Hausa Novels

Hakki Ne Hausa Novel Zahra Surbajo

Hakki Ne Hausa Novel Zahra Surbajo

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra surbajo_

 

*Bissimillahirrahmanir rahim.*

 

_wannan littafi me suna asama k’irk’irarran labarine,ban yishi dan wani ko wata ba in kunji abun da yay dede da rayuwarku arashine_

 

_Abun da ze zamo alkhairi Allah ya bani ikon rubutawa,ya kaudani daga akasin hakan_

 

*Sadaukarwa ga Hauwa’u Muhamnad Danjuma Nbs keffi,Alherin Allah ya kai miki*

 

*1*

 

“Na rantse da girman Allah duk shegen da ya kuma dukarmin d’a a layin nan se yasan ya daka,uban wa ya haifamin yaran da zan zauna ay ta dukarmin”cewar hajiya inna dake ta faman zage zage atsakar layi,makwabta duk sun leko suna kallonta.

 

Seda tayi masifar ta iya masifa sannan ta kad’a kanta ta koma cikin gidanta dan ta rarrashi d’an nata da aka daka agurin wasa shi da yara yan uwansa.

A zaune ta samu yaron yana wanke fuskarshi datasha kuka.karasawa kusa dashi tayi ta dafashi tace,”kai ma ne modibbo ko kadan baka biyo halina ba,da ka biyo halina to wlh da kudi akace suyi ma haka bazasuyi ba,dan san da zakaci ubansu wasani”

 

Yaron d’an kimanin shekaru goma shabiyar,D’ago ido yayi yakalli mahaifiyar tashi yace cikin taushin murya,”inna to meye ribar yin fad’a da mutane kullum,be da wata fa’ida”ya fadi yana kokarin mik’ewa.

 

“Dalla can jani talau kawai,ay sekaje kaita bari ana jibgarka,”cewar inna cikin jin haushi.

 

Murmushi yayi sannan yace cikin ladabi”inna ta takaina

 

Murmushi yayi sannan yace cikin ladabi”inna ta takaina Allah yabar min ke,batun gaskiya inna,gwanda daban rama ba sabida kinga su mada kowa yasan basa ji,in mukayi rigima cewa za’ayi tafiyata d’aya dasu shine kawai yasa na hakura”

 

Kwafa inna tayi sannan tace”can ta cakalkale maka,Shiyasa mutallib ke burgeni be barin ta kwana,ni b’ace min da gani sullutu kawai'”

 

D’an rusinawa yayi yace”Allah ya huci zuciyarki inna ta”yana gama fad’i yasa kai ya wuce zuwa d’akinshi.

 

Muje zuwa.

 

Surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

Zahra surbajo

 

*Dedicated to Hauwau muhammad danjuma nbs keffi*

 

*2*

 

Modibbo tunda ya shige d’aki yake share kwalla dan inda sabo yasaba da fad’an na innar tasa.

 

Mutallib ne yashigo d’akin da saurinsa rai ab’ace ya k’arasa gun d’an uwan nasa yace yana huci”Dan uwa naji ance su mada sunma taron dangi sun dokeka agun wasa da gaske ne?”ya tambaya yana huci.

 

A hankali Midibbo ya kalli d”an uwan nasa yace”da gaske ne mutallib amma ay na barsu da Allah”be jira yagama jin meze ce ba ya juya da gudu zuwa waje yana fad’in”Wlh basu daki banza ba duk shegen daya kwana lafiya shiyaso”

Inna na zaune taga shigewarshi da gudu,ay bata tsaya d’aukar mayafi ba ta biyo bayanshi da gudu tana gyara d’aurin zaninta tana fad’in”maza jarumi na,me share kuka na,karka barsu seka rama masa maza ka kwato kimar gidanku”

 

Shiko mutallib tunda ya falla dq gudu seda ya isa majalisar su mada,duk wanda ke gurin seda ya kwasheshi da mari,nan ko sukayo kansa,cikin ikon Allah basuyi galaba akanshi ba har aka rabasu,ya juyo ya dawo gida.

 

A k’ofar gidan yasamu inna tsaye tana masa abunnan da akewa k’auraye”chau chau nawa,Alkah de ya biya yan maza,”murmushi yayi yace”naci uwarsu inna”

 

Jan shi tayi zuwa cikin gida tana murna,modibbo koda suka shigo cikin gidan be fitoba zaman shi yayi.

 

*FARKON LABARI*

 

Malam Habu dattijone d’an kimanin shekaru sitti da biyar,bafulatannin jihar katsinane awani gari da ake kira Kaita.

Matar shi d’aya me suna Fatima yaransu na ce mata inna, da y”ay”ansu biyu maza,na farin sunanshi Muhammad,amma suna cemasa Midibbo sabuda sunan baban malam yake dashi,se me binsa mutallib,tun daga kan mutallib inna ko ta samu ciki sede ya zube,har daga karshe ma bata kara samu ba.

 

So na gidan duniya inna ta d’orashi akan y’ay’anta,k’uda akan dole yake tab’a mata su,amma dan wani mutum na layi binka zatai har gida taji baasin dukar mata d’a.

 

Shekarun madibbo goma aduniya shi kuma mutallib bakwai Allah yaywa mahaifinsu rasuwa.

 

Duk d’awainiyarsu seta dawo gun inna,dan taki ba kowa y’ay’an ta yarda ta fita tai aykatau ta kawo musu abin bukata.

 

Akan y’ay’anta,zata iya cin mutuncin kowa daya tab’a mata su.

 

Tun kan rasuwar malam yake jan kunnenta bisa mugun son da take nunawa y’ay’an amma tayi burus abunta.

 

Mutanen anguwa har sun ganota,shiyasa ko ina gulmarta sukeyi ita ko ko ajikinta.

 

Mutallib yaro ne me jini ajika dabe barin kota kwana,sha yqnzu mqgani yanzu,sab’anin Modibbi da kwata kwata beson damuwa bare yay hayaniya,rayuwarshi cike take da sanyin hali.

 

*wannan kenan*

 

*Cigaban labari.*

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

Zahra surbajo

 

*Dedicated to hauwau muhammad danjuma nbs keffi*

 

*3*

 

A kwai shak’uwa me k’arfi tsakanin modibbo da mutallib,shiyasa mutallib be jure a wulak’anta masa d’an uwa be d’auki mataki ba.

A nata b’angaren inna tafi son mutallib sabida shi beda hak’uri,ko kad’an ga zafin zuciya,hakan yasa take kallonsa a matsayin jarumj.

Shi ko modibbo kota kanshi bata bi dan tace sullutune shi wanda besan ciwon kanshi ba.

 

A b’angaren kulawa da iliminsu kuwa inna na iya bakin k’ok’arinta wajen ganin sun samu ilimi wadatacce,har zuwa yanzu da suke secondry school.

 

Inna ta tsaya tsayin daka,dan ganin y’ay’anta sun haska a duniyar ilimi,modibbo nada k’ok’ari sosai,yayin da mutallib kuma se anci kwakwa yake fahimtar abu.

 

Haka rayuwarsu ta kasance,suna matukar k’aunar junansu sede shi modibbo ba me son tashin hankali bane..

 

BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYAR.

 

Sanye yake da farar rigar ma’aikatan lafiya,hannunshi rik’e da wasu takardu,ya nufi wani office cikin sauri.

 

Modibbo Habu Kaita kenan,matashin likita d’an kimanin shekaru talatin da haihuwa.

 

Koda shigar shi office d’in mutanen dake ciki suka mik’e da sauri suka had’a baki gurin fad’in.”likita ya ake ciki ta haihu?”

 

Goge gumi yayi sannan yace”Gaskiya sede kuyi hak’uri amma ayki za’ayi mata,dan d’an a gicciye yake munyi iya yinmu abun yaci tura,yanzu zaku bada kud’in ayki dubu shabiyar sannan ku kawo jini leda uku,”

 

Jiki asanyaye wani wanda nike kyautata zaton shine mijinta yace,”likita ataimaka mana don Allah,wallahi bamu da dubu sha biyar,amma za’a samu dubu biyar,agurinmu,ataimakemu jinin kuma adebi nawa”

 

D’an nazarinsa modibbo yayi sannan yace “ba damuwa,Allah ya bata lafiya”

 

Takarda ya rubuta musu suka sa hannu sannan suka je suka biya kud’in,shi ya cika musu dubu biyar din,suna ta masa godiya.

 

Minti talatin ya kwashe yayin gudanar da aykin sannan ya kammala,yaciro yaro namiji sankacece.

 

Seda ya tabbatar komai lafiya sannan ya fara shirin komawa garin su,wato Kaita.

 

A Dutsen safe yake ayki,a asibitin gomnati na garin,yana daukar albashin dubu hamsin duk wata,

 

Da albashinshi yaci gaba da d’aukar nauyin karatun muatallib

annan yaci gaba da kula da gida,sabida tun samun aykinshi inna ta dena neman kud’i,acewarta lokacin hutunta yazo.

 

Da la’asar ya iso gida,akan mashin d’inshi lifan.wanda da k’yar inna ta barshi ya siya acewarta lokacin siyan beyiba.

 

A tsakar gida yasameta,duk’awa yayi har k’asa yace”inna ta barka da gida na dawo, ya ayki?”

Murmushi tayi sannan tace”sannu da zuwa modibbo,ina nan nayi tsuru ance hanyar dutsen safe an yanka wani,hankalina duk ya tashi nace to Allah dawo da modibbo lafiya”

Murmushi yayi yace”eh inna nima ina gun ayki naji ana labarin Allah de yakawo kwanciyar hankali ak’asarmu baki d’aya”

 

“Ameen”cewar inna

 

Daga haka suka d’an tab’a hira,sannan ya mik’e yashige d’akin su shida mutallib domin yad’an kintsa.

 

Muje zuwa

.

 

Surbajo for life

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE.*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra Surbajo_

 

*salam kuyi hakuri jina shuru da kukayi,rasuwa aka mana ta mutane goma shadaya lokaci guda se yau akai bakwai,muna fata da adduar Allah yasa can yafi musu nan,amin*

 

*4*

 

Yau asabar modibbo baya zuwa ayki,yayin da shi kuma mutallib be zuwa makaranta suna gida.

Zaune suke a d’akinsu suna hirar rayuwar duniya,mutallib ya d’an gyara zama yace.

 

“Bross wai don Allah se yaushe zaka yi aure ne?wallahi bana son ganinka a haka ,30years no be beans fa”ya k’arasa maganar cikin alamun damuwa.

 

Murmushi modibbo yayi sannan yadafa k’anin nasa yace.”Mutallib komai lokacine,nima inaso inga nayi auren amma matsalar daga inna ne tace batason in auri macen da zata rabani da ita”

 

Tsaki mutallib yayi sannan yace”wallahi yaya kana da matsala,yanzu shikenan dan tace haka se ka k’i yin aure,wallahi tun wuri kasamu mace ka aura,k’imar ka setafi k’aruwa a idon duniya da gun Allah”

 

“Zanyi katayani da addu’a”cewar modibbo yana murmushi.

 

Hirar su suka d’an tab’a,sannan suka mik’e dan su shirya tafiya d’aurin auran d’an k’anin babansu,da za’ayi a wani gari me suna YARDAJE dake can kusa da zangon daura.

 

K’arfe biyu agarin na yardaje tai musu,kowa yasha fararen kaya,se gaisawa suke da ‘yan uwa da abokan wasa.

Angonne yashiga tsokanar modibbo yana cewa”wallahi d’an uwa wannan azumin in yazo bakai aureba semun kad’a maka gwauro”

 

Gaba d’aya gurin dariya suka sa masa,wanda shi midibbo ko murmushi yayi kawai.

 

Suna nan tsaye lokacin d’aurin aure yayj suka d’unguma zuwa gidan sarkin garin wanda amaryar ‘yace agurinsa.

 

Bayan ankammala d’aurin aurene,tawagar angwayen suka d’unguma zuwa gidan da amarya take da k’awayenta.

 

Bayan sun fito an gaggaisa ne idon modibbo ya hango masa wata kyakkyawar farar yarinya tsaye can d’an nesa dasu sanye da irin kayan da k’awayen amaryar suka sa,sede d’inkin dake jikinta shi ze nuna maka cikakkiyar ‘yar birni ce kuma wayayyiya,

Kunnenta sanye cikin bluetooth,yayin da hannunta rik’e da wayarta kirar iphone,

 

Ta had’u iya had’uwa,gata da sassanyar murya,tunda ta gaishe su so d’aya bata k’ara magana ba.

 

Gaba d’aya hankali da tunanin modibbo yatafi kanta,yayin da zuciyarshi ta kamu da zazzafar k’aunarta.

 

Amaryarce me suna zainab ta d’an k’ara matsawa kusa da angon nata tace “yaya SHAHEEDAN kaduna fa tazo itama,”

 

Murmushi angon me suna kabeeru yayi sannan yace”Shaheeda manya,ay na hangota ta wani ci magani irin ba wasan nan”

 

Dariya sukayi,sannan Zainab ta waiga ta kira ta,da sauri modibbo yawaiga dan yaga wacece Shaheedan.

 

A hankali cikin takunta na k’asaita ta iso gun amaryar fuskarta d’auke da murmushi daya kara k’awata fuskarta,ta kamo hannun amaryar tace cikin sanyin murya,”bestie me ya akayi ne?”

Murmushi amaryar tayi tace “naga kin kame a kwana ne shine yasa nace bari in kiraki kizo ku gaisa da yaya da ‘yan uwansa dasu kazo daga kaita,”ta k’arasa maganar tana kallon modibbo tana dariya.

 

Shiko tunda ta ‘karaso gunsu ya rasa natsuwarshi,shiyasa bema san me ake ba.sa’banin mutallib wanda ke ankare da hali da yanayin da yayan nasa ya shiga sakamakon zuwanta gurin.

 

Muje zuwa

 

Surbajo for

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra Surbajo_

 

*5*

 

Hankalinshi be dawoba seda yajiyo muryar amaryar tana fad’in,”Shaheeda wannan shine modibbo,babanshi sinior brothern baban yaya ne,dsame mother dsame father”

 

D’an Duk’awa k’asa tayi sannan tace ad’an kunyace”Ya modibbo barka da warhaka”cewar shaheeda.

 

Murmushin jin dad’ine ya kubcewar modibbo,da sauri ya amsa mata da cewa”barka de,kina lafiya?”

“Lafiya lau”ta bashi amsa.

 

Tana gama gaisheshi tagaida mutallib da angon sannan ta wuce zuwa cikin gida wanda shi sam modibbo beso hakanba.

 

Basu jima sosai ba sukai musu sallama suka koma cikin gida, su kuma tawagar ango suka nufi motocinsu,har sun shiga mota,mutallib,ya d’an d’auki excuse,ya fita be jima ba ya dawo suka tafi.

 

Tunda suka taho modibbo ya rasa meke masa dad’i,gashi be amshi numberta ba har suka rabu,shi de daga uhm she uhm uhm har suka iso kaita.

 

Wasa wasa Modibbo ya rasa natsuwarsa kullum da tunanin shaheeda yake kwana yake tashi, gashi shi irin mutanennan ne masu zurfin ciki,bare ya Sanar da da wani ya bashi shawara.

 

Cikin k’ank’anin lokaci gaba d’aya ya gama fita hayyacinshi da tunanin shaheeda

 

Duk halin da yake ciki mutallib na lura dashi,ya fahimci so ne ke dawainiya dashi wanda har ya fara tausaya mishi.

 

Zaune suke suna hira irin ta y’an uwa,mutallib yacewa modibbo “d’an uwa kana cikin damuwa amma ka kasa sanar dani ko wacce irice,shin hakan da kayi dede ne?”

Murmushi modibbo yayi sannan yace “ko kad’an mutallib hakan be dace ba,amma na rasa ta yadda zan fara sanar dakai d’inne amma kayi hak’uri”

 

Ajiyar zuciya mutallib yayi sannan ya mik’e ya sa hannunsa acikin aljihu ya ciro wata takarda ya cillawa modibbon sannan yace”Gata nan ta amfaneka dan nasan zeyi wiya in ba itace maganin damuwarka ba”yana kaiwa nan ya sa kai ya fice daga d’akin.

 

A hankali modibbo ya d’auko takardar yana dubawa *SHAHEEDA LABARAN MATO* shine sunan daya gani an rubuta a takardar k’asan sunan kuma ga numbar wayarta.

 

Sunan nata kawai daya gani modibbo ji yayi kamar shawagi yake a sararin samaniya.

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra Surbajo_

 

*6*

 

Rasa abinda zeyi yayi,tabbas yasan numbarta mutallib yasamo masa,to amma in ya kirata me ze ce mata?shine damuwarsa.

 

Kwanciya yayi akan gado sannan yasa numbobin a wayarsa ya danna kira,cikin sa’a ko ta shiga,ba’a jima ba yaji sautin muryarta,tana masa sallama,lumshe ido yayi sannan ya bud’e,bakin sa yay masa nauyi da k’yar ya amsa sallamar sannan ya k’ara da.

“Shaheeda kina lafiya?”

 

Jin muryarsa sosai shaheeda ta firgita,dan ko a mafarki taji ta zata iya ganeta,dan tun da ta d’ora idonta akanshi a ranar da suka had’u Allah ya jarabceta da sonshi,sede ta rasa yadda zatayi taga ta samu damar sake ganinsa.asanyaye ta amsa masa”lafiya lau ya modibbo,ya kukaje gida?”

 

Modibbo jin ta ambaci sunanshi seda ya mik’e zaune,ya cire wayar akunnensa ya kalla sannan ya sake mayarwa yace”ya akai kikasan ni na kiraki?”

 

murmushi tayi sannan tace”Ya mutallib ne yace ka turoshi inbaka numbata,so lokacin wannan sabon layine ba wanda yasanni dashi har kama i yanzu in ka cire relatives d’ina shine yasa”murmushin shima yayi,azuciyarshi yana godewa Allah daya bashi mutallib amatsayin d’an uwa dake gane abinda yake da buk’ata batare daya furta ba.amma afili cewa yayi”Allah sarki,da har na d’auka ko duba kika fara”dariya tayi med’an sauti sannan tace”rufamin asiri in mutu maza su kaini ba mata ba”gaba d’aya dariyar sukayi sannan modibbo yace

 

“Shaheeda inason ganinki,dan akwai maganar da nike son yi dake amma bata waya bace,dan akwai buk’atar mu hadu tukunna,”

 

Dogon numfashi taja sannan tace”to ya modibbo,duk sanda ka shirya ina gida,kuma ina maraba da zuwanka”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace”nagode sosai Kuma insha Allahu cikin week d’innan munanan tafe,”

Daga haka hira suka d’an tab’a kad’an wacce yawancinta tambayoyi da amsa ne.daga bisani sukai sallama.

 

Cike da nishad’i modibbo ya lalubo mutallib a waya,ya buk’aci ganinsa,ba jimawa ya shigo d’akin fuskarshi d’auke da murmushi yace”Angon Shaheeda ya akayine?”modibbo be bashi amsa ba illa iyaka janyo shi da yayi ya rungume yana fad’in”Bani kai amatsayin d’an uwa na d’aya daga cikin baiwar da Allah yay min,mutallib nagode sosai,

,Allah ya bani ikon saka maka”

 

Shima rungumeshi yayi yana fad’in”duk wanda yasamu d’an uwa kamarka ya kasa faranta ransa ya modibbo lahirarsa da kallo”gaba d’aya suka tuntsire da dariya sannan suka samu guri suka zauna,modibbo yafara da cewa.”mutallib munyi magana da shaheeda kuma ta amince da na ganta,sede inda matsalar take kasan farin sani inna bazata barni inje kaduna gunta ba”

 

Murmushi mutallib yayi sannan yace”d’an uwa in Allah fa ya baka uwa irin inna to dole ne fa kaima kazama wayayye ta yadda zaka iya bi da ita ba’a samu matsala ba,dan haka kawai cemata zakai seminer zakaje ta yini guda ko kwana d’aya,abune daya shafi aykinka,kaga shikenan seka fece abunka”duka modibbo yakai masa suna dariya,da wannan shawara ta mutallib yay ayki inna ta barshi harda binshi da addu’o’in adawo lafiya.

 

Ranar jumma’a ya shirya cikin shiga ta kamala ya wuce garin na kaduna.

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra Surbajo_

 

*masoya littafina ku bibiyi wannan littafin hakki ne in ma bakya karantawa ki tara sabida nan gaba zaki bukata kar kice aturo miki baa turo ba kiji haushi,surbajo by name as you all know me i no de carry last😂 trust me*

 

*masu bibiyar shafina na instagram da Facebook shima duk zaku samu acan da wattpad*

 

*7*

 

Da misalin k’arfe biyu na rana ya iso kofar gidan nasu shaheeda,wanda da taimakon waya ya gane.

 

Da fara’arta ta fito domin tarbarsa,bakinta ko rufuwa bayayi,fad’i take “ya modibbo ko a mafarki ban zaton sake ganinka ba,sannu da zuwa,kasha hanya”murmushi yayi me d’aukar hankali yace”se kuma gani azahiri ba amafarkiba”

 

“Shigo de daga ciki yaya na,na barka a tsaye”cewar shaheeda tana dariya.

 

Juyawa tayi zuwa cikin gidan yayin da shi kuma ya mara mata baya cikin tafiyarshi me d’aukar hankali,a sit room ta ajiyeshi,inda komai an tanadar masa na motsa baki.

 

Bayan sun zauna gabatar masa da abinci tayi,duk yadda taso taki cin abincin seda modibbo yasa ta suka ci tare, akunyace tasa hannu suka ci.

 

Bayan ya kammala,sun dan natsa ne,ya tattaro duka hankalinsa kanta inda ya fara magana da cewa”Shaheeda ni de sunana muhammad Habu kaita wanda aka fi sani da modibbo,nayi makaranta tun daga primary school har zuwa degree dina a katsina state,inda a yanzu ni karamin likitane a wani kauyen dutsen safe dake kauyen garinmu,shekaruna 30,ban tab’a son kowa ba bare akai ga batun aure,tunda Allah yasa na fara ganinki shaheeda kin tafi da duk wani nishad’ina,Allah ya jarabceni da matuk’ar kaunarki,don Allah ki tausayamin ki soni kamar yadda nake sonki”yak’ara sa maganar cikin raunin murya.

 

Tunda ya fara magana shaheeda wani dad’i ya lullub’e sassan jikinta,tabbas tafi kowa dacen samun masoyi,duba da yadda yake sonta.

 

Shuru tayi tana wasa da hannayenta,yayin da modibbo ya tsureta da shanyayyun idanuwansa yanason jin amsarta.

 

A hankali tace”ya modibbo,naji dad’in bayaninka,sosai kuma na gamsu, kuma batun yanzuba na yaba da natsuwa da hankalinka Allah yashige mana gaba na karbi soyayyarka da dukkan zuciyata”ta k’arasa maganar cike da jin kunya,yayin da shi kuma ya sauke wata ajiyar zuciya gami da yiwa Allah godiya.

 

Daga haka suka shiga hira irin ta masoya,har zuwa lokacin sallar la’asar ya fita zuwa masallaci ya gabatar da sallah sannan yadawo tai masa iso gun mahaifiyarta.suka gaisa tasa musu albarka gami da fatan alkha’iri.

 

A garin ya kwana a hamdala hotel wanda yafi kusa da gidan nasu shaheeda,gari na wayewa ya kamo hanyar kaita bayan sunyi sallama da shaheedar kamar karsu rabu.

 

Koda ya iso gida cike da nishad’i inna ta tarbeshi yabata tsaraba sannan ya wuce d’akinsu,dan ya d’an huta.

 

Koda mutallib yadawo be b’oye masa yadda sukayi da shaheeda ba ya sanar da shi.sosai yatayashi murna gami da fatan alkhairi.

 

*Wacece shaheeda labaran mato,*

 

Shaheeda labaran mato haifaffiyar unguwar rimi dake cikin birnin kaduna,su biyar ne agun iyayensu duka mata,itace autarsu,gaba d’ayan su yan boko ne, gidan,

 

Mahaifinsu ya rasu tun shaheeda na yarinya,sunan mahaifiyarsu hajiya Hadiza suna kiranta Ammi,yayyanta mata hud’u kuma duk sunyi aure,

 

Suna da rufin asiri dede gwargwado,dan mahaifiyarsu ‘yar kasuwa ce,dan wani lokacin har dubai take fita ta saro kaya.

 

Yawancin ‘yan unguwarsu ‘ya’yan mace suke ce musu,sabida kawai su wayayyune,ga ilimin boko,dan shaheeda degree gareta afannin mass com,haka sauran yayyanta.

 

Wannan kenan

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra Surbajo_

 

*ki tara zaki nema agaba kar aki turo miki kiji haushi,😁*

 

*masu comments ina gani ina godiya sosai,Allah yabarmu tare,*

 

*8*

 

Soyayya tayi k’arfi sosai tsakanin modibbo da Shaheeda,wanda kowa a danginta yasan da soyayyarsu,

 

Sab’anin shi modibbon in banda mutallib ba wanda yasan da batun dan inna har yau batasan labarinba.

 

Mahaifiyar shaheeda ce ta buk’aci ganin modibbo,bayan yaje ne ta buk’aci daya turo iyayensa atsaida magana,

 

Jiki asanyaye modibbo yabaro kaduna zuwa gida.

Gaba d’aya jinshi yake kamar wani mara lafiya,har zuwa dare modibbo beda sukuni.

 

Koda sukazo cin abinci ma shi kasa ci yayi sabida tunanin da yay masa yawa.

 

Mutallib ne ya kai dubansa garesa cike da kulawa yace”D’an uwa gidan su shaheeda sun buk’aci katuro iyayenka ko?”da sauri modibbo ya waigo yana gyad’a masa kai bakinsa har hard’ewa yake yace”wallahi mutallib shine yasa kaganni cikin wannan tashin hankalin,na rasa mezan cewa inna “ya k’arasa maganar cikin rauni.

 

“Ka kwantar da hankalinka,insha Allahu kai da shaheeda zaku mallaki juna,kazama jajirtaccen namiji komai zezo da sauk’i yanzu kabani wuk’a da nama komai ze dede ta”

 

“Na baka mutallib pls ka taimaka”cewar modibbo cike da damuwa.

 

K’arasa cin abincin sukayi sannan mutallib ya mik’e ya fice zuwa d’akin inna dake zaune kan tabarma tana jin radio.

 

Shigowar mutallib d’in ce tasa ta kashe radion ta yalwata murmushin kan fuskarta tace “Auta na mowan ‘ya’ya,ya akayine?”

 

Guri yasamu kusa da ita yazauna sannan yatattaro dukkan natsuwarshi sannan yace cikin tattausan lafazi.

 

“Inna Alamu sun gwada kamar baki,rike shekarun da kika haifemu ba ko?”ya wurga mata tambayar gami da bin ta da ido.

Duka ta kai masa gami da fad’in”kaci gidanku Auta,ni d’ince bansan shekarunku ba?to yayanka yana cikin shekara ta talatin kai kuma ta ashirin da bakwai”

 

.”good,”cewar mutallib gami da gyara zamanshi sannan yaci gaba da cewa”Inna keda baba kuna da shekaru nawa nawa kuka auri juna?”

 

Cike da mamaki ta kalleshi,tanason tagano manufar tambayar tashi amma takasa dan haka amsa ta bashi da cewa”babanka ashirin da biyar ni sha biyar,menene ya faru ne mudallabi,?,”

 

Wasu hawaye ne suka biyo fuskarsa masu zafi na tausayin d’an uwansa,sannan yace”Inna yaya modibbo yanzu shekarar sa talatin da haihuwa,in kin mantane zan tuna miki,yaya modibbo yajima da balaga,shi baligi ne inna me cikakkiyar lafiya,yana buk’atar mace akusa dashi ahalin yanzu ki taimaka kibarshi yayi aure da wacce yake so ko hankalinshi ze kwanta”yak’arasa maganar cikin kuka.

 

Baki bud’e inna take kallon mutallib,sabida tsananin mamakin maganganun nasa.da kyar ta iya ce masa.

 

“Wacece wacce yake son ?aina take,’yar gidan wacece?”sune tambayoyin inna.

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra surbajo_

 

*mummyn yara ina godiya da irin comments danake samu daga gareki Allah yabar zumunci yabarmu tare,*

 

*Inna ibrahim kime,😍💕💖*

 

*9*

 

“Sunanta shaheeda labaran mato,’yar garin kaduna ce,sun had’u a bikin kabeeru da mukaje yardaje, suna matuk’ar k’aunar junansu”cewar mutallib batare da tsoron komai ba.

 

Shuru inna tayi tana nazarin maganar kamin tace”to naji ka amsomin adireshin gidansu zansa abincikamin tarbiyarta insun dace se ayi”

 

Rungumeta mutallib yayi yana me nuna farincikin shi afili yace “mungode inna”yatashi yafice dagudu zuwa d’akinsu yana shiga yaywa modibbo albishir sosai yay farin ciki da jin cewa inna ta yarda yay aure.

 

Ita ko inna wani malulun bak’in ciki ne ya tokare zuciyarta jin cewa modibbo nada wacce yakeso batare data sani ba

 

Wayarta ta janyo ta nemo wata numba ta danna kira,ba’a jima ba aka d’aga,koda aka d’aga ba gaisuwa ba komai tace”hajiya sabuwa ina cikin matsala”daga can b’angaren wacce aka kira da hajiya sabuwa tace “hajiya inna wacce irin matsala kuma?”

 

“Yaronki mana modibbo nason sani a masifa,wai wata yakeso a kaduna,wallahi hankalins yanzu haka atashe yake”

 

Salati hajiya sabuwa tayi sannan tace “ke ko kina wanne gangancin hakan ta faru,?”kwashe duk yadda sukayi da mutallib tayi ta sanar da ita,

 

Sannan ta k’ara da cewa”wallahi ba abinda yafi d’agamin hankali se hajiya inno,kinfa san komai yanzu in taji da wanne ido zan kalleta ni inna nashiga uku”

 

“Ay baki shiga uku ba ma se in taji labarin “cewar hajiya sabuwa

 

“Sabuwa kwakwalwata ta cushe ki bani shawarar abunyi wallahi ji nake kamar zanyi hauka”

 

“Dole ki fito ki sanar dasu gaskiyar lamari,cewa kinwa hajiya inno alk’awarin aura mata modibbo,nan da sati uku masu zuwa,tun wuri ya hak’ura da wancan yarinya ba samunta zeyi ba,amma inkin k’i to ko zaki shirya yin aman duk kud’in data baki”

 

Tirkashi

 

Muje de zuwa

 

Surbajo for life

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_zahra surbajo_

 

*Billy shantally tawa takaina,ina godiya masoyiyata🥰*

 

*10*

 

Gwauron numfashi hajiya inna taja,sannan tace”zan sanar dashi sabuwa insha Allahu komai ze tafi dai-dai”sallama sukayi takashe wayar.tana saka abubuwa da yawa acikin ranta.

 

A daren mutallib yakawo mata address d:in gidan su Shaheeda ba tare da tunanin komai ba.

 

Washe gari tun asuba inna ta fice daga gida bata zame ko ina ba se kaduna,bata sha wiya ba ta gano gidan,kallo daya taiwa gidan ta raina arzikinsu,makwabta ta dan tambaya game da gidan nan ko aka labarta mata cewa yayan macene.

 

Inna de bata baro garinba seda tai arba da shaheeda,inda munafikin dake mata bayaninsu ya nuna mata ita lokacin ta rako k’awarta k’ofar gida.

 

Sam shaheedan bata yimata ba,dan haka tasha alwashin raba wannan soyayyar kota halin k’ak’a.

 

Bata iso gida ba se k’arfe goma na dare lokacin su modibbo sun fita nemanta sabida basu ganta ta dawo ba.

 

Mutallib ne yafara ganinta da sauri ya matsa kusa da ita yace”inna ina kikaje kin d’aga hankalinmu”ya fad’i cikin yanayi na damuwa.

 

Rab’awa tayi ta shige cikin gidan ba tare data bashi amsa ba,haka suka biyota abaya zuwa cikin gidan.

 

Kan tabarma tahau ta zauna sannan tace “wash Allah na wallahi na gaji daga kaduna nake gidan su Shaheeda”

 

Azabure suka kalli juna sannan dukansu suka zauna gefen tabarmar suna fad’in”Gidan su Shaheeda kuma inna?”

 

Turo d’ankwalinta gaba tayi sannan tadan gyatsine fuska tace”tace eh fa ko laifine?”

Asanyaye suka girgiza mata kai.

 

Ci gaba da magana tayi cikin isa da k’asaita tace”modibbo sam wannan ‘yar macen bata dace da kai ba kuma ba zaka aureta ba,bama wannan ba na jima da yi maka mata,dan haka shaheeda ko wata shigenta bata da matsugunni agidanka idan har nice na haifa”

 

Agigice modibbo yake kallon mutallib shima shi yake kallo,bakinsu har hard’ewa yake wajem tambayar”dawa kika masa matar?”

 

Hankali kwance tace “Da hajiya Inno ta can gangaren layi”,

 

Ba modibbo ba hatta mutallib seda ya girgiza da jin sunan amna dan ya tabbatar se yace mata.

“Inna wai Hajiya Inno Babar su jagudu?”

 

Murmushi tayi sannan tace”kwarai kuwa ita”

 

“Kai Inna tun wuri ki sauya tunani kamin hakkin modibbo ya waiwayeki,taya yana saurayi zaki had’ashi aure da mace ‘yar shekara sittin,wanne irin son kai ne wannan inna?”cewar mutallib yana kuka kamar ranshi ze fita.

 

Afusace inna tayo kanshi da fad’in”ka iya bakin ka mutallib wallahi inka tunzurani da hajiya sabuwa zan had’a ka kaima”.

 

“Ko hajiya tsohuwace inna ni nafi k’arfin haka shima modibbo da yasan inda ke masa ciwo baze yarda ba”

 

Kanshi inna tayi tana zazzaga masifa tana kai masa duka da kyar modibbo yasamu ta natsu,tsugunawa yayi a gabanta yana kuka yace.”Inna ta son da nike miki yazarce na kowa aduniya,nafi k’aunar farin cikin ki kan nawa innata,in har aurena da hajiya inno ze saki farin ciki inna ta na amince kisa a daura,Allah ya bani hak’urin miki biyayya”ya k’arasa maganar cikin matsanancin kuka.

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_zahra surbajo_

 

*Surbajo for life lovers only,group na masoya na dake active tsawon sheka hudu batare da ina cikiba banma san dashiba se yanzu,kai wannan wacce irin soyayyace,ni zahra mezancewa Allah daya wuce godiya,Duk masoyina akonina kake afadin duniya surbajo ina sonku,tnks you group admin jamila Allah yabar mu tare*

 

*11*

 

“Ka samawa kanka lafiya”cewar inna tana huci.

 

Mik’ewa tayi tanufi d’akinta harta kai bakin k’ofa ta juyo tacewa modibbo,”gobe da k’arfe sha biyu na rana Hajiya inno zata zo zance gunka saura inji ka mata ba daidai”

 

K’ara rusunawa yayi idonshi na fitar da kwalla yace”to inna ta zaki sameni be biyayya insha Allahu”

 

Shigewa d’aki tayi ba tare data sake bi ta kansu ba.

 

Daga modibbon har mutallib d’in ba wanda yayi yunkurin motsawa yabar gurin sunanan tsugune har aka kira sallar asuba,dukansu kuka suke.

Kiran sallar ne yatashesu agurin sukai alwala suka wuce masallaci.

 

Koda akaje sujjadar k’arshe modibbo be dago da wuriba,rushewa Allah yayi da kuka yana fad’in.

 

“Ya Allah nayi biyayya,ya Allah nayi biyayya ya Allah nayi biyayya,kadubeni da idon rahama ka sauk’ak’amin rayuwata,ka zabamin innata amatsayin mahaifiya Allah banyi fushi ba ya Allah in Inno ka zab’amin amatsayin mata Allah kar kasa nai fushi,nagode ma Allah kadubeni”😭yak’arasa addu’ar cikin kuka,sannan ya d’ago.

 

Koda suka baro masallaci gida suka dawo mutallib d’akinsu yawuce kai tsaye,dan beson ganin inna.

Modibbo ko d’akinta ya wuce da sallamarshi ya shiga d’akin,dakyar ta amsa masa,murmushi ya k’irk’iro sannan ya k’arasa gurinta kamar ba abinda ke damunsa ya tsuguna agabanta yace”innata barka da asuba da fatan kin tashi lafiya?”

 

Ba laifi tadan saki fuska tace”lafiya lau”daga haka bata sake cewa komai ba,se daga bisani zuwa can tace.

 

“In kace zaka biye wa mutallib asara zakai tayi arayuwarka,kaga de na farko hajiya innon nan y’ar majalisa ce, gata da kud’i ga hanyoyi,kaga in ka aureta har kasar waje fita zatai da kai kaima kasamu ka murmure,duk abinnan da nikeyi dan kai nakeyi ba kuma dan bana sonka ba amma kanaso ka biyewa wancan shashashan ku rasa duka”

Murmushi yayi afili yayinda zuciyarshi ji yake kamar wutar matatar man fetur aka kunna mata,dakyar yace”hakane innata Allah yashige mana gaba”

 

Shuru ne yabiyo yar hirar tasu kana daga bisani ya mik’e ya fice zuwa d’akinsu.

 

Atsaye yasamu mutallib yana kai gouro yana kai mari,cikin k’unar rai mutallib yace masa”nufinka ka amince da auran waccan tsohuwar guzumar kabar shaheeda?”

 

“Kusan hakane mutallib,tunda haka inna take so dole in mata biyayya,shaheeda kuma hak’ura nai da ita, ba barinta nai ba”suna cikin maganar wayarshi tai kara da sauri ya karasa k’an wayar ya d’auka,dan yasan me kiran tun daga sautin wayar.

 

Shaheeda ce,anatse suka gaisa sannan yace mata”baby ta dama ina shirin kiranki se gashi kin kira,dama wata magana nakeson sanar dake ina fata da addu’ar Allah yasa kimin fahimta me kyau”

 

Dagacan b’angaren tace”insha Allahu ya modibbo zan fahimceka nayi alk’awari”

 

Daga haka modibbo kwashe komai yayi ya sanar da ita,ayko ita kuka shi kuka,da kyar yashawo kanta tai shuru,sannan tace cikin dusasshiyar murya “na yarda da kai modibbo fiye da kaina,karka damu kaje kai auranka shaheeda takace ya modibbo shekaru d’ari matuk’ar kana raye kaje ka dawo shaheeda ina gida zaman jiranka,”tana kaiwa nan ta kashe wayarta,

 

Koda ya kirata ta kashe wayar gaba d’aya tsugunawa yayi agurin yana kuka kamar mace,da kyar mutallib ya rarrasheshi yay shuru,zuga shi ya shiga yi kan ya bijirewa auran amma ina fafur yak’i yarda .

 

Muje zuwa

 

surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: [9/25, 11:22 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_zahra surbajo_

 

*ku tara gaba zaku nema kar aki turo muku kuji haush*

 

*12*

 

Tun sha d’aya da rabi nasafe inna tasa modibbo ya shirya ya zauna zaman jiran hajiya inno,se fad’a take masa kan kar ya sake hajiya inno ta gano dole tai masa.ba,a son ransa ze aureta ba.

 

Shide ba baka se kunne jinta kawai yakeyi.

 

Sunanan zaune hajiya inno ta k’araso acikin wata farar mota k’irar benz2019,yan rakiyarta kuma amotoci guda biyu na jamian tsaro kallo d’aya zakai mata kasan kud’i sun zauna ajikinta,doguwace fara ga jiki,ba laifi tana da kyan fasali,bakinta kwai hak’orin maka guda biyu fari da gold,sede kallo d’aya zakai mata kasan gogaggiyar y’ar duniyace,hajiya inno magaji kenan y’ar majalisa me wakiltar karamar hukumar kaita a Abuja.

 

Cikin takun isa da k’asaita ta shigo cikin gidan yayin da y’an sandan dake kula da ita suka tsaya a waje,PA d’inta ce kawai ta biyota d’auke da jakarta.

 

Inna har tuntube take gun sauri duk’awa ta gaishe da hajiyar,da kyar ta amsa mata sannan tace”ina mijin nawa?”

 

Akid’ime Modibbo shima ya zube agabanta kamar yadda yaga inna tayi cikin gigita besan sanda yace” gani umma”ba

 

“What!!!wacece ummar taka,haba ina laifin ma ka kirani baby ko honey”cewar hajiya inno,

 

Inna har k’warewa takeyi yayinda ta waigo gun Modibbon tana fad’in”baby sunanta daga yau”

“To inna naji”

 

“Taso muje gidana mayi hirar acan dan nan warin kwatar can har yafara damuna,”cewar hajiya inno sanda ta juya zuwa waje,ba musu modibbo ya mik’e yabita abaya.

 

Gidan baya ya shiga inda take driver yajasu zuwa gidanta daya gaji da had’uwa.

 

Awani falo na musamman ta saukeshi,kan kace me ancika masa tebur da abinci kala kala.

 

Modibbo be iya shan koda ruwan gidanba bare. Wani abu waishi abinci.

 

Hajiya inno ita tai ta surutunta yayinda shi ko daga uhm se uhm uhm,har zuwa la’asar suna tare afalon seda ya gaji yace mata.

 

“To ni zan wuce”

 

Shagwab’e fuska tayi tana fad’in”kai haba de tun yanzu?,koda yake rana ita yau ay kadawo gidanma gaba d’aya da zama naga ta saurin tafiya”

Murmushi modibbo kawai yayi,danshi ya k’osa yabar gurin.mik’ewa tayi tashiga d’akinta sannan tafito hannunta d’auke da wata jaka, tamik’a masa tace

“Gasunan ba yawa,ka raba gida biyu ka bada sadaki da rabin rabin kuma ka sallami gidanku”

 

“To nagode Allah saka da alkha’iri”daga haka ta rakoshi har bakin k’ofar falon tayi ya fice ya shiga motar da zata mai da shi gida,ita kuma ta koma ciki.

 

Koda yazo gida be samu inna a gidan ba,dan haka d’akinsu yashiga,jakar data bashi ya bud’e,kud’i ne aciki koda ya zazzagosu maira milyan biyu ne aciki.

 

Beyi mamaki ba dan yasan tafi k’arfin kud’in.

 

Yana nan zaune mutallib yashigo d’akin,da kud’in yay tozali da sauri ya k’arasa gun d’an uwan nasa yace”D’an uwa wannan kud’infa?”

 

“Umma inno ce ta bani”cewar modibbo batare daya san me yace ba.

 

Wata mahaukaciyar dariya mutallib ya fashe da ita har yana rik’e ciki yace”wallahi fa sede umma innon fa kam,”

 

Se alokacin ya tuna da sunan d’aya kirata,shima murmushin yayi.

 

“‘Wannan kud’in na menene ya modibbo,ina fatan ba seda kanka zakai agareta ba?”cewar mutallib cikin yanayin tuhuma.

 

Gyara zama modibbo yayi sannan yace”mutallib ko in ansa ko kar in ansa inna ta riga ta gama siyar danj,to ya zanyi?”

Nande yakwashe duk yadda sukayi da ita ya sanar dashi.

 

Shuru mutallib yayi yana jinjina lamarin,tabbas yasan gaba akwai kallo.afili kuma seya nuna shi beji dad’in amsowar da yayin ba.

 

Fafur mutallib ya hana modibbo ba inna kud’in inda ya shawarceshi daya tara su,kar ya sake ya tab’a sabida gaba.

 

Da shawarar yay ayki nan take ya ware miliyan guda na sadaki, d’ayan kuma yaba mutallib d’in ya ajiye masa.

 

Haka modibbo yaci gaba da jewa gun inno hira,🤣badan ranshi yaso ba.

 

Sati guda inna tasa na auren dan haka dangin babashi ta aykawa,abunka da k’auye da kud’i basu tsaya bin ba’asi ba suka d’ungumo kaita dan d’aurin auren.

 

Ta b’angaren hajiya inno har gyaran jiki tayi dasu magungunan mata dan megidan yaji tsab.

 

Haka tasashi dole sukaje hoton pre wedding,god’ai god’ai da ita haka taita rungumarsa ana musu hoto,

 

Ba laifi sunyi kyau sabida hajiya inno nada kyau.

 

Kan kace me duk ta d’ora su akan social media,nanko akaita ce wa “wani yay wuf da uwar wasu”

 

Akwatina biyar ta cika mishi da kayan maza nagani na fad’a masu tsadar gaske,duk an d’inkosu d’inki na zamani.

 

Koda drivernta ya kawo masa ya bud’e ya gani kayan sun burgesa.

 

Amma acan cikin zuciyarshi jinsa yake kamar me shirin zuwa lahira ko kad’an be murna da auren…

 

Haka dubban jama’a suka shaida auran modibbo da hajiya inno inda masu munafunci nayi masu fatan alkha’iri nayi,shiko mutallib ko zuwa d’aurin auren be jeba

 

Hajiya inno ko taro tayi me rai da lafiya aka tayata murnar auren nata.

 

Da daddare misalin k’arfe tara inna tai kiran modibbo tai masa fad’an auren,harda cemasa “yi nayi bari na bari bata karya wuya modibbo,wallahi inka mata biyayya sekaga abin ya d’ore har aljanna Allah de yay maka albarka kaje kaita hak’uri danshi aure d’an hak’uri ne,muma duk haka akai mana”shiko in banda hawayen bak’in ciki ba abinda yakeyi,wato shine ma zeje yayi biyayyar auren bashi za’a biba dank’ari🤣

 

Sunanan zaune motar d’aukar Ango tazo,🤣

 

Haka mutallib ya rakoshi har mota yana tuntsira dariya yayin da shi kuma angon fuska rufe da d’an k’aramin towel yana goge hawaye ya shiga bayan motar a haka akaja motar aka tafi dashi,shide mutallib dan dariya cikinshi har ciwo yake masa sabida abun shi se yay masa kama da kai amarya ba Ango ba🤣🤣🤣

 

Muje zuwa

 

Surbajo for life.

[27/09, 10:51 am] +234 806 650 5531: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*HAKKI NE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 

_Zahra Surbajo_

 

*Masu tambayar page 11 ku dena shine page 12.*

 

*13*

 

Har bakin k’ofar falon direban ya kawo shi,jiki asanyaye ya bud’e k’ofar motar ya fita.

 

Ya jima tsaye bakin k’ofar falon kamin ya murd’a k’ofar yajita abud’e ya shiga da sallamarshi.ba kowa a falon dan haka guri ya samu kan kujerun falon ya zauna.

 

Shuru shuru ba wanda ya fito shi kuma besan kan gidan ba dan haka nan kan kujerar yay zamanshi.

 

Hajiya inno na falon sama zaune taji motsin shigowarshi,to ta d’auka ze hauro saman jin shurun tayi yawane yasa ta sauko da kanta,

Akan kujera tasameshi zaune,da sauri yakai dubansa gunta ya mik’e da sauri yad’an rakub’e agefen kujerar.

.ita ko cikin takun isa da k’asaita ta iso gabanshi fuskarta d’auke da murmushi,ta d’ora hannunta akan kafad’arshi ta matse shi sosai,tace “shine baka hauro sama ba ka zauna anan”

 

Modibbo wanda kunyar duniya tabi ta kamashi,da kyar yace “wallahi bansan kan gidan bane shiyasa nai zamana anan”

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Murmushi tayi sannan. Ta kamo hannunshi,tace”to ay daka dudduba base ka gane kan gidan ba”

 

Shuru yayi kawai yana jinta,jan hannunshi tayi suka haura sama inda d’akunan bacci suke.

 

Wani had’ad’d’an d’aki takaishi wanda ya gaji da had’uwa ta zaunar dashi a gefen gado sannan ta dafa cinyoyinshi tace tana wani d’an lashe leb’e”nan shine d’akin ka,na gaban wannan kuma nawa,d’akunan k’asa kuma na yara nane, jagudu da aslamiyya,suna Uk yanzu haka suna karatu,amma suna zuwa hutu”

 

Murmushu yayi,yace”Allah sarki hakan nada kyau nagode sosai”shafo gefen fuskarshi tace”kasameni ad’aki in ka gama”

 

Daga haka ta juya ta wuce d’akinta,shiko wata ajiyar zuciya yayi me nauyi,sannan ya mik’e ya shige toilet yasakarwa kanshi ruwa,ya d’auro alwala,ya fito ya zira doguwar riga ya shimfid’a abun sallah yayi nafila raka’a biyu sannan yayi shafa’i da wutiri ya jima yana addu’o’i daga bisani yasha ya kwashe abun sallar ya cire rigar yaje ya haye gado yay kwanciyarshi yakashe wuta.

 

Be jima da kwanciyaba bacci yay awon gaba dashi.

 

Muje zuwa

 

surbajo for life

Leave a Comment

error: Content is protected !!