Hausa Novels

Farrah Hausa Novel

Farrah Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

FARRAH

 

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

 

 

 

 

1️

KAUYEN KUDURI

Babban rapi ne sosai da ruwa ke gudana aciki yana kaida kawowa, ruwan rafin gashinan ja kalan kasa, ta baki bakin rafin kuma duwatsu ne manya manya da kanana kanana masu kyau ruwa na zuwa na hawa kansu yana komawa, ga mataye manya da yara sama da su dari duk an kachame gaban rafin ana wanki yanda kasan gasan wanki akeyi ana hayaniya ana wake, wani dankwaleliyan rana da ake kodawa daya fito mai zafin gaske ya haska ko’ina hakan yakarama wajen kyau.

Zauna kan wani dutse wata yar matashiyan budurwa take ga uban kaya agabanta data wanke gakuma wasu masu uban yawan a gefenta da batariga ta wanke ba, ahankali zufa ke gangarowa daga gefen fuskanta suna diddiga acikin ruwan, wasu yan mata guda biyu ne tsaye kan dutsen abayanta suna sanye da zani daban riga daban sai wani koren dan kwali akansu hannayensu duka rike da rake sunasha suna kalle kallen sauran matayen dake wanki awajen, daya daga cikinsu ne tace “Rakiya wlh muzamuci wanan gasar, kalli su Lami da Tani ko rabin wankin nasu basuyi ba” wacce aka kira da Rakiya juyawa tayi ta tofar da raken dake bakinta sanan takalli wacce ke zaune agabansu data basu baya tana wankin kayan tace “wai ke barakiyi sauri ba Farrah saisu Tani sun rigamu” kara saurin wankin tayi batare datace uppan ba, Rakiya taja tsakin takaici takalli kawartata tace “wlh kaman nakashe yarinyar nan nakeji, saina tabbatar dana wulakanta ta akauyen nan Atine” zubar da tsakin bakinta Atine tayi tace “yo wulakantawa kuma na nawa meya rage? Bayan kun riga kun kurmantar da ita, gashi kuma tariga tazama jakan gidan ku” ta tabe baki tana kallon bayan yarinyar tace “ke kiyi dasauri ko wlh barakici abincin rana dana dare ba duka kinsan halin yan gidan dakike” duk maganan dasukeyi tanajin su bata cemusu komi ba sai kara saurin wankin datayi tagaji tun safe wani safe tun jiya bakinta baiga abinci ba aiki kawai takeyi, duk suna tsaye awajen bata kara minti talatin ba takarasa wanke uban tulin kayan dayarage tass dayake Allah ya yita da zafin nama, kaman jira suke tagama wani kalan hankadeta Rakiya tayi tafada cikin rafin tsundum Rakiya tadauki kayan data wanke itada Atine sukahau ihu suna mungama wankin mu, matan wajen suka bisu da kallo ana hayaniya kaman basune suka hankada mutum a cikin ruwa ba, ahankali taciro kanta daga cikin ruwan tasa hannu tashare fuskanta ahankali tana bude idanun, wasu kalan fararen idanun takedashi tass kwayan idanunta kuma light brown ne ba baki ba, giranta acike fam da gashi baki sidik dake neman hadewa duka biyun, goshinta gabaki daya gashi ne dasuka kwanta sabida ruwan data fada, ahankali takebin kowa da kallo yanda su Rakiya ke tsalle suna murna sunzo na farko agasan wankin anjima zasu karbi kyauta wajen mai gari dawani tukuici na musamman, gently tafito daga ruwan sanan tamike tsaye ahankali, ko kadan batada wani tsawon kirki, itadai bazaka kirata da gajera ba sanan baraka kirata da doguwa ba dan batada tsayi ko kadan gashi batada kiba kaman ka hureta tafadi, dariyan dataji anayi yasa tadan juyo su Rakiya ne da kawayenta kemata dariya suna nunata, daya daga cikin kawayen su Ladidi tace “da idanuwanta kaman na mussa” suka kara kwashewa da dariya, Rakiya tace “wada kawai kurma” dasauri ta wuce tana tafiya dasauri sauri duk inda tabi ana kallonta ahaka hartakai gidan su acikin kauyen, gida ne matsakaicin gida na kasa, tura kyaure tayi tashiga cikin gidan gidan fess fess babu kowa gidan tasan Inna nachan gidan mai gari yaran gidan kuma koba’a gayamata ba ta tabbata suna chan rafi, wajen garken tumakan gidan da shanaye tayi sanan ahankali ta tura wani kofa dake wajen daya sadata dawata Yar karaman daki dako Leda babu akasan dakin sai uban jan kasa dake kasa, babu komi adakin sai wani bakin zanin gado dake chan gefe da alamu nan ne gadonta ashimfide akasa sai wani kullin zani dawajen tayida saurinta ta warware wata kodaddiyar doguwan Riga tadauka agurguje tacire na jikinta ta saka sanan ta dauko wani hula ta cire hulan kanta daya jike wasu dogayen gashi suka zubo har wajen waist dinta tattare gashin tayi ta tura a hulan sanan tafito ta shanya kayan kan igiya sanan ta tsaya chak tabi gidan da kallo cikinta nawani irin kukan yunwa, komawa da baya da baya tayi ta jingina da bango ahankali tana kallon kitchen dinsu da aka zagaye da langa langa, takai kusan minti biyu ahaka sanan ta tsugunna ahankali jin kaman zata fadi tana kallon kitchen din still, yunwan datakeji jitake kaman ko mutum aka bata yanzu hakan nan zata iyaci, bakinta har wani rawa rawa yake fararen idanunta na juyawa sosai, ganin kaman zata mutu yasa taji wani kalan karfi yazo mata tai kitchen din dagudu tana zuwa ta bude tukunyar wata shinkafa ce dafa duka datai jajir kaman ansamata color atukunyar wani irin yawu taji ta hadiye cikinta yay wani kalan kugi na yaga abinci, batasan lokacin da marfin tukunyar hannunta yafadi kasa ba tasa hannunta cikin tukunya ko kadan bata damu da zafin abincin ba tashigaci kaman wacce tai shekaru aduniya bata sami abinci ba.

 

 

Sallaman Inna dataji atsakar gidan yasa gabanta yay wani kalan mummunan fadi dawani irin bala’in sauri ta tashi daga gaban murhun tana komawa da baya da baya bakinta duk manja hakama hannunta bama tasan ina zataba tsabagen yanda jikinta kerawa, duk duniya babu wanda take tsoro kaman Inna, ko muryanta taji jikinta kyarma yake, cin karo datayi da uban tukwane dake jere a kitchen din yasa suka watse sukai wani uban kara dayasa Inna dake tsakar gida tana cire hijabi tace “waye agidan nan? Ina baduka yaran nan suna rafi ba” tai maganan tana yin hanyar cikin din chak ta tsaya ganin marfin tukunyar abincin su akasa gakuma Farrah dakeyi kaman zata binne kanta cikin tukwannen dasuka baro akasa jikinta na bala’in kyarma tana kallon Innan dake wani irin kallonta da mugayen idanunta tanabin bakinta da hannayen ta da Farrah tashiga gogewa ajikin riganta da kallo, cikin wata irin bakar rai tace “yanzu kuma sata kika faramin Farra’u? Wato gudowa kikayi kika dawo gida kowa nachan rafi eh? In ciyar da ubanku sanan inciyar dake Yar ruko, Farrah nine fa Inna Basira kin manta wacece ni”? Wani irin bayanta Farrah tashiga bugawa ajikin bangon datake tsaye kaman ginin yafadi takeji tabi tagudu hawaye yashiga saukowa daga idanunta tana girgiza mata kai, juyawa Inna tayi tashige wani daki dake nan inda take tsaye bata wani jimaba tafito rike dawata zaftareriyan adda tace “ai kin tuna wanan addan ina? Wlh wlh wlh yausaina kasheki” tai inda Farrah take tsaye, wani kalan ihu na kurmaye Farrah tashiga yi dayar siriruwan muryanta dabayama fita da kyau, duk duniya batada abinda take tsoro kaman Innan su, duk inda taganta takan mata kallon dodo ne ma, kafin takai wajen kawai ta sume, cikin fushi Inna tace “wlh ko mutuwa kikayi sainasa kinyi na biyu” tadaga addan zata chakamata kaman daga sama taji an kwalamata kira. “Basira! Basira! Basira! Sau nawa nakiraki” chak tajuyo jin muryan Malam dan batazaci yana gida ba, wani dan siririn magidanci ne yafito, idanunshi sundan tashi sun kumbura da alamu bacci yasha, hannunshi rike da buta yana tsaye bakin kofa yana kallonta girgiza kai yayi sanan yakai bakin buran zuwa bakinshi ya tsayaya ruwa sanan yasauke hannunshi kasa ya kuskure bakinshi sanan ya zubar da ruwan kafin yasake kallonta cikin harshen shi dababu hausa sosai yace “ina gujemiki hukuma Basira, ina gujemiki hukuma amman bakiji, babadan matan megari dasuka rufamiki asiri sukasa mai gari yama yan sanda magana ba da yanzu kina chaji offis, amman ga fili gamai doki baran hanaki ba ki kasheta, bismillanki” yay maganan yana zare mazagiyar wandonshi da hannu daya yana tafiya zuwa hanyar bayi, cikeda fushi dakuma cin mutunci tace “malalacin miji kawai, kullum baka da aiki sai baccin banza daga safe har dare kana turaka nadafa nabaka barakaje nemaba, ahaka kuma ka kawomin yara, in ciyar dakai na ciyar dasu tunda gani banza ko bansan ciwon kaina ba” fitowa yayi daga makewayen yana binta daga ita har Farrah datake asume dakallo yace “kinga nahanaki nace karki kasheta? Banfa ceba duk yanda kikaga dama kiyi ai gamai fili gamai doki, inda kina bata abinci zata miki satan abinci ne, wanke muku jiki ne kawai yarinyar nan batayi agidan nan Basira, kodan uban aikin datake muku ai kya ciyar da ita” cikeda fada ta taho inda yake duke zai fara alwala tace “Malam kai meya hanaka ciyar da ita? Ina diyar kanwanka ce da akawa cikin shege eh, daga zuwa tasha saida nono tafara karuwanci aka duramata cikin su, wlh kafita daga idanuna Malam inba hakaba kaima nakusa koranka daga gidan nan mara zuciya kawai, na mace” mikewa tsaye yayi yana wanke kafa sanan yatashi yana addu’a kafin yakalleta yace “idan kin isa ki koran nagani shedaniya kawai” ihu tayi tana tafi tace “gaka nan babban shaidani mai matacciyar zuciya, kana kwance ni zan fita nema, daidai da kayan jikin ka nina siyamaka akasuwan gabari, dawo kaciremin silipas dina ai nina sayo na kafan ka” juyowa yayi ya wurgamata harara sanan yabude kyaure yawuce yafita itakuma tajuyo tana kallon inda Farrah take azube asume tana kara kallon addan data Yar akasa tai kwafa, tasan maganan malam gaskiya ne saisa kawai tafasa kasheta amman ta tsani yarinyar nan ta tsaneta ta tsaneta she wish zata iya kasheta taje ta Yar batare daya tada tambaya ba datayi hakan wlh, komawa dakin data ciro addan tayi ta ijiye sanan tafito takoma dakinta tazauna tana karkada kafa.

 

Shigowa gidan yayi bayan yay sallan la’asar, Farrah dake kwance asume inda take a kitchen yabida kallo yana tafiyan nan kaman iska zai kwasheshi yafadi tsabagen rama sanan yashiga dakin, Inna dake zaune atsakar falon ta bishi da mugun kallo dan kaman tashakeshi takeji, wata Yar karaman radio dake kan Yar kodaddiyar tv su yadauka yana jawo antenna radio waje sanan ya kunna yana murza tasha yana kokarin kamo tashar BBC,

 

Inna dake ballamai harara tace “tirrr wlh kayi asara arayuwanka mai mataccen zuciya kawai” sake tabe baki yayi sanan yadauki taburman dake nannade an jinginar dashi a tsaye gefenta yawuce yafito cikeda cin zarafi da mugun son yakulata tace “nagadai tabarman ma tawace nina saya mara zuciya” shimfida tabarman yayi agaban dakin sanan ya ijiye radio yamike tsaye yasake kallon Farrah a inda take sanan yawuce butanshi dakenan inda yabarta anan tsakar gida dazun dayay alwala yakarasa yadauka dayake da ragowan ruwa aciki yana kara girgiza butan dan gane iya ragowan ruwan dayake ciki sanan yawuce inda take ya tsaya a kanta dan kallonta ya tsaya yanayi yay jim kaman mai tunanin wani abu rabon da yadaura idanunshi akanta wlh yama manta hakanan ganin fuskan marigayiya kanwarshi yayi kaman ita lokacin datana sa’an Farrah, girgiza kanshi kawai yayi sanan yadaga butan yashiga tsiyaya mata ruwan ciki kan fuskanta yana kiranta. “Ke, Farra’u, ke!” Yakirata da karfi ahankali tashiga motsi tana yatsine fuska jin ruwa akanta saikuma kaman wacce aka tsungula tawani mugun zabura tamike tana kara wargaza tukwanen dake wajen tana ihun kurame dayar muryanta, Malam daya bita da kallo yace “zakici gidan ku ne, da idanuwanki kaman na shaidanun ruwa, ko agidan wa kika koyo sata kije ki zubar dashi gidan nan kasheki zasuyi kikace sata zaki dinga musu, yo ke bakima tausayin kanki Iyye, jibi jikinki babu nama kodaya, bakida suturan arziki, tsabagen bakin wahala abinci sai wanda aka yammiki kuma kice zaki dingawa masu ciyar dake sata, Farrah anya kinason kanki kuwa da zaman lafiya”? Gyadamai kai tayi ahankali tana goge hawayen dasuka zubomata da bayan hannu kanta akasa dan itama bata iya kallon Malam, binta yayi da kallo daga sama har kasa yace “wuce ni ki zubamin abincin naci kirufe tukunyar dakika yadda marfin akasa” kaman jira Inna take azuciye tafito daga dakin tazo kitchen din tana tafi tace “wlh bazaka cishi ba Malam, mai tauraro kasayamin koko ajino moto eh? Sule biyar dinka babu a abincin nan dan haka wlh barakaci shi ba, kekuma dan ubanki kwarto dahar yau baki sani ba idan kin isa kitaba abincin nan kiga idan ban guntule wayan nan fararen hannuwan naki ba” dukawa Farrah tayi tana sunnar da kanta kasa tana kulle idanu jikinta na kyarma bala’in tsoron Inna take, inhar tana gidan batada kwanciyan hankali, dan kallon Inna Malam yayi sanan yadan saci kallon tukunyar yanda yaga shinkafar tai jajir yaji ranshi yakara biyawa bazai iya mata zuciya ba cikinshi yashiga kugi, dan murmushi yayi yakalli Inna yace “wai Kodai yau matan mai gari basu biyaki kudin aikatau bane naga ranki abace ne Basirata” harara ta ballamai tace “kanka akeji munafuki” tajuya zata wuce dasauri ya chapke hannunta cikeda muryan lallashi da lallabawa yace “yakuri dan Allah ki zubamin shinkafar nan wallahi yunwar tsiya nikeji” fizge hannunta tayi tace “bakariga kajita ba, bani kazauna kake gaggayama maganganu ba sabida wanan shegiyar kurman beben yarinyan dabata da amfanin duniya balle nalahira yanzu ai saikaci babu kokuma ita taje tanemo tadafa tabaka kaci” gabanta yasha dasauri yakalleta cikeda so yace “haba mana Basira, naface kiyakuri fa, kizubamin naci fita zanyi naje wajen Luku zandawo da kudi kinji” dauke kai tayi tareda rungume hannayenta aciki, washe baki yayi ganin yasoma shawo kanta yace “haba surukan Mai Gari, Maman mai farin jini ke bakiga yanda akema yarmu Rakiya layi ba, saisa nima nai na’am da dan Mai Gari zata aura kaman yanda kika fadi, yarinyar ki saidai mahassadi eh Yar matata, bakiga Rakiya ba jajur da ita uwa hurun ini” wani kalan washe hakora Inna tayi tace “yo ai har yanzu batakai Farrah ja ba saisa nasayo mata wani mai akasuwan gabari nasa tana shafawa, ance idan ta shafa zata kara haske fatar nan tai jazur, wanchan Yar kam saisa nake tabbatar data wuni aikatau arana sabida ta dafe tai baki, bata isa ta kwacema y’ata farin jini ba, bebiya kawai” takarashe maganan tana zubawa Farrah dake tattare tukwanen wajen harara, sanan tai wani irin murmushi tayi tana juya idanu, Malam dake kallonta kaman solobiyo yakara make murya yace “to adan zubo min” juyawa tayi tana murmushi tace “gobe ma ka karamin rashin kunya zanga mai baka abinci Malam” tawuce kitchen din ko kallon Farrah batayiba tadauki kwano a kwando tadeboma Malam shinkafar ranta nakara baci sabida yanda Farrah taci shinkafar sanan tarufe tukunyar tajuyo tace “kitashi kiwuce ki debo ruwa kicike kowani tulu na gidan nan inba hakaba nalahira saiya fiki jin dadi Al Qur’anin ubangiji” sanan tawuce takaima Malam abincin tazauna kusa dashi suna zance.

 

 

 

Ahankali tamike tsaye wani babban tulu tadauka tadaura aka sanan tafito daga kitchen din wani cinyayyen sidadden silipas wari daban daban tadauka a tsakar gidan tasaka sanan tawuce tafita daga gidan, daga Malam har Inna babu wanda yadagakai yakalleta.

 

 

 

 

Dasauri take tafiya abinta as usual dan sotake tagama cika ko’ina kafin mangariba tayi dan ba’a zuwa rafin idan Magrib yayi kuma rafin yamafi rafin wankinsu nisa, tayi tafiya mai tsawo kaman daga sama taji ankirata. “Ke Kurma” chak ta tsaya tana kalle kallen ko’ina babu kowa a hanyar, wani kalan murmushi tayi dayawani irin kawo cikakken annuri fuskanta cikeda kokarin son tai magana dan ga dukkan alamu tasan waye yakirata tace “taaaaaa…ffff….fa” wani irin dirkowa wata yarinya Yar matashiya tayi daga bishiyan mangwaro dake gefen hanyan da Farrah ke tsaye tana sanye da zani da riga na fulani kanta da dankwali baki na silk kana ganinsu kansu daya itada Farrah saidai tadanfi Farrah tsayi kadan itama farace sol kana ganinta kaga cikakkiyar yar fulani, wani kalan murmushi tayi takaraso gaban Farrah dake kallonta tamikamata mangwaro daya itama tarike dayan na hannunta tace “waike Kurman nan nace dole saikin kira sunana ne, barakije kiji da Kurmancin kiba iyye, sunana Shafa, ba Taaaa….ffff…..fa ba koyayama kike kiran sunan oho miki yar rainin wayau kawai” wani kalan murmushi Farrah tayi da saida ita kanta Shafa ta tsaya tana kallonta hakan yasa Farrah tahadiye murmushi da hannu tamata alamun me?, girgiza matakai Shafa tayi sanan ta tabe baki tasa hannunta daya takarbe tulun daga saman kanta tamaida nata kan tace “ni tausayi kike bani, muje naraka ki debo ruwan, rikemin mangwaro na nidai” tabata mangwaron dasauri takarba tana murmushi suka wuce, Shafa tace “Modibbo yakara tsareki a hanya”? Girgiza mata kai tayi dasauri alamun a’a, Shafa tace “yawwa, duk randa yakara tsareki karki nuna kina tsoronshi kawai kice yakiyayeki bakison matsalan su Rakiya, kindaisan yanda Rakiya keson Modibbo, ki kiyaye su” Gyadamata kai tayi alamun to tana murmushi duk kauyen nan Shafa kadai ce kawarta ita kadaice mai sonta, Shafa akwai baki kaman reza, gata da karfi tasha shiganma Farrah fada, har Rakiya tama duka akan Farrah dan ta tsani yanda ake wulakanta yarinyar sabida ita Kurma ce batada uwa da uba akauyen, son datake mata ne ma yasa bata taba kiranta da asalin sunanta Farrah saidai takirata da Kurma dan kowa yaji yes Kurman kauyensu ce kawarta. “Ke Kurma” Farrah taji ankirata dasauri takalli Shafa dataga tana kallon gabansu, ganin wasu maza su kusan shidda gaban rafin suna zazzaune sun zagaye murhu suna dafa shayi yasa Farrah ta tsaya chak batare data kara tafiya ba kanta akasa, binsu da kallo itama Shafa tayi su Modibbo ne da abokanenshi suna dafa shayi gashinan farare dogaye kana ganinsu kaga yan fulani duk sun dago suna binsu da kallo suma, dauke kai Shafa tayi tajuyo takalli Farrah, hannunta tasa takama hannun Farrah tace “muje kinji Kurma” binta Farrah tayi gabanta nafaduwa dan ko hada hanya tayi da Modibbo bala’i yake zaman mata agida.

 

 

 

Wani dogon saurayi ne yatashi tsaye fari kal dashi kana ganinshi zakasan shine Modibbo sabida yanda yabi Farrah da kallo kaman yaga abinci, abincin ma gangariya, yana sanye da manyan kaya kal kal dasu babu datti dan Baban shi ne mai gari so sunada kudi gashi shine Magajin mai gari dan shi kadaine dan Maigari namiji, karasowa inda suke aduke gaban rafin yayi yana zuba hannu a aljihu yana kallon Farrah dabama taganshi ba ahankali yace “Farrah” dawani irin sauri daga Farrah har Shafa suka juyo suna kallonshi, hannun Farrah Shafa takama ta iza kan tulun dake cikin rafin tace “rike tulun nan Kurma” sanan tamike tsaye takalli Modibbo tace “Hamma Modibbo kaga bamasan bala’i kuma bama neman fitina karabu da Farrah dan Allah, nasan sabida ita ka kafa majalisa agaban rafin nan dan kasan tana zuwa debo ruwa, inhar kanason Kurma dagaske bazaka dinga jazamata bala’i ba bayan kasan Rakiya sonka take, kumama Hamma Modibbo waye zai barka ka auri Kurma iyye, dan Allah kafita harkan yarinyar nan ka tausaya mata, ka tausayama maraicinta haka mutanen kwarai suke” tunda take maganan yake binta da kallo saida tagama yanuna kanshi cikeda isgilanci yace “wai dani kike Shafa’atu?” Kwashewa da dariya abokanen sukayi ganin rainin wayon da Modibbo yama Shafa, daya daga cikin su yace “Modibbo bakin ciki take ba ita kakeso ba kawarta kakeso” wani mugun kallo Shafa tamai shikuma Modibbo yabi ta gefen Shafan yay inda Farrah take datake kokarin daukan tulun ta daya cika da ruwa zata iza bisa ka ganinshi yasa atsorace tasaki tulun zatai baya dasauri Modibbo yasa hannu yadauki tulun yarike yana kallonta yace “zona iza miki” girgizamai kai tayi ahankali kanta akasa taki zuwa, ahankali yataka zuwa gabanta yana kallon yanda jikinta kerawa sanan yadaura mata tulun aka dawani bala’in sauri kaman mazari tajuya zata wuce yace “bansallameki ba ai” chak ta tsaya batare data juyoba, hannunshi yatura a aljihu sanan yaciro ledan biscuit na Oreo dazun nan aka kawoma Mai gari biscut din daga binni nashine amman yakici dan yabata wani murmushi yakarayi yasan zata fara sonshi dan babu wanda yataba ganin irin biscuit din akauyen nan zuwa yayi tagabanta yamika mata ledan ta kalla sanan ta girgixamai kai ahankali yace “biscuit ne daga binni ki karba kona kama hannunki nasamiki” Shafa tadan kalla kaman zata fashe da kuka ganin haka yasa cikin fushi yace “idan Shafa kesaki tai abu kotahanaki kiyi abu zansa akoresu daga garin nan” akufule Shafa na tattauna baki tace “mafashi” dasauri Farrah tamikamai hannunta jin zaisa akori su Shafa, gently yasamata biscuit din yana murmushi sosai dasauri tawuce Shafa ma ta watsama dukansu harara tawuce shikuma yabita da kallo saida suka bace sanan yakoma inda suke ya zauna yana murmushi abokanenshi sukace “wai kai mezakayi da kurman nan ga hadaddun matan kauyen nan dake mutum maka kanace ma kurman nan mara galihu” wani kalan murmushi yayi yana karban shayin da aka zubamai a kopi kaman mai tunani yace “kap matan kauyen nan babu mai baiwar da kurman nan kedashi” Muji yace “wanan gajeran gata kurma wani baiwa tafi matan garin nan dashi Haba Modibbo Kodai magani tamaka ne” murmushi yayi sosai yadan kurbi shayin sanan Ya hadiye yace “aradun Allah duka kauyen nan babu wanda yakai kurman nan kayan alatu ajiki, ahaka da wahalan da komi kaga kidirmon datake dashi kuwa balle ma nacigaba da bata dadi ina bata su kaza da biscuit’ din binni” yay dan dariya yana sake kurban shayi, tabe baki Muji yayi yace “kaima kasan kozaka mutu kanadai magajin gari baza’ataba barinka ka auri Kurman nan ba, babu wanda yasan ubanta, ance kanjamau yakashe uwarta ma, dataga tana shirin mutuwa ta tattaro da ita da yaran nata suka dawo nan kauye tazo tamutu anan” tabe baki Modibbo yayi yasake kurban shayin yajaye kofin daga bakinshi sanan yadagakai yakalli abokanan nashi daduk suke kallonshi suna jiran amsan shi dan dariya yayi yace “yo uban me kukeso nafadi muku? Kuda kunku kunsan ba aurenta zanba ai hakan yabaku amsan manufata akan kurman” wani kalan kwashewa dukansu sukayi da dariya suna tafi, Tanko yanunashi da yatsa yana kadakai yace “Modibbo, Modibbo anyi dan iska awajen nan wlh” suka kara kecewa da dariya, murmushi Modibbo yayi yace “gobe zaku kawomin ita dakina na gangare idan duhu yayi” tafi sukahau yi, Muji yace “kace kai Modibbo gobe Kwanan ango lahiya lau ne kaida Yar kurman ka” dariya Modibbo yayi yace “dasafe gobe zan kawo mata kwai da cinyan kaza da shayi, nabata dadi tabani kindirmo”.

 

 

 

Tofah jama’a ana wata gawata!

~Sai mun hadu mako nagaba dan jin yanda zata kaya tsakanin Modibbo da Farrah, shin Allah zai kubutar da ita daga hannun Magajin Maigari koko tana ruwa?? Kubiyoni danjin cigaban wanan kayataccen labarin na FARRAH wanda ni M Shakur ke kawo muku dahaka nace Bissalam~

Leave a Comment

error: Content is protected !!