Hausa Novels

FHATEEHA HAUSA NOVEL

FHATEEHA HAUSA NOVEL

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Fhateeha*

*~free novel~*

 

 

*~Writing by Zainab Sageer Shi’eetawah~*

 

 

*Gargadi*

Banyar da wani ko wata ya juya min littafiba kije kiyi taki fasa har idan kunni yaji gangar jiki ya tsira

 

*Tsokaci*

Labari na qagaggen labarine ban yi don wani KO wata ba so Idan kinga yazo dai dai rayuwarki kiyi hakuri

 

*Jinjina*

Ina mika jinjina ta a gareki yar uwata abin alfahari na *Aunty kausar*(real kausy) ina godiya mai yawa a gareki Allah yabar kauna

 

 

*Page1&2*

 

 

____________________

Kwance take a daya daga cikin kujerun dake cikin madai daicin parlon hannun ta rike da waya tana buga game wanda ya dauke mata hankali har bata san lokacin da Maman ta tashigo parlon ba

Sai saukar dukan da taji a gadon bayanta

Wani tsalle tayi ta sauko daga kan kuje ran tana ihu tana cewa

” wayyo bayana ya fashe mama kin fasa min baya ” ta karesa fada tame sosa bayan ta

Mama dake tsaye tana kallon ta tace

 

” au nine zan fasa miki bayan? To bari kiga fasa baya ” tajuya tana neman abin duka

Ai ganin haka d yasa yarinyar nan mike da gudu tabi hanyar fita daga parlon tafito tsakar gidan su tana ihu tare da cewa

“hajiya kizo ki taimake ni mama zata kasheni da duka”

Wata mata ce naga ta fito wata karamar hanya hannun ta rike da buta da alamu daga bandaki ta fito.

Sakin butan tayi akasa tayo kan yarinyar nan da ke rike da baya ta kuka

 

“Waya tabamin ke shalelena wani mugun ne wllh bazan yarda ba babu wanda aka tsana a cikin gidan nan sai shalelena saboda ba a kaunar ta to bazan yarda ba babu wanda zai tabata in barshi ko waye ehee”

 

Matar ta fada tare da kamo hannun yarinyar da takira da shalelen ta

Itakuwa shalele kara narkewa tayi ajikin Matar tana jan majina kamar wata karamar yarinya tace” ba mama bace kawai ina kwance tazo ta kama duka na ban yimata komai ba ”

 

Jan hannun ta hajiya mama tayi tana cewa ” zo muje gurin Haliman Inji dalilin taba ki”

Binta tayi suka numfu parlon mama ko sallama babu

 

“Ina Haliman? Halima! Halima!! Halim….. ”

Fitowan mama daga daki ne ya katse mata kiran datake mata

 

“Lafiya yaya kikemin irin wannan kira? Me yafaru? ”

“Au tambaya na ma kikeyi to bansani ba nace ban saniba yanzu Halima tsakanin ki da Allah abin da kikewa yarinyar nan ya dace kenan? kullum cikin tsangwama da kyara

To wllh na gaji bazan dauka ba ”

 

Cewar hajiya mama cikin fusata kamar ita aka daka mama tsaye tana kallon Ikon Allah abinnan yana bata mamaki duk da bayau tasaba ganiba amman nayau yafi bata mamaki saboda ganin yadda hajiya mama take masifa kamar ita aka taba.

Kai gaskiya akwai alamar tambaya kan lamarin nan domin dai ita tasan wacece hajiya mama amman dai…….

 

” ke Halima wannan wani irin wulakanci ne ina magana kin saki baki kina kallona”

 

Maganar hajiya mama ne ya katsewa mama tinanin ta

 

” to yaya me zance miki? *Fhateeha* fa ba yarinya bace da kullum za Ana mai mai ta mata Abu daya

Wanke wanke fa nasata tun dazu Amman takiyi tazo ta kwanta tana game duk abin da nace tayi min sai tayi man gardama bazatayi ba

Tana kallo ay ba haka Halisa keyi ba amman ke yaya sam baki ganin abinda take takeyi amatsyin kuskure ”

 

“Eh bana ganin shi a matsayin kuskure kuma bazan gani ba idan kuma kina so kinuna min bani na haife ta bane sai ki nuna min din ”

 

Hajiya mama ta fada cikin hassala,

Girgiza kai mama tayi cikin murmushin ta kaici sannan

 

Tace ” yaya ba haka nake nufi ba amman kiyi hakuri idan kinji haushina ”

Tana gama fadan haka tajuya tashige cikin dakin ta tabar sunan tsaye

 

Duk wannan budirin da akeyi fhateeha na makale abayan hajiya mama tana jin su ko ajikin ta domin dai idan da sabo tasaba jin irin wannan takaddamar da sukeyi akan ta

Ita dai tarasa mai son ta na gaskiya tsakanin mama wato mahaifiyar ta dakuma hajiya mama kishiyar mahaifiyar tata amman gaskiya tafison hajiya mama saboda aganin ta hajiya mama tafi mama son ta

Saboda hajiya mama tana goyon bayan duk wani rashin ji da zatayi kome zatayi hajiya mama zata kareta.

Sabanin mama da take takura mata a ganin fa amma.

Hajiya mama taja hannun fhateeha suka fita daga parlon

Suna fitowa daidai kuma matar gidan ta uku ta fito daga kitchen hannun ta rike da karamar roba

Kallonsu tayi shekeke sannan taja uban tsaki

Tace

“shi dai munafuki baiji dadin rayuwar shiba ”

Juwowa hajiya mama tayi da sauri tace

 

“Ke saude dawa kike? ”

Dasauri saude tace

” a’a yaya ba da ke nake yiba ”

 

“OK kin ceci kanki da kin gane kuren ki” cewar hajiya mama ta cigaba da tafiya

Fhateeha ce tajuyo ta watsawa Matar harara sannan ta juya.

Girgiza kai tayi kawai sannan te hucewar ta dakinta

Hajiya mama ko dakinta suka shiga fhateeha tasami guri ta zauna tana cewa

 

” hajiyata ina Halisa taje naga ban ganta ba ne”

 

Hajiya mama dake kokarin shiga daki tace

” na aike ta gidan hajiya Salamatou zata karbo min sako”

 

Fhateeha tayi saurin cewa ” shine baki aikeni ba”

 

Hajiya mama tace

” a’a shalelena banasan ki wahala ne shiya sa ”

 

Amman a zuciyar ta cewa take

” in ayke ki salan ki tona min asiri ko shegiya sai na ga bayanki ke da uwar ki dangin mayu…… ”

 

“Shiyasa nake son ki hajiyata Allah ya barmin ke ”

 

Fhateeha ta fada cikin jin dadi

Murmushi hajiya mama tayi mai cike da ma’anoni masu yawa

Sannan tace ”

Matso shalelena inason muyi wata magana dake”

 

Tasowa fhateeha tayi tama tso kusada hjy mama inda tasami guri ta zauna

Hajiya mama ta shafa kanta sannan tace

 

“Ina son ki nutsu ki fahimceni sosai ”

Fhateeha tace “to hajiya ”

 

Hajiya mama tace “Ina san kisani cewa duk duniya babu mai sanki da gaskiya kamar ni bazan so abin da zai cuceki ba duk wata shawara da zan baki me kyauce

Maganar gaskiya shine Halima bata sanki bata kaunar ki da ita da wancan munafukar matar saude kiduba irin yadda Halima take takura miki sam bata kaunar ta ganki cikin farin ciki kullum cikin takura ki takeyi

Yanzu duba fa yan kananun kayan da kike sawa ma cewa tayi ki dai na gashi suna miki kyau sosai dama kuma ke me kyauce ”

 

Ta karasa maganar ta washe hakora.

Fhateeha kuwa tashiga dogon tinani akan maganar hajiya mama

Tabbas tasan abin da ta fada gaskiya ne to amman abin dubawa anan shine taya zatace mama bata sonta ita fa ta haifeta kuma a ce bata son ta?

 

“Tinanin me kikeyi ne shalelena ”

Kallon ta Fhateeha tayi bayan gajeran tinanin da ta tafi

 

Tace” hajiya nayar da duk gidan nan kece kadai me sona na amince kinamin son da ko Halisa bakima ta shi nagode hajiya kuma namiki alkawarin duk abin da kikace nayi zan yi miki shi insha Allah ”

Wani shi’umin murmushi hajiya mama tayi mai cike da ma’anoni sannan tace

 

“Shiyasa nake kara sonki shalelena ”

Murmushi kwai fhateeha tayi batare da tace komai ba

Hajiya mama tace

“yauwa gobe zamuje kasuwan saban gari dake zan siyo miki wasu babbin kananan kayan kinji? ”

 

Cikin farin ciki fhateeha ta rungume hajiya mama tana cewa

 

“Sai hajiya ta wllh ina yinki irin sosai din nan ”

Dariya tayi kawai hajiya mama tayi

 

Ni kam mai kawo muku rahoto ina gefe ina kallan iko Allah

Sai yanzu na sanu damar kare mata kallo

Fhateeha yarinya ce yar kimanin she kara goma sha bakwi

 

Farace kal irin farin nan me daukar ido sannan doguwa ce amman ba can ba tana da murjewar jiki tana kuma da dogon fuska mai dauke da manyan idanu masu kama da na mage tana da dogon hanci da dan qaramin baki dai dai misali ga dogon gashi ta mai kyau Masha Allah

Fhateeha komai nata mai kyau ne wannan kyan nata yana daya daga cikin abinda yasa samari ke rududuwan zuwa wajen ta sai dai ita sam ba ta takan su ita tun da tasami wanda take sonshi yake sonta ay tagama kuma shiyasa bata takan su sam

 

“Assalamu’alaikum”

 

Naji sallaman abayana najuya dan ganin wacce tayi sallaman

Wata yarinya ce wacce bazata huce tsarar fhateeha ba tashigo parlon jikin ta sanye da dogon hijabi har kasa

Fhateeha ce ta amsa sallamar tamike da sauri tana cewa

 

“Oyoyo my sister sannu da dawowa ”

Rungume juna sukayi

 

“Nayi fushi shine kika tafi baki ne meni bako? ”

 

Cewar fhateeha tana me bata face

 

“Sorry sis wllh hajiya ce tace nayi sauri na dawo kar na dade kuma nasan idan mukaje tare sai mun dade shiyasa shiyasa ban neme kiba Sorry”

Dariya Fhateeha tayi tace

 

” lahhhh sis bako mai fa dama wasa nake miki ”

 

“Idan kun gama shiriritar sai kuzo nan ”

Suka tsin kayi maryar hajiya mama tana musu nagana

Juyawa sukayi suka shiga cikin parlon suna shiga fhateeha tace

“Hajiya ta bari naje nayi wanka ”

 

“To shalelena maza kije kiyi”

 

Ta amsa da “to”

 

Tajuya ga Halisa tace

 

“sis sai na fito”

Tace

“to sai kin fito”

Ta sa kai ta fita

Tana fita Halisa taja wani uban tsaki tare da cewa hajiya wllh na tsani yarinyar nan bana kaunar ta sam

Hajiya Fhateeha tafini komai na rayuwa

Tafini kyau tafini ilimi boko da na islamiyya tafini farin jini agurin samari samrina daga mai gadi sai Dan acaba haba hajiya itako masu kudi ne kezuwa wajen ta hajiya banida burin da yahuce na auri mai kudi hajiya fhateeha tafini komai hajiy……”

 

Kuka yane yaci karfin ta ta fada jikin hjy mama tana matsanancin kuka

Cikin mugun bacin rai hajiya mama tace

 

“Kiyi shiru Halisa ta nima bana kaunar su wllh wllh wllh ko zanyi yawo tsirara saina saka ahlin Halima kuka sai na lalata rayuwar fhateeha………

 

*Idan naga ruwan comment zan ci gaba*

 

*Comment*

*Share*

*Editing*

 

*mai kaunarku a koda yaushe Zee Shi’eetawah*

 

*~Mrs Salman ce✍🏻~*

Leave a Comment

error: Content is protected !!