GOGE MANIYYI DA TSUMMA ƊAYA BAYAN SADUWA
Tag: Maniyi
Daga cikin abubuwan da aka yi umarni mu nisance su akwai wannan:
Annabi SAW ya na cewa: “Ya Ali! Kada ka kusanci matarka face sai kana riƙe da tsummanka daban, ita ma tana da nata tsumman daban wanda za ku goge abinda ya fito muku na daga maniyyi, domin idan ku ka goge da tsumma ɗaya adawa da ƙiyayya za su mamaye zukatanku har sai sun raba aurenku”.
Zahirin gaskiya wannan ya na cikin abubuwan da su ka jawo hankalina na yi wanan rubutun, saboda a gaskiya yanzu babban abin da ya zama jigon lalacewar auren zamaninmu kenan, shi ya sa na zaɓi kiran wannan taƙaitaccen rubutun da “Auren Zamani”.
Za ka ga ma’aurata su na son junansu, sun yi aure cikin mutunta juna da kuma girmama juna, iyaye da dangi a na murna da sambarka, amma ko wata ɗaya na kirki ba za su yi ba sai a fara samun saɓani, kuma wallahi wannan, ba zan yi kaffara ba, shi ne mafi girman dalili, saboda Annabi SAW ne ya faɗa, ba ni ba, cewa matuƙar a ka sami irin wannan to fa a hankali gaba da ƙiyayyar juna za su fara shiga zukatan ma’aurata sai a fara mayar da abin da ba laifi ba laifi, a rasa ina ne bakin zaren matsalar, a ƙarshe dole a rabu ba don kuma ana so ba.
Matasa su na cikin wannan damuwar, kuma sun rasa mafitar wannan lamarin, to matuƙar kai matashi ne ka kiyaye wannan, ke ma ki kiyaye wannan in dai ki na son aurenku ya yi ƙarko.
Allah yasa mudace Yabamu Nasara a Rayuwa.
Call 09074490029
WhatsApp 08163132543
ALKHAIRAT ISLAMIC MEDICINE CENTER KANO HOTORO