Sirrin Rike Miji

Hanyoyin da zaki cusawa mijinki kaunar ki

Hanyoyin da zaki cusawa mijinki kaunar ki

 

 

 

 

Daga Yusuf Shuaibu

Kasancewa sau dari mafi yawancin mata ba san irin hanyoyin da za su bi ba wajen cusa wa miji kaunarsu a cikin zuciya.

To akwai hanyoyi da dama wadanda suka hada da kissa da kuma kisisinan da mace za ta iya amfani da su domin ganin ta cusa wa mijinta kaunarta a zuciyarsa.

Irin wadannan dabaru ba wani wuya ko wahala suka da shi ba wajen gudanar.

Sai dai mata da dama ba sa iya aiwatar da irin wadannan dabaru. Ga wasu dabaru kadan na yadda za ki jawo soyaya da kaunan mijinki a cikin zuciyarsa cikin sauki.

Karanta Hakkokin mace akan mijin ta

Wanka tare: Ba duk mata suka kasancewa suna yin wanka tare da miji, hakan kuma yana kara dankon soayya ba.

Ko da kuwa ke ba za ki yi ba, to ki yi kokarin ganin kin cuda shi sannan kin wanken shi kamin shi ya daureye kansa. Wannan salon dabaran mallakar miji yana da tasiri matuka ga duk macen da za ta saba yi wa mijinta hakan za ta sami soyayyarsa cikin sauki.

Girki na musamman: Ki kasance kana iya wa namiji girki na musamman da kika san yana so, shi ma wani salo ne na mallakar miji cikin sauki.

Kada ki ji kyashin kashe abun da ya fi abin da ya baki na hada wannan abinci. Duk macen da za ta yi amfani da wannan dabaran na girki, to za ta cusa wa mijinta kaunarta cikin sauki, domin babu wani namijin da bai sha’awar a yi masa girki na musamman a cikin gidansa.

Cin abinci tare: Cin abinci tare da mijinki shi ma wani salo ne na mallakar miji. Ko da miji yana cin abinci da abokai ko ‘yan’uwa, ki rika samun wani abinci ko kayan kwalama na musamman da za ki rika ba shi a lokacin da kuke ku biyu ku ci tare.

Gaisuwa cikin ladabi: Ki kasance mace mai gaida mijinta cikin ladabi duk safiya idan kun tashi.

Haka kuma ki zama mai masa maraba cikin kauna idan ya dawo daga aiki. Ki kasance mai masa fatan alkairi a lokacin da zai fita nema ko aiki.

Ka da ki zama mai mita: Yawan mita ga miji nan take kike fita daga zuciyar namiji. Ki zama mace mai barin magana nan inda aka yi ta ba tare da kin ci gaba da mita ba a kan abun da ya wuce.

Kada ki zama mai zafin kishi: Wasu matan na dauka cewan idan suka nuna wa namiji zafin kishi zai sa ya sota, sam ba haka ba ne.

Mata masu zafin kishi akasarinsu suna rasa aurensu saboda wannan kishin nasu.

Ki zama mai nuna kishinki dai-dai bakin gwargwadon da shi miji zai rika gudun yin duk wani abun da zai saki kishi. Amma idan kin zama mai zafin kishi a kullum, za ki rika samun matsala da mijinki. Yadda hakan zai sa ki kasa samun soyayarsa kamar yadda ya kamata.

Babu ruwanki da duba wayarsa: Mata da dama sun rasa mazansu saboda mugun halinsu na binciken wayar mazajensu.

Rashin daukar wayar miji wani dabara ne na mallakar mijinki cikin sauki, amma ba dukannin mata suka san wannan sirrin ba.

Ki yi kokarin wajen gamsar da miji, ka da ki gaza wajen gamsar da mijinki a duk lokacin da yake bukatarki.

Gamsar da miji na sa shi ya kasance yana matukar son matarsa yana kuma fata da burin ganin ya yi rayuwarsa da ita.

Wadannan wasu ne daga cikin dabarun cusa wa miji soyayya cikin sauki ba tare da wahala ba.

Ya kamata mata ku rungumi wadannan abubuwa ba sai kun tafi wajen boka ba ko malami kafin ki iya mallakar miji.

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!