Hausa Novels

Fatymasardauna Hausa Novels

Fatymasardauna Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

FATYMASARDAUNA

 

* by meeerarh*

 

 

*1*

 

🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

 

Takasance kalar macen datakeso tazama, tanayin rayuwan ta Kaman yanda takeso, babu wanda yake takuramata, ko iyayenta basa matsamata tayi abunda bataso.

 

Saboda sun yarda da ita, sun san bazata taba jawowa kanta abun da zatayi dana sani ba, takasance mace wacce take yin duk abunda takeso, Kuma wacce take samun duk abunda takeso.

 

Tana rayuwane according to yanda ta tsara, musamman fannin soyayya, tana soyayya da duk wanda take so batare datasha wahala ba Kuma badan wani abu ba, kawai yakasance tun tasowanta bata taba neman abu tarasaba.

 

So she is use to it,a duk sanda zatayi sabon saurayi takanji hakan ajikinta ta hanyar yawan bugawar da zuciyan ta takeyi a koda yaushe, akwai mutane biyu datake so Kaman rayuwan ta, AMEEN dakuma AMJAD.

 

Sudin cikin samarinta sutakeyiwa son dabatasan kalarshiba, Kuma acikin su biyun AMJAD yakasance na farko a zuciyata tana mishi so irin wanda batayiwa ko wane dan adam shi, ya kasance wani sashi na jiki da zuciyan ta.

 

Amma ‘kaddarar data kasance taka baka isa ka guje mata ba, ‘kaddararta takasance mafi zaman kaddara saboda ko amafarki bata sakawa ranta rayuwa da wanda ba Amjad ba .

 

AMJAD yakasance ‘kanin matar mahaifinta ne Kuma a gida daya suke zaune tun suna yara.

 

Ayaune 5 ga watan December shekara ta dubu biyu da ashirin da daya ‘kaddara tayi sanadiyyar juyewar rayuwarta.

 

‘Kaddara tayi sanadiyyar shigarta wani hali da wata rayuwa wacce Bata san sanda zata fita ba, wata kila har abada wata kila Kuma jarrabawarta Kenan.

 

Tafiya take da waya a hannun ta tana duba abu a ciki, dariya take yi wacce daka gani kasan tana cikin matsanancin farin ciki.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Lofan gate tabud’e kasancewan daga islamiyya take Kuma islamiyyan a kofan gidansu yake, yaune ta rubuta takardan karshe na gama secondary school.

 

Kuma yaune mahaifin ta yabata kalan wayan da tafi so arayuwan ta, so murna biyu take ciki abun da bata saniba yau rayuwan ta zai canja daka farin ciki xuwa bakin ciki,koda ta shiga gate na farko anan ta iske malaminta wanda yake Kaman yayanta, so ta tsaya suna Magana akan sabuwar wakar da zasuyi sai wayan ta yayi ringing.

 

Koda taduba sai taga ABEY MY LOVE, mahaifinta Kenan wanda take kira da ABEY , receiving na call din tayi sannan ta shiga gate na biyu, tana karasa shiga kunnuwan ta sukajiye mata abun da yayi sanadiyyar sa taji Kaman rugugin tsawa a xuciyar ta.

 

Daman tunda ta dauka batayi maganaba tana sauraron abunda mahaifin ta yake fada acikin wayan,

 

D’IYATA, SUNAN DAYAKE KIRANTA DASHI KENAN, KINSAN DUK WANI MAHAIFI BAZAI SO YA ZA’BARWA ‘YAR SHI ABUNDA ZAI CUTAR DA ITA BA, KUMA NASANKI KINA YIN DUK ABUNDA NA UMURCEKI DASHI SHIYASA NAKE ROKON ALFARMA DA KI AURI YAYANKI HABBAN , IDAN KIKAYIMUN HAKAN ZANJI DADI KUMA HAKAN ZAI SAKANI FARIN CIKI.

 

Hannun ta taji yafara rawa wayanta na shirin faduwa, dakyar da ikon Allah ta iya tashi ta karasa shiga gate din dazai sa da ta da ainihin cikin gidan, tana karasa shiga kai tsaye part din mamanta ta nufa.

 

Ko da tashiga siser dinta Hamdan tana palorn su a zaune , a bakin kofa ta zube tana maida numfashi , dai dai lokacin wani kiran ya sake shigo wa wayan ta.

 

Dakyar ta iya daga wa, saboda batason jin abunda Abey zai fada mata.

 

Koda ta dauka idanun Hamdan na kanta, sai tasaka wayan a handsfree , ananne Hamdan taji meyake faruwa , daganan Abey yabama Fatouma mintuna 30 tayi shawara.

 

Ananne Hamdan tatada masifa saboda mama bata nan, rike hannun Fatouma tayi suka shiga dakinta sannan ta dauki waya ta kira yayansu Musty , ba’afi mintuna biyar ba sai gashi ya shigo dakin ranshi amatukar bace.

 

Bai tsaya sauraren komai ba yafara yiwa Fatouma fada, wai ai saboda sunga tanada saukin kai shiyasa sukeson su hadata da wanda be dace da ita ba, yace mata idan Abey yasake kira tace batason shi akwai wanda takeso.

 

Gaba daya bata cikin natsuwar ta shiyasa ta daga mishi kai alamun taji mai yace, hannun Hamdan yaja suka fice daga dakin, ita kuwa Fatouma washroom tashiga.

 

Tana shiga tasakar wa kanta ruwan sanyi sabo da ji takeyi Kaman ana yanka naman jikinta, a lokacinne Kuma wani irin kuka yazo mata.

 

Wanda a tsawon rayuwar ta bata taba yin kalanshiba, ana cikin hakanne Kuma Hamdan tashigo , sosai hankalinta yatashi ganin halin da Fatouma take ciki, dai dai lokacin Kuma wayan ta yayi ringing.

 

Wani irin buga wa zuciyan ta yayi wanda hakan ya farune saboda tasan Abey ne yake kira, Hamdan ce ta dauko wayan daga cikin ‘daki tare da daga kiran tasaka a handsfree.

 

Muryan Abey yafito daga wayan yafito yana fading, mintuna talatin sun cika ‘diyata menene amsarki, Hamdan nacewa tace aa.

 

Amma a zuciyar ta tanajin komai mahaifin ta ya nema a gurin ta bai kamata ta’kiyi ba saboda kamar ta sabawa Allah ne, saboda tasan mahifinta bai taba matsa mata tayi abuba.

 

Kuma yana yimata duk wani abu da take so, batare da wani dogon tunaniba, ta amsa mishi da cewa, ABEY ALLAH YA ZABA MANA ABUN DA YAFI ZAMA ALKHAIRI.

 

Wani irin kallo mai cike da tausayi Hamdan take yimata, shikuwa Abey cike da farin ciki yake saka mata albarka bayan wasu sakanni yayi hanging call din.

 

Jawo ta Hamdan tayi ta rungume ta hawaye na zuba a idanun ta, saboda tasan qanuwar ta zata cutu a wannan auren, saboda hakurin ta da rashin Magana, shi kuma wanda za’a aura mata sam ba mijin daya kamata ta aura bane.

 

Sai da Fatouma tayi kuka har idanuwan ta suka yi jawur sanna Hamdan ta d’ago ta suka dawo cikin dakin, gudun kar sanyi yashige ta yasa Hamdan ta taimaka mata ta canja kaya tasha magani sannan ta kwantar da ita tare da ficewa daga dakin.

 

Wani irin rawa jikin ta yakeyi saboda Abey yace anjima Hammad zaizo , Kuma tasan dole tare da AMJAD zasuxo , saboda tasan su abokaine.

 

Zuciyar ta bugawa takeyi Kaman zata faso ‘kirjin ta saboda har tanajin karan bugun a waje, wayan ta ta dauka tare da kamo numban AMJAD tayi dialing, ringing daya ya dauka tare da fadin “Fatouna”.

 

Wani rin kuka mai daga hankali ta saki wanda yasa zuciyar AMJAD bugawa da mugun karfi, bai sake cewa komai ba ya kashe wayan ya nufo cikin gidan , Hamdan naganin shi tasan mai faruwa ta faru , sunan shi takira.

 

Dukda baya cikin natsuwar shi hakan bai hanashi tsayawa ba, tasowa tayi ta karaso inda yake ta kama hannayenshi guda tare da fadin, “duk abunda yasamu dan adam kaddararshice a hakan”.

 

Ku rungumi kaddara ayanda tazo muku inshaAllah zakuci ribar hakan.

 

Jaye hannayen shi yayi yanufi dakin Fatouma hankali atashe , saboda yazaci wani abunne yasame ta.

 

Koda yatura kofan, tana kwance hawaye na tsiyaya a fuskan ta duk wani mai imani dole ya tausaya mata, dasauri ya karasa gurinta , tana ganin shi ta mika mishi hannu.

 

Akwai abunda bakin ta yakeson fada amma harshen ta yayi mata nauyi, yana karaso wa ya tada ita daga zaunen tare da rungume ta Kaman wanda za’a raba da mahaifiyarsa.

 

Sai lokacin Fatouma ta iya bude bakin ta tafara magana, “Hammana , (dayake haka take kiranshi), Hammana ka yafe mun nayi sandiyyar rushewar rayuwar mu.

 

Wallahi ina sonka son da ko kaina bana yiwa shi, ina ji idan na rasa ka Kaman na rasa numfashina, yau na yanke wani hukunci ba tare da sanin ka ba, a sanadiyyar hakan inaji Kaman bazan kara mintuna arayeba.

 

Inaji kaman naci amanan ka naci amanan soyayyar da kakeyimun, amma Kuma nasan bazakaso insa’bawa Waleed ba Kuma nasan bazaka ga laifi na ba.

 

Hammana kayimun kowane kalan hukunci amma karkace zaka yi fushi dani, karkace zaka saka zuciya ta cikin bakin ciki, kayafemun, nan da wata daya za’a dauramun aure da Habban”.

 

Kaman saukan aradu haka AMJAD yaji wannan maganan akunnuwan shi, bai san sanda ya ture ta bayaba tareda tashi daga kan gadon ya….

 

ya Allah am so interested in this book yanzun aka fara labarin karda kubari abarku abaya

 

Gamai bukata yanemeni ta wannan number08085056584

 

#fatymasardauna

 

#meeerarh

[30/07, 12:36 am] +234 706 743 6567: *fatymasardauna*

 

*by meeerarh*

 

*2*

 

Kaman saukan Aradu haka AMJAD yaji wannan maganan akunnuwan shi, baisan sanda ya turetaba tare da tashi daga kan gadon yana mai dafe kanshi da yake Neman tarwatse wa, ganin haka ne yasa zuciyar Fatouma bugawa da mugun karfi .

 

Juya wa AMJAD yayi tare da nufan kofan fita daga dakin, saida yakai kofa sannan yabjuyo yace mata , “Fatouna ina miki fatan alkhairi a rayuwar auren ki, Allah ubangiji yasa gidan zamankine , Allah ya hada kawunan ku, dan Allah karbkiyi abun da Abey zaiyi fushi dake .

 

Ya wuce koma a gurin ki, amma ina me tabbatar miki daga rana mai kama data yau bazan sake farin ciki ba, bazaki sake ganin murmushi na ba, zan tayaki yiwa mahaifinki biyayya.

 

Sannan gobe zan koma London idan an fara biki zan dawo , saboda bazan so bananan ayi auren farin ciki na ba , Fatoouna kina da muhimmanci arayuwata, kisani har abada ke ce farin cikin Amjad, kuma bazan daina sonkiba har karshen rayuwana .

 

KISANI KE CE RAYUWATA KE CE RUHINA ,KECE DUNIYATA, IDAN DA RABO ZAN SAKE GANIN KI IDAN KUMA ALLAH YA DAUKI RAINA, ZAMU HADU A AL’JANNA ZANGA ‘YA’YANKI” , yana gama fadan hakan ya juya yafi ce daga dakin .

 

Ganin ya ficene yasa Fatouma sulalewa a kasa tana numfashi sama sama.

 

A palo kuwa ganin Amjad yafita da hawaye a fuskansa yasa Hamdan tashi tanufi dakin Fatouma, ganin halin da take ciki ne ya sakata saurin karasowa , hannunta Fatouma tarike da matukar karfi wanda hakan yasaka Hamdan runtse idanuwan ta da matukar karfi, cike da jin zafi acikin zuciyar ta.

 

A can waje kuwa Amjad na fita daga cikin part din yaci karo da maman su, ganin da yayi matane yasa wani irin kuka yazo mishi , cike da karyewar xuciya ya karasa inda take ya rungume ta.

 

Runguma yayi mata irin wacce daka gani kasan zuciyar sa tayi rauni, rungumeshin tayi itama tana shafa bayan shi, sai da yayi kuka har rauninsa yabayyana sannan ta dagoshi ta shiga share mishi hawayen dake cigaba da zuba a fuskan shi,magana tafara yimishi a cikin rarrashi.

 

“Shh Amjad dear kar kayi kuka, komai yayi zafi maganin shi Allah, kuma nasan kai mai imanine akan komai, nasan kasan Allah ne ya kaddara koma meye amma yanxu kayi shiru addu’a ce maganin wannan kukan naka”.

 

Tana gama fadan haka taja hannun sa suka juya suka nufi part dinsu  , dakin shi ta nufa kai tsaye tare dashi, suna shiga ta sakashi wanko fuskan shi tare da kwanciya a kan gado , sai da taga ya natsu sannan ta fice a dakin.

 

Tana tafiya tana tuno irin karyewa da raunin data gani a cikin idanuwan shi, lokacinne kuma abokiyar zaman ta ta fado mata a rai , wacce take yayar Amjad , kuma ‘kanuwa agurinvta mai tsananin hakuri, da kau da kai, wacce Allah yayiwa rasuwa shekaru kadan dasuka wuce.

 

Wanda kuma tasan da tana raye Amjad din ba zaiyi kuka haka ba, numfashi tasauke asanda ta karaso kofar da zata sadata da part dinta.

 

Koda tashiga palon ganin babu kowa yasa ta nufar  dakinta, ta zo wuce wa ta kofar dakin Fatouma taji suna Magana tsakanin ta da Hamdan.

 

Abun da tajine ya sakata tsayawa domin jin karashen maganar.

 

“Kina jina Fatou kiyarda da mahaifinki, a farko nayi tunanin dan a cutar dake akayi wannan hadin.

 

Amma dana duba tsananin son da mahaifinki yake yi miki sai naga ashe babu yanda za’ayi uba yacutar da ‘dan daya Haifa acikinsa.

 

Habban, shine alkhairinki shine duniyar ki kuma shine lakhirarki right now , kiyiwa mahaifinki biyayya.

 

Nasan mama kanta idan taji wannan maganar, bazatayi bakin cikiba, Habban bayada wani mummunan hali , kawai dai daga yanayinkine, kina da sanyi shiyasa na zaci hakan zai zama cutarwa agareki”.

 

Murmushi maman tayi tare da turo kofan tashigo bakin ta dauke da sallama, ganin mama tashigo fuskanta dauke da murmushi yasa Fatou saurin goge hawayen dake afuskan ta saboda batason ganin bacin rai a fuskar maman ta.

 

Kuma ta san matukar taga yanayin ta wannan murmushin xai kau daga kan fuskan ta,ganin haka yasa mama kara fadada murmushin dake kan fuskartan.

 

Saboda tana da yakini saboda kar ranta ya ‘baci Fatoun ta goge hawayen, kuma aran ta tana farin ciki da samun ‘ya’yan da zasu yankewa kansu hukuncin daya dace koda bata raye.

 

Karasowa inda suke tayi tare da da xama a tsakiyan su, kwantowa kowaccensu tayi a kafad’an ta ita kuma ta daura hannayenta akawunansu ta fara Magana .

 

“Yarana sun girma har an fara Magana ba buni aciki, so a fadamun me ake tattaunawaa, takarasa maganan tana kallon Hamdan”.

 

Hawayen dake fuskan ta ta goge tare da fadawa maman abun da ke faruwa, cikeda karfin guiwa maman takalli fatou tace mata, “ALKHAIRINE SHIDIN AGURINKI , YANDA KIKAYIWA MAHAIFINKI BIYAYYA BAZAKI TA’BA GANIN BA DAIDAI BA A RAYUWARKI, NI MAHAIFIYARKI NAYIMIKIN ALKAWARIN HAKAN.

 

“Now tashi maza ki wanke fuskarki, duk idonki sunyi kananu fuskan ki yayi ja”, tana fadan hakanne tana tashin Fatoun daga zaunen datake.

 

Ganin yanda mahaifiyar ta tayi farin cikine ya sakata sakewa ta fara wasu abubuwan, ganin tasaki ranta ne yasa Hamdan sakin nata ran , dukda tasan acikin ranta tanajin zafi.

 

ASALIN FATOUMA

 

Alhaji Muhammad Sardauna, shine sunan mahaifinta, inda yake dan kasuwa mai rufin asiri, yanada mata guda biyu, Hindu ta farko mai kimanin shekaru 18.

 

Mahaifiyar Fatouma, saikuma Wafiyya matarsa tabiyu mai shekaru 19, a rana daya aka aura mishi su kasancewar daya za’binsace wato Hindu.

 

Ita kuwa Wafiyya mahaifinshine ya aura mishi ita, kasancewarvta yarinyar amininsa, kuma mahaifinshi babban mutum ne Alhaji Habib sardauna.

 

Sunyi zaman amana da mutunci a tsakaninsu, inda bayan shekara daya da auren Hindu ta haifi yaranta guda biyu mace da namiji, wadanda sukaci sun MUSTAPHA ana kiranshi da Musty da UMMULKHAIR Hamdan.

 

Sosai sukayi farin ciki da wannan ‘karuwar , bayan shekaru uku har lokacin Wafiyya bata samu ciki ba, tun ba ta damuwa ganin hakan bai damu mijinta ba.

 

Har itama yafara damunta, alokacinne suka yanke hukuncin ta dauko Amjad saboda babu dadi zama mutuum daya, dukda Hindu ta so tabata Musty amma taki, so lokacin Amjad yana shekaru 3 ne , Amjad kanine agurin Wafiyya .

 

Bayan wasu shekaru Hindu ta kara haifo yarinyarta kyakkyawa wacce take kama da mahaifin ta sak inda ranan suna taci sunan mahaifiyar Alh sardauna .

 

Inda ake kiranta da fatou, tun tasowar Fatouma, Allah yahada jininta da Amjad, sosae soyayya tashiga tsakaninsu har girmansu.

 

A lokacin da Fatou take da shekaru sha biyu Allah yayiwa Wafiyya rasuwa, sosae wannan gida sukayi kukan rashin mace mai hakuri.

 

Bayan shekaru uku Amjad ya bayyanarwa Fatou abun da ke ransa agame da ita, babu wani bata lokaci ta amince masa , dagananne Allah yasaka wata iriyar shakuwa a tsakanin su fiye da chan baya…..

 

Ohk done for the day

#MEEERARH

*fatymasardauna*

 

*by meeerarh*

 

*3*

 

A lokacin da Fatou tacika shekaru sha biyar,  soyayyar ta da Amjad babu Wanda bai sani ba.

 

Saboda irin kula da affection da ke tsakanin su, aduk inda dayansu ya zauna tabbas sai anyi maganar dayan.

 

Sosai maman Fatou tayi farin ciki da wannan abun , saboda tasan yanda Amjad yake da tsananin kyawun hali, a lokacin taso fa’da wa Abey.

 

Amma ganin cewa Fatou yarinyace , sai ta bari akan sai ta gama secondary school, a lokacin da  take shirin fa’da mishi kuma sai ta ji wannan maganar, ita kuwa ba abun da za tace sai dai godiya ga Allah.

 

CIGABA.

 

Sosai Fatou ta koma wani iri sanin da tayi cewa Amjad yabar kasar ya saka ta kara shiga wani hali, saboda gani ta keyi ba zata sake ganin saba har abadan.

 

Yau kwanaki biyar Kenan da Abey yayi mata wannan maganar, amma har lokacin basu taba yin ko da gaisuwa da Habban ba.

 

Abunda ya ‘daure wa Hamdan da Musty kai Kenan, ganin cewar ha’da su a kayi amma ace ba zaya iya kiranta ba.

 

Tun da akayi maganar ma bai ‘kara zuwa gidan ba, kodai baya sonta ne.

 

Duk da cewar basu ji da’din ha’din ba , amma haka suka ‘karfafa mata guiwa cewar lallai ba zatayi dana sani ba.

 

Haka rayuwar ta cigaba, ana saura kwana biyu a ‘daura aure kasancewar babu wani abu da akayi a bikin, ‘yan uwa ma tsirara kawai suka zo kasancewar familyn nasu ba suda wani yawa.

 

Amjad ya dawo ana gobe ‘daurin aure, ko da ya shiga gida gurin Abey yafara zuwa ya gaishe shi sannan ya wuce part din su shida Musty.

 

Yayi freshen up ya kwanta, karfe 6:30pm ya tashi, ganin cewar har anyi sallan magrib ya sakashi kiran sunan Allah , thinking of abun da ya sameshi har yakai yanzu yana barci shida tun 11 am ya dawo.

 

Tashi yayi yayi sallolin da suka wuce shi sannan yayi wanka bayan yayi isha’i kuma ya nufi cikin gidan.

 

Koda ya shiga cikin harabar part din mama, Fatou na kofar palon zaune hannun ta riqe da picture dinsu ita da shi lokacin dayayi proposing dinta.

 

Dafe daidai sautin zuciyar sa yayi saboda yanda take duka da matsanancin karfi.

 

Kafin ya dawo ya zaci zai iya jure rashin ta, amma ganin da yayi Mata yasa duk wani karfin guiwa daya ke dashi ya rugurguje.

 

Itakuwa Fatou jin idon mutum akan ta ya saka ta ‘dagowa,  yana ganin ta yayi saurin fita daga part din.

 

Da sauri Fatou ta bishi  tana kiran sunanshi,”Habiby , Habibyy please ka tsaya ka saurare ni, koda wannanne zai zama magananmu na karshe , please”, ta’karasa inda yake tare da zubewa a gurin.

 

Shima ganin ta zauna akasa ya sakashi zama yanda zasu fuskanci juna.

 

Hannuwan sa guda biyu ta riqe a cikin hannayen ta , wani irin yanayi mai matu’kar wuyar fassara wa suka shiga .

 

Wani irin yawu mai ‘daci Amjad ya ha’diye yana jin kaman yadauke ta su gudu.

 

Amma idan yayi hakan bai yiwa Abey adalci ba, mutumin daya raine shi kaman ‘dan cikin sa.

 

Hannayen sa ya cire tare da miqewa tsaye, har ya juya zai bar gurin ya sake juyo wa tare da fa’din.

 

“Kitashi ki dauko mayafinki mufita yawon karshe”, wani murmushi ne ya kufcewa dukansu a sanda suka tuno irin rayuwar da suka yi.

 

Da sauri tami’ke tare da fa’din “ka jira ni anan please kar ka kuma tafiya kabar ni”, juya wa tayi takoma part din.

 

Bayan wasu mintuna ta fito sanye da sweatpants da longsleeve tshirt kanta kuwa p cap ne, gaba’daya komai  fari tasaka har sneakers ‘dinta, tayi kyau sosai duk da ramar  datayi .

 

Tana ‘karaso wa ta kama hannu shi suka nufi compound ‘din gidan , motan shi yabude kiran Mercedes kalan baki , bayan sun shiga ya ja suka fice a gidan.

 

Downtown restaurants Gombe state, a bakin gurin yayi parking ya fito sannan ya bu’de Mata ‘kofa itama ta fita.

 

Kin tafiya tayi sai bayan yayi nisa ya lura cewa bata binshi,  juyo wa yayi ya fara dube dube , a bakin motan ya hangota ta du’kar dakai ‘kasa.

 

Koda ya dawo yaja hannun ta tafara turje wa,  wata irin posh dariya yayi da ya sakata yin murmushi dan tasan meyake shirin yi.

 

Yi yayi kaman zai tafi sai kuma ya juyo tare da ‘daga ta sama ya fara tafiya, nan take tafara ‘kyal’kyalewa da dariya kaman ba ita bane take cikin matsananciyar damuwa ba mintuna ka’dan da suka wuce .

 

Bayan shi ta fara bubbuga wa tana fa’din “Amje ka saukenifa”, aikuwa nan take ya sauke ta dan bayason sunan da take kiran shi wai Amje.

 

Tana ganin ya sauke ta ta fara gudu saboda ta san me ta aika ta,  ai kuwa in no time yafara binta a baya,  nan take hankulan mutane ya fara dawowa kansu.

 

Acikin mutanen kuwa har da Habban, ko da ya gansu sosai ransa ya ‘baci, ai kuwa baiyi wata wata ba ya nufi inda suke fuskan shi kaman bai ta’ba dariya ba.

 

Amjad kuwa da yake gudu sai ji yayi an jawo rigar shi da ‘karfi har saida ta yage,  cikin matsanancin shock ya zaro ido saboda yasan ba Fatou bace.

 

Da ‘karfi ya juyo da niyyar kaiwa ko waye duka, idanun shi sukayi tozali da Habban.

 

Daidai lokacin Fatou ta qaraso inda suke tare da fizge hannun Habban daga jikin Amjad tare da shiga tsakanin su.

 

Mr Man waye kai dazaka taba shi da kazamin hannunka? ,  idanu Habban ya zato tare da nuna kanshi cike da bacin rai ya ce “ni kike tambaya waye ni” ?.

 

Hannayen ta ta sar’kafe a kirji tare da fa’din, “yes kai din nake tambaya sai akayiwa”.

 

Murmushi ne ya ‘kwacewa Amjad dan shi kadai yasan wannan halin na Fatou akwaita da Jan magana.

 

Cikin karfin hali Habban yace “Fatou gobefa za’a daura mana aure amma kikece wa wayeni , duk dan saboda wannan wawan”.

 

Nan take Amjad ya ha’de fuska tare da matsar da Fatou gefe yace,  “oh hello ya isheka , dakake cika baki cewa gobe zaka aure ta ka ta’ba kiran ta tun da aka saka muku rana.

 

Ko ka zaci ban san waye kai ba,  kabi ahankali banada kirki kai kafi kowa sanina, so u better look out what is coming out of your mouth”.

 

Cike da bakin ciki Habban ya jawo hannun Fatou yana fadin come mu tafi gida sai na fa’da wa Abey abun da kikeyi da wannan mutumin.

 

Ko taku biyu baiyi ba ya ji an riko hannun sa , hannun Fatou dayake cikin nashi ya ji an cire , koda yajuyo Amjad yagani a gabanshi fuskarshi babu alamun sauki.

 

Saida kirjin shi yabuga ganin yanayin Amjad din kuma yasan dalilin hakan , saboda yata’ba Fatou ne.

 

Wani irin naushi yaji abakin shi da ya sakashi gigicewa, bai dawo daga duniyan da ya tafi ba ya kuma jin wani naushin.

 

Cikin tsananin zafin rai Amjad ya nuna shi tareda fa din, “idan ‘kazamin hannun ka ya kuma ta’ba ta wallahi sai na raba ka dashi.

 

Habban kabi ahankali kai ka san na san waye kai , zan iya ‘bata komai, saboda ban da proof shiyasa ban tunkari Abey ba.

 

Don’t provoke me,  banada kirki akanta , itadin rayuwata ce kuma alfaharina ce, bugun zuciyata ce, kuma kasan abune mai wuya a ta’ba bugun zuciyar mutum”.

 

Yana gama fa’dar haka yaja hannun Fatou suka bar gurin, driving yake yi amma hannun Fatou yake gani cikin na Amjad.

 

Sosai Fatou taso tambayar shi akan Habban din amma tana tsoron halin da zasu shiga su duka.

 

Ahaka har suka dawo gida babu Wanda ya yiwa wani magana,  bayan mintuna biyu da tsayawar su aharabar gidan babu wanda ya fita daga Motan.

 

Cikin dakiya Amjad ya ce “kishiga gida kar mama taneme ki kin ga goma ta kusa zan shigo idan nayi wanka”.

 

Hawayen da take ‘ko’karin riqewa ne suka gangaro kan fuskan ta, ganin hakan yasa shima nashi hawayen suka gangaro.

 

Cikin sanyin murya tafara magana,

“Amjad , daga wannan daren na haramta a gareka, inajin ciwon hakan, idan na tuna wani zan aura ba kai ba, zuciyata zafi yakeyi.

 

Idan na tuna gobe ne aure na dawani raina ba’kin ciki yake shiga,ina fatar Allah yasaka mana da mafificin alkhairin shi”.

 

Tana gama fa’dan hakan ta fara ‘ko’karin bude motar, ganin hakan yasa Amjad yayi saurin riqe hannun ta.

 

Aikuwa kaman Jira ta keyi ta juyo da rungume shi kaman her life depends on it.

 

Cikin matsanancin rauni da ciwo dukkan su suka saki kuka mai tsananin ban tausayi.

 

A dai dai wannan lokacin kaddarar ta koma rababba,  a wannan daren rayuwa tazo musu da wani sauyi,  a dai dai cikin motarnan Fatou da Amjad  suka kasa……

 

So tired InshaAllah gobe zan Baku wata part ….

 

Mekuke tunani yafaru wace kalar kaddarace takuma samunsu kubiyoni dominjin menene

 

Wattpad @meeerarh

*fatymasardauna*

 

*by meeerarh*

 

*4*

 

 

 

 

 

A yayin da numfashin su yake gauraya da na juna, yayin da kowannensu yakejin bugun zuciyar ‘dan uwansa,

 

A dai dai lokacin ne ruhin kowanen su ya ji yana bu’katar kasance wa da na juna.

 

Bayan mintuna sha biyar da da suka yi rungume da juna,

 

Amjad yayi karfin halin raba jikinsa da na ta , amma sam ta’ki bashi damar yin hakan.

 

Cikin dishashiyar murayar ta da ta sanja lokacin ‘daya tafara mishi magana tana kara shige wa jikin sa,

 

“Please Hammana karka bari wannan damar ta wuce mu.

 

We need this, muna bukatar hakan, idan ka bari na tafi yanzu ba lallaine mukara kasancewa haka ba.

 

Amjad kaine kawai a zuciya ta, let’s do this please”.

 

Wani irin numfashi ya ja cike da matsanancin bugun zuciyar ya ce, Fatouna bai kama ta muyi hakan ba.

 

Gobe ne auren ki, kuma mukayi hakan ba muyi kanmu adalci ba.

 

Cikin mutuwar jiki ta taso daga jikin sa tare da ha’de bakin su guri daya, kaman daman jira ya keyi .

 

Yana jin hakan ya ‘kara matso da ita jikin sa yana me cigaba da kissing din ta hawaye na zuba daga idanuwan duka su biyun.

 

Jikin ta ta cire daga nashi tare da bu’de motan ta fita, numfashi ya sauke da karfi tare da jingina da kujeran dayake kai .

 

Bai ankara ba ya ji ana ‘ko’karin janshi,  shanyayyun idanuwan sa ya bu’de cikin mutuwar jiki .

 

Koda yaga ita ‘dince lumshe idanuwan sa ya kuma yi tare da fita daga motan.

 

Part dinsu ta fara janshi , tafiya yakeyi amma sam hankalin sa baya jikin sa,  ya naso ya ce mata abun da suke shirinyi bai dace ba.

 

Amma sam bakin sa yayi nauyi,  kuma shima ya na son hakan ,amma Abey fa bai kamata suyi mishi hakan ba.

 

Bai ankara ba yaji tana ‘ko’karin bu’de kofan ‘dakin sa.

 

Shi tsoron sa ‘daya ma kar Musty ya shigo dan yanzu kusan karfe sha daya yasan zai iya shigowa ko da yaushe.

 

Dakin nasa suka shiga,  bata ‘bata lokaciba tafara ‘ko’karin cire kayan jikin ta.

 

Ganin hakan ya ‘kara tsorata shi saboda shi ya zaci da wasa takeyi,  hannunsa ta jawo tare da hawa saman royal bed dinshi dake cikin dakin.

 

Kasa ta du’ka tare da fa’din, “a yau inaso katabbatarmun da soyayyar ka a gareni.

 

Idan dai har kana sona da gaske ka kar’bi budurcina , ni kuma bazan ta’ba yin danasanin mallaka maka shiba.

 

Ina so na zama mallakin ka kuma tawannan hanyar kawai hakan zai yu, ko da ban aure ka ba.

 

Zan ji da’di idan na tuna kaine wanda ya fara sanina amatsayin ‘ya mace, dan Allah Amjad na ro’ke ka”.

 

Tana gama fadar hakan tadawo saman gadon tareda kwantawa akan jikinsa.

 

After 40minutes

 

Hawayene ke zuba akan fuskanta tareda murmushin farin cikin datake ciki.

 

Ba zata ce bata ji zafin abun da yayi mata ba, amma farin ciki ya  lullube wannan zafin.

 

Kara shigewa jikin sa tayi tare da fa’din “nasan kana jin kunci,  amma hakan da kayi zai saka duk san da ka tunani , zaka tuna wannan moment din.

 

Ina farin ciki sosai fiye da yanda kake tunani, nagode Hammana nagode sosai,  zan ciga ba da son ka har karshen rayuwa na”.

 

Hawaye ne suka gangaro daga idanuwan sa,  “Fatou kisani ke ce rayuwata,  kece karfin guiwana.

 

Ina ba’kin ciki idan na tuna cewa na karbi budurcinki batare da aure na akankiba.

 

Munyi zina abun da Allah yahana, mun yiwa kanmu rashin adalci.

 

Amma ina farin ciki sosai a zuciya na,  bansan dalili ba,  ki tashi kiyi wanka ki koma gida.

 

Idan kinshiga ki cewa mama dani kika fita , mun ajiye memories dinmu na karshe,  ba zatayi miki fa’daba.

 

Bayan wasu mintota bayan ta gama kimtsawa tanufi kofar fita tana tafiya dakyar.

 

Zaro idanu tayi saboda ……

 

ALHMDLH xamu tafi hutu mu ayi sallah lafiya …..bye bye

 

​

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


1 Comment

Leave a Comment