Gidan mata hudu hausa novels

Gidan mata hudu hausa novels

 

 

 

 

 

 

 

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

[Page = 1-5

Kyawawan Mata ne Zaune a katafaren gidan Kowacce Fuskarta ba Annuri sai kallon kallo sukewa junansu

Murjanatu itace tafisu zazzafan kyau wanda inka kalleta saika dauka balarabiya ce gata fara qal tamkar Tsada ba digon baki ajikinta saina tsakiyar kwayar idonta.

Murjanatu ce kadai fuskarta babu Rashin Annuri akasarin ta sauran matan da kowacce ta hade ranta zuciyoyinsu na musu ciwo na irin cin mutuncin da Mijinnasu yagama yi musu yanzun minti biyar data wuce

Zaman jiran tsammaninsa suke yana cikin Dakinsa yana waya da mahaifiyarsa yana jiran ta cewarta inta bada umarnin korarsu ya basu red card kawai

Ita murjanatu Babu abinda yake damunta dan ita kome Irfan zaiyi mata baya ɗaɗata da ƙasa sbd ita macece mara zcy kuma bata fushi ko kadan sannan Irfan shike sonta dama ba ita ke sonsa ba atun farkon tafiyarsu

Idon murjanatu yana kan fuskar Kishiyarta me bi mata ta uku kenan wato Nuratu da ake kira da Nurr wacce ita kuma Nurr din ta É“ata fuska ko kallon arziki bataiwa Murjanatun ba sbd yanda ta tsaneta ita kuma Murjanatu mugun Son Nurr takeyi

Kusa da Nurr Amaryace Laila wacce batafi Wata Uku da zuwanta gidan ba idonta yayi jajir tasha kuka ta godewa Allah domin kusan duk akanta ake wannan ballin itace silar komai,dalilinta yau hankalin mutan gidan ya tashi.

Laila nata goge hawaye tana mai nadamar Auren Irfan yaro da kudi wanda itace ta siyawa kanta komai sai gashi ba’aje koina ba tafara Nadamar Shigowa gidan Qalbinta Irfan

Zinariya itace Uwar gidan Irfan yaro da Kudi wanda take zaune kusada Laila ta tsikara É—aurin kallabinta zuwa gaban goshinta kadan take jira tayi masifa.

See also  Mu gani a kasa Hausa Novel Complete

Nurr Ta dago idonta takalli Murjanatu ta galla mata harara

Murjanatu ta kashe mata idanu tana murmusawa hankalinta kwance fuskata ba tashin hankali

Kowacce saida gabanta ya fadi ganin fitowar Irfan a sukwane fuskarsa ba fara’a

ya tsaya atsakiyarsu yana kallon kowacce cikin isa da gadara kana ya fara da uwar gida Zinaru da akewa laÆ™abi da Zinariya yace mata ” Zinariya kinfi kowa sanin halina gaba da baya amma kina kallo aka karya doka ta ackn gidannan,zinariya kinfi kowa sanin koni wanene idan Raina ya baci bana ragayya amma kema kika biyewa wadannan karnukan matan….. “Kai dakata bajakade!!! kalleni ka kara kallo niba karya bace Da gatana da darajata kuma walh inka kara cemin karya sainace Maka ‘yar gajera ce Karya…. “Ke me kike nufi?Rashin kunya zakiyimin? Wacece gajerar,? 😂😂uwarsa take nufi fans

Murjanatu ta gatsina masa baki tace “Oho maka!!shafa kaji!! nidai na fada bakuma zanji tsoron kara fada ba walh,indai aka sake aibatani saina gayawa mutum wacce tafi wannan ciwo…. ya kawo hannu cikin fusata zai mareta ta kauce cikin azama da zafin namanta tayi baya

ya daki iska

ya nunata da yatsa “JANA Kishiga hankalinki ke kadaice cikin matana kike min tijara irinta ‘yan bariki…walh koki gyara kokuma kiringa cin duka..

da gatsali murjanatu tace “yo da Auran me mukai?inba Auren bariki ba Antaba yin Aure mace ta Aurar da É—anta inba agidanku ba,ace ayi mutum bashida Uba bare Dangin Uba….😏😏 mmtttss Aikin banza kawai..

zuciyarsa ta kawo iya wuya yayi kanta ya shaqota sbd ta tabo masa inda yake masa ciwo a Kullum,tabbas Jana ita kadaice tafi yi masa gorin Uba a duniyar Allah Ta’ala dan haka yau me kwatarta sai Allah

See also  Yar Goni Hausa Novel Complete

kowacce ta tsorata dashi ganin yanda yake dukan Jana a ciki ya matseta a jikin bango yana naushinta

ita kuma sai ihun nemon ceto takeyi tun tana zaginsa bakinta yaqi mutuwa har taxo tana cewa “wayyo nashiga uku zai kasheni ku kawon É—auki.

Kowacce tsoronsa take dan idan ransa ya É“aci baya ragawa kowa agidan, babu wacce batasan halinsa ba sun san FaÉ—an nasa zai iya juyewa kansu inhar sukaje ceto dan haka kowaccce saita juyar da kanta tana hasaso nata hukuncin idan ya gama da Jana.

gaban Nurr yaringa bugawa Fat!fat!fat tanajin Tausayin Jana kodon yanda take bata kulawa ackn gidan duk da tasan ba kulawar Allah da Annabi bace tunda Jana dai batada hali mai kyau tana taɓa Maɗigo lezz shiyasa Nurr ke baya baya da shiga sabgarta yawan tabata da takeyi yana ci mata tuwo Akwarya duk da bata dauki hakan a wata manufa ba

ji take kamar ta tashi taje ta ceto ta amma tana jin mugun tsoron abinda zaije ya dawo saita kara yin lif akan Kujerar datake kai

Zinariya ce tayi namijin Kokarin zuwa ta fusgo Murjanatu ta fado jikinta tana kuka tana xagin Irfan

Tunkude irfan zinariya tayi tana fadin “haba MAN ka kyaleta mana waikai wane irin mugune, baka da Aiki sai bugun mata,wai me mata sukai maka ne kake cin Zarafinsu haka? gaskiya sai Allah yasakawa mata akanka MAN.ko so kake ka kasheta inkyaleka.?

Irfan ya kalleta da jajayen idanuwansa yace “Gara na kasheta na huta da wannan gorin da takemin walh sainayi maganin duk dan iskan da zai ringa wurgomin irin wannan lafaxin daya futo daga bakinta dan bazan dauki raini ba walh.

See also  Zafin So Hausa Novel Complete

Murjanatu ta zame jikinta tayi dakinta tana fadin ita yau saita bar masa gida ta gaji da halinsa

Nurr ta tashi ahankali tabi bayan Murjanatu sbd ta rarrasheta bazata bari ta fita a wannan daren ba Tana ‘ya mace Allah sarki Nurr ciwon ‘Ya mace na ‘ya mace ne dama😁

Murjanatu tana kuka tana hada kayanta a Trolley tabbas dama ba harga zcyrta ta Auri Irfan ba Asiri yayi mata ita akwai wanda take so har yanzun dole ce ta kawota gidan Irfan gidan Masifa,a kullum nadamar saninsa takeyi

jin anshigo dakin nata yasa ta dago a sanyaye takalli me shigowar

Nurr ta rakuɓe ajikin Kofa bayan tashigo takurawa Murjanatu idanu tana mai tausaya mata sbd itakam Nurr akwai Raunin Zcy ga tausayi ga sauri Kuka

wani sanyi taji azcyrta ganin Nur namata kallon tausayawa dan haka saita langwabe tana marairaice fuska tace “Nurr kema kin tausayawa min ko? Nasani!Walh nasan bani kadai nake kaunar ki ba Nurr Kema kina sona kawai kin kasa sakin jiki ki nunaminne sbd matan Gidan nan.

Nurr dai batace komai ba saikallonta da takeyi

Jana ta matso kusa da Nurr ta kamo hannunta ta zaunarta akan Makeken gadon dakin tahau fadin “My Nurr Kalli jikina duk ya farfashe, walh MAN mugune, Allah ya isana bazan yafe masa ba,Walh nayi nadamar Aurensa Allah ya tsine…. Da sauri Nurr ta rufe mata baki tana fadin “Haba Aunty Jana mijin kine fa,ba kyau Zagin miji,plz kiyi hkr kada ki kara magana kibarwa Allah komai kuma kema ai da laifinki Rashin kunya fa kike masa haba Aunty Jana.]

KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇👇👇

​

 

Preview: [DOWNLOAD COMPLETE BOOK 👇]
 

Name: Gidan Mata Hudu Hausa Novels
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: MYNOVELS.COM.NG
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books
Groups/Writers: Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: July, 2021

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top