Hakkokin Aure Abisa Alqur’ani Da Sunnah
HAKKOKIN AURE ABISA ALQUR’ANI DA SUNNAH
DARASI NA 10
ZALUNCIN MAZA AKAN MATANSU
ZALUCIN IYAYE AKAN ‘ƳA’ƳANSU
SAKAMAKON MASU AIKATA HAKA
• Iyaye ku sani cewa: ‘Ƴa’Æ´an ku suna da hakki akanku na ku tabbatar da sun auri miji nagari mai addini mai tsoron ALLAH, mai kuma kyawawan É—abi’u, bamai tarin dukiya ko mulki ba kaÉ—ai.
• Wajibi ne idan zaku aurar dasu, ku nemi shawararsu akan shin suna son wanda zaku aurar dasu garesu, bawai kawai zaku É—auki mace kubashi bane, kuma ashe azzalumi ne, koda kuwa auran dangine wajibi ku bincika É—abi’unsa.
• Wajibi ne ku aurar da ‘Æ´a’Æ´anku ga wanda suke so ba ga wanda ku kuke so ba.
• An haramta muku aurar da ‘Æ´a’Æ´anku ga wanda iya kune kuke sonsa, amma ‘Æ´a’Æ´anku basa son shi.
Abu Huraira (R.A) Yace:
Manzon ALLAH {s.a.w} Yace:
Ba’a aurar da bazawara har sai tayi umarni, kuma ba’a aurar da buduruwa har sai tayi izni,
Sai sahabbai su kace: Tayaya iznin nata yake?
Sai yace:
Iznin buduruwa shine: Tayi shiru idan an ambata mata wanda take so.
[Bukhari ne ya rawaito shi]
Sharhi:
Wannan hadisi kai tasye yana mana nuni da hani akan aurar da bazawara face sai tayi nuni da cewa itafa tana son aure,
Haka kuma ba’a aurar da buduruwa face sai an nemi izininta akan wanda akeso abata, idan ta aminta dashi, idan kuma ta kasance mai kunyace, to ayayin da iyayenta suka tambayeta sai tayi shiru, ko kuma ta É—an gyaÉ—a kai, ko tayi murmushi.
Amma idan kuwa ta nuna bata son-shi, to kada ku aura mata shi, idan kuka aurar da ita ga wanda bataso,
WALLAHI duk abinda ta aikata na rashi biyayya na zunubi a gidan auranta, to ku iyaye kune kan gaba acikin zunubin.
Nana A’isha (R.A) tace:
Anbawa Barirah zaÉ“i akan mijinta yayin da aka ‘Æ´antata.
[Bukhairi da Muslim]
Wannan hadisi yana nuni da cewa ita Barirah baiwa ce sai aka ‘Æ´anta-ta, to dama batason mijin nata, sai kuma Manzon ALLAH {s.a.w} ya bata zaÉ“i bayan auranta ya mutu, kuma tace ita bata son-shi,
Indai har Manzon ALLAH {s.a.w} da yafi iyaye hakki akan ‘Æ´a’Æ´ansu bai tilastawa baiwa ta auri wanda bata so ba, to kuwa ku iyaue bai halatta agareku ku tilastawa ‘Æ´a’yanku auren wanda basa so ba.
CUTARWAR NAMIJI AKAN MACE
• Wajibi ne duk wanda zaiyi aure daga cikin maza ka tabbatar da kanada abinda zaka iya ciyar da ita da sauke dukkan hakkokinta na sutura da sauransu.
• Wajibi ne ka tabbatar da kana da lafiyar da zaka iya gamsar da ita, kada ka aurota kazo ka kasa gamsar da ita a lokacin jima’i, wannan hakkine dake É—auke da kaso 40 acikin aure,
• Idan har kasan baka da lafiya, to kada ka soma yin aure, domin zaka iya jawowa matarka ta faÉ—a cikin masiba, ko ta fara zina a bayan idonka saboda kai baka iya gamsar da ita, ko ta fara lesbian, ko kuma ta rinÆ™a istimina”i
• Kuma duk abinda ta aikata kana da rabo acikin zunubin domin da kana gamsar da ita, da bata aikata wancen aikin ba.
• Maza ku sani rashin gamsar mace a gurin kwanciyar aure yana da giramn zunubi,
• Kamar yadda idan ka kirata akace tazo gareka koda kuwa tana kan tandar suya ne, akace idan bata amsa kiranka ba, to fushin ALLAH zaihau kanta, to kaima idan ta nemi hakkinta ka hanata, kaima fushin ALLAH zaihau kanka, domin kowa biyawa junanku buƙata wajibi ne,
• Yadda kake da hakki akanta, haka take da hakki akanka.
• Yadda bazata shiga aljannah idan ta cutar dakai, haka kaima bazaka shiga aljannah ba idan ka cutar da ita.
• Yadda idan mace ta koka ga ALLAH mijikta yana mai gamsuwa da ita zata shiga aljannah, haka kaima idan ka koma ga ALLAH matarka tana mai gamsuwa dakai zaka shiga aljannah.
• Yadda idan ta saɓa maka zata shiga wuta, haka kaima idan ka tauye mata hakkinta zaka shiga wuta, ku daina wani ganin wai aikai namiji ne, addini ya baka power akan mace, WALLAHI kana zaluntarta wuta zaka shiga.
• Rashin kalamai masu daɗi, da tarairaya da zama kana hirar da matarka, kanajin matsalolinta kana bata shawara kana taimaka mata,
• Zagin matarka da cin mutucinta, da rashin nuna kulawa idan tayi maka abu domin ta burgeka, da rashin bata lokacinta sai dai ka tafi hira gurin abokanka, ƙarshe ma ka kwaso zunubai masu yawa,
• To ka sani duk wannan abin lokaci zaizo, kai da ita zaku tsaya agaban ALLAH a ranar alÆ™iyama, za’ayi muku hisabi, zaka biyata hakkokinta daka tauye mata, kuma idan bakayi sa’a ba, sai an tattaro sallarka da azuminka da komai naka na aikin lada na shekara 30 basu gama biyanta hakkokinta na shekara É—aya tak daka zalunce ta ba.
• Sannan kuma duk iyayen da suka san cewa ‘Æ´arsu tana fuskantar irin waÉ—nan ababen a zaman aurenta basu kira mijin da ita sunyi musu shari’a ta adalci ba, to suma ALLAH zai tambayesu a ranar alÆ™iyama.
• Kada ka sake ka auri ‘Æ´ar mutane alhali kasan bazaka iyayi mata adalci ba, kada ka sake kayi karambani yakai É—an uwa,
• Yafi maka alkhairi ka mutu ka koma ga ALLAH da laifin bakayi aure ba, idan ALLAH ya tambayeka, kace ya UBANGIJI na inajin tsoron bazan iya-yi mata adalci bane, ina tsoron nazo gabanka da hakkin matata akaina, a dalilin wannan tsoron sai ALLAH yai maka rahma, saɓanin kaje gaban ALLAH da hakkinta akanka.
• Da yawan maza yanzu basu da lafiya, zaka ga mutum ga tarin dukiya, ga kayan abinci ga komai, amma bai iya komai ba a yayin kwaciyar aure, wannan wane irin namiji ne.
• Yaku iyaye muna kira gareku kuji tsoron ALLAH kafin ku aurar da ‘Æ´a’yanku kuyi Æ™oÆ™ari kusan lafiyar wanda zaku bawa ‘Æ´a’Æ´anku,
• Wajibi ne a tambayi lafiyarsa shin kanada lafiyar da zaka iya gamsar da ita, ko babu, wannan wajibi ne.
• Idan kuwa ba haka ba, to kada ku haɗa auransu, domin duku, dashi, da ita zaku iya rasa aljannah a dalilin auran, zaije yayita zaluntarta, ita kuma zataje tayita saɓawa ALLAH kuma duk ɓarnar datayi kuma zakuyi tarayya ne acikin zunubin.
ALLAH duk waÉ—anda suke cikin irin wannan masiba ka kawo musu É—auki, ka bawa mazansu lafiya cike da adalci da tausayawa.
ALLAH duk wanda suke fama da matsala ta ciyarwa da ababen jin daÉ—in rayuwa ka taimakesu ka yaye musu ka yalwata musu.
ALLAH ka tabbatar da zaman lafiya da Æ™aunar juna a tsakanin ma’aurata daga cikin mu.
ALLAH ka kawar da dukbwata fitina dake kai kawo a tsakaninsu baki É—aya,
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.