Hausa Novels

Hafsat Hausa Novel

Hafsat Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

HAFSAT

 

*RUBUTA LABARI**

*MAMAN SHUREM*

 

 

*🌙MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙*

 

 

*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’*

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~~~~~~~~

 

 

Gajeren Labari ne ban yi wannan littafin dan cin zarafi wani ko wata ba sai dan In bawa masoyana nishaɗi

 

 

 

*BABI NA DAYA*

Hafsat Hausa Novel

 

 

Tafiya take yi cikin sauri dan Jiya ta makara gashi yau ma haka ta san Yau Hajiya Saude sai ta yi mata masifar nan da ta saba yi ma ta, haka ta ƙaraso gida zuciyarta cike da fargaba kai tsaye wani tangamemen falo ta shiga, wanda zan iya kiran shi da Aljannar Duniya Saboda tsarinshi, da haduwar shi bakinta ɗauke da Sallama ba ta jira an amsa mata ba dan tasan babu kowa a falon, wata ajiyar zuciya ta yi sannan ta fara goge -goge ba ta dauki wani lokaci ba ta gama, sannan ta kunna turaren Wuta kicin ta tafi shi ma sai da ta gyara ko ina sannan ta fito,zama ta yi akan Kafet din da ya ke a shinfiɗe a tsakiyar falon tare da yin tagumi tana tunanin ko lafiya Hajiya ba ta fito ba,afili tafurta “bari muji ko ba lafiya ba”

zuwan ta bakin ƙofar ya yi dai-dai da fitowar Alhaji Nasir baya ta yi tare da durƙusawa,

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

ta ce”Ina kwana”

wani ƙayataccen murmushi ya sakar mata wanda ita kanta ba ta san kona menene ba, daƙyar ya iya amsawa da “kin tashi lafiya?”

ba tare da ta sake kallon in da yake ba,

 

ta ce”lafiya lau da ma na gama aiki ne to sai naga Hajiya ba ta fito ba shine nace lafiya dai ko?”

murmushi ya yi Akaro na biyu,

sannan ya ce” lafiya ƙalau ta yi tafiya ne amma yau zata dawo”

“to Allah ya dawo da ita lafiya”

Amin ya ce tare da ƙarasawa falon zama ya yi

ya na tunanin Hali irin na Saude wai ace ka na da mata amma da ita da babu duk ɗaya,

amma bakomi zan san abin da zan yi,wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ta re da kiran “Hafsat! Hafsat! Hafsat!” da sauri ta zo tare

da cewa “Alhaji ga ni..

maza ki haɗo min shayi ”

amsawa ta yi da “to Alhaji”

ba yan ya kammala shan shayin ne ya kira ta da sauri ta zo za ta durƙusa dakatar da ita, ya yi ta Hanyar ce mata “A’a ba na son haka daga yau karki kase yi min haka ba na so kinji ko.”

ita dai ba ta ce masa komai ba kai kawai ta ɗaga Alamar to,

nuna mata kujerar da take kallon Wacce yake Azaune ya yi tare da cewa” zauna zan yi magana da ke.” juyawa ba yan ta ta yi akan taga kodawa ya ke magana, amma ba taga kowa ba hakan yasa ta Tabbatar da ita ya ke yi babu musu ta zauna a kan kafet, din da yake a tsakiyar kujerun Falon wanda kana takashi ƙafafunka har shigewa suke yi,

kallonta ya yi tare da girgiza kai sannan ya ci gaba da cewa “ina so kinatsu ki tattara min hankalin ki guri ɗaya saboda ba na son wasa,”

To kawai ta ce ita dai jinshi take yi amma gaba ɗaya tsoro ya mamaye zuciyarta dan Wallahi idan Hajiya ta zo ta sameta, akusa da mijinta tofa kwananta ya ƙare

“Hafsat! Hafsat!!” da sauri ta ce “Na’am”

” kinga ki kwantar da hankalinki Hafsat tam tayarki zan yi”

shiru tayi azuciyarta ta na cewa wacce irin tam baya kuma?, sai da taji ya ce “ko ba za ki iya bani amsar ba ne” ba ta ce komai ba wasa da yatsun hannuta ta ke yi gir-giza kan shi ya yi tare da cewa “kin yi makaranta kuwa?…

ba tare da ta ɗago kanta ba ta ce” na gama furamare sakamakon bamu da kudin da za a biyamin inci gaba shiyasa na haƙura”

shiru ya yi na ɗan wani lokaci sannan ya cigaba da cewa

kina son kici gaba…

ɗago kanta ta yi da nufin yin magana sai ta kasa cewa komai,

shirun da yaji ta yi ne

ya ce ke nake sauraro idan ba ki da ra ayi ne shike nan

zaki iya tafiya abinki”

ɗauke kanshi daga kallon inda take ya yi tare da ɗaukan jaridar da take a kusa da shi,

har ta tashi sai kuma ta dawo kallonshi ta yi cikin sanyin murya ta ce “Um..Eh.. Am dama ina son sai na yi magana da Umma ne duk yan da mukayi zan sanar da kai”

“to sai na jiki amma inaso kar ki wuce yau ko gobe” “in Sha Allahu

godiya tayi masa sannan ta tafi,

cike da zumuɗi ta iso gida Sallama ta yi amma shiru ƙarasawa ɗakin tayi shigarta keda wuya wata ƙara tasa sakamakon umma da tagani kwance cikin Jini, ƙarasawa ta yi inda take cikin matsanancin tashin hankali kuka take ta na faɗin”wayyo Allah na yau na shiga uku Umma karki mutu ki bar ni Umma ki tashi me yasa baki faɗa min maganinki ya ƙare ba, haba Ummna”

jijjigata ta kama yi amma shiru babu Alamar rai A tare da ita, da sauri ta ɗebo ruwa shafa mata A fuska ta yi har sau uku amma shiru nan take hankalin ta ya ƙara tashi,

da sauri tafi to da ga ɗakin dagudu ta shaga gidan su Jamila Ummin su Jamila ta na Alwalah faɗawa jikinta ta yi akiɗime ta ce “dan Allah ku temakamin Ummana zata mutu gata can akwance cikin jini,”

cikin rashin fahinta Ummi ta ce “Subhanallahi me ya sameta haka?”

“nima ban sani ba”

“to tashi mutafi”

Yanda tabar ta haka suka zo suka sameta da sauri suka ɗauketa dama kafin su shigo sun tsaida mai mota da yake abakin Titi gidan su yake,

Haka suka sata amota sai asibiti

 

Hajiya Saude ce da kawarta Hajiya Turai zaune A gaban Boka kallon juna sukayi sakamakon sanar dasu mazajen su za su ƙara aure nan ba da jimawa ba,

hankalin su ne ya tashi cikin tsananin ɓacin rai Hajiya Saude ta ce

“haba boka Warkau ni fa da kai na dogara, amma har kai da bakin ka ka ce mijina zai yi min kishiya Wallahi koda zan yi yawo tsirara ba zan taɓa barin Alhaji ya yi aure ba,

idan ba za ka iya hana shi yin wannan auren ba sai ka faɗa mi In nema wani,Gari da yawa”

ta ƙarasa maganar ne tare da tashi ta ɗauki jakarta ta juya baya za ta fita,

Dariyar boka ce ta dakatar da ita sakamakon ɗakin ya na wata irin girgiza,

 

______lokacin da suka iso asibitin sun yi sa’a an garbe ta babu laifi sun ba ta temakon gaggawa inda aka tabbatar da ciwan Diabetes (ciyon suga) ne, kuma ba ta bin ƙa’idar abincin irin na masu ciwon ,

cikin tashin hankali Hafsat ta ce “likita yanzu idan tana cin abinci irin wanda ake so za ta warke?”

murmushi ya yi wanda ka na ganin sa kasan na tausayawa ne sannan ya ce “In sha Allah amma ki kwantar da hankalin ki za ta samu sauƙi”

“to Allah ya sa likita”

da Amin suka amsa,

 

______Alhaji Nasir kuwa bayan Hafsat ya bi da kallo tare da lumshe idanuwanshi ya ce “ban san so ba sai ranar da na fara ganin ki ban san daɗin so ba sai da kika shigo Rayuwata,

Ban taɓa son wani abu a duniyar nan narasa ba dan haka ina jin ajiki na kema ba zan rasa ki ba zan ci gaba da roƙon Allah ya mallaka min ke, A matsayin Uwar Ya’Ya na”

haka ya yi ta saƙa da warwara har lokacin tafiyar shi office ya yi,

 

Hajiya Saude tsabar fargitar da ta yi ba ta san lokacin da ta faɗa kan Hajiya turai ba,

 

A fusace Boka ya ce “ke baki isa ki yi komai akan auren da mijin ki zai ƙara ba kai ba ke ba ko gurin waye ki kaje sai dai ya yi miki ƙarya kuma idan ba kiyi ahankali ba to duk abin da ya faru dake ke ki ka jawa kanki dan haka abu ɗaya zan iya yi muku shi ne zan mallaka muku su sai yan da kuka yi da su, amma da sharaɗi maganin da zan baku karku bari wani yaga lokacin da zaku sashi”

 

da sauri suka kalli juna tere da haɗa baki su ka ce “mun amince boka in dai zamu ju yasu kamar Masa a Tanda”

 

Dariya ya yi mai firgitarwa tare da cewa

“an gama, to amma wannan Aikin ba irin wancan ba ne dan haka zan shiga ciki kuma ba na son jinkiri”

 

cikin rashin fahimta Hajiya Saude ta kalli Hajiya Turai ta ce “ki fahimtar da ni me yake nufi ne”

 

wani kallon banza ta watsa mata tare da cewa

“kina nufin duk bokayen da kike bi babu wanda ya taɓa kwanciya da ke?”

 

“kwarai kuwa sunfi buƙatar in ba su kuɗi”

“Tab to wannan idan har ya duba yaga Aikin sai ya kwanta da ke to fa sai ya kwanta da ke sannan Aikin ki ya yi kyau dan haka idan ba za ki Iya ba to ni dai zan iya”

 

ta ƙarasa maganar ne tare da shigewa ɗakin

 

MU HADU A CIGABA

 

DAGA ALƘALAMIN

MAMAN SHUREIM



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Hafsat Hausa Novel]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

08117990509

Leave a Comment

error: Content is protected !!