Hausa Novels

Gobe da nisa Hausa Novel Complete

Gobe da nisa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

GOBE DA NISA

Page 1

Na Pharty BB

 

BismillahilRahmaninRaheem

 

 

Ahlin gaba ɗaya farin ciki suke da murna domin samun wannan karuwar abin da basu zata ba, wanda suke ganin abu ne mai wuya samun shi, duk da ya kasance murnar wasu a ciki suke hakan bai sa sun bayyana a fuskarsu ba suka bari a zuci. Ƙaramar walima aka haɗa a gidan, aka ci aka sha kowa na taya wacce abin farin cikin ya sameta murna.

Idan ka dubeta kuwa yadda kyakkyawar fuskarta take annuri zai ba ka tabbacin tana farin ciki da wannan rana, burinta ya cika saura mafarkinta da kaso sittin shi ne abin da ya taimakawa rayuwarta tsawon rai. Jama’a da dama suna ganin hakan ba mai yiwuwa bane saboda kankantarta kuma mace ce.

Sunanta ta ji an ƙira, ta juya tana amsawa wacce ta ƙirata cikin sanyin muryarta na marar son hayaniya. Kanwar mahaifiyarta ce Aunti Babie, cikin murmushi ta ce.

“Zamu wuce gida Mariya, Allah ya taimaka yasa a shiga a sa’a.”

 

Mariyatul Kibdiyya cikin muryarta mai daɗin sauraro ta ce.

“Amin Aunti na gode. Sai na zo muku.”

 

“Babu komai, ai ke yanzu babu zama.”

Aunti Babie ta faɗa tana saka yaranta a gaba suka fita a falon, Zakiyyah tabi bayan mahaifiyarta tana yiwa sauran ƴan matan sallama sai bayan kwana biyu.

Suna fita Mariyatu, Haneefa da Ummi Aisha suka gyara falon ganin yadda aka mayar a hargitse.

A haka kowa ya watse wanda suka zo tayata murna aka bar ƴan gidan. Suna gamawa ɗakinsu suka wuce, kai tsaye bathroom suka yi rige rigen shiga ganin magriba ta yi, alwala suka yi suka gabatar da sallah, kasancewar cikinsu a cike yake basu bi takan abincin dare ba kowace ta nemi guri ta zauna tana ɗaukar wayarta.

Haka suka zauna suna chat suna hira jifa jifa wanda duk Haneefa da Ummi Aisha ne, Mariya daga umm sai a’a nata, haka har dare ya yi suka gabatar da sallar isha’i. Bayan sun idar suka fita suka yi wa Umma sai da safe suka dawo ɗaki suka kwanta.

 

Washegarin ƙarfe bakwai da rabi cib Mariya da Haneefa suka gama shirinsu na tafiya aiki. Mariya yau ne ranar farkonta, wanda dalilin samuwar aikin yasa ahlin haɗa mata walima jiya a gida suka zo yi mata murna.

Haneefa cikin uniform din nurses fari, ta yi kyau abinta.

Mariya kuwa cikin bakin doguwar riga baki, sai baby hijab fari da ya rufe kirjinta, ya haska farin fatarta ya fito mata da tsantsan kyawunta, duk da bai kamata ba hakan baya hana mutum hango zubin halittarta. Fuskarta fiyau babu wani kwalliya sai hoda da man baki da ta sanya don girmama dokokin aikinta.

Bayan sun gaishe da Umma a gurguje suka hau yin breakfast da mai aiki ta gabatar jera a dining.

Haneefa ce ta fara gamawa ta miƙe, ta kalli Umma da take zaune ta ce.

“Umma wai Abba bai farka ba.”

 

“Yana falonsa.”

Umma ta faɗa daga inda take zaune tana duba wasu kayyaki da aka kawo mata.

Haneefa ta juya kalli Mariya ta ce.

“Ki gama muje gaishesa sai mu wuce.”

 

Miƙewa Mariya ta yi don ta kammala kenan, ta ɗauki handbag ɗinta tabar gurin. Ganin haka Haneefa yin gaba Mariya tabi bayanta zuwa falon Abba, a hanya suka haɗu suka ƙarasa.

Da sallama suka shiga gaba d’ayan su, Abba ya amsa musu yana zaune saman kujera hannunsa ɗauke da remote yana kallon labaran safe, yayinda yake sanye da jallabiya. Guri suka samu suka zauna, cikin ladabi suka gaishe dashi. Da fara’a a fuskarsa ya amsa musu tamkar koyaushe. Suka miƙe Haneefa tana cewa.

“Abba zamu wuce aiki.”

 

“A dawo lafiya.”

Ya faɗa yana binsu da kallo suka fita, musamman Mariya da yaga kwalliyarta ya karɓeta.

Bayan fitar su adaidaita suka shiga kowacce ta wuce wajen aikinta.

Mariya tunda ta hau mashin har ya sauƙeta bakinta da addu’o’i, yau ne ranar farkonta aiki bayan interview da suka sha aka tantance aka zaɓa masu ƙoƙarinm aka basu aikin, hakan yasa duk a tsorace take.

Da bismillah ta saka ƙafarta cikin ma’aikatar, tana shiga ta fara bin harabar wajen da kallo. Ba wani ma’aikata bane babba amma tsarin gini ya fita mai kyau, ginin zamani ne hawa ɗaya bene. Kallon wajen ta ci gaba da yi idanuwanta suka hango mata waɗannan suka yi interview tare.

Cikin sauri ta ƙarasa wajen su, ta musu sallama suka amsa mata daga nan ta ci gaba da tsayawa. Mintuna biyar da tsayuwarta taga kowa yana gyara tsayuwar sa, ita ma nata ta gyara tana kai kallonta kan mutanen da suka dumfaro su.

Mutumin da ya musu interview ne tare da wasu biyu, wanda ɗayan lokacin da ake mata interview yana office din amma bai ko kalli inda take ba balle ya tofa, sai ɗayan da bata san shi ba.

Tsit gurin ya ɗauka bayan isowar su, baƙon fuskar cikin su ya musu sallama tare da fara gabatar da kanshi gare su da sauran cikin harshen turanci.

“Ni sunana Barrister Hamza, wannan Barrister Waliy Abubakar sai wannan oga kwata kwata Judge Nuhu. Barkanku da zuwa wannan kotun, da fatan za ku yi aiki tukuru kamar yadda ya kawoku, wanda muke sa ran kuma nan da shekara ɗaya kun zama baristocin kanku, ku fito gaban court a dama daku a fafata.”

 

Kowa jinjina kai ya yi alamar gamsuwa, hakan yasa ya ci gaba da faɗin. “Follow me, a nuna muku office dinku.”

Daga haka ya fara tafiya.

Suna ƙoƙarin bin bayan shi cikin amo mai ɗauke da daɗin murya suka ji maganar Barrister Waliy ya shiga dodon kunnuwansu.

“Kowacce ta nemi suit(coat), ba ma son wannan baƙin abayan.”

 

Gaba daya kallon shi suka yi, suka ga ya fuske tamkar ba shi ya yi maganar ba, sai ma juyawa ya yi ya fara ƙoƙarin barin wajen cikin takunsa na kasaita cike da kwanji.

Da kallon mamaki ƴan matan musulman wajen suka bishi. Musamman Mariya da wannan dokar nashi yake ta kai kawo a kunnuwanta, tunani take ta ya ya za ta saka suit a yadda take.

Tafiyar da suka fara domin bin bayan Barrister Hamza ya dawo da ita hankalinta. Da sauri ta bi bayan su, office aka kaisu wanda yake a floor ƙasa, yana da girma wanda yake ɗauke da table shida, kowanne da computer akai. Cikin su aka zaɓi mutum shida, uku maza da mata uku ciki har da Mariya. Sauran aka yi gaba da su.

Sai da suka gama zaba sannan Mariya ta samu ta zaune kusa da mace. Dafe kanta ta yi tana tunanin anya za ta iya wannan aikin da ta ɗaukarwa kanta alƙawarin yi tun ba takai haka ba, wanda shi ne mafarkinta da burinta har tana ganin GOBENTA DA NISA wanda ba zai zo ba balle burinta ya cika. Amma yau ne ranar farko har ta fara sarewa.

‘Yanzu aka fara.’ Wani sashe na zuciyarta ya faɗa mata haka, hakan taji ya ƙara mata ƙarfin guiwa kamar koyaushe idan ta sare zuciyarta tana bata kwarin guiwa.

Kanta ta ɗaga ta buɗe idanuwanta lumshasshu, da bismilla ta kunnan computer taga ya kawo. Bincike ta fara a ciki ko za ta yi gamo da wani abun a ciki, cikin mamaki kuwa ta hango folder ɗaya a gefe da alamar creating ɗinsa aka yi ko turawa, ciki ta shiga nan taci karo da case ne da ake so ta ƙarasa, ga gundarin jawabin kaɗan da zaman shari’ar da aka yi na farko, saura ta binciko da kanta, ga sunan mutanen da ake case din a kansu da sunan unguwa har da lambar waya. Idan ta gama ko tana bukatar ƙarin bayani ta tuntubi Barrister Waliy don shi ne akan shari’ar.

Numfashi ta sauƙe jin da wanda aka haɗata, ta ɗauke idanuwanta saman computer ta kalli sauran mutanen wajen, nan taga duk hankalin su yana kan computer alamun sun nuna suma sun gamu da irin nata ne. Kanta ta mayar ta ci gaba da karantawa daki daki tana fahimtar case ɗin akan wani ne ya yi wa bazawar cikin gidan da suke haya ciki, ita ta dage nashi ne shi kuma ya musa, shi ne iyayenta suka kawo ƙara.

Mariya abin ma dariya ya bata don yadda ta gano shekarun mutumin tsoho dashi, ita kuma ƙarama sosai yar shekaru ashirin da uku. Haka ta ci gaba da duba shari’ar da duk abin da za ta fahimta, ta ɗauki sabon folder da suke saman table ɗinta ta fara rubuta duk abin da tasan zai mata amfani.

Sosai ta dukufa a aikinta, babu mai yiwa wani magana cikinsu don babu sabo tsakanin su, hasalima yau ne haɗuwar su ta biyu. Basu samu kansu ba sai ƙarfe biyu, suka dakatar da aikin suka fita zuwa masallacin da yake ɗauke da gefen maza da mata.

Alwala suka yi suka shige kowanne ya gabatar da sallah, bayan an idar Mariya taji daɗin saka Abaya don ya taimaka mata bata sha wahalar neman hijab ba. Amma a hakan ana neman hanasu sakawa, dole kenan su fara yawo da hijab a jaka don yin sallah.

Fitowa ta yi bayan gama addu’o’inta, inda taga sun nufa wajen cin abinci ta yi ita ma. Bayan ta shiga ta zauna tasa aka kawo mata doughnuts da fresh milk mai sanyi, cikin nutsuwa ta ci ta kammala ta miƙe, ta nufi gurin biya ta biya ta bar wajen.

Office ta koma ta ci gaba da yin aikinta cikin nutsuwa, sai yanzu hankalinta ya fara kwanciya da wannan aiki nata, sam babu takura sai rashin sabo wanda tasan gaba kaɗan za ta saba har ta samu damar cikar nata burin da mafarki.

Karfe biyar suka tashi, kowa jiki ya yi tsami don rashin sabo. Sallama suka yiwa juna kowa ya kama gabansa. Mariya napep ta shiga ta nufi gida, wani bacci bacci take ji sai lumshe lumshashshun idanuwanta take tana buɗewa wanda hakan ƙara mata kyau yake.

Har ƙofar gida ya kaita ta sauƙa ta ba shi kuɗinsa ta wuce ciki, da sallama ta shiga ta hango motar Abba alamar ya dawo.

Ɓangaren su ta wuce ta shiga da sallama, Umma da Abba suka amsa mata. Umma tana faɗin.

“Manyan baristocin ƙasa.”

 

Murmushi Mariya ta yi har dimple ɗinta suka lotsa, wanda ko ya ya tayi da fuskarta sai sun lotsa tsabar yadda suke da saurin shigewa. Ta duka tana faɗin.

“Ina wuni Umma?” Ta juya gefen Abba da shima sanyayyar murmushi yake binta da shi ta ce.

“Abba ina wuni.”

 

Gaba ɗayansu suka amsa mata cikin kulawa da tambayarta aiki.

Cikin sanyinta ta ce

“Allahamdulillahi.” Sannan ta miƙe ta wuce ɗakinsu.

Kwance ta samu Ummi Aisha, kasancewar ta yi sallar la’asar saman gadon ta zube ƙafafunta suna reto a ƙasa, cikin makoshi ta furta.

“Wash! Na gaji.”

 

Ummi Aisha ta gyara kwanciyarta tana kallonta ta ce.

“Manya Barrister, sannu da ƙoƙari.”

 

Da ƙyar Mariya ta ce. “Yawwa.”

Ta miƙe tana cire baby hijab ɗinta ta ce.”Aiki ko wahala.”

 
Littafan Hausa Novels

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

“Ke kika sa kanki aikin maza. Bar ni da baking ɗina hankali kwance.”

Faɗin Ummi Aisha tana dariya ta sauƙa a kan gadon.

Mariya leɓbenta ta cije ba ta mata magana, bayan ta rage kayan jikinta ta miƙe ta shiga bathroom. Ruwa ta watsa ta fito ta saka doguwar riga na shan iska, ta saka ƙaramin hijab iya guiwarta sannan ta fita.

Yadda ta barsu haka ta dawo ta samesu sai ma ƙarin Ummi Aisha da ta hango a dining, can ta nufa ta ja kujera ta zauna, ta buɗe warmers din saman dining ta ga akwai ragowar abinci. Plate ta ɗauka ta zuba sannan ta zauna ta hau ci ganin Ummi Aisha tana tare da ita.

Sosai ta ci ta kwara da ruwa kafin ta miƙe, ta kai plate din kitchen ta fita, bata tsaya a falon ba ta wuce ɗakin su ta ɗauki wayarta ta kwanta. Haneefa ta ƙira ta sanar mata ta dawo, ita ma ta sanar mata tana da night duty sai safiyar gobe zata dawo.

Daga haka suka kashe wayar, Mariya ta miƙe ta shiga bathroom ta ɗaura alwala ta fito ta samu Ummi Aisha ta shigo ɗakin. Sallah ta fara ita ma Ummi Aisha ta shiga bathroom ta yi alwala ta fito ta fara sallar.

Bayan Mariya ta idar ta haye saman gado ta sake ɗaukar wayarta ta kunna data don ganin sakwanni da ba ta samu gani ba tun safe, ashe nutsuwa shi yake kawo mutum ya wuni yana chat.

Babu wani dogon hira tsakinta da Ummi Aisha don Mariya ba ta son surutu sam, idan ana hira maganarta a kirge yake ko da cikin ƴan uwanta ne balle bare.

Daga murmushinta mai kyau sai umm da a’a, hakan yasa mutane suke mata kallo ta cika jan aji da miskilanci, ita kuwa har ranta ba haka bane, tayi ta zuba surutu ne ba ta so balle tsiwa da bata sanshi ba sam, abin gabanta shi ne kawai a gabanta.

Bayan ƙiran sallar isha’i Mariya ta miƙe ta gabatar, da ta idar ta ɗauki kayan baccinta na riga da wando ta saka ta haye gado. Addu’o’i ta yi ta shafa ta kwanta tana cewa Ummi Aisha.”Sai da safe.”

 

“Aiki ya nukurkusa wata.”

Faɗin Ummi Aisha tana dariya. Ita dai Mariya murmushi kawai ta yi ta rufe idanuwanta, don so take bacci ya ɗauketa ko don ta samu ta farka da wuri don tafiya aiki akan lokaci.

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!