Hausa Novels

Gidan Dadi Hausa Novel Complete

Gidan Dadi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Gidan Dadi Hausa Novel

…Na dade ina tunanin rayuwata a kauyen yankin kindau, Da zamana a birnin Lagos da kuma yanzu da na sake samun rayuwata acikin MASARAUTA. Lalle Allah shine masanin gaibu. Ko da wasa ban taba kawowa rayuwata garuruwan da na zauna ba. Ajiyar zuciya na ja na sauke ina mai cigaba da istigfari.

Gidan dadi

Qarar murda handle din kofar da akayi ne yasa na juya daga kwanciyar da nayi. Ban dire idanuna a ko’ina ba sai kan Ya Mukhtar da hannunsa ke dauke da bargo da kuma fulalluka.

Ya zubawa ilahirin jikina kallo. Hakan ya sa na sauya fuskata hade da jan zanin gadon da nake kai na tukwikwiye da shi,

 

“Menene hakan Ya Mkay?”

 

Ajiye kayan yayi akan gado ya shiga sosa keyar sa.

 

“Naki ne…”

 

“Ga bargo na anan da fulalluka wadatattu”

 

“Bakya tsoro ki kwanta anan ke daya ?”

 

“Tsoron me zan ji? Lokacin da ummanmu ta rasu ma ni daya ke kwana a daki. Da nazo na koma Lagos nanma ni daya ke kwana a daki. Kaga kuwa ai ba maganar tsoro anan. Nagode maka. Amman ka koma da su. Don kaga gashi ai akwai bargo ga fulo daya, biyu , Uku, hudu, biyar ..” Na karasa ina mai kirga pillows din dake kan gadon da nake.

 

“Bazan iya barin ki ke daya ki kwana anan ba Fateemah. Zuciyata ta ba zata taba kwanciya ba.”

 

“To ni dai kaje ka kwanta kuma dare ne yake kara yi”

 

“Korana dai kike Fateemah ”

 

Bance masa komai ba. Ya gama neman maganar sa yatafi.

Karanta Littafin Haihuwar da namiji

Na sake runtse idanu na , Naja bargo na kashe fitilu. Ba’awani jima ba sai gashi ya sake shigowa.

 

“Zuciata ta kasa sukuni Fateemah. Zance na gaskia ban amunta ki kwana anan ba ke daya..”

 

“Dan Allah kaje ka kwanta Ya Mkay..”

 

Biris ya mun ya shiga shimfida bargon hannun sa akan carpet din dake gaban gadon.

 

“Menene haka?”

 

“Hakan ce ta kawo haka”

Ya ban amsa kan sa tsaye.

 

Ban sake bi takan sa ba, Na dakko fulalluka na jere su a gefe da gefen karshen gadon. Sannan na kudundune kai na acikin bargon har fuskata. Na rirrike sa da hannu na.

 

Inata salati a haka bacci ya dauke ni ban farka ba sai da akai kiran sallar faari na asubah.

 

Nayi matukar mamakin yanayin dana tsinci kai na ciki. Na tukwikwiye Ya Mukhtar tamkar za’a kwace mun shi. Yayinda hankali kwance yake baccin sa fuskar sa qumshe da murmushi.

 

Nayi nayi na zare hannun sa daga tallafonin da yayi na kasa. Hannuwan sa duka biyu yana saqale dasu a jikina. Ta hanyar riko tundaga ruwan cikina zuwa bayana. Yayinda ni ma na riqe shi gam gam. Yayiwa kansa matashin kai da kirji na.

 

Na dubi yadda yake baccin sa kansa akan kirjina hankali kwance yana futar da numfashi. Wani tukukin bakin ciki ne ya ishe ni. Nashige tureshi da karfin karfina .

 

Mirginawa yayi hade da bude idanun sa yana adduar tashi daga bacci.

 

“Sissy.,.”

 

“Ya Mkay meye haka? Taya akai kana kwance a kasa ka dawo nan?”

 

Murmushi ya saki hade da cije qasan leben sa.

 

“Baki tuna komai ba?”

 

Ji wata tambaya marar kan gado dan Allah . Takaici yasa na shiga kokarin sauka kasa. Da sauri ya dago ni yanata nishi

 

“Ajiye ni ma na, Put me down ”

 

“Shut up ” Ya ban amsa cikin muryar umarni.

 

Har bandaki ya kai ni ya dire . Ya shiga haki yana bubbuga kirjin sa,

 

“Kai yan drama na kokari. Suyita rena mana hankali yadda suke daukar mata kaman jarirai ashe karyane mugun nauyi ne da ku. ”

 

Na yamusa fuska hade da juyawa wajen sink na shiga duba mouthwash dazan kuskura baki na.

 

“Ko baki ji me nace ba ne…”

 

“Naji mana, TubarkAllah. Kuma ai shisshigi ne tunda ba wanda yasa ku dauke mu ”

 

Murmishi naga yayi. Ya shigaa tahowa inda nake. Ja baya na dinga yi ina masa kallon ya ishe ka

 

“Wai meye haka Ya Mkay?”

 

Shiru yayi ya qi amsa ni. Gashi gadan yake nufo ni yana mai sakin wani munafukin murmushi .

 

“Wayyo. Ka bari…!!!”

 

“This is my home, I can go anywhere I want. Duk inda na ga dama tunda gida na ne.” Ya karashe cikin isa da iko.

 

Har bango muka kai ina mamakin rashin kunya irin tasa. Na runtse idanu na da dukkanin qarfi na.

 

Ina jiyo busar numfashin sa akan kofofin hanci na. Nide sam naki bude idanu na.

 

Mukhtar ya tsurawa Fateemah idanu tamkar zai hadiyeta saboda madaukakiyar kaunar da yake mata.

 

“Fateemah…. ”

 

Sam ban amsa shi ba sai ma sake matse jikina da nayi.

 

“Fateemah na, Mai sunan kakata, Sunan kanwata, Sunan cousin dina ga ki kin zama matata.  ”

 

“Ta wucen gaadi ba.  N”

 

Ban karasa ba ya sakar mun wata sumba agefen kumatu na

 

“Haba Y ..”

 

Ban rufe ba ya dora leben sa akan nawa. Na dan bude idanu na akan fuskar sa da idanun sa ke a lumshe.

 

“Yàaa”

 

Nanma ya sake kaiwa wata gefen wuyana.

 

“Ina qaunar ki Fateemah with all my life, My soul . I love you sooo much.”

 

Samu nayi na juyar da fuskata gefe. Bai ce komai ba ya kai hannun sa kan madannin fitilar dake saman kai na ya kunna ta. Take bandakin ko’ina ya gauraye da hasken lantarki.

 

“Matsoraciya dama ni fitila zan kunna fa.”

 

Nide ban ce masa komai ba , Ya gama neman fitinar sa ya matsa daga wajen. Sai dana bari ya kammala komai tukun sannan na kama ruwa na yo wanka na kuma dauro alwala.

 

Ko da na koma cikin daki ban tarar dashi ba. Don haka na isa wajen kofa kawai na murza mukulli. Sai dana tabbatar ta kullu tukun sannan na koma na tada sallah. Don tuni, Har an fara kiraye kirayen assalatu.

 

××××

 

 

Bayan na idar da sallar da nayi na kammala dukkanin addu’oin na. Dan kwantar da kai na nayi akan sallayar na kwanta. Nan take bacci yayi awun gaba da ni …

 

Ban farka ba sai da rana ta fito. Ta dallare ni ta window. Na tashi da addua a baki na.

 

Cire hijabin dana kudundune nayi na shiga cikin bandaki. Wanka nayo na tsane jiki na.

 

Na dubi kayana dake cikin akwati ina mai nazarin wanda zan saka. Bakina na cuno tunawa da ko lefe baa mun ba. Saboda ban kai matsayin ba

 

Na zura wata doguwar atamfa da mummy ta dinkamun a Lagos. Banyi wata kwalliya ba. Illa dai nabi lungu da saqo na shafe jikina da body mist din kamfanin yerwa incense and more na kuma shafa khurmah hade da shafa antiperspirant din ta. Wadda ke tsatstsafe gumin hamma ta, Ta kuma saka hammata qamshi. (08095215215)…

 

Man lebe na shafa akan baki na sai kwalli dana saka. Kai tsaye na wuce parlor. Kai na na fara zurawa kafin gangar jikina tabi bayana.

 

Hamdalah na saki ganin baya parlor . Ba kuma ya dinning. Sai kulolin abinci da notepad da akayi rubutu akan center table.

 

“Will be right back my dearest wife. Ga abinci nan kici. Love you ”

 

Kulolin na bude. Chips ne acikin jarida dake cikin food flask din, Sai miyaar hanta da soyayyen kwai . Gefe daya kuma shayi ne da yaji kayan tea sai qamshi yake.

 

Bansan sanda na matso da center table din gaba na ba. Na debi iya yadda zan iyaci. Da sauri nayi Bismillah na fara ci. Gaskia ba karya komai yayi dadi wallahi. Tas na cinye na gyatse hade da hamdala.

 

Na tattara komai na kai kitchen. Cikin wanke wanken da nake yowa na jiyo sallamar su shida muryar Mubeena dake biye dashi.

 

“Do you truly like her?”

 

“I loved her Mubeena. Haramun ne?”

 

“Bance haramun bane. But this is not fair. Soo not fair. Haba Mukhtar. Yar aiki zakayi auren sirri da ita? To ina matsayar aurenmu da kai.?”

 

“Ba sai nan da shekara daya ba? Ba sai kingama medical school ba? Na meye ba zanyi aure ba?”

 

Bansan sanda na barar da plate din da nake wankewa ba. Ji kake tararsattse ya fashe.

 

“Fate….”

 

Bai karasa ba na isa gabansa. Idanuwana suka kada sukayi jajir dasu. Cikin kololuwar baqin ciki da tsantsar takaici na dube shi. Yatsana na daga santar fuskar sa. Cikin fushi na ce dashi.

 

“Meye manufar aurena da kayi na tsawon wata 6. Okay dama wannan ne uzurin naka? …”

 

“Ke shi kike g…”

 

Na dubeta na watsa mata harara .

 

“Ban kai aya ba. Ba dake nake ba, Da shi nake dayasan abunda ya qulla. Wallahi nayi dana sanin amincewar da nayi na aure ka. Nayi dana sanin yarjewar ka danayi na dauka kai din mai gaskia ne. Nayi dana sanin shigowa ta MASARAUTA. Anci amanata, an batamun rayuw..”

 

Ban karasa ba ya riko hannayena yana kokarin jefa idanun sa cikin nawa.

 

“Wallahi ba yaudarar ki nayi ba, I married you for love not because of other reasons . I loved you at first sight . W….”

 

Tattakewa nayi na ture hannun sa daga jiki na. Jikina har kyarma yake saboda tsabar zuciya.

 

“Karka kuskura ka karasa, Macuci, Maha’inci, Maci ama…..”

 

Ban karasa ba ya sake zaburowa. Ya riqeni ga gam ajikin sa. Sai mutsu mutsu nake , Ina janye shi daga jikina amma ko gezau beyi ba.

 

Gashi ita kuma Mubeenan sai riqo shi take ta baya.

 

“Dan Allah ka kyaleta Ya Mkay. Ni tun farko da ka bi ta shawara ta ba zaka auro ta…”

 

Cikin zafin nama na yakice hannuwan sa daga jikina.

 

“Cika ni Mukhtar, cika ni..” Sosai na shiga yakice hannuwan sa. Hawaye se yar tsere suke a fuska ta.

 

“Mubeena kike kowa? I’m not petty being. Ki denamun kallon lowclass. Wannan har miji ne? “Fada nake sosai ina daga hannuwana setin sa.

 

Sosai ta shiga zagi na, Tana gasamun maganganu. Nayi kanta Mukhtar ya hanani ta hanyar janyo ni ya rungume.

 

“Cika ni, Sakar ni… Ka kya…”

 

Rufe bakina yayi da wata iriyar sumba mai ratsa magudanar jini da tsoka. Duk wata jijiya ta jikina mai karamun kuzari sai data saki. Duk wani kwari da bakina ya samu sai daya kashemun. Na tsinci kai na cikin hawaye. Hawayen dana rasa dalilin zubar su.

 

Mubeena dake kallon sa gaho a tsaye , Yatsa a baki taja tsaki tana wurga musu harara. Kafin cikin takaici da kololuwar bacin rai ta fuce da sauri tana jera tagwayen tsaki…….

 

 

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!