Hajaru Complete Hausa Novel
Tag: Hajaru Complete Hausa Novel
BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM
Bankaɗa labulen dake jikin wani ɗan akurkin ɗakin wata matsakaiciyar mace wanda duk shekarunta bazasu wuce talatin da ɗoriya ba,gajera ce baƙa ,gabaki ɗaya kamannin ta bashi da kyawun gani,idanuwan ta kaɗai abinfirgitar wa ne da tsoro ,ga bakin ta duk dussan goro da ta tara shi me uban yawa,jikin nan duƙu duƙu ga jurwaye a kan ƙafafuwan ta da damtsen hannun ta, kayan jikin ta atamfa soso ne da tasha ruwa ta gaji da ko ɗewa ga gamin baki riga daban zani daban kallabi daban,hango ta akwance a kan tabarman kaba yagalgalalla yasa matar ta lailayo wani uban ashar ta watsa tare da juya wa a ƙufule ta nufi inda tukanan randar ruwa suke ta kamfato a cikin wata ƙwarya ta dawo ta hankaɗa labulen bata wani yi sanya ba ta watsa mata shi a jiki.
Firgigit matashiyar yarinyar da batafi shekaru sha huɗu ba ta miƙe tana soshe soshe,sa shi guda kuma ruwan sanyin na ratsa jikin ta,ga yanayin sanyi da muke ciki,jin sanyin take tun daga ɗan yatsar ta har cikin ƙwaƙwalwar kanta yana ratsa sassan jikin ta na jini,zazzare manyan idanuwan ta da suke farare kamar madara kawai take yi jikin ta na kyarma, bata gama se ta natsuwar ta ba ta ji saukar manyan ashar daga bakin Inna Wuro.
“Don kutumar ubakin shegiya mayya kina juya ido kamar kin samu sabon kurwa baza ki wuto ki wuce ki É—au tallan nonon ba,wallahi ki ka dawo min da kwantan shi se naji kamar in kashe ki,Æ´ar iska watsatstsiya kawai,ni de na bani da jaraba,anzo da agola anmutu an barmin bala’i da tsiya me ruwan mayu kawai,kurwata kurrr ,li’ilafi Æ™afa dubu so dubu,za ki fito koko zaki kafe ni da shegun idanuwan nan kalan na karuwan birni”.
Tunda ta fara magana kai na yana ƙasa,idanuwana ya zuddar da zafaffen ƙwalla,zuciyar na kamar ta fasa ƙirji na ta fito,wani ƙululun baƙin cikine ya tokare mani ƙahon zuciya,wannan wane irin azababben talla ne tunda farar safiya,wai yaushe zan samu ƴanci ne kamar ko wani ɗa?,wai shin ina dangina suke?,sum sum kamar munafuka na wuto na raɓa ta gefen Inna Wuro ba tare da na tanka ta ba,tsinkakken silifas ɗina da yasha ɗauri da leda ya gaji har yaba uku lada na saka,ban damu da jiƙaƙƙen kayan jiki na ba ko kaɗan don bani da wanda zan sauya ko na ce zan sauya ,kai tsaye fankacecen tsakar gidan mu na nufa na in da na hango ƙwaryan nono har biyu ga baƙin leda a gefe ,ban damu da in wanke ido ba ko ƙafa ta ba,kasan cewar na yi sallah subahi,tsayawa na yi gaban ƙoren ba tare da na yi magana ba,iskan bishiyoyin gidan mu na kaɗawa yana ƙara ratsa cikin jikina ,jijiyoyi da ɓargo.
“Eh dole ki banza ki Æ™yaleni shegiya annamimiya,ga mahaukaciya na magana ba,toh HAJARU uwar ki Balki ki ka Æ™yale tana kabari tana ansa tambayar mala’iku,in ta kasa a jibge ta da sandar wuta,munafuka wacce ta tsotse mugun hali a nono kawai”,ta Æ™arashe maganar da jan wani É—an guntun tsaki.
Wani ƙololon baƙin ciki ya ƙara tokare min maƙoshi,jin baƙaƙen kalmomi masu kama da garwashin wuta Inna Wuro na watsamin tana jiɓan ta su ga mahaifiya ta, miyasa Inna ki ka tafi ki ka barni a dangin da ba susan daraja da mutunci na ba?,me ya sa ki ka barni a ahalin da ba nawa ba?,ina dangin ki suke da baki kai ni ba?,ko dangin mahaifina?,tarin tambayoyin nan da babu me bani amsan su,su kaɗai ne suke min yawo a ƙwaƙwalwa.
Jin bangazar da aka yi min ne ya sa ni saurin dawowa daga duniyar tinanin da na lula,saura kaɗan in faɗa kan ƙoren nonon da ke gabana Allah ya tsare ni nasan da na lahira ya fini jin daɗi,har yanzun idanuwa na na ƙasa,ta wutsiyar ido na bita da kallo anan nagane Indo ce,in da sabo na saba,fiye da haka ma zata yi min in de Indo ce don sam bata da mutunci ko mis ƙala,saukar marin da na ji ne akan kumatun ka na ya sa ni saurin ɗagowa a firgice ina kallon Inna Wuro da take ta huci kamar zakan ya a gabana.
Ban gama tantance zugin marin ba,na ƙarajin saukar wasu lafiyayyun guda biyu dama da haggu,wannan karan ba Inna Wuro ba ce Indo ce ta kwasa min marukan,abin ku da farar mace take fuska na yai wani jaaa kamar an ƙonani,saboda tsananin kaɗuwa take na nemi hawayen dake ido na na rasa,idona ya bushe ƙam kukan zuciya kawai nake,na zahirin ya gagara fitowa.
“Muguwa me mugun hali,asarar nonon zaki min,kin kare mata hanya,don baki son zuwa talla,talla halal ne a gidan nan akan ki HAJARU ,ko mutuwa ki ke kina dawowa,ko zaki mutu se kinje shi,in yaso in kin mutu ma je mu É—auko gawar ki,Hajaru ki buÉ—e kunnen ki kiji da kyau,ba za a kawo mana agola ba,a mutu a barki,gayan tsiya gayan na ayare,gayar arna a idi,kina zaune inciyar dake,in baki je tallan ba,ni ki ke so in É—auka,koko in É—aura ma me uwa a gidin murhu,to ahir É—inki,har gaban abada Indona baza ta taÉ“a tallaba ko a cikin mafarki ne,se de ke shegiya me baÆ™in ido”.
Sauke wani nannauyan ajiyar zuciya na yi tare da dafe cikina da ye wani Æ™ugi,se yanxun na tina rabona da abinci tun jiya da rana,shima nonon akuya na fake idon Inna wuro na tatsa na sha,ya rabb na ambata can Æ™asan zuciyata ,sam baÆ™aÆ™en kalaman Inna wuro sun dena É—aÉ—ani da Æ™asa in da sabo na saba jinsu sun zamomin jiki,ba abinda zata yi ya zamomin baÆ™o ,cikin sanyayyar murya zuciya ta cike da zullumin yanzun tundaga gidan fura zanje har kasuwar gada a Æ™afa,ga baÆ™ar yunwa,”Inna Wuro kamamin in É—aura akaina”,na faÉ—a idona a Æ™asa.
“Da ya fi miki”ta faÉ—a a taÆ™aice,bata jira na kama ba ta É—au Æ™oren gaba É—aya ta É—aura min akai na kasancewar banda wani tsayi sosai ta fini tsawo,baÆ™ar ledan ta É—auko ta samin a hannu,na juya da zumar tafiya banyi aune ba kawai naji,É“angare guda kuma Inna wuro ta buga wata Æ™ara tare da.
“Da ya fi miki”ta faÉ—a a taÆ™aice,bata jira na kama ba ta É—au Æ™oren gaba É—aya ta É—aura min akai na kasancewar banda wani tsayi sosai ta fini tsawo,baÆ™ar ledan ta É—auko ta samin a hannu,na juya da zumar tafiya banyi aune ba kawai naji,an bangaje ni Æ™ore da ke kaina sun tudde Æ™asa gaba É—aya sun fashe nonon ya kwaranye ga Æ™asa,É“angare guda kuma Inna wuro ganin abunda ya faru da Æ™oren ta ,ga nonon da ta ci burin inna dawo ,ta aika bakin titi a sayo mata tsire me Æ™uli Æ™uli da burodi ,hakan da ta gani ya sa ta buga wata Æ™ara tare da zubewa Æ™asa ta É—aura hannu akai kamar an mata mutuwa tana ihu, gefe na koma jikina na zanzana yana É“ari,ina bin Auwalu da shigowar shi ya bangaje ni da gangan da kallo,ko a jikin sa,kallon uku saura kwata ya yi min tare da jan dogon tsaki ya ja karan sa ko kallon in da Æ™oren suka fashe be yi ba ye cikin gidan.
“Yanzun Hajaru don tsabar baÆ™in ciki don baki son zuwa talla shine ki ka tudda nonon,wallahi Inna wuro ki lakaÉ—a mata dukan da se ta kasa motsi ,ba uban da ze Æ™wace ta,ai iskanci ne ya ke cinta so take ta nuna ta isa wiyan ta ya isa yanka ta yi matuÆ™ar raina ki”,faÉ—ar Indo da fitowar ta kenan daga Æ´ar bukkan su,sanye da kayan makaranta farin hijjab ,farar riga koren wando,kafaÉ—an ta rataye da Æ´ar jakar buhun ta take maganar tana galla min harara,ni kaina da ke Æ™asa ban ma san tana yi ba.
Kafin na ankara naji hucin Inna wuro akai na bata yi wata wata ba ta jani Æ™iyyyyy….. a Æ™asa har zuwa bakin rijiya ta janyo igiyarguga ,ni zaki ma iskancin iya shege,ni zaki tuddar ma nono ga Æ™asa ,baki son tallan ne Æ´ar baÆ™in ciki kawai,in baki tallan ba ni ki ke so naje miki,uban waye ubanki ?,koko Indo ki ke so ta je tabar karatun bokon?,to a hir É—inki shegiya me mugun hali wanda ta tsotsa a nono kawai,Cikin kuka na ce wallahi.
Hajaru hausa novel
Auwalu ne ya hankaÉ—e ni ba da gan gan na yi ba,kuma kema kina kallo, tace lallaiyarinya na ga me na kalle me sharri zaki laÆ™aba ma Auwalun da ba ruwan shi aaiko jikin ki zai gaya miki ni zaki kawo wa zancen banza zancen wofi ta sa Æ™afa ta ta ture ta ta faÉ—i ta rinÆ™a lafta mata igiyargugar kamar ba É—an mutum take duka ba tasa Æ™afa ta take mata ruwan ciki,wani irin kuka yaÆ™wace mani taci gaba da jibga tamkar zautacciya hankali tashe Innaro mai dambu ta zagayo gidan ko lulluÉ“i babu a tare da ita “kai jama,a lafiya me ke faruwane a gidannan? Inna wuro ta tsaya da dukan tana huci,”barni da Æ´ar iskar yarinyar mai Dambu nema take ta samin hawan jini,niÆ™i niÆ™i ina fama dasu inkai gwauro inkai mari wai don dai a samu a rufama kai asiri amman Æ´ar iskan yarinyar nan bata gani kawai an mutu an barni da jaraba da bala’i dangin tsiya arna a idi ba dangin uwa balle na uba yanzu ace kamar Hajaru wai ta ce.
Hajaru hausa novel
Auwalu ne ya tudda min nono har Æ™ore biyu bayan ina gani sharri ne ta yi masa ,in hana ido na bacci in tatse nono ga tsire ina son ci mugun hali irinna wannan munafukan anannamimin data sha a nono so take taga bayana wallahi ba zaki gani ba se de in ga naki”,tana magana tana haki,Me Dambu tac e eh kam gaskiya baki kyauta wa kan ki ba,yanzun har kinfi son aita jibgar ki irin haka,da kije talla,ai duk Æ™aruwan kune kan ki kikai ma mugunta ba su kaÉ—ai ba”.
TaÉ—an numfasa tana kallo na kafin ta Æ™ara zaro ido a,Inna wuro yaya nake ganin yarcan kamar bata motsine?,ta Æ™ara matsawa tana tattaÉ“a ta ,ta É—ago da sauri hankali tashe ta ce wallahi Inna Wuro bata motsi”,ta ce kai haba mai Dambu da gaske ki ke?Inna mai Dambu ta É—aga hannun ta ta saki taga ya tafi yaraf alamar ba rai Inna Me Dambu ta kwasa da gudu tana gyara É—aurin zani tana faÉ—i da Æ™arfin ta na shiga uku ni Mero,ta rasa me zata yi da Æ™yar ya seta natsuwar ta ta je cikin rijiya ta kantamo ruwa ta watsa mani gaba É—aya na firgi ta na tashi tana faÉ—ar wayyo Inna wuro kiyi haÆ™uri.
Me Dambu ta riÆ™e ta “ke yi shiru da allah aita Æ™yale ki Inna Wuro ta sauke wani nannauyen numfashi na shiga zare na mujiya Mai Dambu, ta miÆ™e tana faÉ—in ni na tafi amman dan Allah Inna wuro ki dinga kula kisan irin dukan da zaki dinga mata don kar kije ki É—aure kan ki da kan ki Inna Wuro ta sake jan gwaron numfashi kafin ta ce inshaAllahu zan kiyaye mai dambu ta fice abinta Inna wuro ta juya ta shige É—akin ta ta bar ni a nan ,na rarrafa na nufi É—an akurkin É—aki na.
Hajaru hausa novel
Na haÉ—a kai da gwiwa inata faman ban jima ba, barci ya É—auke ni ina i faman jan ajiyar zuciya akai akai.
Ba ni na farka ba se azahar naji mamakin baccin da nayi kuma yau Inna wuro bata tashe ni ba,ina niyar miƙewa naje na kama ruwa kuma na duba naga akwai koko na sa ma hanjin cikin na da yake a nannaɗe,don rabon na da abinci tun jiya da rana,shima ƙamzo na samu na sa ma hanjin ta,wannan wane irin baƙar rayuwa ce.
ina Innani na take ta tafi ta barni a Æ™angin rayuwa a hankali na duba kayan da ke jikina,na sauke wani nannauyar ajiyar zuciya kayan sunyi dauÉ—a har sun fita hayyacin su,duk da kasancewar su kayan fulani farare tass na saÆ™i,da zaren da akai musu kwalliya ne yasa ake gane kayan fulanine,don saÆ™in ya dafe dauÉ—ar datti ya sauya musu kala ,ni kaina rabon da inyi wanka har na mata,ga shatin datti a lungu da saÆ™on jikina,ba abinda ke tashi a jikina daga Æ™arnin nono se watin datti,Æ™awa É—aya bani da ita don kowa na gudu na saboda dattin dake jikina,a hankali na miÆ™e ina dafa cikina don hancina sun nan naÉ—e na É—aga yagalgalallen labulen É—akin nawa da rana ya gama kashe shi ,fitowa na ya yi dai dai da……..!
MORE COMMENTS
MORE TYPING
​
Name: | [HAJARU HAUSA NOVEL ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | November, 2021 |