Hausa Novels

Gidan Zawarawa Hausa Novel Complete

Gidan Zawarawa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ga masu buƙatar na tallata masu hajar su kasuwancin su ta online zasu biya 2k

 

 

 

_BHUZUWA EMPIRE_

_Alhmdllh duk kan Godiya ya tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, alhmdllh allhmdllh ina kuke Matan Aure masu fuskantar matsaloli a gidajen Auren su?. Maza halarto taskar BHUZUWA EMPIRE domin warware maki duk kan wani matsalarki, gyaran Aure albarkacin fiyayyyen halitta da yardan Allah zakiga chanji an yi anga haske anga sauyi…. Sirrikar mallaka tare dana farin jini mu ke bayarwa…. Domin samun cikakkan ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan numbern 09061466409._

 

 

 

*”GIDAN ZAWARAWA Ga mai buƙatar cigaban labarin zai turo 300 normal payment,vip 500, Spc payment 1k. Zaku turo MTN card ta wannan number 08081202932… ko ta ku tura ta wannan account ɗin… 6037312299 mohammed Aisha Keystone.*

 

 

Zakuna iya magana da marubuciyar ta wannan link ɗin👇🏻.

https://wa.me/message/75RF7QJ2LYGXP1

 

 

*Bismillahir rahmanur Raheem*

 

 

“Magana nake daku ku duka ku fito daga waje na ganku ku, kuma ku ganni… Na gaji Uwale wlh ki san yanda zaki yi da wa’anan Ƴaƴan naki, ba zai yiwu ba, bazan iya cigaba da ajiye riɗa² n balagaggun mata harda ƴan shekara kusan Arba’in a gida na ba… Su kusan bakwai haba….

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Ya isa Malam, nace ya isa don Allah, ai wlh dawowar yaran nan namu a matsayin zawarawa alheri ne gare mu matuƙa, kuma ni ban taɓa baƙin ciki da hakan kaman yanda kai kake iƙirarin kullum kai kana yi ba. Me suke tsinta a gidan Auren banda uƙuban Ƴaƴa maza!! Ahir wlh kar ka ƙara bin mun ƴaƴana da bugun baki, nan nan fa Malam bala kalli yanda Zulai ta koma kaman ba ita ba, tun da tabar wannan ƙadararran Auren nata… Mama Uwale ta ƙarke magana tana gyara tsayuwarta haɗi da doran hannun ta saman ƙugun ta, tana sauke numfashi da nurfamfashi kaman wacce tayi tseren gudu… Nan ko tsaban tuno da wahalar da Zawarawan ƴaƴan nata suka sha ne a gidan mazajen su yasa ta yin hakan”.

 

Aa Uwale wannan ba dai dai bane ba, uhm uhm Uwale??. Malam Baala yayi mgn yana kallon mama uwale Da take aikin kumburin wuya.

 

Ganin bata basa amsa bane yasa shi cigaba da cewa ” Uwale ki tattara ƴaƴan nan duka ki mai dasu ɗakunn mazajen su, idan kuma ba haka…. Sai ya girgiza kai yana cigaba da cewa” kina jin sunan gidan a bakin mutanen unguwa, kar azo mana wani sharrin na dabam.

 

 

Ho_ho_ho ni Jikan Auwalu salisu, balki da barmani !! Kai malam Tom tsoron wa nake ji A wannan ƙasƙantacciyar unguwan ? Sun daɗe basu yi damu ba, wanda ya fasa jabbara_uban shi,nace Uban wanda ya fasa mutum idan ya isa ya tare ni face to face in yi maka ta ƴan boko, su tare ni fuska da fuska nace malam Bala…..

 

 

Inalillahi wainaillaihir rajiun… Yiiiii.. Yiiiii wayyo ni Rabi ni Alhaji zai yaudara? Yiiiii… Ihun Rabi ya katse su daga jain jan da suke yi…. Salati Malam ya hau yi a zuciyarsa yana faɗin na shiga uku.

 

Da Sauri Mama Uwale ta kalli Rabi da ta iso inda suke kamun tace” Ke Rabi mene? Me ya faru haka kk shigo mun da kuka kaman wanda aka ce maki Uwale da Bala sun mutu??.

 

Hannu Rabi tasa tana sharce hawayen fuskanta haɗi da sharce majina tana faɗin Mama Alhaji ya sake ni!!.

 

Kawai sai ta kuma rushewa da kuka.

 

Wani dogon tsaki Mama Uwale taja cike da rashin damuwa tace” Tom sai mene?. Alhaji dai alhaji dai na gidan malam bala, gidan nan dai da gidan Ubanki da ake ɗorawa a rana sau ɗaya sun fi wannan gidan da ake kwana da Kwanaki ba a ɗaura sanwa ba, shi dai Wannan yaro ya sakeki.

 

To ai Alhmdllh abun da zamu yi kenan … Rabi shiga ɗaki yanzu ne zaki fara hamdala ga Allah da ya raba ki da wannan ƙajagan… Kema ki zama Ƴar gari irin yanda sauran ƴan uwanki suke, ku samo irin gitattun firgitattun mazan nan kaman Larabawa.

 

Jin haka yasa Rabi ta nufi Ɗakin Mama Uwale sum² tana shigewa .

 

Uwale wannan wacce irin rayuwa ce kika zaɓa mawa kanki da rayuwar ƴaƴanki? Shifa Aure ba ruwan ki da talaka ko mai kuɗi duka Allah yayi su… Malam malam?? Don Allah kaje abun ka, kai ne kake da wannan taƙawan, amma a yanzu tuni an bar wannan yayin fatawa da taƙawan naka… Idan yarinya ta Auri mai kuɗi to gadan arziƙinnan zasu yi har Ƴaƴa da jikoki , haka idan ta auri talaka zasu yi ta gadon talauci don haka ni wanga batu naka ba zan taɓa ɗaukarta ba… Kaga ma tafiyata….

 

 

Juyawa tayi tana barin malam bala da baki buɗe ta shige madafi. Duk da haka Malam cewa yake yi ” Haba wa Uwani sai kace ba Fulani kike ba?.

 

Ai sai kayi itama Waccen data kwashi jiki ta tafi rugar zata dawo, don ba iya zama zata yi ba, shekarun ta ya Girma mawa zaman can, Don haka zata dawo ne, kuma zanci mata inshaallh.

 

 

*****

 

 

 

*South America*

Wani studio ne na gani Maƙil da mutane iya ganin ka, fili ne babba wanda babu kowa a cikin wannan filin sai Masu buga wasan…. Wanda duk kan su ma tasa ne turawa yan South America da kuma ɗaya tilo ɗan South African. Ihun jama’a na wannan wurin ne yasani maida hankali garesu da sauraren su jin sunan da suke kira kaman Haka:Muhammad FULƁE.

 

Muhammad Fulbe shi ne abun da nake ƙara nanatawa kenan a ƙwaƙwalwata, kamin idona ya sauka akan wani matashin saurayi da bazai haura 27 ba a duniya ya amsa ƙwallon yana mata wani irin bugu na expact Yana yanka abokanan gogayyan nasu ƴan ƙasan brazil. Sai a sannan na fahimta amsan ƙwallon da yayi ne yasa mutane wannan ihun suna kiran sunan shi.

 

Tun da ya amsa ƙwallon nan bai saki ba sai da ya jefa ta ga ragar brazil , yayin da nake jin maganan chocer ‘n su yana mgn da gô.. Goal Goal fulbe… wanda nan take filin aka hau ihu a Go!!!haɗi ƙirar sunan Muhammad Fulbe.

 

 

Ɗaga mawa mutane hannu yayi yana tsalle wanda nisan shi da ƙasa ya kai 5mtr. Wanda wannan yasa nan take wasu daga cikin ƴan kallon farin cikin Muhd Fulbe yaci suka fara sumewa gau nan take… Wannan ne ya saka aka hura whistle alamun an tashi wasan ƙwallon ƙafan.

 

*****

 

Mama uwale ce tsugunne da sanyin safiya tana gyara wake a filin tsakar gidan nata, Sam bata lura da shigowar ta ba sai maganan ta da ta ji cikin sanyayar muryar ta tana cewa.. Mama barka da safiya.

 

Juyowa tayi tana bin ɗiyar nata da kallo, wanda fuskanta kadai zai tabbatar maka da akwai abun da ke damun ta… Sam bata yi kuma mmkin ganin dawowa ta a yanxu ba, don ta san dama fati Sam bazata iya zaman ruga nan tasu ba.

 

Bata amsa gaisuwa nata ba sai cewa tayi auta na kece da sanyin safiya nan… Tom shiga ɗaki ina zuwa yanzu kinji auta.

 

Ɗaga mata kai fatima tayi tana nufan ɗakin mama uwale……. Bayan kaman mintuna biyar mana uwale ta tsane waken nata tana biyo bayan fatima don ta damu kwarai da ganin yanayin ɗiyar nata……

 

 

 

 

 

Zulai ne ta kalli Rabi da ta rafka wani irin Makeken baƙin glass tana washe haƙora haɗi da juyi gaban sauran ƴan uwan nata Zawarawa tana cewa ” Ya kuka ganni??… Kafin su bata amsa suka ji sautin jan tsaki… Mtswwww ɗan tsaki Fati tayi tana kawar da kanta gyefe guda, yayin da sauran Su Zulai da su Atika ke ihu suna faɗin kin haɗu baby.

 

Mamaki ne da takaici ya kama Fatima tana ƙara nanata sunan da suka kira Mata Ƴar kusan shekara Arba’in dashi wai Baby ?? Wannan yasa ta ƙara jan tsaki a karo na biyu. Ke fatima lafiya kike yi mawa mutane tsaki? Cewan Zulai cike da mazurai da fitina.

 

“Yi tayi kaman bata ji su ba, wanda a hasale su kusan biyar duka yayin ta zawarawan sukayo kanta suna faɗin Uban wa kike mawa tsaki tsaka kika gani anan wurin ko mene?.

 

Jin hayaniyan da ya ɓalle a Ɗakin yasa Mama Uwale ɗago labulen Ɗakin tana faɗin lafiya? “. Muryar Fatima ta ji tana masu magana da cewa” kuna bani mamaki Adda, dukan ku fa ba yara bane ba, babu ɗan shekara 35 a cikin ku, ko ni kaina ƙaramar ku shekarana kusan 30 nake a yanzu, ZAWARCI bafa hauka bane, in dai kuna son maza na gari su zo wurin ku sai mun natsu mun zama cikakkun kamilallun mata na gari…

 

A hayyeeeee ya sayyada Fatima “. Suka yi maganan harda sakin guɗa a tare, Zaki rufe mana baki ko sai mun tattaka ki a nan wurin?. Atika tayi maganan tana bin ta da wani irin kallo.

 

A’a Ahir kar wanda ya taɓa mun Autana, maza fito ki basu wuri, na hana ki shiga sabgar da bata ki ba ko?. Mama uwale tayi maganan tana kallon Fatima da ta Mike A hankali tana nufan wurin kayan ta. Me kike yi kuma anan ne? Cewa Mama Uwale.

 

A hankali ta kalli mama Uwale tana faɗin zan koma Rugar Su Baffa ne.

 

Tayi mgn tana daukar wani Ghana most go nata tana yin waje….. A sauka lafiya yanda kikaje kika dawo haka yanzu ma zaki yi aikin banza ɓur inji tusa… kullum kina yawo cikin daji ta ina zaki samu alhazai, bama alhazai ba samari gajoji ma bazata samu ba. Cewan Rabi tana ficewa daga Ɗakin da FAƊIN mama sai na dawo.

 

A dawo lafiya Mama Uwale tayi mata, kamin ta yi saurin juyawa tana nufan Ɗakin ta da Autan nata ta shiga don ɗaukar sauran kayan ta a dole tayi fushi da zaman gidan, dama haka take yi duk idan baƙin cikin gidan y ishe ta sai ta tattara ta tafi rugar Su Mama Uwale, tafi jin daɗin zaman can fiye da zaman gidan mahaifin ta, duk da a can ɗin ma akwai masu yi mata shagwuɓe da habaici akan rashin Aure, amma yafi mata zaman gidan Iyayen nata a hakan”.

 

“to pah Yau rigiman Autan nawa ya tashi… Abun da Mama ke faɗi kenan ta shiga Ɗakin don ta rarrasheta…

 

 

 

*Littafin na kuɗi ne normal payment 300, vip 500, Spc 1k zaki iya turo da katin Mtn ta wannan number 08081202932 ko ta wannan Account ɗin… 6037312299 Mohammed Aisha keystone.*

 

 

1)Gidan ƙwarata 200

2)Ƴar Aikina 100

3)Siyasata 200

4)Bafullatanan ruga 200

5)Walijaam 200

6)Dijama ƴar fulani 100

7)Kawaliya 200

8)Ƴar Waye 200

9)Ƴar maula 100

10)Bintoto

11)Ƙwaryar sama 200

12)Habibi daiman

13)Habibi daiman Return

14)Zuma da maɗaci 200

15)Gidan zawarawa 300

Duka wannan littafan za ku same su akan sassauƙar farashi inshaallh💃💃. Akan 2500 duka harda Gidan Zawarawa 💃💃.

 

 

اللهم اغفر لأبي ورحمه وعف عنه وأكرم نزله ووسع مدخله و ادخله الجنة مع الأبرار يا رب العالمين

 

 

 

@alheri Writer’s asso.

1 Comment

  • Aslm yan uwa ina tare daku dan inason karatun hausa novels amma yanzu ko zansamu complete in auren yarinta

Leave a Comment

error: Content is protected !!