Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
Hajiya Gwale Hausa Novel Complete
Inayiwa Al’umma musulmi gabakidaya Barka da sallah Allah ya maimaita mana..
Da sunan Allah mai Rahama mai Jin kai nafara wannan littafin ya Allah ka haneni rubuta abunda ze gurbata tarbiyyan Al’umma kabani ladan fad’akarwa.
Ya Allah kasa yanda muka fara lafiya mu kare shi lafiya…
Ka karemu da yan hassada ka hanemu dayiwa wani hassada…
Ka azurtamu da halal ka hanemu da cin haram komin kankartar sa…
Ya Allah kasa muyi kyakkyawan karshe ka shirya mana zuri’ar mu………
Kasa Albarka acikin neman mu….
Fitacciya Daga cikin kungiyar Jarumai writ associat .
Godiya ta musamman ga Bestie Dina (Maman Nusaiba) Allah yakara hada kan mu.
Maman Amatullah jinjina agareki Kawar Arziki.
Ina Masu son a musu tallah na kasuwanci su ,toga dama ta samu zaki iya Bina ta pc mu daidai ta inringa daura miki akan page Dina.
Mai tallah shikeda riba.
IKILIMA ADAM
(kyauta Daga Allah)
Wayyo Allah! WaYyo
Allah!! Ataimaka mun gudu take shararawa iya k’arfin ta cikin dajin Allah babyn dake bayan ta yanata rusa uban kuka Alamun ya jigata…
Mazan dake bin ta wajen su shidda n’a hango ‘kowannen su rike da makamai, suna harba bindiga amma baya samun ta…
Sai kaucewa take…..
D’are ne sossai misalin karfe shabiyun d’are touchla ne hannun ta take haska gaban ta..
Su kuma suna rike da fitilar wayoyin su…..
A’cikin wannan yanayin ta buga uban tsalle ta fada wani kango mai cike da kayoyi yaron nata dan wata biyun dake kuka iya karfin sa muryan sa ta shake da gajiyawa da kukan da yake.
Allah yataimake ta barci barawo yayi awon gaba dashi…..
Su kuma wayanda suke bin sahun ta ” sai zagaye zagaye suke suna nishi sama-sama…
Ogan tafiyar su cikin tashin hankali yace taya mukayi sake *RAI DAYA* ta gagare mu kamawa…..
Cikin su wani yana huci sama-sama tareda haska tochla cikin ciyayin nan yace Mun shiga uku mun lalace in shugaba yasan Wannan matar ta kubuce mana bazamu ji da dad’i ba….
Wayar babban nasu ne yasoma ring yana dubawa yaga shugaban nasu ne ” cikin tsananin fargaba da tashin hankali d’asuka bayyana a fuskar sa..
Yace Ranka ya Dad’e wallahi gamu cikin jejin nan wallahi ta bace mana babu ita babu Alamun ta Ko kukan dan nata mun daina ji……
Dagacen bangaren cikin tsananin tashin hankali yana ciza labbansa ga wani uban Zufa ne t’a karyo masa nan da nan hantar cikin sa suka kada…
Na’urar dake gaban sa yasoma dandannawa yana zufa yace kash amma dai babu waya hannun ta..naso inyi trakin din layin nata insan inda tabuya….
Yaron nasa yace gaskiya oga tun agida tabar wayar nan..
Cikin tsawa Shugaban yace maza kuci gaba da neman ta ‘tana cikin jejin nan ku haska wayoyin naku n’a tabbatar kukan dan nata zai sa kusan inda tabuya……
Itakuwa tana cikin wannan kango sai zazzare idanu take’ nishi take fitarwa à hankali tareda toshe bakin nata……à hankali taleko kai ba abunda kake gani sai fararen Idanun ta cikin wannan uban duhun take dan lekawa taga Ko sun tafi ne….
Ganin suna d’af da ita ya sata kara cusa kanta cikin kango innaliahi wa’inna ilairajun kadai take maimatawa à zuciyar ta tareda kankame yaron dake sauke ajiyar zuciya akai akai……
Ihu mai firgitarwa sukaji Daga Sama wanda alamu sun nuna kura ce…
Ta nufo su Gadan-Gadan suna ganin tahowar kuran nan habawa suka ari n’a kare gudu suke tsulawa shima Kuran iya karfin nasa yake bin su…..
Suna gudu iya gudu har suka isa kan tsakiyar jeji wannan kuran sai haushi take ta samu nama….
Itakuwa ganin Kura be tsaya ba hakan yasa tasa taci gaba da gudun nata uban kaya suna hannun ta ‘ wanda sune suke bata matukar wahalar gaske….
**************************************************
Bayan shekara Ashirin da biyar 25 yrs……..
Baffa ne zaune kofar gidan nasa zaune yana shawarar yanda zekoma birni dan soma kasuwancin nasa…..
Abokin sa malam Adamu ne zaune kusa dashi suna zantawa…
Yace baffa kaiko inka je birni wa da wa kasani ne….
Baffa dariya yayi irin tasu ta manya yace ah lallai Adamu kace wani abu ‘ ina ruwana da sanin wani abirnin nida doya zan ringa kaiwa…
Kaga Ummulkhairi so nake in sata boko..
Kuma dana bincika bokon ance wai tayi girma tunda yanzu shekarun 13 aduniya shiyasa za’a sata aji shidda din firamari school…
Kuma nayi magana da wani malamin dake kula da makaranta sunce su kansu basu taba ganin wanda ya gina makarantar ba komai nasa umarni ne koda ya siya filin ance wasu ne yaturo suma din wayanda yaturo din basu taba ganin sa ba….
Rike da baki Malam Adamu yace ikon Allah yau nakejin sabon Al’amari to taya haka zata kasance ne?…
Wai ma ya sunan wanda keda makarantar ne? yajefo masa tambaya…..
Baffa yace Karma sunce *JAN ZAKI*
Kai kai wai daman wannan shahararren makarantar n’a Jan zaki ne..
Habawa shiyasa makarantar tacika haduwa da tsaruwa wallahi ashe ba banza ba…
Kuma makaranta ga mugun Arha kamar ta gwanati cewar Malam Adamu……
Ance wannan makaranta shine n’a talatin daya bude À Nigeria kuma dukan su irin gini d’aya ne ansa Jan zaki……..
Ihun Ummul Khairi sukajiyo innaro n’a bugun ta…
Baffa ya ce ”la kamar muryan ummu ” malam Adamu yace “ita ce mana”
Babu bata lokaci sukayi cikin gidan koda suka isa gidan iske Innaro sukayi sai dukan ummul Khairi take babu sassauci…..
Baffa cike dajin zafin wannan bugun yace “ke Safara’u ki sakar mun “ya nace…
Saboda baki san zafin haihuwa ba shine za kiyi ta dukan marainiyar Allah”?..
Kuka sossai Innaro ta fashe dashi tana salati tace “yau Baffa ni zakawa gorin haihuwa?.
Malam Adamu cikin takaici yace dole ya miki gorin haihuwa mana jibi har waje akejin karar bugun da kike mata Saboda kin samu jaka Ko ?
Wai shin ma laifin me tayi miki ne?..
Kallon su suka maida Akan ummul Khairi dake rusa uban kuka iya karfin ta…tana shure-shure akasa cikin kukan shagwaba ganin baffa tace wallahi Baffa saika auro wata matar in bahaka ba ni ka kaini gun d’angin uwata sossai take ihu tana shure- shure….
Babba durkushewa ya yi ya D’agota Daga zaune tareda mikar da ita suna face din juna..
Babban rigar sa kodaddiya ya tattaro yana kuka tareda soma goge mata hawayen yace “Haba Khairi dîna yar Baban ta kiyi hak’uri wallahi banson nisa dake ne shiyasa ga yayan ki Saifudeen baya zama gida kullum yana birni gun kai Albasa cikin kasuwar jahar Katsina”….
Kara rusa wani uban kuka tayi cike da sakalci tace shikenan baffa ni kadai zanta zama Innaro tana cin zalina takarashe zancen tanama innaro gwalo batareda baffa ya gani ba….
Innaro Salati ta dauka tana yarfe hannun cike da takaicin su tace “DUK abunda zakuyi sai dai kuyi kuma ni wallahi baki isa kice sai Baffa ya sake ni ya auro wata eheee” tana karkada kugu….
Malam Adamu yace “ai mugun halin ku ke sakawa a sake ku inban da tsabar mugun ta yarinyar nan batada uwa fa kwananta daya a duniya uwar ta , ta rasu.
Sossai Baffa da Malam Adamu suka hau Innaro da fada sossai.
Kamar zasu bige ta .
Itakuwa Khairi rarrashin ta sukayi..
Dakyar ta yarda zata zauna gidan dan taji Al’kawarin za’a tura ta makarantar boko Jan Zaki……..
**************************************************
Wanene Baffa…
Baffa sunan sa Ibrahim Mohamed wanda yake cikin garin karamar hukumar Funtua Katsina State…..
A unguwar jabiri layin yan bokolo yake zaune inda anan ne gidan iyayen sa suke…..
Ya auri Matar sa ta Farko Amina wanda ta haifa masa “yaya uku….
Saifudeen
Sultana
Ummul Khairi
Matarsa Amina yar garin Funtua ce itama iyayen ta suna zaune ne a unguwar Mata….
Soyayya mai tsananin shakuwa Baffa ya yi da matar sa wanda a lokacin iyayen ta bashi suke son ta aura ba kasantuwa talaka ne. beda komai Albasa yake talla…
Amina ta hadu da manyan masu Arziki kama Daga kan gwamna ‘attajirai biris taki yarda da kowa..
Baffa take so bata bukatar soyayyan kowani Attajiri…
Mahaifin ta yace tunda tace Mai tallan Albasa take so abata Amma da sharadi babu su babu ita..
Ya za’ayi duk dangin su babu wanda ya auri matsiyaci sai ita…
Hakanan dai akayi auren..
Tunda tace taji ta Amince
Tun daga wannan lokacin yan uwan ta suka cire hannu kan ta….
Bata isa ta tako kafarta tazo gidan iyayen ta ba…
Da tazo korar ta suke hakanan take hakura cikin kuka da bakin ciki
Take komawa gidan bukar su n’a Jan kasa…..
Baffa Sam baya son wulakancin da ake mata in taje gidan nasu shiyasa ya haramta mata zuwa gidan nasu….
Haka sukayi ta rayuwa cikin tsananin talauci wataran a wuni da yunwa
Har Allah ya arzuta su da “yaya uku…
Washe garin ranar da ta haifi yar ta na ukun Aranar ne baffa ya dauko ta zekai ta Asibiti dan ayiwa yarinyar Allurar rigakafi …
Suka hadu da wasu yan yan iska mutane su Shidda sai fadi suke ita ce…
Daya n’a cikin su yace yau shekara 13 kenan kullum sai mun zo unguwar nan.
Anya kuwa itace matar da muke bibiya kamar n’a miji take goyo
kaga nasan yanzu dan nata ya girma zekai shekaru 12 yanzu fa yake ma yan uwan sa misali.
dayan yace Alkur’an itace kuka sani Ko takara wani haihuwa ne awannan kauyen
Kuma wallahi mungaji dazuwa unguwar nan shekara shabiyu kenan kila wani auren takara nidai koba ita bace to suna mugun kama.
me kuke jira ne…maza ku harbe ta wallahi itace Ko mun huta shekara da shekaru muna abu daya..
Cikin tsananin tashin hankali Amina take kallon su bakin ta na rawa tace wallahi tallahi bansan wacce kuke nema ba.
Bani bace kama ce…
Dan Allah kumun rai karku kashe ni
Kunga mijina Na Nan auren saurayi da budurwa mukayi, cikin gigita take magana tana kokarin ajiye jaririyar ta a kasa.
Baffa be Ankara sai jiya yi sun harbawa matar tasa Alburushi daya akan ciki daya akan Fuska….
Nan take ta yanke jiki ta fadi daman koda suka fito sai Fadi take Baffa nifa yau wallahi inajin kamar mummunar Al’amari zefaru dani…
Yace mata ah Ah babu komai Adu’a itace maganin musiba…
Ganin Amina tana kalmar shahada rike da hannun Baffa dake kuka iya karfin sa jaririyar sai tsala ihu take…. Bebi ta kan ta ba.
Cikin muryan wanda rai ke d’af da barin jikin nata
Tace Baffa ga Ummul Khairi nan karike ta Amana dan Allah karka bari tayi maraici..
Tana gama fadin haka tayi kalmar shahada nan da nan rai yayi halin sa..
Ganin ta mutu ne suka d’au hoton Jinin jikin nata…
Basu tsaya wata wata ba suka haye mashinan su guda uku Kowanne su ya goya dan uwan sa abaya……
Baffa Innaliahi wa’inna yake Furtawa cikin kuka da tashin Hankali
ya mugun fita hayyacin sa yana Girgiza ta yana Ihu “wayyo! Jama’a kuzo ku taimakeni Wayyo!! Wayyo!!! ina jama’a suke yana ihu cikin tsarkewan murya bakin sa na rawa yana Girgiza ta sai Fad’i Aminatu dan Allah ki Bude Idanun ki”
Dan Allah karki mutu Wayyo Amina n’amiki Mafarkin Jin dad’i da Arziki anan gaba za ki tafi ki barni…..
Inkika tafi waze raini Ummul Khairi.
Kan kace me wajen gabadaya makil da jama’a kowa nata sallallami suna ihun nan da nan suka hau koke koke……
Wata makociyar Amina kuma Aminiyar ta mai suna Rashida cikin kuka take Girgiza Amina datake kwance fuskar wasai cike da Annuri kamar zata budi baki tayi magana gawar ta.
Ganin Aminan bata Ko numfashi yasa ta rufe mata idanu nan take wajen kowa yanata fad’in ALLAHU Akbar wannan wani irin zalunci ne…
A iya sanin mu Amina bata fad’a kowa nata ne…
Wasu Azzalumai ne suka kashe ta me tayi musu ne….
Babu bata lokaci jami’ar tsaro suka iso wajen sossai suka tsora ta ganin wannan matar yanda akayi mata kisan gilla.
Aune-aune suka shigayi suka gama dube-duben su awaje kallon su suka maida akan Baffa dake kokarin fita hayyacin Alamun ze sume….
Basuyi wata wata ba suka dauke sa cikin gaggawa kai tsaye Asibiti suka nufa dashi inda Likitoci Gêneral hospital Funtua suka raja’a akan sa…..
Itakuwa makociyar Amina daukan Jaririyar tayi takai gidan nasu inda taci gaba da basu nono ita da yar ta datake goyo…
Mahaifan Amina labari yaje musu akan Mutuwar yar su ” sossai sukayi sansani suka nufi gidan Baffa koda suka isa wayam babu kowa agidan ..
Cikin tashin hankali suka nemi a nuna musu gidan Iyayen Baffa…
Awulakance suka Shiga gidan ganin gidan duk laka ne ruwa cike à tsakar gidan bangon gidan da ya yi bakin kirin gawayi suke kallo cike da mugun tsana suka karaso gidan nasu….
Mahaifin Baffa yana kuka zaune shida yan uwan sa duk sun jejeru suna kwasar gaisuwa….
Firgit suka tashi ganin d’angin Amina sun shigo da ruwan bala’i sai Fadi suke dangi matsiyata wallahi sai munyi shari’a daku yar ta mu kuka kashe mana…
Sossai babban yayar Amina ke kuka tana kokarin cin kwalar rigar……..
Taku Har Kullum KYAUTA Daga Allah..
Karku Manta Paid book…
Free Page guda goma kacal zan baku…
Barkan mu da Sallah Allah ya mai-maita mana…
Allah yajikan iyayen mu da kakannin mu da dukan musulman duniya Ameen ya Allah.
https://play.google.com/store/apps/details?id=mynovels.com.ng.gidanuncle
​
Name: | [Hajiya Gwale Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Pingback: Ni da Yaya Arman Hausa Novel Complete | My Novels