Gangar Shedan Hausa Novel

Gangar Shedan Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Gangar Shedan Hausa Novel

MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION

Labari mai taba zuciya da ban tausayi.Wannan labari ya kumshi darusa dadama da ilimantarwa yana kuma nuni da irin halayan da mata sukan jefa kanunsu ciki a sakamakon biyewa *ruÉ—un zuciya*

 

 

*Note* ban yarda wani/wata ba su sauyamin labari ba.idan kuma kika sauyamin labari ba tare da amincewata ba banyafe ba.

Page 1&2

Gida ne wanda yake d’auke da É—akuna wajan 20. Daganin tsarin gidan ko ba’a fada maka ba hakan ze taba tar maka da cewa gidan kwaruwai ne.

 

 

A tsakar gidan na iske maza da mata suna zaune a cikin katuwar rumfar gidan, sunata faman yin modi wasu daga cikin su na hura hayaƙin taba, wasu kuma shaye-shaye suke yi hankalinsu a kwance, babu ɗaya cikin su wanda yake da shigar musulunci dukanin su kayan jikin dasu gara babu musaman ma matan dan su mazan daga me gajeran wando, sai wanda ya ɗan suturta ya sa boxers .

Wata mata ta fito daga cikin wani ɗaki ba ƙaramar mace bace tana da jiki, uwa uba hips ɗinta da suke rinjaya ta dan da ƙyar take ɗaga su uwar daba kenan, uwar ƴan iska ina yaron daya gagari uwarsa da ubansa yazo ga uwar sa,

 

 

idan ka gagari uwarka kazo uwar daba zata d’auke ka tabaka daki ka z’auna ta mayar dakai É—anta(wa iya zubila Allah kayi mana tsari da wannan mata).

Suna ganinta aka soma yimata kirari ita kuwa sai juyi take tana ƙara ɗaga kanta sama, ana tafiyar kasaita.

See also  Yar Gan Gan Hausa Novel Complete

Wani daga cikin su ya d’auko mata kujera ta zauna tana faÉ—in, “wai ina yarinyar nan take yau ban ganta ta fito a gidan nan ba gashi ha Æ™arfe 1:00pm ta kusa” tana maganan tana tauna cingum. Wata daga cikin su, ta mayar mata da amsa cikin maye”ai tun jiya bata fito daga É—akin ta ba, kinsan fa jiya ta É—uri ruwa dayawa( tana nufin wai tasha giya da yawa) kwaÉ“e ta uwar daba tayi tace”ke rufe min baki kin wani karkace baki kina magana magana da wata fuskarki mumuna”(ni kuwa nace to kaji fa karfin hali É“araho da sallama, bata fiki kyau ba duk dama kin sha bleaching )tashi tayi ta nufi wani É—aki dake jerin É—akunan da ta fito daga cikin shi, soma bugun dakin tayi tana kiran.

 

Gangar Shedan

 

“Teema, Teema”shiru kake ji ba’a amsa mata ba sake bugawa tayi tare da kiran sunanta,a matuÆ™ar fusace ta buda É—akin tace “wai uban waye yake bugamin kofa haka”, masha Allah na faÉ—a yayinda wata yarinyar ta fito kyakkyawa ce ba Æ™arya fara ce ba sosai ba, tana da tsayi ba sosai ba, tana da shape sosai, gata da boobs ga hips masha Allah,

 

Gangar Shedan Hausa Novel

gashinta har bayanta ga d’an bakinta pink da dara-daran idanunta, tana sanye cikin riga da wando black batada d’an kwali a kanta, uwar daba ta kalle ta tace”haba teema meyasa kike min haka ne wai, naga baki tashi bane shiyasa nazo naga Lafiya”, hararar ta tayi tace “ina ruwanki da lafiya ta ni na saka ki kizo ki tashe ni,

See also  Alhakin So Hausa Novel Complete

 

 

wai bana faÉ—a miki ba, kada ki sake zowa Æ™ofar É—aki na ba”, hakuri uwar daba ta bata ta fice ta koma É—akinta, Ita kuma wannan yarinya da aka kira da Teema taja Æ™ofar d’akinta ta rufe.

 

 

Raslan da Rasma Hausa Novel

Tofa yanzu labarin yasoma
~shin menene tsakanin Teema da uwar daba da bata tsoranta haka?
~menene maƙasudin zaman Teema a cikin wannan gida ?
~shin wai wacece Teema?

Duk wannan zaku samu wannan amshoshin ku dai cigaba da bibiyar labarin

Daga taku har kullum
Y’ar lelen d’an lele

​

 

 

Name: [GANGAR HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


7 thoughts on “Gangar Shedan Hausa Novel”

  1. Pingback: Hausa Novels Littafan Hausa Guda 10000 Masu Dadi JIKI NA YAKE SO COMPLETE HAUSA NOVEL | My Novels

  2. Pingback: Yan Ashawo Hausa Novel | My Novels

  3. Pingback: Ina Mafitah Hausa Novels Complete | MY NOVELS

  4. Pingback: Akan Dadiro Na Hausa Novel Complete | My Novels

  5. Pingback: Masarautar Qamar Hausa Novel Complete | My Novels

  6. Pingback: Deen House Hausa Novel | My Novels

  7. Pingback: Gwauro Hausa Novel Page 1 to 10 | My Novels

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top