Hausa Novels

Farin Cikin Rayuwa Complete Hausa Novel

Farin Cikin Rayuwa Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag:  FARIN CIKIN RAYUWA

 

 

 

*STORY AND WRITTEN*

BY

 

*RAHEENAT M ABBAKAR*

_(Meeraheenat)_

 

 

_Da sunan Allah me rahama mai jin k’ai_

 

 

 

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata’ala, tsira da aminci su k’ara tabbata ga annabinmu, farkon k’aga k’arshen aika wata annabi Muhammad s.a.w*

 

 

*Komai tsanani komai wuya Allah shine abin godiya, bazan tab’a gajiyawa ba gurin fad’in _Alhamdulillahi_ , domin Allah shine ya ara min rai da lafiya har na kawo wannan lokaci, ikonsa ne har yasa na d’aura hannayena da sunan fara rubuta wannan labari, na gode wa Allah na sake gode masa, ya Allah ina rok’onka dan isa da ikonka yanda na fara rubuta wannan litttafi lafiya kasa na kammalasa lafiya, Allah ka saka min hannu kar ka barni da iyawata, ya Allah ka kaifafa tunanina ka tsarkake min harshena, ka nufe ni da rubuta Alkhairi ka hane ni rubuta sharri, ya Allah kasa duk wanda zai karanta wannan labari ya amfana da ko da kalma d’aya ne, ya Allah karka nufe wani da karantawa lokacin ibadunka ameen*

 

 

 

*Tabbas na ga masoyan k’warai, sosai Allah ya nuna min masoyana wanda duk iya wuya muna tare, dama wai haka soyayya take ? Sai kaji ana fad’in ina sonki, ina yinki, kina bada kala, jinjina gareki, ashe wai duk rubutunki ake ma wannan ba ke ba, tabbas masoyi yana nufin wanda zai kasance tare da kai cikin ko wani irin yanayi, wanda zai iya amfani da dukiyarsa k’arfinsa a kanka ba tare da yaji ko d’ar a ransa ba, wanda zai saka farin ciki ko da shi baya ciki, wannan shine ake kira da masoyi, duk wanda ba zai iya cire wani abu daga aljihunsa ya siya wani abu da ka kasa dan ka k’aru dashi ba wannan be cancaci kiran sunansa masoyi ba, dama rubutun namu ake so bamu ɗin ba, bana da ra’ayi na siyar da novels ɗina, to amma sai na ce bari na jarabawa masoyana, to adai yi walƙiya ta haske idanun kowa, duk ina godiya sosai ga wad’anda suka cire kud’insu su siya novel d’ina, Allah ya bar k’auna na gode na gode, a ci gaba da gashi masoya*

 

 

_Jinjina ta musamman tare da tukwicin ƙauna wanda shi ma yake na musamman ga masoyana na ƙwarai, wanda suka iya cire kuɗin aljihunsu suka sai littafaina, na gode na gode Allah yabar ƙauna, haƙiƙa na amince ku ɗin masoyan Raheenat ce na ƙwarai, kun nuna min ƙauna da soyayya, kunyi haƙuri dani tare da yi min uzururruka a dukkan nawa ta, na gode muku sannan ina yi muku fatan alkhairi a rayuwarku da zuriarku, wallahi har cikin zuciyata nake ƙaunarku kuma nake alfahari daku, ku ɗin kun zamto tamkar ƴan uwana na jini, one love guys

 

 

 

 

Sadaukarwaka ga familyna

 

_Wannan karan sadaukarwar taku ce ƴan uwana abin alfaharina, ko yaushe kuna maƙale a zuciyata kun zamo bugun numfashina, kune ni, ina sonku kuma ina alfahari da kadancewarku ƴan uwana kuma jinina, Allah ya ƙara ƙarfafa mana zumuncinmu ya ƙara haɗa kawunan mu ya kuma kau da shaiɗan a tsakanin mu ameen ya rabbi_

 

 

 

Page 1

 

 

 

 

Kano state 5:30pm

 

Yammaci ne me cike ni’ima sabida iskar da yake kaɗawa me daɗi, tuƙi takeyi cike da natsuwa yayin da karatun Alqur’ani ke tashi a cikin motar ƙasa-ƙasa, tuƙi takeyi idanunta na zube bisa kwalta, yayin da wacce ke zaune gefenta take waya cikin ƙasa da sauti fuskarta na bayyana murmushi wanda zai yi maka nuni da tana jin daɗin wayar da takeyi ɗin, duk da cewa idanunta da nutsuwarta na saman kwalta amma rabin hankalinta na kan wayar da *Zeey* ɗin keyi wanda babu abinda wayar ke sakata sai jin takaici, a hankali ta kai hannu ta ƙara volume ɗin ƙira’ar dake tashi a motar wanda dama Zeey ɗin ce tayi ƙasa dashi sabida wayar da takeyi, tana ɗauke hannunta Zeey ta kai nata hannun ta ƙara yin ƙasa dashi, da sauri ta ɗaga fararen idanuwanta ta watsasu bisa fuskar Zeey ɗin tana jifanta da wani kallo tare da sakin tsakin da yayi dai-dai da tsaida motartata da tayi.

 

Ita ma Zeey kallonta tayi tare da kallon inda ta tsaida motar sannan ta dawo da kallonta kanta tana me yin sallama da wanda suke wayar, saida ta ɗaura wayar bisa cinyarta sannan ta buɗe baki tace “meye na tsaida mu bisa hanya kuma *Maryam* ? Sannan wai meye matsalarki da wayata ce.?”

 

Idanunta na kan Zeey tace cikin wata irin tattausar murya “na tsayar da motar ne dan ki fice min a moto matuƙar zaki ci gaba da wayar, maganar matsalata da wayar ki kuma kin fi kowa saninta, kunnuwana sun gaji da sauraron yaudararrun kalaman ku daga ke har shi wanda kike ikirarin zaki aurar, haba! Duk babu komai a zuciyarku sai ƙarya da yaudara! Kowa abinda ke zuciyarsa daban abinda bakinsa ke faɗa daban! To ni na gaji, in zakuna wayarku ki daina yi a gabana daga yau, in ba haka ba komai na iya faruwa, na tsani ƙarya wallahi!.”

 

Karanta Littafin Yarima Ashman

Kallon ƙaramin bakinta da take maganar Zeey keyi tunda ta fara har ta dasa aya, murmushi ta saki me sauti tace “Maryam wai me yasa ke abokiyar adawata ce ne ? Meye na ƙarya da yaudara anan dan Allah.?”

 

Wani kallo ta jefi Zeey dashi tana sakin wata guntuwar tsaki tace “ai har kullum zan ci gaba da zama abokiyar adawarki matuƙar baki sauka akan wannan banzan aƙidar naki ba, ƙarya da yaudara kuma ai shine abinda ya cancanci kiran kalamanku dasu, domin yaudarar junanku kukeyi akan kuna son juna, kuce dai kuna son abubuwan juna, wallahi ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba bakya son Alhaji Ahmed, kuɗinsa kike so kamar yanda shi ma surar jikinki da kyawunki shine abinda yake so kuma yake ruɗarsa, Zainab kullum dai ina faɗa miki kuɗi ba sune *farin cikin rayuwa* ba, ki tsaya kiyi tunani da kyau.”

 

 

Murmushi Zeey ta kuma saki tana gyara zamanta tace “Diyana tawa, kina bani mamaki wallahi, taya ma zaki ce kuɗi basu ne *farin cikin rayuwa* ba, kuɗi sune komai Hajiya, in kana da kuɗi za kayi komai haka ma zaki iya yin komai, duk wanda kika ji ya ce kuɗi ba suyi ba to be san daɗinsu bane, in kana da kuɗi zaka taka wanda ka so kayi abinda ka ga dama babu me tanka ka, yes! Kuɗin Alhaji Ahmed nake so domin ko yana dasu, na tabbata in na auresa zan huta in fantama yanda nake so, zan hau duk motar da naso na ga dama, sannan in zaga duk ƙasar da na ke so, na saka suturar da na ke so, na taka wanda na ke so, nayi abinda na ke so, to ki faɗa min in ba kuɗi ba meye zasu yi min duk wannan.?”

 

Numfashi Maryam ta sauke tana sakin murmushi da ya bayyanar da tsantsar kyawunta, cikin sanyin ta da zaƙin sautinta da Allah ya hore mata tace “kullum dai tunaninki kenan Zainab, eh kuɗi suna iya saka mutum yayi komai, kuma kuɗi in kana dasu za kayi komai, sannan duk abinda kika zana kuɗi za suyi miki su tabbas, to amma abinda nake so ki sani shine abubuwan da kika zana basu kaɗai ne mutum ke da buƙatar su a rayuwa ba, kuma basu kaɗai ne zasu baiwa mutum farin ciki da nutsuwar da yake so ba, har yanzu dai ni dai ina nan a kan bakana kuɗi basu ne *farin cikin rayuwa* ba, akwai farin cikin rayuwar da kuɗi ba zasu baki ba, sannan akwai farin cikin da kuɗi ba zasu iya siya miki ba, amma tunda kin gaza fahimtata muje a haka, kowa ya tsaya akan aƙidar da yake ganin shine masa dai-dai, da sannu rayuwa zata nuna mana wanda yafi gaskiya.”

 

 

Jingina bayanta Zeey tayi a jikin seat tana faɗin “dama haka kika faɗi tun ɗazu da baki tsayar damu kin ɓata mana lokaci kan kwalta ba, ni dai yanzu mu ƙarisa gida dan ina bukatar hutawa.”

 

Girgiza kai Maryam tayi tana tada motar tare da maida ƙira’arta ta bawa motar wuta suka nufi gida cikin zuciyarta tana addu’ar Allah ya ganar da ƙawarta kuma aminiyarta abinda take son ta fahimta……

 

 

 

****

 

 

Kaduna state 2:40pm

 

 

Cikin yanayi na damuwa ta shigo tsakar gidan nasu da sallama a bakinta, mahaifiyarta da ƙanninta da ke zaune suka amsa mata suna binta da kallo suma fuskokin ko wannensu kana kallo zaka san ɗauke take da damuwan, balle yanda suka ga Hafsat ta shigo babu alamun nasara a abinda taje nema, zama tayi kusa da mahaifiyar tasu cike da gajiya da yunwa tace “sannu da gida Mama.”

 

Kallonta Maman tayi tana faɗin “yauwa Hafsat, ba dai nasara yau ma ɗin ko.?”

 

 

Ƙwalla ne ya ciko idanun Hafsat, cikin rawar murya tace “Mama wallahi ko da na je Kawu ko kallon arziƙi beyi min ba, gaisuwata ma daƙyar ya amsa, ko da na faɗa masa buƙatar da ta kawoni wajensa sai cewa yayi shi kuɗinsa bana banza bane balle ya rinƙa rabonsa ga mutanen gari, Mama wai mu Kawu ke kira da mutanen gari.”

Ta ƙarisa tana fashewa da kuka.

 

Ta maza Mama tayi ta maida nata hawayen tana faɗin “kiyi shiru Hafsah ki bar kuka, komai yayi tsanani yana tare da sauƙi, Allah ya san damu, na tabbata watarana komai zai zama labari zamuyi farin ciki da yardan Allah.”

 

 

Hannu ta saka tana share hawayen da suke ta gudu a saman kumatunta tace “Mama sai yaushe ne wannan *farin cikin rayuwar* da kike ta faɗa zai zo ? Mama tun tashina na ganmu cikin wannan yanayi har yau kuma be canza ba, tun Baba na raye muke fuskantar wannan rayuwar har ya bar duniya komai yana nan sai ma ƙara taɓarɓarewa da yakeyi, sai yaushe ne zamuyi farin ciki Mama ? Sai yaushe ne mu zamu ji daɗi ? Anya kuwa Mama zamu risƙi wannan *farin cikin rayuwar.*?”

 

 

Share guntun hawayenta Mama tayi tana faɗin “Rashida kar kiyi saɓo mana, ai ba’a taɓa cire rai da rahamar Ubangiji, in Allah ya so za muyi farin ciki zamuyi ne, in kuma a haka ya rubuta mana rayuwar babu yanda zamuyi, yanzu ma Alhamdulillahi kawai zamu faɗa tunda ya barmu da lafiyarmu, kuma duk halin nan da kike kallonmu ciki akwai waɗanda suka fimu, to kinga ai dole mu gode Allah, kuyi haƙuri da dukkan wani hali da zamu tsinci kanmu a cikinsa, Allah yasan damu, kuma jarabawarsa ce, dan haka sai muyi addu’ar cinyewa.”

 

 

Ita da ƙanninta uku da su ma ke share hawaye suka gyaɗa kansu cike da aminta da zancen mahaifiyar tasu, cikin sanyin murya Hafsat tace “to Mama yanzu me zamu ci.?”

 

Ajiyar zuciya Mama ta sauke me ƙarfi tace “ki tashi ki tattara wancan kwalayen da Abdul ya roro ki kunna wuta ki ɗaura ruwan ɗumi ko shi mu samu mu ƙurba, nasan ƴan hanjinmu zasu warware mu samu sassaucin yunwar da muke ji, sai mu ga abinda Allah zai yi zuwa anjuma kuma.”

 

Jiki a sanyaye Rashida ta miƙe dan aiwatar da abinda mahaifiyarta tace……..

 

 

 

 

****

 

 

 

Zaria 11:30am

 

 

 

 

Wata matashiyar budurwa da bazata gaza shekara sha bakwai ba na hango ta fito daga wani shagon aski dake nan cikin ƴar ƙaramar kasuwar maɗaci dake a cikin garin Zaria hannunta riƙe da roba irin wanda masu saida abinci ke amfani dashi, daga cikin shagon wani saurayi na faɗin “Rashida ki zubo min abincin nima ki kawo min.”

 

Waigowa tayi ta na faɗin “wallahi Dauda yau bana baka abinci ko cokali ɗaya ne matuƙar ba kuɗaɗena ka bani ba.”

 

Cikin kwantar da sauti wanda ta kira da Dauda ya ce “haba Rashida kar muyi haka da ke, kema kinsan zan baki kuɗinki.”

 

Taɓe baki tayi tana faɗin “dama yau muka saba da sai kayi min wannan daɗin bakin.”

 

 

Cikin wata murya na mayaudarar samari yace “ki zubo min wallahi yau zan haɗa miki kuɗaɗenki Ummu har da ƙari matukar zakiyi min yanda aka saba.”

 

Fuska ta washe tana faɗin “da gaske ka keyi Dauda.?”

 

Yana kallon idanunta yace “kinsan dai ba zan miki ƙarya ba ai, ke dai je ki zubo min abincin kawai sauran sai ya biyo baya.”

 

Murmushi takeyi tana me ci gaba da tafiya take faɗin “kadai san masu kauri zaka ƙara, dan bana baka kaya ka kwasa ni kuma ka barni da biya ba ga kuma ciwon jiki.”

 

Dauda yana wata ƴar iskar dariya ya ɗan ɗaga muryarsa yanda zata jisa yace “karki damu, yau aljihuna akwai nauyi.”

 

 

 

 

 

 

 

Muje zuwa

 

 

 

 

 

 

 

Kuna buƙatar na ci gaba ?

 

 

 

 

*To ga Raheenat ta dawo bayan dogon lokaci, ina fatan zamu ɗaura daga inda muka tsaya koma fiye da haka ?Comments naku shine zai tabbatar min da hakan*

 

 

 

 

 

Meeraheenat ce

 

*FARIN CIKIN RAYUWA*

 

 

 

 

 

*TSORY AND WRITTEN*

BY

 

*RAHEENAT M ABBAKAR*

_(Meeraheenat)_

 

 

 

 

 

*SADAUKARWA GA FAMILYNA ABIN ALFAHARINA*

 

 

 

 

PAGE 2

 

 

 

 

Kano

 

 

 

 

Saukowa takeyi cike da nutsuwa daga upstairs cikin shigar riga da wandon Pakistan ruwan pink yayin da ta yi rolling da mayafinsa, jakarta saɓe a kafaɗarta, sosai kayan suka karɓi jikinta kasancewarta me hasken fata.

 

Kai tsaye dining area ta nufa inda mahaifinta da mahaifiyarta da ƙaninta suke zaune suna break, kujera ta ja ta zauna tana faɗin “barkanku da wannan lokaci Ummi and Abbu.”

 

_(Kasancewar sun gaisa tun bayan sallar asuba, dan ƙa’ida ne da zaran ta idar da sallah ta gama addu’ointa kafin ta koma bacci zata bi ɗakunan iyayan nata ta gaidasu sannan ta koma ta kwanta)_

 

Fuskarsu cike da annuri suke kallonta, Abbun nata ne ya fara faɗin “barkanki dai my daughter, sannu da fitowa.”

 

Murmushi tayi wanda ya bayyanar da fararen haƙoranta tace “yauwa Abbu.”

 

Ummi ma tana murmushi tace “barka my love har kin shirya kenan.?”

 

Fuskarta be gushe da murmushin da ke samansa ba tace “eh Ummi, break kawai zanyi sai na wuce, kinsan na faɗa miki yau lecture namu na safe ne, 9:30 zamu shiga.”

 

Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa Abbu ya kalla yace “to sai ki hanzarta dan yanzu 8:45 ne.”

 

Tana janyo cup dan haɗa tea take faɗin “insha Allahu Abbu.”

 

Hafiz ne yace “good morning Aunty Maryam.”

 

Kallonsa tayi da murmushi saman fuskarta tace “morning how are you my lovely brother.”

 

Shi ma yana murmushi yace “im fine Auntyna.”

 

Tana juya tean da ta haɗa cikin cup take faɗin “masha Allah, haka na keso dama na ji.”

 

Kallonsu kawai iyayan nasu keyi suna murmushi, zuciyarsu cike da ƙaunar yaran nasu wanda su kaɗai Allah ya mallaka musu.

 

 

Tea kawai tasha ta miƙe tana goge bakinta da tissue tana faɗin “Ummi and Abbu ni na tafi sai na dawo.”

 

Ummi ta fara faɗin “to Allah ya kiyaye ya tsare ya bada sa’a daughter.”

 

“Ameen Ummina”

Ta faɗa tana saɓa jakarta, Abbu ma cewa yayi “ki kula sosai daughter Allah ya tsare ya dawo mana da ke lafiya.”

 

Cike da jin daɗi tace “ameen ya Allah Abbuna, na gode da addu’oin ku.”

 

 

Tana ƙoƙarin barin dining ɗin Zeey ta shigo falon bakinta da sallama, amsa mata sukayi Maryam na takowa zuwa falon take faɗin “sarkin ƴan makara, ai da baki shigo ba sai-dai ki sameni a school dan yau ba zan tsaya shiga gidanku ba.”

 

 

Harararta Zeey tayi ba tare da ta bi takan maganarta ba ta nufi dining tana faɗin “ni dai bari na gaisa dasu Ummi.”

 

Taɓe baki Maryam tayi ta nufi ƙofar fita tana cewa “ki sameni a mota, in kuma wallahi ki kayi zamanki sai-dai ki tadda ƙurar motar.”

 

 

Cikin sauri Zeey ta gaisa dasu Abbu itama sukayi mata addu’ar ta fito da sassarfarta dan tasan kaɗan daga aikin Maryam ce ta tafi ta barta.

 

 

Aiko tana fitowa ta iske har ta tada motar, buɗe wa tayi da sauri ta shiga tana faɗin “ke fa wani lokacin ba mutunci ne da ke ba.”

 

Tana bugawa me gadin nasu horn take faɗin “kamar yanda ki ke ba.”

 

Murmushi Zeey tayi tace “Merona kar dai har yanzu fushi kike dani.?”

 

 

Tana ficewa a gidan nasu tace “fushi da ke akan me Zainab.?”

 

 

Zainab na kallonta tace “akan maganar jiya mana.”

 

Murmushi tayi tace “akan me zanyi fushi da ke ni ko Zainab ? Ba fa a jiya nasan halinki ba, kuma ba a jiya muka fara irin hakan ba, ke aminiyata ce wacce muka tashi tare, nasan ki nasan halinki, saidai ma na bai wa wasu labari, ra’ayinmu ne kawai yasha bambam, ke inda kika fuskanta daban haka nima inda na fuskanta daban, to ba kowa sai ya riƙe ra’ayinsa ba.”

 

 

Murmushi Zeey tayi tace “kuma ra’ayina yafi na ki ba.”

 

 

Dariya Maryam tayi tace “ban yi miki musu ba, kamar yanda dai na faɗa miki ne jiya, kowa ya tsaya akan ra’ayinsa, rayuwa ce zata nuna mana wanda nasa yafi na wani, kuma waye yafi gaskiya.”

 

Cike da rashin damuwa Zeey tace “shikenan, Allah ya ara mana rayuwar, zaki gane nafi ki gaskiya kam.”

 

Murmushi kawai Maryam ta yi tana me ci gaba da tuƙinta har suka iso cikin school ɗin nasu…

 

 

*****

 

 

 

A jere suka fito suna hira abinsu, fuskokinsu kaɗai zaka kalla ka tabbatar basa da damuwar komai, fitowarsu kenan daga lecture nasu na ƙarshe, dan haka kai tsaye suka nufi gurin motarsu.

 

 

Tun daga nesa suka hangosa tsaye jikin motarsa hannunsa riƙe da makulli yana jujjuyashi, Zeey ce ta kalli Maryam fuskarta ɗauke da murmushi tace “Maryam ga fa mutuninki nan.”

 

Harararta Maryam tayi tare da jan tsaki tana me kau da kanta daga kallon inda yake, ƴar siririyar dariya Zeey ta saki tana faɗin “wai me yasa kika tsani wannan bawan Allah ne haka Maryam.?”

 

Ba tare da ta kalleta ba tace “tsanarsa ? Ni na haliccesa da zan tsanesa ? Ni ban tsanesa ba, kawai dai bana ra’ayinsa ne, beyi min ba, wannan kawai shine.”

Ta gama faɗin hakan dai-dai sun iso inda yake, ba tare da ta nuna tasan da tsayuwarsa ba ta nufi inda motarta ke fake ta fara ƙoƙarin buɗewa, cikin sauri yace “Maryam tun ɗazu ke fa nake tsayuwar jira, amma ya zaki zo ki wuce kamar baki ganni ba.?”

 

Wani irin juyowa tayi irin da gasken nan bata gansa ba sai lokacin da yayi magana tace “lah Sadam dama kai ne tsaye ? Ai ban lura kai ne ba shi yasa.”

 

Kallonta yakeyi yana mamakin yanda ta nuna bata lura dashi ba alhali yasan tun kafin ta ƙaraso ta gansa, sai kawai shima ya waske ya nuna mata hakan ne ya saki murmushi yace “ni ne Hafsat, tun ɗazu na ke jiran fitowarki ai.”

 

Ita ma murmushin ta sakar masa tana faɗin “Allah sarki, kuɗi zaka bani ne halan.?”

Tayi maganar cikin sigar zolaya.

 

 

Dariya ya saki dan yasan shashantar dashi take son yi yace “in su ki ke so ai sai na baki duk da nasan kinfi ƙarfin su.”

 

Murmushi tayi tace “wa ya faɗa maka ana fin ƙarfin kuɗi, duk kuɗin ka kana son ƙari, baka ga ɗangode har yau nema yake yi ba.?”

 

 

Fuskarsa ɗauke da murmushi yace “hakane kuma, amma ni abinda zan baki yafi kuɗi muhimmanci.”

 

Ɗan yatsina fuskarta tayi tace “am Sadam kaga daga lecture muka fito nayi matukar gajiya da yawa ina buƙatar hutu, ka bari zamuyi waya kawai.”

 

Yasan neman zille masa takeyi, amma jin tace zasu yi waya yasa ya saki murmushi yace “okay shikenan, ya kamata dama kije ki huta sai na kira ɗin.”

 

Hannu ta ɗaga masa kawai alamar bye ta muɗe motar ta shige, Zeey ta ƙariso itama ta shiga sannan tayi ma motar key suka fice daga makarantar, yana kallon motar tasu har ta fice sannan ya sauke numfashi ya shiga nasa motar shima yabar makarantar…

 

 

****

 

 

Suna tafe Zeey ta kalleta tace “Maryam me yasa ba zaki baiwa Sadam dama ba, ni sam banga aibun guy ɗin ba, yana da kuɗi yana da kyau to me ya rage kuma.?”

 

Ɗan kallonta Maryam tayi kana ta ɗauke kanta sannan tace “yana da kuɗi yana da kyau, sai aka ce miki sune abin so ga namiji kaɗai.?”

 

 

Zeey na kallonta tace “sosai ma kuwa, yana da masu gidan rana wanda zaka fantama yanda kake so, sannan yana da kyau wanda babu raini duk inda ka shiga dashi, a nawa ganin babu sauran wani abu, to me zaki nema kuma.?”

 

Maryam tace “hali na ƙwarai da addini da sanin kima da darajar ɗan adam.”

 

Taɓe baki Zeey tayi tace “to gani nayi dai Sadam baya da wani mummunan hali, to wai ko yana dashi halin nasa zaki ci.?”

 

Juyowa Maryam tayi ta na mata wani irin kallo sannan ya maida hankalinta ga tuƙi tana faɗin “Zainab bansan ranar da zaki canza ba, wannan halin na ki shine hanya ta farko da zai saka ki cikin matsala a rayuwarki, halin mutum abin dubawa ne sosai in aka ce za kuyi zama ne dashi irin ta aure, domin shi aure zama ne da kake saka ran zaka yi sa har abada da mutum, to in aka ce baya da halayyar ƙwarai taya zaka ji daɗin wannan zaman dashi ? Bama wannan ba Zainab, Sadam ban san sa da wani halayya me muni ba, kawai ni dai beyi min bane bana ra’ayinsa, bazan ce bana sonsa ba sabida ban isa ƙin halittar Ubangijina ba, amma ban taɓa jin son aurensa ba, ban taɓa masa kallo na mijin da zan zauna dashi ba, kuɗi kyau ba shine abin da na keso ga mijin da zan aura ba, hasali ma ni bana son mijin da yafi ye kyau da kuɗi, domin kyau da kika gansa hatsari ne babba, Zainab a tsarina na fi son na auri miji me rufin asiri, kuɗi basu taɓa ɗaɗani da ƙasa ba, na tashi cikin gidan kuɗi, amma sam basu taɓa birgeni ba, ni har yau ban yanda cewa kuɗi sune *farin cikin rayuwa* ba, babu komai a cikin kuɗi sai wahala da ƙalubale, duk na mijin da yake da kuɗi sosai da wahala ki ga yana da lokacin matarsa yanda ya kamata, ni ko macece me son ko yaushe in ganni tare da mijina cikin kulawarsa, Zainab ina so ki fahimta ba komai kuɗi sukeyi ba, sannan halayyar mutum da addininsa abin dubawa ne in aka ce za kayi rayuwa ne dashi na har abada, ni bana ra’ayin auren me kuɗi, ina son namijin da zai riƙeni da amana ne wanda zai bani dukkan kulawarsa me addini da sanin darajar ɗan adam, wanda zai san darajata, ko baya da kuɗi zan zauna dashi har ƙarshen rayuwana ba tare da ƙorafi ba.”

 

 

Shiru Zainab tayi tana nazarin maganganun Maryam kafin daga bisani ta saki wani dogon numfashi tace “amma Maryam ni a nawa ganin kinyi ma kuɗi mugun fahimta ne kawai, sam yanda kike tunani ba haka suke ba, ni a nawa in ka auri me kuɗi ai ka gama hayewa, baka da wani matsala fa, amma rayuwar talauci babu komai cikinsa sai wahala da ƙunci, sannan a ganina halayyar mutum ba cinsa za kayi ba, eh yana da kyau ace mutum yana da halayya na ƙwarai, to amma kuma in yana da kuɗi ai zasu ɓoye aibunsa koda yana dashi, har yanzu ni dai ban yarda da rayuwar talauci ba, kuɗi kawai, ko duba ki kayi da iyayen mu kaɗai zai saka ki ƙara son rayuwar daula, kuma kina maganar masu kuɗi basu fiye kula da iyalansu ba, to meye amfanin zaman mijin a gida ? Ya fita kawai ya nemo, yanzu iyayenmu wani damuwa kika gansu a ciki dan Allah.?”

 

 

Dariya Maryam ta saki tana faɗin “lallai Zainab na yarda kinyi nisa saidai Allah ya ceto ki, sannan dan Allah in zaki iya kije ki samu iyayenmu mata ki tambayesu suna jin daɗin zaman auren da sukeyi yanda suke so ko kuwa ? Amsar da suka baki zaki iya ƙara saka sa cikin maganganuna ki auna su, wataƙila zaki gane gaskiyar abinda na ke faɗa miki, sannan wani abu guda ɗaya, su iyayanmu maza suna iya ƙoƙarin su gurin kula da matansu bakin gwargwado, kuma duk da haka ina tabbatar miki basa baiwa iyayenmu irin kulawar da suke buƙata saidai suna kwatantawa, amma ki sani ba kowanne me kuɗi ne ke da irin halinsu ba, samun irin sun yana wahala ki fahimta.”

 

 

Taɓe baki Zeey tayi tace “ni dai ban ga wani rashin jin daɗi ba a cikin rayuwar iyayanmu, ke ne dai har yau kika kasa fahimta, basan me yasa kike adawa da duk wani abu da zan faɗa ba, kina bani mamakin yanda kike nuna kuɗi basa da wani mahimmanci a rayuwar ɗan adam kamar ba a cikinsu kika ta so ba, ke kullum zancen ki kenan kuɗi basu ne *farin cikin rayuwa* ba, to sai ki faɗa min abinda ya fisu saka farin ciki a rayuwa, na ga ke ma yanzu sabida su ne kike farin cikin da kike ciki, baki nema komai kin rasa ba, bakya da wani damuwa, dan haka ni banga aibun su ba, kuma ba zan taɓa yarda na auri mijin da baya da masu gidan rana ba.”

 

 

Murmushi Maryam kawai tayi tare da faɗin “Allah ya taimaka Zainab, dan Allah da ga yau to karki ƙara kawo min wannan zancen, kowa ya bar ra’ayinsa cikin zuciyarsa, kowa yayi abinda yake ganin masa shine daidai faƙat.”

 

Wayarta Zainab ta hau dannawa tana faɗin “hakan ma yafi.”

 

Daga haka babu wanda ya sake magana a cikinsu……

 

 

 

******

 

 

 

 

Zaria

 

 

 

Sai da ta leƙo da kanta ta tabbatar babu kowa a wajen sannan ta fito daga ɗan ƙaramin ɗakin kwanan samarin dake ƙofar gida tana ƙara gyara gyalenta take faɗi ma wanda ke ciki “ni na wuce sai kuma gobe.”

 

Yana daga kwance yace “shikenan sai mun ƙara jonewa goben, amma da so samu ne mu sake haɗewa da yamma ki ƙara lasa min wannan zumar taki da kullum zaƙi take ƙarawa.”

 

Harara ta sakar masa tace “ka dai sani bana fitowa da yamma, goben ma ba lallai na baka ka lasa ba, dan akwai masu buƙatar hakan wanda suka fika sakin hannu.”

 

Dariya yayi yace “Rashida ke dai sam bakya da godiyar Allah wallahi, yanzu fa dukkan kuɗin da ke jikina na zube miki amma kina faɗa min magana.”

 

Taɓe baki tayi tace “ni ka ga tafiyata kafin wani ya zo giftawa ya ganni, sai mun sake haɗewa.”

 

Ko amsarsa ba ta jira ba ta sa kanta ta bar gurin, kai tsaye gurin saida abincinta ta nufa ta tattara kula da robobinta da ɗaura wa almajiri suka nufi gida dama ta saida abincin tun ɗazu ta tsaya amsar kuɗaɗenta ne gurin samarinta, dama sai ta gama shaida abinci zata bisu ɗaya bayan ɗaya tana amsar kuɗinta bayan sun gama jagwalgwalata sai a bata kuɗinta tare da ƙari……

 

 

 

Muje zuwa

 

 

 

 

 

Meeraheenat ce

Leave a Comment