Hausa Novels

Ga irinta nan Hausa Novel

Ga irinta nan Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

GA IRINTA NAN

_(LOVE STORY

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE

*MANAZARTA WRITES ASSO

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Complt na littafin 07084653262

 

 

*DANDANO*

*1*

Cikin tsananin gajiya da ishirwa nake tafiya. burina kawai na isa gida na samu na watsa ruwa a jikina na kwanta na hutawa rayuwata. gabana ne ya fad’i! lokacin dana tuna d’an iskan yaron nan yana gari nasan da wuya ya bar ni na sha ruwa a gidan Khalid mugun fitinan nan yaro ne wallahi……..Daf da zan shiga layin namu motar Alhaji Nura take kokarin fitowa.

Ga irinta nan Hausa Novel

d’auke kaina nayi na bashi hanya domin ya wuce! girgiza kaina nayi ganin yayi parking din motar ya tsaya cikin raina nace”Ai dama na san sai ya tsaya, gilashi ya sauke muka had’a ido fuskata na saki na ce”Alhaji barka da rana.” Cikin kulawa yace.”Barka dai Sa’ida ya aiki.”? Nace” Aiki Alhamdullihi.” kokarin wuce wa nake ya dakatar dani da fad’in “Sa’ida ina al’kawarinmu.”? Gefan hijab d’ina nasa na goge gumin fuskata nace” Alhaji al’kawari yana nan ina so na ware ranakun da zan fara gudanar da aikin naka.”

 

Yace.”Me zai hana ki ware ranaku biyu a cikin sati wato alhamis da juma’a tunda a ranakun yaran basa zuwa isilamiyya in yaso idan sun dawo daga boko misalin biyu ko uku sai ki dinga shiga kina musu lesson d’in.”

 

Shuru nai ina nazarin maganarsa nace”Shikkenan Alhaji zan duba maganarka insha Allahu.” Yace.”To godiya nake gimbiya duk shawarar da kika yanke sai ki kira waya ta ki sanar dani.”

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Nace”To shikkenan babu damuwa.” Har nayi yunkurin barin gurin ya dakatar dani! cikin k’osawa na tsaya amma ban nuna masa ba, kudi ya miko min kusan dubu biyar…..murmushi nai nace”Kasan ba zan kar’ba ba Alhaji na gode.” da sauri na bar gurin ina mamakin yawan kyautar da yake min duk had’uwar da zamuyi sai ya dauki kudi ya bani bayan uwar hidimar da yake mana a gida……..Tun kafin na karasa na hango shi dogare a bakin kofar gidan namu yana sanye da k’ananun kaya 3qutar da singlet wacce ta matse shi gabad’aya suffarsa ta mazantaka ta bayyana Gabana ya yanke ya fad’i! duk sanda zan ganshi a haka hankalina yakan tashi ni kaina ina mamakin halin da nake shiga wannan dalilin yasa idan yana gida bana sakewa sosai mutukar zai dinga shige da fice a gidan babu sutturar arziki a jikinsa.

 

Fuska a murtuke na ‘karaso….”Malami Bani hanya na wuce.” babu wasa nayi maganar.

 

Hanyar ya sake tarewa yana kallona da ‘batacciyar fuska yace.”Aunty Sa’ida me ya tsayar dake a gurin wancan mutumin.”? wani irin kallo na watsa masa nace”Ina ruwanka da shiga sabgar da bata shafeka ba, dan Allah ni bani guri na wuce na gaji.”

 

Hanya ya matsa min naja tsaki had’e da kokarin ra’bashi na wuce kawai naji ya matseni a jikin kofar fuskokinmu suka hade numfashin mu na had’uwa.

 

 

Cikin fad’uwar gaba na tureshi! nayi saurin fad’awa soron ina addua akan Allah yasa wani bai ganmu ba! hannuna ya rike yana marairaice fuska yace.”Kina so zuciyata ta buga ko na hanaki kula wancan Alhaji kin raina magana ta ko.” Cikin takaici nake kallonsa a fusace! nace”Wallahi Khalid ranka zai ‘baci! mutukar baka fita harkata ba shin wai ni sa’arka ce da zaka dinga yi min iskanci.”

 

Zuba min idonsa yayi fuskarsa a had’e yace.”Ni ina sonki Aunty Sa’ida kuma kin san Allah baki da miji sai ni da kika raina zaki gane baki da wayo.”

Yana gama maganarsa ya fita, na dinga kallon bakin kofar ina mamakin maganarsa, bani da miji sai shi! Lallai Khalid baida hankali da tunani. tsaki naja na shiga gidan raina duk babu dadi.

 

“Ummatu sannu da aiki.” ciki-ciki ta amsa min ban damu da yanda ta amsa maganata ba kawai na shige ciki gidan, Gwaggo kakarmu na samu tana kad’in lagwani! hijab na cire na nemi guri na kwanta ina mayar da numfashi.

 

Kallona tayi tana cigaba da kad’in ta tace” Yau kin dad’e baki dawo ba Sa’ida anya baki fara yawace yawace ba ni wallahi wannan aikin naki ban yardar dashi ba.”

 

 

Cikin mamaki na kalleta, tace”Ai da gaskiyata wane irin aiki ne wannan da za’a fita tun karfe takwas ba za’a dawo ba sai karfe uku ko biyu haba jama’a.”

 

 

Murya na rawa Nace”Gwaggo mai kike nufi dani.”? ba tare da wata damuwa ba tace”Abinda nake nufi ai kin san shi.”

 

 

“Kina nufin ina yawon karuwanci kenan.”? da sauri tace.” Ooh! ni kada ki daura min jakar tsaba ba haka nake nufi ba.” hawaye na zuba nace”To meye na cewa baki yarda da aikina ba wato kema kin fara daukar magana aikaina ko.”

 

 

Shuru tayi tana cigaba da kad’in ta, komawa nayi na kwanta hawaye wani nabin wani! nace”Wato saboda ‘kasa ta rufe fuskar mahaifina shiyasa kike nema ki d’ora min kazafin na zina kamar bake kika haifi ubana ba.”

 

 

“Kinga Sa’ida kada kisa hawan jinina ya tashi da wannan magana taki ta isheni haka aiki kije kiyi tayi tunda ba zakiyi aure ba sharrin zina da bin maza dole jama’ar gari suyi miki.”

 

 

Da sauri na mike Nace”Gwaggo na gaji zan tattara kayana na koma gurin mahaifiyata tunda keda kika haifi ubana kin kasa yi min uziri a rayuwa ta ni ba ni zan dauki kaina nakai gidan aure ba sai ranar da Allah ya nufa to tunda kun kasa fahimta zan bar muku gidanku.” Saukowa nayi na fara hada kayana,

 

 

Kayan kad’in ta ajiye a gefe tace”Ke Sa’ida bana son shashanci da rashin tunani babu inda zakije kinji na fada miki maganar aure kuma ba zan fasa yi miki ba har sai kin tsayar da miji zanja bakina nai shuru to kaji.”

 

Jakar kayana na dauka na kama hanyar fita, sai ta fashe da kuka da fad’in” Au! takani zakiyi ki wuce to bari Babanku Iro ya shigo zan fada masa rashin mutuncin da kike min.” Saboda nasan banyi abinda take zargina dashi ba yasa ko sauraranta banyi ba na fita daga dakin da kayana a hannu, haba jamaa na gaji da masifar Gwaggo.

 

Turus! nayi ganin Baba Iro a tsaye suna magana da matarsa! ya kalleni yana kokarin yayi magana! Gwaggo ta fito daga daki tana kuka da fyatar majina da sauri ya karaso gurin yana fadin”Gwaggo lafiya kukan me kike.”? Ta ‘kara rurucewa da kuka da fadin”Gatanan saboda nai mata maganar aure shine ta hada kayanta wai gurin uwarta zata koma shine har tana sa kafarta tana taka ni ta wuce.”

Da sauri na kalleta ina mamakin sharrin ta gwaggo tsohuwa mai sharrin tsiya.

 

Baba Iro murmushi yayi inda sabo ya saba raba fad’a tsakanin mahaifiyar tasa da ‘Yar d’an uwansa Yace.”Haba Sa’ida in da sabo ai yaci ace kin saba da halin Gwaggo me yasa ba zakiyi hakuri ba yanzu da kika had’a kayanki ina kike nufin zuwa.” Gwaggo da sauri tace” Zataje can gurin Uwarta ne.” Cikin k’unci nace” Baba Iro wai kamar gwaggo itace take min k’azafi to meye amfanin zamana da ita.”

 

“Aa ni kada kiyi min sharri Sa’ida daka fada miki gaskiya sai kice nayi miki sharri.” Baba Iro yace.”Gwaggo maganar ta ‘kare haka.” Tace.”To kace mata kada ta tafi dan taurin kaine da ita.”

 

Baba Iro yasa hannu yana kokarin kar’bar jakar hannuna, nace”Baba dan Allah ka kyaleni na tafi wallahi na gaji da rashin hakurin gwaggo ka gafarce ni idan maganata ta ‘bata maka rai.”

 

Yana ‘kokarin magana ya shigo gidan hannunsa ri’ke da leda indomee yaje ya siyo, babu walwala a fuskarsa yace.”Me yake faruwa ne naga duk kunyi cirko-cirko a tsaye.”

 

Da sauri gwaggo tace”Yawwa d’a nagari ka ganta nan wai barin gida zatayi saboda nai mata maganar aure.” wani irin kallo yayi min kafin ya kalli jakar kayana dake hannun mahaifinsa, cikin yanayin takunsa ya karaso inda muke jakar kayan ya kar’ba hannun mahaifin nasa ba tare da yace wani abu ba ya shige dakin Gwaggo da jakar gwaggo bayansa tabi tana surutai!

 

Baba Iro ya kalleni a nutse yace.”Sa’ida kiyi hakuri kinji ko gwaggo tun kafin ta tsufa take da rikici ki fahimci halinta sai ki zauna lafiya kada wani sa’bani ya sake shiga tsakaninki da ita kice zaki bar gida nan shine tushenki, sannan kuma inaso ki bawa Alhaji Nura dama ya turo da maganar aure kamar yanda ya nuna alama.

 

Nace”Kawu babu wata maganar aure data ta’ba shiga tsakanina da Alhaji Nura kawai muna gaisawar mutunci dashi ne.” Cike da mamaki yace.”Sa’ida babu maganar aure data ta’ba shiga tsakanin ki da Alhaji Nura amma yake mana hidima a gida.” murmushin takaici nayi nace.”Wallahi Kawu babu maganar aure a tsakanina dashi.” girgiza kansa ya shigayi yana mamakin maganar, yace.”Shikkenan to tunda kince haka dukkaninmu zamu cigaba dayi miki addua akan Allah ya baki miji nagari.” a cikin zuciyata na amsa da ameen. gurin ya bari nima a sanyaye na d’aga labulan dakin Gwaggo na shiga, abinda naji suna tattaunawa yasa gabana fad’uwa….

[17/11, 7:13 pm] +234 708 465 3262: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*

_(LOVE STORY🌺)_

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

 

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Complt na Littafin. 07084653262

 

 

 

*2*

“Haba ‘Da nagari ai idan da gaske kake wallahi ni zan baka goyon baya kaga sai ayi towo na maina dama hausawa na cewa gida bai koshi ba ai ba za’a kai wa dawa ba insha Allahu Sa’ida matarka c…..Shigowa ta dakin ya hana ta k’arasa maganar. gabad’aya ita dashi suka bini da kallo, ni kam jiri ne naji yana nema ya zubar dani a gurin dan tsaf na fahimci akan abinda suke tattaunawa Khalid yayi masifar raina ni da har yake iya bud’ar baki ya furta min kalmar so ina a matsayin yayarsa wacce ta girme masa nesa ba kusa ba na rasa wane irin tsaurin ido ne da yaron a matsayina da tsayin shekaruna sai nake ganin bai cancanta ya iya kallon tsabar idona yazo min da wata banzar maganarsa ba, Khalid da wayo na da shekaruna yayi girman jikin da yake tunk’aho dashi kuruciyarsa kaf a gaban idona yayi ta amma yau wai an wayi gari ni yake tare wa hanya yana cewa yana so.

 

Kwanciya nayi ba tare dana cire hijabin jikina ba kawai na dinga bin su da kallo ina jin tsantsar takaici a cikin zuciyata ni kam ko zan rasa miji a gidan duniya ban ga abin aure a jikin wannan mara mutuncin yaron ba.

 

Tun sanda na kwanta a gadon yake min wani d’an iskan kallo irin na manufarci a hasale! nace”Wallahi idan baka daina yi min wannan d’an iskan kallon ba sai ranka ya ‘baci shashashan yaro mara kunyar banza da wofi.”

 

‘Bata fuskarsa yayi dan har sai da fatar saman goshinsa ta tattare haka yake tun yana yaro idan ransa ya ‘baci sai goshinsa ya tattare ya watsa min kallon banza had’e da girgiza kansa…….Yana kokarin yin magana ta riga shi da fadin” Ke Sa’ida meye kuma na kiransa shashasha ina laifin wanda zai tallafe ki ni wallahi naji dadin maganar da yazo min da ita duk girmanki da shekarunki ba zaki gagareshi ba dan mace komai girmanta bata fin karfin namiji.”

 

Tsaki! naja ba tare da nace komai ba na juya musu baya….’Kawataccen sajan fuskarsa ya shafa idonsa ‘kur! a mazaunanta da yake bala’in ‘kwa-‘kwa! duk da da hijabi a jikinta hakan bai hanashi ganin tudunsu ba, ya dinga jin wata lafiyayyar sha’awa na taso masa, a sanyaye ya kalli Kakar tasu yace.”Gwaggo ga indomee na nan ki dafa min zanje na dawo.” da sauri tace”To d’a nagari bari na kunna risho ai ina da kalanzir a ciki.” Fita yayi daga dakin yana shafa sumar kansa.

 

Sama-sama nake jin surutan ta kafin bacci mai nauyi yayi gaba dani……Can cikin baccin naji maganarsa sama-sama! “Haba gwaggo kefe ba’a abin arziki dake yanzu dan Allah haka ake dafa Indomee duba kin zabga mata ruwa sai iyo take a ciki kawai kinsa nai asarar kudina.” Zaune na mike nai saurin cire hijabin jikina jin yanda ya jike da gumi! ina kallonsa yasa hannu yana sosa kansa idonsa kur! a kirjina. girgiza kaina kawai nayi na fara yunk’urin mikewa……Tace.”Sa’ida duba dan Allah wai duk wannan gwanintar da nayi masa ban birgeshi ba cewa yake banyi daidai ba.”

 

Tukunyar indomee din na kalla da sauri na dauke kaina jin dariya na nema ta sub’ce min indomee guda uku amma ta cika tukunya da ruwa indomeen tayi tsululu duk ta narke a ciki………Yace.” gwaggo bafa zanyi asarar kudina ba ki cinye wannan indomee ki bani dari ukuna ba.” da sauri tace .” Wallahi baka isa ba ba zanci kayan atini ba hakan nan zaka daure kaci idan kuma ba hakaba Sa’ida ta baka wata indomee tunda tana da ita in yaso sai ka kaiwa babarka ta dafa maka tunda ni ban iya ba.”

 

Ta’be bakinsa yayi yace.”Sai dai na kwana da yunwa akan na kar’bi abunta ni ba shashashan namiji bane kamar yanda take kira na nafi karfin ta ciyar dani sai dai ni na ciyar da ita.”

 

Gwaggo sakin baki tai tana kallonsa sai kuma tayi dariya da Fadin”Khalid jarumi a gida da wajan ya’ki ka burgeni kwarai da gaske yanzu dai kayi hakuri akan ‘barnar da nayi maka.” Girgiza kansa yayi yace.”Bafa zan hakura ba bari ma ki gani.” da sauri ya fara lalaben inda take ajiye Pose d’inta….

Da sauri ta ri’ke gefan rigarsa “Aa Khalid kada ka daukar min kudi wallahi zanyi maka rashin mutunci idan ka daukar kwabo a cikin jakata…..Fita nai daga dakin na barsu suna bugawa dama inda sabo sun saba idan ‘yan abin arzikin na kusa suyi ta mutunci idan kuma ‘yan tsiyar na kusa suyi ta bugawa, Gwaggo san kudin tsiya ne da ita duk neman da take ba zata ci a cikinta ba sai tai ta tara kudin tana ‘boyewa a cewarta sai auran Sa’ida ya tashi sai tayi mata kayan daki da kudin……Pose din ya bude yaga kudi dan’kam ‘yan dubu dubu duk sunfi yawa, yace.” Lallai tsohuwar nan kudi ne dake duba dan Allah Jakarki kamar ta matar alhaji.”

 

Tana kokarin fizge jakar tace”Khalid wannan kudin da kagani ba nawa bane kada ka dauki ko kwabo a ciki.” Murmushi yayi yace.”Haba gwaggo ina ganin kudi ki hanani kin san Allah sai na dauka.” dubu daya ya zara yasa a aljihunsa ya mika mata jakarta, aikuwa ta dinga yi masa mita tana surutai dariya yayi ya kama hanyar fita daga dakin da fadin”Ki cinye indomee da kika dafa ni kuma anjima zanje tevur din mai shayi.” Tace.”Kaji dai dashi saboda kai zan sanjawa jakata guri haka kawai ba zaka zo kana daukar min kudi ba.”

 

Ni dai Ina alwala ina dariya a cikin raina gwaggo san kudi Khalid son kudi koda yake dole Khalid yaso kudi tunda dan makaranta ne yanzu haka yana daf da kammala karatunsa a jami’ar Bayero dake jahar kano yana zuwa gida duk bayan wata guda yayi hutu na kwana biyu ya koma makarana..

 

‘Dakin na shiga na sameta tana ta surutai uffan bance mata ba dan har yanxu haushinta nake ji akan irin abubuwan da take min, na gyara dadduma a nutse na fara kokarin tayar da sallah, tace”Sa’ida dan Allah ungo wannan jakar tawa ki ‘boye min Khalid ya gane inda nake ajiyeta nasan kuma shikkenan kafin ya tafi sai ya tatike ni.”

 

Ba tare dana kalleta ba nace”Ki ajiyeta nan na idar da sallah.” tace”To ‘yar albarka, tukunyar indomeen da sauke daga kan risho tana fad’in “Waye zai ci wannan ai ko almajiri ba zan bawa ba zubar dashi zanyi dan ni banga abinso a wannan abincin ba…..har na idar da sallah gwaggo bata fasa surutai ba nace” Yau me aka girka a gidan.”

 

Ta’be bakinta tayi ‘kasa-‘kasa tace”Kin san halin matar gidan da jarabar son d’anwake shi tayi masifaffiyar mata kawai na haifi d’ana amma tafi ni iko dashi dama nasan Rabi tana bin malamai akan Ibrahim.”

 

Cikin mamaki na kalleta halin gwaggo sai ita surukar ta ma bata kyale ba kullum cikin zaginta take amma ba tayi a gaban idonta sai a bayan idonta dan itama Ummatu bata daukar raini mara mutuncin kanta ce nace”Gwaggo dan Allah ki daina wannan halin ki zauna lafiya da kowa yanzu meye amfanin zagin Ummatu har kina cewa tana asiri.”

 

Baki ta rike tana kallon hanya tace.”Ke! Sa’ida maganar ta isa haka kada ki d’aga murya taji amma ni tuntuni Uwale ta tabbatar min da cewa Ummatu ba’a zaune take ba tana yawace-yawacan malamai wai shin bakya ganin ko kara ta ajiye babanku baya iya tsallakawa gashi muma ta daure mana baki dik abinda tayi a gidan shine daidai sannan kice nai mata sharri.”

 

Nace”Gwaggo ki rabu da Uwale munafuka ce wallahi tana so ta had’a ki rigima da surukar ki ita kuma ta zauna lafiya da tata idan ba hakaba meye na cewa Ummatu na bin malam……bakina ta rufe tana zazzare ido irin na rashin gaskiya tace.”Haba Sa’ida nace dake ki daina kiran sunanta kada taji haba jama’a yarinya ba’a sirri da ita mtssw maganar a barta haka.”

 

Murmushi kawai nayi na mike tsaye ina ninke dadduma, ta mika min pose din nata da fad’in “Kar’bi ki adana min kada ya shigo ya sake daukar min kudi.” karba nayi na bude gurin da nake ajiye tufafina nasa key na kulle……….Da yake idan mun dauki albashi duk abinda nake bukata naci da sha dana d’aurawa ina siyan abina na ajiye duk ranar da akayi abinda bana ra’ayi sai nayi girkina naci na koshi, fita nayi tsakar gida na dauko doya a kicin na zauna tsakar gidan ina feraye wa.

 

Fitowa tayi daga dakin da buta a hannunta Gwaggo duk rintsi bata bari yara suyi mata wasa da butar alwalarta kullum butar ta cike take da ruwa Macace mai tsafta da kula da ibadah dama dan adam tara yake bai cika goma ba, ganin ina feraye doya yasa ta washe baki da fad’in “A lallai kice yau dadi zamu ci a gidan.” Murmushi nai ina kallonta gwaggo akwai kwadayi amma bata yarda ta fitar da kudinta ta siyi abinda take so ba.

 

Nace”Eh lallai doya da kwai zan soya nayi miyar alayyahu saboda haka ke zaki bayar da kudin ‘kwai dan banda kudi.” shuru tayi tana kallona dariya ta kusa ta su’bce min.

 

Tace.” Inji dai guda biyu zai isa.” Nace”Haba gwaggo a wannan uwar doyar za’a sa ‘kwai biyu guda biyar zaki siya.” tace”Haba Sa’ida ‘kwai biyar nawa kenan.”? kai tsaye nace”Dari uku da hamsin.” shuru tayi tana nazari kafin ta girgiza kanta tace”Bari dai nai sallah muyi maganar haba Jama’a yanda rayuwa nan tayi wahala kice ‘kwai biyar ina laifi biyu ko uku.”

 

Bin ta nayi da kallo ina k’unshe dariya gwaggo kenan mai kwad’ayin tsiya…….Hayaniyarsu naji yo daga waje kafin nayi wani yun’kuri sun shigo gidan su uku, babu walwala na daga kaina ina kallonsu su biyu suna sanye da kayan ‘kwallo (ball) mayar da kaina kasa nayi na cigaba da abinda nake naji yace.”Salim ku jira ni nasa kayana na fito.” Suka ce okey kayi sauri dan Allah.” cikin zuciyata nace “Aikin kenan.” ” Aunty Sa’ida barka da Yamma.” a nutse nace” Barka Salim ya kuke.” ya d’an sosa kansa yana mirmushi yace “Lafiya aunty muna fatan kina lafiya.” ” Lafiya Kalau nake.” shuru gurin yay na minti biyu na dago kaina kawai sai naga sun zuba min ido! cikin ‘bacin rai nace”Salim kaima ka fara zama mara kunya ko.”? da sauri yace.”Aunty mai ya faru.”? girgiza kaina nayi nace”Kuje waje gashinan fitowa daga yau kada ku sake shigowa gidan nan tunda duk kun zama baligai.”

 

Wannan magana da tayi a kunnasa ya karaso gurin yana mata kallon daya saba “Akan me zaki hanasu shigowa gida abokaina ne na ‘kuruciya kin sansu kin san iyayensu kuma iyakacinsu nan bakin ‘kofa ko wani yayi miki abinda bai kamata ba.”

 

Nace”Khalid na hanasu shigowa gidan nan saboda bai kamata ba su tsaya a waje ka fito ka samesu.” Girgiza kansa yayi yace.” Keda Gwaggo babu nauyin auran kowa a kanku meye dan abokaina sun shigo kike fita kina yawo a titi gardawa na kallonki a ofis d’inku na malaman makaranta akwai baligan da suka ci uwar abokaina a kuyanci kike mu’amula dasu baki damu ba sai dan kawai abokaina sun shigo gida kice su daina shigowa ba zai yiwu ba.”

 

“Khalid ni kakewa rashin kunya.”? ba tare daya kulani ba yace.” Salim ku muje dan Allah.” gaba yayi suka rufa masa baya, girgiza kaina nayi aikuwa zan samu Baba Iro da maganar dole ya tsawatar musu akan su daina shigowa mutane gida kai tsaye………….

[17/11, 7:13 pm] +234 708 465 3262: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*

_(LOVE STORY🌺)_

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

 

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Complt na littafin. 07084653262

 

 

 

*3*

Motsin fitowarta daga band’aki yasa nai saurin kallon gurin, asuwakin ta dake kan taga (window) ta dauka tana gyarawa tace”Surutun me nake ji ne ina bandaki naji kamar muryar Khalid kuna sa’insa.” shuru nayi mata saboda nasan ko na fada mata dalili bai zama lallai ta bani gaskiya ba, zama tayi kan kujera ‘yar tsuguno tana kokarin sanya asuwakin a bakinta tace.”Sa’ida in dai akace wannan namiji ne to komai ‘kan’kantarsa jagora ne, idan kina hantarar Khalid wani sa’in haushi kike bani dan duk ‘kan’kantarsa da kika raina watarana shine zai jagorance ki.” Kallonta nayi ina mamakin maganarta “A’ina Khalid din zai jagorance ni gwaggo dan Allah idan zaki fad’i magana ki dinga tsayawa kina tunani kafin ki fad’a yaro ‘kan’kani kina maganar zai jagorance ni Khalid mai ya sani a rayuwa.”?

 

Tana goge bakinta da asuwakin tace”Oho! ni dai na fad’a miki gaskiya ki daina raina Khalid da ‘kan’kantar shekarunsa komai girmanki ba gagararsa zakiyi ba.” Cike da bacin rai nake kallonta, ta d’auraye asuwakin ta ajiye shi a gefe cikin nutsuwa ta fara d’aura alwala.

 

Kaina na girgiza ina jin tamkar zuciyata ta tsage saboda ‘bacin rai gwaggo ta iya kuntukawa mutum abin haushi tayi kamar ba tayi ba, tabbas da wata ko wani ne yayi min wannan banzar magana wallahi sai nayi masa rashin mutumci amma da yake itace babu yanda na iya da ita dole nayi hakuri dan idan nace zanyi magana zata iya yanko wata maganar da zata tarwatsa min zuciya amma idan ba haka ba me zanyi da Khalid bayan manyan mazan dake sona a waje.

 

Sai da na daidaici cewa ta idar da sallahr na shiga dakin, tana zaune kan dadduma cikin hijabi da carbi a hannunta tana ja, ka’ida ne dama idan ta idar da sallar la’asar sai tayi zaman lazimi nace” Zan dauki kudin ‘kwan a Pose d’inki.”

 

Kanta kawai ta d’aga min na bude sif din na dauko pose din nata na zuge! gudar dari biyar na dauka na mayar da sif din na rufe…… fita nayi domin na samu yaron aike cikin ikon Allah na hango almajirin gidan Alhaji Nura ni’ki-ni’ki da kayan miya a hannunsa, da sauri nace”Sule dan Allah siyo min ‘kwai kantin Dauda.” da sauri yace.”To aunty Sa’ida.” kudin ya kar’ba ya tafi na juya da sauri na koma cikin gidan, Ummatu na samu ta fito daga gurinta tana d’auraye kwanuka. sannu nayi mata ta amsa ciki-ciki. wucewa nayi ciki ina girgiza kaina na rasa abinda na tsarewa Matar kwata-kwata bata kaunata duk abinda takeyi min a gidan na ganin ido ne.

 

Har yanzu Lazimin take sai kawai na shiga kwashe kayan wanke-wanken dake dakin na kaisu bakin rijiya na ajiye,

 

Wani irin kallo naga tana bina dashi kafin ta shiga bin kayan wanke-wanken da kallo tace”Sa’ida dan wulakanta abinci shine kika fito da abinci kika zuba masa ruwa idan bakwaci ai sai ku bawa almajirai shima wanda yake kawowa yana shan wahala kafin ya samo ya kawo amma na lura daka ke har Gwaggon bakwa tausaya masa.”

 

Jikina a sanyaye nace”Wallahi na manta ban duba ba na zuba ruwa akai kin san ni bana cin d’anwake shiyasa to ban san abinda ya hana Gwaggo cin nata ba.”

 

 

Da sauri tace”To yaya kuwa za’ayi taci bayan taga kina feraye doya ai ba zataci ba ni banta’ba ganin kwad’ayayyiyar tsohuwa irin wannan ba.”

 

Kallonta nayi ina mamakin maganarta tsaki taja ta cigaba da aikinta, Gwaggo ta bankad’a labulen d’akinta ta fito tana fad’in” Surutan me nakeji ne nifa bana san husuma a gida.” Ummatu aikinta ta cigaba dayi bata tanka mata ba nace.”Gwaggo babu wata husuma da zata faru ki koma d’aki.

 

Tace.”Ummatu naji kamar kina maganar d’anwake ko.”? Tace.”Eh hakane Gwaggo Sa’ida ta fito dashi naga ko d’aya baku ci ba shine nake mamakin hakan ai da kun san ba zakuci ba sai kuyi min magana na rage garin.”

 

 

Tace.”Au!! Sai na fada miki ? Rabi tuntuni fa kin san ni D’anwake bai dame ni ba me zai sanya ki dimanci yi mana shi a gida.” Da sauri tace.”To gwaggo shi aka bani akace na sarrafa shi Maigidan daya kawo shi zakiyi wa wannan maganar.” Gwaggo bakinta ta ri’ke tana jijjiga kanta

 

Ganin al’amarin na nema ya girmama yasa na shiga basu hakuri….Ummatu kwanukan ta ta dauka ta shige gurinta, Gwaggo ta zungura mata bakinta tanai mata yen-yen! da hannu. Dariya ce ta kusa ta su’bce min, ta ri’ke hannuna ‘kasa-‘kasa tace”Rabu da ita Sa’ida ‘bakin ciki takeyi ganin kin yanka doya zaki soya tunda ta fito da hassadarta a fili ko d’and’ane kada ki bata mu cinye kayanmu.” Tsabar dariyar dake cina ta hanani bude baki nai mata magana da sauri na tsuguna domin wanke kwanukan. ta cigaba da magana ‘kasa-‘kasa! nace “Dan girman Allah gwaggo ki tafi ki zauna a daki kada taji wata magana ranta ya ‘baci matar nan iya ‘kokari tanayi dake duk wata rashin kunya da takeyi miki kece kike janyowa kanki.”

 

Tsaki! taja tace”Kinga na bar maganar yanzu ina canji na na ‘kwai ina lazimi naga kin dauki dari biyar.”

 

Ina kokarin bata amsa Sule ya shigo! sai ta hau washe bakinta tana kallon ledojin hannunsa dan ta dauka Alhaji Nura ne yayo aiken daya saba…….Yace.”Aunty Sa’ida gashi.” Kar’ba nayi nace.”Nagode Sule.” ya juya ya fita daga gidan bayan ya gaisheta…ta kalleni da fadin” Ganin ledoji a hannunsa Wallahi na dauka aike ne Alhaji yayo mana.” shuru nai mata na cigaba da wanke-wanke na sai ta bar gurin tana surutai irin wanda ta saba.

 

 

Ina daf da kammala soya doyar ya shigo gidan jikinsa bud’u-bud’u! d’auke kaina nayi ciki-ciki na amsa sallamarsa, bece min komai ba ya nufi bakin rijiya ya cika bokiti da ruwa yana wanke jikinsa, kamar wacce akace d’ago kanki ki kalleshi naga jikinsa jagab! yana kokarin cire rigar jessi d’in jikinsa cikin gaggawa na kauda kaina daga kansa gabana ya dinga faduwa ganin yanda gajeran wandon jikinsa ya ji’ke jagab dik ya manne masa a jiki girmansa ya fito sosai…… zama yayi bakin rijiyar ya cigaba da wanke jikinsa sam babu wata damuwa a tare dashi.

 

Har ya gama abinda yake a gurin ban sake kallonsa ba ta gefan idona naga tashinsa daga gurin, ajiyar zuciya na sauke cikin zuciyata nace”Khalid Allah ya shiryar da kai hanya mai kyau.

 

Bayan na gama sai na d’ora ruwan wanka na d’auki fulas din doyar na nufi daki dashi ,karo muka buga da ita tace.”Yawwa gwanda da da kikayi kika gama magariba tayi nima yanzu alwala zan d’aura.”

Ajiyar zuciya kawai na sauke na bata hanya ta wuce na shiga dakin fulas din hannuna na ajiye na fito domin nima na daura alwalar.

 

Sai da nayi wanka tukkuna na samu sukunin zama naci soyayyar doyar. lokacin ita Gwaggo har taci ta koshi ta kishingida tana saurarar redio, zaune ta mike tana gyara daurin dankwalinta tace”Sa’ida badan hali Rabi ba kisa mata biyu a plate a miqa mata ta mayar da yawu.”

 

Nace.”Aiko baki fad’a ba dama sai an bata hakkinta.” komawa tayi ta kwanta tana sake gyara ma daidaicin fulas din dake gabanta.

 

Nace”Wannan fulas din na gabanki meye a ciki.”? Tace.”Doya ce na ajiyewa Khalid saboda nasan yana san doya da kwai shima.”

 

Karamin tsaki naja nace”A maimakon ki ajiyewa Kawu sai ki ajiyewa wani Khalid Baba Iro shi yafi cancanta ki ajiyewa doya ba wannan yaron ba.”

 

Tana gyara redion ta tace.”Khalid nayi niyyar ajiyewa doya saboda haka sai ki shafa min lafiya.” Ta’be bakina nayi a nutse na fara cin doyar dake gabana ina had’awa da lemo.

 

Labulan d’akin ya d’aga yana magana, tayi saurin mi’kewa zaune da fad’in “Yawwa yaro nagari shigo kaci doya da kwai da zafin ta.”

 

Baiyi niyyar shiga dakin ba amma ganin mutuniyarsa cikin ‘karamar shart irin ta shan iska yasa ya shiga dakin ya zauna suna fuskantar juna….fulas din ta tura gabanshi da fadin” Gashinan da zafin ta dan bata jima da gama soyawa ba.”

 

Girgiza kansa yayi yace.”Bana bukata.” da sauri na kalleshi ina mamaki! nasan halinsa da kwadayi dole shima zaiyi sha’awar doyar amma kai tsaye yace baya so.”

 

 

Gwaggo jikinta ne yayi sanyi tace”Saboda me ba zaka ci ba.” Babu walwala a tare dashi yace.”Gwaggo daga ranar dana cigaba da cin abincin Aunty Sa’ida zata cigaba da raina ni daga yanzu mutukar abu nata ne a gidan nan to kada ki ajiye min idan ina bukata zan siyo da kudina.”

 

 

Tace.”Aa wannan ai doyar ce kawai tata amma ‘kwai ni na siya da kudina dan Allah ka daure kaci.” Girgixa kansa yayi yana duba wayarsa. Yace.”Gwaggo bafa zanci ba wallahi koda zan kwana da yunwa kuwa.”

 

Ba tare dana kalleshi ba nace”Kanka ka cuta yaro.” Uffan bece min ba ya cigaba da dube-dube a wayarsa.

 

Nace”Gwaggo ai sai ki ajiyewa Kawu dama shi yafi cancanta da ki kyautatawa ganin irin dawainiyar da yake.” cikin jin haushi tace.”Ke! banyi niyyar bashi ba haba jama’a kin dameni da wani Kawu to bazan bashi ba ga wanda nayi niyyar bawa tunda yace baya bukata gobe da safe naci kayata.”

 

Shuru nai mata na cigaba da abinda nake, dakin yayi shuru na tsayin minti uku, kaina na d’ago kawai muka had’a ido dashi gabad’aya hankalinsa na kaina ya zuba min shegun idanunsa na fitina.

 

Nace.”Naci maka bashi ne da zaka sani a gaba kana kallona.” shuru yayi bai ce komai ba kuma bai daina kallona ba. Girgiza kaina nayi na mi’ke na fita daga dakin na barsu.

 

Kan tabarma na zauna ina duba waya ta ya fito daga dakin yana sanya takalmansa na kauda kaina…..”Aunty Sa’ida.” naji ya kira sunana cikin sanyi murya. a nutse na kalleshi, ya lumshe idonsa tare da shafa sumarsa yace.”Wallahi kin had’u auntyna duk inda ake neman cikakkiyar mace kin kai duk sanda nazo gida hutu da tsananin sha’awarki nake komawa skull.”

 

Gabad’aya ji nayi yawun bakina ya bushe! na dinga kallonsa ina mamakin tsagerancin sa Murmushi yayi ya had’e yatsun hannunsa yayi heart 💘 Ilov u auntyna muuuuhhhh!.” ya hura min iskar bakinsa. kafin nayi aune har ya fice daga gidan, kaina na sunkuyar ‘kasa gabana ya dinga bugawa sosai al’amarin ya firgitani anya kuwa yaron nan bai fara shaye-shaye ba! ? ni kam ina zan kai kaina da wannan abin kunyar dole sai na tasar masa a tsaye zai daina yi min wannan iskancin, jikina a mutukar mace na mike na shiga dakin na kwanta ina tunanin matakin da zan dauka a kansa..

[17/11, 7:13 pm] +234 708 465 3262: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*

_(LOVE STORY🌺)_

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Completed na littafin..07084653262

 

 

*5*

“Sa’ida tun kafin mu fito daga ofis nake miki wani irin kallo. sai nake ganin kamar kina da damuwa a ganina ban cancanci ki ‘boye min abinda ke damunki ba tunda nima duk wani abu da yake damuna bana ‘boye miki.”

Hauwwa ce kenan wannan maganar a lokacin da suke cikin motar ta domin komawa gida.

 

Ajiyar zuciya na sauke nace.”Wallahi Hauwwa ba ‘karya ki kayi ba ina cikin damuwa na kuma rasa yanda zanyi na warware ta al’amarin dai sai godiyar Allah.

 

Murmushi tayi tace.”Haba ‘kawata abokin kuka shi ake fad’awa mutuwa ki fad’a min damuwarki ko akwai shawarar da zan iya baki.”

 

 

Murmushi nayi nace”Dama ina tunanin fad’a miki ki kayi magana Hauwwa kin san wannan yaron na gidanmu ko.”?

 

Tace.”Khalid ko bashi kike nufi ba.”? Nace.”Shi nake nufi Hauwwa Khalid ya takura min a gida wallahi wai saboda tsabar rashin mutunci da raini kamar ni zai duba yace yana so.”

 

 

Hauwwa dariya tasa tana kallona da mamaki a tare da ita, tace.”So.”? Ta’be bakina nayi nace.”Kwarai kuwa Hauwwa Khalid sona yake dan duk wasu alamu ya nuna har da fad’awa Gwaggo wai zai aure ni yaron da a gabana ya girma meye nasa ban sani ba amma da yake yanzu yaga ya fini tsayi da girman jiki shine yake furta min wannan kalma.”

 

 

Hauwwa draving take tana girgiza kanta tace.”Sa’ida Khalid yayi tsaurin ido amma kuma idan an duba tarihi za’a ga bai yi laifi ba tunda hakan kamar sunnah ce mai zai hana ki aure shi tunda hakan (BA HARAM BANE) Littafin Binta Umar Abbale.

 

 

Wani irin kallo na watsa mata “Hauwwa wannan wace irin magana kikeyi me zan aura a tare da Khalid bana tsammanin zan iya auran ‘karamin yaro a yanda nake a haka nafi bukatar cikakken namijin mai kima wanda yasan rayuwa amma auran yaro mai ‘karanci shekeru akwai kalubale a ciki.”

 

Murmushi tayi tace.”Sa’ida wane ‘kalubale kike hangowa a tattare da auran Khalid? Yaro kyakykyawa da siffar mazantaka Khalid bai da makusa matsalar kawai kice bashi da kudi sannan kuma bashi da aikin yi in banda haka menene abin ‘ki a tare dashi.”?

 

 

Girgiza kaina nayi nace.”Hauwwa Ra’ayi na ne kawai haka bana sha’awar auran k’ananun yara dan sai nake ganin kamar basu san meye aure ba wannan dalilin yasa gabadaya bana kulasu nafi tsayawa na saurari magidanta masu iyali da suka dad’e a cikin harkar.”

 

 

Hauwwa ta’be bakinta tayi tace”Sa’ida mazan fa suna suka tara kamar yanda matan ma suka tara duk kallon kitse kike musu ni zan fad’a miki wannan kinga dai ni bazawara ce ko to wallahi ba zan auri namiji ba sai na tsaya na duba tukkuna saboda ni kad’ai nasan bala’in dana shiga a gidan aurena kafin na fito.”

 

 

“Hauwwa kenan kin san kowa da tunaninsa amma gaskiya bana yi miki sha’awar auran ‘karamin yaro domin kinfi ‘karfinsu ki auri namiji daidai dake dan Allah kada kibi son zuciyarki daga baya kizo kina nadama.”

 

 

“Sa’ida kin san Allah ko d’an 20years ne yazo da niyyar aurena na gamsu da shi sai na aureshi domin hakan ai ba haramun bane akan naje na auri babba nazo na sake shiga wata matsalar gwara na auri yaron na cigaba da rainonsa har yayi ‘kwari.”

 

 

Cikin wani irin yanayi na mamaki nake kallonta…..tasa dariya da fadin”Kina mamaki ne.”? Girgiza kaina nayi nace.”Sosai kuwa idan kin auri dan 20years kin auri d’an cikin ki ko ba haka bane.”

 

Still tana dai dariyar tace.”Aa Sa’ida bana san sharri a ina na haifi dan shekara ashirin Walid yarona na farko duka shekaransa tara Safna kuma shekararta bakwai.”

 

Nace”Kin gani ai tunda kika haifi dan shekara tara kin zama uwa me zai baki sha’awa a gurin auran karamin yaro dan shekara ashirin.

 

 

Hauwwa baki ta ta’be tace.”Ke Sa’ida bari dai na fito miki a mutum! ni Hauwwa ina da tsananin bukata wannan dalilin ne ya janyo mutuwar aurena domin babansu Walid bashi da maida hankali a wannan gurin yafi mayar da hankalinsa gurin neman kudinsa nasha wahala a hannunsa Sa’ida ina fada miki Walid da Safna tsanani rabo ne yasa aka haife su saboda babansu sai ya shafe wata biyu ko uku bai had’a shimfida dani ba, kullum yana yawo a jirgi sai kace tsunsu shi dai ya samu kud’i ni kuma ya barni cikin wahala da bukata wannan dalilin yasa na yankewa kaina shawarar yanke zama dashi dan ba zan iya da halinsa ba.”

 

Na jima ina mamakin maganarta kafin nace.”To Hauwwa shi ‘karamin yaron da kike ‘kulafuci a kansa kina da tabbacin zaki samu abinda kike bukata mazan fa duk kusan haka suke tunda dai ba ‘kwan’kwasawa zakiyi ki gane daidai dake ba .”

 

 

Murmushi tayi tace.”Sa’ida ana ganewa wallahi shiyasa ai nace miki kafin nayi auran sai na tantance tukkuna kuma ina rokon Allah ya bani daidai dani.”

 

 

Nace.”Ta ina zaki gane jarumin namiji Hauwwa.” murmushi tayi tace.”Sa’ida kenan.” draving d’inta ta cigaba dayi ta barni cikin tunani nima irinta ce mai yawan sha’awa da son soyayya shiyasa gabad’aya na shiga tunanin ta inda zan gane jarumin namijin da zai iya daukar lalurata……Alhaji Nura ne ya fad’o min a rai na dinga tunanin siffofinsa dogo ne mai ma daidaicin jiki kwayoyin idanunsa jajaye ba irin na Khalid ba da kullum suke da haske, nace”Hauwwa tunda kin’ki fad’a min ai na gane.”

 

Tace.”Yawwa ai dama so nake ki gane sai kiyi min bayani.” Dariya nayi nace.”Kamar dai Alhajina ina nufin Alhaji Nura ya cancanta da wannan sunan.

 

Shuru tayi tana nazari tace.”Eh gaskiya kam kwayoyin idanunsa ma sheda ne ina miki sha’awar auransa gashi yana bala’in sonki to amma ai matarsa ce matsala Sa’ida a rayuwata bana san kishiya wallahi.”

 

 

Ajiyar zuciya na sauke nace.”Hauwwa ni wallahi kishiya bata firgita ni za’bin Allah kawai nake nema idan Allah ya kaddara Alhaji Nura ne mijina babu ruwana da matarsa tunda ba itake aurena.”

 

“Hakane Sa’ida to ina rokon Ubangiji Allah ya za’ba mana abinda yafi alkairi.” na amsa da ameeeen ya rabbi……Da wannan hirar ta sauke ni a bakin layin mu ta juya kan motar hannu na daga mata da fadin”Nagode ‘Kawata sai gobe idan Allah ya kaimu.” ta amsa da “Ameen Allah ya kaimu lafiya.” sai da ta bar gurin sannan na nima na bar gurin……..

 

 

Tunda na hangoshi a zaune a kofar gidan naji gabana ya fadi! hakika Khalid ya zame min ‘karfen ‘kafa, kici-kici nayi da fuskata, kafin na karasa naga ya mi’ke ya shiga gidan, ajiyar zuciya na sauke naji dad’in hakan saboda na tsani kallon da yake min……Ina shiga soran naji an fizgo hannuna kafin nayi aune naji ya ru’kun’kume ni ta baya! numfashinsa naji yana fita da sauri da sauri ya d’ora kansa a kafad’ata sosai ya ri’ke ‘kuguna! gabana ya dinga fad’uwa! murya na rawa nace.”Khalid wane irin iskanci ne wannan? zaka sake ni ko sai nai maka rashin mutumci d’an iskan yaro kaw……Kafin na ‘karasa naji yayi cikin bayan k’yaure (‘kofa) dani, a zabure! na juyo fuskokinmu suka had’u guri guda!

 

Hawaye ne naji suna kokarin kufce min wane irin fitinan nan yaro ne wannan? matseni yayi a kirjinsa yana kiran sunana cikin wani irin sauti “Aunty Sa’ida kina so na mutu ko? ki taimakawa rayuwata kada ta salwance.” hawayen takaicin da nake kokarin dannewa sune suka kufce cikin rawar murya nace.”Khalid sake ni.”

 

“Um!um! Aunty naji dadin rungumeki ki bari na samu nutsuwa ina cikin tsananin damuwa.”

Yafad’a yana goga gefan fuskarsa a tawa.

 

Shuru nai jikina gabad’aya ya mutu ko yaya nayi motsi da niyyar kwace jikina zai sake matseni sai wani irin nishi yake!

 

 

“Khalid ni kake wa wannan iskancin ko? ni kake matsewa a soro saboda baka da mutunci Khalid.”! murya a sha’ke nake magana.

 

 

” Aunty Sa’ida har abada babu tozarci a tsakani na dake abinda kikayi min d’azu ya ‘bata min rai ko abinci na kasa ci Aunty me yasa zaki za’bi wancan Alhajin ki barni me nai miki ko ni ba namiji bane.”

Cikin sanyin murya yake maganar yana yawo da hannunsa a jikina.

 

 

“Khalid ka daina mafarkin abinda ba zai faru ba kasan Allah duk maitarka akaina sai ka hakura dan ni nafi karfin’ka kaje ka nemi daidai da kai.”

 

 

Fuskata ya d’ago yana kallona, naga idonsa yayi jajawur a take tsigar jikina ta tashi! fuskata na fizge! da sauri na daga hannu da niyyar kwad’a masa mari! yayi saurin ri’kewa.

 

Girgixa kansa yake Cikin ‘kunar zuciya yace.”Ni nafi karfin ki mare ni auntyna! na amince ni maye! ne amma akanki aunty Sa’ida ba zan fita a rayuwarki ba sai na tabbatar da cewa kin zama mallakata mu zuba ni dake.”!

 

Tsaki naja na tureshi da fadin”Shashasha mara hankali kawai.” gabana ya tare cikin ‘bacin ran da banta’ba ganinsa dashi ba yace.”Kada ki ‘kara kirana da shashasha zan baki mamaki.”

 

“Me zakayi min.”? nafada ina watsa masa harara……Murza yatsun hannunsa yayi yace.” Sai ranar da kika ‘kara kirana da kalmar sannan ne zakiga abinda zanyi.”

 

“Mtwwws! tsaki naja na ra’ba ta gefansa na shiga gidan…..Ajiyar zuciya ya sauke bayan shigewarta gidan ya shiga shafa kirjinsa yana lumshe ido har yanzu yana jin tudun nonowanta a kirjinsa, cikin mutuwar jiki ya fita daga gidan.

 

 

” To shikkenan Uwale zan duba maganarki wallahi dama nima sai da nayi wannan tunanin ace yarinya kwata-kwata bata so ayi mata maganar aure bayan tana da mane ma dole ne a nemi taimako.” Uwale na kokarin magana na shiga dakin, sai ta washe baki da fadin”Babban mace hakima kin dawo kenan sannu lallai kin dauko rana.”

 

Sama-sama na gaisheta na cire hijab din jikina na fita daga dakin na tsani alaqar Gwaggo da Uwale ko kad’an……Bayan fitarta Uwale tace.”To shikkenan Gwaggo sai kinzo ina sauraranki.” Gwaggo mi’kewa tayi domin yi mata rakiya tana fad’in “Insha Allahu gobe zanzo sai muje Allah dai ya rufa asiri.” kallo na bisu dashi ina tunanin inda zasuje….Gwaggo ta dawo gidan tana kallona a fakaice kafin ta shiga dakin, mikewa nai na bi bayanta domin na kafa mata hujjata akan irin iskancin da Khalid yake min.

[17/11, 7:13 pm] +234 708 465 3262: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*

_(LOVE STORY🌺)_

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

 

 

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar Complt na Littafin. 07084653262

 

 

 

 

*4*

Sa’ida cewa nayi fa ki sawa Rabi doyar nan kada mu wayi gari ta dinga yar mana da habaici kin san dai halinta bata da hakuri.” Gwaggo ce ke wannan maganar a lokacin da take kokarin shigowa dakin da buta a hannunta da alama bandaki taje.

 

Zaune na mi’ke ba tare da nace mata komai ba na fara kokarin bud’e fulas din dake kan tabarmar ta. ido ta tsira min a lokacin da nake zuba doyar tace.” Bafa cewa nayi ki kwashe mata ba guda biyu kika sa mata ta isa tunda itama idan tayi soye-soyen ta ba bamu take ba.”

 

Nace.”Gwaggo dan Allah abin duniya ya daina rufe miki ido mecece doya da ‘kwai tun d’azu duk kin damu kanki.”

 

“Sa’ida kada ki fad’a min magana akan Rabi na lura kema asirin nata ya fara tasiri a kanki ai sai kije ki ‘karata ke da ita.” shuru kawai nayi mata na fita daga dakin.

 

Ummatu na zaune a gurinta tana saurarar redio na shiga da sallama a bakina, kallon mamaki ta shiga bina dashi, nace.”Ummatu doya ce na kawo miki.” Babu yabo babu fallasa tace”To nagode.” Kar’ba tayi ta ajiye kusa da ita nace”To sai da safe.” kamar bata so tace.”Allah ya tashe mu lafiya.”

 

Koda na koma dakin gwaggo samunta nayi har ta kwanta bacci kan gadonta redion ta a kusa da kanta tana saurara Gwaggo bata kashe redio kullum a kunne take kwana shiyasa kullum cikin siyan batir take da daddare idan ta isheni da shuuuuu! zan tashi na kashe amma idan ta farka sai ta kunna alhalin ko wace tasha sun rufe, al’amarin Gwaggo nada wuyar sha’ani.

 

 

Da wuri na tashi nayi duk abinda na saba karfe bakwai da rabi na shirya tsaf a gurguje na karya kummalo nayi mata sallama domin tafiya gurin aiki…..Shuru tayi min ba tace komai ba nace.”Gwaggo kina ji ina magana ko.”? kallona tayi da fadin.”Me kika ce.”? cike da mamaki nake kallonta nasan sarai taji abinda na fada amma wai tambayata take, ajiyar zuciya na sauke nace.”Na tafi sai na dawo.” a maimakon tayi min irin adduar data saba sai kawai naji tace.”Umm!! juyowa nai ina kallonta nace”Gwaggo ba zakiyi min addua ba.”‘

 

“Sa’ida kyaleni dan Allah kije kawai ni da wannan aikin naki gwara babu kullum kina yawo a kan titi zagade-zagade babu mijin aure duk wannan kyawun naki da kyawun surar zai tashi a banza a wofi wannan al’amari yana damuna.”

 

Jim! nayi ina kallonta kafin nace.”Gwaggo Al’amarina ya daina damunki komai da kika gani yana da lokaci ki cigaba dayi min addua.”

“Umm.”! ta sake fada tana ta’be bakinta, kaina na girgiza kawai na kama hanyar fita daga dakin, karo mukaci dashi a lokacin da yake ‘kokarin shiga, yana sanye da singlet fara kal da 3qutar fuskarsa ta nuna alamun bai jima da tashi a bacci ba.

 

Cikin kulawa yace.” Aunty Sa’ida ki bari yanzu zamu fita cikin a daidaita sahun Salim sai mu kai ki makarantar taku.”

 

Ba tare dana kalleshi ba nace.”Bana bukata.” da sauri na ratse shi na wuce! Ina jin sautin muryar Gwaggo tana surutai wanda suke nuni da jin haushin abinda nai masa.

 

 

Sai da nayi dana sani akan k’in kar’bar tayin da Khalid yayi min domin nafi karfin minti goma sha biyar a tsaye a bakin titi wani abun hawa na haya bai gilma ta gabana ba motocin gida ne kawai suke wuce wa, dama wani sa’in ina fama da irin wannan matsalar ta rashin abin hawa, wani lokacin kuma ina fitowa titi nake samu yau dai al’amarin sai addua dan tamkar anyi musu gori ko kuma wa’inda suka tafi yajin aiki, agogon dake daure a hannuna na duba takwas saura minti biyar gashi karfe takwas da minti goma nake da Period ajiyar zuciya na sauke ganin adaidaita sahun nasu na kokarin fitowa daga layin duk abuna dole nayi hakuri na shiga mutukar baso nake na makara ba, Motar Alhaji Nura na sake hangowa tana bin bayan babur d’in nasu, saurin dauke kaina nayi ina kallon hanya tabbas nasan sai ya tsaya yayi min magana gashi gabad’aya ban yanke hukunci akan maganarsa ba gabad’aya ma na manta munyi magana dashi jiya.

 

Aikuwa gabana yayi parking ya sauke gilashin motar fuskarsa dauke da k’ayataccen murmushi yace.”Ranki ya dad’i an fito kenan.”? sakin fuskata nayi nace”Eh wallahi Alhaji barka da asuba ya kwanan iyali.” ? cikin kulawa yace.”Lafiya kalau sun tafi skull yanzu me zai hana ki shigo na rage miki hanya.” Yafada yana kallon kwayar idona, ina kokarin magana adaidaita sahun nasu ta tsaya kusa dani. da sauri nayi ‘yar dariya da fad’in”To nagode Alhaji dama na jima a tsaye babu abun hawa.” cike da jin dadin kar’bar tayinsa yasa hannu ya bude mota kofar had’e da fad’in ”bisimillah.” ba tare da na tsaya na saurari maganar da Khalid yake min ba na shiga motar da murmushi na mussaman a fuskata duk dan na cuzgunawa zuciyar yaron……Motar ya kunna muka bar gurin ko da wasa banyi kuskuran kallonsa ba so nake na ‘kuntata masa dan saboda nasan ya tsani ya gan ni tare da mutumin bayan haka kuma inaso na nuna masa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane ni ba matar ‘kananun yara bace.

 

 

Khalid iskar dake gurin ya kaiwa naushi! rai a ‘bace ya shiga kai kawo a gurin zuciyarsa kamar zata tsaga kirjinsa ta fito saboda tsananin kishi! Salim yace.”Khalid dan Allah shigo mu tafi ka rabu da ita.” Yana huci! ya shiga motar, Salim ya mika masa pure water da fadin”Kar’bi kasa zuciyarsa tai sanyi kar’ba yayi kamar gaske sai kawai yayi wurgi dashi kan titi lips d’insa ya ciza da fad’in “Allah Salim wannan Alhajin idan baiyi wasa ba sai nayi masa rashin mutunci babu ruwana da wani kud’insa da shekarunsa wallahi mutukar bai fita daga harkarta ba sai na bashi mamaki.”!

 

Salim girgiza kansa yayi yace.” Khalid idan da zan baka shawara ka d’auka sai nace maka ka rabu da Aunty Sa’ida saboda nasan kai kanka kasan ba tsaranka bace aunty Sa’ida matar manya ce ganin idonka babu wani gajarabul d’in mutum da yake tunkararta duk masu nemanta manyan mutane ne kana dai kallo da idonka duk kudi da muqami irin na Alhaji Nura idan ya ganta rawar jiki yake mata.”

 

 

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yana kallon abokin nasa yace.”Salim duk abinda ka fad’a akan auntyna gaskiya ne wallahi ni kaina ina mamakin tsaurin idona a kanta Salim na rasa yanda zanyi wallahi aunty Sa’ida ta shiga zuciyata tayi kakagida! a cikinta, Salim bari na fad’a maka wani sirrina da ba kowane yasan dashi ba, tun inada shekara goma sha takwas a duniya na fara mafarki da ita haka zan wayi gari jikina a ‘bace! to tun daga sannan na gane cewa na balaga na zama cikakken namiji wallahi Salim babu ranar da zan kwanta bacci banyi mafarkinta ba kuma kai idan kaga irin rayuwar da muke da ita a mafarkin sai kayi mamaki wallahi sosai nake sex da ita ina jiyar da ita dadi tana jiyar dani! na rasa yanda zanyi da wannan masifar Salim ko a skull haka nake fama da wannan jarabar dan dai kawai adduar iyaye na tasiri a kaina amma da badan haka ba da tuni na nemi hanyar da zan biyawa kaina bukata.”

 

 

Girgiza kai Salim yayi yace.”Gaskiya Abokina na tausaya maka domin ni tuntuni na gane son maso wani kake yi domin jikina na bani aunty Sa’ida bata sonka duba da irin halin ko’in kulan da take nuna maka me zai hana kayi ya’ki da zuciyarka akan abinda kasan ba zaka samu ba.”

 

 

Ranshi a ‘bace! yace.”Salim idan kaga na daina bibiyar Aunty Sa’ida to aure tayi kai wallahi ko aure tayi ba zan hakura da ita ba saboda bata da wani miji sai ni wannan dalilin ne ma yasa na samu gwaggo na fad’a mata maganar ina ganin ko kowa ya’ki amincewa ita zata goya min baya.”

 

 

Salim yace.” Khalid ina jiye maka wahala wallahi na fada maka Aunty Sa’ida tafi karfinka ka hakura kawai.” a fusace! yace.” Salim wai wannan wace irin magana ce kake? a’ina ka ta’ba ganin mace tafi ‘karfin namiji! Auntyna nada 28year ni ina da 23year sai ka fad’a min ina tazarar take kai ni a yanda nake jin jarumta idan an had’a min iri-irin ta goma zan iya dasu ballantana ita da tun a mafarkina na gama da ita na fad’a maka a mafarkina fa tuntuni na gama mata aiki.” Salim ya fashe da dariya yana dukan sitiyari yace.”Kai Khalid wallahi baka da mutunci wato dai yanzu kana nufin fanko kake kallonta.”

 

Murmushi yayi ya d’an sosa tarin sumarsa yace.”Aa mafarki daban Zahiri daban yanda nake sarrafa ta a mafarkina to inaso na sarrafata a zahiri wallahi sai na ‘kure duk wata fitinar ta.” Salim ya dinga dariya yana fad’in Khalid baka da dama wallahi Allah ya baka aunty Sa’ida ka more ‘kuruciyarka dan wallahi nima ina son mace mai kyau da tsarin jiki irin nata kullum kamar ‘kara mata ‘kuruciya ake.”

 

Murmushi yayi yace.”Nagode da addua abokina.” Wasu mata ne suka tsayar dasu, Salim yace.”Hajiya ina zakuje.”?

“Gidan Murtala.” matar ta fada tana kallonsa, yace.”To ku shigo muje.” da sauri suka shiga, shi kuma yaja babur din suka bar gurin.

 

 

****

Cikin murya mai taushi yace.”Ranki ya dad’e har yanzu banji daga gareki ba inaso ki sha’ku da iyalina kafin Allah ya kawo ki cikinsu shine babban dalilin da yasa nace kina shiga gidan a cikin ranaku biyu kinayi musu lesson itama matar gidan tuntuni nayi mata bayani kuma ta amince da manufata.”

Alhaji Nura ne ke wannan maganar a yayin da suke tafiya a motarsa.

 

 

Ajiyar zuciya na sauke na d’an kalleshi da gefan ido mamaki sosai nake da maganarsa yana sona da aure amma kuma yana kawo wata gurguwar magana mara ma’ana Ta yaya zan dinga shiga gidansa da sunan yiwa yara lesson bayan da maganar aure a tsakaninmu hakan sam bai dace ba, ita kanta matar gidan da ta amince da hakan nayi mamaki amma dai nafi zargin gatse tayi masa tunda mafi akasari maza basu sanshi ba.

 

A nutse nace”Alhaji ni ina ganin ba lallai sai na shiga gidanka nayi wa yara lesson zamu sha’ku dasu ba, hakan kamar bai dace ba tunda har magana aure ta shiga tsakanina da kai a yanzu sai mu bari muga abinda Allah zaiyi idan har Allah ya kaddara aure a tsakanina da kai yara basu da matsala insha Allah zan tsaya na kula da harkar karatunsu amma maganar na dinga zuwa nai musu lesson ka ajiyeta.”

 

D’an murmushi yayi yace.”Sa’ida kenan ai da amincewar matar gidan nake miki wannan maganar ina ganin hakan duk ba wani abu bane tunda duk an riga an zama d’aya.”

 

 

“Alhaji kenan na yarda da amincewar matarka amma ni a ganina hakan ba kamata ba dan Allah kayi hakuri da wannan maganar domin ina ganin hakan shi yafi alkairi.” Yace.”To shikkenan tunda kince haka yanzu a’ina maganarmu ta kwana? inaso wannan karon ki bani dama na turo da magabata na akan maganar auranki.” Jim! nayi ina nazarin maganarsa “Insha Allahu zan kira wayarka idan na koma gida.” Cike da farin ciki yace.”To masha Allah Nagode ‘kwarai Sa’ida sai na jiki.” Murmushi kawai nayi ban sake magaba ina dai jinshi yana ta bani labarin yaransa sai da dariya yake gaskiya yanda na fuskance shi yana da son yara sosai……..cikin wannan halin ya sauke ni bakin gate din makarantar da nake koyarwa a nutse nace”Alhaji nagode kwarai.” kokarin bud’e mota nake yace.”Idan kun tashi ina iya turo direba ya dauke ki.” Da sauri nace”Aa Alhaji bani da matsalar abin hawa idan zan koma gida domin ‘kawata Hauwwa tana da mota tana rage min hanya.” Yace.”To shikkenan ranki ya dade a fito lafiya.” Nace.”Insha Allah nagode.” motar na bude na fita da sauri na daga masa hannu hade da fad’in “A sauka lafiya.” cikin sauri na nufi cikin makaranta kafin na shiga sai da muka gaisa da masu gadi cikin mutunci sannan da sauri na shige ciki…….

[17/11, 7:13 pm] +234 708 465 3262: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*

_(LOVE STORY🌺)_

*NA*

_BINTU UMAR ABBALE🍒_

*MANAZARTA WRITES ASSO..*

 

 

 

PAID BOOK

Ga masu bukatar complete na Littafin ..07084653262

 

 

*6*

“A a Sa’ida ba na son sharri! A ina kuka had’u da Khalid d’in da har za kiyi masa wannan gundumeman sharrin! yaron da tun d’azu ya fita dan babu yanda banyi dashi ba ma ya zauna ya ci abinci yace baya ci sannan kawai kizo kice yana k’okarin lalata dake a soro.”

 

Ina ‘kokarin magana Ummatu ta bankad’a labule ta shigo dakin da fad’in”Wace magana naji kuna yi ? kuna kuma kiran sunan Khalid.” Gwaggo tace.”Ke! Rabi abinda ba’a sa da kai ba dad’in kallo gare shi a’ina kikaji mun kira sunan Khalid da har zaki bankad’a labule ki shigo a fusace!

 

Murmushi tayi tace.”Gwaggo kenan duk fa maganar da kuke a kunne na ke Sa’ida ki shiga hankalinki dani wallahi wato Khalid din za kiyi wa sharri sabida baki da kirki to tun wuri kije ki nemi d’an iskan da yake lalubeki a soro amma ba Khalid ba.”

 

 

Ido na zuba mata har ta ‘kare maganarta ban tanka mata ba, Gwaggo tace.”To tunda dai kin fad’i abinda ya kawo ki tafi kuma wallahi kada naji maganar nan a bakin kowa mutukar maganar nan ta fita dukkaninku sai ranku ya ‘baci.”!

 

Ummatu ta’be bakinta tayi ba tare da tace uffan ba ta kad’a kanta ta fita daga d’akin.

 

Duk yanda naso na daure kasawa nayi hawaye na zuba nace.”Gwaggo wato ni ce ‘yar iska lalatacciya ko? dukkaninku baku yarda Khalid zai iya aikata abinda na fad’a ba kun goya masa baya ya cigaba da bibiyata ko okey to shikkenan Gwaggo yanzu na gane matsayina a gurinki dan gashinan a zahiri kin nuna min cewa kinfi kaunar Khalid a kaina alhalin duk kece kika haifi iyayenmu to babu komai Gwaggo kinji na rantse da Allah duk ranar da Khalid yayi kuskuran sake ri’ke min hannu sai na d’auki tsatstsauran mataki a kansa.”Cikin zafin zuciya nake maganar.

 

Tace.”To me zakiyi masa idan ya ri’ke miki hannu naga dai shine zai aureki to meye abin tayar da hankali kuma.” Da sauri nace.”Dake dashi zan kai ku gurin alkali sai kiyi masa bayanin da ki kayi min yanzu.”

 

 

Ha’barta ta ri’ke tana girgiza kanta tace.”Lallai Sa’ida ni zaki kai gurin alkali.”? “Kwarai kuwa mutukar baki daina daurewa Khalid gindi ba wallahi sai na dauki wannan matakin.” shuru tayi tana kallona, nasan mamakina take, dan na ‘kara tsoratata nace” Yanzu ma bari na kira wani abokin aikina wanda d’an uwansa yake aiki a kotun musulunci ta kasuwa na fad’a masa dukkanin abinda yake faruwa.” Da sauri ta rike hannuna tana kokarin kar’be wayar tace.”Sa’ida ashe baki da hankali kina so ki tona mana asirin gida.”

 

Nace.” Wane irin zan tona asiri ai gaskiya ce idan mun je gaban alkali sai kuyi bayani dake dashi wanda kike daurewa gindin.”

 

Hannunta na rawa tace”Yi hakuri dan Allah abar kaza cikin gashinta domin hakan yafi mutunci zan samu Khalid din naja masa kunne ya daina ta’ba ki tunda dai ba’a d’aura aure ba.”

 

 

Nace.”Shin yanzu kin yarda da maganata akan Khalid din ko kuwa baki yarda ba.”? Da sauri tace.”Haba na yarda mana dama sabida kada maganar tayi tsayi ne yasa ki kaji nace ban yarda ba amma nasan Khalid zai aikata kuma zanja masa kunne kiyi hakuri kinji ko.”

 

 

Ajiyar zuciya na sauke nace”To wannan karon dai na hakura idan ya ‘kara kwatantawa to zai ga abinda zai biyo baya.” Tace.”Bama zai ‘kara ba insha Allahu.”

 

Mi’kewa nayi na fita daga dakin ina jin tana fad’in”Kizo ka abincin naki ai tuntuni na shigo miki dashi daki.” Nace.”Wanka zanyi tukkuna.” Da sauri tace.”To shikkenan sai kin fito.” Bakin rijiya na nufa na cika bokiti da ruwa na dauka na kai bandakin, dakin na koma domin cire kayan jikina.

 

 

Bayan sallahr isha’i kasancewar ana zafi a gari gashi babu wuta sai mukayi shimfid’a a tsakar gida muna hira, Ya shigo gidan cikin rashin ‘kwarin jiki ya zauna kusa da ita da fad’in “Wash Allah Gwaggo na gaji wallahi nayi mutukar galabaita.”

 

Zaune ta mi’ke tana gyara daurin dankwalinta tace.”Yaron kirki ina kaje ne kuma me kayi ka gaji kana yawo cikin ka babu komai ina fata dai ka samu wani abu kaci.”?

 

Ajiyar zuciya ya sauke ‘kasa-‘kasa ya d’an kalli mutuniyar tasa kafin yace.” Wallahi Gwaggo har yanzu banci abinci ba Yau Salim ne ya jani yawo cikin adaidaita sahunsa.” Tace.”Allah sarki to ina fata ka samo d’an kwabo da d’ari.” Goshinsa ya murza yace.” Na samu me kike bukata.”?

 

Baki ta washe tace.”Ina bukatar Gashashshiyar kazar Malo mai nama.” Dariya yasa yana kallonta yace.”Gwaggo kina san dad’i a rayuwarki duba dan Allah kin iya fad’ar Malo mai nama.” itama dariya tasa harda tafa hannu tace.”To yaron kirki waye baya san dad’i ai mutukar ban takura maka ba to ka siyo min kazar malo mai nama.” Khalid ya dinga dariya yana kallonta.

 

Takaicin abinda suke ya isheni sai kawai na dauki wayata ina dubawa, naji yace.”Gwaggo ko kudin kenan yau sai kinci kazar Malo.” Yun’kurawa yayi ya mi’ke tsaye yana kokarin sa takalmansa yace.”Auntyna ke me kike so.”? Banza nai masa, Tace.”Sa’ida kina ji ya nayi miki magana ko babu dai kyau gaba.”

 

Ba tare dana kallesu ba nace.”Bana bukatar komai.” Tayi sauri tace.”Kaji wai bata bukata.” Yace.”Okey to babu damuwa ai ” hanyar fita ya nufa tace”To ina jira dan Allah kada ka fita abokai su ri’ke ka har nayi bacci.” Yace.”Yanzu zan dawo nima yunwa nakeji ai.” tace.”To kafin ka dawo bari na fito maka da abincinka.” Ba tare da yace wani abuba ya fita daga gidan

 

 

Mi’kewa tayi ta shiga daki ta dauko masa fulas din abincinsa kana ta dauko kofin silba ta ciko masa da ruwan randarta tazo ta ajiye a kusa da ita.

 

Kallonta nayi rai a ‘bace nace”Gwaggo keda zaki sanja masa fuska saboda laifin da yayi shine harda dauko masa abinci ko da yake ai nasan kin manta tunda kinga ya samo kudin siya miki kaza idonki ya rufe to har yanzu ina nan akan bakana.”

 

 

“Aa Sa’ida ban manta ba ina sane ina so yaci abinci ya huta sai nai masa maganar.” “Umm! nace naja bakina nai shuru! jin maganarsa shida abokansa a soro yasa na mi’ke na shiga daki, yana shigowa kai tsaye ‘kofar Ummatu ya nufa da fad’in ” Gwaggo ina zuwa.”

 

Da sauri tace.”Aa zo ka bani leda ta kafin ka shiga bana so ta za’be abinda ka shigo dashi.”! Dariya nasa ina mamakin ‘karfin halin Gwaggo mata ta haifi d’anta amma ta fita iko dashi…..Dawowa yayi da baya ya mi’ka mata leda guda tace.”To yawwa yanzu naji magana ka fito ga abincin naka.” Yana ‘yar dariya yace.”To Gwaggo.” Gurin mahaifiyar tasa ya nufa domin itama ya bata tata ledar.

kwance a d’an tsakar gidanta ya sameta da Mafici a hannu tana firfita shigowarsa yasa ta mike zauna tana kallon ladar hannunsa…..Zama yayi gefan tabarmar da take zaune yace.”Ummatu me zai sanya ki takura kanki bakya fita babban tsakar gida kisha iska sosai.”

 

Girgixa kanta tayi tace.”Khalid ‘kyaleni anan yafi min kwanciyar hankali akan na fita Gwaggo ta fad’a min ba’kar magana.”

 

 

Yace.”Ummatu idan da sabo yaci ace ki saba da halin Gwaggo wata irin macace mai wani irin hali bayan haka kuma akwai rikicin tsufa a tare da ita.” Girgiza kanta tayi tace.”Khalid dama ai kai baka ganin laifin Gwaggo duk abinda tayi daidai ne a gurinka.”

 

 

Girgiza kansa yayi yace.”Ba haka bane wallahi Ummatu yanzu a matsayin na shekarun Gwaggo dole ayi mata uziri shiyasa kikaga duk abinda tayi nake biye mata saboda samun nutsuwarta ba wai bana san laifinta bane.”

 

 

Tsaki taja tace.”Duk da da akwai tsufa to da akwai iskanci wannan tsohuwar guda ce Khalid ni kad’ai nasan irin takaicin da take kuntuka min a gidan nan.”

 

 

Yace.”To kiyi hakuri dan Allah komai mai wuce wa ne gashi kema na siyo miki nama.” Kar’ba tayi tana duba ledar tace.”Sai da ka kai musu suka za’ba tukkuna ni aka kawo min saura ko.”

 

Girgiza kansa yayi yace.”Aa Ummatu duk d’aya ne wallahi dake da Gwaggon.” Tace.”Ai kamata yayi ka daina daidaita ni da ita tunda ni na haifeka idan kana neman albarka sai kayi min biyayya.”

 

Yace.”Ummatu dan Allah ki daina irin wannan maganar wallahi dake da Gwaggo duk daya kuke a gurina ke kika haifeni dole kina da martaba ta mussaman a gurina Gwaggo kuma itace ta raine ni har na girma Gwaggo bata san ‘bacin raina komai ta samu nawa ne abinci wannan Gwaggo bata ci sai tare dani sai dana na tafi makaranta tukkuna muka raba kwano da ita Gwaggo takan iya hana cikinta abu ta ajiye min Ummatu kada ki manta Gwaggo itace tayi rabin dawainiyar Karatuna idan tayi sana’arta haka zata tattara kudin ta bani nayi hidimar makaranta dasu duk lokacin da nazo hutu sai ta bani kudi wata bukatar zata taso Gwaggo tayi Baba yayi a haka fa akayi ta tafiya har Allah ya kawo ni wannan lokacin da nake daf da kammala makaranta kinga kuwa dole na kyautata mata domin ta taka muhimiyyar rawa a rayuwata.”

 

 

“Khalid wato ka sani a gaba kanayi min gori ko? to ko banyi maka hidima ba ai ba zaka iya biyana irin dawainiyar cikin ka da haihuwar ka ba, saboda haka kada ka sake sani a gabana kana kawo min wata banzar magana.”

 

Shuru yayi yana jinta sai fad’a take masa yace.”To Ummatu kiyi hakuri dan Allah insha Allahu ba zan kara ba.” Shuru tayi masa ta mike ta nufi kicin plate ta dauko tazo ta zauna tana kokarin sa naman a ciki…..mikewa yayi ya fita daga gurin, nan ya samu Gwaggo a kashingid’e har taci ta gyatse tana gyangyad’i! zamansa a kusa da ita yasa da sauri ta tashi zaune tana fad.”Khalid ka fito.”

“Umm.” kawai yace ya zauna ya dafe kansa, cikin kulawa tace.”Menene yake damunka.”? Shuru yayi yana girgiza kansa, ‘kasa-‘kasa tace.”Kada ka damu da barazanar Sa’ida akan abinda kayi mata d’azu nan ta titsiye ni tanayi min jaraba wai sai ta kaimu kotu ni dakai.”

 

Cike da mamaki! yace.”Akan wane dalili zata kai mu kotu kuma me nayi mata da har take wannan furucin.”? Da sauri tace.”Yi magana a hankali Dan bana tsammanin tayi bacci.”

 

Tsaki yaja ‘kasa-‘kasa yace.”Me tazo tace anyi mata.”? Gwaggo murya a ‘kasa tace.”Wai cewa tayi kana tare ta a soro kana lalubeta.”

 

Yanda Gwaggo ta fadi maganar yasa dariya ta ‘kwace masa yace.”Ni sharri kawai tayi min abinda ma yau ban yini a gida ba.” Gwaggo tace.”To nima haka nagani ta shigo fuska a murtuke ta dinga jaraba dan har mahaifiyarka taso ta biye mata na shiga tsakaninsu, jin tana maganar kaimu gaban alkali yasa na bata hakuri nace zan ja maka kunne.”

 

Yace.”Gwaggo da kin sani ma baki wahalar da kanki gurin bata hakuri ba ni ba d’an iska bane da zatayi min irin wannan sharrin nima zan dauki mataki a kanta dan kafin ta kaini ‘kara kotu ni zan kaita tunda tayi min sharri.”! Sosai ya fitittuke yake kare kansa Al’amarin ya dinga bani mamaki! dan duk maganar da suke ina jinsu raina kuma ya ‘baci sosai da naji Gwaggon na rarrashinsa har tana cewa ai dama tasan Sharrin nai masa ba zai aikata ba, naji tamkar na fita naci masa mutunci sai dai kawai na taushi zuciyata na hakura na kyaleshi ina tunanin irin matakin da zan dauka a duk ranar da ya sake kuskuran ta’ba jikina..

 

Leave a Comment