Gidan Gandu Hausa Novel Complete

Hotunan Soyayya da Kalaman Soyayya

Gidan Gandu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

……………..Gidan gandu,gidane daya kunshi mutane fiye da 300 a muhalli daya banda wanda sukayi aure wasu suka tafi cirani wasu kuma tantirancin su ya hanasu zaman gida,tunda ga baki kofar gidan mutum yasan wane irin gidane saboda yawan kofofinsa tun daga kan kakanni,iyaye,jikoki,tattaba kunne da saurensu.

***** ****** ******

 

______lokacin safiyace dan baifi 9:30am na safenba,gidaje a kowa yana kokarin aikin gabansa inda masu himma kam yayansu sun dade da tafiya makaranta,maza kuwa wasu sun tafi gona.

Shiru cikin gidan kakeji babu wata hayaniya kowa yatafi harkarsa,bayan yasamu abinda ya sawwaka ya zuba a cikinsa,sai iya kofar kawu shehu wanda dama su kullum cikin fada suke,da inna larai da kuma inna karima.Dakin yan matan gidan ma bakowa sai wata matashiyar budurwa a kwance tana zuba bacci kaman ba gobe,ta dade batayi motsiba can kuma sai ta yi wata mika irin ta wanda ya more da baccinnan,gyara zamanta tayi a bakin katifar tata tana bubbuga kai da kuma jan majina da irin kaman mutum ya shaki kura,

“Kai shiyasa dadina da BURGU yasan DULAH (wiwi),mai kyau yanzu mutum zaiji shi a caji,duk wata gajiyarka saikaji ta tafi,inda ana samun mai kyau haka yaushe mutum zaice yayi asarar kudinsa kuma ai…………”

Katsewa tayi da zancen nata jin wayar ta irin yan nokia dinnan ta dau kara ta cika dakin,juyawa tayi tana yatsina fuska ta dauki wayar kafin ta saka a kunnenta,

“Menene??”

Shine abinda tace tana daga kiran,sai kuma tayi shiru danjin maganar da ake a daya bangaren,

“Hmm indai kaji kira a wajen alhaji sama’ila toh siyasah ce ta kariso yana so ayi masa aiki,toh wallahi kaji na fadamaka inhar ya hau kujerar nan yamanta da mu,to sai yayi dayasanin sanina a cikin rayuwarsa,dan saina masa abinda har ya mutu bazai mantaba,kuma kasan zan aikata,dan haka yanzu ka fada masa,inya amince kazo kadaukeni mutafi a san abin yi,yanzu dama nake maganar ka dan naji dadin dular jiyannan akwai caji baaaba,…………shikenan kazo ka daukeni sannan kace arnan yara su shirya ganinan zuwa yanzunnan”

Fitowa tayi a dakin tana wani garwaya hanya irin na iya shegennan can kuma sai ta dauki bokati dama da ruwa aciki da alama wani ne ya ajiye,

“Keee SAMEEMAH ruwa na ne na ajiye”

Juyawa tayi tana kallon mai maganar cikin daga ido,

“Toh so what dan nakine,ajiyewa zanyi dan naki ne,inkuma kinga a tawani sako na kwakwaiwarki ya nuna miki ina tsoronki ta kizo ki karba,kin manta ina da labarin guntun sabuluna da kikayi wanka dashi?koh an gaya miki bansaniba,dan dai munayin hankali ne kullum shiyasa muke barin koh ta kwana”

“Iyyyeee Ku zo ku jimin wata magana wai sameemah ceh tayi hankali,da kuwa anyi ruwan farin ciki a garinnan,kuma narantse kika shiga wanka da ruwannan saina miki abinda yafi na ruwana,dannima inada wajen zuwa da safennan”

“Keh sameerah ya isheki haka,maida min maganar inbaso kike daga ke har mazinacin bazawarinnaki dazaki wajen sa na juya rayuwarku ba,kuma inkin fasa daukar matakin banza shashasha”

“Kai lallai ma yarinyar nan,a haifeki a gaban mutane amma ki dunga yiwa mutum maganar da uwarsa bata isa yimasa ,shegiya yar daba kawai”

“Hhhhhhh gwanda dakika fadi abinda yake bakinki amma bari na fito nasameki a cikin gidannan yau wallahi mai rabani da ke koh…………..hmmm”

Sauri sameerah tayi tabar wajen dan yanda taga ran sameemah yabaci ba abinda bazata iya mata ba ,na rashin mutunci,takaicinta daya ma,yarinya karama ta takura musu ta addabesu,gashi sunyi waya da bazawarinta Saminu,yace zaizo yadauketa su tafi bikin abokinsa a Kaduna tana ta murna,yanzu tasan dole saidai ta tafi ba wanka, saboda gudun haduwarsu da sameemah a yau,dan tasan in ba hucewa tayiba,tsab zata aikata abinda tace.

Bata dade ba a bandakin ta fito,har yanzu fuskar ta ba fara’a saboda sabanin dasukayi da yayarta sameerah dazu wanda suke uba daya su da itah,dakinnasu ta shige ta nufi hanyar wajen kayanta,dan daki kawai suka hada da yan matan gidan amma kowa shirginsa daban ,gwanda su wani lokacin in wata tayi samuwa ana zama a ci ana dariya da yada zance,amma sameemah in ta shigo da abu a gabansu zata cinye in ya isheta ta bawa karanta BINGO.

Mayuka ta fitar lotion masu gyara fata ta mulke jikinta kafin ta dauko wasu kaya na saki irin na farauta amma anyi musu dikin irin na mata riga da wando.

Bayan ta gama saka kayanne kuma aka shafa hoda kafin aka dauko bakin jambaki wuluk ta shafe karamin bakinta dashi ,ga kuma kwalli da tayi masa saku kasa da sama,dan saida girar ta kusa hadewa da saman ido,juyi tayi a gaban madubinta kafin ta dauki gyalen ta nadeshi a kafada ta fito daga dakin.

A bakin hanyar fitarta daga dakin suka ci karo da wani dan anguwarsu yana rataye da yar gidan inna larai a kafadarsa,yarinyar sai kuka take bazata wuce shekara bakwai ba,Sameemah ce ta fara ganinsa tareda Tambayar “lafiya”

“Ahah seemah jar wuyah(haka kowa ke kiran sameemah a waje)wallahi a hanyar shagon ilu naganta a kwance jini yana binta hine dana tambayeta tacemin wai Labiru ne abokin yayanta Manu yayi mata haka”

“Ayyah Toh sannunka da kokari zaka iyah tafiya”

Bayan ya tafine sameemah ta dauki yarinyar tayi kofar su inna larai din da ita,

“Inna larai! inna larai!! Inna larai!!!”

Suna cikin habaici kowa yana kofar dakinsa ita da inna karima,sai ta zuyo tareda cewa,

“Ke miyene kike ta jundumamin kira kaman zaki cinyeni”

“Iyyeh hakanee abin(sameemah ta fada tana ajiye hanifan a gababan inna larai) toh gashinan,yar tatsitsiyar yar kice wani gardin ya fardeta ,kona ce yabudeta a ledarta,saiki zo ki dundumata da ruwan zafi ba masifa zaki tsaya yiba,itama alamu kwadayinnata ya kaita ta shiga sahu tun lokacin ta ba yiba”

“Lallai sameemah abinda zakice ma kenan,wanne dan tsinanniyar ne wannan?”

“Waye kuwa banda Labiru abokin danki Manu,bake kike manna masa itaba dan kinga yana siya mata shayi da safe,bakuda aiki sai kwadayin tsiya,saiki dundumata ta samu ta ware,ko tayi harkar da kwarin jiki,ni na tafi inna dawo da kaza na dan bata,kota maida jinin da yazuba,in kuma nima bandawo ba tacan tacan,ga wannan kisaya mata ibrofen saboda zafin jiki(tafada tana mikawa inna larai din naira hamsin).

Wani wawan tsalle inna larai din tayi tareda buge kudin dayake hannun sameemah,kafin tabita da wani ashar mai dumi.

Inna karima kuwa tana gefe tana zuba uwar dariya kamar makogaranta zai fito dan mugunta,komawa kanta zagin yayi,cikin haushi inna larai tayi kanta suka rukume da fada,tana zaginta tana kururuwa kan gari ya gari.

Ganin mutanen gidan sun fara sanin abinda yafarune,yasa sameemah zagewa ta fice daga gidan.

Tana fita ta samu Burgu a kan mashin yana jiranta,burgu yana ganin ta fito ya tada mashindin yafara diri,dalewa tayi suka fara tafiya,yana bata labarin yanda sukayi da alhaji Sama’ila,duk zancen dayakeyi bata kulashi ba saima umarni da ta bashi cikin karamar magana,

“Ka saka su dodon dawa su kama Labiru dan malam sule,su kaimin shi gidan karangiya,su dan tabashi kafin naje wanjansa gobe”

“Shugaba reza mai yayi haka?”

“Bai shafeka ba kayi yanda nace kawai”

“Wai yau labiru yaga ta kansa tabbbb”

Da haka har suka isa gidan kungiyar tasu burgu bai sake cewa komai ba saboda yaga yanda shugabar ta murtuke fauska.

Gidane da akayi wajen da langa langa saikuma,dakuna na bulo guda biyu da kuma dakuma dan tsakar gida.

Babu KO sallama haka suka saka kai ,inda kowa yatashi yana yi mata barka da isowa,dakin dayake farko ta shiga,tareda hakimcewa akan wata kujera wadda aka saka tebur a gabanta,sukuma suka zauna a sauran kujerun dakin,

“Uhm uhm,kaman yanda kuka sani wannan kungiya ta kafu bada iya taimakona ba harda naku,sannan muna abune bisa tsari,in munyi abu saida dalili toh dan haka,ba mason katsalandan da yan sanda,alhaji Sama’ila yaba mu aikin ragamar siyasarsa,dan haka zamuje yau ,amma iya mutum shidane zasu biyomu sauran nasaka burgu yabaku aiki,shi zai fadamuku mai na sakashi yasa ku aiwatar kuma kunsan banason ganganci,dan haka k kula,kai kuma ASUSU,(tafada tana nuna wani dan saurayi a gefen burgun a zaune),nawa muke dashi acikin bankinmu na kungiya?”

“Eh shugaba iyah dubu talatinne”

“Toh kabawa dodon dawa dubu goma yah,yasayo mana suyar kaji da lemo,sannan kuma ka tambayi burgu inda ake saida dulah mai caji ka sayo mana,dan wacce ka kawo wancan sati ta asarar kudi ce kawai,inna dawo daga wajen alhaji Sama’ila akwai shagali”

Ihu wajen kowa yadauka mai feduwa sunayi,

“Sai ogah kina abinda kika so,sai shugabar gidan gandu,da girman kujerarki,sai reza ki yanki wanda yasayeki idan ya kuskuren rikeki ba dadaiba,kuma dole ya gyara yayi aiki da ke,ehhhhhhooooool”

“Toh ya isa haka maza ayi haramar fita aiki kuma”

Kowa tashi yayi inda masu kamo labiru suka tafi bayan burgu yayi musu bayani,sannan masubin shugaba seemah jar wuyah kuma suka bita a baya da mashinan su,sai gidan alhaji Sama’ila.

 

Toh farkon farawa kenan a cikin littafin gidan gandu,daga taskar sady-sakhna,kuci gaba da bibiyar littafin da sannu zamu nishadantar daku yanda yakamata inshaallah,nagoda ga duk daukacin masoyan wannan littafin.

 

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

 

Kar ku manta da

 

#comment

#share

#like

#follow.

 

____** *GIDAN GANDU* **____

❤❤By sadi-sakhana❤❤

 

 

Wattpad username:SAKHNA03

 

 

❤02❤

 

Labirune a zaune shida abokansa suna shan rake a baki rafi,kai kace ba abinda ya aikata hankalinsa kwance kaman tsumma a cikin randa,yana cikin zance sai waigawa kawai yayi yaga bakowa a gefensa kamar dama ba zaune suke shida mutane ba,tun kafin yayi magana yaji an toshe masa baki,yayinda wani duka ya jiyarci keyar sa ta baya,daga nan bai sake jin komai ba sai duhi daya lullube ganin sa.

Sun gumarsa sukayi suka sabashi a bayan mashin din daya daga cikinsu sai gidan karangiya.

Zefashi sukayi a kasa kaman kayan wanki yayinda daya daga cikinsu yace,

“Kai baaaba yanzun zamu dabashi kaman yanda shugaba reza tace kokuma kawai mubarshi ta ji dashi”

“Haha nayi dakon kawoshi a banza wallahi saina dan tabashi,dama inajin haushinsa sani ne bakayi ba,shine fah wanda yayi shunemu a wajen yan sanda lokacin da muka sato akuyar hajiya delu zamu babbake mu maida maiko,kasani ai dakyar muka sha,badan shugaba jar wuyah tananan ba da tuni sun tara mana jini da majina”

“Gaskiyarka arnan mazaje,dole mudan mauleshi koh kadanne,dan babu abinda na tsana kaman masu bakaken kayannan(yan sanda) yan banza saikaace cinnaku”

Dariyar yan daba suka sa baki dayansu kafin daya daga cikinsu yasamu daidai duwawun labiru ya narka masa sandar hannunsa,wani wawiyar zabura yayi ya mike yana rarraba ido akan kowane dayansu.

Daya daga cikonsu ne wanda shine ya daki labirun da alama shine shugaba idon sa ya dau kwalli kaman tsohon dan farauta,

“Heeege gama karemu da kallo yau uwarka zaka ci a wajennan dan ma bamusan mai kayi ba,amma tunda ka tabo shugaba yau kataryarka sai tayi jawur a wajen mu”

Yana gama magana ya hau tabkar labiru kaman an aikoshi wajensa.

Saida sukayi masa lilis kafin suka barshi yashe a wajen tareda rufo kofar suka bar wajen.

Basu wane dade su sameemah suna tafiya a hanyaba suka iso gidan alhaji Sama’ila,gidane sannane kowa yasanshi saboda siyasarshi,a bakin kofar get din gidan suka yi parking din mashinansu kafin suka tunkari mai gadin wanda yake zaune akan benci yana jin radio,burgune yafara masa magana cikin gadara,

“Kai dattijo maza shiga gidan ka sanar da mai gidan isowar mu”

Bai ce komai ba sai tashi da yayi ya shiga gidan dan aiwatar da abinda suka sakashi saboda tsira da mutuncinsa,bai dade da shiga kuwa ba saigashi yafito,

“Eh na Shaida masa isowarku yace kushiga daga ciki”

“Shikenan dattijo godiya muke”

A parlorn baki suka sameshi ya baje akan kujera tareda ware cinyoyi yana shan iska,saboda kibar da yayi irin ta yan siyasa,washe bakin nan yayi yana musu barka da zuwa.

Sameemah ceh ta kalleshi tana yatsine fuska bayan ta zauna akan kujerar daya daga cin parlorn,dora kafa daya kan daya tayi kafin tace,

“Kafin a fara komai alhaji hada wannan cinyoyinnaka waje daya tukunna,dan banji dadin zama ba da ganin yanda ka wani ware kafafu kaman mai jiran kaciya ta biyu”

Cikin kunya da kuma dariya irin ta yan duniya ya hade kafafunsa waje daya amma da gani baiji dadin yanda sameemah ta disga shiba a gaban yaranta,saidai babu yanda zaiyi tunda shiyake nema a wajensu.

Maganar abinda yatarasu suka farayi gameda campaign daya ke so suyi masa na mutane,Musamman matasa na birni da kauye,sameemah ceh tayi saurin katseshi tareda cewa,

“Dakata harda kauye kakeson muyi maka ko iya cikin gari,sannan kanason mukula da ta bangaren yan sanda ko kuma ba ruwanmu dasu?”

“Eh kowanne nakeso ayi nidai kawai na samu na hau zabennan shikenan burina yacika”

“Toh sharadinka shine;zaka bada rabin kudi yanzu sauran rabi kuma saika hau zabe,amma idan ka hau zabe ka manta da mu,toh kasani sanda ka sauka a mulki saidai kanemi wani garin ba dai nan ba,dan bana barin bashi ko ranka zaka sayar saika biyani kudina bai dameni ba,sannan idan wani yarona ya shiga hannun hukuma kai ke da alhakin fito dashi ,idan ka yarda da sharruda na,kayiwa burgu magana zai kawo maka takardar saka hannu”

Gilas ta fitar daga jin jakarta ta toshe fuskarta kana ta mike tsaye har ta juya zata fita can kuma ta dawo,

“Am karka manta,inada lawyer wanda ba’a siyansa da kudi,karkayi kokarin wani kuskure,dan ni ba irin sauran yan dabar bane,ku tashi mutafi yara”

Kowa mikewa yayi kaman dama umarninta suke jira,sun zo dadai kofar fitane suka hadu da wani gogygyen dan siyasa da alama yafi alhaji Sama’ila ma matsayi a siyasar.

Tsayawa yayi kaman wani gunki ya tsare sameemah da ido wanda ta bashi hanya tun dazu ya wuce,ganin shiru kaman bashida alamar wucewa ne yasata dagowa dan ganin mai yake kallo haka,wani dan isakan kashe mata ido yayi tareda lashe baki irin na yan duniyar nan,dayake itama shugaba ce a wajen cikin sakanni ta gano mai yake nufi,take kuwa ta mayar masa da martani ta hanyar daga masa girarta ta hagun,

“Kibani numberki idan bazaki damu ba mana”

Ba wani bata lokaci tafara karanto masa yaronsa yana copy akan wayar datake hannunsa,saida suka gama yace,

“Banjin sunan zazzakar kazar ba?”

“In min hadu zakaji abinda yafi suna ma”

“Shikenan idan kinshirya zamuyi waya ”

Bata sake cemasa komai ba tafice daga cikin parlorn.

Bayan sun gaisane shida alhaji Sama’ila,sai yayi shiru kaman mai tunani yana ta murmushi shikadai,alhaji Sama’ila ne yakatseshi ta hanyar cewa,

“Amma alhaji BALA naji dadai kuwa harkar da kuka kulla kaida seemah jar wuyah”

“Au Ashe kajimu,gaskiya na samu dami a akala dan dagani zatayi dadin harka sosai”

“Hmm alhaji bala kenan,anya kuwa kadauki dami mai kyau kuwa,karfah ka dauki dan maciji ina……..,..”

“Kai kai alhaji Sama’ila menene kuma na wannan maganar,babu abinda yafaru kabar ma wannan zancen muyi abinda yakawo mu kawai”.

A wajen fita waje kuwa bayan sun zo hawa mashin,burgune yakalli sameemah da Mamaki abinda yafaru,

“Amma shugaba maganar da kukayi keda wannan alhajin anya ba matsala kuwa”

“Me nake Tunani,ka fara mantani ne,gaskiya yakamata ma na fara sabon aiki dan ina ganin nayi laushi dayawa tunda har kuke min wannan kallon kaman kuna gaban kannenku mata na gida”

Basu sake cewa komai ba sai burka mashinansu dasukayi kowa ya dale,dan da alamar sun jiyo gargadi da kuma fushi a cikin muryar tata.

Acikin gidan gandu kuwa tun safe ake abu daya har rana ta fara zafi lokacin daura abinci amma babu alamar zasu daina hayaniyar dasukeyi.

Inna larai kuwa tun ana jiyo muryarta da karfi harta fara dushewa saboda masifah,kawu shehu ne yayi sallama ya dawo daga gona,tun daga wajen kofar gida yakejin masifar da akeyi wanda inda sabo yariga ya saba,saidai daya shigo gidanne yakula da kofar tasa cike take da mutane kaman ana rabon kudi,karo sukayi da baba umaru (baban su sameemah)wanda shikuma gadin makarantar primary anguwar yake wanda antashi kenan ya dawo gidan,

“Ahah shehu yadai kana kallon gaban ka kuwa?”.a kokuma maganin abinda yafaru?,ai kin fi kowa dabbanci da irin wannan kwakwalwar taki,baku da aiki sai shege kishi da fada,shi kadai kuka iya kawai”

Baba umarune ya rike kawu shehu wanda yake ta zazzagawa larai masifa saboda tsabar ransa yabaci,daki ya wuce yadauko yarinyar wanda jikinta yayi zafi rau saboda Zazzabin daya hau Jikinta.

A hanyar fita suka hadu da mazan gidan guda biyu,da Sule dakuma Bashari wanda dukkansu yayan baba umaru ne,

“Yawwa kai sule bi bayan kawunka shehu ku tafi asibiti ,kai kuma bashari zo mu tafi wajen yan sanda”

Hakan kuwa akayi kawu shehu suka tafi asibiti,wanda ganin zasu tafi yasa inna larai dauko gyalenta tabiyo su har waje,saida baba umaru yasaka baki kafin kawu shehu yabar ta bisu asibitin,saida tayi ta rusa musu ihu tukunna aka barta ta tari mashin tabi bayansu.

A wajen su baba umaru kuwa,saida suka bi layi tukunna suka samu layin yazo kansu,dan sandanne yakalli su baba umaru amma idon sa yafi tsayawa akan bashari da alama yaganeshi,

“Malam muna tsaye amma bakace mana komai ba”

“Eh ina jinka menene yake tafe daku”

Saida suka tsara masa, abinda yake faruwa tas kafin ya yamutsa guska yace,

“Hakikanin gaskiya babu inda zamuje kamo wani dan ya taba wani mutum a gidan gandu,saboda kuma da wani a cikin gidanne ya aikata mukaje kamoshi da kyar zaku bari dan sandan yafito da ransa in ya fito ma to saikun sanja masa kamanni kuwa.

Toh fah yadai gidan gandu??

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published.