Hausa Novels

Haihuwar Fari Complete Hausa Novel

Haihuwar Fari Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

Kwance take akan carpet tayi matashin Kai da trow pillows da aka kawata falon dasu daya ta dora kanta ta Jera biyu a kasa ta azza kafafunta ga ciki yai mata tirtsa tsa a gaba abubuwan cine duk an jere mata gasu nan ta bantali wancen ta Aje Tana yatsina ta ajje tajawo wancen ta Dan bantala ta ajje.

Kunsan ciki in yatsufa da alama kam ba laifi mutuniyar taku Akwai tukunyar hanci a da yanzun da cikin ya tsufa sai hancin ya Kuma dunkulewa yai sama fuskar nan kamar an kwaba alkubus Amma a Haka take ta babbaje kofofin hanjin Tana takama.

Sallamar Mai gidan ce tasa ta Dan waigo Tana tale baki wai zatai shagwaba.

Wayyo Allah sunan Wata wai ita lantana Dan juyawa mijin yayi ya kumshe dariyar shi Dan wallahi Har ga Allah matar tashi Dariya take bashi yo duk halittun ta sun sauya idan Kuma Ya Dara agabanta yasan ya na ruwa kusa da kada
Haka dai ya daure bai Dara ba gadara so Yana cewa ” a kaga uwar biyu Ana Hutawa ne?” Miko mishi hannu tayi alamar yakamata ta tashi taimaka Matan yayi ya ta tashi Tana nishi tace ” wane Hutu Kai Kuma dama Kai nake jira ka dawo kaga edd na Yau ya cika a ka’ida Kuma Yau nake shirin tarbar jaririna Amma Kai kamar Ka manta to na hada kayan haihuwa wanka kawai zanyi inshirya mutafi asibity inyi in haihu in huta Dan Yau kam bani kwana da cikin nan ”

Kallonta yake sake da baki yace “yo Haka ake nakudar? Naga lafiyar ki lau ko damunje asibityn kawai haihuwa zaki? ”
Tace yo dama abin ba duk rakin banza bane mata su dage Sui ta shirirta Dan kawai zaki haihu? Kama ni muje in shirya Dan ni har shaddar Yau na fiddo kasan Kuma waccen siyayyar da muka je nazabo match din takalmi da gelen jakar ce na hakura Tunda ga ta kayan baby da zamuje da ita”

Girgiza Kai yai yamata yanda takeson shikam zaiga yanda za ai wannan labour shi dai yasan haihuwa ba wasa bace
Mamaki bai Kuma kashe shi ba Sai da suka shiga dakin komai ta shirya ya girgiza Kai lallai da gaske take,

Bata bata lokaci wurin wankan ba ta Fito Yana zaune ya buga tagumi ta Fito aka dauko matukar masu kamshi aka mulke Jiki dasu Sabbin pants da bra dasu under skirt duk aka saka aka bi jiki da kwankwatsetsiyar shadda ta welcome to the world baby aka saka ga takalmi Mai tsini aka chogala tsaf ta Fito Sai dai wannan tulluwar hancin datai sama idanu sun koma mitsi mitsi
Ta Kalle shi tace “lokaci nata kurewa Banson in haihu a gida nafiso in haihu asibity yi da jiki dauko kayan haihuwar muj”

Tai Gaba Tana taunar cingam k’as k’as GA Kuma karar takalminta nabada nashi sautin kwas kwas GA Kuma kamshin turaren da ta bule Jiki dashi wayar ta take dan Danna wa sannan ta kara a kunne.

 

” hello haseena Najiki shiru baki kirani ba” tadan saura ra jin me Tacemin bsngaren Ke cewa,.

Ta wani tabee baki ta katseta da cewa ” Ke duk karyar banza ce ba gani ba Yau ne haihuwar Amma rass Dani ko Dan ciwon Kai Babu ai wallahi ni dama duk jinsu nake to mukam dai gamu munyi shirin haihuwa daga nan Sai labour room ni ALLAH ya isa ma zanyi wa baturen da yasaka wa dakin haihuwa sunan kwadago ma wallahi, ko Meye aciki?” Tacan zatai magana ta katse ta dacewa ” Ke zaki sagar min da guiwa sai kinzo gani my pink jet Dan Yau kam zaiyi arrived” ta katse wayar tana kamewa gaban mota ga no restpect an kwamaea fuska nace hmm.

 

shigowa motar yayi bayan ya saka kayan back sit ya tafa suka dauki hanyar asibityn da take awo Tana ta lissafin siyayyar da bata karasa ba.

Gashi Har ranar haihuwar tazo
sun iso lafiya Tana ta huhhura hanci ga falleliyar wayarta a hannu ta Dan jingina jikin motar Kafin ya Fito aka shigo da Wata keke napep Har ta kauda idonta Kuma sai ta mayar ganin an kawo gadon dora marasa lafiya akai Kama Kama aka dora matashiyar kan gadon sai kwarzaza ihu take Tana tsine wa mijin da yamata cikin ga ranar fitowar shi yazo Amma yabarta da bala I ita kadai.

Dariya ta kwashe da ita hada cire glass din idonta Ta fara bawa mijin labarin ihun da yarinyar take tace ” sakaryar ta dage Tana ta ihu kamar wacce za a cire wa rai to mu da yake Allah yayo mu ajinin bayin ALLAH ba gamu ba rass kilanma Tana nan Tana shirme ta ganni na Fito Da Dan jaririna a hannu ina kasheka da smiles ko Abban nurain? ”

_mu D’an Dara Tafiyar ba Mai tsayi bace anyi kawai Dan nishadi mu hadu a page na gaba muji yanda labour Oum nurain zai kasance_

_mata masu abin duniya Kuna shaaninku_

 

 

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!