Kannywood News

Fitacciyar yar fim Zainab booth ta rasu

Fitacciyar yar fim Zainab booth ta rasu

Yar wasan fina-finan Kannywood, Hajiya Zainab Booth, wadda ke jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rasu bayan fama da rashin lafiya.

Ta rasu ne a birnin Kano da daren Alhamis, a cewar danta Umar Booth, a tattaunawarsa da BBC.

Ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, hakika Allah cikin ikonsa ya yi wa mahaifiyarmu Hajiya Zainab Booth rasuwa bayan fama da rashin lafiya, ta rasu a daren Alhamis da misalin karshe 9 na dare, za a yi jana’izarta a yau Juma’a idan Allah ya kai mu.

Ta rasu ta bar ‘ya’ya hudu, maza biyu da mata biyu, wato Ni Umar, sai Amude da Maryam da kuma Sadiya, sai jikoki guda biyu,” in ji Umar.

Umar ya kara da cewa za a tuna da Hajiya Zainab Booth da son zumunci da yawan yin addu’a, sannan ita din uwa ce ga kowa don haka ne ma duk inda ta shiga za ka ji ana kiranta Mama, Mama.

A kwanakin baya ne dai marigayiyar ta yi fama da rashin lafiya lamarin da ya kai har an yi mata aiki a kwakwalwa, kamar yadda ‘yarta Maryam Booth ta dinga wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.

Marigayiyar ta kasance daya daga cikin taurarin Kannywood da ‘ya’yanta uku suka kasance su ma taurari.

Leave a Comment

error: Content is protected !!