Hausa Novels

Guguwar Fansa Hausa Novel Complete

Guguwar Fansa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[25/09, 11:24 am] +234 806 650 5531: GUGUWAR FANSA

 

Free “`Book“`

 

Labari/Rubutawa:LAILAT

ABDULLAHI

 

 

———————————————-

Page 1

 

Ƙaramin gidan gona ne mai dauke da dakuna guda biyu da ƙaramin kitchen na langa-langa,sai kuma kewaye shima guda ɗaya da aka kewaye da langa-langar.

 

Idan ka cire wannan ɗan karamin gidan da ke tsakiyar wata ƙatuwar gona,iyakar hangenka bazaka hango komai ba face wani irin ƙaton daji mai matuƙar ban tsoro saboda yanayin dare da kuma dogayen bishiyoyin da suka yiwa dajin rumfa kamar dama can jera su akayi,iyakar jin ka bazaka ji komai ba face kukan tsuntsaye da sauran ƙanana halittun da ke rayuwa acikin wannan dajin.

 

Acikin ɗaya daga cikin ɗakunan da ke cikin wannan gidan gonar ne na hango wani ɗan ƙaramin haske da alama akwai wanda baiyi barci ba,wata mata na hango ko nace matashiya wadda shekarunta bazasu gaza 25 zuwa 30 ba,zaune take ga alama tayi duk iya kokarinta barci ne ya ƙi ɗaukarta shine dalilin da yasa ta tashi zaune,ganin ta ƙurawa gefenta ido yasa na kalli gefen nata,wani mutum na hango da alama mijinta ne barcinsa yake hankalinsa kwance yana ta sauke numfashi cikin natsuwa da alama bashi da wata damuwa.

 

A hankali ta ɗauke idonta daga kan mijin nata tare da miƙewa tsaye,ciki na hango a jikinta wanda ya kai wata 6,jingina tayi da bangon dakin tare da faɗawa cikin tunani a zociyarta take cewa”ya zama dole FOLA ya ɗauke ni daga wannan mugun dajin haka kawai muna zaune cikin gari kusa da mutane,mun dawo inda babu kowa sai tsuntsaye muna rayuwa saboda taƙamar iyayenshi suna nan,su kan su iyayen nashi mamaki suke bani duk da suna da halin da zasu iya komawa cikin gari kusa da mutane suyi rayuwa irin t…….tunaninta ne ya katse bayan taji ana kiran sunanta a hankali da wata irin murya da ta kasa tantance muryar yara ce ko ta manya.

 

Saurarawa tayi sosai domin taji daga ina muryar nan ke fitowa,sai kuma taji tsit aranta take cewa”kila kawai tsoron da nasaka araina ne yasa naji kamar ana kirana”taɓe baki tayi alamar rashin damuwa tare da juyawa da nufin ta koma makwancinta,sake jin kiran tayi wannan karon idan ba kunnenta bane sai taji kamar muryar da ke kiran nata har da kuka take yi,kuma tabbas wannan muryar macece.

 

Cikin sauri ta juyo tana kalle-kalle domin wannan karon tsoro ne ya fara kamata tana tunanin waye ne yake kiranta cikin wannan tsohon daren,idanma taimako ne wani yake nema miyasa sai ita,ita da tazo jiya-jiya tunaninta ya tsaya cak data tuno da surukarta watau uwar mijinta,saboda tasan su biyu ne kadai mata a gidan tunanin hakan da tayi yasa tsoron da take ji ya ragu sosai,kofa ta nufa ta zare sakatar a hankali ta fita kai tsaye inda dakin surukan nata suke tana nufa..

 

Turus taja ta tsaya ganin kofar dakin a rufe babu alamar an buɗe ƙofar,kai ita fa ji tayi har da jan rago suke alamar barcin nayi musu dadi,shashshekar kuka ta rinka jiyowa daga can bayan dakunansu inda wata ƙatuwar rijiya take kuma anan suke ɗibar ruwan amfaninsu na yau da kullum,jikinta ne ya fara kyarma tsoro da fargaba nan take suka samu matsugunni a zociyarta,juyowar da zatayi domin ta koma dakin su ne taga abinda yasa zociyarta buguwa da karfi….

 

 

LAILAT ABDULLAHI

Share

Comment

Fisabilillah…

[25/09, 11:24 am] +234 806 650 5531: GUGUWAR FANSA

 

Free Book

 

Labari/Rubutawa:LAILAT ABDULLHI

 

———————————————-

Page2

 

 

Juyawar da zatayi domin ta koma ɗakinsu ne taga abinda yasa zociyarta buguwa da karfi,nan take miyun bakinta ya kafe tsoro mai tsanani tare da nadamar fitowa suka kamata duk a lokaci guda.

 

Yara ne ta gani su Ukku suna tunkaro inda take,duk da wurin duhu ne amma tana kallon yaran nan tasan bawai yara ne na Allah da annabi ba,ja da baya fara yi cike da matukar tsoro su kuma yaran suka cigaba da tunkararta,wata irin walƙiya akayi wadda ta haske gidan gabaɗaya duk da kuwa ba lokacin damina bane,yaran ta gani suna daf da ƙarasowa inda take,yaran wani irin yanayi garesu daga ganinsu ba suyi kama da mutane ba,kamarsu iri ɗaya ce duka su ukkun,tunkararta suke suna wata irin dariya mai haɗe da wani irin amo wanda hakan ya tilasta mata toshe kunnuwanta.

 

Karo tayi da wani ƙaton dutse a ƙoƙarinta na gujewa waɗannan yara,faɗowa tayi akan dutsen nan take goshinta ya fashe jini ya fara zuba,kafin tayi wani yunƙuri na tashi yaran nan sun cim mata suna cigaba da ɓaɓɓaka mata dariya,ƙanƙame jikinta tayi ta rufe idonta domin gani take kawai mutuwa zatayi,zance zoci ta fara yi akan me ya fiddo ta acikin wannan daren,miyasa ta kawo kanta ga halaka,tunanin nata ne ya tsaya da taji dariyar da sukeyi ta kara karfi.

 

Su take yi tayi ihu ko wani acikin gidan ya kawo mata ɗauki,amma da ta kwatanta bude baki zataji tamkar bata da murya ganin bata da mafita yasa ta fashe da wani irin marayan kuka,domin gani take kawai ƙarshenta yazo,ji tayi kamar daga sama yaran sun hada baki da wata irin murya mai amo sunce AUNTY har sai da wurin ya amsa.

 

Kafin tayi wani yunƙuri sai taga ɗaya daga cikin yaran ya miƙo mata wuƙa tare da cewa”gashi ki fito mana da ɗan cikinki muyi wasa”a razane take kallonsu tana girgiza kai wuƙar ta kalla tana sheƙi,da farko bata ga wuƙa a hannunsu ba,to yanzu ina suka same ta,tsawar da taji anyi mata yasa hankalinta ya dawo jikinta wuƙar da ke hannun yaron ya sake miƙa mata,dole zaki ciro mana yaron da ke cikinki muyi wasa idan kuma kin ƙi zamu kashe ki sannan mu ɗauke yaron da kan mu ɗaya daga cikin yaran ne ya furta haka,wuƙar taga ni a hannunta batare da tasan yanda akayi tazo hannunta ɗin ba kuma da ƙarfin tsiya taga hannunta da ke riƙe da wuƙar ya nufi cikinta.

 

Cikin muryar da bata fita ta fara roƙon su akan su bar mata cikinta,ɗaya daga cikin yaran ne yace”dole ne mu ɗauki FANSA kamar yanda muka ɗauka wurin sauran matan da suka gabace ki”.da ƙarfi taji wuƙar ta fara taɓa mata ciki su kuma yaran dariya suka cigaba da yi mai firgitarwa,kiran sunanta tare da tunkaro inda suke shine yayi sanadiyar ɗaukewar komai,kamar dai anyi ruwa an ɗauke,wuƙar hannun nata ce taga babu sannan yaran suma sun ɓace kamar dama basu taɓa wanzuwa ba,haska ta taga anayi tare da jin muryar mijinta yana tambayarta abinda take yi anan cikin wannan daren.

 

 

LAILAT ABDULLAHI

Share

Comments

Fisabilillah

[25/09, 11:24 am] +234 806 650 5531: GUGUWAR FANSA

 

Free Book

 

Labari/Rubutawa:LAILAT ABDULLAHI

 

———————————————-

Page3

 

ƙarasowa yayi inda take tare da miƙar da ita daga zaman ‘yan borin da tayi ya nufi ɗakin su da ita,tambayarta ya ke miye ya fiddata waje ita kuwa shiru tayi tare da ƙura mashi ido maganar duniya yayi amma ita dai bata ce da shi ko ci kanka ba,gajiya yayi da tambayar ta ganin cewa bazata tanka mashi ba yasa ya juya ya kwanta ya cigaba da barcinsa.

 

Ganin ya kwanta yasa itama raɓawa gefensa ta kwanta sai dai saɓanin shi da barci ya ɗauke shi,ita kuwa tunani ne ya dauɗeta,tunani take wai miye ke shirin faruwa da ita ne,kuma wace irin FANSA ce yaran ke cewa suna ɗauka,shin dama kafin ita akwai matan da suka rayu a nan wurin,shin wai to miye ma asalin mijin nata,ita dai tasan yace mata yana da uwa da uba har da ɗan’uwa guda daya,amma baya ga haka bata san komai game da shi ba,bai kuma taɓa yi mata wata magana da ta danganci labarin shi ba,tarin tambayoyi da ke cikin kwakwalwarta ne yasa a wannan daren dan dai kawai barci yana ɓarawo shiyasa ya iya saceta,batare da ta samo koda amsar tambaya guda daya ba.

 

Bugun ƙofar su da akeyi ne ya tashe ta daga wahalallan barci da ya ɗauketa cikin mutuwar jiki taje ta buɗe kofar hasken da ya shigo ɗakinne ya tabbatar mata da gari ya waye,tsaye bakin ƙofar ta su wata mata na gani farat ɗaya idan mutum ya ganta zaiyi tsammanin mahaukaciya ce sabon kamu,ko kuma irin ‘yan borin nan da harkar ke gara musu tana da manyan idanuwa masu kalar abin tsoro gashi kuma ta rambaɗa musu kwalli sai idanuwan sukayi kamar ta shafa musu bakin gawayi,ita ba gajera ba,kuma ba doguwa ba.

 

Suna haɗa ido da matar dan cikinta ya juya da ƙarfi saboda firgitar da tayi da ganinta,duk da kuwa bawai wannan ne karon farko da ta fara ganin sirikar ta ta ba,cikin rawar murya ta fara gaisheta kanta ƙasa saboda bata marmarin sake kallon wannan fuskar,bata amsa gaisuwar da take mata ba sai ma cikin wata irin ƙatuwar murya tace”wai ku kuwa yau lafiya kuka shige ɗaki kuna ta faman barci,kusan wannan shine karo na ukku da nazo baku tashi ba”ba ta jira amsar ta ba,ta miƙa mata wata langa da ƙaramin bokiti tace”ga kalacin ku nan ki tashe shi kuci,ku ci yanzu tunda kinga bake kaɗai bace,ga kuma magani nan ki tabbatar kin sha bayan kin ci abincin”tana gama maganar ta miƙa mata tare da juyawa tayi tafiyarta.

 

Tsaye take riƙe da bokitin da kuma langar ta ƙurawa bayan sirikar ta ta idanuwa har sai da ta ɓacewa ganinta,kafin ta kauda idonta tare da sauke ajiyar zociya ta juya itama ta shiga na su ɗakin,zama tayi tare da buɗe bokitin maganin wani irin JAN ruwa ta gani kamar JINI ga wani irin karni da ruwan ke yi cikin sauri ta toshe hancinta tare da rufe bokitin,a ranta kuwa cewa tayi ni ce wai zansha wannan ƙazantar da sunan magani lalle akwai ƙura,langar da aka ce kalacin nasu ne aciki ta ƙurawa ido tana wasiwasi aranta ta bude ko a’a,shahada tayi ta bude langar abinda ta gani cikin langar ne yasa ta zare idanuwa tare da mikewa tsaye jikinta na wani irin kyarma..

 

LAILAT ABDULLAHI

Share

Comment

Fisabilillah..

[25/09, 11:24 am] +234 806 650 5531:

 

 

/:

 

———————————————-

4

 

Kallon kwanon take a razane idonta kamar zai faɗa ciki,kauda idonta tayi daga kan silbar ta ƙurawa inda mijinta ke barci ido yana ta barcinsa hakalinsa a kwance yayin da ita ya barta da ganin abubuwan ‘,dawo da idonta tayi akan silar tsuntsaye ne guda biyu gasassu a nufin su amma a idon duk wanda ya gani to zai kira su ne ƙonannu ne,baƙiƙirin suke sai ƙauri marar daɗi ne ke fitowa.

 

Tagumi tayi tare da zubawa kwanon ido wai wannan shine abincin da mutane ke ci tafaɗa aranta,lalle dole ta bar gurin nan ko an amince ko ba’a amince ba ina ita ina rayuwa irin wannan mai kama da ta ahalin JINNU,ita fa gani take anya waɗannan mutane ne kowane mutum da ke wurin kala yake mata da abin tsoro,mijinta ne kawai ke da ɗan sauƙi-sauƙi.

 

Firgigit tayi ganin kamar ƙonannun tsuntsayen da ke cikin kwanon nayi mata dariya tsaye ta tashi da sauri ta matsa kusa da mijinta tafara tashin shi da ƙarfi cewa take”ka tashi kaga abinda nake gani,ka tashi kada kwakwalwata tafara samun matsala”tashi yayi da sauri yana kalle-kalle iya dubansa bai ga komai ba dawo da kallonsa yayi a kanta ganin da yayi mata a razane yasa ya kamo hannunta tare da raɓa ta jikinshi ya fara tambayarta abinda ke faruwa,kwanon da ke tsakar ɗakin take nuna masa a razane.

 

Tashi yayi tare da miƙar da ita tsaye ya nufi wurin wannan kwanon tare da ƙokarin buɗewa wai miye ya razana ki ne da kwanon ya sake tambayarta,maƙale take a bayan shi cike da tsoron sake ganin abinda ta gani tace masa”tsuntsaye ne aciki kuma wallahi dariya suke”dariya ta bashi babu shiri ya fara dariya yana cewa”tsuntsaye da dariya kuma safna wace irin almara ce wannan”.ganin yana nema ya mayar da ita mahaukaciya ne yasa ta yin tsit da bakinta tare da tsuke fuska,buɗe kwanon yayi yana cigaba da dariyarsa zagayowa da ita yayi yace mata”ina tsuntsayen da ke dariyar”.

 

 

Murza idanuwanta tayi sannan ta sake kallon kwanon baki buɗe ganin babu tsuntsaye babu dalilin su,asalima waina ce aciki da ke ta kamshin mai ga siraci tana yi alamar da zafinta sosai,cikin dariya ya lakuce mata hanci tare da furta matsoraciya kawai yayi gaba abinsa tare barin ɗakin kuma fa babu tsuntsayen tafaɗa tare da tsugunnawa tana kallon kwanon,to ina suke miyasa ni kaɗai na gansu fola bai gansu ba,wani sashe na zociyarta ne yake fada mata safna kodai tsoratar da kikayi ne jiya da dare yasa kike ganin komai a bai-bai,tafi yadda da wannan tunanin shiyasa hankalinta ya ɗan fara kwanciya,har ma ta fara ƙoƙarin kimtsa ɗakin nasu ta kakkaɓe ko’ina ta share da yake ita ɗin

macece mai tsafta cikin lokaci kaɗan ɗakin yayi gwanin kyau,duk da ba wasu kayan ɗaki bane masu kyau acikinsa.

 

Bayan ta gama ne tazo gaban kayan kalacin na su ta zauna saboda ta fara jin yunwa to amma miyasa zata yadda taci abincin da bata yadda da wadda ta girka shi ba saboda gudun kada ta cutar da ita dan ita tafi tunanin mamar fola matsafiya ce,fola ne ya shigo tare da nufar wurin abincin shima buɗewa yayi tare da fara ci kallonta yayi yaga shi take kallo babu alamun zata fara ci,bazaki ci abincin bane ya tambaye ta,ita kam ta san da kunya tace bazata ci abincin da mahaifiyarsa ta girka ba to idanma ya tambaye ta dalili tace masa bata yarda da uwarsa bane ko me…

 

 

[25/09, 11:24 am] +234 806 650 5531:

 

 

/:

 

———————————————-

5-6

 

Ganin da tayi ba sarki sai Allah yasa ta saka hannu tafara cin abincin duk da ranta baya so to amma ya zatayi bata da zaɓi,tunda anan ɗin bata da kowa kuma bata da komi sai yadda sukayi da ita zata yi hakuri taga iya gudun ruwan su kafin haƙurinta ya fara ƙarewa domin ita kam koma miye bazata cigaba da zama anan gurin ba.

 

Bayan sun kammala cin abincin ya miƙe tare da cewa”zan ɗan fita nan baya gurin baba”itama tsayen ta miƙe tace masa”magana nakeso muyi akan komawarmu LEGOS”.

 

Murmushi yayi tare da cewa” ba dai har kin gaji da gidan namu ba kar fa ki manta kece kika sako ni a gaba da nacin son ganin iyayena,ya daga kwana ɗaya kacal ki fara maganar komawa,kuma ai sati guda mukayi dake zamuyi anan ɗin”.yana gama maganar yayi gaba abinsa.

 

Bin bayansa tayi da kallo tana tuna lokacin da ta hana shi saƙat akan ita fa dole ya kaita taga iyayenshi,a duk lokacin da tayi masa magana ya kan ce mata”kiyi haƙuri da san ganin wani nawa SAFNA ni kikeso kuma ni ɗin gani tare da ke zan kuma cigaba da kasancewa tare d ke har mutuwa”.

 

Ganin tunanin baya da amfani yasa ta tashi itama ta fita domin zuwa gurin mahaifiyarsa duk da ita tsoronta take yi,to amma dai dole zata kusance ta tunda ta auri ɗanta.

 

A tsakar gidan ta ganta tana ‘yan ƙananan aikace-aikace tunda ta fito taga matar nan ta dakatar da duk abinda take yi tare da ƙurawa cikinta ido,har taƙaraso inda take bata sani ba kiran sunanta da tayi ne yasa ta dawo cikin hankalinta tare da wanyacewa da cewa har kin fito.

 

Amsa mata tayi aranta tana mamakin kallon ƙurullar da wannan aljanar matar kewa cikinta tambayarta tayi mama miye zan kama miki da shi,kallonta tayi tare da yi mata wani shu’umin murmushi mai wahalar fassarawa tare da cewa “kije kawai yarinya kije ki huta babu aikin da zakayi anan,kije zakayi aiki amma da sauran lokaci”.

 

Rashin gane inda maganar ta ta tadosa ne yasa ta nemi tsintsiya tafara share gidan,ita kam ko bata yi aikin gidan dan su ba,tayi domin kula da lafiyarta da kuma ta abinda ke cikinta.

 

Babban abinda ya bata mamaki da wannan aljanar matar kamar yanda ta rangaɗa mata shine duk lokacin da ta ɗago idonta sai taga ita take kallo,da kuma sun haɗa ido sai tayi sauri ta kawar da kanta cigaba da shararta tayi domin ta lura idan ta biyewa abubuwan da take gani na mamaki game da wannan matar to babu makawa hatta mijinta sai dai ya nemeta ya rasa.

 

Bayan ta kammala ne tace mata tanaso tayi wanka wata hanya ta nuna mata da ta nufi bayan ɗakinta tare da cewa”akwai rijiya ta can baya ki ɗauki bokiti kije can ki jayo,rijiyar bata da zurfi”bata amsa mata ba amma dai ta ɗauki bokitin tare da nufar inda ta nuna mata ɗin.

 

Tafiya take tana ‘yan tunane-tunanenta har ta karasa bakin rijiyar da ke cikin wata duhuwa,itace ne masu ganye da yawa suka kewaye rijiyar hakan yasa wurin yayi duhu.

 

Ruwan taja domin ita dama can ba baƙuwar jan ruwa a rijiya ba ce domin gidansu suna da rijiya,iya waɗanda zata iya ɗauka taja ta juyo domin komawa taji ance”ki gudu yarinya lalle ki gudu rayuwarki tana cikin haɗari”waigawa tayi bata ga kowa ba kuma bata ga komai ba.

 

Ajiyar zociya tayi ta cigaba da tafiya kai tsaye banɗakin ta wuce da ruwan,bayan ta ajiye ruwan ta koma ɗakinta ta cire kayan jikinta ta ɗauko zani ta ɗaura sannan ta yapa ɗankwali a saman kanta ta fito ta nufi banɗakin.

 

Tana shiga banɗakin ta cire zanen ta ɗora shi akan langa-langar da ke banɗakin ya zama na dai jikinta babu komai idonta ta rufe tare da fara wanke fuskarta.

 

Juya bayanta tayi tana cigaba da yin wankanta hankalinta a kwance,jikinta ya bata cewa wani yana leƙenta da sauri ta juyo domin ganewa idonta wane marar kunya ne wannan.

 

Miye zata gani uwar mijinta ce dai take leƙata yayin da take zindir tana wanka,ganin ta ganta yasa ta sauka da sauri,ita kuma da sauri ta ida zubawa jikinta ruwa ta ɗaura zaninta tafito har tana tuntuɓe burinta bai wuce taji dalilin da yasa take leƙenta acikin banɗakin ba.

 

Tana fitowa kai tsaye inda ta ganta ta nufa,tsaye take ta juya bayanta ta ƙurawa hanyar rijiyar nan ido safna kuwa bata kula da abinda take ba ita dai amsar tambayarta take buƙata.

 

Safnar cikin ladabi ta cewa maman”mama naga kamar kina leƙa banɗaki ko wani abu kika yar ne na tayaki dubawa”murmushin da ya zame mata jiki tayi tace”BANI BACE BA”safna tace”mama kece domin na ganki da idona,to idan bake bace waye ne yake leƙa ni?”.

 

Kallonta tayi tace”yarinya nace miki bani bace”buɗe baki safna tayi da niyyar ta sake cewa wani abu tsawar da taji maman ta daka mata ne yasa ba shiri ta haɗiye maganar.

 

 

 

.

Leave a Comment

error: Content is protected !!