*⚠️ Ban yarda a canja min ko da harafi daya na littafin nan ba, balle kuma har a saffara shi a dora a Youtube ba tare da izinina ba, yin haka kan iya janyo wa mamallakin Channel din babbar matsala dan haka a kiyaye!*
_Hasbunallahu Wa Nimal Wakeel_
*GOBE NA…*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
Free Page 1️⃣
*GUSAU ZAMFARA STATE NIGERIA.*
*Gusau Rd/Sokoto Rd*
*_Jifatu Shopping Mall_*
*_3:16pm_*
Madara ta fi komai yawa a cikin abubuwan da na siya, ba dan komai ba sai dan sanin cewa mahaifina ya fi bukatar tea fiye da komai a yanzu. Gwando daya na cika da siyayyar kayan ciye-ciye da tande tande sannan na dauki wani kwando na cika shi da da wasu abubuwa na bukatun yau da kullum kamar sabulun wanka da wanki da turare sai kuma omo.
Bakar abaya ce a jikina sai dan karamin mayafinta wanda hakan ya bani damar rika duka kwandunan na nufi gurin biya Amal na bayana rike da biscuit dinta. A saman dan teburin da suka tana dan lissafa kaya na dora kwandunan sannan na saka hannuna a jaka na ciro atm dina na rike a hannu ina jiran ya gama da wadanda suka gabana ya fara da ni sai na biya da pos din da yake gurin, domin na saba indai ban ciro albashi gaba daya idan na siye abu ina biya ne da atm.
Sai da ya gama da mutum biyu sannan ya fara da nawa, sai da ya gama lissafa komai kamin na mika masa kudin ya fara dauko leda yana sakawa, ni kuma a iya sanina idan kai siyayya a jifatu sai ka biya suke saka maka a leda su sallameka.
“Nawa ne?”
“Hajiya an biya”
Ya fada min yana ga aikin harhada min kayan a leda. A take gabana ya yanke ya fadi har sai da na dauki yan awanin sannan na sake tambayarsa.
“Waya biya?”
“Gashi can a waje”
Juyawa nai na kallin wajen sai n hango Abdallah tsaye jikin motarsa idonsa akan wayar da yake dannawa. Dauke kai nai na cigaba da kallonsa har ya gama saka kayan a leda sannan na mika hannu na karba.
“Thank you”
“No mune da godiya Hajiya”
Da duka hannayena na riko ledodin na nufo kofar fita Amal na rike da gefen rigata muka fito, ko da wasa ban kalli inda Abdallah yake tsaye ba balle har ya ga fuskata duk kuwa da na san hakan ba zai hana shi yi min magana ba idanya tashi.
Bakin titin na nufo ina ta tafiya ina sai jin maganarsa nai bayana.
“Ban biya kudin dan ki min godiya ba, kuma na san ba zaki min godiyar ba, amman ai ko kallona kya yi na dan ji sanyi ko?”
Tsayawa nai cak na juyo na watsa masa wata banzar harara fuskata a hade kamar bakin hadari. Sai dai da alama harar tawa dadi take masa domin murmushi ne ya cika masa fuska har ya cire farin gilashin idonsa yana kallona. Dauke kai nai na cigaba da tafiya sai jin nai ya riko hannun Amal wanda hakan yasa na juyo da sauri sai ganinsa nai yana danka mata kudi a hannu.
“Ku hau napep da wannan kin ji Amal nasan ko na ce na kai stubborn mother dinki a mota ba zata je ba”
Amal bata ce masa komai ba ta karbi kudin daman haka take indai kudi ne da biscuit bata kin karba ko a hannun waye, jan hannunta nai muka cigaba da tafiya.
“Yanzu na baro mijinki a can gurin damba area tare da abokansa da wasu mata”
Sake juyowa nai karo na biyu na dubeshi da duba na bakincikin jin kalaminsa da kuma na tsanar ganin fuskarsa.
“Miye ribar da zaka samu idan ka labarta min wannan? Kana tunanin zan yarda da kai? Mi zai saka mijina neman wasu matan banza a waje?”
“To ni ma dai shi na gani, namijin da zai aje mace kamarki mi zai saka ya nemi wasu a waje?”
“Baka tsoron Allah Abdallah saboda baka gudun taka dokarsa, kana isgili da ganganci ga dokokin aure da kumana Allah, shin zaka jidadi idan wani namijin ya kula matarka? Wani namijin ya iya furta wata mummunar kalma akanka gurin matarka? Kai baka kishin kanka? Daga yau karka sake yi min wata magana da ta shafi mijina ni mijina ba mazinaci ba ne, na lura kai baka san darajar aure ba kuma baka san kimar kanka ba balle har ka iya tsare mutuncin iyalanka”
“Na san darajar Aure Halimatu, na san martabar aure, kuma ina mutunta aure da duk wani mai aure, kawai dai ina son ki ne, ina son ki san kamanni da hallita suna canjawa amman zuciya bata taba canjawa, alakar da ke tsakanina da ke ba zata taba yankewa ba, ko bayan so ai ni dan’uwanki ne ko?”
“Ajinabi ba, kuma ina fatar ka san da hakan”
Ya gyada min kai yana murmushi. Ni kuma na juya na cigaba da tafiyata.
“Da ni nake da mace kamar ke ba zan bari ko tawaye na ya kalleta ba, balle kuma har wani namijin ya tsaya magana da ita, zan yi duk abunda zan yi na kare mutuncinta da martabarta”
Ban sake kulashi ba balle har na tsaya sake ce masa wani abun, na yi sa’a ina kaiwa titin na samu napep a take na daga mata hannu ta tsaya na shiga.
“Yan mangurora zaka kai ni”
“Dari biyu”
“Zan dai baka dari da hansi”
“To muje”
Sai da na fara saka ledodin hannuna na shigar da yana ta hudu wato Amal sannan shiga na zauna.
“Momy ga kudin”
Amal ta fada tana miko min kudin da Abdallah ya bata, karba nai na saka a jakata ina hade yawu, kamar hadin baki ina saka kudin karamar wayata tai ringing sai na fiddo hannuna tare da wayar ganin number surukata yasa ni saurin dauka.
“Assalamu Alaikum Hajiya”
“Na’am Halimatu kina lafiya?”
“Lafiya kalau Hajiya ya jikin?”
“Al-hamdulillah, na ce kin fadawa Aminu maganar kudin nan kuwa?”
“Eh Hajiya na fada masa”
“Idan ma baki fada masa ba ya kamata dai ki fada masa, har yanzu na ji shiru be ce komai ba ban sani ba ko baki fada masa ba, idan ma baki fada masa ba ya kamata dai ki fada masa yanzu, kuma izuwa yanzu ya kamata ace kina fahimtar cewar uwar miji ma kamar uwa ce, duk abunda ya shafe ni ya kamata ace kina daukarsa da muhimmanci”
“Wallahi na fada masa Hajiya, amman zan sake masa magana”
Bata ko bari mun yi sallama ba ta katse wayar, hakan kuma alamune da ke nuna cewar yau a fusace ta kirani. Haka na ke da yan’uwansa idan suna bukatar abu sai dai su kira su ce nai masa magana bayan ni kuma ba magana ta hake ji ba, mahaifiyarsa ma ta fi kusa da shi amman ita ma kanta sai dai tace na fada masa tana bukatar abu kaza da kaza, saboda gani suke komai na kame na mallake shi sai abunda na ce yake yi. Ko da yake shi ya nuna musu hakan domin a duk lokacin da suka bukaci abu ko da naira biyar ne sai yace balle nai magana da Halima, ganin hakan yasa suka dauki ido da baki suka dora min wai na mallake shi, ni kuwa nasan da zan samu mallakar kamar yadda suke zato da ba haka ba.
Har kofar gida mai napep din ya kai mu na fita na ciro kudinsa na mika masa sannan Amal ta fito tana bata fuska wai rana sai kace a kafa muka zo. Ganin motar Abdulhamit wato tawayen Abdallah fake gefen icen da ke kofar gidanmu ya tabbatar min da zuwansa, daman can ya kan zo jifa jifa ya gaishe da su Mama.
Ina gaba Amal na bayana tana kukan rana, gidanmu gidane mai yan mata da samari ina shiga yan matan gidanmu wato kanne waenda muke uwa daya uba daya da kuma waenda muke uba daya suka hau ihu da murna ganina.
“Oyoyo Anty Halima”
Da sauri kananna suka zo suka rika ledar hannuna, dayar kuma ta dauke Amal tai sama da ita tana dariya, daman haka gidan mu yake yana da wahala ka iya banbance yan dakin mu da waenda muke uba daya domin mu ba musan wani abu wai ubanci ba ko kuma yayan kishiya. Sai da na fara shiga dakin Inna na gaisheta sannan na nufi dakin mahaifiyata
“Maraba da Sadiya”
Cewar Mama da murmushi a fuskarta, ni kuma na zauna saman kujera ina mika mata gaisuwa tare da gaisawa da Abdulhamid.
“Yau kuma nan aka zo?”
“Eh Wallahi ya gida ya yaran?”
“Lafiya kalau”
“Yanzu ko na ke tambayarki aka ce kin kwana biyu ba ki zo ba”
“Wallahi yanzu na rage fitar nan sosai saboda abubuwan sun yi yawa ga hidimar yara ga zuwa gurin aiki idan na dawo kuma nai aikin gida, ba ni da hutu ne Wallahi”
“To Allah ya taimaka ni zan wuce”
“Tun yanzu”
“Tun dazu na zo fa, nan na ci abincin rana ma”
“To a gaishe da su Hajiya”
“Za su ji”
Ya mike tsaye yana ciro makullinsa a aljihu, banbancinsa da Abdallah kadan ne ta wajen hakoransa na gaba dayan ya dan kare kadan sai kuma yanayinsa da ba na Abdallah ba, amman kama iri daya ni kaina ba dan banbanci tufafi ba da motar da na gani a waje idan har na shigo be bude baki ya min magana ba zan iya cewa Abdallah ne.
Sai da Mama ta raka shi har gurin motarsa ta dawo, sannan take labarta min shinkafa ce ya kawo musu yar gobnati, daman haka familyn Baba suke suna da son zumuncin da son yi ma wanda ba shi da karfi a cikinsu, musamman ma Baba da suke ganin baya aikin komai kuma ga ciwon kafar da yake fama da shi, ga kuma iyali rututu mashallah, domin yan matan dakinmu kadai su hudu ne, idan aka cire ni da nake ta biyu da kuma yayana Maimunatu wace ke aure Kano da yaranta, ga kuma yayan Inna su ma su bakwai duka mata sa dai ita ta aurarda matanta hudu saura uku.
“Kai shinkafar nan mai tsada, Allah ya saka musu da alheri”
“Amin”
Ta amsa tana tambayar ina na baro su Namra da Salim.
“Suna gidan kanen babansu kin san yau weekend ne wai yace zai kaisu yawo tare da yaransa shine suka tafi Amal ce kawai ta ki zuwa”
“Ita sarkin lakuwa daman kullum tana nan manne da ke, idan kika haifo wani sai na ga yadda za tai”
Cewar kanwata Amina, ni kuma nai dariya na ce.
“Aa yar auta ce ai”
Kausar ta ce
“Ba wani auta wata zaki haihu mu ga karshen lakuwa”
Ban bi ta kansu ba na kalli Mama ina dariya na ce
“Ga sabulu nan na kawo muku, sauran siyayyar ssai wani watan”
“Babu komai Allah ya miki albarka”
Daman haka nake wata siyayar da ban yi ba a wani watan na ke musu ita saboda ni ma kaina ina yi ma kaina wata lalurar domin ba komai namiji yake dauke ma ba, balle miji irin nawa, daman kuma can maza ba sa son ba ni ba ni wannan yasa na tsaya kai da fata akan aikina, a duk lokacin da an karbi albashina sai nai ma kaina da iyayena lalurar da bata gagareni ba.
Bayan sallah la’asar na shiga dakin Baba na gaishe shi na bashi dubu biyar a cikin albashina kamar yadda na saba masa ko wane wata bayan siyayyar da na ke, yayi murna kuma ya min addu’a sannan na taso na fito harabar gidan inda kanenna suke zaune na zauna muna ta fira, a gurin Maryam na ga wani slim tea da kawarta ke saidawa na siye daya, ba dan ina da tabbacin yana yi ba sai dan neman rabuwa da kibar da na ke ko dan na huta da ci mun fuska da Abbah Adnan ke yi.
“Wai Anty Halima kin gama karanta Littafin Zaki kuwa?”
Jawahir ta tambaye ni. Ni ko na tabe baki ina murmushi.
“Hmmm na karanta gaskiya ba laifi littafin yayi dadi, wannan iya gata da soyayya da Aliyu ke nuna ma Ataa”
“Wallahi nima soyayyarsu ta tafi da ni, idan nai aure haka zan yi da mijina”
Ta karasa tana rage murna dan kar Inna ko Mama su jiyota. Sai muka kwashe da dariya.
“Ai auren yanzu ba wani soyayya a ciki Jawahir sai dai kawai hakuri da neman aljanna, amman duk wata soyayya ta littafi karki saka ran samunta a gaske, ban ce ba a samu ba ana samu amman kadan ba da yawa ba”
Na fada ina tuna irin tsarin rayuwar da na shirya ma kaina da mijin da na aura kamin aure, sai dai ina yin aure sai na tarar da ba haka ba daga lokacin da na fara haihuwa kuma sai na ga canji a gurin mijina, har ta kai yanzu bana burge shi saboda na yi kiba na yi fadi litattana ta canja daga budurwa zuwa mai aure da yara hudu.
Haka dai muka cigaba da firarmu gurin dariya mu yi har akai magariba, bayan na yi sallah na shiga dakin Mama na bata dubu biyar na bawa Inna budu biyu sannan na dauko Amal muka fito kannena biyu suka rakoni. Na samu napep nai min jinga daga unguwar zuwa igala quarters zai kawo ni dari biyu, a take na shiga su kuma suka kama hanya.
Ko da muka isa na tarar Abban Adnan ya dawo domin na ga motarsa a harabar gidan tun kamin na shiga, da sallama na tura kofar falon na shiga, sai dai be amsa min ba kuma be dago ya kalli inda na ke ba, yana zaune saman cushion idonsa akan tv yana kallon hausa bakwai suna haska wani hausa film da ban tantance shi ba, jin muryar yara a upstairs ya tabbatar min da sun dawo kenan suna dakinsu domin shi kadai ne a falon.
“Sannu da zuwa yanzu ka dawo?”
Be amsa ni ba sai wani cin magani da yai ya kalleni.
“Karki sake tura min yara gurin yawo, kin tura su kuma kema kin fita yawon ki”
“Ba yawo naje ba gida naje kuma na fada maka kamin na tafi”
“Na dai fada miki, bana son yarana suna zuwa gidan kowa, kuma na fada miki ki aje aikin nan bana so saboda aure na auro ki ba dan ki rika fita zuwa aiki ba”
Bance masa uffan ba, idan sabo na saba da jin maganarsa ta na aje aiki, ni kuma na gagara ajewar kamar yadda yake bukata saboda be dauke min duka lalurorina ba, kuma ga iyayena suna da bukatar taimakona a yanzu, aikin ma da be fi shekara uku da farawa ba. Amal ta tafi kusa da shi ta zauna shi ko hankalinsa na kan tv sai yabon kyau Fati washe yake, na san yana yin hakan ne saboda na ji haushi kuma na ji, domin har yanzu na kasa sabawa da halinsa na yabon kyawun wasu matan a gabana. Ina jin ba dadi idan ya yabi wace bata da jiki ko ya nuna yana son mace marar jiki saboda na san ni din ba siririya ce ba, duk kuwa da kasancewar ba wata shahararriyar kiba ce da ni ta kaico ba, kuma na san matukar mutun be ce min kyakkyawa ba to ko ba zai kira ni da mummuna ba, domin ni ma ina da kyau na iya yadda Allah ya ga zai dace da ni, ina da haske sai dai ba can sosai ba.
Upstairs na nufa dakin yarana na fara shiga na sai na samu Adnan da Aiman suna buga game a system dina, Namra kuma tana kwance saman gado ta rufe ido sai juyi take, cike da damuwa na zauna kusa da ita na kai hannu ina shafa bayanta.
“Namra lafiya?”
“Momy cikina ke ciwo sosai”
“Me kika ci?”
“Banci komai ba”
Ta fada cikin kuka ba tare da ta bude idon ba.
“Adnan me Namra ta ci? Ta ci yaji ko?”
Sai a lokacin ya dago har ya lura da ba dawo, ya zo inda nake da murnarsa shi da Aiman suka dafa ni.
“Momy kin dawo?”
“Eh me Namra ta ci?”
Adnan ya ce
“Wallahi ban sani ba, Baba Sadi ya kai mu gurin wasa yara ita kuma ya fita da ita yace zata raka shi wani guri kila can ta taci wani abun, domin da suka dawo ta rika cewa cikina na ciwo”
“Namra kin ci wani abu a can?”
“Ya siya min nama na ci kuma da yaji a ciki amman kadan ne yajin na ci saboda kin ce na daina cin yaji”
“To yajin ne ya saki ciwon ciki, bari na jika miki kanwa”
Ya fada ina mikewa tsaye na nufi kofar fita, Aiman ta biyo ni a bayana yana fadin shi ma zai sha, daman haka yake duk abunda ya ga yar’uwarsa Namra ta sha shi ma sai ya sha komai dacin abun saboda tsabar rigima.
*If you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
7/20/21, 8:28 AM – Buhainat: Ziyarci YouTube channel dina mai suna Taskar Khadeeja Candy domin samu duka littafaina a Kyauta
https://youtu.be/P9GOP9cqP6Y karku manta ku danna min subscribe Comment & Share.
*GOBE NA…*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
2️⃣
Sai da na jika mata kanwar ta sha na shiga dakina nai sallah isha’i, ina sallamewa nai saurin mikewa tsaye na nufi inda wayata take tana ringing na duba na yi zaton ko Abban Namra ne da farko sai dai ganin bakuwar number yasa ni aje wayar har sai na koma saman carpet har sai da na gama tasbihina nai addu’a ma mijina nai ma kaina da iyayena sannan na nemawa yara na shiriya. Daga bisani na mike tsaye na nufi inda wayar take aje na dauka na sake kiran layin da aka kirani da shi.
“Assalamu Alaikum”
Ni na fara mika sallamar kamin wanda na kiran ya fara min sallamar.
“Wa’alaikissalam Halimatu”
“Na’am Ranka ya dade”
Na gane cewar ogana ne na gurin aiki wato oga Dahiru.
“Ki yi kokarin hada document dinka kamin gobe ina da bukatarsu”
“To ranka ya dade”
“Kuma ki yi saving din wannan number ita ma number ta ce”
“To ranka ya dade”
Daga haka ya kashe wayar be sake ce min komai ba, ni ma kuma ban ce ba, daman kuma me zan ce masa, bayan kiran da yake min ma yana damuna balle kuma har nai wata magana da shi, zauna nai bakin gadon ina ta mamakin dalilin kiran da oga Dahiru yake yawan min a duk lokacin da yake bukatar wani abun, shin yana manta cewar ni ma ina da aure da iyali kamar shi, ban san miyasa yake son kira akan abunda be kai ya kawo ba, ba kira kadai ba har wasu abubuwna da yake min bana jindadinsu, domin duk abunda na ke ina kokarin kare mutuncin aure da kuma na yayana da mijina.
“Momy ni dai gobe idan mun dawo daga scul gidan zan dawo ba zan je gidan Baba Sadi ba”
Namra ce ta shigo tana wannan maganar tana wani bata fuska kamar zata fashe da kuka.
“Saboda me?”
“Bana son zawa can Momy dan Allah”
“Ki yi hakuri Mamana, idan kun dawo nan gidan ba wani abun za ku yi ba, kuma kin ga ba girki balle ku ci, amman can Momy Hassana tana girkawa, za ku samu ku ci”
“Momy to ki daina zuwa aikin nan pls ko kuma mu rika zama a gida a haka muna jiranki ki dawo”
“Mamana akwai abunda ake miki a gidan ne da baki so?”
Ta girgiza kai alamar aa sannan ta kwantar da kanta jikina.
“Cikin ya daina ciwo?”
“Eh amman yana min kadan-kadan ba sosai ba”
“Zai daina In-Sha-Allah, na zubo miki abinci za ki ci?”
“Za mu ci tare Momy zan wanke hannuna ba zan saka miki datti ba”
Murmushi nai mata sannan na mike tsaye na fito daga dakin na sauko downstairs. Ban samun Abban Namra a falon ba, daman kuma ban saka rai ba domin ba kasafai yake dawowa da wuri ba, idan kuma har ya dawo to sai idan wani abun zai yi ko zai dauka amman dai ba haka nan kawai zai dawo gida da wuri ba ko kuma ya wuni ba. Tuwon da na girka dazun kamin na fita na zubo miyar kuka sannan na fito bakin kofar kitchen rike da abincin ina kiran Adnan domin bana son sai na zauna ya zo yace min zai ci abincin.
“Adnan Aiman za ku ci abinci yanzu?”
Babu wanda ya amsa ni a cikinsu balle kuma har su sauko kasan da sunan cin abincin, sai Amal da ban kora ba.
“Ommy Ommy zan ci abinci”
“To zo ki ci yar autana”
Na fada ina karasa fitowa falon sannan na zauna kasan carpet din na zaunar da ita saman kafafuwana na soma bata.
“Namra zo ga abincin”
Da sauri ta sauko ta shiga kitchen ta wanke hannunta sannan ta saka min a plate, loma uku zuwa hudu kawai tai ta cire hannunta wai ta koshi.
“Cikin ne har yanzu Namra?”
“Eh ciwo yake min”
Ya fada tana yamutsa fuska sannan ta kwanta a gurin ba tare da ta wanke hannunta ba, ni kuma ban matsa ba ganin gata jindadi har sai da na gama sannan na dauke plate din na kai kitchen na wanke hannuna da na Amal a can sannan na dawo na dauki Namra na shigar da ita dakinsu na cire mata tufafin jikinta na nai mata wankan dare kamar yadda na saba musu na saka mata kayan bachi sannan na kwantar da ita, Adnan nan kam sai da nai kamar ina yi sannan ya bar gabar system din ya tafi yai wanka nai ma Aiman suka kwanta, ni kuma na dauke system dina na fito na baro musu dakin.
Dakina na dawo na kwanta gefen gadon Amal ta haye min kafafuwa tana kokarin fara kukanta na banza. Wayata na dauka na kunna data dama bana samun hawa online sai da dare idan yara sun yi bachi kuma na gama komai, grps din muna na Nothen Women’s Advice na fara budewa na duba chat din sannan na shiga na Salma pre-order na duba abubuwan da ta turo cikin har da injimin wanki wanda na fi kowa bukatarsa a cikin gidan nan saboda wanki da nake na yaran nan gashi kwana biyu sun lalata. Ban bar online din ba sai kusan sha daya da rabi na dare, sannan na tashi Amal wacce a lokacin ta dade da fara bachi a take ta saka min kuka daman ta saba ko ba ai mata komai ba tana kuka balle kuma an yi da dalili. A haka nai mata wanka na saka mata tufafin bachinta na goyata saboda na samu ta daina min kukan.
Dakin yaran na koma na ciro musu dayan set din uniform dinsu na dora musu a inda na saba aje musu sannan fito na shiga kitchen din n dauko abincin Abbah Namra na kai masa dakinsa duk kuwa da na san ba lallai ne ya ci ba domin ba ko da yaushe yake cin abinci a gida ba. A falo na fito da laptop dina na duba document din da oga Dahiru yace na shigo da su na fida su dabam a cikin wata folder sannan na rufe laptop din na koma dakin yara na kwantar da Amal. Na shiga nawa dakin nai wanka na saka kayan bachi na dawo dakin Abbah su na kwanta a take bachi yai gaba da ni abun ka da wanda ya gaji. Can cikin bachin nawa ina jin lokacin da Abbansu ya shigo duk yadda na so na dago nai masa sannu da dawowa sai na kasa saboda bachin da ya ci idona.
Washe gari tun da asuba na tashi, sallah ce farkon abunda na fara yi sannan gabatar da addu’o’ina suma ba duka ba daman idan ba weekend ba bana samun tsayawa nai yi su gaba daya, ina saukowa kasa na shiga kitchen na shiga shirya musu abincin makaranta da kuma na karyawarmu, bayan na firaye dan na fasa kwai sannan na shiga dora ruwan zafin, Amal ce farkon tashi daman haka take tafi kowa rigima ko a dare idan ta motsa bata ji ba, indai yan rigimar suna nan sai ta saka kuka ta dawo dakinmu ta kwana.
“Ommy Ommy”
Ta fada tana murja ido cikin kuka.
“Minene Amal?”
“Bachi”
“Je ki dauko zane”
Sai kawai ta fashe da kuka, haka yasa dole na cire dankwalina na goyata da shi na cigaba da aikina. Ban tashi su Adnan ba sai da na tabbatar na shirya musu komai na makaranta sannan na tashe su nai musu wanka suka sauko kasa na hada musu tea kawai suka sha suka hau sama suka shirya cikin uniform dinsu kasancewar yau monday. Ni kuma na shiga cikin dakina na dauko kudin napep na saka hijab dina na fito na saka yarana a gaba muka fito har Amal muka nufi titi ina kokarin taron napep sai ga makocinmu kuma mijin kawata Hajara ya faka gefenmu tare da yaransa a cikin motar ya sauke gilashin motar yana miko min gaisuwa, sai da muka gaisa sannan ya ce da su Adnan su shigo motarsa suka shiga da saurin ganin yaransa daman can makarantarsu daya kuma yana yawan wucewa da su idan zai kai nasa yaran, wani lokacin ma har gida yake aikowa yace su fito zai kaisu makaranta. Sai da suka shiga motarsa sannan na juyo na dawo ni da Amal ina yanje da hannunta muka shigo cikin gida. Tea ta na dazun da bata karasa shanyewa ba na mika mata sannan na nufi dakin Abbansu, tufafin daya cire na jiya na fara dauka dan hade su da waendan kayan daudan nashi, al’adata ce duba aljihun rigarsa da wando kamin na saka su a kayan dauda saboda cire masa duk wani abu nasa da yake cikin aljihu. Rigar na fara dubawa sannan na saka hannuna a aljihun wandonsa, sai na ji abu kamar kwalin wani abu ina cirowa na ga kwalin kwandon sai dai ba cikakke ba da alama an yi amfani da shi. Ni a
Kadai na san abunda na ji a wannan lokacin a take jikina na dauki rawa kamar dai yadda zuciyata ma take ta bugawa da karfi idanuwa na cika da hawaye. Juyawa nai ina rike da kwandon din a hannuna na kalli Abbah Namra da yake kwance saman gado yana ta sharar bachinsa hankalinsa kwance ni kuma nawa hankalin a tashe da kwandon a hannu. Dayan hannuna na saka na share hawayena da suka zubo na dauke kayan na fita da su, sai dai har nai aikin da nake na shirya Amal nai wanka nai shirin aikina hawayen ba su daina min zuba ba, ni kuma ban fasa sharewa da hannuna ba. Kamar yadda na saba yau ma na hada masa komai nasa na karyawa na shigar masa da shi dakinsa na kai masa, sai dai ban same shi a kwance ba sai na samu ya shiga bandaki da alama yana wanke baki ne, a can na baro Amal na fito na sauko kasa na nufi dinning na hadawa kaina tea amman sai na kasa sha saboda bacin rai da ke cikin raina, i decided na aje tea din na dawo saman cushion na zauna na dafe kaina. Wannan karon ba hawaye na ke ba wani abun ya ke jin ya tsaya min a zuciya marar misaltuwa daker na ke iya hadeye yawu da numfashi. Na kai minti talatin a haka sannan na tashi na koma dakina na dauko kwalin condom din na nufi dakinsa, kamin na kai hannu na tura kofar dakin na jiyo sautin dariyarsa hakan ya tabbatar min ko dai yana magana da Amal da take dakin ko kuma waya yake, ban yake dayan biyu ba na ji yana fadin.
“Na samu hutu satin nan ina kike son muje?”
Hakan yasa ni dauke hannuna daga jikin kofar daman can rikawa kawai nai ban tura ba.
“Kaduna? To yayi ba matsala zan shirya mana komai, amman kamin na turo account dinki zan saka miki wani abu sai ki yi siyayyar da kanki kin san ni ba zan iya zuwa siyayya yanzu ba, kuma kin san idan ina fita da ke yau da gobe za a iya fara cewa wani abu”
Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana ni ji ba, domin mutun ne mai daga murya idan yana magana da wani ko da kuwa kadan-kadan yake yi. Ji nai kamar ba zan iya sauraren firarsu suka ba hakan yasa na murda kofar dakin na shiga ina kokarin maida hawayen da suka cika min ido.
“Oh Okay Faruk sai na shigo”
Shine abunda ya fada sannan yai hanzarin kashe wayar, ya gyara zamansa yana kokarin fara cin abinci, ko da wasa ban bar wata alama da zata nuna cewar na fahimci da mace yake waya ba, duk kuwa da kasancewar bana iya sauya yanayi na rashin jindadi da walwala dake tare da ni a yanzu. Zaunawa nai gabansa.
“Ina kwana”
Na fada ba tare da na kalleshi ba. Shi ma bana tsammani ya kalleni kamin ya amsa min sai Amal kawai yake wasa da ita yana bata abincin shi ma yana ci.
“Jiya Hajiya ta sake min maganar kudin ac”
“Ai sai ki ce mata kin fada min magana, ni Wallahi na manta amman yau zanje na fada kudin In-Sha-Allah”
“To Allah ya bada iko”
Be amsa min da amin ba sai ya dago ya kalleni.
“Ya akai kin san bana son ana tsare ni idan ina cin abinci akwai wani abun ne?”
Har zan mishi maganar condom din sai kuma na hade yawu na gabatar masa da abunda na san ba lallai ne yai min ba.
“Jiya ne naga wani injimin wanki da ake order daga waje shine na ce ko zaka saka min wani sai na hada da abunda yake hannuna sai na siya na huta da kai wanki”
“Ba ni da kudi yanzu, ina albashinki? Ko aikin kawai kike ba a biyanki?”
“Ana biyana mana kai ma ai ka sani domin da su na ke rage wasu abubuwan nawa”
“To ki siya da shi ni ba ni da kudi yanzu, da kin ga mutun ya zauna kin fara masa maganar kudi kenan shiyasa ko zama gidan nan bana son yi kuma baki da lokacin magana sai lokacin da nake cin abinci”
“Irin wannan lokacin kawai nake samun damar magana da kai Abban Namra, baka dawowa da rana sai idan wani abun zaka yi da dare kuma sai 12 ko 1 kake dawowa”
“To ni dai ba ni da kudi yanzu”
Ya fada yana wani kara hade fuska. Sai na aje masa condom din da ke hannuna murya a sanyaye na ce.
“Ga wannan na gani a cikin kayan da ka cire jiya”
“Oh jiya Bala ya bani ajiyarshi na manta na bashi abarsa”
Ya fada kai tsaye kamar gaske ba tare da ya kalleni ba. Idanuwana cike da kwalla na ce
“Ko dai na wanene Allah ya sani kuma yana jiran kowa a madakata”
Ina fadar hakan na mike tsaye sai dai kamin na kai tsayen ya rigani yana daka min tsawa.
“To me kike nufi? Zagin kike ko kuma Allah ya isa za ki min? Wai mi yake damunki ne Halima? Daman munanan mata kun fi komai bakin hali ku ba kyau ba sai sakawa mutum damuwa da bakin zargin tsiya”
“Ba ni n hallici kaina ba Abban Namra, kuma saboda bana da siffar da kake so a jikin mace ba shi yake nufi ka bi wasu matan ba, kai kanka kasan ba haka ka aureni ba, auren shekara goma sha biyu bana kwana biyu ba ne, dole wani abu a jikina ya canja, na haihu har hudu dole jikina ya bude, ka dinga jin tsoron Allah Abban Namra….”
Kamar jira yake na kare a take ya wanka min wani mahaukacin mare mai zafi kamar garwasun wuta, kamin nai ihu Amal ta fara fashewa da kuka ta rike masa kafa damn ta saba masa haka ida da su Namra da Adnan idan yana dukana, ni kuma ban tsaya komai ba ya juya da sauri na fice daga dakin ina kuka.
“Dacan bana tsoron Allah aka ce miki? Wawuya kawai”
Shine kadai abunda na ke iya jiyo yana fada bayan na baro dakin, da gudu na dawo dakina na zauna kasa na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya.
7/20/21, 8:28 AM – Buhainat: https://my.w.tt/kmm6u2LFKbb
*GOBE NA…*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
3️⃣
Kuka nai mai isata sannan na tashi na shiga bandakin na wanke fuskarta na fito na nufi gaban madubin na dan shafa mai kadan da hoda sai dai hakan be boye kumburin da fuskata da kuma idanuwana sukai ba.
Hijab din da yai yanayi da farar atamfar da nake saye na dauka na saka sannan na dauki wayata na saka a jakata na dauki laptop din na saka takalmi na fito daga dakina. Yau ban tsaya bin ta kan Amal ba balle har na kaita da kaina gidan kanensa daman wani lokacin shi yake kaita idan na fita na barta a gunsa wani lokacin kuma ni nake kai ta sai dai idan ni na kaita ta fi min kuka saboda takuwa irin nata. Na saba daman a duk lokacin da zanje aiki sai dai naje a napep ba dai ya kai ni ba, kusan tun da na fara aiki sau biyu ya taba rage min hanya ya kai ni da motarsa, babu kuma yadda ban yi ba da shi akan ya siya min mota amman ya ki ba dan bashi da hali ba, sai dan ya fi son nai ta wahalar zuwa aiki a napep ga kuma kai yara scul da nake duka a napep, ya bar ni da dawainiya kala kala kamin a dan bashi da halin dauka ba sai dan keta irin na shi.
Har na shiga napep ban daina tunanin wayar da naji yanayi da wata ba, ciki har da zancen kudin da zai bata bayan ni na roki alfarmar ya cika min na samu na siye injimin wanki yace min ba shi da su, ga kuma zancen hutun daya samu har yana fadin wane gari take son suje, ada can kam na kasa yarda cewar Aminu yana neman matan banza duk kuwa da kasancewar ina ganin chat dinsa da wasu matan wani lokaci ko kuma na ji yana fira da su, sai dai a nawa tunanin irin chatting din nan ne na budurwa da saurayi da maza suke yi, wanda ba zaka iya raba maza da shi ba, sai dai ganin condom a aljihun wandonsa ya tabbatar min da abunda Abdallah yake yawan fada min, sukar auren da yake min na uban diyata yau na tabbatar da shi, no matter what Aminu zai fada min ba zan taba yarda ba, taya abokinsa zai bashi ajiyar condom miyasa shi ba zai aje da kansa ba sai ya bashi ajiya? Ban san lokacin da kuka ya kubuce min ba, ashe tun da na soma tunanin nake hawaye ban sani ba.
“Hajiya Lafiya dai?”
“Lafiya kalau dan Allah juya da ni inda ka dauko ni”
Na fada ina jan majinar hancina,tare da saka hannuna na share hawayena. Kamar yadda na umarce shi haka ya juya ya koma, sai dai ban bari ya karasa ba na tsayar da shi na sauka na bashi kudin shi, daman ba gidan zan koma ba, gidan su kawata Hajara zan je na saba zuwa can a duk lokacin da abun duniya ya taru yai min yawa ita kanta da zarra ta ganni ta san akwai wata matsalar. Sallamar da nai cikin muryar kuka ce ta karantar da ita ina cikin wani hali.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’u”
Shi ta furta amaimakon ta amsa min sallamar, ta aje Affan da ke hannunta saman kujera ta taso ta nufo inda nake ta dafa ni ganin kamar ba zan iya karasowa saboda kukan da ya koma min sabo.
“Halimatu”
“Na’am”
Na amsa daker, sannan na zauna a kujerar da ke kusa da ni ita ta zauna kusa da ni tana ta kallon kukan da nake cikin damuwa, har sai da nai wanda zan iya sannan na labarta mata abunda ya saka ni kuka a yau.
“Wata kila da gaske ajiya aka bashi, ki rika kyautata masa zato dan Allah”
Kaina na daga na kalleta.
“Idan wacan ajiya aka bashi wayar da na ji yana yi fa?”
Sai tai shiru domin a nan bata da amsar ba ni, ina da tabbacin babu wani abun da zata fada da zai kare shi a nan.
“Ba zan ce kunne ki be ji daidai ba, amnan ina son ki sani yawancin mazan nan haka suke, suna nan kashewa matan waje kudi ko da kuwa ba su yi ma na gida ba, ki yi hakuri Halima”
“Ko da yaushe idan na fada miki damuwa nai shiru kike cewa, ba ki tunanin hakurin nan zai iya zame min illa? Wallahi na gaji Haraja na gaji”
“Karki gaji da bautar Allah, ki dauki aure a matsayin idaba kuma ibadar da ta fi ko wace wahala, dan’adam be tana yin hakuri ya kasa cin ribar hakurin ba, idan rashin kyautawa Aminu baya kyauta miki amman ki yi hakuri wata rana za ki ji dadi”
“Yaushe zan jidadin? Tun da na haifi Adnan nake fuskantar wulakanci daga gurin Aminu har yau, haihuwa ta hudu kawai yake min wannan abun ime kike tunani a gaba? Ya GOBE NA zata kasance? Ina jin kamar babu wata matar auren da zata iya hakurin zaman auren da na ke da Aminu, shi ya min yan’uwansa su min ya zan ji?”
Dafani tai tana min magana a hankali
“Suna nan da yawa wadanda suka fi ki hakuri Halimatu, wasu ko abincin basa samu amman haka suke hakuri su zauna, ke ko har yana aje miki abinci ko da bashi da dadi ya dai baki lokacinsa ne kawai baya bashi da wasu hakokin, shin idan ba ki yi hakuri ba Halima so kike na ce ki kashe aurenki ki koma gidanku da zama cikin kannenki? Ya matan gidan ku a yanzu taskwas ne so kike a fara kirgawa da ke a zaurawan unguwarku? Ki tashi hankalin iyayenki da na yayanki? Kina da tabbacin shi wani mijin da zaki aura baya nema mata ko kuma zai baki lokacinsa? Ki bar yayanki su tashi a hannun wata wacce ba uwarsu ba? Adnan shekararsa goma sha daya kuma shine babba shi din ma kina da tabbacin zai iya yi ma kansa wata lalurar balle kuma sauran?”
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’u.
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’u.
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’u.”
Shine abunda nake ta furtawa na dafe kaina.
“Ki yi taka tsantsan da aurenki Halima saki daya ya rage a tsakaninku, wani abun ko dan yaranki ai kya yi hakuri ki zauna da mijinki a haka, kuma ki gode Allah da har mijinki yana amfani da Condom din, wasu mazan kamar tumaki suke babu ruwansu da kariyar kai, kuma wani lokacin mu kan mu mata muna da matsala, Halima ko yan gyare gyaren nan ba ki yi su kuma maza basa son haka, mace sai da gyra ko da ko baki haihuwa ba balle kin yi haihuwa har hudu”
“Namijin da ba ya maka kallon sha’awa Hajara wani gyara zan tsaya yi akansa? Idan ma nace zan yi gyara zan bata kudina da lokaci na ne a banza”
Na fada ina share hawayena.
“Ba haka ba ne, ba jira za ki yi har sai shi ya kawo kansa gareki ba, ke ma zaki iya yin wasu abubuwan na wayewa da janyo hankalin mijinki izuwa gareki, su ma matan waje ai ai janyo hankalin mazanjenmu suke har su kao garesu”
Kallonta nai ina sauke ajiyar zuciya.
“Hajara yace na daina burge shi wai shi baya son mata masu kiba, kuma shi yanzu farar mace yake so ni kuma ba fara ce fes ba, kuma ina da ji ba siririya ba ce ni, bana ganin ina da wani sauran digon kyau da zan iya jan hankalin Aminu da shi a yanzu”
“Bayan jan hankali, zamantakewar aure tana bukatar tattauna da fahimtar juna, kin rigani aure Halima amman kamar na riga ki karanta halin maza, ki zauna da mijin ki bashi hakurin abunda ya faru dazun ki nuna masa ke ce mai laifi ko da kuwa shi ne da laifi kuma ki fada masa zaki kiyaye, abu na biyu ki lura da abunda zaki iya canjawa sai ki yi kokarin yi, yar kwaliyar nan t tarbon miji ki rikayi mana haba Halima sai kace ba wayayya ba?”
“Namijin da baya dawowa sai 12 ko 1 na dare shi zan yi ma kwaliya? Kuma ya riga ya furta cewar bana burgeshi a yanzu duk wani abun da zan yi aikin banza ne Hajara”
“Ki gwada dai, akwai wasu kayan mata masu kyau anjima za a kawo min zan aika miki ki gwada amfani da su, ki maida komai ba komai ba Halima dan Allah ki yi hakuri ki zauna ko dan yayanki”
“Da ma kin bar kayanki, rabon da Abban Namra yai mu’amala da ni tun daga lokacin daya fahimci ina da ciki, daman can ba bukatana yake ba balle kuma yanzu”
“Ba daga nan take ba, ke dai ki yarda da ni ki gwada dan Allah, wanna kam ba mota ba ko jirgi kika ce kina so sai ya siya miki”
Kai na gyada mata ina tabe baki gare da sake share hawayen da suke min zuba, jin motar mijinta yasa na mikewa tsaye, kamin mijinta ya shigo falon nai mata sallama na fita da sauri domin ba kasafai na ke son yana ganina a gidan ba, ba dan komai ba sai dan tsaron mutuncin aurena.
Daga gidansu Hajara kai tsaye gurin aikinmu na nufi, sai dai ban shiga Office ba sai da na biya ta gurin masu printing na cikin company nai printing documents din sannan na shiga cikin office din.
Na shiga a lokacin da wasu sun dade da shigowa ma’aikatar wasu kuma yanzu suke shigowa a yayinda wasu kuma sai anjima za su shigo kowa da yanayin aikinsa da kuma lokacin shigowarsa. A inda muke zaune mu uku ne a Office din daga ni sai wasu abokan aikina biyu duka maza, daga ni sai Kabeer sai kuma Emmanuel wanda yake ba bahaushe ba. As usual idan na shiga ina gaishe da duk wanda na tarar a office din, idan kuma su suka tarar da ni suna miko min gaisuwa cikin mutunci da girmamawa.
Yau kam Kabeer kawai na tarar na office din hakan na nufi ya riga Emmanuel shigowa kenan.
“Good morning Kabeer”
“Morning Halimatu”
Na mika masa gaisuwar a lokacin da nake kokarin zaunawa, shi kuma ya amsa min yana baro bangarensa zuwa inda nake zaune.
“Kamar kina cikin damuwa yau kin karya kuwa?”
Haka yake min a lokacin dana shigo office din yana kokarin kula da ni kamar matarsa duk kuwa da na san kular bata Allah da Annabi ce ba, na san yana da wata manufar akaina
Hannu ya kai zai taba jikina sai nai saurin buge masa hannun na mike tsaye cikin bacin rai na ce.
“Miye haka Kabeer taba ni za kai? Ka manta da ina da aure ko me? Wai miyasa kake min wasu abubuwan kamar baka cikin hayyacinka ne?”
“Halima kenan, ni da ke mun zama daya a nan fa? Miye laifin dan na na taba jikinki?”
“Idan a gurinka ba laifi ba ne ni a gurina laifi ne, ina da aure har da yara hudu abunda ban aijata shi da budurcina ba ba zan aikata shi da aurena ba”
Ina fadar hakan na dauki documents din na wuce zuwa office din ogan mu, na yi zaton yana cikin musamman da na ga ya kirani jiya yace na shigo da takardun nan a zaton ko da saffafe zai duba su amman sai gashi ban same shi a office din ba. Hakan yasa na dawo nawa office din na zauna na soma aikina, gaba dayan ranar Oga Dahiru be shigo ba, haka ma wunin ranar Kabeer be ga wata sakewa a tare da ni kamar yadda ya saba gani ba. Har muka tashi daga aikin ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be yi kokarin yi min magana ba.
Kamar yadda na saba bayan na taso daga aiki na wuce gidansu Baban Sadi wato kenen mahaifinsu domin dauko yarana daman yana daukarsu tare da yaransa ya kai su gidansa idan an tashi scul har sai idan na taso aiki na biya na dauko su a Napep mu dawo. A bakin kofar falon muka gaisa da matarsa sannan na kirasu suka fito banda Namra.
“Ina Namra?”
“Tana can part dinsa ai kin san indai yana nan to tana can part dinsa, ko fita zai yi da ita yake fita Allah ya hada jininsu”
Cewar Safiya matarsa. Ni kuma nai murmushi ba tare da tunanin komai ba na kalli Aiman na ce yaje ya kirata na saka Amal da Adnan a gaba muka nufi gate da zimmar Namra da Aiman su cin mana. Kamin mu fice daga gate din gidan sai gasu sun ci mana Namra na ta sharar kwalla idonta ya yi ja sosai.
“Ke lafiya?”
“Cikina ke ciwo”
“Oh wannan ciwon cikin ya matsa miki, bari yanzu idan muka muka je gida su Adnan suka wuce Islamiya sai na kai ki asibiti”
“To Momy”
Ta amsa min cikin kuka har sai da ta bani tausayi. Napep na tara na saka yarana sannan na shiga muka nufo gida. Indomie na fara dafa musu suka ci sukai shirin islamiya sannan na dora tuwo na shiga nai wanka nai ma Namra na shirya ta, sannan na fita na kira Kausar wata kanwar makociyata wacce budurwa ce daman na kan kirata ta rika min wasu abubuwa. Ita na barwa girkin sannan na ja Namra muka nufi Asibitin Yarima ganin likitan yara na maraice.
Ba mu tararda jira kamar safe ba, daman da maraici ba a cika taruwa ba, a lokacin da muka shiga dakin likita ya tambaye ta komai ta fada masa yadda take jin cikin nata yana mata ciwo, sannan na rubuta mana hoto da awon fitsari sannan na rubuta mata magani. Sai da na kaita akai mata hoton fitsarin kuma suka ce a kawo na safe wanda zata fara yi kamin ta ci komai. Maganin ne kawai ban siya mata ba muka dawo. A saman kujera ta kwanta ni kuma na shiga kitchen na dora miya domin ko da muka dawo Kausar ta toke mana tuwon.
Daf da magariba Adnan suka dawo daga makarantar islamiya, daker na tattara su sukai sallah sannan na kwashe miyar na zuba musu nasu na sako nawa ni da Amal muka ci Namra kan ko ruwa kasa sha tai, hakan yasa na dauki wayata na kira shi. Sai da ta dade tana ringing sannan na daga.
“Ya akai?”
Shine abunda ya far tambaya, ni kuma na mika masa gaisuwa
“Ina wuni?”
“Lafiya Kalau”
“Namra ce bata da lafiya tun jiya cikina na ciwo shine na kaita asibiti dazun suka bamu awon fitsari da hoto kuma suka rubuto mata magani”
“Wa kika tambaya kamin ki fita? Da izinin wa kika fita?”
Sai na kasa amsa masa domin na san bana da gaskiya a nan, be kamata na fita ba tare da na tambaye shi ba, sai dai na san idan na tsaya tambayarsa ba lallai ne yace na tafi ba domin duk wani abu daya fito daga bangarena baya daukar sa da muhimmancin wata kila ma zai ce kashin kudin ne zan ja masa.
“Ka yi hakuri dan Allah”
Be amsa min ba yaja tsaki ya kashe wayar. Ji kuma na sauke ina jin raina ba dadi a take abincin ya fita raina daman da safe ban iya karyawa ba.
“Adnan je ka kira min Kausar ta siyo ma Namra magani a chemist”
Da sauri ya tashi daman dan son yawo ne shi da Amal a take ta rufa masa baya har da gudunta. I decided na aiki Kausar din na bata kudin da ke hannu ta siyo mata maganin kamin shi ya gama fushinsa ya siyo mata. Adnan na fita sai ga Afrah ta shigo wato yar Hajara da bakar leda a hannuna.
“Wai ga shi Momy tace a kawo miki”
Karba kawai nai na aje ba dan ina tunanin amfani da shi ba, domin na saba amfani da irin abubuwan nan ban taba ganin ribarsu ba, sai dai na ji wasu matan suna labarin abu kaza yana da kyau ko yana yi, ni dai nawa mijin bayan nuna min idan ma na sh wata kila kuma ni tawa hallintar bara karbar irin waennan abubuwan. Afrah na fita sai aka sake turo kofar falon aka shigo wannan karon Sa’adatu ce kawata.
“A a maraba da manya”
Na fada ina dariya.
“Ah ai kune manya kuna cikin irin wannan gida haka ga uwar daula ai kukan ku kukai dacen auren mu mata kawai muka rako duniya”
“Uhmm”
Kawai na iya fada domin yawancin mutanen da suke zuwa gidana suka ganin kyakkyawan falona da gidan sai su tai min kallon kamar na fi kowa dacen aure.
“Bari dai na kawo miki ruwa”
Na fada ina nufar kitchen, ita kuma ta hau tambayar ina Amal da sauran yaran.