Hakurina Ya Kare Hausa Novel Complete

Hakurina Ya Kare Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

HAK’URI NA YA K’ARE

 

 

writting by

 

*MARYAM BINT ABDURRAZAK SALIS (Oum Mashkur)*

 

Marubiciyar

*suhailat* free book

*ba a san maci tuwo ba…* sai miya ta k’are paid book 300

*rud’in shed’an* had’in gwiwa free book

 

And now

HAK’URI NA YAK’ARE

Gajeren labari free book

 

 

*ABIN LURA*👇

*Labarin ya faru a gaske hakazalika wacce abin ya faru a kanta tana buk’atar kulawar ku wajen bata shawarwari sannan tana cikin cikin dukkan groups d’ina na book idan kuka bata shawara zaku samu lada.*

 

*TSOKACI*

*An canza sunaye da kuma garuruwan da abin ya faru saboda tsaro*

Hakurina Ya Kare Hausa Novel Complete

 

 

*True life storie*

 

 

Labarin kaso 97% gaskiya ne ubangiji ya bamu ikon amfani da abinda labarin ya k’unsa.

 

 

Ina godiya ga Allah mad’aukakin sarki da ya bani ikon rubuta wannan gajeran labari, wanda labari ne na gsky ina ptn zamu amfana da abinda muka karanta.🙏

 

 

 

Page 1&2

 

Kamar yanda kowanne bawa da akwai k’addarar sa da Allah ya k’addara masa me dad’i ko akasin haka, Zahra yarinyar mace me kimanin shekara 28 ta tsinci kanta cikin tsanani da k’uncin rayuwa sakamakon matsi da takura ta uwar miji.

 

 

Ta fara bani labarin ta ni *Oum Mashkur* kamar haka.

 

“Na kasance tun ina yarinya k’arama nake da buri da son in kasance jornalist, haka ma mahaifi na yana da burin nayi karatu me zurfi, babu laifi muna da rufin asirin mu dai-dai gwar-gwado gidan mu babu rashin ci da sha sutura da sauran abubuwan na rayuwa, ina da yayyu 2 maza Abdullahi da abdurrahman yayinda nake da k’anne 4 mata 2 ilham da ihsan maza biyu abdurra heem abdul maleek, mu 7 kenan har da ni zahra.

 

 

 

Rayuwar gidanmu me sauk’i ce,bama tsauwalawa kanmu kasancewar da haka aka tarbiyantar damu, baba na headmaster ne ya karanci 6angaren da ya shafi addini, hakan tasa muma yaransa ya fi bamu k’arfin ilimin addini, an sanya ni a Makaranta ina kimanin shekara 6 a duniya sosai nake karatu babu wasa na fara Makaranta tun daga raudha hak’ik’a Allah yayi min baiwar k’wak’k’walwa, wacce duk gidanmu har yanxu ba a samu Wanda ya fini ba, don a lokacin bazan ta6a manta wa ba nasha kyaututtuka a Makaranta kasancewar ana bada kyauta ga 123 ni kuma bana wuce wannan position d’in, muna aji hud’u muka sauke alk’urani me girma Wanda a wannan lokacin ina da shekara 11 ciff ni kad’ai ce y’ar mitsitsiya a cikin su hakan tasa ranar sauka aka dinga nuna ni ana d’aga ni, hotuna kuwa nasha su da malamai da manyan bak’i.

 

 

 

Saida nayi shekaru 7 a primary daga raudha zuwa aji 6 ba’a ta6a yi min demotion ba, lokacin mun zana jarabawar shiga k’aramar secondary kasancewar Makarantar tamu had’e take da boko don tuni na iya had’a hausa da tsirarun kalmomin turanci, na zauna wata 3 bana zuwa ko ina, kafin jarabawar mu ta fito daga baya, baba na ya nema min wata makatantar islamiyya a gain wacce a cikin na fara hadda, lokacin da results d’in mu ya fito, sai ya kasance secondary d’in Makarantar naci, aikuwa nace bana so don a lokacin mu a ganin mu ci baya ne kiyi primary kuma kiyi secondary duk a makaranta d’aya.

See also  Tsantsar Izza Hausa Novel

 

 

Makarantar gomnati aka samo min na fara zuwa js 1 babu laifi ina d’an ja saboda buri na na zama jornalist har yanxu yana nan, kullum zaka ganni da radio a kunne a gaskiya lokacin babu wayoyi sosai daga Nokia sai starcoms ds, haka duk girman radio zan rage volume na d’aure ta tamau da d’an kwalina ina aiki ina ji musamman ranar da babu makaranta, wuni zanyi da ita a kunne dukkan wasu gidajen radio da suke garin mu na gama sanin su, takai ta kawo hatta ma’aikatan da naji muryar mutum zan gane wanene, nasha fasa radion baban mu, har ya gaji ya siyo min y’ar k’arama kachibo aikuwa abin nema ya samu nan na k’ara dagewa da jin radio, haka zalika nasha yin bacci da radio a kunne na, sai dai mama tazo ta cire min radio da hijabi Wanda shima komai zafi dashi nake kwanciya tunda na fara fahimtar na fara girma.

 

 

 

 

Haka rayuwar dai ta cigaba da tafiya ina zuwa makaranta ta boko da islamiyya Wanda zuwa wannan lokacin na haddace izu 30 suratul kahfi, a k’a’idar makarantar idan kayi 30 zaka dawo ka gyara sannan ka d’ora, da yake Allah bai nufa na haddace qur’anin ba sai gashi tunda na dawo zan gyara 30 d’in na sanya shiririta a karatun nawa, Wanda shine musabbabin kasa k’arasa haddar tawa Wanda kuma nayi nadama akan hakan.

 

 

Bayan an bamu certificate na gama makaranta na samu wata islamiyya a layinmu na fara koyarwa a lokacin albashi na 500 ne, kuma da yake a wancan lokacin da d’an sauk’in rayuwa ina abubuwa masu yawa da kud’in albashin na d’auke ma iyaye na kud’in break da kuma na kayan kwalliya ds.

 

Na fara zama budurwa don lokacin shekaru na 15 kuma tun a lokacin na fara samari sai dai babu Wanda na ta6a bawa damar zuwa gidan mu sai mutum d’aya shima sau d’aya yazo daga wannan lokacin kuma ban k’ara yadda na kawo wani ba har saida Allah ya kawo min Wanda na aura hakan ce tasa ni ban yi wata soyayya da yawa ba.

 

 

 

Wata ranar week end ina gida wankin uniform d’ina nake yi kamar koda yaushe na mak’ala y’ar k’aramar radio na a kunne, na d’aure ta tamau da d’an kwalina, mama tana d’aki yayinda muke ta faman shirme ni da k’anwata ilham wacce ita ke bi na tare muke wankin da ita sai wasa muke yi da ruwan wankin.

 

 

 

Sallama muka ji anyi wata mata ce, kusan y’ar uwa mama ta d’auke ta saboda kasancewar garinsu d’aya ne, bayan ta shigo muka gaida ita sai wani bina take da kallo Wanda hakan tasa naji duk na tsargu, mama ce ta fito tana mata maraba kafin su wuce d’aki, tunda tazo na tsinci kaina cikin kasala da sanyin jiki ga kuma yawan fad’uwa da gaba na yake yi, bamu saba zuwa d’aki ba musamman idan mama tayi bak’i amma ba don haka ba da na shiga don kuwa haka kawai na tsinci kaina da son jin abinda tazo dashi, ba yau ta saba zuwa gidan ba sai dai irin kallon da take bina dashi ya sanya ina ji a jiki na akwai dalili.

 

Ta d’an dad’e a gidan kafin ta fito, a lokacin tuni mun gama wankin na shiga kitchen zan d’ora abincin rana sai dai duk abinda nake jiki na a sanyaye yake, muryar mama naji tana k’walla min kira, k’irji na ya buga da k’arfi cikin sauri naje kiran da mama ke yi min, kallo na tayi ganin yanda duk na shigo a firgice kafin tayi murmushi tace.”samu guri ki zauna zuhra.”

See also  Budaddiyar Soyayya Hausa Novels Complete

 

Ba tare da nace komai ba na zauna ina kallonta, “kin san abinda ya kawo lami?” Ta fad’a itama tana kallo na, girgiza kaina nayi, mama tace.”Wai tabawa ce ta aiko ta akan suna so anemi izni wajen baban ku, saboda d’an tabawa mujahid zaizo ya ganki ai kin sanshi ko?”

 

 

Shiru nayi ina tunanin waye ma mujaheed a gidan tabawa tabbas na sanshi sai dai na manta kamannin shi kasancewar koda aike na gidan su akayi bana ganin sa saboda bai cika zama a gida ba, sai dai nasan k’anin sa kamal saboda ajin mu d’aya a islamiyyar da na fara hadda shi kam ya haddace ma, ganin nayi shiru mama tace. “Ko baki gane shi ba” Na d’an gyara zama sannan nace. “Na sanshi mama amma yanxu bazan gane shi ba.”

 

“Shikenan bari babanku yazo idan ya amince sai yazo ku sasanta junanku.” Mama ta fad’a lokacin da take mik’ewa tsaye, binta nayi da kallo cikin zuciya ta ina wani tunani, koda baba yazo aka sanar dashi sam bai k’i ba kasancewar yasan iyayen sa ba wani dogon bincike za’a yi ba, hasali ma sun had’a gari d’aya hakan tasa muke ganin su tamkar y’an uwan mu, don haka aka sanar da mama lami kamar yanda muke kiranta, cewa an bashi izinin zuwa ya ganni, ranar juma’a kuwa sai ga mujahid, ban san wani irin yanayi nake ciki ba farinciki ko akasin haka, kwalliya nayi sannan na fita muka zauna a reeler mujahid ba fari bane bak’i ne sai dai yana da kyansa dai-dai gwar-gwado ba shi da tsayi sosai sannan bai cika gajarta ba, to a ranar da ya fara zuwa waje na ya bani dama akan naje nayi tunani akansa inda yace nayi masa amma yakamata nima na fad’i ra’ayi na akansa ya bani kwana biyu, da haka muka rabu koda na koma gida mama ta fara tanbaya ta yanda muka yi dashi ban 6oye mata komai ba na fad’a mata kasancewar mama tana jan yaranta a jiki itace abokiyar shawarar mu mazan mu da matan mu, kallo na tayi kafin tace. “Amma ke zuhra ya kike ji a ranki game dashi?”

 

 

Cikin jin kunya nace.”idan kun amince dashi mama nima na yadda. ” murmushi mama tayi sannan tace. “Shikenan zuhra ubangiji ya za6a miki abinda yafi alkhairi.”

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
A cikin raina na amsa sannan na mik’e, a gaskiya a lokacin babu son mujahid ko kad’an a raina kawai dai ganin iyaye na sun kar6i maganar da hannu biyu ne don ni har lokacin ban san soyayya ba saboda kwata-kwata shekaru na 16 ne, haka dai muka cigaba da kasancewa da mujahid tsawon shekara d’aya a lokacin tuni an kawo kud’i 15k na gani ina so, a hankali sabo me k’arfi ya shiga tsakanin mu dukda kasancewar sa k’aton miskili sam bai ya iya bud’e baki ya fad’a maka yanda yake jin ka a ransa, kullum idan yazo zance rabin hirar sa wa’azi ne, ni kuma Allah ya sani ni ma’abociyar soyayya ce ina so a yabe ni koda yake bani kad’ai bace dukkan mace tana son hakan koda k’arya aka yi bata kai yanda aka fad’a ba tana jinta tamkar sarauniya, ni kam na rasa wannan tun kafin auren ma, koda kalmar i love you bata ta6a had’a ni dashi ba, nima kuma nauyin fad’a masa hakan nake yi.

See also  Sanadin Besty Hausa Novel Complete

 

Wata 4 da kawo kud’i aka kawo akwatin sa rana irin wannan me nombobin wacce ake saitawa ta dafaffiyar roba, guda d’aya ce aka ciko ta da kaya, daga gidan mu ma ansha hidima da bak’i abubuwa kala-kala akayi har da su kaji, shekara guda suka sanya, tunda ga wannan lokacin mafarki na na zama jornalist rushe don kwata-kwata a lokacin ne muka shiga ss1, kenan ma ko candy bazan yi ba za’a yi auren, wannan dalilin ne yasa da yazo nayi masa complain akan a k’ara lokacin bikin don in samu ko candy ne inyi, k’iri-k’iri ya nuna bazai iya bari a k’ara ba sai dai yayi min alk’awari koda bayan auren ne zanje na zana jarabawar colapaing da neco da wa ec Wanda hakan ne zai sa a bani takaddu na, jin haka yasa na amince na bar maganar a k’ara biki, yau da gobe sai Allah a kwana a tashi har lokaci yayi, an kawo lefe aka sanya sati 2 cikin ikon Allah sai ga lokaci yayi, haka aka d’aura min aure da mujahid ina da 18 years, dama ya sanar dani a gidan su zamu zauna nasha kuka kafin a tafi dani gidan miji na, mama na da baba dukka sai da nemi yafiyar su hatta yayye na da kuma k’anne na, k’anwata ilham haka itama ta dinga kuka dukda tarin k’uruciyar da take dashi hakan bai hana ta kukan rabuwa dani ba.

 

 

 

Sam babu nisa tsakanin gidan mu da gidan su mujahid amma duk da haka saida aka kawo motocin d’aukar amarya ina kuka aka tafi dani, koda muka je gidan k’anwar mama aunty suwaiba, ta rad’a min in shiga da bismillah ba tare da musu ba nayi yanda tace, saida aka kaini d’akin suruka ta goggo tabawa tayi mana addu’a da ptn alkhairi sannan aka wuce dani d’aki na Wanda shine k’arshe a gidan parlor and bedroom ne d’akin da bathroom na wanka a ciki, bayan kowa ya watse aka barni da y’an k’awaye na, saiga angwaye kamar yanda yake a al’ada haka suka danyi barkwanci kafin suyi mana addu’a suka tafi.

 

 

 

Gidan su mujahid suma ba wani kud’i ne dasu ba rufin asirin Allah ne, baban su birkila ne wato magini, yayinda ahima mujahid abinda yake yi kenan, washe gari da safe kasancewar abokan sa sun yi masa kara, kayan shayi me yawa suka had’a masa harda k’wai da indomee hakan tasa ya had’a mana tea muka sha daga nan ya fita da kaina na fita na gaida suruka ta da sauran bakin da basu tafi ba, tunda na dawo d’aki ban k’ara fita ba har y’an uwa na suka zo sune suka d’an ebe min kewa, da rana aka aiko wai na bada kwanuka a zuba min abinci na d’auki food flaks me kyau na bayar sai ga wata irin dafaduka ni dai tunda nake ban ta6a ganin jaloup haka ba don dai ko a idon baza ta baka sha’awa ba balle kayi k’ok’arin kaita bakin ka fara ce tas sai tsalli-tsallin attaruhu da albasa babu alamar an sanya mai a cikin ta ma, ni dai kasa cinta nayi sai yara na bawa wad’anda suka zo, ni kam ko yunwar ma ba ji nake ba haka y’an uwa na suka gama yi min y’an gyare-gyare sannan sukayi min sallama suka tafi.

 

 

 

Da daddare ma aka k’ara cewa na bada kwanuka a zuba mana abinci na bayar sai dai me ina bud’a flask naga tuwon masara miyar kuka, sosai nayi mamakin wannan al’amarin a matsayi na na sabuwar amarya me matsayin kwana d’aya yakamata in d’an samu canji a nawa tunanin kenan….

 

 

 

To masu karanta wannan labari kun dai ji amarya me kwana d’aya aka had’a da tuwo a rayuwa ta birni.

 

 

 

Oum Mashkur



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

​

 

 

Name: [Hakurina Ya Kare Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top