Hadin Iyaye Hausa Novel Complete

Hadin Iyaye Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: HADIN IYAYE

Bismillahir rahmanin Rahim

 

Ya Allah yanda kabani dama nafara rubuta wnn littafi ubangiji yagwadimin na gamashi lafiya

 

Page 1

 

 

A unguwar tsamiyar dila sokoto, yan mutanen unguwar sunta shi da bidirin daurin Auren ya yansu, mutane bila Adadin sun shaida daurin Auren Hanifa da Muhammad bisa ga sadaki naira dubu hamsin, lakadan ba Ajalan ba”ga banbadawa suna ta banbadanci su, can natsinkayo Ango yaci uwar shadda sky blue Sai maiko take fuskarsa ba yabo ba fallasa bazaka iya gane Yana cikin farin ciki Koh Akasin hakaba, gadai shinan tsaye ya hadu iya haduwa duk inda namiji ke amsa sunansa yakai namiji, yasha bakin glass Yan uwa nata farin ciki Abokanan Ango nata Kai kawo Baki yaki rufuwa nayo gefen uwayen taron mahaifin Ango Alh Kabir

Da mahaifin Amarya Alh Abubakar daka kalleso kasan suna cikin farin ciki Mara misaltuwa” cikin wata runfa suda Abokanansu Ansha Ado cikin farar shadda Yar ubansu, gefen Ango koh wani bayan ko wani minutes sai yaja tsaki yana yamuna fuska” Amir dake gafenshi ne ya kallesa yace” ya Akayine naji kana jan tsaki Ango a madadin farin ciki, yaune fa aka shaida daurin Auren ka da masoyiyar ka, ai yaka mata ka saki fuskar ka adan dinga mana smile ko”

Shidai baice masa komai sai ma kikewan da yyi ya kallesu tare da tabe baki yace ” toh idan ka gama shirmen maganar taka zaka iya tahowa, kuma idan zaku saya sauraron wanan dan iskanne to kuyi tayi ni dai banda lkcn ku” yana fadar yayi gaba abunshi”

dariya suka kwace dashi suna cewa” mun ganoka ai borin kunya ce ke damun ka”

 

 

 

 

 

Cikin gida Koh da gudu kanwar Amarya Mai suna Rufaida tafito Tana kwalawa kakarsu Inna kira, Inna! Inna !! zo kiga halinda Hanifa take ciki” Inna ta tashi da sauri tai hanyar dakin cikin tashin hankali, tana shiga dakin ta kalle Hanifa kwance tamkar ba Rai Ajikinta, Akidime ta karaso inda take kwance ta riketa, tana kiran sunan ta amma shiru k’ikeji, cikin tashin hankali tace ” ke jiki kiramin mahaifiyar ku” dato Rufaida ta fita da gudu, Umma dake kokarin shiga kitchen ne ta kalle Rufaida dake Numfashi tana haki tace ” me yake faruwa haka?”

halinda Hanifa take ciki ta fada mata” innalillahi wa inna ilaihi rajiu’n!!” Cewar da sauri suka nufi dakin, Umma nashigowa tayi wurin Hanifa da sauri Tana girgizata Amma ba’alamar motsi tattare da ita dukan sun rude sun taru a Akanta kowa na kiran sunan ta Amma shiru kakeji da sauri Inna tace” Rufaida takira min Umar ” mahaifin su kanen” Akai Hanifa Asibiti da sauri Rufaida tafita cikin taron Yan daurin Auren ta Kira Baba Umar Shima cikin tashin hankali suka shigo gidan, yana yinda take ciki Akidime shi sosai gashi yazo dakin ya taradda halin Hanifa take ciki Inna tace “yakira mata Muhammad da sauri yadauki waya ya kira Muhammad yace yazo yaga halinda Ake ciki nan da Nan Sai gashi dama Yana dayan bangaren Acikin gidan bai tsawa wata wata ya dauki Hanifa yafito da ita dama Baba UMAR ya dauko mota yasata Shima yashiga Inna tashiga da Umma jummai ta shiga yaja motar Aguje suka nufi hospital uduth da sauri likitoci suka karbeta Aka shigar da ita emergency room, su kuma tsaya sukayi kowa da addu’ar da yake”

See also  Hanyar Magance Wannan Dabi'ar Na S*x Call/Chat

 

 

 

 

 

 

Agida Ko hankalin kowa A tashe yake saboda halinda Haneefah take ciki, kowa da Abinda yake sakawa Acikin zuciyarshi” Sai dai fatan Allah yabata lfy”….su big father da Baba ma sun tafi Asibiti suga halinda Ake ciki saboda Sai daga baya sukaji halinda Ake ciki”…….

 

 

 

Asibiti kuwa likitoci sun d’ukufa a k’anta ganin sun daidata nunfashita da ayanzu yake sama² da kyar dai suka samu numfashinta yadawo dai dai, kowa Sai sharce zufa yake sukai mata Allurar bacci suka samata Karin ruwa sannan suka fito Suna fitowa Baba da big father suna isowa sukayi wurin su” Doctor Bello yace” su sameshi office yana fadar haka ya wuce suka bishi a baya gaba Dayan su harda MD suka shiga office din”

Doctor yanunama big father wurin zama ya zauna yafara bayani yace ” Alhaji gaskiyar yarku Tana dama da damuwa Mai yawa inkunsan Abinda yake damunta gwanda Amaganceshi da wuri wuri Tana gaf da kamuwa da ciwon zuciya maitsanani” su dukansu suka kalle juna cikin jimamin Al’amarin sukacema Doctor insha Allah za’akiyaye yace” Masha Allah yanzu munsamu numfashinta ya dai daita munyi mata Allurar bacci yanzu zamu jira tatashi muga yanayin jikinta nata idan da sauki saimu Bata sallama idan da saura gaskiya saita Dan kwanta Alura da lafiyarta kwana biyu” sukace ba damuwa…”

 

A gida hankalin yaki kwanciya Saida suka kira Abba yasanar musu halinda Ake ciki hankalinta wakwanta sannan tagayawa saura Sunnan kowa yasamu natsuwa Akaci gaba da jimami….

 

 

 

Su Abbane suka shiga dakin da Haneefah take suka samu Tana bacci suka fito sukace zasu koma gidah sunbar mutane suna jiransu Inna tace “zata zauna suje kawai sukayi Allah yakara sauki sukawuce sukace zasu dawo Anjimah suka tafi Akabar baba Umar da Inna da MD

See also  Bakar Daula Hausa Novel Part 1

 

 

MD yashigo dakin yazuba mata ido Yana kallonta yaga duk tarame tayi baki a rasa yace”ko Uban me yasa mata damuwar ohoo” wani zuciyar yace “Auren ka Man” Nan take yaji ransa na Kuna saboda kiyayyar da take Masa take cikin wnn halin, dan k’aramin tsaki yyi dabai fitaba ya rinse idonsa da sukayi jajir ya fada tunani yanda zaman su zai kaya” ta bashi da Baba Umar yyi ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya fada” Baba yace “yazo suje yabar mutanensa haka yafito daga dakin sukabar dije da zummar zasu dawo Anjimah Suma dije tamike tai dakin Tana kallon jikar Tata cike da tausayi ya za’ayi haka Allah yakaddara koba komai MD yayanta zai riketa Amana Sai dai rashin shiri da basuyi tsakaninsu

 

Hmmmmmmn haka Inna taja numfashi tafada tunanin Yaya makomar Auren zata kasance.

 

 

Page 2

mmn wa yannan yara Yaya zasu kasance ita dai Haneefah tsiwa da rashin kunya, shi kuma Muhammad miskilanci da son girma, bayason raini ko kadan gasu San basashan inuwa guda to sudai Allah yagani iyayen yarannan suna son damkon zumuncin yakara haduwa sosai shiyasa suka hada wnn Aure bayan Yan matsaloli da Aka samu,

kallon Hanifa dake bacci tay tace Allah yabaki lfy Haneefah

 

 

A gida kuwa Muhammad na shiga dakinshi ni yarinyar Nan zata nunama duniya Bata kaunata, harda Suma Dan An daura Aurena da ita, saki yaja yana sauke Ajiyar zuciya maikarfi, dafe kansa yyi da yake matukar sarawa masa, zuciyarsa nazafi idanunsa sunyi jajir Yana lumshe idonsa kwanciya yyi yana tunanin…. sai ga Amir yashigo Yana tambayarsa jikin Haneefah yace” da sauki” okay Allah ya bata lafiya, gasu hafis can suna jiranka zasu wuce tunda ita Amaryar batada lfy, har A tashi sabon bikin tarewa cike da shakiyanci “Koh motsawa bayyi ba bale yay tunanin zai tashi a hankali yace “kaje kawai kasan yanda zakayi ni banajin dadi” Zaro ido Ameer yace” ai dole tunda masoyiyarka batada lfy” ya fada yana dariya” shidai baice masa komai ba” toh my man nidai bari baje wajensu Allah ya baku lafiya Ango da Amarya” da harara ya bishi dashi har ya bar dakin, lumshe gajiyayyun idanunsa yyi domin har wani zazzabi_zazzabi yakeji a jikinsa”

See also  Ni da Malama ta Hausa Novel

 

 

Su big father na dawowa Aka Ida sallamar kowa suka zauna tattau nawa da junansu Akan tarewarsu Haneefah idan taji sauki gwanda Ahade waje Daya Koh zasu sasanta kansu

 

 

Asibiti kuwa Inna sai sheshshekan”kuka take Haneefah kawai taji ya tabbar ta mata ta tashi’ t Haneefah kiyi hkr, nasan watarana zakiyi Alfahari dashi ba Alfahari nakeba Ina da tabbacin bazaki tabasamun miji irin Muhammad ba kiyi hnkr ki rungumi wnn Auren kodon farin cikin iyayenku” Shi yayi biyayya yaji maganar iyayenshi kema kiyi biyayya ki Amshi taki kaddarar nasan zakiyi Alfahari da wnn Auren, taci gaba da Bata Baki harta samu tai shiru takira.doctor yazo yaduba yaga babu damuwa yarubuta musu magani ya sallamesu, ta dauko waya tai Kiran baba Umar tace yazo yadaukeso An sallamesu Sai gashi yazo yadaukosu suna shigowa Daya Yan biki suna Nan Aka wuce da ita bangaren Inna Anata shigowa Ana mata sannu

Tana Amsawa Amma zuciyarta na mata kunah sosai idan tatuna waih Andaura mata Aure da Yaya MD kuka kawai tafashe dashi sosai tamkar ranta zaifita yazatayi zaman Aure da Yaya MD Wanda baya kaunarta” ga shegen girman Kai da miskilanci tsiya” duk suka hadu Sai yayi mata mugunta. sannan Ace zasuyi zaman Aure tayay? tayaya Inna tashigo tasameta Tana kuka sosai tahau lallashinta dakyar’ tasamu tadaina kuka tajata suka shiga toilet tahada mata ruwan wanka tace tayi wanka tafita tabarta tabata lokaci kafin tayi wankan tai brush tafito tadauko kayanta dake dakin Inna tasaka saiga Inna tashigo da Abinci farfesun kan rago yadahu luguf Sai tashin kamshi yake da tea da yaji kayan kamshi tace Maza taso kici kiji karfin jikinki haka tasaukoh tafara Shan tea hanjinta suka warware tafara cin kan Saida taji cikin yacika sannan ta ture takoma takwanta lokacin magriba tagabato kowa yafara watsewa Sai wa yanda zasu kwana Nan.

 

 

A bangaren Muhammad Koh yana nan Yana fama da zazzabi sosai haka yatashi ya dauko magani yasha yayi sallah magrib yakoma ya kwanta Yana rawar dari ya wani kudundune cikin bargo……………..

 

 

 

 

*More comment and share more typing wollah*

 

 

*Yanzu wasan zai Fara hadin kanku nake bukata*

 

*Zeenbash ce*

 

 

 

1 thought on “Hadin Iyaye Hausa Novel Complete”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top