Hausa Novels

Haihuwar Da Namiji Hausa Novel Complete

Haihuwar Da Namiji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: HAIHUWAR DA NAMIJI

 

Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu.

 

 

 

I’m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I’m

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 08066268951

 

 

 

 

 

 

*Page 1&5*

 

 

*_27_6_2022 Monday_*

 

*MEDICAL CENTRE HOSPITAL KATSINA*

 

“Innalillahi wa’inna ‘ilaihirraji’un, wayyo Allah na doctor!!! Mutuwa zanyi kakiraman umma ta ”

 

“Sorry madam sorry, ƙoƙarta kiyi nishi da ƙarfi”

 

doctor jabir ya faɗa cikin tausayawa.

kanta tashiga girgizawa tana zubar da hawayen a zaba.

 

kusan awa biyu suna kanta amma babu alamun zata haihu, kuma ga na ƙudar na yunƙurowa, zufar da doctor jabir yayi ne ya goge tare da duban nurses ɗin dake tayashi aiki yace

“gaskiya matar nan idan muka barta haka zata iya rasa ranta da abinda ke cikinta dan haka aiki kawai za’ayi mata”

 

“hakane sir nima nayi wannan tunanin” cewar sister fati.

 

safar hannunshi ya zare ya jefata a shara yace “Ku shiryata Ku kaita ɗakin operation yanzu, ke sister Fati kije can waje da sauri ki Kira mijinta yazo ya saka hannu”.

 

“OK sir” duk suka ambata kowa ya kama abinda aka sashi.

 

 

Da sauri taƙarasa gareshi tsaye yake yana kaiwa da komowa ƙagare yake azo ayi mashi albishir ɗin ta haiho mashi cikar burin shi, yana ganin nurse ɗin ta nufoshi da hanzari ya isa gareta yace “ya yane? ina fatan ɗana ya fito lafiya?”

batare da ta kula tambayar da yayi mata ba tace “Alhaji doctor yace kaje office ɗinshi da sauri yana jiranka”.

 

babbar rigarshi ya tattare yace “ok”

 

yana shiga office ɗin bayan yayi sallama doctor ya amsa tare da nuna mashi wajan zama, bayan ya zauna yace “doctor ance kana kirana ina fatan ba wata batsalar ta samu *ƊA na ba*?”

 

takarda doctor ya miƙo mashi yace “Alhaji a kwai buƙatar sa hannunka anan domin matarka tana cikin wani hali dan gaskiya ba zata iya haihuwa da kanta ba abinda ke cikinta yayi girma da yawa, sai anyi mata tiyata kana”.

 

amsar ta kardar yayi yace “yo ba dole ɗana yayi girma ba saboda tanacin abu mai kyau mai tsada,ai banasan ta haifaman ramamman ɗa shiyasa nake saya mata komi take buƙata harma da wanda bata buƙata indai zai sanya ɗana girma da lafiya” ya ida faɗa tare da miƙa ma doctor takardar bayan ya saka hannun.

Karanta Littafin Siradin Rayuwa Hausa Novels

amsa yayi yace “Alhaji tunda kuka zo kaketa maganar *HAIHUWAR ƊA NAMIJI* bayan ba mu zamuce ta haifi namiji ba,Allah shine yake bada mace ko namiji ba muba, kawai kayi fatan Allah ya sa ayi aikin lafiya shine kawai”.

 

cike da ɓacin rai yace “kaga doctor banasan wani shirmai dallah ni kaje kayi abinda ke gabanka koko harsai ɗana ya mutu kana zaku kawoman gawa?”

 

kai doctor jabir ya girgiza domin yana ganin alamum wannan mutuman yanada ƙarancin ilimi a taire dashi.

 

da hanzari ya bar officeɗin ya nufi ɗakin da aka kaita.

 

yana shiga tuni nurses ɗin sun haɗa komi shi kawai suke jira domin matar na ƙara jigata da yawa, yana shigowa wasu suka saka mashi rigar da zai sanya domin yin aikin, allura ya fara haɗawa yana cikin haɗata Maryam dake kwance cikin halin mutuwa ta saki wani dogon nishi saiga haihuwa cikin hukuncin ubangiji da sauri doctor jabir ya shiga taimaka mata har ta fiddo ƙatuwar ƴarta, cike da murna nurses ɗin suka ɗauki yarinyar bayan ya dubata yaga ta samu ƙari saboda girman jaririyar yayi mata ɗinki tare da allura dan tasamu nutsuwa kallan su yayi yace ” in kun ƙimtsa ta kuje kusanar da mijinta”

 

bayan sun shirya yarinyar cikin tsadaddin kayan sanyi masu kyau sai santin yarinyar suke saboda kyawunta ga kuma kayanta masu tsada wanda a ƙalla zasukai dubu talatin, hotuna sukaita ɗauka da yarinyar dan baƙaramin burgesu tayi ba, sister Alawiyya ce tayi saurin cewa bari taje takai albishirɗin haihuwar (ita burinta mai kuɗi ya kawo matarshi haihuwa taje ta faɗa domin tana sabomin kuɗi masu tsoka a wajan su) cike da yanga take tafiya tana ƙara hasaso kyautar da zata samu a yau dan taga alamun mutuman mai kuɗi ne sosai jifa sayayyar kayan haihuwar da yayi.

 

tana ƙarasawa gareshi tace

 

“barka dai Alhaji”

“yauwa barka anyi aikin ne?”

 

cikin salon cin ƙuɗi tace “Alhaji albishirin ka?”

 

“goro fari fatt” yafaɗa cikin sauri

 

“Alhaji madam ɗinka ta haihu batare da anyi mata aiki ba”.

 

“cikin zaƙuwa da ƙagara yace “mita haifa??”.

 

idanu ta farfara ta lanƙwasa murya “Ta haifi ƙatuwar budur”…..gamm taji ya nausar mata baki yace “budurwar ubanki ta haifa?”

 

babbar rigarshi ya naɗe haryana tuntuɓe ya nufi ɗakin banka ƙofar yayi ya shiga nurses ɗinda ke riƙe da jaririyar suna ganinshi suka ajeta kan bed ɗinda aka tanadar ma jarirai suka haɗa baki wajan faɗin “Alhaji Allah ya raya”

 

ko kulasu baiyi ba ya ɗauki ɗiyar sai bacci take hankalinta kwance, wandon sanyin da aka samata ya zamai ya wangaleta anan ya tabbatar da mace aka haifa mashi, cikin zafin nama ya dan gwarar da ita a kan bed ɗin wani lafiyayyan mari ya sakarma Maryam dake baccin gajiya.

 

 

Bashiri ta bude idanun ta ta sauke su a kanshi, atsawace yace “tashi munafukarnan muguwa macuciya Dan kutumar ubanki mace nace ki Haifa man?”

 

wasu siraran hawaye ne suka sauko mata a kumatu haryau tana mamakin mijin nata yana abu kamar wani daƙiƙi., kafin tasamu damar yimashi magana ya ƙara wanketa da maruka har biyu yana zaginta saida doctor jabir yashigo domin ɗaukar wata taƙardar da ya manta kana ya riƙeshi yana bashi haƙuri, ingijeshi yayi “ai kaima munafikin ne da alamu masanya akayi man domin ni an tabbatar man da *HAIHUWAR ƊA NAMIJI* za ayiman amma kunzo kunyi kutun kutun kun hana, ke kuma” ya nuna maryam da yatsa

 

“kisan uban wannan yarinyar tun wuri danni ba asararre bane da zanyi wahala da ita ba kuma wallahi daga yau sisina bazaki sake ganiba waɗanda kika cima wallahi sai kin biya su”

 

kayan da sukazo dasu na haihuwa da magungunan da aka saya da komi harta da kayan da aka sama jaririyar saida ya tattara ya kwashe doctor jabir sai haƙuri yake bashi amma sai zaginshi yake, haka ya kwashe komi yabar asibitin cikin tsananin ɓacin rai.

 

“madam kiyi haƙuri dan Allah kada hakan ya da maiki ki kwantar da hankalinki kinga ɗazu namaki awon hawon jini, jininki ya hau sosai” doctor jabir ne ke wannan maganar yana rubutu akan takarda sister fati ya miƙamawa yace “yi sauri kije parmacy ki anso waɗan nan magungunan kana kicema doctor hindatu taba ki kayan jarirai yi maza dan Allah”.

 

“OK sir” ta amsa ta fice daga ɗakin

 

“Doctor Dan Allah Dan annabi ka rufaman asiri kada kasanar da ƴan uwana abunda ya faru idan sunzo” Maryam tafaɗa tana share hawaye.

 

da mamaki ya kalleta yace “kamar ya kada na sanar dasu,kina nufin duk wannan cin zarafin da yayi maki kada a ɗauki wani mataki?”

 

kanta ta girgiza “ni komi yayiman babu wanda ya isa yayiman magani inba Allah ba dan haka na haɗaka da girman Allah kada ka sanar”.

 

da ido kawai ya bita “wata ƙila tana cikin zafin ciwo ne”. ya faɗa a zuciyar shi.

 

“wai dama daga ke sai shi kuka zo ne?”

 

“eh”

 

“ok ga waya idan kin riƙe wata number ki kira sai azo maki” ya faɗa yana miƙa mata wayar shi.

 

 

Alhaji

 

rai ɓace ya bar asibitin kamar wani zararrai gidan shi dake g.r.a ya nufa a mugun guje hon yayi ta dannawa kamar ya tada unguwar, mai gadi ya rugo da gudu ya ɓuɗe mashi jikinshi na ƙyarma.

 

saida yayi parking kana yazo yasamu baba mai gadi dake ƙoƙarin rufe gate ɗin “da kata malam dan iskanci gidan kamar na ubanka da zan dunga hon amma kaƙi zuwa ka buɗe man?, to yi maza ka tattara kayanka ka koma inda ka fito na sallamai ka”

 

 

har ƙasa baba mai gadi ya ɗuƙa “Alhaji dan girman Allah kayiman rai wallahi Allah nazagaya bayan gida shiyasa, kada ka koraini wannan ai…..”

 

hannu ya ɗaga mashi “kasani sarai bana magana biyu dan haka kada ka kuskura na dawo na iskeka anan”.

 

cikin gidan yashige wata siririyar ƙofa yabi ya buɗe wani ɗaki ya shiga ya ƙara shiga cikin wani.

 

saida ya shiga ɗakuna bakwai duk a cikin ɗaki ɗaya kana ya bayyana awani ɗaki gaba ɗaya ɗakin ja ne komi na ciki. jikin wani ƙaton bango ya tsaya saida ya tuɓe kayanshi duka kana ya fara wasu sanbatu tuni bangon ya buɗe sai ga mutane suma zindir sun bayyana…..

 

 

 

 

tofa mike shirin faruwa anan? Ku biyoni sannu a hankali danjin cikakken labarin, karku manta free book ne amma zai iya komawa paid book saboda rashin comment

 

09039556566

 

Leave a Comment