Guntun Goro Hausa Novel

hotunan bikin ummi rahab

Guntun Goro Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

GUNTUN GORO

 

 

 

_Zainab Habib(Mom Islam_

 

 

*✨TEAM GAWURTATTU BIYAR5✨*

 

 

 

Dama gareku masu son a tallata muku hajarku, cikin farashi mai sauƙi ku tuntuɓi wannan number 08141799224

 

_Bismillahir rahmanir rahim_

 

🆓🅿️1-2

 

_Gargaɗi!! Gargaɗi!! Gargaɗi!! ban amince a sauyamin littafi ,ko a ɗoraminshi a wata ƙafa ba tare da izinina ba! wannan littafin mallakar Zainab Habib ne, yin hakan zai iya sawa ince nabar mutum da Allah! ina roƙon Allah yasa kamar inda muka fara littafinnan lafiya Allah kasa mu kammalashi cikin ƙoshin lafiya amin_

 

Asabar shida ga watan bakwai ,shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu, 11:1am

Zaune nake gaban Abbana hannuna bisa kumatuna, idona kuwa nakan ciwon ƙafarsa wacce munyi magani har mun gaji.

“Ilham” Abba ya kira sunana cikin sanyayayyar muryarsa wacce duk sanda naji ya kirani da ita jikina ke kyarma sbda nasan babu lafiya.

“Na’am” nace kaina a ƙasa ina jiran inji abinda Abbana zai cemin “Ilham kinga wannan ciwon ƙafar tawa daɗa ta’azzara yake, gashi duk wata dukiya da muka mallaka a halin yanzu mun tashi babu ko sisi, ciki harda gonakin mahaifiyarki duk kince in siyar na siyar Allah baisa an dace ba”, kallon Abbana nayi idanuna na zubar da ƙwallah nace “Abba to yanzu ya zamuyi gashi ƙafar daɗa rarikewa take?”

yamutsa fuska Abbana yayi lokacin da yake ɗago ƙafar alamun zafi takeyi masa,

“Da zaki amince Ilham da na nema miki aikatau a gidan Alhaji Abdullahi Zakin Naira “a gigice na ɗago kaina dana sunkuyar ina kallon Abba kafin nace” aikatau kuma Abba ?ko ka mance kai da kake cemin baka shiri da iyayen da suke tura ƴa’ƴansu aiki amma kai da bakinka kake kiramin inje inyi aiki” na faɗa gabana na dukan uku-uku, tabbas inda abinda na tsana bai wuce ace gani a gaban wasu sai nayi musu wanke-wanke da shara sannan zasu bani abinda zanci ba,cikin mamaki da tsoro nace “,Abba mezan gani haka ?kuka kakeyi ?, cikin muryar kuka Abba yace “Ilham bawai ina nufin ki dauwama kina aikin bane, nidai burina a bada kuɗin aikin naki in sun yarda mu fara zuwa asibiti tunda ,har yanzu bamu taɓa tunanin zuwa ba ko za’a dace” yanayin da naga Abbana ya shiga ya jefani cikin wani hali, nace “Abba ka nemo wata shawarar amma wannan batayiba” na miƙe rai a ɓace, a dole ina ganin Abba yanason ya sa a wulaƙantani, yo inba wulaƙantawa ba, yace inje wani gida aikatau bacin nasan zubar da mutunci ne, duk da nasan bashi da cikakkiyar lafiya .

Kai tsaye ɗakina na nufa, na kwanta saman katifata wacce taji zanin gado milk color ,kasancewar a ƙasa take duk da hakan bai hana zanin gadon ɗame ƙatifarba .

Kaina na kifa a kan pilo tare da tuno maganar Abbana ta gurin aikatau “ya illahi” na ambata idona na zubar da hawaye ,daga nan bacci yayi awon gaba dani.

Ganin na shiga ɗaki baba ya ɗogara ƙafarsa cikin ƙarfin hali ya wuce ɗakinsa, zuciyarsa fal baƙincikin ƙin amincewata da buƙatarsa.

Bani na tashi ba sai waje ƙarfe biyu dai-dai ,ina mutsike idona na fito tsakar gida ina cewa “gaskiya nayi bacci mai nisa taɓɓ yaushe rabona dayin wannan barcin ?”,

Bayi nashiga na ɗauki buta na kama ruwa kana na fito nayi alwalah, na nufi ɗaki dan gabatar da sallah, ina idarwa na shafa adu’oi na ,na miƙe na ninke sallahya na cire hijab kana na fito tsakar gida tambayar Abba mai zamu dafa zuwa dare .

Da sallama na shiga ɗakin nasa ,bayan ya amsa na tsuguna kafin nace “,Abba me za’a dafa ɗazu da safe ma raguwar gari nasha da suga” rai a ɓace Abbana yake kallona ,wanda yasa na fara tsorata dan tunda mahaifiyata ta rasu lallashina yake, amma yau shine dayimin irin wannan kallon?, na tambayi kaina cikin tsoro.

“Tashi ki bani guri bana son ƙara jin maganarki” Abba ya faɗa yana nunani da hannunsa, Innalilahi wa inna ilaihirraji raji’un na ambata a fili kafin nace,”Abba ko nayi maka laifi ne?” abinda Abbana baya yimin naga ya kuma yimin wato harara, shidako mugun kallo baya min haka kuma ko me nakeso shi za’a dafa, kasancewar ana yawan kawo mana sadakar abinci .

Jiki a sanyaye na tashi nabar gurin idona tabb da ƙwallah, ina shiga ɗaki suka zubo,

Har aka kira sallahar la’asar Abba bai cemin komai ba, har akayi magrib ko kulani ma bayayi, balle yaji nayi masa magana.

Tunowa nayi, ashe akan ƙin amincewa da buƙatarsa da naƙi yine yasa shi yin fushi dani,

Kiran sallahar Azhar da akayi ne ya sani fitowa daga ɗakina, saboda inason idan nayi alwalah nayi sallah inje gidansu Muhibba ƙawata wace muka gama secondary tare, in aro nera ɗari, ina tsaye ina shirin shiga bayi naji Abbana na sauke numfarfashi kamar wanda yayi uban gudu, da sauri nayi ɗakin cikin mamaki na gansa a zaune yana kuka ga ƙafar na zubar ruwa, “mun shiga uku” na ambata sai kuma na fashe da matsanancin kuka, bansan lokacin da nace “Abba na amince ,na yarda zanyi aikatau domin samun lafiyar ƙafarka”,

Albarka Abba ya dinga samin har cemin ga ɗari biyar in siyo taliya a dafa ko mai da yaji ne, tunda bama rabo da kayan abinci amma yau kam bamu da taliya ta ƙare.

Ganin fara’a a fuskar Abbana yasa nima naji farinciki sosai,

Na miƙe na haɗa wuta na ɗora sanwa, ruwan na tafasa na zuba taliyar, na tsiyayo manja na yanko albasa, bayan taliyar ta dahu na sauke na juye a kwando,na ɗora manja nasa albasa, ina gama haɗa komai na zubawa Abba nasa, nima na zuba nawa.

Ɗakinsa naje munacin abincin muna hira har muka gama, Abba ya miƙe ya kuskure baki, dan gabatar da sallaha ni kuma na dawo ɗakina nayi tawa sallahar, tare da kwararo adu’oi akan samun lafiyar Abbana.

Washe gari,bayan anyi sallah Abba yayi tasa a gida sbda ƙafarsa, ina idarwa naje na gaishesa ya amsa cikin sakin fuska, na fito na haɗa wuta,wutar na kamawa na ɗora ruwan wanka haɗe da ruwan kunu, yanayin zafi na ɗiba naje na sirka kana na nufi bayi kasancewar soso da sabulun yana can, cikin sauri nayi wanka na fito,lokacin ruwan yanata tafasa na dama kunun zuwa anjima nasa gasara na sanya suga,na ɗauko kofin baba na sanya masa na shiga ɗakinsa da sallama, amsawa Abba yayi fuska a sake ,na durƙusa nace “Abba ga kokon naka “Abba ya karɓa yana sanyamin Albarka na fice .

Cire hijab ɗin dana fito daga wanka nayi,na janyo ledar kayan kwalliyata, cikin ƙwarewa irin tawa a fannin ado da kwalliya na tsara kwalliya mai ɗaukar hankali, bayan mayukan dana shafe jikina dasu masu ƙamshi mai daɗi, miƙewa nayi na buɗe akwatin kayana na ciro doguwar rigar milk color anyi mata flawoyi da pink ɗin zane wanda yai matuƙar fito da kyan rigar, bayan na feshe jikina da turare na kawo rigar nasa,nayi rolling ɗin mayafin rigar a kaina tare da kallon kaina a mudubi” murmishi nayi kana nace Alhmdulilh, na ɗauki glass ɗina no respect nasa, wanda ya rufe ilahirin fuskata, duk wanda ya ganni zai ɗauka ƴar wata alhajin ce sbda irin shigar da nayi koni jin kaina nake a sama lol, farin takalmi da farin mayafi na ɗauko kana da sarƙa da warwaro da ɗankunne duk na maƙalasu, tunowa nayi ban sanya agogon hannuna wanda nake gayu dashi sbda a zahiri baya aiki kawai dai ina sawa ne.

Kunsan in mutum yayi wanka,musamman ma yaci tsaleliyar kwalliya baya son ya dinga tafiya cikin rashin tsari, to nima a nawa ɓangaren haka ne, tafiya nake kamar ƴar wani mai muƙami, kofin danasha kunu na fito dashi, Allah yasa nayi wanke-wanke, ina daga bakin ƙofar ɗakina ina kallon fuskata a mudubi na ɗaga murya nace “Abba yanzu ƙarfe nawa?”Abba ya kalli agogon wayarsa kana yace “ƙarfe goma saura minti uku (9:57am) “To” nace, dan ba haka naso ba, naso ace ƙarfe sha ɗaya ne yanzu, na zauna har ƙarfe goma sha ɗaya (11:00) dai dai na fito haɗe da janyo ƙofar ɗakina,naje ɗakin Abba nace Abba zanje gidansu Muhibba “Abba yake kinsan dai banason ki fita ki kai yamma koh ?”Abba insha Allah ba jimawa zanyi ba”,

Abba yace “a dawo lafiya” nafice.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Kai tsaye na fita,

Bakin titi na nufa ina jiran napep,

Wata dalleliyar mota fara sol mai masifar kyau ta biyo ta gabana,saura kaɗan ta bigeni “cike da masifa haɗi da huci na jin haushin abinda mai motar ya yimin, naja tsaki mtsw, sai kuma naga motar ta dawo da baya tayi parking a gabana, rage tsayin baƙin gilashin motarsa yayi, na kusa dashi yace “ƴam mata dan Allah kiyi haƙuri” cikin yamutsa fuska na nuna wanda yake mazaunin driver da hannu kafin na fara zazzaga musu ruwan masifa ina cewa “banda tsabar wulaƙanci da rainin wayo shi drivern makaho ne ?”ko baya gani ne?, inda abinda yafi bani haushi bai wuce, ƙin kulani da drivern yayi ba, sai wani shan ƙamshi yake “Ibrahim sai da nace maka bazan dawo ba bana son raini amma kaga abinda ka janyo mana ko ?”wanda saurayin ya kira da Ibrahim yace “afuwan Mubin, kamar inda ake yabon ahalin gidanku gurin tarbiya da sanin mutuncin juna bai kamata ka sauya naka halin ba” Ibrahim ya ƙarshe zancen yana dafa kafaɗar Mubin.

Niko raina ya gama ɓaci sosai gashi ban sami adai-daita sahu ba, gashi sun wani taremin gaba nikuma nakasa matsawa tsabar inajin ruwan masifa.

Ibrahim ya leƙo da kansa, cikin sanyaya murya yace “ƴan mata kiyi haƙuri dan Allah”,

Shiko Mubin ɗin tsaki yaja tare da cewa “aikin banza aikin wofi ni kaga ba tsayawa jiranka zanyi ba “jibeki mitsw”

Mubin yaja mota kamar wanda zai kuma bi ta gabana.

Iya jin haushi naji haushi ji nake kamar zanyi kuka tsabar baƙinciki, gashi inajin kamar inkoma gida.

Kallon jikina nayi naga ai yama watsamin kwatami, na dafe kaina cikin zafin rai nace “anyi shege ɗan kutumar uba Allah sai ya saka min, inhar kere na yawo zabo na yawo watarana zasu gamu, ina tsaka da tunani naji mai napep na cewa “hajiya tafiya ne?”

Idanuwana nayimin zafi nace eh zakaje ɗorayi ?” mai napep yace “naira ɗari” batare da na taya ba nace tom muje ,

Muna tafiya ina tuno wulaƙancin Mubin da bani haƙuri da abokinsa Ibrahim yayi, nuna masa ƙofar gidansu Muhibba, bayan yayi parking nace dan Allah yayi haƙuri in shiga in amso kuɗi “mai napep ɗin yacemin babu komai”.

Cikin sauri na shiga, tare da yin sallama nayi sa’a Muhibba na zaune tana latse-latse a wayarta, gefe kuma mahaifiyarta ce take bawa ƙaninta nono, ina ƙaƙalo murmishi nace “Muhibba bani nera ɗari “mahaifiyarta na washe baki tace “ah Ilham kece a gidan ?”ta miƙomin ɗari biyu, na amsa na kaiwa mai napep ya bani chanji,

Dawowa nayi ina murmishi nace “Ummi ga chanjin “Ummi tace “kibarshi kawai Ilham muje ciki” Muhibba tana dariya ta fara tsokanata tana cewa “wannan wankan fa ?”nayi dariya kafin nace “,na zuwa gidanku ne” muka shiga ɗakin Ummi dukkanmu,

Bayan mun gaisa da Ummi ta tambayeni ya jikin Abbana, nace mata yaji sauƙi, daga nan ta fice muka sha firarmu nida Muhibba “ya na ganki wani iri kamar kinyi ciwo gashi idonki kamar kinyi kuka ?”Muhibba ta tambayeni,

“mtsw Muhibba na haɗu da wani shege wanda kansa ke rawa walhi da tuni kunji labari yasha ban ban an kaɗeni “Muhibba ta dafe ƙirji tana cewa” na shiga uku garin yaya “cikin ƙosawa da bada labarin, sbda bana son in dinga tuno abinda yayimin yasani cewa “iskanci kawai “,

Bani nabar gidansu ba sai da muka yiwa Ummi gyaran ɗaki da wanke-wanke, muka sake gyara ɗakin Muhibban, kasancewar gidan babba ne, yasha siminti ɗakuna biyar ne a gidan, ɗay na Ummi ɗaya na Muhibba ɗaya kuma na baban Muhibba ɗaya na baƙi ɗayan kuma yana mazaunin kitchen ne.

Bayan mun sanya turaren wuta a gidan lokacin munyi sallahr Azhar muka shiga kitchen muka fere dankali na hausa muka soya, kasancewar sunada miya.

Idan naje gidansu Muhibba sai ka rantse gidanmu ne,

Ƙarfe 6:pm na ɗauko mayafina ina cewa “Abbana yace kar in daɗe lallai yau zansha faɗa sosai” Muhibba tasa dariya tana cewa “Ilham akwai tsoro gaskiya, to gashi bakici abincin ba ai saiki tsaya dan bazaki tafi bakici ba” Ummi na jinmu tana dariya, har nayi hanyar waje Ummi ta ƙwalamin kira na amsa kana nazo, baƙar leda naga ta miƙamin tace “aiko gashi na ƙulle miki a leda” murmishi nayi ina tattaba dankalin kana na rufe baki ina cewa “Ummi harda miya?,

Ummi tace” eh to ki gaida baban bak kice ina gaishe shi “,

Muka fito tare da Muhibba muna tafe muna hira, sannu a hankali muka iso bakin titi na tari napep zuwa anguwarmu Rijiyar lemo, Mukayi sallama da Muhibba.

Ina komawa gida na rangaɗa sallama, duk da nasan zansha faɗa,

Shiru naji babu alamun motsin Abba a gidan, cikin ƙanƙanin lokaci na tsorata dan ko sallahar magrib ba’a kira ba ana harama, a iya sanina tunda Abba ya haɗu da ciwon ƙafarnan ya dena yawan fita amma yau ina yaje ?, na tambayi kaina batare da tunanin ai babu wanda zai ani amsa ba.

Ban kawo komai a raina ba sbda banji wani yanayin damuwa a jikina ba, dan haka na wuce ɗakina na buɗe kana na ajiye dankalin cikin roba, fitowa nayi tsakar gida ina mai cire no respect ɗin idona nahau tunani,

Kiran sallahar magriba da akayi ne ya sanyani miƙewa naje na ɗauro alwlah na dawo na shimfiɗa sallahya na kabbara sallah, ina idarwa na fito tsakar gida na ɗauki kujera ƴar tsugunno na zauna tare da rafka tagumi, abinda ya fara yimin ciwo shine rashin waya da bani da ita, har akayi sallahar isha’i aka idar har ƙarfe tara Abba shiru, babu shi babu alamunsa..!

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

 

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*

_Ummu Affan_

 

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*

_Ummu Maher_

 

3, *GUNTUN GORO..*💥

_Mom Islam_

 

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

_Mrs Bukhari_

 

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*

_Miss Hajo_

 

 

Guda ɗaya N300

Guda biyu N500

Guda uku N600

Guda huɗu N700

Guda biyar 1k

 

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

 

 

Fatima Rabiu Sunusi

0037219728

StanbicIBTC Bank.

 

 

Shaidar biya tanan 👇

0810 433 5144

 

 

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

 

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

 

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

 

Guda biyar 1000f

Guda huɗu 700f

Guda uku 600f

Guda biyu 500f

Guda ɗaya 300f

Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp

+227 84 50 64 76

 

 

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

[01/09, 2:15 pm] +234 803 192 1625: *💥GUNTUN GORO..!💥*

 

 

_Zainab Habib(Mom Islam_

 

 

*✨TEAM GAWURTATTU BIYAR*

 

 

Dama gareku masu son a tallata musu hajarsu cikin sassauƙan farashi suyi magana ta wannan number 08141799224

 

 

Free page 3-4

Cikin tsananin damuwa na fice, kai tsaye shagon Dauda dake kallon ƙofar gidanmu na nufa, ina zuwa na samu da mutane na nemi kan dogon bencin dake ajiye a gefe na zauna tare da rafka uban tagumi, leƙowa Dauda yayi cikin zolaya yace “,ƴar Abba me kikeso nasan dai bakya wuce kayan kwalliya .kasancewar yana siyarda su cosmetics ne,

Niko nafara nisa a tunani sbda a halin yanzu Abbana kawai nake tunani, tunda naga dare yayi.

Ganin bance komai ba,

Cikin ɗaga murya Dauda yace “ƴar Abba…

Da sauri na ɗago jajayen idanuwana na kallesa kana nace “na’am “,

“Akwai damuwa ne na ganki haka ƴar Abba..”

Nace “ɗazu na fita nabar Abbana a gida, nadawo kuma na samu baya nan “,

Na ƙarashe magnar ina share hawayen dake sintiri a fuskata tashi ɗaya.

Gani nayi Dauda ya fito ya zauna can nesa dani sai naji yace “haba ƴar Abba ai da kin kirashi a waya da kinji inda yake “,

Nidai burina kawai inji abinda ya sami Abbana sbda kwata-kwata hankalina ba a kwance yake ba.

Dauda yace “ai wani Alhji ne yake taimakawa marasa lafiya shine Abban naki suka tafi shida Malam Ahmad, sbda akwai babban asibiti a cikin gidan bayan haka ma ina tunanin yabawa Abbanki gida a cikin gidan nasa, kinsan gidan kamar gari guda yake “,

Tunda Dauda ya fara magana nake jin zuciyata na zafi, duk da nasan taimakawa Abbana za’ayi to ni me yake nufi dani ?,in zauna a gidan ni ɗaya ko kuma kawai ya daina sona ne, bayan kafin in tafi sai da nace masa na amince zanje aikatau ɗin.

Maganar Dauda ce ta dawo dani daga tunanin dana fara tafiya, na miƙe jiki a sanyaye nace “to na gode barin koma gida “,

Tsabar baƙinciki ne ya hanani kiran Abba a waya, na koma gida naci kuka na godewa Allah, haka na kwanta banci komai ba,

Kiran sallahar asbha tare da ruwan da naji anfarayi ne ya tasheni, sbda tashi ɗaya gari yaɗau sanyi, abin rufa na ɗauka tare da fitila naje nayi alwalah na dawo na kabbara sallah, ina idarwa nayi adu’oi na ninke sallahyar tare da komawa na kwanta dan ji nake kamar bani da lafiya.

Bani na tashi ba sai da gari yayi haske sosai na miƙe ina salati, na ɗauko dankali na da na kasaci tsabar bakinciki, ba tare da na yi masa komai ba, na juye a kwano nasa miyar Allah ya taimaka batayi tsami ba na faraci.

Ina gamawa na ɗauraye kwanukan naje na hura wutar ruwan wanka, wutar na kamawa na ɗora ruwa, cikin ikon Allah yayi zafi na juye naje nayi wanka, ina fitowa na wuce ɗaki da gudu sbda sanyi da akeyi.

Duk da bacin ran da nake ciki bai hanani yin kwalliya ba, duk da yau ba wata kwalliya nayi ba, bayan mai dana shafa sai powder da tozali dana sanya a idona, na nufi gurin kayana na ciro doguwar rigar ta atamfa mai ratsin blue da fari tana ɗauke da manyan flowers, anbi kowanne gurin ado da stone fari mai ƙyalli, kasancewata mai jiki amma ba can ba, da tsayi dai-dai misali yasa rigar tayimin ɗass dama ɗinkin agwada ne.

Bayan na gama shirina na nemi guri na zauna na fara tuno maganar Dauda mai shago, dayace min wai Abbana yana gidan wani Alhji kuma zai taimaka masa,

“Shin Abban yasan Alhajin ne? ko kuma ciwon ƙafar ne ya ishesa “,ni kaɗai naketa sumbatu na haɗe da fashewa da matsanancin kuka.

Sallamar malam ahmad ne ya sanyani miƙewa ina share hawayen fuskata da hannu badan zanyi tunanin hodar dana shafa ta goge ba sbda ina cikin damuwa.

“Wa’alaikumussalam”

Na amsa masa fuska a tamke, a iya tunani ne shine yayiwa Abbana hanya, tunda gashi shi ya dawo amma Abbana yana can.

Har cikin gidan ya shigo ya tsaya a bakin ƙofa yana mai kallona haɗi da cewa “,Ilham Abbanki ne ya aikoni, yace wai ki shirya za’azo ɗaukarki da misalin ƙarfe ɗaya na rana “,

Kallonsa kawai nake sbda, tsanarsa da nakeji yasa magana ma na kasa yi masa tunda haka ya zaɓarwa Abbana duk da nasan Abban ba yaro bane.

Cikin takaici na buɗi baki kamar mai koyon magana nace “to”

Na koma ɗaki, shima ya fita.

Ina nan zaune a ɗaki in saƙa in warware har lokaci ya tafi,

“Nakasa gane inda Abba ya dosa, yana nufin zamubar gidannan kenan mu koma gidan wani?, wannan ai ƙasƙanci ne “,

Na faɗa ina mai jin ciwon tafiyar da Abbana yayi.

Kiran sallahar ƙarfe ɗaya danaji anyi ne yasa gabana tsananta faɗuwa na miƙe ina ambaton sunan Allah, gashi kaf garinnan babu danginmu sai ƴan uwa da abokan arziƙi, “to gurin wa zani ?wazai taimaka min ?” da wannan tunanin naje na ɗauro alwalah na dawo na kabbara sallah, ina idarwa na dinga kwararo adu’a akan idan tafiyar nan tawa ba alkairi bace Allah ya wargatsata.

Horn ɗin mota da naji a ƙofar gidanmu ne yasa gabana tsananta faɗuwa na miƙe kamar mara gaskiya ina ta zancen zuci.

“Aslamu alaikum ” naji an rangaɗo sallama batare da nasan maiyin sallamar ba, na amsa da wa’alaikumus salamu “na yafo ƙaramin mayafina na fito domin inga mai sallamar.

Ina fitowa naga wani matashi hannunsa riƙe da mukullin mota yana kallona, nima kallonsa nake daga ƙarshe “nace kana son wani abu ne ?”

Drivern yace “dama ance inzo mu tafi ne ” mtsw naja tsaki, a hassale nace inji wa ?nifa babu inda zani kaje ka cewa Abban ni babu inda zani karma ka kuma dawoww idan ka sake dawowa wallahi sai nayi maka ihu ince waiyo ga kwarto “.

Dajin haka driver ya haɗe hannayensa

biyu alamun ban haƙuri yace “naji bazan kuma dawowa ba, amma kizo o mu tafi jikin mahaifinki ya tsananta “,

Abinka da ɗa da uba nayi sauri na shiga ɗakina na ina kuka na ɗauko wata ƴar ƙaramar jakata wacce ke ɗauke da kaya kala huɗu sai hijab biyu da niƙab da safa na fito ina cewa “muje “muryata har rawa take.

Bayan drivern ya shiga nima na shiga gidan gaba muka shilla titi.

Cikin hukuncin ubangiji muka iso Sharaɗa, a baki wani tangamemen gida naga drivern ya ɗan tsaya yana danna horn alamun a buɗe masa, niko sai ƙarewa tsarin gidan kallo nake, har ga Allah gidannan ya haɗu, sai kace ba’a talauci a duniya ?” na tambayi kaina ina daɗa ƙarewa gidan kallo kamar ƴar ƙauye .

Tafiyar da motar naji tanayi ne ya sani, mayar da hankalina ga inda muka dosa,

Muna shiga sai na raina kaina, sbda iya haɗuwa gidan ya haɗu, gashi ƙato ga flawoyi masu kyau ga gurare daban daban, kama daga gurin wanka harda gurin lilo, can gefe kuma wata haɗaɗɗiyar kujera ce mai masifar kyau.

Bayan drivern yayi parking yayi min izini da in fito, na fito da ƴar jakata wacce na ɗora a kan cinyata tun shigata mota,

“Biyoni muje ciki”

“To “nace masa ina bin duk inda naga yayi.

Wata hanya mukabi wacce ta sadamu da haɗaɗɗen palon gidan, nanfa naci gaba dabawa ido abincinsa ta fannin kallon kujerun dake zagaye a palon, daga ganin tsarin gidan zaka tabbatar da naira tayi kuka, balle ka shigo ciki,

“Kizauna ”

Drivern yace min na zauna kamar inda ya faɗa.

Gani nayi ya tafi ya barni, bakajin ƙarar komai sai na AC daTV, a halin yanzu kallonTV baya gabana sabda, burina kawai inji inda Abbana yake,

Na jima a zaune, kafin wata farar mata mai jiki a ƙalla zatayi shekaru hamsin ta fito, farace tass fuskarnan tata tasha fashin goshi, hannunta kuwa yaji zobunan gold, cikin fara’a ta ƙaraso ta zauna kujerar dake kallon tawa kafin tace “ashe har kun iso “,to waye ya faɗa mata?”,

Katse tunanin nawa nayi da cewa “eh ina yini hajiya “,

“Lafiya lau ya karatu ya ƙoƙari “,

Na amsa da lafiya lau ina mai sunkuyar da kaina ƙasa.

Miƙewa naga hajiyar tayi taje gaban wani katon fridge mai rijiya ta ɗauko min ruwan gora, ta buɗe wani bokiti ta ɗibo min cincin da ta ajiyemin a gaban wani tabur dake gabana, har yanzu bata zauna ba naga ta wuce ciki, bata jima ba sai gashi ta fito hannunta riƙe da plet na abinci, mai ɗauke da shinkafa da miya da vegetable, ta ajiye a gabana.

“Kici ƴata nasan ba lallai kinci abinci ba ”

“To “kawai nace na fara cakular abincin kamar wacce take koyo,

Ban wani ci da yawa ba na ajiye cokalin nasha ruwa, ina jira inji musabbabin kawoni gidannan amma har yanzu banji tace “komai ba “,

Sai da muka ɗau tsawon lokuta a zaune kafin naji tace “kece Ilham ko ?”

Na amsa da “eh hajiya nice “good babanki ne yasa a taho dake a bisa yardarsa akan cewar zaki fara aiki a gidannan, da kuɗin da za’a biyaki a kaishi ayi masa magani “,

Gabana na tsanannta faɗuwa idona ya kaɗa yayi jajir nace “eh na sani ina Abban nawa ?”

Hajiyar tace “yana hospital ana yi masa aikin ƙafar “,

“Wato har Abba yakai kansa batare da ƙara shawartata akan ko na amince da aikin na ko ?hmm lallai Abba “,

Na faɗa ina ce mata “to Hajiya ko zan iya ganinsa ?”,

“Eh zaki iya ganinsa sai dai ba’a gidannan yake ba yana asibitin Murtala “, a razane na dafe ƙirji tare da cewa “asibitin Murtala kuma ashe abin yayi yawa, nida akace yana asibitin gidannan “na faɗa ina share hawayen da suke ambaliya a fuskata, Hajiyar ta ɗaga waya ta danna number driver, bai jima ba yazo ya durƙusa a gabanta, cikin bada Umarni Hajiya tace “ka kai Ilham asibitin da aka kwantar da babanta, driver yace “an gama hajiya taso muje “na miƙe jiki a sanyaye, dole nabar kayan anan na wuce muka shiga mota muka lula asibitin.

Muna isa, driver yayi parking tare da cewa “kiyi sauri lokacin ziyara ya kusa ƙurewa “nayi azamar fitowa, yana gaba ina binsa a baya, har muka shiga wani ɗaki mai lamba 5, muna shiga na hango Abbana a kwance an naɗe ƙafarsa da bandeji , iya yau ya rame sosai, nikam na rasa ganewa shin ciwon ne ya tashi ko kuma shine ya kawo kansa har yanzu ban sami mai bani amsa ba, tarin da naji yanayi ne ya sani ƙarasawa kusa dashi ina cewa “Abba sannu ya jikin ”

Cikin murya irin ta marasa lafiya Abba yacemin “jiki da sauƙi na warke yau akayi aikin zuwa jibi idan sunga jikin ya warke sunce zasu sallamemu “,nace to alhmdulilh Abba yanzu gidan aikin kenan zan koma ?”Abba yacemin eh man ai sai kinyi na wata bakwai “,na zaro ido, saboda kar in tayarwa da Abbana hankali yasani ɓoye damuwata nace masa karka damu Abba, lafiyarka ta fiyemin komai a duniya, farinciinka shine nawa, samun lafiyarka itace farinciki na “Abba ya shafi kaina yana sanyamin Albarka, shigowar likitan dake dubashi ne yasa na koma kan kujera, sai yanzu driver yace “baba ya jikin dai ?” Abba ya amsa fuska a sake, “na sami sauƙi alhmdulilh “,

Driver yace “zamu wuce toh “babu inda na iya haka muka dawo gidan su Hajiyar, wannan karon na sameta ita da wani saurayi wanda nake tunanin kamar na san fuskar, nazari na shigayi tare da tinanin a ina na taɓa ganinsa ?”,

Kyakkyawan saurayi ne dogo fari tass ɗan shekara 32yrs fuskarsa masha Allah, a taƙaice dai shiɗin ba mummuna bane,

Kansa na kan cinyar hajiyar yayinda gangar jikinsa ke kan kujera 3 sitter, da sallama na ƙarasa kafin nace “hajiya mun dawo “Hajiyar na faɗaɗa fara’arta tace “ƴata zoki zauna “, ta nuna min kujera mai zaman mutum ɗaya, yaron nata da naji ta kira da my son naji yace “momy wannan kuma wacece ?”,hajiyar ta shafi kwantaccen gashin kansa kafin tace “,ka mance maganar da akayi da dadynka jiya akan ƴar aiki da kuma rashin lafiyar mahaifinta ?”gani nayi ya taɓe baki haɗi da galla min harara, nikuma sunan data kirani dashi ne yai mugun ɓatamin rai, wai ƴar aiki mtsw.

“Oh momy yanzu taje ta gyaramin part ɗina Ibrahim na nan zuwa anjima “waro ido nayi, sbda a halin yanzu na ganoshi sarai, ga kuma yanayin maganarsa kamar ta mace, wato shine ko ?”lallai zan gasa maka aya a hannu ” na faɗa ina kawar dakai daga kallonsu.

Nasan shikam bai ganeni ba, amma ni na ganesa, sbda wannan ƙaton gilashin danasa wanda ya mamaye ilahirin fuskata, jira kawai nake inji hajiyar tace “tashi ki tafi “, amma shiru ina zaune kamar gunki, ganin hajiyar bata sake wai-wayata ba, yasani kallon TV badan ina fahimtar abinda akeyi ba, kawai dai mutanen dake drama nake kallo a tashar arewa24.

Bayan wasu sa’oi,

Najiyo muryar hajiyar na cewa “ke Ilham jeki gyara part ɗin my son anjima yanada baƙo “na amsa da toh “dama burina inbar gurin nagaji da zama agurinsu,

“Ina ne part ɗin?”

“My son oya jeka nuna mata yau tazo fa “,

Fuska a yamutse haɗi da kallon ƙyama da wulaƙanci, ya yaso bai cemin komai ba ya fita a ƙofar shigowa palon Hajiyar nima na bishi,

Mun ɗanyi tafiya sannan naga mun iso wata ƙofa mai ɗauke da mudubi, yana zuwa ya danna wani abu a jikin bango naga ƙofar ta buɗe, ya shiga nima na shiga, irin haɗuwar palon hajiya kusan iri, ɗaya da nasa, amma a nashi palon akwai wani tangamemen Frame mai ɗauke da photonsa wanda ya baiyanar da kyawun fuskarsa, gashi gunin ban sha’awa murmishi yake, niko nace “duk wannan cin maganin da yakeyi dama yana dariya ?”,

“Inkin gama nuna ƙauyancin kizo ki wanke min toilet ki gyaramin ko ina nabaki 30mins “rai a ɓace na kallesa sai kuma na sunkuyar da kai, banason in nuna raina ya ɓaci ya sami damar turamin haushi, batare daya nunamin toilet ɗin ba ya fice yana waƙa ƙasa-ƙasa.

Zubewa nayi akan kujera tare da zuba tagumi nace “shikenan na ƙanantar da kaina na shiga uku, koma zagina mutan gidan sukayi haka zan daure Allah ka wadatamu “,

Cikin azama na miƙe na buɗe wata ƙofa wacce nake da tabbacin nan ne bedroom ɗinsa, sbda gado dana gani da mudubi da drowa, gadon na fara gyarawa kafin nace na wanke toilet nama rasa ya zanyi in tsara abinda zanfara, duk abinda yazo min shi nakeyi, tashi ɗaya na gama gyara komai cikin hanzari na kunna burner nasa turaren wuta ƙamshi ya game ɗakunan duka..!

 

 

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

 

 

 

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*

_Ummu Affan_

 

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*

_Ummu Maher_

 

3, *GUNTUN GORO..*💥

_Mom Islam_

 

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎

_Mrs Bukhari_

 

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*

_Miss Hajo_

 

 

Guda ɗaya N300

Guda biyu N500

Guda uku N600

Guda huɗu N700

Guda biyar 1k

 

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

 

 

Fatima Rabiu Sunusi

0037219728

StanbicIBTC Bank.

 

 

Shaidar biya tanan 👇

0810 433 5144

 

 

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

 

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

 

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

 

Guda biyar 1000f

Guda huɗu 700f

Guda uku 600f

Guda biyu 500f

Guda ɗaya 300f

Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224

 

 

 

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.