Hausa Novels

Gimbiya Sabrina Hausa Novel

Gimbiya Sabrina Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*GIMBIYA SABRINA*

 

*(The kingdom of)*

*(isolation)*

 

 

 

*Zahra Surbajo*

 

 

*PAID BOOK 500*

 

 

_Bismillahirrahmanirrahim_

*Duk me buƙatar yasamu nishaɗi,ya wa’azantu,ya shiga shauƙi irin na zazzafar soyayya to ya kasance da wannan littafi,ɗauke yake da salo na musamman ki siya ki karanta 500 ne kacal*

 

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

 

 

*07044600044*

 

 

*FREE PAGE 1*

 

 

 

“Ta kwarankwatsa ba nice nayiwa lawahinnan kahi ba,Ɗahuru ne ɗan gidan su ladingo”cewar wata kyakkyawar yarinya wacce bazata fi shekaru goma sha huɗu da haihuwa ba.

Lokacin da malam Ayuba ya kamata tana masa kashi a gonar albasar shi.

 

“Ɗahuru agidan uban wa,ay da kaina na kamaki kuma se na zaneki ciki da bai ta yadda gobe ma in kika ga gonata zaki kiyaye”yana kaiwa nan ya waiga neman bulalar daze zaneta.

 

Sanin da tayi malam Ayiba be iya duka na wasa bane yasa tayi wuff ta duƙa ta ɗebo ƙasa a tafin hannunta,yana waigowa ta juye masa ƙasar a idanunsa.

 

Ƙwacewa tayi daga ruƙon da yay mata ta arta da gudu kamar barewa,tana zuwa,kusa da wani yaro me keke yaron yafara faɗin”yo sauri ki hau mu arce gahi nan ya biyomu”

 

Da sauri ta hau bayan keken tana faɗin”bahi wuta ɗahuru,Malam Ayuba mugune”

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Ayko ɗahuru tuƙa keken yake da dukkan saurinsa,suka shilla cikin jeji,tana waigowa ta hango malam ayuba akan nasa keken,a kiɗime take faɗin”wuta ɗahuru ze cimmana”

 

Ƙara dagewa yayi yana tuƙawa amma ita gani fake be sauri hakanne yasa ta diro akan keken ta fara tura masa baya azatonta tafi keken gudu.

 

.Ayko tayi tuntuɓe ta faɗi,shiko ɗahuru tuni ya ɓace akan kekensa dan gudun da yake yi.

 

Saura kaɗan ya cimmata ta miƙe da gudu,ta fara kwana kwana ta yadda baze iya kamata kai tsaye ba,a haka suka ƙarasa cikin gari.

 

 

Da mahaukacin gudu ta nufi gidan su ƙawarta jummalo dan tasamu mafaka acan,to daman yayan jummalo ɗin yayi aure shida matarsa suna ɗaki ta faɗa musu da mahaukacin gudu.

 

Sintir suke suna ƙoƙarin raya sunna tai wannan dirar mikiya,da gudu ta fito tana ƙara tana faɗin “malam ayuba na tuba,kaje ka sanarwa me gari yayan jimmalo murtala bashi da wando shida amaryarsa,in bazaka ba ni ka barni inje in faɗi dan a hukunta su”ta faɗi lokacin datazo tasha gabanshi da wani arnen gudu,dan a tsorace take gun ƙoƙarin ya kauce mata ne shi yafaɗi a ƙas wan warrrr itako tabi ta kanshi ta falla da gudu zuwa fadar megari dan kai ƙarar mata da miji bisa kamasi da tayi ba wanduna.

 

 

Muje zuwa

 

ki biya ki karanta

 

Surbajo for life

Leave a Comment