Falalar Kwanaki Goma Na Watan Zhul-hijjaa 

Falalar Ƙwanaki Goma Na Watan Zhul-hijjaa

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tabbas Waɗannan Ƙwanakin Farko na Watan ZHUL-HIJJA Suna da Wasu Abubuwa Wanda Suke Muhimmai Ne, Wanda Babu Wasu Ƙwanaki da Suke dashi, Sabida takaitawa mai Karatu Zamu Kawo Kaɗan daga Cikin Su, ga Sunan Kamar Haka:

Lallai Allah Maɗaukakin Sarki yayi Rantsuwa da Waɗannan Ƙwanakin a Cikin Littafin sa Mai Girma da Ɗaukaka inda yake Cewa, (Walfajr-Walayyin Ashr) ba Ƙoƙwanto Akan Cewa Rantsuwa da Waɗannan Ƙwanakin yana Nuna Falalar Su da Darajar a Wajen Allahu Swt._ _Allah Maɗaukakin Sarki ya Ambace Su da, (Ƙwanaki Sanannu) Kuma ya Shar’antawa Ɓayin Sa da Su Ambace Su a Cikin Ambato na Musamman, Inda Allahu Swt yake Cewa, (Kuma Ku Ambaci Allah a Waɗannan Ƙwanaki Sanannu) duba Cikin Suratul Hajji Ayata (28)._

 

Kasancewar Su Ƙwanaki ne da Allah yafi Son Aiki a Cikin Su Fiye da Wasu Ƙwanakin, Kamar Yadda ya Zo a Cikin Hadisin Abdullahi ɗan Umar Allah ya Kara yarda Gare shi inda yake Cewa, Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi yana Cewa, (Babu Wasu Ƙwanaki da Suke da Daraja a Wajen Allah Kuma Aiki a Cikin Su yafi Kowanne Soyuwa a Wajen Allah Fiye da Waɗannan Ƙwanaki na Watan ZHUL-HIJJA, don haka Ku yawaita yin Kaɓbara da Hailala da Tahmidi a Cikin Waɗannan Ƙwanakin)._

 

Kasancewar Su Sun fi Falala da Daraja akan Ƙwanakin Karshe na Watan Ramadan Kamar Yadda Shekhul Islam Ɓin Taimiyya ya Faɗi yayin da aka Tambaye Shi Wanne yafi Falala a Tsakanin Su, (Goman Karshe na Watan Ramadan, da Kuma Goman Farko na Watan ZHUL-HIJJA) Sai ya Amsa da Cewa Ƙwanaki Goman Farko na Watan ZHUL-HIJJA Sune Suka fi Falala akan Ƙwanaki Goman Karshe na Watan Ramadan, amma Ɗararen Goman Karshe na Watan Ramadan Sun fi Ɗararen Goman Farko na Watan ZHUL-HIJJA Falala._

See also  Wankan Janaba Yanda ake wankan Janaba da rabe rabensa

Karanta Tarihin Annabi Yusuf

Domin A Cikin Su Akwai Aikin Hajji Wanda yake Shi Rukuni ne daga Cikin Rukunan Musulunci._ _Wannan Kaɗan Kenan daga Cikin Abubuwan da Waɗannan Ƙwanaki Goma Na Farkon Watan ZHUL-HIJJA Suka Keɓanta da Su, Sannan Akwai ibadu da Ake son ayi Su a Cikin Waɗannan Ƙwanakin Wanda Shari’a ta yarda da hakan._

 

_Mu Haɗu a Rubutu Na Gaba Insha Allahu._

 

*_Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah WhatsApp Group._*

 

*_TELEGRAM_*

https://t.me/zaurenmuslimwomenmatazallah

 

*_FACEBOOK_*

https://facebook.com/groups/627525074709973

 

*_MUHAMMAD TUKUR JALINGO_*

Domin Shiga Wannan Group Ki Turo Mana Da Cikakken Sallama, Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Kai Tsaye Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka

08164223447 Or 08151796429

This Group Is Only For Women Please.

1 thought on “Falalar Kwanaki Goma Na Watan Zhul-hijjaa ”

  1. Assalamu alaiku ykk ya aiki gaskiya najidadin wannan littafi allah yakara lpy da basira daga aminatu m isma il garo nagode

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top