Hausa Novels

Fatalwar Mijina Hausa Novel

Fatalwar Mijina Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

[Kamar dai kullum sun kammala gudanar da soyayyarsu as usual amatsayinsu na mata da miji,bayan komai ya daidaita,kowannensu ya juyawa dan’uwansa baya tare da kara jan blanket suka rufe jikkunansu dashi har kai kuwa,ba’a wani dau tsawon lokaci ba wani nannauyar bacci yayi awon gaba dasu.

 

_*°•2:15AM•°*_

 

Ji kake tasss!!! K’arar fashewar glass asaman tiles wanda hakan ne ya tada Zayba agigice tana salati,abinda yasa har taji k’arar kuwa shine don fankar dakin akashe take,dake ana cikin lokacin damuna ne shiyasa suka kasheta sabida ko’ina yadau sanyi,toh kuma dayake acikin tsohon dare ne,ko’ina so silent shiyasa k’arar ta shigeta dak’yau.Kasa kunni tayi tana jiran ta sake jin wannan k’arar sannan ta tantance koma menene.Ai kuwa ji kake tassss! Wani glass din ya sake fashewa kuma ga dukkan alamu ah downstairs ne,can parlor,k’arar tayi mugun firgita Zayba,wani uban k’ara ta fasa tare da mirginawa ta rungume Usamah mijinta,abin mamaki Usamah kuwa ko motsawa beyi ba balle asaka ran cewa shima yaji wannan k’arar har ya tashi afirgice kamarta.

 

Atsorace ta furta”U..saa..maaah wai baaka jin karar fashewar abu ah downstairs ne?”

 

Wani karar daya fi nada ne ta sake ji kuma,ta sake sakin wani ihu tare da dada kankame Usamah wanda baima san ana yi ba,bayan tsoron yadan saketa,saita cikashi ta soma kai masa bugu agadon baya axuciye kuwa tana fadin”Usamah wai wannan wani irin bacci ne haka?bacci sai kace baccin mutuwa da har ka kasa jin karar dani nake jiyowa?mtsww bara naje na dubo abina don nasan kana ji sarai miskilanci ne dai kawai kake ji,walhi ina gaya maka ka dena wannan banzan halin naka na k’yaluwa babu k’yau ehe.. ”

 

Bema san tana yi ba donko motsawa beyi ba,ita kuwa duk azatonta halinsa daya saba yi ne ya gwada mata wato banzartar da mutum.Sannu ahankali ta diro,ta soma takawa atsorace don duhu ya mamaye ko’ina,bazata ma iya tantance inda direction din switch yake ba,don haka saita koma da baya ta dauki wayarta dake karkashin fillo,abin mamaki koda ta danna wajen ‘flashlight🔦’,sai yaki bada wutar,sau uku tana gwadawa amma wutar taki kunnuwa,don haka sai tayi amfani da hasken dake jikin screen din wayar ta fice daga dakin atsorace xuwa downstairs.

 

Cikin sanda take takawa sannu ahankali,steps bibbiyu take ta tsallakewa don ta samu ta isa makeken falon da wuri,tun kan ta gama sauka ta soma jin some strange sounds,dakatawa ta danyi cike da tsoro don gabaki daya dukkan ilahirin jikinta rawa yake tamkar wacce ruwan sama yaiwa dan banzar duka,hirarraki marasa ma’ana take ta jiyowa wanda bazata iya tantance ko meh ake fada ba,muryoyi daban daban ne kawai keta mata kuwwa akunne kuma ta rasa daga ina ne suke fitowa,can kuma taji sautin dariya mai hade da kuka irinna ban tausayin nan,dube dube ta somayi cike da tsoro tana haska wurare tare da taimakon hasken dake jikin screen din wayarta.

 

Ji tayi an fizge wayar an jefar akasa,ai kuwa ta fasa wani irin razanannen ihu,jikinta ya dauki rawa sosai fiye da da,ta dan duƙa zata dauki wayar,taga wayar ya matsa gaba da kansa,gwalalo ido tayi waje cike da tsoro da kuma mamakin wannan al’amarin,wai waya ke matsawa da kanshi ba tare da an tabashi ba,kara matsawa tayi don daukashi akaro na biyu,wayar na ah last step ne na matattakalar benen.Sai gani tayi wayar ya karashe sauka kasa sosai don har can tsakiyar makeken falon aka kaishi.Shanye mamakinta da tsoro tayi,ta sake tunkaren inda wayar yake akaro na uku,tun kan ta karasa kusa dashi taga wutar wayar ta dauke gabaki daya,abin yayi matukar bata mamaki don ta sanya hasken wayar ne ah sleep for 30mins kafin ya mutu,kuma fitowarta daga cikin daki ko 10mins bata kai ba,don haka beci ace har hasken ya dauke ba cuz 30mins beyi ba.

 

Tama rasa meye next step dinta don gabaki daya falon ma kamar kara masa duhu akai,ko kadan babu haske sai dan haske hasken farin wata wanda beyi wani haske sosai ba.Can ta soma jin kamar ana banging windows,kadan da kadan aka soma,cikin tsananin tsoro ta soma matsawa kusa tana fadin”Wane.. ne awurin?” ta fada cikin ƙaryewar murya.

 

Karar fashewar kwalba ta jiyo daga bayanta,da sauri ta waiga tace”Wai don Allah wanene keta tsoratani haka ne?”

 

Soma jaa da baya tayi,can taji taci karo da wani abu,atare suka fasa wani uban ihu,adaidai lokacin kuma bulb light din falon suka soma kawo wuta suna daukewa,haka aka cigaba da flashing light din ana daukewa,cike da tsoro Zayba ta juya don ganin wanda ta bigen dashi,tare da taimakon wutar daketa flashing yana daukewa taga fuskar.

 

]

KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇👇👇

 

 

Preview: [DOWNLOAD COMPLETE BOOK 👇👇👇]
 

Name: Fatalwar Miji na
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: MYNOVELS.COM.NG
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books
Groups/Writers: Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: July, 2021

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!