Hausa Novels

Fitar Rabo Hausa Novel Complete

Fitar Rabo Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Fitar Rabo Hausa Novel Complete

{ Love story }

 

NA

*AUTAR MANYA*

 

Bisimillahir Rahmanir Rahim

 

001

 

*GARIN KANO*

_Ɗorayi Ƙarama Goburawa_

 

Ranar litinin da misalin ƙarfe goma da rabin safiya.

Ƙaramin asibitin shaka tafi na goburawa na, nan unguwar goburawa dake cikin garin kano ƙarƙashin ƙaramar hukumar gwale, *Ɗorayi ƙarama Primary Health Care*

 

Cikin asibitin shakatafin wata baƙar budurwa mai kimanin shekaru Ashirin da biyu cif a duniya Doguwa ce mai ƙiba, wadda idan ka dube ta zaka ce takai shekaru kusan ashirin da biyar sabida girman jikinta sedai a haƙiƙanin shekarun ta na haihuwa bazata gaza shekaru Ashirin da biyun ba.

 

Kallo ɗaya zaka yi mata ka kirata da kyakykyawa sabida baƙinta mai kyau ne tana da manyan idanu tare da dogon hanci, girarta cunkus take da gashi wanda har kusan haɗewa yayi laɓɓanta masu kauri ne baƙaƙe kalar fatar jikinta ga wani gashi daya kewaye fuskarta wanda harya gangara wajan sajenta.

Tana da cikar halitta sosai wadda za’a iya sanya ta cikin jerin cikakkun ƴammata.

Sanye take cikin fararen kaya na riga da wando da ɗan ƙaramin hijabi irin na ma’aikatan lafiya (nursing) Zazzagawa take cikin jerin marasa lafiyan dake cikin rumfar asibitin na ɓangaran { general opd} tana duba katinan su cike da zafin nama take aiwatar da aikin nata.

Cikin lokaci kaɗan ta gama da na wajanta Na nan ɓangaren { general Opd), Ta shiga cikin office ɗinsu wanda aka ware musu shi na ɗalibai masu sanin makamar aiki ( practical student)

Zama tayi a saman dogon bancin dake ofishin ta ɗauko wani dogon littafi ( log book ) tare da sanya biro tana rubutu acikinsa takai minti biyar tana  Rubuta dukkan abin da tayi a wannan rana, kafin ta kammala ta rufe littafin sa’annan ta miƙe ta fita waje.

 

Da wata farar budurwa suka ci karo zata shigo office ɗin cikin murmushi farar budurwar tace mata.

“A,a *Nuriyyah* se ina kar dai har kin tashi?”

Zaro idanu tai kaɗan tare da cewa.

“Duba time fa zainab tayaya zan tafi idan aka zo duba mu fa”

Dariya zainab ɗin tayi tare da cewa.

“Matsala ta dake tsoro,To base muce baki da lafiya ba”

Murmushi tayi tare da cewa.

“Zanje na siyo pure water da Alala sabida ina jin yunwa tunda nazo nake tsaye seda na kammala duba marasa lafiyan ɓangare na sannan na sami sukuni zee bara na ƙarasa kafin na kifa”

Tafaɗa cikin azama batare data jira cewar ƙawar tata ba ta nufi bakin gate

 

Jerin masu kayan saidawa zazzaune a bakin asibitin Nuriyyah ta ƙarasa wajan mai saida ruwa domin tafi buƙatar shi a kusa dan ishirwa take ji sosai.

Ta miƙa mai nera hamsin wadda ta fito da ita daga cikin ɗari biyu wanda kuɗin hannun nata sun kama ɗari biyu da hamsin kenan cif.

“Ruwa zaka bani na naira ashirin”

Tafaɗa  wa mai ruwan.

Amsa mata yayi kana ya bata ruwan tare da canjin.

Gefe taja tare da tsugunnawa takai ruwan bakinta ta shanye ɗaya gudan kuma ta wanke fuskarta.

 

Tana ƙoƙarin nufar wajan mai sayar da alala taja ta tsaya saka makon sa’insar data gani ana yi a tsakanin wasu ƴammata damai adai dai ta sahu dake gefen gate ɗin asibitin.

 

Ƙarasawa tai wajan su da sauri taɗan ja ta tsaya tana sauraran mai  ɗaya daga cikin ƴammata take faɗawa mai adai dai ta sahun.

Cikin kwantar da kai budurwar tace masa.

“Dan Allah malam kai haƙuri, Umminmu ce ba lafiya muka kawota wannan asibitin mun fito agigice ne shiyasa bamu fito da kuɗi ba amman yanzu yayar mu anty nabila zata zo seta baka”

Wata ashar! ya lailayo ya maka wadda ta sanya Nuriyyah ƙara zare idanu tana kallon ikon Allah kafin ta farga har taji muryar shi yana magana kamar haka.

“Kunsan Allah baku isa ba wa zaku mayar ɗan wahala na ɗauko ku daga wancan lungun na kawoku nan sannan kuzo kunai min shirme ina sam ku kwashe waccan tsohuwar daga mashin ɗina ku bani haƙƙina nayi gaba”

Cikin sauri ɗayar wadda batai magana ba tace masa.

“Dakata malam karka kawo mana zancen banza har ka gaya mana rashin mutunci muda muke da Yayan daya fika zafin kai billahil lazi ka adana kalaman ka ga ummin mu tun kafin Yayanmu, yazo yaji kana yinsu don tabbas zaka ja wannan akwalar mashin ɗin naka ne da zubabbun haƙora”

Tafaɗa cikin bala’i.

Ɗayar ce ta taɓota tana ce mata.

“Haba hussaina mai yasa baki da haƙuri ne? bafa a gadara da iskanci insha Allah Yaya,ma baze ji ba kuma bana son ki gaya masa dan kinsan halin shi”

Sannan ta Dubi mai babur ɗin tace masa.

“Dan Allah kai haƙuri karkai fushi ba kyau”

Tafaɗa kamar zatai kuka!

 

Da ɗunbin mamaki Nuriyyah ta ƙaraso wajan su sallama tai a nitse.

Tare da kallon mai bawa mai mashin ɗin haƙurin sannan tace mata.

“Mene ne ya haɗa ku dashi? ba marar lafiya kuka kawo ba se kun rasa kati lokaci naja fa”

Murmushi Hassanar tai tare da cewa.

“I ummi mahaifiyar mu muka kawo sedai sauri da gigita sune suka hana mu fito da kuɗin mashin duk da ba a nesa muke ba muna nan gaba layin gidan goburawa to muna jiran yayarmu dake aure acan layin ta fito ne semu basa kuɗin amman yaƙi se tijara yake mana”

Ta ƙarashe maganar cikin sanyin murya.

Kallon su Nuriyyah tai tsaf farare ne kyawawa sedai sutturar jikinsu ma kaɗai ta nuna mata dai duk kanwar jace ma’ana irinta ne suma ƴaƴan talakawa.

Murmushi ta sakar mata tare da cewa.

“Allah ya bata lafiya”

Kuɗin Alalan hannunta naira ɗari biyun nan ita ta miƙawa mai mashin ɗin tare da bashi haƙuri.

Sannan tace musu su shigo da mahaifiyar tasu tayi gaba abinta.

 

Sakin baki sukai suna binta da kallo lallai duk inda aka ce Allah an gama magana ko ina akwai Allah ba da ban ita ba da sedai suyi haƙuri da tijarar mai baburin.

 

Nuriyyah haka ta koma cikin asibitin ta zauna tana jiran su yunwa na sasaƙarta ga ruwa tasha ciki ya rarake.

Amman hakan bai dameta ba kasancewar ta mace mai raunin gaske mai tsananin tausayi dajin ƙai muddin tana da shi wallahi bazata iya wuce mabuƙaci ba shiyasa ba ƙaramin tausayi suka bata ba wannan yasa tai ƙundun balar basu kuɗin karyawar nata ita in taje gida ta samu wani abun taci.

 

Sallamar su gabanta ita ta sata jan dogon numfashi kasancewar tana zaune ne a tsakiyar rumfar da aka tanada dan zaman marasa lafiya da masu amsar kati daga gefe kuma bancine da teburi domin zaman nurse’s ɗin asibitin.

Ɗago kyawawan idanunta tai tare da duban su.

Dafe suke da dattijuwar mace Wadda kyan jikinta na fulanin usul ya ɓoye shekarunta domin kallo ɗaya zaka mata kasan ta haɗa tsatso da fulani.

Duba da yanayin ta fara ce jajir doguwa marar jiki se tsabar madarar kyawu da Allah yayi mata wadda daga ganin ƴan biyun nata kyawunta ma suka ɗauko.

Cikin sakin fuska Nuriyyah tace.

“Sannu! mama ku zaunar da ita ina zuwa”

Ta miƙe cikin azama ta nufi wajan yankar kati saura na mutum ɗaya ma ya ƙare sabida rana tayi domin idan kana son kati da wuri kake zuwa.

Ta amsa ta dawo wajansu tai sallama ta zauna sunan mahaifiyar tasu ta tambaya cikin nutsuwa hassanar tace mata.

“Aisha muhammad”

Domin ita hussaina baƙin cikin mai mashin ɗin ɗazu ya tsaya mata arai ta kasa magana se mitar baƙar maganar sa take aranta.

“Meke damun ta?”

Ta kuma tambayar su.

Cikin tsanaki hassana ta dubi mahaifiyar tasu tare da ce mata.

“Ummi ki mata bayanin yadda kike ji sannu umminmu”

A hankali matar ta ɗago kai ta dubi Nuriyya sannan ta fara yi mata bayani wanda Nuriyyah ta tabbatar ba komai ke damunta ba se lalurar hawan jini wadda ke son motsa mata a halin yanzu.

Rubuce rubuce tai akan katin sannan tace mata.

“Dama kina da hawan jini ne mama ko kuma?”

Murmushi mai ciwo matar tai tare da cewa.

“Ina dashi ƴata kwana biyu ban sha magani ba shine keson tayar mini,se kuma zazzaɓin dana ke kwana dashi kullum nake tashi”

Nuriyyah bata ce komai ba ta cigaba da rubutunta.

Seda ta gama sannan ta miƙe ta nufi cikin wani office,Likitan dake zaune acikin office ɗin ta samu bayan tai mai sallama ta miƙa mai katin ya amsa ya karanta ya ɗago da murmushi yace.

“Welldone fatimah gaskiya in an kammala an samu upper muna buƙatar ki anan but amman zaki rubuta mata injection ta kwana uku sabida akwai maleria dole se an mata allura”

Murmushi tayi da girmamawa ta amshi katin ta koma wajan su ta rubuta alluran tare da miƙawa hassanar tace mata.

“To ƙawata ga drug’s nan na rubuta mata tare da allura na kwana uku seku je chemist ku saya domin nan bamu da waɗannan magungunan sun ƙare”

Godiya sosai hassana tayi mata sannan tace.

“Amman dan Allah in babu damuwa ko zamu dinga zuwa gida kina mata allurar naga kina da kirki indai anan kusa kike”

Hassanar ta faɗa.

Dariya Nuriyyah tai wadda ta ƙawata fuskarta sannan tace.

“Lah ba’a nesa nake ba ina layin Abba kwastom kina cewa gidan Malam mai babban Allo za’a kawoki har gidanmu gida na biyu mai rumfar almajirai fa”

Zare idanu hassana tai sekuma tai dariya.

“Nasan gidan malam mana da muna kai surfen gero gidan”

Murmushi Nuriyyah tayi.

“I kam da innarmu tayi surfe kam”

Sannan tace.

“Sunana fatima Amman ana min laƙani da ( Nuriyyah ) kuma ni ƴar gidan ce kuma ƴar innah mai surfe da malam Ba aiki nake a wannan asibitin ba ni ɗalibace nazo practical na Lavel two daga makarantar School of health tecnology ina karantar _Community health estention workars_ (chew) sauran shekara guda na kammala insha Allahu tun wancan practical ɗin da muka fito na lavel one banyi wasa ba na tsaya na koyi abubuwa da dama a wajan na gaba dani wannan tasa a wannan karon ma ban sha wahala ba na sami gogewa sosai ina allura in sha Allah zanyi mata”

 

Kallon kallo hassana da hussaina sukai basu ce komai ba sedai mamakin ta sukai na yadda tace ƴar gidan malam ce amman suka ganta anan sanin a ƙa’idar ƴaƴan malam ko candy basayi ake masu aure da almajiran gidan malam ɗin.

“Kumin kwatancen gidan ku nazo nai mata har gida ba matsala”

Sukaji muryarta.

Murmushi sukai atare a wannan karon hussaina ce tai magana.

“Kina shiga layin gidan gobirawa ke koda ga layin ku ma ki ce kina son a nuna miki gidan su *ZAKI* ko yaro ƙarami kika sa ze kawo ki gidanmu zanma yi mamaki in baki san shiba”

Hussaina ta faɗa mata hakan.

Ɗage gira Nuriyyah tai.

“Ban san shiba nikam zanzo insha Allah,Layin ma naku yau zan fara shigarsa ƙarewa ma”

Dariya sukai atare.

Sannan sukai mata sallama suka wuce ummi nata shi mata albarka…………

 

*YA KUKA GA WASAN*?

AUTA.

08142105218

*FITAR RABO*

{ Love story }

 

NA

*AUTAR MANYA*

 

002

 

Cikin sanyin jiki Nuriyyah ta ƙarasa cikin office ɗinsu, Ta soma haɗa ƴan tarkacenta lokacin Ƙarfe sha biyun rana sabida haka sallama tayiwa zainab dake zaune tana shigar da aikinta acikin logbook da sauri zainab ta ɗago tana ce mata.

“Wai yau bazaki jirani ba tun wuri zaki tafi?”

Yatsina fuska nuriyya tayi tare da cewa.

“Zee yunwa nake ji wallahi ina gudun kar ulcerta ta tashi gwara naje gida naɗan ci wani abun, Idan su mudam sun shigo kyace musu na wuce”

Murmushi zainab tayi haɗi dayi ma Nuriyya fatan alkairi sannan ta cigaba da aikinta.

Nuriyyah fita tayi cikin wani irin ɗaurewar ciki take tafe kamar wadda ƙwai ya fashewa acikinta ga rana ta ƙwalle ga yunwa kafin taje gida idanunta yayi jajir Duk sun fito kanta har wani juyawa yake.

Layinsu ta ƙarasa sautin karatun alkur’ani yana tashi acikin rumfar Almajiran dake ƙofar gidansu Alamun yau basu tashi daga karatu da wuri ba.

Ƙofar gidan nasu cinkus yake babu masaka tsinke sabida tarin almajiran malam amman haka ta raɓe ta kutsa kai cikin soron gidansu.

Tana gab da shiga soro na biyu taga mutum a gabanta.

Sanƙamƙam ya tsaya ya wani tokare mata hanyarta.

Ko ba’a faɗi mata ba tasan ba kowa bane ba se Nazir ɗan maƙotansu.

Haɗe ranta tayi tamau tare da cewa.

“Malam gafara kona tureka in wuce”

Tafaɗa da ɗaurewar fuska.

Murmushi yayi mai sauti kafin yace.

“Ni dama zaki tureni ɗin ai dana ji daɗi, Dan Allah Nuriyyah ki dena min wulaƙanci Allah ya jarabce ni da sonki ke kuma kin kasa gane hakan”

Wani banzan kallo ta watsa mai kafin ta raɓe ta gefen shi ta wuce jita ke kamar ta shaƙe shi wani irin haushi yake bata sam Bata ƙaunar Nazir wani irin haushi yake bata.

 

Da sallama ta shiga ƙaton tsakar Gidan nasu wanda ɗakin innarta shine a farko se ɗakin baba sabuwa abokiyar zaman innah sekuma ɗakin malam nasu nacan gaba se wani kewaye wanda ɗakunan samarin gidan ke ciki.

Takalmanta ta tuɓe tare da yin sallama a bakin ƙofar ɗakin innah ta shiga cikin ɗakin ta aje jakarta tare da hayewa saman gadon ƙarfan innah tana mai lumshe idanunta hannayenta dafe da ruwan cikinta.

Ta ɗan jima a kwance kafin innah ta shigo ɗakinta.

Ɗan washe baki innah tayi ganin nuriyyah kwance a saman gado kafin tace.

“Dama nacewa sabuwa kamar ke nake ji a soro, har Maryam na cewa bara ta leƙa se sabuwa tace bake bace ba har kun tashi sannu da hanya bari na zubo miki ɗan wake yanzu maryam ta kwashe shi”

Wani yawu nuriyyah ta haɗiye muƙut! sabida tsabar yadda daman take a buƙace da abincin kafin ta ɗan juya tana lalubo mafici tana firfita jikinta wanda har lokacin zufar data ɗauko bata bar jikin nata ba.

 

Sallama innah ta ƙarayi a karo na biyu cikin ɗakin hannunta ɗauke da langar miya wadda ta cikota da ɗanwake ta shanano manja da yaji tare da ruwan randa mai sanyi a cikin kofi ta ajiye a saman ledar tsakar ɗakin sannan ta miƙe ta nufi gaban nuriyyah tace mata.

“Taso auta kici karya huce”

Tura baki nuriyyah tayi tare da ɗan lagwaɓewa kana ta furta.

“Innah ki hawo min dashi nan Allah ko tashin na kasayi”

Salati innah ta hau yi tana furta.

“Kefa daɗina dake ragwanta yanzu ƴar tafiyar da kikai ce ta sakaki wannan galabaitar Nuriyyah ina tausaya miki ranar da kikai aure fa wallahi ba namijin daze ɗauki wannan gandar”

Matso hawaye Nuriyyah ta soma tare da fara shure ƙafafu tana Ƙunƙuni.

Abin al’ajabi innah ce ta ɗagota kamar wata ƙaramar yarinya ta soma rage mata hijabin jikinta tana ce mata.

“Tashi auta maza sauko kici karya huce ga ruwan wanka can na ɗora miki in kinyi sallah kiyi wanka ku wuce makaranta Yau naji malam yace ku zakuyi zaman sauka”

Da sangarta da komai nuriyyah ta sakko daga saman gadon tana wani tura baki gaba ta soma cire farar rigar jikinta tana watsarwa a tsakar ɗakin innah na ɗebewa tana ninkewa.

Zani ta jawo daga saman ƙofa tai ɗaurin ƙirji tana ƙoƙarin zama Aka ɗaga labulan ƙofar Aka shigo, Ganin wanda ya shigo ɗakinne yasa nuriyyah ta kama kanta daga wannan shagwaɓar data kewa innah muzurai yake yana lalube a ɗakin yasha babbar riga da carbi a wuyan shi kana ganinshi kaga alarammah.

“Jidu kwa lafiya ka shigo kana ta min lalube acikin ɗakina ko ka bani ajiyar wani abunne?”

Se lokacin wanda ya Shigo ɗin ya ɗago kanshi kamarsu ɗaga da Nuriyyah komai nasu ɗaga dan hatta gashin kirar nasu sak sedai bam bancin shi namiji ne ita mace kuma a girme ze girmeta sedai ta fishi gaɓɓan girma domin shi bai da jiki kamar yadda itama innarsu bata da jikin, haka zalika kamannin innar su suka yo babu ko tamtama.

“Innah ina neman tawadar ɗazu ne malam ya sakani wani rubutu to kuma na laluba ban gani ba ha na fita na saka a siyo min”

Taya shi dubawa innah tayi bata gani ba Seta fara lalubar haɓar zaninta ta kunce ta ɗauko naira hamsin ta bashi.

“Seka bayar a siyo maka wannan kuma in angani daga baya sekai amfani da ita”

Girgiza kai yayi da sauri.

“A’a innah ina da kuɗi ki barshi”

Sannan ya juya ya dubi saitin nuriyyah datai tsuru-tsuru tana juya ɗanwaken data kasa ci sabida tsoron Ya jidu kartai wani abun ya bugeta.

“Ke Ban hanaki wannan zaman ba haka tarbiyar gidan nan take ki zauna da ɗaurin kirji?!”

Da sauri ta lalubo farin hijabinta ta sanya tana mai gyara nutsuwarta.

Ɓata rai innah tayi tare da hararen jidu sannan tace masa.

“Shige ka fita yarinya ta dawo daga wajan aiki bazaka ɗaga mata hankali ba uban baƙin Halin tsiya”

Innah ta faɗi masa haka ido rufe.

Wata harara Abdulmajid Ya makawa nuriyya kamar zeyi kuka ya dubi innah da tarin damuwa yace.

“Innah kina sangarta yarinyar nan da yawa wannan soyayyar da kike nunawa nuriyyah tayi yawa ina gudar Miki ɓacin ranta mudai semun faɗa muku gaskiya innah duk da bakya so, Amman fisabilillahi yarinya se abun da taga dama Duk Ƴaƴan  gidannan mata waya taɓa haye Secondry in ba ita ba? Shima malam ya biye miki tana yawo a unguwa da riga da wando ita bata yarda ba nursing ana zaginta wallahi ba da ban malam ba bazatai wannan makaranta  ba,aure zatai kamar ko wace ƴa ga Naziru nan yana ta naci amman tana wulaƙanta shi sabida Bakya son laifinta”

Ya faɗa a zuciye tare da take wa nuriyyah hannu ya wuce yabar ɗakin.

Kuka ta sanya tana yarfe hannun nata A kiɗime Innah ta matso tana duba mata hannunta ranta a matiƙar ɓace tabbas bada ban Jidu ɗanta bane ba dase ta ɗauki mataki akan taɓa mata auta dayayi.

“Ki haƙuri autata Duk duniya kece sanyin idaniyata naci burika akanki kala-kala sabida haka ki rufe idanu da kunne kiyi karatunki da kyau kuma ki taimakawa dukkan mabuƙaci nina tabbata Allah ze ɗaga darajarki amman ki dinga kula Naziru banda yi masa wulaƙanci”

Hawaye Nuriyyah ta share tare da cewa.

“Ni Allah nagaji zan gayawa malam kullum Se ya jidu ya duke ni, Kosu yaya Salisu basa yimin abin da yake mini suda ma muke baba ɗaya”

Tagumi innah ta rafka da tsananin raɗaɗin Abin da jidu kewa Autar tata.

08142105218

Leave a Comment

error: Content is protected !!