigowar ta ɗakina
Mama da daman jiran kadan take tace “ke kike biye mata bilkisu, idan nice ke sai dai mu hadu a can, idan ta gaji da shan bulalan latti sai ta shiga hankalin ta”
“Ai mama ita ba,a dukan ta, sai dai mu da,aka raina”
Zaro ido mama tayi cikin mamaki “saboda me, ko tafi sauran ɗaliban girma ido ne?”
“Ba wanda ya isa ya doke ta, principle da kanshi son ta yake sannan mallam mu maza kowa haba haba da ita yake”
Cikin jin haushi na suri jaka ta nace “magulmaciya ai bance dole sai ki biyo mani ba,daga yau bana so” fita nayi na wuce ta
Mama ce ta fara kwala min kira “Nadiya nadiya dawo nan ki karya karki tafi”
Ina ni har na kai kofar gida ban juyo ba, bilkisu tace “mama kiyi hakuri sai mun dawo” da gudu ta same ni har na tare abun hawa shiga tayi “wallahi Nady baki da kirki, yanzu abunda kika ma mama kin kyauta kenan”
Juyuwa nayi na watsa mata manya idanuna cikin tsiwa “ina ruwan ki da rayuwata, nifa bana son sa ido”
Ba tare da damuwa ba don ta saba da halin ƙawar nata tace “ba sa ido nake maki ba yanda kika ma mama ce ban ji daɗi ba don allah ki rinƙa sausauta ma kanki wannan hali”
Na buɗe baki zan sauke mata masifa mai keke nafef ya tsaya dai dai mun iso bakin get din makaranta kwaffa nayi ban kulata ba na shigewata ciki,wannan ranar har aka tashi ina fushi,
___________”wanene na ganshi tsaye dake jiya Nadiya?” ya Yusif ya tambaye fuskar shi daure (yusif yaron goggo fatima ƙanwar baba)
Cikin ko in kula nace “nifa ya Yusif ban gane wanda kake nufi ba”
Ok ashe ba shi kadai bane dole kice min baki gane ba, to mai farar mota, yanzu ai kin gane?” ya faɗa cikin matukar kishi
Kai ya Yusif akan Sagir kake bata ranka, bafa nina nuna masa gidanmu ba muna dawowa daga makaranta ya biyoni a baya”
“Bana son jin wannan tsarin naki kullum da wanda zakice ya biyo ki idan ba ke kike basu fuska ba ta yaya zasu rinka bibiyarki tunda ba ke kadai bace mace a wurin” ya faɗa cikin zafin kishi
Cikin jin haushin yanda yasani gaba da masifa yasa nace “wai an maka dole ne ka tafi mana,ni wallahi na gaji da wannan masifar ba daman ka ganni da wani shi kenan ka kamani da faɗa,ko aure na kake sai haka”cikin tsiwa nake magana harda jijjiga
Mamaki ne ya hana shi magana sai daya ga na juya zai shige gida sannan yace “yanzu Nadiya ni kike faɗa ma wannan maganar?”
A zuciye na juyu “na faɗa kai baba nane, waye kai?”
“To wallahi na fasa barin ki ki ƙarasa makarantar baba zan faɗa ma ya mana auren zaki karasa a dakin ki”
Kuka na rushe dashi “ni ban yarda ai ba haka mukayi dakai ba,saura shekara daya na gama,don allah kar kasa Baba yamin aure yanzu”
Cikin rarrashi don yasan faɗan shi bazai kaishi ko ina ba yace “ya kike so nayi Nadiya kullum cikin fargaba nake akan yanda samari ke kawo maki hari,ki bari kawai muyi aurenmu nadiya shekara daya ne kawai maki ki kammala karatun shi a gidana na miki alkawari zan bari ki cigaba da karatu har sai kince ya isheki”
Turo baki nayi “nidai ban shirya ba”
Wani shiri zakiyi Nadiya banda wanda nake shirya maki, na roke ki ki bari na faɗa ma baba tunda ina da aikin yi” shekara daya kenan daya fara aikin costom
Soyayyar mu da ya Yusif tun na kuruciya ce har girman mu tun iyayenmu na daukar ta a shirme har ta zama ta gaske, matsala ɗaya ce kawai muke fuskanta shine goggo fatima kwata kwata bata son taraiya ta da ya yusif shi kuma duk yanda take nuna mashi bata so ya gagara rabuwa dani ko ince mun gagara rabuwa da juna,soyayyar da muke ma juna daga indallahi ne, baya jin ƙyashin kashe min ko nawa ne, duk ranar birthday na yakan ciko mani akwati da kaya sannan ya daukeni zuwa duk wurin shakatawa mu dawo da tsaraba fal hannuna, idan kika duba dakina kalolin akwati ne kala daban_daban wanda duk shekara ya Yusif yake bani gift
Bana taba rasa kudi cikin account dina daga lokacin dana kai shekara sha shida duk karshen wata dubu talatin yake saka min, duk wani sabon kaya na yayi komai tsadar shi sai ya yusif ya saya min,
Tafiya muke a hanyarmu ta dawowa daga islamiyya dukkan su sanye suke da nikaf ni kadaice bansa ba ko hijab dina baikai kasa ba tun malamai na min faɗa har suka gaji suka kyaleni, ansha kora ta gida kuma bai hana gobe na tafi da fuskata buɗe,
“Nadiya wannan mutumin kullum muka biyo hanyar nan ya kama binki da kallo kenan har mu bace mai” shamsiyya ta faɗa
Dago idona nayi na kalle inda take faɗi, caraf idona ya faɗa cikin na wani matashi dake zaune kofar gidan biredi,gabana ya faɗi, duk da a zaune yake amma daga ganin shi dogo ne karfaffe ba bari bane kuma baza,a kira shi da baki ba kalar fatan shi mai kyau ne,fuskarshi kuma yana min yanayi da fulani kamar yanda sumar shi take a nannade irin nasu, sai dai yanada manya manyan idanu farare tas da yake lumshe su, fes yake cikin riga t.shirt baƙa da wando fari, hararen shi nayi tare da mishi tsaki bayan na gama kare mashi kallo, na kauda kaina,
[02/10, 8:53 pm] +234 816 330 9566: *🛖🛖FAƘIRII🛖🛖*
*DAGA ALKALAMIN ✍️*
*Khadeeja Umar*
(Ummu hamnat)
*Page 11&12*
Not edit
Kuka nake rerawa tun shigowa ta gida Sale kuwa yasha allah ya isa, mama ce data gaji da jin kukan da nake ta leko “ban ce kimin shiru ba, ranki zai baci nadiya, idan kin kwaso iskancin ki ba inda kike saukewa sai kaina, mai ya hana shi Yusif ɗin ki tsaida shi ki mishi kuka saini da kika raina, to wallahi ranki zai baci”
Cikin kuka nace “Mama ba wannan almajirin bane ya aiko kirana na zatan ya yusif ne shine da ya yusif yazo sai yace yana sona a gaban ya Yusif, na ƙara rushewa da kuka”
Tafa hannaye Mama ta shiga yi “inna lillahi wa inna ilaihir raji,un yanzu Nadiya bazaki fasa halin ki ba, shi almajirin ba mutum bane,kika sani ko shine mijin naki”
Wani sabon kuka nasa harda shure_shuren kafafuna “bana son shi bana son shi na tsane shi kuma allah ya isa idan ya kara zuwa wuri na”
Dariya mama tayi “sai kiyi amma ki tabbatar kafin isowar Babanku kin ma mutane shiru” nan ta barni ina ta tsine ma Sale da yasa ya Yusif yayi fushi ya tafi bamu ko gaisa ba
___________ Tun daga wannan rana kullum Sale sai yazo, wata ran in fita wata ran duk faɗan Mama bana zuwa, kamar yau ina zaune da littafin riyadus salihin ina nazarin inda Baba ya kara biya min kafin ya fita, yaro yayi sallama
“Ana sallama da ya Nadiya a waje” yaron makocin mu bilal ya faɗa
Ɗago kaina nayi na zabga mashi harara da manyan fararen idanuna “bace ka bama mutane wuri, kace bana zuwa”
Mama dake tsintar wake zaune kusa dani kai ta girgiza “allah ya shirya ki”
Baki na turo na cigaba da karatuna, don nasan ba kowa bane sai naceccen Sale ne don idan ya Yusif ne a waya yake kira na, Baba ne ya shigo
“Barka da dawowa Baba”
“Yawwa mamana” har ya wuce ya waigo “bakece ake jira bane a waje”
“Kila kai zataji maganar ka tun ɗazon yaron nan ke tsaye waje” mama ta faɗa tana mikewa
Fasa shiga ɗaki yayi ya juwa waje ya daɗe kafin ya dawo,
Wata shakuwa ce ta shiga tsakanin Sale da Baba ban san abunda ya shiga kan baba ba ,kullum cikin yabon kyawawan halin Sale yake, ni kuma yana shan wulakanci a wurina, wani abun mamaki tunda Sale ya fara sallama kofar gidan mu ba wanda ya kara sallama dani daga cikin masu zuwa wurina, tun ina mamaki har yanzu tsawon wata hudu da muke tare,
*Ranar da bazan manta dashi ba*
Cikin ɗoki nake shirina na tarban ya yusif dazai zo yau , don marabin mu da juna sati huɗu kenan ya tafi wurin aiki sai jiya ya dawo, Mama ko sai dai ta kalleni ta girgiza kanta, ba daɗewa ya iso cikin gida ya shigo ya gaida Mama sannan muka fita inda muka saba zama kofar gida, hiran mu muke hankali kwance cikin nishaɗi tare da begen juna, kwatsam kiran waya ya shigo wayar ya yusif da farko share wayar yayi har ta katse wani kiran ya ƙara shigowa wannan karan ma ganin baya da niyyar dauka yasa nace “ya yusif ka dauka mana kasan ko wanene”
Sai da yayi tsaki sannan ya zaro wayar cikin aljihun shi ganin ƙanwar shi ce maryam yasa ya dauka da hanzari “ya akayi ne Maryam?” ya tambaye ta bayan ya amsa wayar
“Yaya umma ce bata da lafiya ga tanan bata numfashi”
Da sauri ya zabura ya mike “ganinan zuwa yanzun nan
Ganin yanda ya tashi hankalin shi tashe yasa nace “lafiya ya yusif?” nima ina mikewa
“Umma ce ba lafiya yanzu zan tafi”
Cikin halin ko in kula nace ” allah yasa ma ta gangara sai muyi auren mu hankali kwance”
Baki da ido ya buɗe cikin matukar mamaki “umman tawa kike cema ta mutu ki huta”
Ɗaga kafaɗa nayi ” to meye ai itace bata son auren mu, ni kuma duk wanda baya son mu tare banki ya mutu ba”
“Daga yau karki kara tunanin kin sanni, bani ba ke” ya faɗa cikin ɗaga murya
Nima cikin jin haushin yanda yake wani ɗaga min murya don nace allah yasa umma ta mutu ai nima ba kauna ta take ba “sai me don ka rabu dani, idan ka cika yusif kar ka kara zuwa wurina” tsaki na buga mai na shige gida,
Daga wannan rana kamar wasa rabuwar mu ya tabbata dalilin yanda kanwar shi da taga yanda ranshi yake bace ta tambaye shi, shine yake fada mata yanda mukayi ashe lokacin Umma ta tashi daga alluran baccin da likita yayi mata, “idan har ni na haife ka na raba ka da ita har abada koda ita kadaice tayi saura mace a duniya, koda bayan raina ka aure ta ban yafe maka ba” shine kalmar da ta sauka a kunnuwansu, ba karamin gigicewa yayi nan take ya zube gaban ta yana rokon ta ta tausaya mashi wallahi yana kaunar nadiya tamkar ranshi raba su kamar sabauta mashi rayuwa ne, haka umma tasa ma idonta toka taki kara kula shi, wannan shine mafarin komai,
Ni kuma a nawa fanni hankalina kwance saboda nasan mun saba haka da ya yusif kwana biyu albarka zai nime ni, inda hankalina ya fara tashi shine tsawon sati biyu ba ya yusif ba labarin shi idan na kira shi awaya bata shiga tun ban damuwa har Mama ta fahimci halin da nake ciki,
“Lafiya kike nadiya kwana biyu kamar baki da walwala,ko wani abu ke damun ki” mama ta tambaye ni cikin kulawa
Rau rau da ido nayi “mama y yusif”
“Mai ya samu yusif ɗin”
“Tun ranar da mukayi faɗa bai kara kira na ba kuma idan na kira shi baya shiga lambar shi” ina shirin sakin kuka
“To allah yasa lafiya don yusif baya da riko, amma kin kira Maryam kin tambaye ta?”
“Itama bata daukar wayar”
“To allah ya kiyaye”
Da yammaci sai ga bakunci goggo fatima zuwan da zan kirashi da bakar tafiya, a wannan ranar nayi dana sanin taraiyata da ya yusif, a wannan ranar nama kaina alkawarin koda ya yusif shine autar maza na hakura dashi, saboda cin mutuncin da goggo fatima tama Mama, ta kirani da mara zuciya natacciya mai kwaɗayi ba kalar rashin mutuncin da bata shuka ma mama ba, hawayen da na gani fuskar mama yasa naci alwashi na rabu da yusif har abada kamar yanda goggon fatima tace idan na cika ƴar halak na rabu mata da yaro ta mashi mata,
Daga lokacin komai ya kare a tsakanin mu farko nayi rashin lafiya don rabuwar mu da ya Yusif sai da Baba ya dinga haɗa min da nasiha da rarrashi, don baba na dawowa Asim ya labarta mai komai, kai kawai ya girgiza tare da cewa allah ya kyauta, sannan ya hada mu ya mana nasiha da kar mu rike abunda goggo fatima ta mana, mu cigaba da girmama ta wata ran sai labari,
Ban haɗa shekara da rabuwa da ya Yusif komai ya fita a kaina dangane dashi, tabbas Sale yacire tuta akan hakurin shi a kaina duk wulakancin da nake mashi bai sa ya rabu dani ba,a lokacin da nake cikin jin zafin rabuwa da ya yusif duk wani zafina akan Sale nake saukewa shi kuma sai dai ya bini da murmushi, saboda hakurin shi har gashi yau Sale shi ke rike da zuciyata,
Ban faɗa maku yanda sunan Sale ya koma Faƙiri ba ….
[02/10, 8:53 pm] +234 816 330 9566: *🛖🛖FAƘIRII🛖🛖*
*DAGA ALKALAMIN ✍️*
*Khadeeja Umar*
(Ummu hamnat)
*page 9&10*
Kwanaki sun cigaba da tafiya babu ranar dazan fita wa lau islamiyya sai naci karo da wannan matashin da muka gani kofar gidan biredi,magana bai taba haɗani dashi ba sai dai idan mun haɗa ido na bishi da harara shi kuma yayi min murmushin dake karamin haushin shi,
“Nadiya zo ki kai ma mallama safiyya kayan nan” Mama take bani sako wurin ƙawarta
Fitowa nayi cikin adona kamar ko yaushe don allah yayi ni da son kwalliya kamar me, “mama daga nan zan biya gidan su billy karki ga na daɗe”
“To ki kula dai karki kai dare”
Ina fitowa daga gida da fuskar matashin saurayin nan naci karo yana zaune kan wani dutse dake tsallaken kofar gidan mu, gabana naji ya faɗi muna haɗa ido dashi, murmushin shi daya saba min shi yayi, da hanzari na kauda kaina, har lokacin gabana bai bar faɗuwa ba, yi nayi kamar zan wuce sai wata zuciya ta bani shawara naje naji matsalar wannan bawan allah da kullum yake bibiyata
“Assalamu alaikum” na faɗa bayan na isa kusa da inda yake zaune
Kauda kanshi yayi cikin mamakina sannan ya amsa “wa,alaikis salam” ya faɗa cikin sanyayyar muryanshi daya dakar min zuciya
Duburburcewa nayi duk abunda na shirya faɗa mashi ya goge a kaina, jakan hannuna na buɗe na ciro dubu biyu na miƙa mashi “gashi bawan allah idan taimako kake nima kabar bina”
Murmushi yayi tare dasa hannu ya amsa “nagode” shine kalmar daya faɗa min idon shi cikin nawa
Da sauri na kama tafiya nabar wurin tare da mamakin amsar kuɗin da yayi don ban zata ba, keke napep da yazo wucewa na tare na shiga, mai keke napep na shirin tashi aka tare shi matsawa nayi gefe don bama wanda zai shigo wurin zama,
Zaro ido nayi cikin kaɗuwa ganin wanda na bari zaune shi ya shigo ba tare da kula da yanda na firgita ba ya zauna kusa dani, kakkama jikina nayi cikin tsoron abinda yasa ya biyoni, waigowa yayi ya kalle ni da wannan dan iskan murmushin nashi, wani tsoro ne ya kara kamani da sauri cikin rawan murya nace “zan sauka anan mallam tsaya”
Me keke napep ya juyu “hajiya magana kike?”
“Ce maka nayi ka sauke ni anan” na kara maimaitawa
Ina kokarin fita daga keka napep din naji maganar data kusa kadani kasa don sai dana dafa jikin napep din *”INA SONKI”* shine sautin daya shiga kunne na daram dan dam shine abinda da kirjina yake bugawa
Na dauki wasu seconds kafin na daidaita kaina tare da bama kaina dariya kila yanzu haka waya yake ba dani yake magana ba ato idan ban da shirme na ta yaya daga ganina haka siddan yace yana sona ba wani kalmar ba wata romance a maganarshi sai zikwai yace yana sona, kokarin mika ma mai keke napep kuɗin shi nake saboda na tari wani,
“INA SONKI, rike wannan a ranki”
Ban samu zarafin karasa mika ma mai keke napep kuɗin ba suka faɗi saboda idona da suka faɗa cikin nashi da yanda yayi maganar idon shi cikin nawa, baya baya na fara ja don yanzu kan na tabbatar wannan mutumin baya da cikakkiyar hankali.
__________zaune muke muna cin abinci tare da Mama, kwatsam wani tunani ya faɗo man a zuciya bansan lokacin da na kwashe da wani irin dariya ba har ina kwarewa, ido suka sa min cikin mamaki Nazir yace “lafiya kike ya Nadiya”
Dariya ta na cigaba dayi
“Mama ce cikin jin haushin wannan dariyar da nake tace “bana son shashanci wani irin dariya ce kike ma mutane haka?”
“Kin san wani abu ko mama, shekaranjiya da kika aike ni gidan mama safiyya wani almajiri ya tare ni wai ni yake so” na karasa faɗa ina sakin sabon dariya
Tsaki mama tayi “to shi almajiri ba mutum bane, ko kinfi karfi tsayawa da irin shi”
Bata rai nayi “haba mama mai zanyi dashi ni da nake da ya Yusif ɗina”
“Uhm abunda dai kullum nake faɗa maki shine ki rinƙa rokon allah zabinshi na alkhairi ba son ranki ba, domin duk yanda kika kai da son abu, idan har ba alherin ki bane ba,gara ki hakura dashi” mama na gama faɗa min ta mike
Gunguni na kama don ina kula da mama idan na kawo maganar auren mu da yusif sai tana min faɗa kamar bata son tarewar mu dashi, duk da bata taba nuna mana a fuska ba ko da wasa balle yanda take mu,amala da yusif ba ruwan ta da abinda goggo fatima take min
Lekowa mama tayi “idan kin gama zagin nawa, ki tashi muyi wancan aikin da wuri kinsan yau baban ku zai dawo”
Muna gama aikin da sauri na shiga wanka don nasan ya Yusif na hanyar zuwa,lokaci mai tsawo na bata ina kwalliya don kawai na burge masoyina , ina cikin daura dan kwali yaro yayi sallama “ana sallama da Nadiya inji wani mutum”
Kallon karamar wayata nayi don nasan ya Yusuf a waya yake kira na idan yazo, ganin tana kunne yasa mamaki ya kamani, “kace ina zuwa”
Sai dana kara feshe ma jikina turare sannan na yafa mayafina dakin mama na shiga na fada mata ,
Waige waige nake ina niman motar ya Yusif amma ban gani ba, ciro waya ta nayi don kiranshi inji inda ya boye , daga baya na naji wata sanyayyar muryan dake faɗar min da gaba yayi min sallama, da sauri na waiga hada ido nayi dashi yana zaune kan dakalin kofar gidan mu,
Matashin rannan ne waigawa bayana nayi don gani ko da wani yake amma banga kowa ba, juyar da kaina gefe nayi zan koma gida naji sautin muryan shi
“Ni na aika kiran ki” wannan karan ya mike tsaye yana doso inda nake
Mamaki ya kama ni wannan mutumin akwai karfin hali amma bari naga gudun ruwan shi,don yau tsaf na shirya mashi rashin mutunci
“Sunana sale” shine kalmar da ya fara faɗa min
Na bude baki ina shirin fara mashi ɗiban albarka naji tsayuwar mota inda muke, wanda babu makawa ya Yusif ne, gabana ya faɗi don banso ya sameni dashi ba, yana gama parking wurin mu ya doso fuskar shi daure,
“Wanene wannan Nadiya?” shine abunda ya fara faɗa
Nan take na ruɗe don nasan yanzu zai fara fushi baya kaunar yana ganina da kowani namiji,
Sale kuma hannun shi ya rungume a kirji yana kallon mu yana jiran yaji amsar da zan ya Yusif,
“Almajirin ne fa dear, wankin takalmana na bashi wankewa yanzu ya kawo min shine nake tambayar shi kudin shi nawa zan bashi” na faɗa cikin yar rudewa.
Hannu ya Yusif yasa cikin aljihu ya ciro kudi ya mika ma Sale, ido ya kura ma ya Yusif yaki amsar kudin, cikin jin haushi ya Yusif yace “don allah mallam ka amsa ka bama mutane wuri” ni kuma ina gefe hankalina tashe ina allah _allah ya wuce
Maida kallon shi kaina Sale yayi na tsawon minti daya sannan yace “ki rike wannan a ranki INA SONKI…
Kuyi hakuri jina shiru kwana biyu da kukayi, bana da lafiya ne, ga wannan mu hadu gobe insha allah.
[02/10, 8:53 pm] +234 816 330 9566: *🛖🛖FAƘIRII🛖🛖*
*DAGA ALKALAMIN ✍️*
*Khadeeja Umar*
(Ummu hamnat)
*Page 13*
Kamar yanda hausawa ke cewa a rashin uwa akanyi uwar ɗaki to shine ya sani fara sauraran Sale ba wai ina wani son shi ba, da nufin idan na samu wani zan sallame shi, gashi kamar wanda ya asirce ni tun da fara zuwan shi wurina har yau ko kare bai sake sallama dani ba, wannan abun na bani mamaki wani lokaci har ina alakanta rabuwar mu da ya Yusif da Sale ne ya raba mu
________ mikewa tsaye yayi “zan tafi sai gobe insha allah don yau gidan biredi biyu nama aiki shi yasa na gaji dayawa ba karamin aiki nayi ba, da kyar na haɗa dubu ɗaya”
Wani malolon bakin ciki ya kamani wai dubun da bai wuce na bashi kyauta ba shine yake faɗa min sai daya yini sannan ya same su, hararar shi nayi tare da tsaki na juya baya na shige gida ko magana ban mashi ba tsabar harakata
Da murmushi ya rakata,
Ina kumburi na shiga gida zaune na samu Mama zama nayi kusa da ita ina saƙin tsaki, mama ce tace “lafiya kika shigo kina ma mutane tsaki”
“Ni da wannan FAƘIRIN ne mana wai duk yini yau aikin dubu yayi shine yake faɗa min don haushi wai ya gaji, to ina ruwana da gajiyar shi”
“Wannan wani irin suna ne kike kiran bawan allah da faƙiri, bana son haka daga yau kar na kara jin kin kira shi da wannan sunan”
Turo baki nayi “to mama idan ban kira shi da FAƘIRI mai zan kira shi dashi, kina gani fa sai yayi zuwa goma ko sisi baya bani idan ma ya bani baya wuce dari biyu don allah ji abun dariya” na karasa faɗa ina dariyan haushi
Nazir da Asim da suke cin abincin dare yace “wallahi Mama sunan FAƘIRI shi ya dace da shi” dariya muka kwashe dashi
Itama Mama murmushi tayi “bana dai son kara jin wannan suna”
“Aiko Mama daga yau sunan shi kenan sai dai kiyi hakuri” na faɗa ina juna kaina jefe
Girgiza kai tayi “allah ubangiji ya shirya ki Nadiya”
**********
Rayuwa ta cigaba da gungura mana da daɗi da ba daɗi tare da FAƘIRI kamar yanda na maƙala mashi da karfi da yaji, har gashi na kammala makaranta duk da a lokacin bikin gama makarantar tawa yayi kokoari don ya saya min turmin atamfa da hijab tare da kayan kwalliya ,
Yanzu haka muna dan ɗasawa dashi duk da wani lokaci idan hali ya motsa min yakan kwashi wulakanci idan na tuna dalilin shine na rasa ya Yusif da sauran samarina ,
Kare min kallo yayi daga sama har kasa, tsaki yayi “yanzu kin kyauta kenan?”
Turo baki nayi cikin shagwaba “to ni me na maka yau?” ganin kallon da yake min nasan ranshi ba karamin baci yayi ba, kuma nasan ba komai bane ya bata masa rai sai yanda na fito yafe da mayafi sannan ina fitowa nayi tuntube takalmi na ya tsinke, kuma karin daɗawa banyi wanka ba don faƙiri kamar mai gani har hanji yake duk randa na fito wurin shi banyi wanka ba sai ya gane koman turaren dana fesa,
“Ki tafi gida zan aiko maki da takalmin, tunda ke bakijin magana ta”
Tabe bakina nayi cikin ko in kula na juya gida, ban daɗe da shiga gida ba yaro yayi sallama ya shigo, bakar leda ya mika min
“Gashi Sale yace na kawo maki”
Kamar nayi cikin farin ciki don da gaske bana da wasu takalmi don duk takalma na da ya Yusif yake saya min duk sun lalace ,wani sabon bacin rai ya ziyarce ni ganin abunda yake cikin leda, takalmin roba irin baƙin nan na dari uku, bansan lokacin da nayi wurgi da ledar takalmin ba, ina fashewa da kukan bakin ciki,
Daukar takalmar Mama tayi “allah yayi ki da iya shege Nadiya yanzu ina laifin don ya sayo maki waƴannan takalmin, kinsan wahalar daya sha kafin ya samu kuɗin, kici gaba da wannan halin, shima idan kika kore shi sai ki zauna cikin gidan tare dani”
Kuka na fashe dashi ina turmuza ƙafa ta “ni nasan yanzu Mama kin bar sona sai wannan faƙirin, duk abunda yayi min baki ganin laifin shi sai nawa, gidan zan bar muku”
“Kifi ruwa gudu ina nan duk inda kikaje zaki dawo ki same mu” shigewar ta ɗaki tayi ta barni wurin ina kuka
________ kiran waya ne keta shigowa cikin wayata ina kashewa don har yanzu ina tare da haushin shi, wannan kira shine karo na biyar daya kira ni abunda bai taba yi ba, faƙiri duk yanda yakai da matsuwa dasun magana dani baya kirana sau uku, idan yayi min kira biyu ban dauka ba, baya kara kira, sai dai ni idan na mashi flashing, daukar wayar nayi tana shirin tsinkewa, shiru nayi bayan daukar da nayi
Murmushin shi mai sanyi yayi wanda har cikin waya sai danaji, sallama yayi min, ciki_ciki na amsa “kina lafiya?”
“Lafiya” kawai nace
Daga yanda na amsa mashi sallama yasan akwai wani abu a kasa “tun bayan komawata gida raina yake a bace, gashi yanzu na gagara yin bacci, tun da naga haka nasan ba komai bane ya jawo min haka sai mamallakiyar zuciya ta, sanar dani wanda ya bata mana rai daya hana mana bacci”
Duk yanda nakai da rashin son faƙiri bansan lokacin daya shiga zuciya ta ba, kuma ba komai bane ya jawo haka sai iya kalaman shi, sannan yasan duk salon yanda zai tafiyar dani a kowani lokaci, idan raina yana bace kamar wanda yake gani har hanji yanzu zaki ga ya kira ni, kuma bazai samu sukuni ba sai yaga na saki raina sannan hankalin shi zai kwanta
“ba kai bane” na faɗa cikin shagwaba
“To ni kuma, duk da bansan laifi na ba, ina niman afuwa kafin na iso don komai dare bazan iya bacci ba sai naga farin ciki ya wanzu saman fuskar ki”
Da sauri na tare numfashin shi don sarai nasan faƙiri tunda yace zai zo ba fashi sai yazo,kuma yanzu karfe goma da rabi na dare, “don allah basai kazo dare yayi kuma na hakura”
“A,a ban yarda gani nan zuwa sai ki faɗa min laifi na”
“Bafa komai bane, ni bana son wannan takalmin da sayo min”
“Shine matsalar? ki shirya gobe idan allah ya kaimu kije shagon kawu Bashir zan faɗa mashi sai ki zabi na dubu biyu, shi kenan an wuce wurin ko,?”
“Eh”
“To yimin murmushi ko zanyi bacci cikin salama” …..
Name: | [Fakiri Hausa Novel] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Leave a Comment